Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Duk da bata da tabbacin musuluncin matasa lafiyanta amma hakan baya hanata yin sallama a duk inda ta shiga,yanzun ma sallamarta ita taja hankalinsu,anyi katari dukkaninsu musulmai ne,don haka suka amsa mata,ta qaraso dakin hannayenta zube cikin aljihun labcoat dinta,idanunta saman fuskar yarinyar tana qare mata kallo,a haka ta iso gaban gadon tana ci gaba da nazarin kyakkyawar fuskar yarinyar.


"Kinga momy na....zatayi miki allura idan baki qarasa cinyewa ba....kuma ma na fasa qawancen dake idan bakici ba" cewar amatu tana karyar da wuya,da alamu ta damu sosai yarinyar taci abincin,kallon amatu bilkisu tayi,kafin ta maida dubanta ga nurse din dake tsaye bayanta kadan da farantan tana tambayarta meke faruwa
"Tunda suka zo taqi cin komai" hannu ta miqa mata
"Bani" ta amshi kwanukan,duk da cewa ba aikinta bane sai taja kujera ta zauna gaban gadon,cikin lokaci kadan abun mamaki yarinyar ta saki jiki da ita harta cinye abincin,abun daya bawa mutanen dakin mamaki,har amatu da bakinta ya kasa shuru,murna ta cikata na ganin yadda ta cinye abincin duka,itama matar dake zaune a can gefe wanda alamu ke nuna tare suka zo,ita ke jinyarta tace
"Lallai likita kinzo da farinjini,Allah ya qara basira" ta fada da harshen hausa,ba tare da tana da tabbacin bilkisun naji ba,don tunda ta shigo da yaran turanci dukkaninsu suke magana,sai data amsa mata da amin sannan tasan tana jin hausar,hakan kuwa yadan bata mamaki,don ta zaci wani jinsin yaren ce daban ba bahaushiya ba,duba da yanayin kalar fatarta na daban,da kuma qira takyau da Allah ya bata.


"Wanne likita ne yasoma dubata?" Bilkisu ta tambaya tana daukan file guda biyu na yarinyar dake gaban gadon,wanda ke dauke da qunshin dukkanin bayanan ciwon nata,daga dukkan asibitocin da suka taba dubata,nurse din ta bata sunan likitan,saita soma buda file din tana karanta kowanne rubutu dake jikin kowacce takarda tana daga tsaye.


Yanayin yadda taga bayanan ciwon yayi tasiri jikin yarinyar ya bata mamaki qwarai,jikinta yayi sanyi,don da alama ya tabata da yawa,saita soma laluben kujera,tana zama kai lokaci daya tana daga kanta ta dubi amatu data damesu da karadi,ta sanya patient din itama bakinta ya bude ta biye mata sunata zuba surutu,cikin harshen turanci ta mata umarni ta rage sautinta ta barta ta duba file din hannunta,da alama itama yarinyar tana ji,don sai taga itama ta qara nutsuwa ta rage hayaniya,bilkisu ta bita da kallo,tana mamakin yadda ta saki jiki sosai da amatu,kamar sun jima da sabawa,sai taji dadi,don haka zai taimaka wajen warkewa da sake gano wasu abubuwan dake damunta da suka gaza ganowa.


A qalla ta dauki mintuna ashirin kyawawa tana bitar files din kafin ta rufe tana sakin nannauyar ajiyar zuciya,a zahirin gaskiya tabata don yi mata aiki yanzu akwai babban hadari,tana da buqatar treatment sosai kafin akai ga batun aiki,don haka ta dubi matar
"Ina iyayenta?" Ta tambayeta tana kafeta da idanu
"Basu qaraso ba tukunna" cikin mamaki ta maimaita
"Basu qaraso ba kaman yaya?,kina nufin basu qasarma gaba daya?,ba tare kuka zo dasu ba?" Kai ta jinjina mata
"Mamarta dai na hanya,cikin satin xata iso"
"Tana hanya?" Ta maimaita tambayar cike da mamaki,wannan wanne irin careless ne?,wadanne irin iyaye ne haka?,yarsu ta cikinsu amma a rasa mai tattaki ya dafa mata baya neman magani?,saita maida dubanta ga yarinyar,take taji tausayinta mai girma ya kamata,verry innocent,bata san damuwa da matsalolin rayuwa ba banda wannan ciwon daya shigeta,hira take sosai da amatu kamar wadda suka jima ko suka saba,tana ta qyaqyata dariya,har hakan yaso baiwa ita kanta matar mamaki.


Dauke kanta bilkisu tayi tana jin wani abu bayan tausayi game da yarinyar me kama da qauna,ta kira dukka nurses din da tasan suna da alhaki wajen kula da yarinyar ta gana dasu,ta nuna musu duk abinda ya kamata ace sun sani,bata bar dakin ba sai da ta soma bata kulawa,tanayi tana jan yarinyar itama da wasa kamar yadda taga amatun tanayi,ta sake mata sosai kuwa itama kamar yadda ta sake da amatu.


Saida sukazo tafiya ta tubure saidai su tafi tare,matar tayi lallashin duniya amma ta kafe,hakanan bilkisu ta dinga qoqarin mata dabara nan ma taqi,itama amatun ranta a bace da alama batason su tafi,daga qarshe dole bilkisun taja kujera ta zauna,sukaci gaba da wasa har sanda bacci ya dauketa sannan suka samu damar tafiya,matar nata yiwa bilkisu godiya kan yadda ta nuna tsantsar kulawa da qauna.


Ko a hanya hirarta amatun ta dinga mata kamar tasanta,bilkisun na jinta,yayin data lula duniyar tunani,tausayin yarinyar da qaunarta take sosai,da alama bata rasa dukkan gata ba,saidai kamar ta rasa kulawa musamman ta uwa,duba da yadda taketa qanqame bilkisun tana kiranta da sunan momy,har suka je gida zancan amatu kenan,haka ta zauna tayita bawa su abdulrahman labarin.


A daren kasa bacci bilkisu tayi,tanata tunani tare da laluben hanyoyin da zasu bullowa ciwon bayan ta gama amsar treatment na sati guda kamar yadda ta tsara ko sati biyu,bata samu ta runtsa ba sai can tsakiyar dare.


Hakan ya saka washegari koda ta shirya fita aiki idanunta akwai bacci a ciki bai wani isheta ba,saiga amatu itama ta farka tangaran sanda take fitowa daga wanka,tana mutstsuka idanunta tana kallon mamin nata
"Mami....." Saita langabe kai,bilkisu tadan bata rai
"Meye?"
"Mami yauma don Allah" sake bata fuska tayi
"Ba inda zakije,ki zauna a gida hakanan" daga haka taci gaba da shiryawarta,bata ankara ba taji ta sakar mata kuka,ita suhaima takeson zuwa ta gani,saita saki baki galala tana kallonta,sannan ta soma fada
"Wanne irin sakarcin banza ne da wofi wannan amatu?,da can dake nake zuwa?,kodon kinga kun samu hutu shine zaki tsiri bina?" Daidai lokacin da ummi zuhriyya tayi knocking qofar dakin ta shigo
"Yaya....yaya,waye ya tabamin mutuniyata?" Dauke kai bilkisu tayi daga wajen amatun tagayawa anty zuhriyya abinda ke faruwar
"Yaushe rabon da su biki banda abinki,shirya qawata kuje kinji" tsalle ta daka ta shige bandaki,ta samu abinda takeso,dama already ta iya wanka abinta sosai,murmushi anty zuhriyya tayi tana duban bikisu
"Da tayi zuwa uku zata gaji da kanta,yanzun ma rashin sabo ne"
"Ummi kawai dai kina daure mata qarqashine saboda 'yar gaban goshinki ce bata laifi,idan hakane shima abdulrahman yace zashi mana" baki ta kyabe
"Ke rabani da wannan sarkin miskilancin tsiyar,duk randa yaji zashin ya magantu da bakinsa,amma nidai tunda yarinyata nason zuwa banga abinda xaisa a hanata zuwan ba" murmushi bilkisu tayi,bata da sauran ta cewa,daga haka suka shiga maganar data shigo da ita.


Bata lura amatu ta debo tarin choculets ba da sauran tarkacen su biscuit saida sukayi nisa,ta dubeta
"Wannan fa?"
"Suhaima zan kaiwa....Allah sarki tana ta cewa daddynta takeson gani,tafi sonshi,shi yake siya mata ya bude mata tasha" shuru bilkisun tayi,har yanzu tana mamakin abinda zai hana iyaye kasancewa da diyarsu,anya ma kuwa iyayenta basu rasu ba?,ba riqonta ake ba?,gaskiya tafi tunanin hakan,tausayin suhaiman ya sake shiga ranta sosai da raya hakan da tayi.


Cikin kwana biyu rak suka wani irin sabawa da amatun,kullum da safe kafin bilkisun ta tashi ma ita ta rigata tashi ta shirya ta zauna tana jiranta,tun tana dojewa ba zata je da ita ba harta haqura ta qyaleta,saiga abdulrahman shima yabi sahun 'yan zuwa asibiti.


Ranar farko da yaje zama yayi abinshi daga nesa yanata kallonsu,kasancewarsa miskili bamai son surutu ba,duk hirar da suke nashi ido,gadon ya zama kamar wajen jinyar suhaima ne da amatu bawai na suhaima kadai ba,kwana biyar amma kamar sun shekara tare,har ya zamana bilkisun kan qara lokacin tashinta akan lokacin tashinta daga aiki na ainihi,john har tsokanarta yakanyi,yakance patient din da ake jama rai yanzu ta zama best a cikin patients dinki madam,dariya kawai takanyi,itama batasan ya akayi yarinyar ta shiga ranta ba,wala'alla sabon daya shiga tsakaninsu ne da yaranta ya jawo hakan.


****** ***** ******


Tsaye yake gaban ammin yana fuskantarta,sanye cikin wasu hadaddun suit masu bala'in kyau da tsada,wanda suka sake fidda kyakkyawar sura da cikar zatin da Allah ya huwace masa
"Zan wuce ammi,hankalina ya gaza kwanciya,gwara na wuce kawai,sodangin ta biyo ni zuwa jibi" sosai take sake danne bacin ranta kan lamarin safwa,ta fuskanci kwata kwata batasan abinda ya kamata ba,don gaba gadi taketa harkokinta kamar ba wani abu tayi ba,ko jiya da fulanin ta kira mom su gaisa ko hakan zai zame musu tuni game da suhaima safwan harda amsar wayar su gaisa tana sakalcin nan nata,ko cewa akayi kasancewarka d'a guda wajen iyayenka hauka ne?,ita kuma mom din harda cewa
"Wallahi kin ganni inata fama da ita ta tafi,wai sai zuwaira ta dawo su tafi tare,ita batasan ya ake treating mara lpy ba,sai aukin kiran yarinyar a waya ta mata hira,na rasa wanne irin sakarci ne ke damun safwa haka" takaici ya hana fulani cewa komai,sai kawai tace
"Allah ya kyauta".


"Jibin zamu taho tare ne in sha Allah,kayi mata sannu da kyau kafin mu iso" daga haka sukayi sallama ya fito.


Sassan mai martaba aka masa iso,ya sameshi zaune tare da wasu hakimai,wanda da alama sun gama tattaunawar data hadasu a wajen,don wasu har sun miqe ma,cikin girmamawa ya isa gabansu ya duqa ya gaidasu,kowanne ya amsa cikin jin dadi da kulawa,saida suka fice sa'annan mai martaba ya maida hankalinsa kan azeez,yadan zuba mishi idanu yana kallonshi,shi kansa yadda yakanga sauyi tattare da dan nashi yana sashi a tunani,amma sai yake zaton girma ne da kuma tsabar kasuwanci babu hutu daya sanya a gabanshi
"Dan kasuwa" maimartaba ya dan tsokaneshi,Kasancewarsa mutum mai barkwanci ga jama'a,murmushi ua danyi yana dan saukar da kanshi qasa,yana qaunar maimartana qwarai kamar yadda yake qaunar amminsa,saidai akwai banbamcin halaye,wani sassauqan mutum mai sauqin hali da ra'ayi,mai saurin fahimta da bada uzuri,wanda bai dauki rayuwa da girma ko fadi ba
"Allah ya qara maka lafiya da nisan kwana" ya amsa mishi cikin ladabi
"Lafiyar dai amin,amma nisan kwana iya abinda muka hadiyo shi zamuyi mu kauce muba wasu waje" ya amsa mishi kamar yadda yakan amsa mishin lokaci lokaci,kai azeez ya gyada kawai sannan yace
"Zan wuce wajen amaryarka brasil" fuskar mai martaba ta sauya
"Idanu dama kawai na zuba maka kaida uwarta ku gama dukka sakarcinku,da ita kanta aishan data zuba muku idanu,bansan rashin hankalin da kuka tafka ba sai a jiya" nan yahau mishi fadan barin suhaima da masu kula da ita kawai zuwa neman lafiya,fada ya dinga yi sosai,kamar yadda ya yuwa fulanin a jiya iya son ranshi,mutum ne shi mai son jikokinsa da basu kulawa,don haka azeez baiyi mamaki ba,yasan zaiyi fiye da hakan ma,ko baya ga haka ma ya tsani yaga an sarayar da haqqin wani ko wanene shi,kanshi a qasa ya bashi haquri sosai,sa'annan yayi masa sallama,bai barshi ya fita ba sai daya shiga ciki da kanshi,ya bada saqon kilishi mai yawa yace akaiwa amaryarsa,yasan yarinyar tana sonshi.


Sosai ya shiga zurfin tunani a mota,wannan karon yanajin indai safwa ba zata iya zama jarumar uwa kamar kowacce uwa ba,to ba shakka zaya dauke suhaima ne ya dinga tafiya da ita duk inda zashi,ko kuma ya karbi sodangi taci gaba da zama da ita a madadin uwarta tunda ita batasan meye ma'anar sunan uwa ba.


Ya saki ajiyar zuciya mai nauyi yana ambaton sunan Allah sanda jirginsu ya daga daga qasa zuwa sararin subhana,hakanan yakejin wasu baqin abubuwa cikin gangar jikinsa da zuciyarsa,wala'alla doki dason ganin diyar tasa ne ya sanya haka,ya sake sakin ajiyar zuciya yana lumshe idanu,qaguwarsa dason ganin ya sauka a qasar brasil na sake daduwa,ya shiga irgen awanni ko mintunan da zasu sadashi da qasar.



*to me karatu?,shin ya zata kaya ne?,ku biyoni muje zuwa*ðŸƒðŸ¾â€â™€ï¸ðŸƒðŸ¾â€â™€ï¸ðŸƒðŸ¾â€â™€ï¸ðŸƒðŸ¾â€â™€ï¸âœˆï¸âœˆï¸âœˆï¸âœˆï¸âœˆï¸âœˆï¸âœˆï¸âœˆï¸âœˆï¸
7/11/21, 4:34 PM - My Mtn Number: 52

*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*

*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*

*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*
_____________________________

*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*
0903 234 5899
Ko
09033181070


Duk wani nau'in abinda yasan suhaiman tana so sai daya siya mata kafin ya qarasa asibitin,a sannan babu kowa cikin dakin,daga ita sai mama rahama,wadda keta faman lallashinta kan ta karbi abinci taci,fir taqi yarda taci din,sai fushi da take,ta hade fuskarta tsam,sakamakon rashin zuwansu amatu yau asibitin gaba daya,wanda hakan ya faru ne saboda ba ranar aikin bilkisu bane,ranar hutu ne.


Ƙofar sukaji an turo,sannan lallausar muryarsa da yawancin lokutta take cike da sanyi da taushi tayi sallama cikin dakin,ya shigo idanunshi na akan suhaiman.


Kallo daya zakayi mata ya gaya maka zallar farincikin da tayi da ganin mahaifin nata,badon qarin ruwa dake hannunta ba,badon kuma riqeta da mama rahama tayi ba da tuni ta diro daga saman gadon zuwa wajenshi,hakan daya fuskanta shima saiya qara azama ya qaraso gareta,ya rungumeta tsam a jikinsa yana jin tausayinta,saidai kuma yaji dadi a yanayin daya ganta,wanda ya nuna mishi tana sakun kulawa dai dai gwargwado,don gashinan ta soma murmurewa,akwai alamun raguwar ciwon tattare da ita.


Sai da suka gama daukin ganin juna,ya baje mata dukkan wani abu da za'a iya ci saman gadon tahau hidimarta sannan mama rahama data koma can sashe daya na dakin ta zauna ta gaisheshi cikin ladabi,ya amsa mata sa'annan ya soma mata tambayoyi game da yadda ake kula da suhaiman.


Amsar data bashi ta masa dadi sosai,sai yaji ya qara nutsuwa da asitin da kuma likitar kanta dake dubata,mama rahama tayi murmushi
"Yanzun ma fushi take saboda likitar batazo ba yau tana hutu,bataga amatu diyar matar ba qawarta,taqi taci abinci yallabai" waiwayawa yayi ya dubi suhaima,duk sai ta langwabe,ya miqa hannu ya amshi abincin wajen mama rahaman,ya dubi suhaima ya tsatssareta da idanu sa'an nan yace
"Oya.....gyara ki karbi abinci" babu musu ta aje duk abin hannunta ta tattara hankalinta ga abincin,ya diba ya soma bata a baki.


Daga bangaren bilkisu kuwa ranar ta tashi kamar sauran ranakun hutu a wajenta,takan sake a gida saboda tasan bata da aiki,hakanan ba kasafai ya fiya fita ba,to yau dinma hakane,sunata sabgoginsu da yaran.


Saidai babu jimawa nabila tayi kiranta,wanda kiran nata yasa dole ta fita kenan,mamarta bata jin dadi,tasan kuwa idan bata yakice taje cikin ranakun hutunta ba,ba zata samu fitar ba,don babu inda take sake fita yawanci idan ta dawo daga aiki to tana gida,a yadda suke da nabila kuma bai kamata ba,shaquwarsu tafi gaban hakan,don hakan,bayan ta gama duk wasu ayyukan gida da takewa ummi duk lokuttan da take free,saita shiga bandaki tayi wanka,kana ta tsaya gaban mudubinta tayi shiri mai kyau cikin kayan da duka amsheta matuqa,suka fidda ainihin gayunta da ya riga yabi jikinta ya zame mata jiki.


Tun tana shiryawa ta lura amatu ta kasa sukuni,sarai tasan meke damunta,so take tace zata bita,hakan yasanya ta hade ranta itama tsam babu wasa,harta gama shiryawa ta yiwa ummi sallama ta fice.


Ta samu jikin mamar nata da sauqi,ta zauna cikinsu suka taba hira,bata kashe awa daya ba ta yiwa nabilan sallama tace zata wuce,amma koda zuwa jibi idan ta tashi daga aiki zata sake biyowa taga jikin nata.


A hanya harta dauki hanyar gida sai kuma suhaima ta fado mata a rai,hakanan taji tana da sha'awar shiga asibitin kodan ta dubata koda ita kadai ce cikin marasa lafiyanta,don haka saita sauya alakar motarta zuwa asibitin,cikin zuciyarta tana addu'ar Allah yasa dr adam baya nan.


Tana tsaka da parking wayarta ta dauki ruri,number din assadiq ce,bata daga ba sai daga gama daidaita parking din nata sannan ta sanya hannu ta dauka tana dab da tsinkewa tana yin sallama.


Idanunsa ya lumshe,yana jin sautin muryarta har tsakiyar zuciyarsa kana ya budesu yana amsa mata sallamar
"Nayi miki zuwan ba zata,kuma saina daki gurbi bakyanan" cikin mamakin yadda akayi ya sami adress dinta tace
"Kana nufin gidanmu?" Kai ya gyada
"Yes,kina mamaki ne?"
kanta ta mirgina,murmushi na qwace mata,wani irin qwaqwqwafi ne da assadiq haka?,anya shi din ba lauya bane ko dan jarida ba?,kafin tace komai ya sake magana
"Ayimin afuwa,so nayi na mamayeki,sai kuma gashi hakan bai samu ba....akwai wani batu mai muhimmanci da nakeso mu tattauna ne akai,idan babu damuwa a sake bani lokaci sai nazo mu gana,amma alfarma nake nema,kar a lulani da yawa zuwa wasu kwanaki,kinga nidin matafiyine kuma baqo,akan hanya nake,kwanaki kadan suka ragemin na tattara nabar muku qasarku" murmushi ya sake kubce mata saboda yadda yayi maganar kamar me neman agaji,idan ba gobe ko jibi ba bata da wani isashen lokaci
"Qasarsu dai,mu tamu qasar nigeria take....babu damuwa,kana iya samuna jibi a gidan in sha Allahu"
"Godiya nake qwarai da gaske" daga haka sukayi sallama,ta kashe wayar tana fitowa daga motar,ta kulleta kana ta nufi ainihin cikin ginin asibitin,cikin takunta dake nuna zallar aji kamun kai da isa cikakkiyar mace.


Bata nufi office dinta ba don bata tunanin ma zata shiga tunda ba aiki ne ya kawota ba,kai tsaye ta doshi sashen da dakin da suhaiman take.


Hakanan taji wani mummunan faduwar gaba sanda ta dora hannunta saman qofar da niyyar budewa,sai tsaya cak tana mamakin yadda bugun zuciyarta ya qara gudu.


,taja numfashi sosai cikin hunhunta ta sauke nannuyar ajiyar zuciya,ta bude idanunta dake lumshe kana ta tura qofar dakin a hankali,tamkar barawon dake shirin shiga wani gida yin sata,inda bashi da buqatar a kamashi.


Kadan qofar ta budu,amma tana iya hango wani sashe daga dakin,a hankali ta soma zagayawa da idanunta cikin dakin,mama rahama dake zaune gefe daya idanunta ga bango,da alama plasma din dake kafe take aiki ta tattarawa hankalinta,sai suhaima dake zaune gefan gado ta zuro qafafunta qasa,tana tauna a hankali da alama batason cin duk abinda take ci din.


A hankali idanun nata suka sauka a kanshi,kyakkyawar fuskarshin nan babu yabi ba fallasa,ya tsare diyar tashi da kyawawan idanunshi masu cike da wani irin sirri da kwarjini na musamman,fuskarshi babu yabo ba fallasa,saidai ga duk wanda ya sanshi zai iya cewa a hakan a sake fuskarshi take.


Dubanshi tayi na sakanni biyar tak taji bugun zuciyarta ya sake dawowa,idan idanunta suna gane mata dai dai,wannan business tycon dinne wanda hotunansa da labarinsa ya zagaye ko wanne lungu da saqo na duniya,saidai a yau tana ganin abu mafi mamaki wanda bata taba kula dashi ba tsahon ganin da takewa hotunanshi.


Kamanni na zahiri muraran,kamannin yaranta 'yan biyunta saman fuskarshi,tamkar kaki yayi ya tofar,wani mugun bugun zuciya data ji fiye da wanda takeji ya sanyata sakin qofar ta koma da baya,ba tare data shirya ba ta tsinci kanta ta doshi qofar office dinta,ta bude kana ta shige zuwa ciki tana jinta cikin wani yanayi da bata tantance wanne iri bane.


"Wanne irin abu kike haka bilkisu?,me yake damunki haka?,daga ganin mutum saiki birkicen?,wala'alla ma babu wata kama da suke,idanuwanki ke nuna miki haka,meye hadinsu da zasuyi kama?" Kanta ta yiwa fada sosai,ita kanta sai taji haushin kanta da kanta,ta miqe ta tsaya gaban dan madaidaicin madubin dake office din ta gyara rollig dinta ya zauna sosai,kana ta dauki jakarta ta fice daga office din bayan ta rufeshi,ta sake durfafar dakin karo na biyu.


A hankali ta sake turawa kamar dazun,saidai a yanzu mama rahama ce kawai da suhaiman zaune,tayi sallama a nutse cikin sassanyar muryarta,cikin zumudi suhaima ke kallonta,bakinta har kunne
"Oyoyo momi...ina amatu na?" Murmushi tayi cikin tsantsar qarfin hali,saboda qamshin turaren da takeji cikin dakin,qamshine daya kama qwaqwalwa da zuciya gaba daya,qamshine daya zauna radama tunaninta tsahon shekaru bakwai,irin qamshin data sani jikin mutum daya,kuma tsahon shekarun bata sake jin qamshin jikin wani mutum na daban ba bayan shi,sai a yau daidai wannan lokacin,sa'an nan cikin dakin asibitin,wanda bata ha kowa a dakin ba face suhaima da mama rahama,don haka ta maida hankalinta kan suhaiman tana cire dukkan wani tunani daya bijiro mata.


Cikin kulawa take duddubata bayan ta tabbatar da cewa komai yana tafiya dai dai,daidai lokacin data gama dubatan ta saqala jakarta wayarta dake riqe a daya hannun nata ta dauki tsuwwa,data duba sai taga sunan anty zuhriyya,babu jinkiri ta daga,magana sukayi ta mintuna biyu sannan ta kashe ta dubi mama rahama
"Zan wuce mama,sai jibi idan Allah ya kaimu,an kirani daga gida ne nayi baqi"
"Babu komai likita,kedai sannunki da qoqari" qarasawa tayi gaban gadon suhaima,wadda tunda taga babu amatu,sannan bilkisun na maganar tafiya tayi kicin kicin,murmushi tayi tana shafa kanta
"Naso na dade kinji baby suhaima,amma jibi da wurwuri zanzo kinji"
"Amatu zatazo?" Sai ta danyi jim,batason mata alqawari kuma bata cika ba,to amma yarinyar ta damu dasu amatun da yawa,zatayi qoqari a kawosu,idan hakan bai samu ba jibi zata qoqarta taho mata da ita
"Idan na samu dama zaki gansu,idan ban samu ba kiyi haquri kinji diyata,jibi in sha Allahu xanzo miki da ita" saita gyada kai a sanyaye,har hakan yasa bilkisun taji babu dadi,yarinyar ta kafeta da ido tana ci gaba da kallonta,kana a hankali ta bude baki tace
"Kice to ina gaisheta" kaita jinjina tana fidda murmushin zallar wayo irin na suhaiman,kamarma wayonta yafi shekarunta yawa
"Zataji" ta sunkuya tayi kissing din goshinta.


Dai dai lokacin daya tura qofar toilet din ya fito,hannunsa riqe da handekherchief guda shida na suhaima daya tsaya wankewa tun dazun,wanda mama rahama tayi tayi ya bari ta wanke amma yace ta barshi zaiyi da kansa.


Yaga sanda aka gama kissing suhaima aka juya,yaga gefen fuskar matar saidai bai samu ganin fuskar gaba daya ba,wani mummunan faduwar gaba yaji ta ziyarceshi wanda baisan dalili ba,kamar wanda aka manne idanunshi a kanta haka ya zuba ma bayanta idanu saboda bashi da ikon ganin fuskarta,harta fice daga dakin cikin nutsatstsen takunta.


Hakanan cikin jikinsa yakejin kamar yasan halittar,kamar ya taba rayuwa da ita waje daya,kamar ya taba sanin wani abu nata.


Sam baisan ya bita da kallo ba,hakanan baisan yaci gaba da kallon hanyar data bi ta wuce ba duk data bacewa ganinsa ba,saida mama rahama tayi gyaran murya,wadda dukka nauyi ya cikata ganin yadda yakebin hanyar da kallo,hakanan suhaima nata masa magana amma sai baijin abinda take fada.


Sashen da mama rahama take ya kalla,kanta na duban qasa tace
"Itace likitar suhaima,itace wadda take magana akanta daxun ita da yaranta take fushi saboda rashin xuwansu" kai kawai ya gyada,sannan ya taka a hankali zuwa gefan gadon suhaima yazauna,yana jin wani mutuwar jiki da kasala,hakanan giftawarta ta kasa barin idanunsa,saiya sanya hannun suhaima cikin nashi yana dubanta,tare da tambayarta me take cewa?.


Washegarin bata samu kaisu ba,hakan ya sanya tayi aniyar tafiya da amatun gobe idan Allah ya kaimu.

***** ****** ****** *****


Tunda ta idar da sallar asuba take saman abun sallarta,hakanan baccin da takan samu ta koma ya qauracewa idanunta,sabanin daa da takan koma ta rintsa koda na minti talatinne zuwa awa daya kafin ta shirya,ya danganta da yanayin sammakon da zatayi,sabanin daa yau din ko kadan bata jin barcin,sai azabar mutuwar jiki gami da kasala da suka lullubeta,lokaci lokaci takanji fargaba da faduwar gaba,hakan ya sanyata ta qara yawa da tsahon azkar din da takanyi duk safiya.




Please Login or Register in order to submit comment