Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels

[10/25, 7:34 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️



RUBUTAWA DAGA
HAFSAT MAGAJI DABO(RUHAZ)





SADAUKARWA GA
MY DAUGHTER SABEEHA
BILKISU Z.YA'U (🅱️K)
AISHA MAGAJI DABO(AMA)






Page 1


Tana zaune a wani d'aki mai kyau na gaske riga da wando ne a jikin ta masu kyau black jeans ne sai white T-shirt kanta a sunkuye ta tallafe fuskar ta da duk hannayen ta sai zubar da hawaye take yi kamar an bud'e fanfo.


Kyakkyawa ce ta gaske doguwa brown skin ke gare ta Mai haske fatar ta har shek'i take yi ga idanun ta masu matuk'ar d'aukar hankali manya da su hancin ta har baka tare da wani irin lips red ga wata siririyar wushirya da ta k'awata tsakiyar kananan hak'oran ta gashin kanta ya zuba har gadon bayan ta na gaban goshin ta kuma ya kwanta luf a gefe da gefen fuskar ta kasancewar ba d'ankwali a kanta.


Sosai take hawaye ba k'akk'autawa har shesshek'a take yi.


Wasu 'yammata ne su biyu suka shiga d'akin suma sanye cikin irin shigar ta sak sai dai su da k'ananan veil a kansu.



Ganin 'yar uwar su na kuka da gudu suka k'arasa sai lokacin na lura ashe da su biyun da suka shiga da wacce ke kukan dukan su kamannin su d'aya kamar an tsaga kara danko babu bambamcin komai tsakanin su daga kamannin su har zuwa tsayin su.



Gefe da gefen ta suka zauna suka sata a tsakiya d'aya a cikin su cikin sassanyar muryar ta ta ce "Haba sabeeha meya faru kike kuka?" Ba tare da mai kukan ta amsa ba ta d'ayan gefen ta ce "Sabeeha sister fad'a mun duk d'an iskan da ya tab'a ki a gidan nan dan wallahi za a hau sama dani," har lokacin Sabeehan bata yi magana ba d'ayar ta Kuma cewa "Haba Sabreen karki kasance mai tayar da rigima mana kinsan dai duk neman maganar ki da tsokanar ki Sabeeha ta fiki amma kinga yau kuka take yi Kuma kinsan da na d'aukar mataki ne da tuni ta d'auka ba tare da mun saniba kamata ya yi mu tsaya muji damuwar ta," ta fad'a tana shirin fara kukan itama.



Wata ce ta tura k'ofar d'akin ta ce "Sameeha kizo yanzu inji yallab'ai," da sauri Sameeha ta tashi ta fice jikin ta na rawa.


Sabreen ta kalli sabeeha ta ce "Haba Sabeeha dear ki fad'a mun mana damuwar ki," sai lokacin Sabeeha ta kalli Sabreen da jajayen idanun ta ta ce "Sabreena wallahi gaba d'aya damuwata ta yanzu akan Sameeha ne ki duba fa abinda waccan wawan yake yi mata ina jin ciwon hakan bansan wanne mataki zan d'auka a kan shi ba ranar nan fa har d'akin nan yazo ya zane ta duk dan muna aiki a k'ark'ashin su ba wai yana nufin duk abinda suka ga dama su yi mana ba Kuma may be bayan hakan aikwai abubuwan da yake yi mata sai dai kinsan ta da zurfin ciki," Sabreen ta ce "gaskiya kam sister Nima na dad'e ina tunanin hakan Amma ko tambayar ta muka yi kinsan ba lallai ta fad'a mana," jinjina kai Sabeeha ta yi ta ce "Dear damuwata ta biyu bai wuce Abbba ba ki duba fa mun baro shi ba lafiya sannan shi kad'ai ne bamu san halin da yake ciki ba Sabreen dear nifa na yanke shawarar kawai gara mu tattara kayan mu mu gudu," zare ido Sabreen ta yi ta ce "me?mu gudu fa kika ce Sabeeha wato so kike muje d'in Kawu ya kashe mu d'in kamar yadda ya fad'a ko Kuma ya yi mana auren da ya ambata?" Tsaki Sabeeha ta ja ta ce "Nifa damuwata akan mahaifin mu ne ba akan Kawu ba," shiru Sabreen ta yi sannan ta ce "Nagane Amma mu bar maganar zuwa nan da kwana biyu kinji?" Gyad'a kai Sabeeha ta yi sannan ta ce "Yanzu dai muje mu ga wanne kira yake yiwa Sameeha," tashi suka yi Sabeeha ta d'auki veil d'in ta irin nasu ta yafa suka fice daga d'akin.



Babban falon gidan suka fita turus suka tsaya ganin Sameeha ta yi kneeling gaban yallab'ai Kamis Wanda suke wa aiki kuka sosai Sameeha take yi tana cewa "Yallab'ai Dan Allah kayi hak'uri bazan sake ba," shi Kuma yana zaune akan kujera ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya sai karkad'awa yake yi ga Kuma wata zabgegiyar dorina a hannun sa.



A zuciye Sabeeha ta yi niyyar yin wajen Sabreen ta yi saurin damk'e hannun ta tana girgiza mata kai tare da janye ta gefe.



Fisge hannun ta Sabeeha ta yi cikin masifa ta ce "Sabreen Wai haka zamu tsaya muna kallon kamis yana yi mana abun da duk ya ga dama yanzu Kuma me ta yi masa?" Cikin tsananin damuwa Sabreen ta ce "Wai fa matar sa ce ta aika waccan tsinanniyar Rashida d'in ta kira Sameeha shine baka gaya mata ba ta koma ta ce da matar yallab'ai wai ta ce baza ta zo ba shine fa d'azu ina cikin yin wanke wanke shine matar yallab'ai ta sameni ta k'are mun zagi Wai ta aika a kirani nace bazan zoba dan haka na shirya karb'an hukunci idan mijin ta ya dawo a tunanin ta Sameeha ce na so ni aka yiwa hukuncin Amma wacce d'azu ta je ta kira ta ganin mu mu ukun Kuma bazata iya gane mu ta ido ba shine kawai ta yi amfani da suna ta kira ta," jinjina kai Sabeeha ta yi ta ce "kinsan Allah sister tun daga kan waccan Rashidan zan fara har zuwa kan Farida sannan na dawo kan Kamis duk kafin na bar gidan nan saina nuna musu kuskuren su," saurin rufe bakin Sabeeha Sabreen ta yi ta ce "Sabeeha dear ki rufa mana asiri kar wani ya ji kinsan fa 'yan aikin gidan nan dukan su munafukai ne,"



Mtswww Sabeeha ta ja dogon tsaki ta ce "Ai ni zanso a fad'a musu ma yanzu fa tuhumar Sameeha ake yi akan laifin da bata san da shi ba kinga wallahi sai na je," tana gama fad'in haka ta juya da sauri Sabreen na Kiran ta amma ko waigawa bata yi ba.


Babban falon ta koma ta ganshi zagaye da 'yan aikin gidan maza da mata domin dama indai yallab'ai Kamis zai yi hukunci sai ya tara duk 'yan aikin gidan ya yi a gabansu saboda wasu su kiyaye.



Ba tare da tsoro ko wani d'ar ba Sabeeha ta nufi wajen gaba d'aya wajen da kallo aka bita har ta k'arasa gaban Yallab'ai itama ta yi kneeling kamar yadda Sameeha ta yi ta ce "Yallab'ai ba ita ce bace nice mai laifin ita ba tasan komai ba," kallon Sabeeha Sameeha ta yi ta girgiza kai ta ce "Wallahi ba ita bace nice," daga bayan su Sabreen ta ce "Yallab'ai dukan su k'arya suke yi nice nayi laifin," Nan fa wannan tace ita ce wannan tace ita ce.



Tsawa Yallab'ai ya yi musu tuni suka yi shiru cikin bud'add'iyar muryar sa ya ce "Karku ce zaku raina mun wayo dan kunga bana wa wanda bai yi laifi hukunci ba wacece mai laifi a cikin ku?" A tare suka ce "Ni ce Yallab'ai," tsaye ya mik'e rik'e da dorinar sa kamar ta dukan jakai yana kallon su.



Sannan ya kalli 'yan aikin gidan ya ce "Waye yake iya bambamce su?" Dukan su ba girgiza kai suka yi domin ba mai iya banbance su.


Saukowa Farida ta fara yi daga stairs tana nufo falon tasha bleaching ta k'oshi sai wani yanga take gaba d'aya 'yan aikin suka durk'usa dan girmamata kallon banza ta yi musu sannan ta zauna kan kujerar da Kamis ya tashi sannan ta kalli 'yan uku ta yatsina fuska tare da jan tsaki.



Sannan cikin muryar ta kamar ta mijin ta ta ce "Rashida," Rashida dake gefe ta matso gaba ta ce "na'am ranki ya dad'e,"


"Wacce na aike ki Kiran ta?" Kallon 'yan uku Rashida ta yi ta ga gaba d'aya kamannin su ba bambamci a zuciyar ta ta ce "ka ji banza ta ya zan iya gane su," a fili Kuma ta ce "Gaskiya ranki ya dad'e bansan wacce bace a cikin su," jinjina kai Farida ta yi sannan ta mai da kallon ta gun su Sabeeha ta ce "Ku dan uwar ku wacece Sameeha a cikin ku," da sauri Sabeeha ta ce "nice Ranki ya dad'e," Sameeha ta ce "k'arya take yi ni ce," Sabreen ta ce "ba haka bace Ni ce Sameeha," Tsaki Kamis ya ja ya ce "Duk ku tashi ku bar nan kafin naci uwar ku," da gudu su Sabeeha suka bar wajen.



Sannan ya mai da kallon sa kan ragowar 'yan aikin ai tun kafin ya yi magana kowa ya watse.


A zuciye Farida ta tashi zata bar wajen ya yi saurin rik'e hannun ta ya ce "Haba sarauniya ta ina Kuma zaki?" Banzan kallo ta yi masa "Meyasa baka had'a dukan su ka zane su ba?" Girgiza kai ya yi ya ce "Sanin kanki ne bana yiwa mara laifi hukun ci,"


"Amma ai kasan yaran nan ba yau suka saba yi mana irin haka ba muna kyale su ba dama d'aya ta yi laifi sai su taho dukan su su ce sune a rasa mai laifin a ciki to daga yau dukan su nake so a hukun ta," ya ce "An gama ranki ya dad'e ai sai abinda kika ce,"



Su Sabeeha kuwa suna barin wajen kowacce ta kama aikin ta Sabeeha ta nufi kitchen domin yiwa Kamis da Farida girki Sameeha Kuma ta tafi shara da mooping Sabreen Kuma wanke wanke.



Da daddare Sabeeha duk ta riga su gama aikin ta ta nufi d'akin su wanka ta yi tare da sallar isha sannan ta haye saman gado ta kwanta bata dad'e da kwanciya ba Sabreen ta shiga itama wanka ta yi da sallah sannan itama ta kwanta kusa da Sabeeha kowacce da abinda take tunani can Sabreen ta ce "Sabeeha dear nima fa na fara tunanin barin gidan nan dan gaskiya na gaji da wannan wulak'ancin," Sabeeha ta ce "Sabreen sister ni hankalina ya dad'e da karkata kan Abba gaskiya," Sameeha ce ta shiga d'akin cire kayan jikin ta ta cire ta shige toilet wanka ta yi tare da yin sallah sannan ta shirya cikin kayan bacci irin nasu sannan ta zauna gefen gadon ta ce "Gaskiya bana son yadda ku ke sa kanku a matsala saboda ni yanzu fa Farida ta gayawa yallab'ai daga yau duk ranar da muka sake yin irin haka dukan mu za a had'a ayi mana hukunci," Sabreen ta yi juyi sannan ta d'ora kanta a jikin Sameeha ta ce "Sameeha dear ki dena damuwa akan hakan baza mu tab'a bari wani abu ya same ki ba," murmushi Sameeha ta yi ta ce "Amma Sabreen sister nifa nayi laifin ba ku ba," tab'e baki Sabreen ta yi ta ce "Kema ai baki yi komai ba domin kama ki akayi da laifin da baki da masaniya a kansa,"



"Amma dear wannan karo na goma kenan fa da irin hakan na faruwa gashi yanzu sunce idan muka sake dukan mu zasu had'a dan Allah kar ku sake gara ayiwa d'aya kawai," mtswwww Sabeeha ta ja wani dogon tsaki tare da tashi zaune ta kalli Sameeha ta ce "Kar su fasa d'aukar matakin sannan Kuma dole ne mubar gidan nan da zarar sun bamu salary d'in mu Kuma wallahi kafin nan saina had'a musu fitinar da basu tab'a tunani ba," a tsorace Sameeha ta ce "Amma dai Sabeeha wasa ki ke wallahi gara masifar gidan nan da ta Kawu Ni dai ban yadda da hakan ba kinsani muna komawa aure zai yi mana Kuma kinsani dole sai ya d'aura miki aure da Sadam d'in da bakya so sannan ya aurawa Sabreen aure da d'an mai gari ni Kuma ya bawa dansa faruk,"



"To kar Allah yasa ya fasa gidan nan dole mu barshi Kuma kaf cikin mu ba wacce ya isa ya yiwa auren dole," ajiyar zuciya Sameeha ta yi ta ce "Amma kinsan tunda ya fad'a sai ya aikata Kuma kinsan wannan ne gida na takwas da Kawu ya kawomu Kuma ya ce idan muka sake guduwa aure zai yi mana Kuma kema kinsan yadda Sadam ke kashewa Kawu damu kanmu kud'i ba yadda za ayi kice baza ki aure shi ba duk da cewar bakya son sa," wani tsakin Sabeeha ta ja ta ce "kud'i yanzu ya fara kashe mana ni da Kuma ku tunda ba rok'on sa muka yi ba Amma wallahi bazan tab'a auren sa ba," haka suka dinga tattauna matsalolin su har tsakiyar dare sannan suka yi bacci.


Washe gari tun safe suka tashi suka sake shiryawa cikin bak'ak'en dogayen riguna iri d'aya suka fita suka fara ayyukan su.


Sameeha na cikin sharar falon Farida Rashida ta shiga falon ture Sameeha ta yi ta wuce ko kallon ta Sameeha bata yi ba saboda hak'uri ne da ita sosai ita kuwa Rashida a zuciyar ta ta ce shegu sai kyau shiyasa na tsane su domin bana so nan gaba idan yallab'ai zai k'ara aure ya auri d'aya a cikin su domin na dad'e ina dakon soyayyar sa a zuciyata.


A fili Kuma ta ce "banza ye kawai," har lokacin Sameeha bata kalle ta ba ganin Sameehan tak'i kulata kawai sai ta je har gaban ta ta tsinka mata mari dafe kunci Sameeha ta yi sannan itama ta d'aga hannu ta rama daidai lokacin Farida ta fito wata uwar tsawa ta daka musu wacce tasa kowaccen su nutsuwa.



Tana k'arasawa ta ce "Mahaukatan ina ne ku rasa inda zaku yi fad'a sai a falona?" Rashida ta ce "Kiyi hak'uri ranki ya dad'e na sameta ne tana shara shine nace ta gyara yadda take shara baya fita shine ta mare ni," kallon Rashida kawai Sameeha ke yi cikin mamakin k'aryar da ta shirga.



Farida ta kalli Sameeha cikin b'acin rai da kuma jin haushin ta ta ce "Ke dan uwarki baki san cewa ko a cikin 'yan aiki Rashida ta daban ce a wajen ba da zaki mare ta?" Bud'e bakin da Sameeha ta yi da niyyar yin magana Farida ta zabga mata mari ta ce "karki kuskura kice wani Abu anan," dafe kunci Sameeha ta yi hawaye na bin fuskar ta.



Tsaki Farida ta ja ta kalli Rashida ta ce maza rama marin da ta yi miki ba tare da tausayi ba Rashida ta dinga zabgawa Sameeha mari har sau uku.


Farida ta ce "b'ace mun da gani shashasha," da gudu Sameeha tabar falon tana kuka ga kuncin ta sai zafi yake yi domin hannun Rashida tafkeke ne.



Da gudu Sameeha ta shige kitchen tana kuka Sabreen dake wanke wanke ta mik'e da sauri ta tare da tana cewa "Sameeha dear maiya faru?" Sai lokacin Sabeeha ta waiga tana kallon yadda Sameeha ta rungume Sabreen tana kuka.



Ajiye ludayin hannun ta ta yi ta k'arasa tana kallon Sameeha damuwa fal fuskar ta sannan cikin b'acin rai ta ce "Sameeha dear waye ya mare ki?" Sai lokacin Sabreen ta lura da shatin yatsun dake fuskar Sameeha.



Girgiza kai Sameeha ta yi ta ce "bakowa," k'ara hasala Sabeeha ta yi ta ce "Kamar ya bakowa ga shatin yatsu nan a fuskar ki waye ya mare ki?" Cikin kuka Sameeha ta zayyane musu abinda ya faru.


Sabreen ta ce "Wai meyasa Rashida ke miki irin haka ne?"


"Nima bansan me nayi mata ba," Sabeeha ta ce "Barta Wallahi kwanan nan zasu raina kansu a gidan nan," Sameeha ta k'arasa gaban Sabeeha ta ce "Sabeeha sister na yadda mubar gidan nan Wallahi na gaji da abinda ake mun kullum cikin yi mun sharri ake," ajiyar zuciya Sabeeha ta yi ta ce "karki damu dear zamu bar gidan nan Amma Wallahi saina fara gyara musu zama," shiru Sameeha ta yi bata yi tunanin hana Sabeeha ba saboda abinda ake mata ya fara isar ta.


Da daddare bayan Sabeeha ta gama abinda take yi ta nufi d'akin su tafiya take yi tana rera wak'ar ta "wata rana sai labari ka zamo mai aikata kairi...," Dif ta yi shiru saboda muryar Rashida ta jiyo daga cikin d'akin su tana cewa "Wallahi Dije ina mutuwar son yallab'ai kullum k'ara son shi nake yi," Dije ta ce "A'a fa Rashida ki rufawa kanki asiri dan wallahi idan Farida ta sani kin shiga uku," Rashida ta ce "Ita d'in banza ke nifa dama duk shige matan da nake yi dan kawai na k'ara samun kusanci da ita ne sannan abinda baki saniba duk wata kulawar da take ba yallab'ai ba wacce ban saniba so nake na gama karantar ta yadda idan na aure shi zan bashi kulawar da ta ninka wacce yake samu wajen waccan banzar damuwata d'aya shine idan har yallab'ai baya sona to Wallahi akwai matsala shiyasa har yanzu ban gayamasa ina son shi ba saboda idan har ya ce baya sona daga ranar korata k'auye zasu yi saboda nasan dole zai fad'awa Farida Amma idan yana sona sai dai kawai ta ji maganar aure daga sama ina shiga Kuma naci uwar ta," dariya suka yi har da tafawa.



Sabeeha dake jinsu ta yi dariyar mugunta a zuciyar ta tace shikenan dama ta samu sannan ta wuce zuwa d'akin su da farin ciki ta shiga d'akin ta yi sallama Sameeha da Sabreen da tun dazu suka gama aikin su suka amsa mata sallamar.



Towel ta d'aura ta shige toilet ta yi wanka sannan ta fito ta yi sallah ta haye gadon ta ce ku tashi kuji wani labari a tare suka tashi suna tambayar ta wane labari bata b'oye musu ba ta basu labarin abinda ya faru dariya suka kama yi Sabreen ta ce "Ni Wallahi banga abin so a wajen yallab'ai ba ku dube shi fa kamar kwad'o," suka Kuma tuntsirewa da dariya Sameeha ta ce "A'a may be k'atuwar muryar ce ta ja ra ayinta," Sabeeha tsagaitawa da dariyar ta ta yi ta ce "Ku barni da su zasu gane basu da wayo," ranar ma haka suka raba dare fira sannan suka yi bacci.




KADUNA


Wasu motocine wajen guda ashirin suka jero gudu suke yi a kan titi na fitar hankali ga jiniya na tashi gaba d'aya motocin hilux ne da sojoji rik'e da bindigu a hannun su gud'a d'aya BMW army colour sai shek'i take yi wata area suka shiga sai da aka bud'e musu gate sannan suka bi wani titi dake tsakiyar layin Wanda bishiyu suka yiwa titin runfa.



Wani had'adden gida ne unguwa guda a wajen suna k'arasawa sojojin dake tsaron gate d'in suka bud'e musu gate suka shiga basu tsaya ba sai da suka kai wajen wani dogon bene Mai kyawun gaske sannan suka yi parking.




Sojojin suka diddiro daga motar gaba d'ayan su suka zagaye army green d'in.

D'aya daga cikin sojojin ne ya bud'e bayan motar sannan ya ja gefe ya k'ame.



Mutumin dake cikin motar ya ziro k'afar sa mai d'auke da wani takalmi Mai matuk'ar kyau irin nasu na sojoji sannan a hankali ya fito.



Wayyo kuzo ku ga kyau iya kyau a wajen guy d'in nan kamar balarabe dogone sosai fari sol da shi har yellow yake yi gashin kansa kamar na indiyawa gashi bak'i wuluk yana shek'i sannan askin dake kansa ma abin kallo ne Yana da dogon siririn hanci ga pink lips abinda zaifi d'aukar hankalin mutum shine idanun sa farare ne kar k'wayar idon Kuma bak'i wuluk kamar yadda gashin kansa yake da Kuma gashin girarsa da ta kasance siririya mai shape kamar zata had'e ga zara-zaran eye lashes kamar mace.



Guy d'in ya had'u iya had'uwa kana kallon sa ka ga k'akk'arfan namiji Yana sanye cikin kak'in su na sojoji Wanda kamar dan shi kad'ai aka d'inka su saboda yadda suka yi masa matuk'ar kyau kamar ka sace shi ka gudu.



Wani b'angare ya kalla ya saki wani sassanyan murmushin da ya bayyana dimples d'insa dake gefe da gefen fuskar sa da Kuma fararen jerarrun hak'oran sa.



Sannan cikin k'asaita ya fara tafiya kan jan carpet d'in da aka shimfid'a masa Wanda a jiki aka rubuta da manyan bak'i WELCOME BACK TO HOME OUR HAPPINESS MG ABDUL MALEEK.



Wata kyakkyawar mata ce a tsaye tasha kyau cikin wani tsadadden less orange colour wuyan ta sanye da sark'ar gold da d'an kunne haka ma zobunan hannunta da warwaron ta duk na gold ne fara ce sol sannan suna kama sosai da MG wato major general.




Gefe da gefen ta wata budurwa ce da Kuma saurayi kyawawa kamar larabawa.


Yana k'arasawa budurwar ta ce "Welcome ya Maleek," cikin dakakkiyar muryar sa mai dad'in sauraro ya ce "Thank you Rinaz," saurayin Kuma ya yi huging d'insa ya ce "Sannu da zuwa ya Maleek," Nan ma ya ce "Thank you Fauwaz," daga haka ya nufi wajen mahaifiyar su wacce tun fitowar sa daga mota take sakin murmushi.




Yana k'arasa ya rungume ta ya ce "I really miss you Ummina," ta ce "mee too I miss you much more my son," sannan ta bashi kiss a goshi ta ja hannunsa zuwa cikin falon.



Falon ya tsaru iya tsaruwa babban falone na gaske Yana d'auke da kujera set uku ga wata tafkekiyar plasma a falon da home speakers ga wani lallausan carpet da wasu fulawoyi da aka k'awata falon da su ta kowacce kusurwa ga wasu show glass na jikin bango dake cike da kayan k'amshi da wata red da blue d'in haske a ciki can gefe kuma had'adden daining ne mai kujeru birjik da Kuma ba babban kitchen tsayawa fad'in had'uwar falon ma b'ata lokaci ne.



Zama suka yi dukan su a falon Ummi ta ce "Son ya hanya?" Ya ce "Ummi hanya lafiya," sannan ya mik'e ya ce "Ummi zanje part d'ina I want to have some rest," ta ce "Ok ga abinci yana jiran ka," yatsina fuska ya yi ya ce "Amma Ummi kinsan ni bazan ci abinci 'yan aikin ki ba?" Murmushi Ummi ta yi ta ce "ai yau da kaina na girka maka saboda ban fita office ba amma kasan dole sune zasu dinga yin girki a gidan nan," shagwab'e fuska ya yi ya ce "Amma Ummi duka fa basu iya komai ba?" Ummi ta ce "ka ga ya isa zan canja ma Mai yi ma girki yanzu kaje idan ka shirya kazo dan Daddyn ka ya bayar da sak'o a fad'a maka sannan ka tabbatar kaje ka gaida Umman ku," tab'e baki ya yi sannan ya yi hanyar fita Yana cewa "To," yana fita Salman ya biyo bayan sa Wanda Salman ya kasance soja ne sannan amintaccen Maleek Kuma d'a a wajen k'awar Ummi.



Kai tsaye part d'insa ya nufa duk inda ka kalla 'yan aiki ne a gidan suna ta hidima duk wacce ta ganshi sai ta gaishe shi tun Yana amsawa har ya dena dan ya gaji da magana.



Tun kafin ya k'arasa sojojin dake wajen suka bud'e masa k'ofa ya shige falone na gani na fad'a ya yi kyau matuk'a komai na d'akin fari ne yasha ado kamar d'akin amarya stairs ya haye nan ma wani falon ne mai kyawun gaske bedroom d'in sa ya shige sannan ya fad'a bathroom sai da ya d'au lokaci sannan ya fito yana tsane sumar kansa da towel cikin k'ank'anin lokaci ya shirya cikin black jeans da red riga sai k'amshi yake zabgawa juyawa ya yi ya fita daga part d'in.


Ko da ya fito sojojin sa suka biyo bayan sa d'aga musu hannu ya yi suka tsaya shikuma ya cigaba da tafiya abinsa har sai da ya je wani b'angare shiga ya yi da sallama a bakinsa wata mata ce kashingid'e a kan carpet ga fruits a gaban ta 'yan aiki zagaye da ita wasu na yanka fruits wasu na mata tausa k'arasawa ya yi ya zauna ya ce "barka da rana Umma," kallon sa ta yi ba yabo ba fallasa ta ce "yawwa," shi kuma ganin yadda take amsa masa ne ya b'ata masa rai ya mik'e tare da fad'in na barki lafiya ya juya zai fita har ya kai k'ofa ya jiyo muryar ta tana cemasa "Ya zaka Tafi baka tambayi Nasreen ba?" Ko kallon ta bai juya ya yi ba ya fice.
[10/25, 7:34 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️




RUBUTAWA DAGA
HAFSAT MAGAJI

Please Login or Register in order to submit comment