Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bai farfad'o ba Doctor yace sai dai a fitar da shi waje saboda ciwon sa ya tashi sosai," Abba da Ummi ma take hankalin su ya k'ara tashi domin ba su yi tunanin jikin nasa ya kai haka ba.




Tashi Sabeeha ta yi ta nufi stairs idanunta taf hawaye wani tausayin kansu ita da Maleek ne ya kama ta tana shiga d'aki wanka ta yi tare da alwala tana idar da sallah ta kwanta saman gado ta fad'a tunani Sabreen ce ta shigo ta zauna gefen ta ta ce "Sister kiyi hak'uri mu ma muna cikin damuwar da kike ciki amma hak'uri Zaki yi yanzu ki tashi muje kici abinci," d'an tashi zaune Sabeeha ta yi daga kwancen da take ta ce "Sabreen na rasa nutsuwa ta bansan me yake shirin faruwa damu ba sweetheart yana asibiti a wani yanayi ta ya ni zan iya cin abinci Sabreen me Uncle yake nufi da maganar sa suna nufin bazai aure ni ba kenan?"




"Please dear ki dawo cikin nutsuwar ki idan Allah ya tsara ke matar Ya MG ce babu wanda ya isa ya hana calm down please," shiru Sabeeha ta yi tana nazarin maganganun Sabreen tabbas gaskiya ta fad'a a hankali ta ji sanyi a ranta sai dai duk yadda Sabreen ta yi da ita akan suje ta ci abinci k'in yadda ta yi haka ta kyale ta.



Su Ummi suna komawa gida suka samu Rinaz kwance ba lafiya Ummi ce ta duba ta ta bata abinci da magani tasha.




Washe gari su Sabeeha suka shirya har da Doctor da ita dama asibitin zata da Kuma Abba suka tafi asibitin suna zuwa suka samu su Ummi suna nan cikin fara'a su Ummi da Daddy suka tare su suka gaisa tare da tambayar mai jiki suka amsa da cewa da sauk'i.



Su Sabeeha suka gaishe da su da tambayar mai jiki Ummi ta ce "Da sauk'i yarana," Daddy ya kalli 'yan uku ya ce "Aysha kina nufin wad'an nan yaran Maryam ne?" Ummi ta ce "Eh wannan Kuma mahaifin su," jinjina kai Daddy ya yi ya ce "Masha Allah," ya fad'a yana kallon su Sabeeha domin mamakin kamannin su.





Tashi Sabeeha ta yi ta nufi k'ofar d'akin da Maleek ke ciki ta lek'a yana nan inda suka barsa jiya hawayen dake taho mata tayi saurin mayarwa sannan ta juya ta koma gefe ta zauna Fauwaz ne da Rinaz suka shiga asibitin domin Fauwaz ya je ne domin yin wanka.




Zama Rinaz ta yi ta gaida su Doctor sannan ta k'arasa wajen Sabeeha dake gefe ta zauna kallon ta Sabeeha ta yi bata ce komai ba ganin haka Rinaz ta fara kwantar mata da hankali sai dai ko uffan Sabeeha bata ce ba domin duk abinda zai fito daga bakin ta kuka ne shiyasa kawai ta yi shiru ba magana.




Tashi Doctor ta yi tare da Abba tace da Ummi "Aysha bari na shiga office," Ummi ta ce "To zan shigo," tafiya suka yi suna tafiya ba dad'ewa Umar ya isa asibitin shima hankalin sa a tashe domin sai lokacin Salman ya Kira shi a waya ya sanar masa.




Haka suka yi ta zaman asibiti da yamma da Doctor ta tashi daga aiki ta ce da 'yan uku su tashi su tafi gida mak'e kafad'a Sabeeha ta yi ga idanu ya ciko da k'walla Doctor bata ja maganar ba tayi tafiyar ta ta barsu dan tasan su Sabreen ma ba binta zasu yi ba.



A haka har aka kwana biyar kullum su Sabeeha suna asibitin har dare amma duk abinda ake yi Uncle bai je duba Maleek ba haka ma Hajiya Asiya Nasreen ma hanata zuwa suka yi.



Ranar kwana na shida Daddy ne ya fito daga part d'in Ummi yana amsa waya da Doctor Kamal suke waya yana sanar da shi yau zai koma Dubai Daddy ya ce "Ok zuwa gobe zamu shigo to," da haka suka yi sallama.



Har Daddy zai shiga mota motar Uncle ta tsaya saitin sa fasa shiga motar Daddy ya yi ya tsaya har Uncle ya fito ba yabo ba fallasa Daddy ya gaishe shi amsawa Uncle ya yi tare da cewa "Ya jikin yaron?" Kamar Daddy bazai yi magana ba sai Kuma ya ce "Yaya kenan aina d'auka Maleek d'an ka ne sai gashi ka nuna mun ba haka bane tunda yau kwanan sa shida a asibiti amma ko da wasa baka je ka ga jikin sa ba amma bakomai tunda kai kaga dacewar hakan," Daddy na fad'ar haka ya shige mota suka tafi karo na farko kenan da yaji d'an uwan nasa baya kyautawa.



Uncle kuwa motar Daddy yabi da kallo baki bud'e yana mamakin Daddy yau shine da fad'a masa magana irin haka wata zuciyar ta ce ka manta d'an gold fa ka tab'a tab'e baki Uncle ya yi a fili ya furta "Aikuwa d'an gold d'in zai ci uban sa," daga haka ya shige mota.




Daddy kuwa yana zuwa ya samu Sabeeha zaune kusa da Ummi tana ganin sa ta tsugunna har k'asa ta gaishe shi cikin fara'a ya amsa domin zuwa lokacin 'yan uku sun gama shiga ransa ya ce "Yarinya ya gajiyar ku?" K'asa Sabeeha ta yi da kanta bata ce komai ba.


Zama Daddy ya yi ya ce "Aysha gobe zamu wuce Dubai doctor zai koma yau," Ummi ta ce "Ok Allah ya kaimu," mik'ewa Sabeeha ta yi ta ce "Ummi bari naje gida zan dawo yanzu," Ummi ta ce "To sai kin dawo," fita ta yi gate d'in asibitin domin samun abun hawa domin ba wanda yasan ta taho sakamakon mafarkin Maleek da ta yi ta ji tana tashi shi take son gani.




Tana tsaye mota ta tsaya a gefen ta ko kallon motar bata yi ba sai dai ta ga kamar motar daga cikin asibitin ta fito bud'e motar aka yi Salman ya fito ya k'arasa wajen ta ya ce "Sabeeha Ina zaki haka?" Ganin Salman ne ta ce "Dama gida zani," ya ce "Ok muje," bud'e mata motar ya yi ta shiga ya shiga ya ja suka tafi.




Tana shiga falon ta samu su Doctor suna breakfast gaishe su ta yi sannan ta wuce stairs da kallo Doctor ta bita ganin yadda itama Sabeehan ta rame saboda rashin cin abinci da damuwa tana shiga d'akin su wanka ta fad'a tana wankan ta ji wayar ta na ringing ko da ta fito bata bi takan wayar ba mirrow ta nufa tayi shafe-shafen ta ta bud'e drower ta d'auko doguwar rigar atamfa irin ta jikin su Sameeha tasa ba ko kwalli a fuskar ta ta ta nannad'e gashin ta waje d'aya ko d'an kwali bata tsaya d'aurawa ba ta d'ora mayafin saman kanta ta d'an fesa turare wayar ta ta ji ana sake kira juyawa ta yi ta d'auki wayar tayi sallama tana zura plat shoes a k'afar ta wani ihun murna ta saki sannan ta fice daga d'akin da gudu.


Falo ta sauka da gudun ta tana zuwa ta rungume Doctor ta ce "Mama ya farka," ko ba su tambaya ba sun san Maleek ne ta kalli su Sabreen ta ce "Sister ya farka," a tare suka ce "Alhamdulillah," domin sun ji dad'in hakan sosai musamman da suka ga Sabeeha na farin ciki haka domin tunda Maleek ya kwanta cuta ko murmushi ba yinshi Sabeeha ke yi ba.



Hanyar waje ta yi tana cewa "Dear ku taho mu tafi,"



"Sabeeha abinci Kuma fa?" Cewar Doctor Sabeeha da ta riga ta yi gaba ta ce "No Mama," mota suka shige driver ya ja sai hospital.




Yana yin parking suka fita da sauri Sabeeha har da gudu take had'awa saboda d'okin zuwa ganin sweetheart d'in ta.





Kai tsaye tasa kanta cikin d'akin cak ta tsaya tana kallon mutanen d'akin su Sabreen ma dake bayan ta tsayawar suka yi.



[10/25, 8:43 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️





RUBUTAWA DAGA
HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ)





SADAUKARWA GA
MY DAUGHTER SABEEHA
BILKISU Z.YA'U (🅱️K)
AISHA MAGAJI DABO (AMA)




Page 20


D'akin babba ne sosai Daddy na zaune a gefen Maleek dake jingine jikin pillow sai Ummi da Fauwaz dake zaune a gefe da Rinaz daga d'ayan gefen kuwa Uncle ne zaune shi da Hajiya Asiya sai Nasreen tasha uwar kwalliya ta k'wama black glass a fuskar ta.




Kasa k'arasawa ciki Sabeeha ta yi sai dai idanunta na kan Maleek da ya rame ya k'ara haske a hankali yake sauke numfashi yana d'an rintse idanu alamun yana cije pink lips d'in sa alamun yana jin jiki shima kallon Sabeehan yake yi kamar ranar ya fara arba da ita.



Tunani Sabeeha ta yi a zuciyar ta ko dai suna magana ne tasu ta family a hankali ta juya zata fita daga d'akin "Sabee na," ta ji muryar sa ta fad'a da sauri ta waiga tana kallon sa ba ma ita kad'ai ba kowa na d'akin da kallo ya bisa domin tunda ya farka ake yi masa magana amma ko sannu yak'i amsawa har an fara tunanin ko wata matsalacce ta daban amma sai gashi ganin Sabeeha ya yi magana hawaye ke shirin saukowa Sabeeha a fuska ya girgiza mata kai d'an murmushi ta yi.



Nasreen kuwa cire glass d'in fuskar ta ta yi tana jifan su Sabeeha da wani mugun kallo Sabeeha kuwa ko lura bata yi ba domin bata ita take yi ba k'wafa Nasreen ta yi ta dunguri Uncle tana nuna masa Sabeeha da ido.



Ummi ta bud'e baki zata yi magana Uncle ya kalli su Sabeeha ya ce "Lafiya zaku zo ku tsaya mana a nan kunga kuyi waje muna magana ne ta ahali bama buk'atar bare a nan," kallo ne ya koma kan Uncle domin mamakin abinda ya fad'a.




Maleek kuwa rintse ido ya yi yana d'an girgiza kai shi kad'ai yasan abinda yake ji amma Uncle na neman k'ara masa wata damuwar.


Har sun juya zasu fita Maleek ya kalli Fauwaz alamun ya yi magana domin shi ba halin yi domin yanayin da yake ciki.




Fauwaz ya ce "Sabeeha ku shigo ga guri ku zauna ba wata magana da ake yi," baki sake Uncle ke kallon Fauwaz ya ce "Dan uban ka ni sa anka ne da zanyi magana kayi?" Bai gama rufe baki ba Rinaz ta ce "Me ku ke jira ne ku zauna mana Nan asibiti ne ba family meeting hall ba,"


"Ya isa mamana!" Daddy ya fad'a cikin d'aga murya sannan ya kalli su Sabeeha ya ce "Ku zauna kunji," sai lokacin su Sabeeha suka zauna a sanyaye.


Daddy ya ce "Alhamdulillah mun godewa Allah da wannan cigaba da muka samu dama gobe muke sa ran tafiya Dubai domin duba lafiyar ka," shiru d'akin ya d'auka Daddy ya cigaba da cewa "Gobe insha Allah zamu je domin a duba mana lafiyar ka," Sabeeha kuwa k'asa ta yi da kanta.



Maleek kuwa rintse idanunsa da suka ji jajir ya yi sannan ya rik'o hannun Daddy ya damk'e hannun sa sosai murya na sarkewar ciwo ya ce "Daddy idan har baza ka amince na auri Sabeeha ba ba amfanin a fitar dani ko Ina domin nasan hakan bazai amfanar da komai ba,"




"Aikuwa sai dai ka mutu domin wannan yarinya baka isa ka aure ta ba kuma ni da mahaifin ka mun riga mun yanke magana batun yau ba Kuma Kai baka isa ka canja mana ra'ayin mu ba," kallon Daddy Ummi ta yi domin jin me zaice amma shiru bai ce komai ba.



Hawaye ne ya gangaro a fuskar Sabeeha a hankali tasa hannunta ta goge Maleek dake kallon ta ji ya yi kamar ana zuba masa tafasasshen ruwan zafi a zuciyar sa ganin hawayen ta take jikin sa ya d'auki wani mugun zafi jikin sa ya fara rawa ya rik'o Daddy ya ce "Please Daddy Ina sonta zan iya rasa rayuwata idan babu ita," take ya fara wani irin numfashi jikin sa kuwa rawa yake yi sosai a rud'e Ummi ta yi wajen sa tana kuka Fauwaz kuwa da gudu ya fita domin Kiran Doctor.



Cikin hawaye Ummi ta kalli Uncle ta ce "Wallahi idan har yarona ya rasa rayuwar sa bazan tab'a yafe maka ba kai waye da zaka haramta abinda Allah ya halatta ko ita 'yar ka ta daban ce da baza a yi mata kishiya ba to idan har na isa da d'ana to sai ya auri Sabeeha," Daddy cikin fusata ya ce "Aysha kina hauka ne Yaya ne fa," d'aga masa hannu Ummi ta yi sannan ta juya inda yake ta ce "Kai shaida ne akan tsanar da yayanka da matar sa suka yiwa yarona wanda daidai iyawar sa yana yi masa biyayya cikin biyayyar sa ne ma ya yadda da auran Nasreen duk dan farin cikin ka ba tare da ya ja lokaci ba amma shi yau gashi a kwance akan gadon asibiti cikin mawuyacin hali akan abinda yake so amincewar ka kad'ai yake buk'ata amma ka kasa amsa masa bayan ba haramun zai aikata ba baza ku kashe mun yaro ba meyasa baza ka fahimci halin da yake ciki ba ni fa uwa ce Ina da hakk'i akan Maleek Dan nayi shiru na zuba ido ba hakan na nufin bana son shi bane nima Ina so na ganshi cikin farin ciki ina so na faranta masa kamar yadda yake faranta mana," Ummi ta fad'a tana hawaye sannan ta cigaba da cewa "Nasan ba kasan dalilin sakin Nasreen da ya yi ba saboda lokacin an hana shi fad'a to ya sake ta ne saboda k'ok'arin kashe shi da take yi ita da mahaifiyar ta wanda wacce ku ka hana ya aura itace ta cece shi," Nan Ummi ta fad'awa Daddy kaf abinda ya faru sannan ta d'ora da cewa "A wannan karon bazan tauyewa yarona hakk'in sa ba idan har Ina raye saina bawa Abdul-maleek farin cikin da yake buk'ata abin nan ya isheni haka kamar yadda yake son yarinyar sa to ni fiye da haka nake son yarona," Ummi ta fad'a tana share hawaye.






Uncle kuwa gumi ne ya keto masa domin jin yadda Ummi ta gama tonawa 'yar sa asiri haka ma Hajiya Asiya duk ta jik'e da gumi ganin irin mugun kallon da Daddy ke jefan su da shi.




Juyawa Daddy ya yi ya kalli Maleek dake kwance da likita a kansa ya rik'o hannun Maleek hawaye na zuba a idanun Daddy na tsabar tausayin d'an nasa ya ce "Allah ya yi maka albarka son da yi mun biyayya sannan na yadda ka aure ta na amince," duk da baya hayyacin sa sai da ya yi saurin bud'e idanunsa ya kalli Sabeeha ya yi mata murmushi sannan ya mayar da idanun sa ya rufe saboda alluran da likita ya yi masa.



Kallon Ummi Daddy ya yi ya ce "Nagode Aysha da tubatar dani abubuwa da dama da ki ka yi," sannan ya taka har gaban Sabeeha ya ce "yarinya Allah yayi miki albarka Nagode da ceton d'ana da ki kayi," a hankali Sabeeha ta ce "Bakomai Daddy,"




Tashi Nasreen ta yi tana buga k'afa ta ce "Wallahi ba a isa ba bazai aure ta ba Daddy kana jin abinda ake fad'a ko?" Fauwaz ya nuna mata k'ofa ya ce "Zo ki fita tun kafin nayi miki duka domin nan ba filin hauka bane," fuuu Nasreen ta fice Uncle da Hajiya Asiya suka bi bayan ta.




Suna fita su Ummi su ma suka fita Sabeeha zuciyar ta fal farin ciki ko zama kasawa ta yi ta kalli Ummi ta ce "Ummi zamu je gida," Ummi ta ce "To daughter ku gaida maman ku," suka ce "To," sannan suka tafi.




Da gudu ta shiga falon ta fad'a jikin Doctor ta ce "Mama finally Daddy ya amince da maganar aure na da ya Maleek," murmushi Doctor ta yi ganin yadda Sabeeha ke farin ciki ta ce "To naji mara kunya ni tashi mun a jiki," tashi ta yi tana dariya ta haye stairs da gudu.


Washe gari Daddy Ummi Maleek suka shirya sai Dubai Rinaz Kuma ta tafi gidan Mama.



Suna zuwa Airport motocin sojojin Maleek tazo da Kuma motar asibiti direct asibitin suka wuce suna zuwa ba b'ata lokaci aka fara duba shi domin ansan da zuwan su.





Sai da su Ummi suka ga an fara duba shi sannan suka nufi gidan Daddy dake can suka yi wanka da cin abinci sannan suka koma asibitin.



Sai yamma sannan doctor Kamal ya fito tare da ragowar likitoci kallon Daddy ya yi ya ce "Friend muje office," bin bayan sa suka yi suna shiga office d'in bayan ya zauna ya kalli Daddy ya ce "Gaskiya friend bai kamata ace ciwon son yana yin gaba haka ba akwai abinda yasa a ransa sosai nasan koma meye shi zai samu nasan ba abinda ya rasa nasan zaku ji da wannan amma dai gaskiya wannan shine mak'asu din fad'awar sa a wannan halin wanda munci nasarar shawo kan matsalar domin munyi masa wani k'aramun aiki sai dai a kiyaye fad'awar sa a irin wannan halin nan gaba domin idan hakan ya kasance komai ma zai iya faruwa yanzu dai yana bacci zuwa gobe zai farka zamu bashi kulawa a nan zuwa sati d'aya," ajiyar zuciya Daddy da Ummi suka sauke sannan suka ce "To doctor mun gode," murmushi kawai ya yi sannan suka fita zuwa d'akin da Maleek yake.




Maleek kuwa sanda ya farfad'o ba laifi jikin sa da sauk'i anan Ummi ke masa albishir da cewar Daddy ya amince da auran sa da Sabeeha ba k'aramun farin ciki ya ji ba har hakan ya kasa b'oyuwa.




A Nigeria kuwa kullum sai su Sabeeha sun Kira Ummi sunyi mata ya me jiki.




Da haka har suka kwana biyar a asibiti jikin Maleek kuwa ya ji sauk'i sosai kamar da gashi ya wani k'ara kyau domin ya kwantar da hankalin sa sosai ga wata kulawa da yake samu daga Daddy da Kuma Ummi.





Sallama likita ya basu suka koma gida Maleek kuwa sai farin ciki yake yi domin so yake gobe ta yi ya je ya ga sahibar sa.





Tun dare da suka Kira Ummi ta sanar da su gobe zasu dawo dan haka su shiryawa tarbar su ranar da wuri su Sabeeha suka yi bacci domin su tashi da wuri su yi shirin tarbar su.




Washe gari tunda suka yi Sallah basu koma bacci ba wanka suka yi sannan suka fita driver ya d'auke su zuwa gidan Ummi suna zuwa ba b'ata lokaci suka fara gyara part d'in duk da ba dirty fes suka k'ara gyarawa sannan suka shiga kitchen har Fauwaz da fitowar sa kenan shima kitchen d'in ya shiga ayi da shi.





Cikin k'ank'anin lokaci gidan ya cika da k'amshin soye_soye da dafe dafe lemuka kuwa sun had'a ya kai kala biyar suna gamawa suka jere komai a daining sannan suka gyara kitchen d'in suka tafi d'aki domin yin wanka.


Tsaf suka shirya cikin shiga ta alfarma kamar ka sace su ka gudu tsabar kyan da suka yi Sabreen Sameeha da Rinaz ne suka fito falo daidai lokacin motocin su Maleek na yin parking a k'ofar part d'in Ummi.


Da sallama suka shiga falon da gudu Rinaz ta rungume Maleek tana murnar ganinsa shi kuwa sai murmushi yake yi wajen su Sabreen ya kalla da suke gaishe da su Ummi ya yi ya ga ba Sabeeha kafin ya yi magana Fauwaz ya fito daga d'akin sa rungume juna suka yi da Maleek.



Gaishe da Maleek su Sabreen suka yi tare da tambayar sa jikin sa ya ce "Alhmadulillah,"





Sabeeha da ta gama d'aurin ta ta nufo down stairs tasha kyau sosai cikin green d'in less kamar amarya.



Tana fara taka matakalar benen idanunta ya sauka akan Maleek da ya yi matuk'ar kyau cikin shigar complete bak'i da ya yi shima kamar ance ya d'aga Kai ya hangota da idanu ya bita har ta k'arasa cikin falon har k'asa ta tsugunna ta gaida Ummi da Daddy tare da yi musu ya mai jiki.




Daddy ya ce "Lafiya daughter mai jiki yaji sauk'i gashi nan," waigawa ta yi ta kalle shi ya hard'e hannayen sa a k'irji yana kallon ta ita kunya ya bata ma.



Stairs Daddy da Ummi suka nufa kallon sa Sabeeha ta yi ta ce "Ya jikin ka?" Sai da ya gama kallon ta sannan ya numfasa ya ce "Alhamdulillah Sabee na," murmushi ta yi shima hakan ya yi hanyar waje domin zuwa part d'in sa.




Wanka ya yi ya dawo part d'in Ummi ya same su a daining baza idanu ya fara domin ganin ta inda zai hango Sabeeha amma babu ita Daddy ya ce "Son yadai k'araso mana," daining d'in ya k'arasa ya ja kujera kusa da Rinaz ya zauna sannan ya ce "Daddy Ina su Sabee na suke?"




Ummi ta ce "Sun wuce gida munyi dasu su tsaya sunk'i," shiru kawai ya yi Daddy ya ce "Ci abincin mana Son," abincin ya fara ci yaci sosai domin abincin ya yi masa dad'i haka ma Daddy girkin yayi masa dad'in gaske.



Yana gamawa ya mik'e ya nufi hanyar fita daga falon Ummi ta ce "Ina zaka Kuma?"




"Ummi wajen ta zani fa," Daddy ya ce "Zonan Son," juyawa ya yi ya koma ya zauna yana kallon Daddy domin jin abinda zai ce.



Ajiye cup d'in zob'on dake hannun sa Daddy ya yi sannan ya ce "Son ka sanarwa da daughter cewar zamu je wajen mahaifin ta Ina so ne muje nema maka auren ta zuwa," washe baki Maleek ya yi ya ce "Wow thank you Dad ai da kaina ma zan sanarwa Mama," hararar wasa Ummi tayi masa ta ce "To ba kai muka ce ka sanar musu ba sarkin zumud'i," dariya Maleek ya yi da ta k'ara masa kyau dimples d'insa suka lotsa sosai ya ce "To Ummi,"




Waigawa Daddy ya yi ya kalli Fauwaz dake gefe yana danna waya yana kora kunun aya ya ce "Abbana," ajiye wayar ya yi ya ce "Na'am Daddy,"




"Dama kaima na fad'a maka ka fito da mata nasan kuma kana da ita 'yar gidan waye?" Fauwaz ya ce "Eh Daddy Sabreen ce sister d'in Sabeen Yaya," washe da baki Daddy ya ce "Masha Allah to insha Allah zuwa jibi zamu je nema muku auren su," jefa hannu sama Fauwaz ya yi ya cafke ya ce "Yes can't wait," dak'uwa Ummi ta aika masa ta ce "Marar kunya kawai,"



Dariya Maleek ya yi ya mik'e ya yi hanyar barin falon zuciyar sa fal farin ciki.




Sabeeha ce zaune gefen gadon su sai murmushi take saki domin ganin Maleek yau cikin k'oshin lafiya ba k'aramun faranta mata ya yi ba ga wani fallele da ya k'ara zama.




Sabreen ce ta shiga d'akin ta fara dube-dube ta ce "Dear kinga earphone d'ina?" Girgiza kai Sabeeha ta yi cigaba da dubawar ta yi Sameeha ce ta shiga d'akin ta fad'a kan gadon ta yi shiru.



Kallon ta Sabeeha ta yi ta ce "Sister lafiya kuwa?" Mirginawa Sameeha ta yi ta d'ora kanta saman cinyar Sabeeha ta ce "Dear guess what?" Girgiza kai Sabeeha ta yi Sabreen ma barin abinda take yi tayi ta zauna gefen Sameeha.





"Hmm ya Umar ne fa yace na sanarwa da Abba zai turo iyayen sa," ihun murna suka saki Sabreen kuwa tashi ta yi ta rawa tana cewa "Wayyo dad'i kice mun kusa mu kwashi kodumo abinmu," Sameeha kuwa tun ihun su na farko ta tashi zaune ta tank'washe k'afar ta tana kallon su.




Daga zaune Sabeeha ta k'waso shoky sannan ta rungume Sameeha ta ce "Congratulations dear," Doctor ce ta shiga d'akin da sauri tana gyara d'aurin d'an kwalin doguwar rigar jikin ta ta ce "Lafiya ku ke aminan Abba irin wannan ihu haka?" Gurin ta su Sabeeha suka yi suka rungume ta suna nuna mata Sameeha.




Sabreen ta ce "Mama ya Umar ne yace zai turo iyayen sa ayi maganar auren su da Sameeha dear," Sabeeha ta ce "Mama ki sanar da Abba ko mu zamu fad'a masa?" Girgiza kai Doctor ta yi ta ce da Sabeeha "Ke ni cikani marasa kunya wato kune zaku fad'a masa ko," sakin ta Sabeeha ta yi tana dariya wayar ta ce ta fara ringing d'agawa ta yi daga can Maleek ya ce "Sabee na Ina waje," ta ce "Ok gani nan," ta kashe wayar ta d'auki mayafin ta ta fice tana cewa "Mama ki fa fad'awa Abba karki manta," murmushi Doctor ta yi cikin jin farin ciki mara misaltuwa.



Sabeeha tana fita ta hange shi tsaye a jikin motar sa da gani sabuwa ce fara sol da ita ya hard'e hannayen sa a k'irji yana kallon ta har ta k'arasa ta ce "Barka da zuwa," har lokacin kallon ta yake yi kamar ranar ya fara

Please Login or Register in order to submit comment