Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hannuna a ciki," sai da Abba ya razana girgiza Kai kawai ya yi domin bai tab'a tunanin Kawu ne ya yi masa haka ba domin a tunanin sa d'an uwan sa ai sai dai yaso cigaban sa amma gashi d'an uwan nasa ne da hannu cikin kashe masa wajen sana'a.




Kawu ya cigaba da cewa "Sannan Maryam ki gafarceni neman Maryam da akayi aka rasa mune sila domin mune muka je wajen bokanya ta yi mana aiki akan a b'atar da ita sannan a mantar da ita k'auyen da duk mutanen k'auyen ballantana mijin ta da yaranta amma da Allah yaso asirin mu ya tonu sai rana d'aya bamu barbad'a maganin da ta bamu ba akan musa kullum ba daga nan bokan ya ta tabbatar mana cewa dole Maryam zata dawo sannan zamu d'and'ana talauci mai zafi haka kuwa aka yi abinci ma gagarar mu yake yi duk wata kadara ta mu sai da muka siyar ga Kuma Zainabu a gida saboda itama asirin da muka yiwa Sadam ya karye shine ya korata gida Dan Allah ku yafe mana munyi hakan ne saboda sharrin shaid'an da Kuma hassada saboda Sanin Maryam wacece da Kuma kud'in iyayen ta hakan ne yasa mana hassada da rashin son cigaban ku amma munyi nadama,"



Abba duk sanyi AC dake falon amma goge gumi yake yi jin aika aikar da yayan sa ya yi Doctor ma jikin ta duk ya yi sanyi a hankali hawaye suka zubo kan fuskar ta jin akan wani Abu na duniya ake neman hallaka ta ga rabata da 'ya'yan ta da aka yi da kuma mijin ta a lokacin da tafi buk'atar su a lokacin da ta rasa nata mahaifan gaskiya su Kawu sun cutar da ita a rayuwa.




Lantana ta ce "Duk abinda malam ya fad'a gaskiya ne amma Dan Allah ku yafe mana dan girman Allah munyi nadama tun ba yanzu ba," wata uwar harara Sabeeha ta zabga Mata domin wata sabuwar k'iyayyar su taji a ranta domin jin duk sune silar jefasu a wata rayuwar a baya wacce ba dan Allah ya tsare su ba da sun fad'a wata rayuwar daban.



Sameeha kuwa hawaye ta dinga gogewa Sabreen kuwa itama tsanar su ce ta ninku a ranta tab'e baki ta yi ta kauda kanta daga kallon su.




Zainabu ta ce "Dan Allah ku yafe mana ba dan halin mu ba mun aika ta laifi dukan mu ko Lantana?" Harara Sabeeha ta wurga mata taja wani dogon tsaki jin yadda 'ya ke gatsa sunan mahaifiyar ta kamar ta Kira sa'ar ta.




Da kallo mutanen wajen suka bita Zainabu kuwa sai wurga ido take yi tana k'arewa falon kallo domin yafi Wanda aka kaisu kyau tana ganin can d'in kamar ba a Nigeria ba sai ga Wanda ya fi shi gashi sunci abincin da basu tab'a cin mai dad'in sa ba ga kaji sai da suka bar su da lemuka.




Abba ya yi ajiyar zuciya ya ce "Yaya tabbas kun cutar da rayuwar mu da ta yarana Amma bakomai Allah ma munayi masa laifi ya yafe mana mun yafe Allah ya yafe mana baki d'aya," suka amsa da "Ameen," Kawu Yana hawaye ya ce "Nagode Habu nagode," Doctor ma ta ce "Nima na yafe muku," godiya sosai suke yi sannan suka kalli 'yan uku tun kafin su yi magana Sameeha ta ce "Mun yafe,"




"Kin yafe dai," cewar Sabreen Sabeeha kuwa wayar k'arya ta fara ta mik'e tabar falon domin idan ta ce zata yi magana to maganar da zata fad'a baza ta yi dad'i ba.



Doctor kuwa ita kunya ma suka bata ta kalli Kawu ta ce "Yaya kayi hak'uri," Kawu ya ce "Bakomai Maryam yarana ne ai Kuma a abinda nayi musu a hakan ma ba k'aramun hak'uri suka yi ba," Doctor kuwa kallon Sabreen dake zaune ta yi kicin-kicin ta yi ta yi k'wafa.



Abba ya ce "Yaya kuje ku huta nasan kun gaji nima zan fita ne," tashi su Kawu suka yi zuwa part d'in da aka sauke su Abba Kuma ya hau mota ya fita.




Da daddare har d'aki Doctor ta samu su Sabeeha ta fara yi musu fad'a baji ba gani sai da ta gama fad'an ta sannan tabar d'akin.




Sameeha ta ce "Dan Allah ku fahimci Mama maganar ta gaskiya ne ku yafe musu ko mu muna yiwa Allah laifi Kuma ya yafe mana duk abinda suka yi mana ba gashi sunyi nadama ba Kuma da sunsan wannan ranar na tafe da baza su aika mana haka ba," tab'e baki Sabeeha ta yi ta fice daga d'akin domin ita tana da wani hali rik'o ne da ita sosai sannan idan tayi fushi akan abu to ana shan wuya kafin ta sauko.




Har Sabreen zata tashi Sameeha ta rik'o hannun ta tana hawaye da sauri Sabreen ta zauna ta ce "Subhanallah dear ki dena kuka please," cikin hawaye Sameeha ta ce "Haba dear kuna ganin ya dace Mama tayi fushi da ku laifin fa da su Kawu suka yi mata yafi namu girma rabata suka yi da duk wani farin cikin ta suka rabata da mu duk da kuwa soyayyar dake tsakanin uwa da yaran ta Amma ta yafe musu meyasa mu bazamu yafe musu ba bai kamata mu zama d'aya da su ba," ajiyar zuciya Sabreen ta yi ta ce "Nagane dear,"





"Yawwa sister me muje mu bawa Mama hak'uri," Sameeha ta fad'a tare da jan hannun Sabreen suka fita daga d'akin a falo suka samu Sabeeha nan itama suka kashe mata jiki da maganganun su tashi ta yi suka tafi bawa Doctor hak'uri amma ta k'udurta a zuciyar ta babu ruwan ta da su Zainabu.



A d'aki suka samu Doctor tana waya da Ummi sai da ta gama sannan ta kalle su ta kawar da kai tashi Sabeeha ta yi ta zauna gefen doctor ta yi Mata side hug ta ce "Kiyi hak'uri kinji Mamana baza mu k'ara ba," Sabreen ma ta rungume ta ta d'aya side d'in ta ce "Please Mama we promise that we will not do it again," ajiyar zuciya Doctor ta yi ta ce "Shikenan na hak'ura ku rungumi 'yar uwar ku ku koyar da ita abinda bata saniba idan tayi ba daidai ba ku nuna mata kuskuren ta bata da wad'an da suka fi ku Allah ya yi muku albarka," suka amsa da "Ameen uwa ta gari," daga haka suka fita daga d'akin.





Washe gari da safe Doctor Abba da Kawu suka je asibiti aka duba shi aka bashi magunguna aka yi masa allurai sannan suka koma gida da yamma Doctor ta kira 'yan uku suka same ta a falo ta ce "Yawwa amininan Abba ku tafi da Zainabu kuyi musu shopping," suka amsa da "To," sannan suka tafi domin shiryawa.





Suna fita compound d'in gidan Sabeeha ta ce "Kuje ku kira ta mu tafi domin nidai bazan je ba," basu ce Mata komai ba suka nufi part d'in da su Kawu suke.





Da Sallama suka shiga falon Lantana da ta k'urawa TV idanuwa ta waiga tare da amsa sallamar tana ganin sune ta washe baki tana yi musu Sannu da zuwa k'arasawa cikin falon suka yi suka gaishe ta ta amsa tana washe baki tab'e baki Sabreen ta yi domin gani ta yi daban da lantana nayi musu fara'a domin ba saba ganin hakan suka yi ba ta ce "Ina Zainabu fa zamu fita ne," Lantana ta ce "Tana ciki Zainabu!," Ta k'wala mata kira.




Daga ciki Zainabu ta amsa ta fito tana ganin su Sameeha ta k'arasa da sauri ta tsugunna ta ce "Ina wunin ku," abin ya basu mamaki amma suka basar suka ce "Lafiya," Sameeha ta ce "Ki shirya zamu fita shopping yanzu," ta ce "To," sannan ta juya zuwa d'akin ta.





Wayar Sabreen ce ta fara ringing Sabeeha ce ke kiranta picking ta yi ta ce "Dear," daga can Sabeeha cikin masifa ta katse ta "Wai me ku ke jirane ku ka barni a waje ba dai wannan banzar ku ka zauna jira ba Wallahi ku ka yi wasa bazan je ba mtsww," ta ja tsaki dafe Kai Sabreen ta yi ta ce "Ya Salam calm down dear,"






"Ank'i ayi calm down d'in," Sabeeha ta fad'a tare da hanging d'in Kira ta bud'e gaban motar ta zauna tana jan tsaki sai gasu sun fito sun nufo motar.



Bud'ewa suka yi suka shiga Zainabu ta kalli Sabeeha ta ce "Ina wuni," banza Sabeeha ta yi mata ta sake cewa "Ina wuni," tsaki Sabeeha ta ja ta ce "Kinga dalla malama karki dameni nace miki banji bane," shiru Zainabu ta yi Sameeha zata yi magana Sabeeha ta d'aga mata hannu hakan ne yasa ta ja bakin ta ta yi shiru.





Har suka je ba Wanda ya yi magana suna shiga suka fara siyayya Sabeeha kuwa kujera ta samu ta zauna tana waya da Maleek can ta mik'e wani ring ne ya d'auki hankalin ta ta d'auka sannan suka nufi wajen biya suka bi ya sannan suka bar wajen.





Direct wajen tailor d'in su suka wuce suka bayar da d'inkuna sannan suka wuce gida har cikin falo Zainabu ta bisu suka samu Doctor tana danna laptop ta ce "Kun dawo "yammata na?" Suka ce "Eh Mama," zama suka yi Zainabu Kuma ta zauna a k'asan carpet ta ce "Mama mungode Allah ya saka da alkhairi," Doctor ta ce "Bakomai ai kema 'yata na d'auke ki," tsaki Sabeeha ta ja a ranta ta ce baki iya fad'awa uwar ki Mama ba sai na neman suna.





"Lafiya kuwa?" Mama ta tambayi Sabeeha Sabeeha ta ce "Kaina ke mun ciwo Mama Bari na shiga ciki," tana fad'ar haka ta d'auki hand bag d'inta ta haura stairs.






Haka rayuwa ta cigaba da tafiya Sam Sabeeha bata shiga harkar Zainabu ko gaisuwar ta bata amsawa duk da Zainabu yanzu part d'insu take wuni amma ko kallo bata ishi Sabeeha ba su Sabreen kuwa sosai suke fira da ita sannan suna son yaron ta Habibu da suke Kira Habibi itama Sabeeha tana kula shi amma idan Zainabu bata wajen haka ma Lantana tana zuwa part d'in su yi fira da Doctor.





Kawu Bala kuwa ya warware tare ma suke fita da Abba inda Abba ya mallaka masa d'aya daga cikin super markets d'insa farin ciki wajen Kawu Bala ba a magana sannan 'yan uku ma sun sake da shi Banda Sabeeha da iya gaisuwa ke had'a su da haka har suka yi sati biyu lokacin bikin 'yan uku ya taho.




Sabeeha ce ta fita compound d'in gidan saboda Kiran da Maleek ya yi mata a tsaye ta same shi yasha kyau sosai cikin k'ananan kaya farare ya had'u sosai sai k'amshi yake zabgawa gashin kansa sai shek'i yake yi k'arasawa ta yi ta ce "Barka da isowa sanyin idaniya ta," murmushin da ya bayyana dimples d'insa ya yi ya ce "Yawwa barkan ki da fitowa matata,"




Zainabu ce Ke tahowa domin zuwa part d'in doctor ta hangi su Sabeeha tsaye ita da wani balarabe suna fira suna dariya murza idanunta ta yi tana so ta tabbatar mafarki take yi ko da gaske ne ba indiye ne a gaban ta a hankali take takawa kamar tana jin tsoro sai da ta k'arasa wajen su ta kasa wucewa ta tsaya kallon Maleek da baisan da ita a wajen ba.



Sabeeha na ganin ta had'e fuska ta ce "Ke Kuma fa zaki wani zo ki tsayawa mutane a nan dalla janye tsunmar rayuwar ki kibar nan," d'an kallon Zainabu Maleek ya yi da sauri ta durk'usa ta ce "Ina wuni," Maleek ya ce "Lafiya," mamaki Zainabu ke yi a zuciyar ta ta ce kunji yana jin hausa sannan ta kalli Sabeeha ta ce "Ina wuni aunty," tsaki Sabeeha ta ja bata amsa ba tashi Zainabu ta yi tabar wajen da sauri kafin wani wulak'ancin ya biyo baya.


Kallon Maleek Sabeeha ta yi ta ce "Mu k'arasa ciki," binta ya yi suka wuce suna shiga falon ya zauna ta kawo masa drink da ruwa ta zauna kujerar dake facing Wacce yake kai ya ce "Baby waccan d'in wacece?" Tab'e baki ta yi ta ce "Yarinyar Kawu ce," take Maleek ya gano Kawu da Kuma abubuwan da Kawu ya yi musu hakan na nufin kenan Sabeeha na rama abinda aka yi musu ne basar da tunanin ya yi ya ce "Me tayi Miki haka?"


"Tayi mun abubuwa da yawa wallahi a rayuwa ita ta fara fad'a min maganar da ta hargitsa mun tunani wallahi sannan yarinyar bata da kunya," d'an murmushi ya yi ya ce "San girma ko?"




Dariya ta yi ta ce "Haba na girme ta fa dan dai kawai ta rigani aure ne," zare ido Maleek ya yi ya ce "Kina nufin tana da aure ne?" Gyad'a kai ta yi ta ce "Har da yaro ma yanzu dai basa tare da mijin nan dai ta bashi labarin sadam," jinjina kai Maleek ya yi ya ce "Lallai wannan d'an rainin wayau ne any way zansan abinda zanyi," daga haka suka canja firar tasu zuwa ta soyayya.


Washe gari Sabeeha na zaune a d'aki tana kallon wani American film a wayar ta Zainabu ta shiga d'akin da Habibu a hannunta sai kuka yake yi bata.




Kallon Sabeeha ta yi batasan wacece ba a cikin 'yan uku ta ce "Aunty Sameeha ce?" Banza Sabeeha ta yi da ita saima tab'e baki da tayi hakan yasa Zainabu ta fahimci Sabeeha ce ta ce "Ina wuni Aunty," Nan ma Sabeeha taba banza ajiyar ta juyawa ta yi a sanyaye zata fita daga d'akin Sabeeha ta ga yadda Habibi ke kallon ta yana kuka sai yaron ya bata tausayi sosai gashi dama tana son yaron sosai.





Zare earphone d'in kunnen ta ta yi ta ce "Ke zonan," waigawa Zainabu ta yi ta k'arasa gaban Sabeeha ta zauna a k'asa ta ce "Gani," tashi zaune Sabeeha ta yi ta ajiye wayar ta gefe inda pretty ke bacci ta ce "Lafiya Habibi yake kuka kuwa?" Cikin mamaki Zainabu ta ce "Wallahi aunty bansani ba tun d'azu yake kuka yak'i yaci komai amma naji jikin sa da zafi," d'an jinjina Kai Sabeeha ta yi sannan ta mik'e tsaye ta ce "Mama tana asibiti kuje ki shirya mu kaisa asibitin su Sameeha dear sun fita unguwa," Zainabu ta ce "To," sannan ta fita daga d'akin Sabeeha ma wanka ta shiga tana fitowa ta shirya a gurguje cikin doguwar rigar less d'inkin buba orange color tasa red d'in mayafi ta d'auki handbag d'in ta da jakar ta ta fice.



A compound d'in gidan ta samu Zainabu na jiran ta Faisal ta Kira suka shiga motar ya jasu zuwa hospital suna zuwa Sabeeha na fita daga mota idanunta ya sauka akan Maleek da Salman ya bud'ewa mota da alama daga cikin asibitin yake.




Shima kamar ance ya kalli gurin suka yi ido hud'u a tare suka sakarwa juna murmushi.




K'arasawa wajen sa Sabeeha ta yi Zainabu ta gaishe shi ya amsa yana kallon Sabeeha ya ce "Sabee na kinzo yin mene a hospital?" Juya fararen idanunta ta yi ta ce "Munzo wajen Mama ne ta duba habibi baya da lafiya," jinjina Kai ya yi.





"To kaima me kazo yi nan?" D'an murmushi ya yi ya ce "Nazo wajen Ummi ne," ta ce "Ok bara naje na gaida ta," Maleek ya ce "Bari na raka ki," sannan ya kalli Salman ya ce "Salman ka raka wannan office d'in Mama zamu same ta a can," ya fad'a yana nuna Zainabu Salman ya ce "Ok sir," ya juya suka jera zuwa cikin asibitin.




Tafiya suke yi suna fira suna dariya abinsu d'an gefen su Maleek ya kalla ya ga wani matashi ya d'auki hoton sa shi da Sabeeha basarwa ya yi sai kuma lokaci guda ya sake kallon inda mutumin yake ya ga wayam babu shi d'an shiru Maleek ya yi yana tunanin to meyasa mutumin ya d'auki hoton su Sabeeha ta ce "My lafiya kuwa?" Girgiza kai ya yi ya ce "Nothing muje," ya fad'a tare da yin gaba yana waige ko zai hango mutumin.




Tura k'ofar office d'in Ummi ya yi suka shiga da Sallama ya zauna kujerar dake gaban Ummi.



A hankali Ummi ta d'aga Kai tana ganin shine ta dafe goshi ta girgiza kai ta ce "Ya salam yanzu kuma wacce rigimar ka dawo sauke mun?" Washe baki ya yi tare da nuna mata Sabeeha da ido kallon ta Ummi ta yi ta ce "Daughter dama tare ku ke shine ka barta a tsaye zauna kinji daughter," zama kan d'ayar kujerar Sabeeha ta yi ta ce "Ummi Ina kwana?" Cikin fara'a Ummi ta amsa ta ce "Ba dai har gida wannan sarkin rigimammun ya je ya taho dake ba akan wannan maganar ba?" Kallon Maleek Sabeeha ta yi ya langab'ar da kai yana kallon Ummi kamar mai shirin yin kuka ya ce "Ummi kiyi shiru," hararar wasa ta yi masa ta ce "Bazan yi shirun ba dole ne na tambayi daughter nata ra'ayin," Ummi ta fad'a tana kallon Sabeeha.



Sabeeha ta ce "A'a Ummi a waje muka had'u da shi," jinjina Kai Ummi ta yi ta ce "Nan yazo yasa mun rigima ai wai next week idan an d'aura auren ku wai Dubai zaku wuce tare ni kuma nace a'a tunda yana da damar da zaku yi wata d'aya a nan d'in gara ku yi tunda idan kun tafi ba ranar dawowa ko kun shirya hakan da shi ana d'aura auren zaku tafi?" Kallon Maleek ta yi ya kashe mata ido ya yi ta kalli Ummi ta ce "A'a Ummi,"




"Sannan bayan hakan ya kuma kawo zancen to wai idan aka d'aura aure a sabon gidan sa da ya gina a nan Kaduna zaku zauna nan ma ban amince ba domin yasan akwai shirin da na shirya idan ku ka dawo daga Dubai ida zaku tare shiyasa nace ya bari sai kin dawo sai ku zauna a d'aya daga cikin gidajen sa ko ku zauna a can gida a part d'insa tunda na wata d'aya ne kawai ko kinfi so ki tare yanzu idan an d'aura auren Dan na gaji da rigimar wannan," Ummi ta fad'a tana dungure masa Kai nan ma signal Maleek ya dinga yi Mata da ido alamun tace Eh amma ta basar kamar bata ganshi ba ta ce "A'a Ummi yadda ki ka tsara d'in yafi zan zauna a can gida tare da ku," cije pink lips d'insa Maleek ya yi ta basar.



Mik'ewa ya yi fuska a had'e ya ce "Tashi mu tafi," mik'ewa Sabeeha ta yi ta ce "Ummi zamu je wajen Mama," Ummi ta ce "To ku gaishe ta," fita ya yi tana binsa a baya.



Tunda suka fita ko kallon ta bai yi ba wai shi fushi yake yi da ita ta ce "My kana jina?" Banza ya yi da ita ta yi murmushi tare da shan gaban sa ta tsaya ta ce "Ka ga ai bai kamata mu rusawa Ummi Shirin ta ba," hararar ta ya yi ya murgud'a baki ya wuce ta gefen ta.



Binsa ta yi tana kunshe dariya ganin yadda ya murgud'a mata pink lips d'insa ta ce "Ka saurareni please," d'an tsayawa ya yi ya ce "Me kuma zaki ce mun Sabee na ba dai ke bakya so ki rusawa Ummi Shirin ta ba to ni kin rusamun nawa shirin Wanda na dad'e da had'a shi kinsan dalilin da yasa na fad'awa Ummi duk haka to duk domin kece nasan kin manta cewar bake kad'ai ce matata ba to Ina so ne mu tafi Dubai tare tun ana d'aura aure amma kince a'a a gidana na Nan ma kince a'a da kanki ki ka zab'i zama cikin gidan mu Wanda nasan dole ne a raba kwana tsakanin ki da Nasreen Wanda idan aka yi hakan idan lokacin kwanan ta yazo a lokacin tafiya ta Dubai to da ita zan tafi kuma kina gani ba ruwana amma da kin yadda ana yin auren mun tafi shikenan," yana fad'ar haka ya wuce ya barta.




D'an tsayawa ta yi tana nazarin maganar sa ita Sam dagaske ta manta da wata Nasreen ji tayi kamar ta koma ta fad'awa Ummi ta yadda da maganar Maleek Amma ba dama a sanyaye tabi bayan sa.




Tana shiga ta same shi a zaune suna gaisawa da Mama itama zaman tayi a sanyaye kamar wacce aka yiwa duka kallon ta Mama ta yi ta ce "Ke Kuma fa lafiya?" Kallon Maleek ta yi idanunta har ya cika da k'walla bata ce komai ba hararar wasa Maleek ya yi mata d'an tab'e baki ta yi kamar k'aramar yarinya na shirin kuka.




Doctor ta ce "Kinga idan kuka Zaki sani a gaba kiyi min to ki fita mun a office sannan ga Zainabu can a motor tana jiran ki gaba d'aya kwanan nan rigima kike ji," Maleek ya d'an yi murmushi ya ce "A'a Mama may be baby bata jin dad'i ne ko baby?" Tashi kawai Sabeeha ta yi ta fice daga office d'in binta da ido Doctor ta yi ta girgiza Kai ta ce "Allah dai ya shirya son zaka yi fama," dariya Maleek ya yi ya ce "Sai anjima Mama," ya fice yabi bayan Sabeeha.




Tafiya take yi tana share hawaye haka kawai take jin wani mugun kishin Maleek na nuk'urk'usar zuciyar ta Wai a hakan ba tun kafin a kaita gidan.




Tana fitowa wajen asibitin daidai lokacin wata jar mota ta yi parking a gaban Sabeeha aka bud'e motar wata budurwa ta fito cikin shigar riga da wando wata ce ta fito daga gaban motar da gudu ta wuce Sabeeha d'an waigawa Sabeeha ta yi ga mamakin ta budurwar da gudun ta ta je ta rungume Maleek.
[10/25, 8:47 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️





RUBUTAWA DAGA
HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ)






SADAUKARWA GA
MY DAUGHTER SABEEHA
BILKISU Z YA'U (🅱️K)
AISHA MAGAJI DABO (AMA)




Page 23


Wani takaicin ne ya sake had'arwa Sabeeha a zuciyar ta da gudu ta k'arasa motar su ta bud'e ta shiga ta ce da Faisal "Muje," ya ja motar suka tafi.




Maleek kuwa janye wacce ta rungume shi daga jikin sa ya yi ya kalli fuskar ta ya ce "Yammatan Momcy saukar yaushe," budurwar Mai suna Haneefa ta ce "Yaya yanzu muka zo fa Ina My sweet mom wajen ta muka zo," kafin ya yi magana d'ayar ma tazo ta rungume shi ta ce "Oyoyo Yaya," ya ce "Hanfa har yanzu bakwa girma ko?" Sakin sa wacce ya kira da Hanfa ta yi ta tura baki ta ce "Kai Yaya duk fa murnar ganinka ce Ina sweet momma fa Ashe har yanzu baka hana momma zuwa hospital ba to yaushe zaka Kai mu wajen auntyn tamu?" Ajiyar zuciya ya yi ya ce "Kun fara ba Ummi na ciki a office gashi nan garin rawar kan ku zaku kashe mun aure,"




"Aure fa Yaya har an d'aura ne Ina take Kuma ita Sweetheart d'in," Haneefa ta fad'a d'an tsaki ya ja ya ce "Kunga ta ga kinyi hugging mijin ta in front of her and batasan alak'a ta dake ba then dama rigima take yi shiyasa ta tafi ni dai yanzu zan wuce," Hanfa ta ce "To Yaya ka kaimu wajen ta," tafiya ya fara ya ce "No idan Kun koma Rinaz ta Kai ku," daga haka ya wuce su Kuma suka nufi office d'in Ummi.


Sabeeha kuwa tana komawa gida direct d'akin su ta wuce tana share hawaye tana shiga ta samu Sabreen Sameeha da Aysha da Kuma Dija waje ta samu ta zauna tare da saurin sai ta nutsuwar ta.





Dija ta ce "Daga Ina haka Sabee?" Ajiyar zuciya ta sauke ta ce "munje hospital ne wajen Mama Habibi ba lafiya so munje an duba shi tare da Zainab," kallon mamaki Sabreen da Sameeha ke yi Mata jin yau ta kula Zainabu har ma sun fita tare basarwa ta yi ta ce "Ina Rinaz Habibty fa?"




"Hmm mun Kira ta fa ta ce zata zo akwai wasu bak'i da take jira su zo may be basu zo bane shiyasa," Sabreen ta fad'a Sabeeha ta ce "Babe's lafiya ku ke kuwa wad'an nan kayan fa?" Dariya Aysha ta yi ta ce "Duk mun siyo su ne saboda mu fitar da anko," girgiza Kai Sabeeha ta yi ta kwanta abinta bacci ne ya kwashe ta.





Lokacin da ta tashi ta tarar basa nan toilet ta fad'a ta yi wanka tare da alwala sannan ta shirya cikin pink d'in riga da siket na kanti tasa farar hula a kanta gashin gaban goshinta ya kwanta luf luf gwanin burgewa ta d'auki wayar ta ta nufi down stairs tun

Please Login or Register in order to submit comment