Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana kallon Maleek domin tunanin sa ya zurfafa akan yarinyar har da ya iya gano wani abu Wanda yake tunanin tana b'oyewa Maleek ne ta katse masa tunani da cewa "Kai karka b'atawa kanka lokaci wajen mamakin magana ta ko ka manta matsayina ta hanyar binciken masu laifi?" Girgiza Kai Umar ya yi kamar dolo ya ce "Lallai kam na Sara maka Amma kana nufin irin wannan wacce ta fita biyu ne duk da ita uku?" Gyad'a kai Maleek ya yi.




"Amma MG Wai auren ta zaka yi?" Nan ma gyad'a kai Maleek ya yi Umar ya ce "Amma Ina hango damuwa a harkar auren,"



"Me kenan?" Cewar Maleek dake kallon Umar.



"Gani nayi kwata kwata yaushe ne aka yi bikin ku da Nasreen sannan yanzu kace zaka k'ara aure?" Kad'an Maleek ya yi murmushin da ya bayyana dimples d'insa ya ce "Manta kawai nikam a kanta ba abinda bazan iya ba," yana fad'ar haka ya haye stairs.




Sabeeha Kuma tafiya take yi tana tunani a zuciyar ta yanzu mai zai faru da na fad'a masa nice ta waccan ranar shin ko laifi nayi masa yake nemana to amma indai ya kasance mai tunani irin nawa ne a iya haka zai gane nice wacce ya gani sannan bazan sanar da Sabreen firar mu da shi ba wata zuciyar ta ce amma kice da Sabreen ko ya tambaye ta tace ba ita bace itama wata zuciyar tace idan har Sabreen ta ce ba ita bace to dole kece saboda cikin ku ya ga d'aya domin dole bazai sa Sameeha a lissafi ba.




Tab'e baki ta yi ta ce zan gani ai shan gabanta da akayi ne yasa ta tsayawa cak tana kallon Nasreen dake tsaye a gabanta tana huci cikin d'aga murya Nasreen ta ce "Uban me kika je yi wajen mijina?" Kallon banza Sabeeha ta yi mata domin ta yanke hukuncin bazata d'auki wulak'ancin Nasreen ba domin idan ta ga tana raga mata to rashin mutunci Wanda ta gani a banzan ce Sabeeha ta ce "Na kai masa abinci mana," huci kawai Nasreen ke yi ta ce "Ke nifa dukan ki ban yadda dake ba sannan baki yi mun ba haka kawai naji na tsane ki," kad'an Sabeeha ta yi dariya ta ce "Nagode da tsana ta zancen yi Kuma ba lallai sai nayi Miki ba idan har nayi wa Yallab'ai," tana gama fad'in haka ta tafi tabar banza a wajen.




Binta da kallo Nasreen ta yi tana tunanin to waye yallab'an da take magana daga bayan ta ta ji Sabeeha ta ce "Bari na rage Miki aiki ba sai kin yi tunani kan wa nake magana akai ba simply ina magana ne akan Wanda aka kawoni gidan nan domin sa," tana fad'ar haka ta tafi tana dariya dan tasan dole ta kunna Nasreen.
[10/25, 7:37 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️




RUBUTAWA DAGA
HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ)




SADAUKARWA GA
MY DAUGHTER SABEEHA
BILKISU Z.YA'U (🅱️K)
AISHA MAGAJI DABO (AMA)



Page 9


Nasreen kai tsaye part d'in mahaifiyar ta ta wuce tana shiga ta samu Umma zaune 'yan aiki zagaye da ita fad'awa jikin ta Nasreen ta yi ta saka kuka mahaifiyar tata cikin rud'ewa ta ce "Lafiya maiya faru?" Cikin kuka ta ce "Wallahi Umma na gaji da abinda ya Maleek ke yi mun," kallon 'yan aikin dake wajen Hajiya Asiya tayi tuni suka bar wajen sannan ta ce "To maiya faru?" Cikin kuka Nasreen ta labarta mata abinda ke faruwa tun daga ranar da tasa 'yan aiki suka yiwa Maleek girki da kuma tura mata Rinaz da yayi ta koya mata girki har izuwa abinda ya faru tsakanin ta da Sabeeha sannan ta fad'a mata abinda Sabeehan tayi mata yanzu sai dai bata fad'a mata abinda ya faru ba ranar da aka kaita gidan ba sai dai tace wai baya bata hakk'in ta.



Cikin masifa Umma ta ce "Ke yanzu akan wata Mai aiki zaki zo kina yimun kuka to Wallahi basu isa ba me akayi akai Abdul-maleek ballantana wata banzar'yar aiki to wallahi sai sun gane kuren su kema kinsan halina sannan zancen hakk'i Kuma karna sake jinsa a bakin ki saboda dama bana buk'atar ki samu haihuwa da shi saboda dama ba zama ne ya Kai ki gidan sa ba so nake mu kwashe duk wata dukiya tashi saboda Sam ni na tsani yaron ita kuma yarinyar ki barni da ita," shiri Nasreen ta yi tana tunanin ita dai gaskiya tana son mijin nata domin irin namijin da take so ne kuma ba ma ita ba ba macen da zata ga Maleek bata ji yayi mata ba ga kyau ga ilimi ga kyau ga kud'i uwa uba bashi da wulak'anci akwai daraja mutane.




Umma ta ce "Ni tashi ki bani waje kin gama bani kunya Wai kizo kina mun kuka akan wata 'yar aiki kamar bani na haife ki ba da bazaki gyara mata zaman ta ba," tashi Nasreen ta yi ta fice tana tunanin lallai ne ta koyawa Sabeeha hankali domin akan mijin ta ba abinda baza ta iya ba.




Sabeeha kuwa tana shiga falon ta samu Ummi ta dawo daga office k'arasawa ta yi ta zauna k'asan carpet inda su Sameeha suke gaisar da Ummi ta amsa cikin fara'a sannan ta ce "Sabeeha daga Ina haka?" K'asa da kanta ta yi ta ce "Dama naje na kai abinci ne," jinjina kai Ummi ta yi sannan ta ce "Ina k'ara baku hak'uri akan abinda ya faru shima Son sai daga baya yaji gaskiyar abinda ya faru Kuma bai ji dad'i ba Yana da son mutane kawai rashin fahimta aka samu," Sabeeha ta ce "Wallahi Ummi bakomai," Nan suka cigaba da fira suna dariya a haka Fauwaz ya shiga ya samesu ya ji dad'in dawowar su shima zama ya yi ya aka cigaba da firar da shi ana dariya Fauwaz duk miskilancin sa yaba son 'yan uku domin suna burgesa gasu da shiga rai musamman ma Sabreen domin tana burge shi akwai ta da barkwanci da surutun tsiya.



Washe gari Ummi ce ta fito cikin shirin zuwa office ta samu Sabeeha tana jera breakfast a daining har k'asa Sabeeha ta durk'usa ta gaida ita Ummi ta amsa cikin fara'a ta ce "Ni zan fita office," Sabeeha ta ce "Amma ai Ummi baki yi breakfast ba," kallon diamond watch d'in hannunta Ummi ta yi ta ce "Wallahi na kusa late ne Kuma akwai patient d'in da zan duba nayi breakfast d'in a office kawai," Maleek ne ya shiga falon yasha kyau cikin black d'in shadda yayi matuk'ar kyau kansa ba hula sai sumar sa da tasha gyara sai kyalli take yi yana zabga k'amshi.




Yana k'arasawa ya ce "Good morning Ummi," ta ce "Morning Son," ya ce "Amma ba fita zaki yi yanzu ba?" Ta ce "Fita zanyi har zanyi late ma Sabeeha ki bashi abinci yaci sai na dawo," tana fad'ar haka ta yi hanyar fita zama ya yi a kan sofa ya ce "Nima Ummi zan biyo ki yanzu," ta ce "Alright sai ka iso," Sabeeha ta ce "Allah ya kiyaye hanya,"


"Ameen," Ummi ta amsa tare da ficewa juyawa Sabeeha ta yi zata koma kitchen d'in ya ce "Ki kawo mun breakfast d'in," ba musu ta had'a masa ta nufi inda yake ta ajiye masa komai kan center table ya ce "Baki iya gaisuwa ba ko?" Kunya ce ta kama ta ta ce "Ina kwana," banza ya yi kamar bai jita ba ta Kuma cewa "Ina kwana," ya ce "Ina fa jinki amsawa ne bazan yi ba saboda rok'a nayi," shiru ta yi tare da barin wajen.




Su Sameeha ne suka shiga falon ita da Sabreen da Kuma Rinaz har k'asa suka gaishe shi ya amsa cikin fara'a Sabreen ta yi magana saitin kunnen Sameeha ta ce "Wow Sameeha dear kalli dimples Wallahi kyakkyawa ne," dariya kad'an Sameeha tayi sannan suka haye stairs zuwa d'akin Rinaz.



Maleek kuwa yana gama breakfast d'in ya fice ya hau mota zuwa hospital lokacin da sojojin sa suka yi parking ya yi daidai da zuwan doctor Maryam tana gama parking ta fita daga motar tasha gayu sai k'amshi take yi lokacin Maleek ya fito daga mota har wajen ta ya k'arasa har k'asa ya tsugunna ya gaishe ta ta amsa cikin fara'a ta ce "Yaron Ummi an biyo ta kenan?" So sa Kai ya fara yi sannan ya nufi cikin asibitin yana tunanin kamar yasan Wanda ke kama da Doctor Maryam amma bazai iya tunawa ba da wannan tunanin ya shiga office d'in Ummi.



A kujerar da patient ke zama ya zauna ya ce "Doctor nazo a dubani ne?" Kallon sa Ummi ta yi ta girgiza kai ta ce "Me yake damunka?" Ya ce "Ciwon nan yake yi kuma sanadin wata yarinya," ya fad'a yana nuna saitin zuciyar sa zare ido Ummi ta yi ta ce "Dagaske kake yi yana yima ciwo muje na duba ka," ta fad'a a d'an rikice dan ta d'auka dagaske yake yi.



Murmushi ya yi ya ce "A'a fa doctor wasa nake yi," ajiyar zuciya Ummi ta yi sannan ta rik'o kunnen sa ta ce "Wato ka mayar dani k'awar tsokanar ka ko?" rik'e hannun Ummin ya yi ya ce "Ouch Ummi da zafi," dariya ta yi ta ce "Kai sai kace ba soja ba," shima dariyar ya yi ya ce "Ummi kinsan wani abu?" Girgiza kai ta yi ya langab'ar da kai ya ce "Banfa san wacece nagani ba waccan lokacin ashe dama su uku ne nasani dai ba Sameeha bace," dariya Ummi ta yi ta ce "Kuma ni ba ruwana ba Kai da kake gano masu laifi wannan ma ka gane da kanka," shiru ya yi ya ce "Shikenan Ummi zan gano ta da kaina," Nan suka yi ta fira abinsu.




Da yamma Sabeeha ce a kitchen tana girki Sabreen na taya ta tana yi tana cin popcorn Fauwaz ne ya shiga kitchen d'in ya samu Sabreen ta zauna kan kujera tana cin popcorn d'in ta gurin ta ya nufa yakai hannu ya d'ibi popcorn d'in ya ce "yane parrot me ki ke yi a nan dan nasan ba wani iya abinci kika yi ba?" Hararar wasa ta yi masa ta ce "Ya Fauwaz nice Wai ban iya girkin ba aikuwa na iya idan nayi ma girki kaci sai kunnen ka d'aya ya tsinke," dariya ya yi ya ce "Tabd'ijan ban yadda ba wai Sabeeha haka ne?" Ya fad'a yana k'arasawa inda Sabeeha ke yi aiki murmushi ta yi ta ce "Ta iya mana," ya ce "Aikuwa zan gani wataran yanzu dai parrot tashi kije ki shirya ki rakani unguwa," tsalle Sabreen ta yi kamar 'yar baby ta ce "Yawwa ya Fauwaz kamar kasan yawo nake so wallahi bari naje na shirya karfa ka tafi ka barni," ya ce "Ok Ina jiranki a falo," ya fad'a tare da fita daga kitchen d'in itama ta fice zuwa d'akin su a can ta samu Sameeha kwance tana bacci.





Hadiza ce ta shiga kitchen d'in ta kalli Sabeeha ta ce "Ya akayi naga Sabreen da gudu haka?" Dariya Sabeeha ta yi ta ce "Wai zata raka Ya Fauwaz unguwa ne shine take murna," Hadiza ta ce "Lallai jinin su yazo d'aya sosai dukan ku ma naga har dariya yake yi muku kuyi ta wasa da dariya," Sabeeha ta ce "Hmm ai haka yake," Hadiza ta ce "Tab Wallahi ba haka yake ba miskili ne duk 'yan aikin gidan nan ba ruwan sa da kowacce iya kaci mu kai masa abinci yaci bai da sakin fuska ga kowa sai yayan sa da sauran 'yan gidan nan amma yayan sa yana da fara'a babu ruwan sa duk da shima bai da shiga harkar mutane amma yana da kirki shi dai idan Kinga ya canja mana fuska to sai dai idan abinci aka Kai masa domin shi bai cin girkin mu amma Oga Fauwaz ya tab'a korar wata 'yar aiki dan kawai tace tana son sa," dariya Sabeeha ta yi ta ce "Ikon Allah," Nan dai suka yi ta fira har Sabreen ta shigo kitchen d'in tasha kyau cikin maroon d'in doguwar riga ta ce "Sabeeha dear nayi kyau kuwa?" Kallon ta Sabeeha ta yi ta ce "Sosai ma dear sai Kun dawo," ficewa Sabreen ta yi ta samu Fauwaz a falo yana jiran ta ta k'arasa ta ce "Ya fauwaz na shirya," ya ce "Wow kinyi kyau muje," suka fita a kitchen Sabeeha ta ce "Ni kuwa na rasa sanda shak'uwa ta shiga tsakanin su Wallahi," Hadiza ta ce "Au Wai baki saniba ni kuwa Ina ganin su a garden suna fira suna dariya," jinjina kai Sabeeha ta yi ta ce "Ok idan kuwa bata nan tana cemun tana garden," Nan dai sukai ta fira abinsu.


Sabeeha na gama aikin ta takai komai daining ta jera sannan ta koma d'akin su tayi wanka har lokacin Sameeha na bacci sannan Rinaz ma bata nan dan haka tana gama Shirin ta ta fice daga part ta fara yawo cikin gidan tana kalle kalle abinta.




Nasreen ce da Umma suka fito zasu unguwa ya yinda 'yan aiki uku ke binsu a baya d'aya na rik'e da hand bag d'in Umma tafiya suke suna fira abinsu Nasreen ce ta fara hangar Sabeeha ta ce "Umma kin ganta can duk da ba lallai idan ita ce amma zo muje," Umma ta ce "sa aninta ne mu da zamu je wajen ta?" ta kalli d'aya 'yan aikin ta ta ce "Ke Huwaila je ki kira mun waccan yarinyar," ta fad'a tana nuna mata Sabeeha.




Huwaila taje ta fad'a mata waigawa Sabeeha ta yi ta kalle ta sannan ta nufi wajen tana zuwa ta kalli Umma ta ce "Ina wuni?" Kallon banza daga Umman har Nasreen suka bita da shi ganin hakan Sabeeha ta ce a ranta ashe irin su d'aya.



Umma ta ce "Ke meye sunan ki?" Ko kallon ta Sabeeha bata yi ba ta ce "Sabeeha nake," jinjina kai Umma ta yi ta ce "To abinda nake so dake tun kafin na shiga maganar ki raba kanki da mijin 'yata sannan ki tsaya a matsayin ki na baiwa,"

"Waye mijin 'yar taki da kike magana Wai?" Nasreen ta ce "Umma Kinga halin ta ko kawai ki bari na kira Daddy na fad'a masa," Umma ta ce "Ki kyale ta ba sai baban ki ya ji ba ni nan zanyi maganin ta," Sabeeha kuwa juyawa kawai ta yi ta tafi tabar banzaye a wajen.




Tafiya suka yi su ma kowaccen su na ayyana abinda zata yi mata ita kuwa Sabeeha ta dad'e tana zaga gidan sannan ta nufi part d'in Ummi tana shiga ta samu Ummi ta dawo tana zaune a falo yayin da Maleek ke tsaye ya ce "Ummi bari naje sai na dawo," ya fad'a Yana yin hanyar fita Ummi ta ce "Tom son," kallon Sabeeha ya yi kamar zai yi magana sai Kuma ya yi shiru ya wuce ta a wajen ya fice.



K'arasawa ta yi ta ce "Sannu da dawowa Ummi," Ummi ta ce "Yawwa ya gidan?" Ta ce "Lafiya Ummi," tashi Ummi ta yi ta ce "Bari naje na d'an watsa ruwa," Sabeeha ta ce "To Ummi,"



Da dadare Sabeeha ce Zaune a gefen k'aton gadon su Sameeha kuma tana kan sallaya ta idar da sallah magrib Sabreen ta siga d'akin ta ajiye ledar hannunta ta kwanta a kan gadon Sameeha ta ce "Sabreen Wai Ina kika je ne haka?" Sabreen ta ce "Wallahi yawo muka je da ya Fauwaz munje wajen cin abinci munje munsha ice cream Kai munyi yawo sosai ga naku nan ma a leda," d'auka suka yi suna sha Sabeeha ta ce "Wai Sabreen dear meye sirrin ne?"


"Na me fa?" Cewar Sabreen Sameeha ta ce "kamar ya tsakanin ki da ya Fauwaz mana," dariya ta yi ta ce "Bakomai kawai jinin mu yazo d'aya ne," shiru kawai suka yi basu k'ara cewa komai ba.



Bayan sati d'aya shak'uwa ce mai k'arfi ta shiga tsakanin Fauwaz da Sabreen kullum cikin yawo suke haka Kuma sun saki jikin su a gidan suna harkokin su kamar gidan su.



Maleek ne ya yi parking a k'ofar part d'in Ummi sai dai tun kafin ya shiga falon yake jin kid'a na tashi mamaki ya fara to waye da wannan aikin shiga kawai ya samu bakowa a falon sai wak'ar dake tashi a falon girgiza Kai ya yi bai kashe ba ya nemi can gefe ya zauna Yana danna wayar sa.




Sabeeha ce ta fito daga kitchen hannunta rik'e da glass cup da zob'o a ciki sanye take cikin pink d'in doguwar riga Mai dogon hannu tana fita falon ta fara bin wak'ar Hamisu breaker da ta cika falon "Duk tsanani ya zam mini sauk'i da cikar samun d'an kirki ka d'orani a mulki tilas ne na tsananta kula kai mini uzuri shi nake maula zana had'a maka daula a guna kaiwa maza zarce domin kullum kai nake zance shigar ka irin ta daban ce Mai sona annurina Kuma angona ni rok'on da nake maka sirrin mu rik'e shi ta damk'e," ta fad'a tana yin juyi tare da d'ebo shoky da hannun ta d'aya.



Maleek dake gefe sai kallon ta yake yi yana dariya ita kuwa batasan Yana wajen ba sai rawar ta take yi ta canja wak'ar zuwa wak'ar Mandydollz ft-selebobo (jealousy) tik'ar rawa kawai take yi.



Juyawa ta yi da niyyar ajiye cup d'in hannun ta kan center table kawai suka had'a ido da Maleek da ke tayiwa rawar tata dariya cak ta tsaya ga wata kunya ta rufe ta kamar ta nutse.




Har ya tashi bata motsa ba ta gaban ta ya wuce ya kashe kayan kid'an sannan ya kalle ta tuni tayi k'asa da kanta sannan a hankali ta juya ta nufi stairs ya ce "Baki ji ba" tsayawa ta yi ba tare da ta waiga ba ya ce "Kece Sabeeha right?" Saurin girgiza kai tayi alamun a'a.



Dariya ya yi ya ce "Hakan na nuna kece Sabeeha saboda haka turomun Sabreen," ya fad'a tare da zaunawa ita Kuma ta haye stairs d'akin Rinaz ta shiga ta zauna kan kujera Rinaz da ta fito daga wanka ta ce "Sabeeha dear yane naji kin kashe kid'an?" D'an sosa goshi ta yi ta ce "Ammm dama yayan ki ne ya shigo shine fa ya samu ina rawa," dariya suka shek'e da ita tare da su Sameeha.



Had'e rai Sabeeha ta yi ta ce "Sabreen kije inji sa," zare ido Sabreen ta yi ta ce "Ni kuma maiya faru?" D'aga kafad'a Sabeeha ta yi ta ce "Oho kije dai," tashi Sabreen ta yi ta fice a zaune ta same shi yana danna waya tace "Ina wuni ya Maleek," ajiye wayar ya yi ya ce "Lafiya zauna mana," zama ta yi k'asan carpet ya ce "Daman zan tambaye ki ne," ta gyad'a kai ya ce "Wani lokaci baya Kun kai Sameeha asibiti right?" Ta ce "Laa aikuwa haka ne ya akayi kasani?" D'an kallon ta ya yi ya ce "Manta kawai cikin ke da Sabeeha waye ya fita siyan magani?"



"Bani bace Sabeeha dear ce ai har wasu 'yan daba suka bita dakyar ta had'u da wani soja shine ya taimake ta ma kasan wani abu ita fa bata sanshi ba Kuma ko fuskar sa bata gani ba amma 'yan garin sunce babban soja ne Kuma sunansa MG Malee...," Shiru ta yi tana kallon sa sai Kuma ta ce "ko dai kaine?" Murmushi ya yi a zuciyar sa ya ce Na jinjinawa surutun ki a fili Kuma ya ce "Eh nine yanzu kira mun ita Sabeehan," tashi Sabreen ta yi ta nufi stairs.




Da gudu ta shiga d'akin ta ce "Sabeeha dear Wallahi shine,"


"Shi wa?" Dukan su suka had'a baki wajen tambayar ta ta ce "Shine sojan da ku ka had'u a waccan ranar sanda Sameeha sister ke asibiti," Sameeha ta ce "Dagaske Wai?" Sabreen ta ce "Wallahi kuwa," Rinaz ta ce "Dama ai ke nake tunani tun lokacin Yaya fa ke ba Ummi labarin ki Wai ya kamu da son ki," Sabreen ta buga tsalle ta ce "Wow love at first sight," Nan Rinaz ta cigaba da basu Labari Sabreen ta ce "Wayyo k'auna Sister kije fa yace," mik'ewa kawai Sabeeha ta yi ta fice tana tunanin wannan abu ba mai yuwuwa bane saboda a haka ma ya suka k'are da Nasreen balle idan ya ce Yana sonta.




Tana fita ta samu waje ta zauna ta ce "Gani," kallon ta ya yi tare da sakin ajiyar zuciya ya ce "Dama zuciya ta tafi aminta da kece wacce nagani amma meyasa waccan lokacin kika tafi?" Tura baki ta yi ta ce "Saboda sauri nake yi," murmushi ya yi ya ce "Sai yanzu na yadda da ba aljana na gani ba domin tun lokacin tunaninki kawai nake yi ban iya cikakken bacci saboda ke ina son ki," kallon sa ta yi sannan ta mik'e ta ce "Ka ga ka dena ma saboda soyayya ni da Kai babu ita," a razane ya kalle ta ya ce "meyasa?"



"Saboda ban shirya karb'an cin mutunci daga wajen matar ka ba ni bana son tashin hankali," tana gama fad'in haka tabar wajen.




Wani Abu Maleek ya ji ya daki zuciyar sa rintse ido ya yi Sam bai ji dad'in maganar ta ba duk da bata ce bata son sa ba.



Tashi ya yi yabar part d'in direct part d'in sa ya wuce ya kwanta akan bed d'insa yana jin wani iri yanzu idan tace bata sona fa wata zuciyar ta ce Insha Allahu bazata fad'a ba haka ya yi ta tunani.





Sabeeha kuwa d'akin su ta wuce ta kwanta akan bed tana tunani anya ya kamata na sanar da shi haka kuwa wata zuciyar ta ce wannan shine kawai mafita domin Nasreen bata da kirki sam musamman akan mijin ta.



Itama tunani taita yi yayinda su Sabreen ke can suna rawar murna Ummi na komawa suka bata labari itama ta yi murna sosai haka ma Fauwaz a nan gaban Ummi ya ce shima yana matuk'ar son Sabreen nan falon ya d'auki ihun murna har da Sabreen saboda itama ba kunya ta cika ba Ummi kuwa murnar da tayi ba a magana.





Da daddare suna komawa d'aki suka samu Sabeeha kwance zama suka yi Sameeha ta ce "Lafiya kuwa sister ya ku kayi da ya Maleek d'in?"



"Wai fa cewa ya yi yana sona Kuma ya dad'e yana sona," Sabreen ta ce "Ke Kuma ki ka ce me?" Tab'e baki ta yi ta ce "Ni kawai nace ya dena ma saboda bazan iya da Nasreen ba," tsaki Sabreen ta ja ta ce "Haba dear ya zaki ce masa haka karki manta ba fa auren soyayya suka yi ba beside ma tunda yana sonki ina ruwan ki da wata banzar matar sa?" Sabeeha ta ce "Hmmm Sabreen kenan akwai matsala a duk sanda na amsa ina son shi domin tunanina na bani akwai abubuwan da zasu faru idan har na amsa buk'atar sa kawai dai ku tayani da addu'a Allah ya zab'a mini mafi alkhairi," suka ce "Ameen," domin jikin su ya yi sanyi sosai.




Maleek kuwa kwana ya yi ba bacci washe gari kuwa har office ya bi Ummi ya fad'a mata yadda suka yi da Sabeeha kamar zai yi mata kuka ajiyar zuciya Ummi ta yi ta ce "Son ka kwantar da hankalin ka tabbas Gaskiya ne abinda ta fad'a akwai rikici a wannan lamarin Kai kanka kasani musamman idan Uncle d'in ku ya samu labari Kuma nasan tsoro take ji akan abinda zai je ya dawo domin bayan hakan ba wani dalili," rik'e hannun Ummi ya yi ya ce "Please Ummi ki taimaka mun Wallahi Ina sonta so mara misaltuwa Wallahi a kanta ba abinda bazan iya ba Kuma na shirya d'aukar ko wanne hukunci daga wajen uncle," shafa kansa ta yi ta ce "Ka kwantar da hankalin ka insha Allah zata amince ka ji ni dai karka sa damuwa a ranka please," bud'e k'ofar aka yi aka shiga Doctor Maryam ce ta ce "Uwa da d'a kuna tattaunawa ne?" K'asa da Kai Maleek ya yi Ummi ta ce "Wallahi kam kin ganshi nan soyayya ce damuwar sa," zama Doctor Maryam ta yi ta ce "To meye damuwar," kaf Ummi ta zayyane mata abinda ke faruwa.





Jinjina kai ta yi ta ce "Tofah ni nasan ka Kai namijin da za a so sannan Mai wuyar samu abinda za a yi kawai ku turo min ita gidana zanyi magana da ita," Ummi ta ce "To ba damuwa zata zo," Nan dai

Please Login or Register in order to submit comment