Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi shi Kuma yana wasa da gashin kanta ya ce "Baby meye sirrin ne naga fa sai wani k'ara kyau ki ke yi kullum?" Far tayi da idanunta ta ce "Kai haba My sai kace kai kullum fa k'ara maka kyau ake yi kasan dawa ka ke kama kuwa?"



Girgiza Mata Kai ya yi yana dariyar maganar sai da ta tsaya kamar mai tunani sannan ta kalle shi tare da shafa sajen fuskar sa ta ce "Kana matuk'ar kama da actor d'in Bollywood d'in nan Mai suna Mahesh babu," d'an juya Mata idanunsa ya yi alamun au hakane ta gyad'a Kai ta ce "Yes bambamcin ka da shi shine ka fisa kyau saboda ka fisa idanu shi idanunsa ba manya bane Kai Kuma naka manya ne sannan Kuma yana yin jikin ku ba d'aya ba Kai jikin ka irin na Rehan Ahmad khan ne na series film d'in nan na shu'uma sai dai shima ka fisa tsayi," kallon ta kawai Maleek ke yi yana murmushi.



"Yawwa My idan Kuma kayi dariya kasan kuwa cewar hak'oran ka irin na Amman Junaid Khan ne sai dai dariyar ka tafi tasa kyau and then Kai kana dimples su Kuma duk basu da shi sai dai gashin kanka kam sak na Rehan Ahmad khan ba bambamci haka ma fatar ka wow gaskiya My ka had'u ga sajen ka mai kashe ni da kyansa," wannan lokacin dariya kawai Maleek ya ke yi mata tura baki kawai ta yi ta ce "Au dariya ma na baka to yadda na fad'a maka ma a hakan kwatantawa nayi domin duk ka wuce nan Wallahi,"



Sai lokacin ya ce "Ok ok na yadda ai baby ke Kuma duk kinfi haka," ya fad'a tare da Kai hannun sa yana shafa cikin ta a tare suka kalli juna suna dariya ta ce "My kaji babyn yana motsawa dama fa daga ji baya ji fitinanne ne," dariya ya yi ya ce "No nikam ki dena cewa yarona mai fitina,"



"To kullum fa sai ya yi ta yi mun wasa a cikina yana naushi na," dariya Maleek ya yi ya ce "To yi hak'uri kinji hubbyna bazai sake ba," ya fad'a Yana kai kansa wajen cikin ya ce "Babyn papa ka dena naushin momman ka a ciki kaji d'an albarka," Nan ma cikin ya Kuma motsawa rungume juna suka yi suna dariya.


"Yawwa My yaushe ne zamu koma gida nayi missing kowa,"


"Uhmm ba rana nifa nafi so mu zauna a nan," zare ido ta yi ta ce "Nikam ban yadda ba Kuma ba Ummi ta ce mu tafi gida ba,"


"Shikenan jibi zamu wuce shikenan?" Noding kanta ta yi cikin farin ciki tana sakin masa wani lallausan murmushi shi Kuma ya sakar masa kiss akan soft lips d'in ta tare da mayar da ita jikin sa ya rungume ta yana jin sonta na ratsa ko wacce gab'a ta jikin sa.


Washe gari sai da suka sake fita duk da ba yadda Maleek bai yi da ita ta zauna a gida ya je ya dawo ba Amma tak'i yadda har da yi masa kuka ganin yadda tasa shi a gaba tana ta aikin kuka ne sai ya ce ta tashi su tafi shopping suka fita inda suka yiwa mutanen gida tsaraba kala-kala sannan suka koma gida bayan sun biya restaurant sunyi take away na kayan ciye ciye suna komawa gida wanka suka yi sannan suka zauna suka yi dinner sannan Sabeeha ta kunna TV tana kallo Maleek kuwa danna laptop d'in sa yake yi.





Ta ce "Yawwa Husby wai meyasa ka ke zaune a nan meyasa baza ka koma 9ja da aikin ba kayi zaman ka a office kawai tunda dama kace Kai zaman office ne naka?" Kallon ta ya yi sannan ya d'an ture laptop d'in ya ce "To Hubbyna ai nan d'in ma a office nake ko kinfi so na koma can?" Gyad'a Kai ta yi ta ce "Eh saboda bazan so ka dinga yi mana nisa ba ni da babyn ka," ta fad'a hawaye na zubo mata.


D'an zare ido ya yi ya ce "Ya Salam! Baby rigima please Bari kukan to Kuma kema ai kinsan bazan dinga barin ku a 9ja na taho nan ba ko,"



"To idan muka taho ai zanyi missing su Ummi Mama da su Sabreen dear," ajiyar zuciya ya sauke ya d'an sosa forehead d'in sa ya furzar da iska ya ce "Ina ga zan cigaba da aikina a nan amma zan koma can d'in ma nan Kuma na dinga zuwa idan buk'atar hakan ta taso kin amince?" Gyad'a Kai ta yi ta ce "Eh na yadda," ranar sun dad'e suna fira abinsu.


Sai dai lokacin da zasu kwanta Sabeeha ta fara jin cikin ta na juya Mata especially ma mararta mazewa kawai take yi bata bari Maleek ya lura da hakan ba har suka kwanta taje duk ta mak'alk'ale shi da marar ta ta juya sai ta k'ara k'ank'ame shi ya ce "Baby da wani abu ne?" Girgiza masa Kai ta yi bai Kuma magana ba ya rufe idanun sa Mai d'auke da zara-zaran eyelashes domin bacci ne sosai a idanunsa saboda ya gaji da yawa.


Sai ya yi nisa a baccin sa zai ji ta k'ank'ame shi sai mutsu mutsu take yi ba tare da ya bud'e idanun sa ba ya ce "Baby da wata matsalacce?" A hankali ta ce "Uhm uhm fa,"



"Ok ki barni nayi bacci ke baki gaji bane kwanta kiyi bacci abinki kinji," ya fad'a tare da d'ora kanta saman k'irjin sa yana shafa bayan ta ita kuwa dad'a yin luff ta yi a jikin sa saboda d'umin jikin sa da ya ratsa nata jikin.



Dakyar wani bacci ya d'auke ta amma tana yi tana farkawa idan mararta ta murd'a mata wajen k'arfe uku na dare ta tashi ta sauka k'asan gadon ta dafe cikin ta tana yarfe hannu saboda azabar da take ji sai da aka yi sallar asuba sannan taji cikin nata ya lafa ta tashi ta yi alwala ta yi sallah tana zaune saman prayer mat Maleek ya tashi shima alwala ya yi ya yi sallah sannan ya sata a gaba Yana kallon ta ganin idanunta sunyi ja ya ce "Lafiya ki ke kuwa baby?" Gyad'a Kai ta yi ta ce "Ina kwana,"



"Lafiya ya babyna?" Kallon cikin ta yi da ya yi k'asa sosai ta ce "Yana lafiya yana gaida Daddyn sa," tashi tsaye ya yi sannan ya d'auke ta cak ya kwantar saman gado ya ce "Maman baby na da baby na su koma bacci," ya fad'a tare da kwanciya gefen ta Sabeeha kuwa dama bacci take ji idanunta har rurrufewa suke yi ta cire hijabin jikin ta ta shige jikin sa a haka bacci ya d'auke ta.


Maleek ya riga ta tashi dan haka ya yi wanka ya shirya cikin wata had'add'iyar tsadaddiyar shadda brown color ta yi masa kyau sosai har hula yasa wajen gidan ya fita yasa d'aya daga cikin soldiers d'in sa ya je ya kawo musu abin breakfast domin baya barin Sabeeha girki sannan ita baza ta ci na 'yar aikin gidan ba sannan shima baza ta barshi yaci ba.



Bayan ya koma cikin gidan zama ya yi saman kujera yana danna wayar sa Kiran Ummi ne ya shiga wayar tasa da mamaki yake kallon wayar sai ya d'aga ko bari su gaisa Ummi bata yi ba ta ce "Kun fara shiri kuwa?" Murmushi ya yi ya ce "Ummi muna kan shiri ne anjima kad'an zamu taso insha Allah,"



"Allah ya kaimu ina Daughter d'in?" K'ofar d'akin ya kalla ya ce "Bata tashi ba Ummi,"



"Ok sai kunzo," Ummi ta fad'a tare da kashe wayar Sabeeha kuwa wani mugun ciwon mara ne ya tashe ta daga baccin da take yi a mugun firgice ta tashi daga baccin ta zame ta sauka k'asan dafe da cikin ta tana yarfe hannu ga wata uwar zufa da ta had'a duk da sanyin AC da d'akin ke yi sai juya Kai take yi Kira take son k'walawa Maleek amma da ta yi k'ok'arin bud'e bakin ta sai ta ji cikin ta ya murd'a a hankali ta Kai hannun ta ta laluba saman gadon ta jiyo wayar ta ta d'auko ta danna number d'in Maleek wanda tayi saving da Life partner ta yi dialing.


Maleek dake zaune a falo ganin kira daga soulmate yasa shi kallon wayar sai Kuma ya yi picking yana d'agawa ta ce "Wayyo My zan mutu," da sauri Maleek ya mik'e tare da nufar d'akin da sauri.



A durk'ushe ya same ta tana kukan wahala ya ce "Subhanallahi Baby bari mu tafi asibiti kawai," ya fad'a tare da k'ok'arin d'aukar ta.



Yunk'urawa ta yi da d'an k'arfin ta tare da sakin wani nishin wahala abin mamaki sai jin kukan jaririya suka yi a tare suka kalli juna sannan suka Mai da kallon su kan baby girl d'in dake ta tsala kuka wata nannauyar ajiyar zuciya suka sake a tare Maleek da kansa ya yanke ciki tare da k'udundune yarinyar a wani lallausan towel Sabeeha kuwa zubewa ta yi a wajen tana maida numfashi Maleek kuwa bai damu da jinin dake jikin yarinyar ba sai ma sumbata da yake ta aikawa yarinyar tako ina.

Shi da Sabeeha suka yi k'ok'arin gyara wajen domin Alhamdulillah ta haihu lafiya ba inda ke mata ciwo a haka suka gyara wajen tsaf sannan suka gyara babyn cikin wasu kayan sanyi masu matuk'ar kyau da laushi kalar purple mai haske.



Yarinyar suka kwantar sannan Maleek da Sabeeha suka shiga toilet shi a lallai sai ya taya ta wanka bata iya ba haka ta hak'ura ya taya ta ta yi wankan ta gasa jikin ta sannan suka fito ta fara shiri shima ya koma toilet d'in ya yi nasa wankan suka fito suka shirya sosai suka yi kyau abinsu Sabeeha cikin atamfa doguwar riga mai mad'auri ta gaba atamfar blue light ne da fari sai Baki a jiki ta yafa mayafi fari da takalmi da jaka Maleek kuwa cikin light blue shadda ya yi kyau har ya gaji sai k'amshi.



Shi dai Maleek bakin sa yak'i rufuwa sai kallon jaririyar tasu yake yi yana jin irin sonta mara misali a zuciyar sa ya jawo Sabeeha jikin sa sai sakar mata kiss yake yi ita kuwa sai dariya take masa ya ce "Baby muje asibiti a duba mun ke sannan mu wuce airport," zare ido ta yi ta ce "Hospital fa My nifa lafiya ta k'alau," girgiza Kai ya yi ya ce "I know amma dai duk da haka sai munje," bata sake magana ba har suka gama Shirin su suka fita compound d'in gidan da yake cike da sojoji da Kuma motoci.



Suna tsaye har aka gama zuba musu tulin kayan su a mota suka shiga sai Airport jiniya kawai ke tashi a Dubai sojojin kansu mamakin haihuwar suke yi.



Sai da suka biya asibiti aka tabbatar da ba abinda ke damun baby da mamanta sannan suka wuce Airport suka shiga jirgi suka d'aga sai 9ja.


Jirgin su na landing suka samu zugar family tare da sojoji na jiran isowar su a hankali suka fara sauka daga matakalar jirgin fuskar su d'auke da murmushi.


A gefe Kuma Ummi ce da Doctor tare da Sameeha Sabreen da Umar sai Fauwaz har ma da Nasreen da Umman ta burin su kawai suka fitowar su Maleek d'in Aikuwa sai gasu sun fito cike da mamaki suke kallon Maleek rik'e da baby a hannu ga Kuma Sabeeha ba ciki.



Ai da matuk'ar murna suka k'arasa wajen su Sabeeha kuwa bata damu da hill takalmi dake k'afar ta ba da gudu ta nufi Ummi ta fad'a jikin ta ta rungume ta sannan ta saki Ummi ta fad'a jikin Doctor ta rungume ta tana dariya yayin da Sabreen Sameeha da Nasreen har ma da su Fauwaz suka nufi Maleek suna kallon kyakkyawar yarinyar dake hannun sa mai kama da baban ta sak.


Wajen su Maleek ya k'arasa ya gaishe su suka amsa cikin fara'a Ummi bakin ta yak'i rufuwa ta ce "Son me nake gani kamar new baby?" Yana dariya ya ce "Eh Ummi Baby ce ta haihu d'azu," ai barin sa suka yi a tsaye suka nufi wajen su Sabreen dake rik'e da yarinyar suna murna har sun rasa inda zasu sa yarinyar.


Waigawa Maleek ya yi ya kalli Sabeeha dake gefen sa ya ce "Kin gani su Ummi ba ta mu suke yi ba zo mu tafi domin na gaji da yawa," hararar wasa ta yi masa ta ce "Lallai ma My d'in nan sai kace kaine ka haihu," dariya ya yi ya ja hannun ta ya karb'i key hannun Adam ya shiga driver seat Sabeeha ma ta shiga suka d'auki hanya ba tare da su Ummi sun ankara ba ya ja motar da gudu yana fad'in "Yanzu sai ki ga 'yan jarida sun cika airport d'in nan ni kuma hakan ne banso," ajiyar zuciya Sabeeha ta sauke ta ce "Nima kam baso nake yi ba kana ganin ranar da zamu tafi inda suka zagaye mu a airport d'in nan," dariya ya yi ya ce "Ke Kuma ki ka so ki nuna musu ke rigimammiya ce ba kuka fa na ga Zaki yi," dariya itama ta yi ta ce "Allah husby naga ba Kai suka fiya ba," haka suka k'arasa gida suna fira abinsu ga mamakin Sabeeha Rashida suka samu a part d'in Ummi tare da su Hadiza suna jera abinci a daining su suka tarbe su.



A airport kuwa yarinyar nan tana ganin so daga hannun wannan sai hannun waccan yarinya kuwa ba dai wayo ba duk Wanda ya d'auke ta sai ta yi masa k'urr da idanu tana kallon sa Sabreen Bata damu da cikin dake jikin ta ba ta yi tsalle ta ce "Wayyyo my heart kalla ka ga blue eyes gare ta wayyo kyau," Sameeha ta ce "Wow nikam dama a barmun," Fauwaz ya ce "Masha Allah yarinyar kama take yi da Yaya har tafi Yaya kyau ma,"



Umar dake gefen Fauwaz sai aikin hoto yake wa yarinyar ya ce "Gaskiya MG ya iya haihuwa wannan kyakkyawar yarinya haka ita ba yar indiya ba ita ba balarabiya ba,"



"Sameeha dear dai ta iya haihuwa," Sameeha ta fad'a tana k'ara kallon yarinyar "Ummi mu wuce gida ina MG d'in?" Umar ya fad'a suna waigawa suka ga ba Sabeeha ba Maleek sai tulin 'yan jarida da suka gani wajen.


Dakyar suka samu suka zille suka shiga motocin su suka tafi gida sai dai yarinya tasa hotuna da videos.


Ga mamakin su suna zuwa suka samu su Sabeeha har sun yi wanka suna zaune a daining suna cin abinci abinsu suna dariya.



A falo su Ummi suka ya da zango da baby girl da wutsil-wutsil da hannu da k'afa take yi Yarinyar daga ganin ta akwai wayo a wajen Umman Nasreen ce ta shiga falon itama ta karb'i yarinyar tana yaba kyan ta itama sai farin ciki take yi domin yanzu Allah ya shirye ta.



Kafin kace me su Fauwaz da Sabreen sai waya suke yi suna fad'ar haihuwar Rinaz dake India kuwa da su Hanfa da Hany har an cika musu wayoyin su da pictures d'in baby.


Su Zainabu kuwa suna jin haihuwar suka tafi gidan Ummi Abba da Daddy har ma da Uncle sai waya suke yi suna tambayar baby domin suma labari ya Kai musu.



Haka Baby da Maman ta ke samun kulawa a ta kowanne bangare ko yaushe gidan zaka samu ana farin ciki ana fira da dariya yayin da baby tana yin kuka hankalin kowa a gidan idan ya yi dubu ta tashi saboda so da k'aunar da ake nuna Mata a haka har ranar suna ta kusa inda ake ta yin shirye shirye ba kama k'afar yaro.



Ana I gobe suna Rinaz ta sauka a 9ja nik'i nik'i da tsarabar da ta yiwa baby su Sabeeha sai murnar ganinta suke yi da daddare Kuma su Daddy suka dira a k'asar har falon Uncle aka Kai musu baby a take Uncle ya yiwa yarinyar kyautar car key domin ji ya yi yarinyar ta shiga ransa sosai.


Washe gari suna gidan a cike yake da bak'i na kusa dana nesa su Hanfa duk sunzo da Mama Aisa har ma da su Aleem domin lokacin ansa ranar hanfa da Ashraf Hany da Alim saura wata d'aya.



Yarinya taci sunan Ummi Aysha amma suna Kiran ta da Alizah kaya kuwa yarinya tasha shi har iyayen ta sun rasa wajen sawa kyauta har da su car keys d'in da ta samu da yamma aka yi gagarumar walima ta gani ta fad'a anci ansha ba k'arya 'yan jarida da gidan televisions suka cika gidan uwar 'ya ta ci kwalliya kamar wata amarya domin idan ba fad'a maka akayi ba baza ka ce ita ta haihu ba.



Walimar babba ce domin har Nigerian army sunje inda a nan ne aka k'arawa Maleek girma daga MG zuwa Marshall social media ko Ina ka shiga su ake d'orawa a haka aka tashi yarinyar da iyayen ta sun samu kyauta babu k'arya.


Ranar da daddare Ummi tasa Sabeeha ta shirya tare da Baby alizah zuwa gidan Doctor domin su yi wankan gida Doctor su Ummi suka yi mata rakiya inda lantana ta tare su cikin farin ciki can aka cigaba da basu kulawa kullum Maleek na gidan hakama su Sabreen da Zainabu kowa ya d'orawa Alizah soyayya.


Satin su d'aya a gidan aka kawo kud'in auren Rinaz tare da saurayin ta Faruk aka sa rana one month hakan na nufin idan akayi nasu Hanfa da sati d'aya kenan Amma Daddy ya ce a had'a kawai a yi.

Haka rayuwa ta cigaba da kasancewa har Sabeeha ta yi arba'in da haihuwa inda a lokacin Kuma zasu tare a sabon gidan su.



Haka suka tare a sabon gidan su da ya gaji da had'uwa Ummi ce ta zuba komai na gidan tun daga compound d'in gidan za kasan mai gidan ba wasa b'angaren kud'i saboda motocin dake parking space baza su irgu ba da nasa dana matar sa da Kuma na baby Alizah balle ka shiga ciki fad'ar had'uwar gidan ma b'ata lokaci ne su Sabreen sai santi suke yi d'akin baby Alizah kuwa ba a cewa komai saboda tsabar had'uwar sa yaji kayan wasa komai na d'akin baby pink ne gwanin sha'awa haka aka watse akabar masu gidan.



A haka bikin su Hanfa ya matso tare da na Rinaz gaba d'aya su Ummi tarkatawa suka yi suka tafi Abuja har dasu Sabreen da su lantana har ma da su Uncle domin dama suna da family house nan za ayi bikin gida ne mai girman gaske Mai d'auke da wajajen hutawa da swimming pools da iska Mai dad'in gaske kasancewar gidan ya yi bayan gari ba abinda kake ji sai kukan tsintsaye sai duwatsu Kai wajen gwanin burgewa.


A nan aka yi shagalin bikin su Hanfa bikin ya k'ayatar ba k'arya kasancewar bikin ya samu gidan naira anyi harkar girma hakama ango faruk ba dai uban dukiya ba haka aka yi biki aka tashi lafiya aka Kai kowacce gidan ta Rinaz ma gidan ta dake Abuja aka kaita kafin subar k'asar zuwa India inda dama a can faruk ke aiki sannan dama Rinaz d'in bata gama karatun ta ba tayi kuka har ta gaji lokacin da su Ummi zasu koma kaduna sai dai ba yadda ta iya haka suka tafi suka barta da angon ta su Hanfa kuwa ba wacce ta yi kuka domin suna ganin basu bar gida ba gasu ga yayyan su Kuma mazajen su sai ma duniyan cin da suke yi gaban mutane.



Bayan komawar su Ummi gida da sati d'aya Arfat tare da mahaifiyar sa suka je suka samu Uncle da Daddy akan cewar a taimaka aba Arfat auren Nasreen inda su Daddy suka ce ba ruwan su su sami Maleek har gida kuwa suka je suka sami Maleek akan maganar da ya nuna Sam bai yadda da hakan ba Mai hankali da nutsuwa zai ba k'anwar sa sai da Sabeeha tasa baki tare da nuna masa cewar Arfat fa nasan Nasreen sannan itama tana son sa sannan da baya sonta bazai jawo mahaifiyar sa har wajen sa ba tunda har ya riga ya samu abinda yake nema a wajen ta da Dan wani abu yake son ta da haka Sabeeha ta shawo kansa ya yadda inda yace sati d'aya kawai za asa bikin Arfat kam bai Musa ba tunda bai da matsalar komai akwai naira aikuwa sati nayi ba a yi wata bid'i a ba sai dinner aka Kai amarya gidan ta.


Haka rayuwa ta cigaba da tafiya kowanne gida suna cikin farin ciki da nishad'i.



BAYAN SHEKARA UKU
abubuwa da yawa sun faru ciki kuwa har auren Salman da Aysha ta wajen aikin hajiya fulani da Kuma bikin dija da Muhsin d'an yayan Ummi da suka had'u a bikin 'yan uku Sabreen kuwa ta haifi twins duk maza kyawawa masu kama da 'yan uku anyi shagali ba kama k'afar yaro yara sunci sunan Daddy da Abba ana Kiran su Aiman da Ammar yaran sun ga gata ba k'arya Sameeha kuwa mace ta haifa Mai kama da Umar sai dai ita fara ce yarinyar kyakkyawar gaske taci sunan Doctor Amma suna Kiran ta ni'imatullah.

Sabeeha ce a kitchen tana aiki ta ji shigowar Alizah da gudu cikin falon ta nufi stairs tana k'wala Kiran "Momma! Momma," cikin hausar ta ta yara da bata gama iyawa ba.



Dafe Kai Sabeeha ta yi ta ce "Wayyo ni Sabeehan Mama naga ta kaina," ta fad'a tare da fita falon ta ce "Alizah me kika dawo yi kuma?"


Kyakkyawar yarinyar dake saukowa stairs tasha kyau cikin farar riga da k'aramun black skirt da toms d'in takalmi da farar safa da necktie da alama daga makaran ta take kallo d'aya zaka yi Mata kasan fitina ta ratsa yarinyar da wayo an gyara mata gashinta kanta an yi Mata two babies da shi ya zubo har kafad'ar ta Tasha jan ribbom ta ce "Momma na manta biro ne a gida ne nazo d'auka," ta fad'a tare da washe bakin ta fararen hak'oran ta suka bayyana dimples d'in ta ya lotsa.



Hararar ta Sabeeha ta yi ta ce "Duk laifina ne da na saki a makarantar dake kusa da gida sai ki dawo sai uku kafin a tashi," k'ifk'ifta blue eyes d'in ta ta fara ta zare idanunta Mai d'auke da zara-zaran eyelashes ta ce "Sorry momma karki ce Zaki canja mun school,"


"Sai Kuma kiyi yarinya canja makaranta ba fashi," Sabeeha ta fad'a tare da komawa kitchen d'in Alizah kuwa hanyar fita ta yi da gudu tana cewa "Na tafi Mama ta see you later," Sabeeha na jinta girgiza Kai kawai ta yi.


Da yamma da Maleek ya dawo ya samu Sabeeha zaune saman kujera tana chart da Sameeha ajiye wayar ta yi ta rungume shi tana masa sannu da zuwa zama ya yi a gajiye ta kawo masa ruwa ya sha ya ce "Ina Alizah fa?"



Kafin ta ce wani Abu sai ga Alizah ta fito da gudu daga sama tana k'ara itama Sabeeha ganin haka ta yi tsalle ta b'uya a bayan Maleek ta b'oye fuskar ta a bayan sa ya ce "Baby Aliz lafiya kuwa," raurau ta yi da ido ta ce "Papa wani Abu ne a d'akin momma zo muje ka gani Ina wasa na kawai yazo," sai lokacin Sabeeha ta kalli Alizah zare ido ta yi ta ce "Kam bala'i ka gani ko My ni kawai Wallahi ka d'auki yarinyar nan ka kaita wajen Ummi ko Mama ko ka kaiwa Sabreen dear ka ga fa inda ta yiwa jikin ta wanka da Mai har ma da jambaki," Sabeeha ta fad'a kamar zata yi kuka.


Shiru Maleek ya yi Yana kallon Alizah shi kansa ya jinjinawa fitinar Alizah ya ce "Yanzu Aliz haka kika b'ata jikin ki,"


"Ni ba wannan ba My kullum ita ce dawowa daga school sai ta dawo sai uku sau hud'u kafin tashi hatta teachers d'in su complain suke akan ta Ni kawai na gaji gara ka Kai ta wajen Umman Nasreen," Maleek kuwa jin Alizah na gudun makaranta take ya had'a rai saboda shi duk fitinar ta bata dame shi ba amma jin tana dawowa daga school sai ya ji bai ji dad'i ba ya ce "Kee! zonan," zare ido ta yi ta ce "Sorry papa ban Kuma ba kaji,"




"Kizo fa nace!," Ya fad'a a d'an tsawa ce Sabeeha kuwa dariya take musu k'asa k'asa a zuciyar ta ta ce gara ya yi maganin

Please Login or Register in order to submit comment