Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nagarta da ake nema a wajen mijin aure to ya had'a su na kuma ba inda za a hana shi aure yana da kyawawan halaye sosai abinda nake so dake shine kiyi ta addu'a kinji aminiyata?" Noding kanta ta yi.



Doctor ta ce "Abinda Abban ki ya fad'a gaskiya ne Sabeeha Maleek mutumin kirki ne fiye da tunanin ki ya kai a so shi ya kuma cancanci samun aure a duk inda ya nema na tabbata idan har kika aure shi zai baki kulawa sosai ko wad'an ne iyaye fatan su Allah ya had'a 'ya'yayen su da mazaje na gari Sabeeha idan har wannan ne kin samu duk da na fuskanci dalilin ki kuma baki yi kuskure akan hakan ba domin duk Wanda yasan Nasreen da Mahaifiyar ta ba wanda zai yi marmarin wata alak'a ko da ta gaisuwa ce ta shiga tsakanin sa da su Sabeeha wata iriyar rayuwa ake yi a cikin gidan nan domin mutum d'aya ke juya gidan sai abinda ya ce kuma wannan shine mahaifin Nasreen kamar yadda Abban ki ya fad'a kiyi ta addu'a Allah ya zab'a miki abinda yafi alkhairi mu ma zamu taya ki,"



A hankali Sabeeha ta ce "To Mamana," domin iya fad'a musu damuwar ta da ta yi taji sanyi sosai a zuciyar ta nan kuwa su Abba suka dinga janta da fira harta saki jikin ta sai dariya take yi.




Farin ciki fal ranta ta mik'e ta ce "Abba Mama sai da safe," sannan ta haye stairs tana shiga d'akin su ta tsaya kallon su Sameeha da suka yi jugum-jugum murmushi ta yi sannan ta k'arasa ta haye saman gadon ta zauna tsakiyar su ta ce "Sisters ku kwantar da hankalin ku dama fa damuwata akan Yaya Maleek ne," bud'e baki Rinaz ta yi ta ce "Ooh ke da ki ka ce bakya yi kuma?" Hararar ta Sabeeha ta yi ta ce "Sanin da kika yi babe ni bani number d'insa ma," bata Rinaz ta yi sai tsokanar ta suke yi ita dai banza ta yi da su ta turawa Maleek text.





Suna zaune tare da Salman a falon sa wayar sa ta yi k'ara jin a special number d'insa ne yasa shi dubawa ya ga an rubuta "Thank for everything," d'an shiru ya yi yana kallon text d'in sannan ya ajiye wayar ya kalli Salman ya ce "Salman kaje ka gama mana booking gobe domin jibi nake so nabar k'asar nan," Salman ya ce "Ok sir," banza Maleek ya yi masa sai ma hararar sa da ya yi ya tashi ya haura stairs.




Tashi Salman ya yi ya fice yana murmushi domin yasan dalilin hararar dan kawai ya Kira shi da sir ne.



Sabeeha kuwa wanka suka yi suka kwanta bacci bayan sun raba dare suna fira.



Washe gari sai 8:00 Sabeeha ta tashi kallon agogon dake d'akin ta yi saurin sauka daga gadon ta yi ta fad'a toilet ta yi wanka dama ta yi sallah tun asuba.





Gaban mirrow ta nufa ta shafa mai cikin sauri powder da lipstick kawai tasa sai kwalli sannan tasa doguwar rigar atamfa mai red and yellow sai ratsin blue d'auri ta yi mai kyau akan ta sannan ta yafa blue mayafi da plat shoes blue ta rataya jaka itama blue ta feshe jikin ta da turare ba k'aramun kyau ta yi ba wayar ta ta d'auka ta fice.




Tun kafin ta sauka down stairs take jiyo hayaniyar su Sabreen a kitchen murmushi ta yi sannan ta nufi kitchen d'in.





Tana Sameeha ta ce "Sabeeha sister sai ina haka?" D'aukar yam boll gud'a d'aya Sabeeha ta yi takai bakinta ta ce "Wa ki ke tunanin zai yiwa ya Maleek breakfast?" Rinaz ta ce "Amma ai ke yanzu ba 'yar aiki bace," hararar ta Sabeeha ta yi ta ce "Naji yanzu zanyi masa ne a matsayina na k'anwar sa kafin na zama matar sa," dariya Sabreen ta yi ta ce "Wow gaskiya ne Sabeeha dear ashe haka kika yi nisa," kanne mata ido d'aya Sabeeha ta yi.





Rinaz ta ce "Sabeeha habibty zan raka ki muje tare," Sabeeha ta ce "Ok Ina jiran ki amma karki dad'e," tare suka fita da Rinaz ita ta wuce d'akin Doctor.






Knocking ta yi a k'ofar Doctor ta ce "Yes come in," shiga Sabeeha ta yi da Sallama a bakin ta Doctor dake zaune gefen gado tana rubuce-rubuce ta amsa mata sallamar.





Tsugunnawa Sabeeha ta yi ta ce "Mamana barka da safiya kin tashi lafiya?" Murmushi Doctor ta yi ta ce "Lafiya k'alau rigimammiya ta tun d'azu naga'yammata na sun fito amma banda ke fatan dai lafiya ko da yake naga kinsha gayu sai ina haka?" Sunkuyar da Kai Sabeeha ta yi ta ce "Lafiya lau Mama uhm da..da..dama," sai Kuma ta yi shiru.




"Uhmm say it out," cewar Doctor Sabeeha ta ce "Mama dama zanje na yiwa ya Maleek breakfast ne," ta fad'a tana wani rintse idanu.




Dariya Doctor ta yi ta ce "To shikenan sai kin dawo driver na waje zai kai ki," ta ce "To Mama saina dawo," ta fad'a tare da ficewa.



A falo suka had'u da Rinaz tare da su Sabreen tare suka fita compound d'in gidan wata had'add'iyar farar BMW suka gani a wajen motar ta yi kyau sosai kamar ka sace ka gudu wajen motar suka nufa suna yaba kyanta sai kyalli take yi ko ba a fad'a musu ba sunsan ta Sabeeha ce wacce tun jiyan Maleek yasa aka kawo ta.





Sai da suka gama shafa motar sannan suka tafi su Sabreen kuma suka koma cikin gidan suna santin motar.



Su Sabeeha kuwa suna isa gidan suka samu falon babu kowa direct stairs suka nufa suka yi knocking d'akin Ummi.




Ummi ta ce "Yes shigo," tura k'ofar suka yi suka shiga suka samu Ummi zaune tana danna laptop har k'asa suka gaishe ta cikin fara'a ta amsa sannan ta ce "Yana ganku ku kad'ai ina ragowar 'yammatan nawa?" Rinaz ta ce "Suna gida Ummi muma zuwa muka yi rigimammiyar Ummi zata yiwa Yaya abinci," kallon Sabeeha da ta yi k'asa da kai Ummi ta yi ta ce "Ayyah daughter meyasa ki ka taho baki kwanta kin huta ba aike yanzu kin dena yi masa girki zansa a nemo masa wata," saurin girgiza kai Sabeeha ta yi ta ce "A'a Ummi dan Allah karki samo wata Allah zanyi,"




Murmushi Ummi ta yi Wanda ya bayyana dimples d'in ta sai a lokacin Sabeeha ta lura ashe wajen Ummi Maleek ya kwaso dimples hatta kamannin sa ma na Ummi ne sai dai dimples d'in sa yafi na Ummi lotsawa sosai.






Ummi ta ce "Banda rigima irin taki daughter har yaushe ki ka baro can kika zo nan yin girki," ta ce "Allah Ummi zan iya," ta fad'a tana mik'ewa ta fice zuwa kitchen.



Tana shiga kitchen d'in Hadiza ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Mun godewa Allah da baki zo ba ba musan ya zamu yi ba tun d'azu yallab'ai ya ce a shirya masa breakfast amma mun rasa me zamu shirya masa wanda zai burge shi," dariya Sabeeha ta yi ta ce "To shikenan kuje abinku bari nayi masa," ta fad'a tare da shigewa can cikin kitchen d'in su Hadiza kuwa suka fita suna hamdala.



Cikin lokaci k'alilan ta gama had'a breakfast d'in ta gama ta nufi d'akin su na gidan.



Da sauri Maleek ke saukowa daga stairs yasha kyau sosai cikin black trouser da farar t-shirt sai shirt bottles one black da ya d'ora a sama sai k'amshi yake zabgawa kallon breakfast d'in dake falon ya yi sai lokacin ya tuna ashe fa Sabeeha bata gidan k'aramun tsaki ya ja sannan ya nufi k'ofar fita.





Har zai fita sai ya tuna yanzu fa idan ya fita baisan lokacin dawowar sa ba gashi yanzu yana jin yunwa sannan shi ba gwanin cin abincin Restaurant ba juyawa kawai ya yi ya koma falon ya zauna ya bud'e abincin.





Wani daddad'an k'amshin girkin ne ya daki hancin sa ko ba a fad'a masa ba yasan Sabeeha ce ta yi girkin domin k'amshin girkin ta ya fita daban zubawa ya yi yaci ya k'oshi sannan ya koma d'akin sa ya yi brush ya fita zuwa part d'in Ummi.



Hankali a tashe Sabeeha ta shiga d'akin su ta fad'a saman gado ta saki wani kuka mai ban tausayi a hankali ta furta "Meyasa Wai meyasa hakan ne me ya yi muku ku ke k'ok'arin raba shi da rayuwar sa," zumbur ta mik'e tsaye ta ce "Bazan tab'a bari ku yi nasara a kansa ba ko da kuwa hakan na nufin rasa tawa rayuwar," tana fad'ar haka ta goge hawayen ta ta yi hanyar fita.




Direct upstairs ta nufa har ta kai hannu zata murd'a handle ta jiyo muryar Ummi tana cewa "Son wai meyasa baka son shan magani ne kasan fa ciwon dake damunka ba ciwon da za a dinga wasa da magani bane duk da naga ya yi sauk'i sosai," murmushi Maleek ya yi ya ce "Ummina ki kwantar da hankalin ki naji sauk'i sannan Ummi gobe nake son tafiya Dubai," kallon sa Ummi ta yi ta ce "Saboda me ko ka hak'ura da Sabeeha ne?" Girgiza Kai ya yi ya ce "A'a Ummi har gobe Ina sonta so bana wasa ba amma Ummi tunda ita bata sona bai kamata a takura mata ba Ummi ni yanzu damuwa ta yi mun yawa ga rashin wacce nake so ga matsalar Nasreen a gefe kuma ga wajen aikina shiyasa zan tafi ko dan tsira da lafiya ta kuma bazan dawo nan kusa ba," cikin tausayin d'an nata Ummi ta ce "Ka cigaba da addu'a kaji son sannan ka tafi da matar ka kaji?" Noding kansa ya yi.




Ganin yanayin Ummi ya canja yasa Maleek yin murmushin da ya bayyana dimples d'insa dake k'ara masa kyau ya ce "Ummi ki ka sanima ko daga nan nayo miki suruka dama akwai wata balarabiya mai suna Surayya dake sona kyakkyawar gaske ce nasan zata kula miki dani sosai," dariya Ummi ta yi ta dungure masa kai ta ce "Marar kunya," suka yi dariya gaba d'ayan su.






Daram dam gaban Sabeeha ke fad'uwa lokaci guda hawaye ya wanke mata fuska a zuciyar ta take fad'in shikenan na rasa shi yanzu gobe zai bar k'asar sannan bazai dawo nan kusa ba gashi kuma zai auro balarabiya fasa shiga Sabeeha ta yi ta nufi d'akin su tana kuka.





Kwanciya ta yi saman gadon su tana kukan rasa Maleek tura k'ofar d'akin Rinaz ta yi ta shiga da Sallama.




Saurin goge fuskar ta Sabeeha ta yi tare da amsa sallamar kallon ta Rinaz ta yi ta ce "Lafiya ki ke kuwa meyasa idanun ki suka yi red haka?" Murmushin yak'e Sabeeha ta yi ta ce "Bakomai Habibty kawai baccin da ya fara d'auka ta ne yasa hakan," shiru Rinaz ta yi ba don ta yadda ba ta tab'e baki ta ce "Shikenan tunda baza ki fad'a mun ba anyway ki tashi mu tafi yamma ya fara yi," girgiza kai Sabeeha ta yi ta ce "Ni anan zan kwana Rinaz please kema ki bari sai gobe Habibty,"





"Saboda me zamu kwana a nan d'in to?" Rinaz ta tambaya Sabeeha ta ce "Kawai nafi so mu kwana a nan," jinjina kai Rinaz ta yi ta ce "Ok ba damuwa Allah ya kaimu goben," Sabeeha ta amsa da "Ameen," fita Rinaz ta yi.






Sabeeha Kuma ta shiga wanka ko da ta fito doguwar riga ta zura ta yi sallah sannan ta kwanta tana shafa jikin pretty dake kusa da ita tunani fal zuciyar ta a haka bacci ya d'auke ta.




Sai yamma sosai ta tashi toilet ta fad'a ta yi alwalar sallar la'asar da bata yi ba gashi lokaci na tafiya tana idar da sallar ta nufi kitchen ta d'ora girki.



Tana gamawa ta jera komai a daining sannan ta koma d'akin su ta zabga uban tagumi gaba d'aya ita tama rasa dame zata ji hawayen dake zubo mata ta goge sannan ta tashi ta yi sallar magrib ta nufi d'akin Rinaz.




Akan sallaya ta samu Rinaz ta idar da sallah zama ta yi gefen gado ba tare da ta ce komai ba kallon ta Rinaz ta yi ta girgiza Kai bata ce komai ba tasan dole akwai abinda ke damun Sabeeha amma tak'i fad'a gashi lokaci d'aya duk ta fita hayyacin ta fuskar ta ta kasa b'oye damuwar ta.




Ko da Rinaz ta buk'aci su je su ci abinci cewa ta yi ta k'oshi Rinaz ta ce "Haba dear wai me yake damun ki ne yau fa banga kinci abinci ba sannan naga kina cikin damuwa sannan yanzu kink'i kici abinci Wai me yake faruwa ne?" Ganin Rinaz ta damu tana neman yin kuka yasa Sabeeha nemo k'aryar da zata yi mata.





Ta ce "Rinaz habibty karki damu kaina ke mun ciwo tun d'azu shiyasa," Rinaz ta ce "Ayyah sorry sister tashi muje asibiti," zare ido Sabeeha ta yi ta ce "Asibiti fa dear kaina fa nace yana ciwo," Rinaz ta ce "Eh mana Ooh na manta bari na sanarwa Ummi," ta fad'a tana yin hanyar fita Sabeeha na kiran ta amma ko waigawa bata yi ba.



Can sai gasu tare da Ummi kallon ta Ummi ta yi ta ce "Sannu Daughter me yake damun ki?" Murmushi Sabeeha ta yi ta ce "Ummi kaina fa ke ciwo kuma bada yawa ba," ajiyar zuciya Ummi ta sauke ta ce "Bari na kawo miki magani," ta fad'a tare da fita daga d'akin.




Dawowa Ummi ta yi da Abinci a plate tasa Sabeeha a gaba ta bata da kanta sannan ta bata magani tasha ta ce "Ki kwanta ki huta kinji daughter?" Gyad'a kai Sabeeha ta yi sannan Ummi ta fita Rinaz tabi bayan ta domin zuwa ta ci abinci.


Tashi Sabeeha ta yi ta d'auro alwala ta yi sallah sannan ta koma ta kwanta duk da tasan ba wani bacci da zata iya tana nan kwance Rinaz ta shiga d'akin tana waya tana gamawa ta shiga bathroom ta yi wanka sannan ta shirya cikin kayan bacci ta kwanta ba tayi tunanin tashin Sabeeha ba domin a tunanin ta bacci take yi ta fara bacci abinta.





Sabeeha kuwa yadda ta ga rana haka ta ga dare domin ita bata tab'a had'uwa da abinda ya hargitsa kwakwalwar ta ba kamar wannan lamarin.




Alwala ta yi ta fara nafila tana rok'on Allah da ya kare su daga sharrin mutum dana aljan tana zaune har asuba ta yi sallah ta yi sannan ta tashi Rinaz itama ta yi.





Gari yana d'an fara haske Rinaz ta koma bacci ita kuma Sabeeha ta yi wanka ta shirya cikin dark purple d'in doguwar riga ba kwalliya a fuskar ta amma tayi kyau sosai kitchen ta nufa ta fara had'a breakfast tana gamawa ta kai daining ta ajiye.



Maleek ne zaune akan gadon sa Nasreen ta shiga d'akin kallo d'aya ya yi mata ya d'auke idanun sa shi har ya manta rabon da ya ganta k'arasawa ta yi ta zauna gefen sa tana kallon sa domin gani ta yi ya k'ara yi mata kyau sosai suna had'a ido ya harare ta wanda hakan da ya yi ita gani ta yi ya k'ara kyau ta ce "Ina kwana ya Maleek," d'an kallon ta ya yi ya ce "Wai ke bakya jin kunyar zuwa waje babu sallama ne?" Ta ce "Sorry ya Maleek," baiko kalle ta ba ya ce "Sorry for yourself," daga haka ya mik'e ya nufi bathroom.





Ta ce "Ya Maleek ina Kuma zaka je zuwa fa nayi muyi fira," ya ce "Ina da abun yi kema ki tabbatar kafin na fito kin shirya domin zamu yi tafiya," zumbur ta mik'e ta ce "Tafiya kuma ina zamu je?" Kallon mamaki ya bita da shi ganin yadda ta rikice daga fad'in zasu yi tafiya ya ce "Yadai?" Murmushi ta yi ta ce "No bakomai," tab'e baki ya yi ya ce "To aje a shirya," daga haka ya shige bathroom ita Kuma ta fita da sauri.


Part d'in ta ta fara zuwa ta had'a kayan ta sannan ta nufi part d'in mahaifiyar ta a zaune ta samu Hajiya Asiya tana yin breakfast ko gaishe ta bata yi ba ta ce "Umma kinji wai Ya Maleek ya ce na shirya yanzu zamu yi tafiya," kallon ta Umma ta yi ta ce "To meye naki da damuwa ki shirya sai dai kafin ku tafi ki tabbatar ya yi breakfast," Murmushi Nasreen ta yi ta ce "To Umma,"daga haka tabar part d'in.



A falo ta ajiye trolley d'in ta sannan ta haura stairs ta shiga bedroom d'in Maleek ta zauna tana nan zaune ya fito daga dressing room d'insa ya yi matuk'ar shan kyau cikin uniform d'insa Wanda ke yi masa kyau a duk sanda yasa k'amshi kawai ke fita a jikin sa da kallo Nasreen ta bi shi a zuciyar ta tana fad'in Anya kuwa Umma dagaske take yi akwai Wanda yafi Ya Maleek had'uwa.




"Wannan kallon fa?" Maleek ya fad'a cikin had'e rai ta ce "Kayi kyau sosai," banza ya yi mata sannan ya ce "Muje," saurin cewa ta yi "Amma sai kayi breakfast zamu tafi?" Kallon ta ya yi ya ce "Kina da damuwa da hakan ne?" Murmushin yak'e ta yi ta ce "A'a gani nayi bai kamata na bari ka tafi da yunwa ba," kallon tsaf Maleek ya yi mata ya ce "Kina da damuwa da hakan ne har yaushe ki ka fara damuwa da naci abinci?" Shiru ta yi tare da yin k'asa da kanta wuce ta ya yi tare da fad'in "Muje ko," daga haka ya fice.




Da gudu Sabeeha ta shiga kitchen ta kalli inda ta ajiye breakfast d'in Maleek sai ta ga wayam babu shi hankali tashe ta fito daga kitchen d'in da gudu ta kalli Hadiza dake goge-goge ta ce "Hadiza ina breakfast d'in ya Maleek ko kin kai masa ne?"




Girgiza Kai Hadiza ta yi ta ce "A'a yau bani na kai masa ba Fati ce ta tafi kai masa," ai Sabeeha bata bari fati ta k'arasa fad'a mata ba ta fice da gudu.



A k'ofa taci karo da su Sabreen amma ko ta kansu bata yi ba ta yi hanyar part d'in Maleek da gudu ganin a yanayin da take ciki ne yasa su Sabreen binta a baya da gudu suna Kiran ta amma ko waigawa bata yi ba ko Kiran nasu ma bata ji.



Sai da ta kai k'ofar falon sannan ta tsaya har zata bud'e taji muryar Maleek na cewa "Ki kai mun abincin part d'in Ummi a can zanci," kad'an Sabeeha ta yi ajiyar zuciya sannan ta ja hannun su Sabreen suka bar wajen da sauri.



Suna shiga falon suka samu Ummi zaune akan kujera sai Rinaz da Fauwaz dake daining suna breakfast.



Rinaz ce ta ce "A'a sisters saukar yaushe?" Ganin su kamar a cikin damuwa Rinaz ta ce "Lafiya kuwa?" Kallon Sabeeha suka yi kallon Sabeeha da idanunta suke tab da k'walla k'iris take jira ta fara kuka Ummi ta yi sannan ta ce "Daughter zo nan ki fad'amun meye damuwar?" A hankali ta taka zuwa wajen Ummi sannan ta zauna gefen Ummi.




Ummi ta ce "Fad'a mun meye matsalar ko ciwon Kai d'in ne?" Girgiza kai Sabeeha ta yi "Ummi ta ce to fad'a mun meye," har ta bud'e baki zata yi magana Fati ta yi sallama a falon ta kalli Ummi ta ce "Ummi dama Yallab'ai ne yace a kawo masa abincin sa nan," Ummi ta ce "Ok ajiye a can," Ummi ta fad'a tana nunawa Fati can gefe wajen wasu had'addun kujeru.




Ajiyewa saman center table Fati ta yi sannan ta fita mayar da kallon ta wajen Sabeeha Ummi ta yi ta ce "Yanzu fad'a mun Daughter meke faruwa?" Hawaye ne ya zubo daga idanun Sabeeha har ta bud'e baki zata yi magana Maleek ya shiga falon Nasreen na biye da shi.


Kallo d'aya ya yiwa Sabeeha yasan tana cikin damuwa itama da kallo ta bi shi domin gani ta yi kamar kullum k'ara masa kyau ake yi ko dan ranar birthday d'insu bata ga kyan sa haka ba ko dan ranar bata gansa a mai haske sosai bane.



K'arasawa wajen Ummi ya yi ya ce "Good morning Ummina," ta ce "Morning Son," d'aga ido ya yi ya zabgawa Nasreen wata uwar harara da sauri ta durk'usa ta ce "Ummi ina kwana?" Cikin fara'a Ummi ta amsa.


Mik'ewa Maleek ya yi ya kalli su Rinaz da suka yi tsilli-tsilli d'aga mata gira d'aya ya yi da idanunta ta yi masa nuni da Sabeeha kallon Sabeehan ya yi da tasa bayan hannun ta tana goge hawaye sannan ya kalli Ummi Rolex watch d'in hannunsa ya ce "Ummi mu zamu tafi," da sauri Sabeeha ta kalle shi.




Fauwaz ya ce "Ya sai tafiya?" Gyad'a kai Maleek ya yi tare da juyawa ya nufi hanyar fita saurin Shan gaban sa Nasreen ta yi ta ce "Ya Maleek ga breakfast d'in can fa," ta fad'a tana nuna masa.



Wajen ya nufa ya zauna Nasreen d'in ta zuba masa chips d'in a plate ta ajiye masa.




Fork yasa ya d'ebo chips d'in ya kai bakinsa ji ya yi an fisge cokalin anyi jifa da shi zumbur Nasreen ta mik'e ta ce "Mahaukaciyar dabbar ina ce ke da zaki hana mijina cin abinci," tsawa Maleek ya bugawa Nasreen ya ce "Kina haukane zaki yi mata irin wannan zagin?" Ya kalli Sabeeha baice komai ba.



Kowa mamakin abinda Sabeeha ta yi yake yi Ummi ta ce "Daughter Mai ya faru ne meyasa zaki hana son cin abinci?" Gyad'a kai Maleek ya yi alamar tambaye ta dai Ummi hawaye ne ya zubo a idanun Sabeeha ta ce "Dan Allah karka ci abincin nan," kallon mamaki ya yi mata meyasa zata ce Kar yaci abincin da ita da kanta ta dafa ya ce "Nikam saina ci domin yunwa nake ji," ya fad'a yana d'auko cup d'in kunun gyad'a ya kai baki saurin rik'e hannun sa Sabeeha ta yi ta ce "Karka sha Dan Allah," Ummi ta ce "Meyasa Daughter?" Da gudu Sabeeha ta isa wajen Ummi ta rik'e hannun ta ta ce "Please Ummi kice kar ya sha idan yaci abincin idan ya ci mutuwa zai yi," wannan karon kowa mamakin maganar da Sabeeha ta fad'a yake yi banda Maleek da ya gyara zaman sa akan kujera.



Nasreen kuwa lokaci guda ta jik'e da zufa duk da Ac dake falon Ummi kuwa kasa magana ta yi Fauwaz ya ce "Amma ta ya kika san hakan?"




"Ya Fauwaz ka yadda dani akwai poison a cikin abincin," a zafafe Fauwaz ya ce "Poison fa waye yasa masa poison a abinci?"

"Nasreen ce tare da mahaifiyar ta kuma sun dad'e suna shirya hakan nasani cewar Nasreen da mahaifiyar ta basa sona sun tsaneni hakan ne yasa suke ta shirin yadda Zan bar gidan nan duk da nayi iya k'ok'arina wajen ganin ba wata hanya da ta had'ani da su amma su hakan bai yi musu ba hakan ne yasa suka shirya cewar Sameeha ta je can domin yin aiki yadda zasu yi amfani da ita wajen sa poison a cikin abincin ya Maleek ni kuma lokacin da aka kawo takardar dake d'auke da lokutan da Sameeha zata dinga zuwa aikin na canja lokutan nake zuwa ba tare da sun gane ni ce nake zuwa ba ta nan ne nake jin Shirin su a duk lokacin da naji Shirin su hankalina yana matuk'ar tashi dan dai kawai bana shiga mutane lokacin ne sai dai kawai a fuskanci Ina cikin damuwa jiya ne naji Shirin su akan cewar zasu zuba masa poison a abinci wanda sunsan idan har yaci ya mutu to dole ne nabar gidan nan domin ba Wanda za a zarga sama dani tunda nice na girka shine suka sa Fati domin ta yi musu aikin Ummi bansan meyasa suke son kashe shi ba Ummi Ina son shi bana so mu rasa shi Ummi rasa shi na nufin rasa tawa rayuwar," Sabeeha ta fad'a tana sakin kuka.



Ummi kanta hawaye take yi domin bata yi tunanin tsanar da Hajiya Asiya ta yiwa Maleek ya kai harta iya raba shi da ransa ba Sameeha Rinaz da Sabreen ma hawayen tausayin Maleek dama kansu gaba d'aya suke yi domin sunsan da Maleek ya ci abincin nan basu da mafita.



Maleek kuwa murmushi kawai saki domin jin maganar Sabeeha ta k'arshe shi yanzu ba maganar kashe shi ce ta tsaya masa a ransa ba kunnuwan sa ke maimaita masa "Ummi Ina son shi bana so mu rasa shi rasa shi na nufin rasa tawa rayuwar,"




Fauwaz kuwa take idanunsa

Please Login or Register in order to submit comment