Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ta yi bata ganshi ba k'ara masa kyau akayi.




Ganin shima ita yake kallo yasa ta d'auke idanunta a kansa bawai Dan ta gaji da kallon sa ba sai dan fushin da take yi da shi cikin burgewa Maleek ke kallon babyn tasa domin shi duk abinda zata yi burge shi take yi.



Da haka suka k'arasa hall d'in da za a gudanar da party da tunda suka shiga compound d'in wajen suke jiyo kid'a na tashi a jere motocin suka yi parking.




Firfitowa su Dija suka yi Sabeeha na tsaka da danna wayar ta aka bud'e k'ofar side d'in ta a hankali ta d'aga kanta ta kalli Wanda ya bud'e motar Aysha ce ta ce "Dear ku fito an K'araso," bata amsa ba ta d'auki pose d'in ta dake gefen ta sannan a hankali ta zira k'afar ta waje ta fita.



Lokacin har Umar ya fito rik'e da hannun Sameeha haka ma Fauwaz yana rik'e da hannun Sabreen.




Zagawa b'angaren da take Maleek ya yi ya tsaya sannan a hankali yakai lallausan hannunsa ya rik'o nata da sauri ta rintse idanunta saboda wani yarr da ta ji yayin da a cikin hall d'in da yake cike da 'yan uwa da abokai da k'awaye suka fara jiyo MC na sanar da shigowar angwaye da amare.



A tsakiya akasa su sannan suka fara takawa a hankali zuwa cikin hall d'in yayinda masu d'aukar hoto ke yi masu video nayi har 'yan gidan televisions duk sun hallaci wajen domin ansan da bikin tun ana sati bikin ake sanarwa a kafafen yad'a labarai da jaridu.


A haka suka shiga cikin hall d'in da ya gaji da had'uwa domin decoration yasha cikin farin yadi da dark green gurin sai bada kalolin fitilu yake yi duk inda ka kalla sai kyalli yake yi yayinda wata had'add'iyar wak'a ke tashi a wajen Mai suna lamba ta destiny boy tuni Dija Aysha Hanfa da Hany sun fara taka rawa yayinda su Alim suka rufe su da lik'i suma suna taka tasu rawar.



Sabreen kuwa mantawa ta yi da ita amarya ce ta fara taka tata rawar yayin da Fauwaz ke ta yata wajen ihu ya d'auka lik'i kuwa yinsa ake yi kamar ba a son dukiyar Maleek kuwa hayaniyar har ta fara damunsa gashi an rufe su sai lik'i ake musu a hankali ya janye Sabeeha suka je suka zauna.




Su Sabreen kuwa sai da suka gama tashewa sannan suka je suka zauna Sameeha ma bata yi rawa ba sai Umar da shima sai da ya taka rawar farin ciki sannan suka zauna.




Ba b'ata lokaci aka fara gudanar da party amare tare da angwayen su har sai da suka gaji da fita tsakiyar fili suka dena fita yayin da Hanfa da Ashraf Hany da Alim banda rawa ba abinda suke yi ana yi musu video lik'i kuwa sun sha shi kamar ba gobe Dija da Aysha ma ba a barsu baya ba yayin da idanun Arif ke kan Dija domin shi har ga Allah sonta yake yi haka aka gama tashewa aka tashi yayinda DJ yaji dad'in bikin domin kud'in da ya samu yafi k'arfin tunanin sa domin Maleek har dollar ya lik'awa Sabeeha duk da ko motsa jikin ta bata yi ba da sunan rawa.



Amma duk da haka a gajiye ta fito daga wajen ga wani wahalallen bacci da take ji jan k'arfar ta kawai take yi Maleek da kansa ya bud'e mata motar ta shiga ya rufe sannan shima ya zagaya ya shiga.


Tunda ya shiga motar idanun sa suke a kanta kallo d'aya ta yi masa ta d'auke kanta ita a dole har lokacin bata sauko daga fushin ba shi abun nata ma ya koma bashi dariya Aikuwa kallon ta ya yi ya fara dariya ya juyar da kansa.




Sheshshek'ar kukan da ya ji ne yasa ya yi saurin kallon b'angaren ta ya ga dagaske kukan take yi sai goge fuskar ta take yi da bayan hannunta a hankali ya k'ara matsawa kusa da ita murya k'asa k'asa ya ce "Mene?" Kallon sa ta yi ta k'ara volume d'in kukan nata.



A hankali ya Kai hannun sa ya ja ta zuwa jikin ta ya rungume ta ya ce "Is okay fad'a mun mene?" Luf ta yi a jikin sa tana hawaye ta ce "Ba kai bane," murmushi ya yi ya ce "Ni ne koh me nayi to?" A hankali ta d'an daki k'irjin sa ta ce "To ba kaine ba ka manta dani ba ka dena kirana ba," ya ce "Ayyah sorry baby bazan k'ara ba kinji?" Noding kanta ta yi domin yasan idan ba hakan ya yi Mata ba ta dinga yi masa rigima kenan.



A haka suka k'arasa gidan Auntyn Dija ana tsayar da motocin mutanen dake ciki motocin suka fita Fauwaz ne ya bud'e b'angaren da Maleek ke zaune ya ce "Yaya mun k'araso," gyad'a kai Maleek ya yi sannan ya Mai da kallon sa kan Sabeeha da tuntuni ta yi bacci a jikin sa saboda gajiyar da ta yi.



A hankali ya zame jikin sa daga nata ya cire babbar rigar sa da dama ta ishe shi ya mik'awa Fauwaz sannan ya fita daga motar su Dija da su Hanfa tare da su Alim su Arif da Umar duk kowa na wajen.




A hankali ya d'auke ta cak ya fito da ita daga motar kamar ya d'auki 'yar baby kallo ne ya koma kansu Sabreen kuwa jikin ta har yana rawa wajen d'aukar su a hoto har tana samun mata ya.



Ganin haka Dija ta bud'e masa k'ofar baya tana gaba yana binta a baya har d'akin ta a hankali ya kwantar da ita a kan makeken gadon yana k'arewar kyakkyawar fuskar ta kallo ya kalli Dija ya ce "Ki tashe ta ta canja wannan rigar," ta ce "To," daga haka ya fice daga d'akin.



Yana fita compound d'in gidan ya bud'e mota ya shiga tare da Muhseen da Kuma Arif sai Umar suka tafi.



Su Sabreen ma bayan sun gama firar su suka shiga cikin gidan a gajiye suka d'akin suka samu Sabeeha sai baccin ta take yi cikin kwanciyar hankali.




Dija ce ta fara tashin ta a hankali ta bud'e idanunta ganin ta kwance a gado yasa ta saurin tashi zaune tana kallon su d'aya bayan d'aya dariya Sabreen ta yi ta ce "Dear yadai?"



"Wane ya kawoni nan Kuma?" Sameeha ta ce "Mijin da zai aure ki mana kunga yadda ku ka yi kyau kuwa da ya d'auke ki," Sabreen ta ce "Bari ki gani," ta fad'a tana nuna mata hotunan da ta yi musu kuma sunyi kyau bata ce komai ba ta mik'e tare da cire rigar jikin ta ta d'aura towel ta shige toilet ta yi wanka tare da alwala.




Maleek kuwa direct part d'in sa suka nufa suna shiga ya zauna akan kujera tare da d'aukar ruwan dake kan center table ya bud'e yasha ya ajiye Arif ya kalli Umar ya ce "Umar yau fa munga love," Umar ya ce "Wallahi kuwa MG irin wannan caring haka?" Tab'e baki Maleek ya yi ya mik'e ya nufi stairs yana cewa "Sa ido sana'ar banza," su kuma sai dariya suke yi masa.



Washe gari ya kama Dinner d'in da Ummi tare da Doctor suka had'a domin taya yaran nasu murna hidima ake yi sosai a gidajen mummyn Umar ma ba a barta a baya ba wajen yi hidimar bikin d'an nata tilo.


Shiri ake yi sosai domin amare ba k'aramin kyau suka sha ba cikin maroon d'in lace Wanda Abba ya yi musu Mai adon silver takalmin su tare da pose d'insu duk silver color mai kyalli haka ma net d'in da aka rufe musu fuska shima silver kyan da suka yi bana wasa bane sai k'amshi suke yi.


Yayinda k'awayen su suka shirya cikin milk d'in lace da coffee head sunyi kyau har da Zainabu wacce itama aka yi Mata kwalliya kamar ba ita ba.




Motoci ne reras a k'ofar gidan antyn Dija sai wacce ka zab'a zaka shiga motocin suka shiga sai hall d'in da za a gudanar da Dinner d'in Wanda yafi na jiya tsaruwa.



Suna yin parking Ummi da kanta tare da Maman Umar su suka fito tarar su Sunsha kyau cikin wani red d'in code net mai followers yellow duk da ba wata kwalliya ce a fuskar su ba amma sunyi kyau har k'asa 'yan uku suka tsugunna suka gaida surukan nasu suka amsa cikin fara'a tare da rungume 'yan uku daidai lokacin motocin su Maleek na shiga wajen Ummi kuwa hannayen 'yan uku suka ja zuwa cikin hall d'in da ya gaji da had'uwa yasha decoration ba k'arya ko Ina sai walwali yake yi da kyalli fitilu kaloli na kawowa a wajen hatta wajen da suke takawa wasu fitilu suke kawowa dangi kowa yasha anko cikin code net coffee da milk head ga table table Nan na zama a can gefe kuma wajen zaman couples d'in ne da ya gaji da had'uwa can kuwa gurin da aka tanadi abinci ne da masu zubawa sai abinda ka zab'a domin girki aka yi kala kala da farfesu kala kala ga gashashshen naman rago dana sa.




'yan uku kuwa sai baza idanu suke domin ganin ta inda zasu hango Doctor can suka hango ta zaune a wajen wasu kujeru uku gurin an k'awata shi sosai da alama gurin su ne ita da maman Umar da Kuma Ummi direct wajen ta suka nufa da sauri.




Doctor da batasan da zuwan su ba unexpected ta ji sunyi hugging d'in ta Suna murnar ganin ta murmushi Doctor ta yi tare da ajiye wayar ta kan table ta kalle su ta ce "Ku nutsu mana a gaban mutane ku ke fa," tura baki Sabeeha ta yi ta ce "Mama fa duk murnar ganin ki ce," ta yi dariya ta ce "To naji shugabar rigimammu," dariya su Sameeha suka sa yayin da su Maleek da suka shiga wajen suke kallon su cikin burgewa haka ma mutanen wajen ba k'aramun burge su 'yan uku da mahaifiyar su suka yi ba.



K'arasawa su Fauwaz suka yi yasha kyau cikin farar Shadda yayinda su Ashraf tare da abokan Maleek suka sa milk d'in Shadda mai aikin coffee Maleek tare da Umar suma farar Shadda suka sa sunyi kyau ba k'arya sai k'amshi ke tashi.


Ummi ce ta je ta ja 'yan uku zuwa wajen da aka tana da domin su ta zaunar da su kallon ta Fauwaz ya yi ya ce "Ummi naga kin had'a su su ukun?" Hararar sa Ummi ta yi ta nuna musu d'an gefen da 'yan uku suke ta ce ga wajen zaman ku can tura baki Fauwaz ya yi ya nufi wajen ya zauna haka ma Maleek da Umar suka je suka zauna kusa da Fauwaz da sai kumbure-kumbure yake kallo d'aya Maleek ya yi masa ya shiga hankalin sa.


Bayan kowa ya zauna Ummi ta nufi kan step tare da k'arbar microphone daga hannun MC ta ce "Firstly i thank almighty Allah countlessly for the special gift that he has given to me it's today my son's became the groom's so I'm very happy and I congratulate them to have a beautifuls bride's so I pray Almighty Allah to bless them with fine fine babies," tafi wajen ya d'auka yayin da Sabreen da Fauwaz suka had'a baki wajen cewa "Ameen," Ummi ta cigaba da cewa "I welcome everybody here and thank for your love and caring thank you once again," tafi wajen ya d'auka.



Haka ma Doctor da maman Umar suka yi nasu gabatarwar cikin harshen turanci daga nan Ummi ta kalli gold watch d'in hannun ta ta kalli hanfa da Hanifa ta ce "it's your turn time na tafiya," tashi Hanfa da Hany suka yi suka hau kan stage d'in karb'ar microphone d'in Hanfa ta yi ta d'anyi gyaran murya ta ce "Akwai wata game da muka shirya sannan a yanzu zamu gudanar da ita a yanzu muke so ko wanne ango a ciki zai tashi ya k'arasa gaban amare sannan ko wannen su zai nuna mana amaryar sa kamar yadda ku ke gani amaren mu they're identical triplets saboda haka we shall see what happens," tafi wajen ya d'auka sannan Hanfa ta ce "Let us start with Ya MG Bismillah Ya MG," d'aga Kai Maleek ya yi ya kalli Hanfa ta ce "Yes you sweetheart," ajiye wayar ya yi a kan table d'in dake gaban sa ya mik'e cikin takun k'asai ta ya k'arasa gaban hanfa ya tsaya.




Kallon mutanen wajen ta yi sannan ta ce "Like we see zamu fara da Ya MG Bari na raka shi sannan Kuma kuna gani wazai zab'o mana," ta fad'a tana jan hannun sa har zuwa gaban 'yan uku da yake ganin kamar ranar kamar su tafi zama d'aya.



Kallon su ya fara yi d'aya bayan d'aya ya fara takan ta farko sannan ya kalli ta tsakiya ya kalli ta d'aya gefen murmushin gefen Baki ya yi Wanda ya bayyana dimples d'insa sannan a hankali yakai hannunsa ya rik'o hannun ta tsakiya.



Dariya Hanfa ta yi ta ce "Even me Hanfa bansan wacece ba sai dai bari muji daga bakin amaryar mu shin meye sunan ta," ta fad'a tana Kai microphone d'in saitin bakin ta.





A hankali cikin sassanyar muryar ta ta ce "Sabeeha," Ihu wajen ya d'auka ana tafi juyawa Sabeeha ta yi ta kalle shi ta sakar masa murmushi nan fa aka fara ruwan yi musu hotuna dama already 'yan gidan televisions suna nan Hanfa ta ce "Bari muji me ya MG zaice da amaryar sa Wanda ya shafi abinda ke cikin zuciyar sa," ta fad'a tana mik'a masa abun maganar karb'a ya yi sannan ya fuskanci Sabeeha da ta yi k'asa da kanta a hankali ya ce "Look at me baby," a hankali ta d'aga Kai ta kalle shi idanunsu ya had'e da juna murmushin ya sakar mata Wanda ya k'ara masa kyau sannan ya ce "U already knew that I love you and I can't stop telling you that from now up to rest of my life in the morning evening or night in the rain or sun I will tell you that I love you I really love you with every breath i take and i can't leave you forever you know my heart beats for you only you,your love is all i will ever need," tafi wajen ya d'auka da ihun samarin wajen Sabeeha kuwa batasan sanda murmushi ya kufce mata ba abin maganar ya kai bakin ta cikin sassanyar murya ta ce "Me too my heart love you and it will never stop loving you,i love you with all my heart," ai Maleek baisan sanda ya rungume ta ba ya sakar mata kiss a forehead d'inta ihu wajen ya d'auka ana tafi.




Hanfa ta ce "Wow this couple so amazing," Jan hannunta ya yi zuwa gefe suka zauna.




Hanfa ta ce "kunga dai Ya MG ya tsallake so bari mu ga shin bro Fauwaz zai wuce ko a'a taso bro," Haneefa ce ta rik'e hannun sa Hanfa na binsu a baya har gaban Sameeha da Sabreen dake zaune yayin da mutanen wajen kowa ke baza idanu ya ga yadda abun zai kasance.





Dam gaban Fauwaz ya fad'i saboda shi gaskiya idan har suna tare baya iya gane Sabreen d'an dafe Kai ya yi tare da rik'e k'ugu yana k'are musu kallo hannu ya kai a hankali zai rik'o hannun Sameeha Sabreen ta kanne masa ido d'aya ya yi saurin rik'o hannunta duk abinda ya faru a wajen mutanen Aikuwa waje ya kaure da ihu Hanfa ta ce "Tofah kunga bro Fauwaz ya kasa gane amaryar sa anya a kaita gidan sa kuwa?" Dungure mata kai Fauwaz ya yi ya ce "Sai ki hana a kaita 'yar rainin wayo kawai," ya fad'a tare da k'wace microphone d'in hannun ta ya fara fallasawa Sabreen sirrin zuciyar sa akan son da yake mata itama haka ana ta yi musu tafi sannan suka wuce suka zauna.



Dariya Hanfa ta yi sannan ta waiga sai kawai ta ga Umar rik'e da hannun Sameeha zare ido ta yi ta ce "Ya Umar to ai ba a yi game d'in ba kawai ta zauna sannan su zama su Uku sannan ka zab'o sarauniyar taka," harara Umar ya aika mata ya ce "Ai ko su goma suke kama sai na gano ta a cikin su," ya fad'a Yana kallon Sameeha da ta yi k'asa da kanta tana murmushi.




Hanfa ta ce "To kamar yadda ku ke gani Ya Fauwaz da Ya Umar wayo suka yi mana saboda haka basu yi nasara ba especially ya Fauwaz saboda haka ya MG shi ke da nasara," ta fad'a tana mik'awa Umar abun maganar ya yi yana hararar ta.




Shima bai b'ata lokaci ba ya fara kwararawa Sameeha kalamai masu sanyaya zuciya haka itama ta mayar masa Nan aka dinga yi musu hotuna sannan suka zauna.


Hanfa ce ta ce "Congratulations once again ya MG zaka k'arbi gift d'in ka daga Ummi immediately after dinner and this the end of this game," tana fad'in haka ta mik'wa Haneefa abun maganar.




K'arba Hany ta yi ta ce "Da farko Ina so naga Ya Alim a nan," Alim dake can gefe ya taso yasha kyau cikin milk d'in Shadda kyakkyawa ne fari domin Mahaifin sa ya yi domin duk gidan su Ummi farare ne so dukan su yaran haka suke farare kyawawa a hankali ya k'arasa gaban Hany ya tsaya tare da kanne mata ido d'aya abun magana shima aka bashi.





"Hany ta ce yanzu zamu gabatar da drama just for our happiness," kallon Alim ta yi ta ce "Start," tana fad'in haka ta juya masa baya ta fara tafiya cikin yanga tare da had'e fuska tafiya take yi kamar zata k'arye saboda rangwad'a gashi ta rik'e k'asan doguwar rigar ankon jikin ta dake Jan k'asa tana taku a hankali.




Yayinda Alim ke binta a baya cikin sauri ya ce "Exuse me," banza Hany ta yi masa hakan ne yasa ya yi saurin shan gaban ta cak Hany ta tsaya tare da yi masa kallon up and down ta ja tsaki tare da kawar da fuskar ta gefe bata ce komai ba.



Murmushi Alim ya yi ya ce "Gaskiya harara ba k'aramun kyau ta yi Miki ba baby," d'an zare ido ta yi tana mamakin abinda ya fad'a sai dai nan ma bata ce komai ba.



Numfasawa ya yi tare da gyara tsayuwar sa ya ce "Komai ki ka yi kyau yake miki na tabbata samun kyakkyawar mace zabgegiya mai kyan tafiya irin ki abune mai wuya a gaskiya daga kallon farko da nayi miki naji kin yi gabas da tunanina please accept my love baby,"



Wata uwar harara ta watsa masa ta rik'e k'ugu ta ce "Ni Kuma bana tunanin kana d'aya daga cikin mazan dake burgeni so find your way out of my own way," tana fad'in haka ta cigaba da tafiya abinta.



Tagumi Alim ya zabga tagumi sannan ya Kuma binta ya ce "yammata a gaskiya Ina sonki,son ki shine abu mafi k'arfi daka iya juya gami da sarrafa gangar jikina ya zuwa aikata duk wani abu daya danganci so da k'auna," shiru ya yi sannan ya dawo gaban ta yana kallon cikin idanunta ya ce "Ba kowane ya cancanta ya zamo sarki ba sai jinin sarauta Kuma mai ilimi gami da natsuwa hak'ika kin cancanci zama gimbiya Kuma sarauniya a cikin zuciyata," sakin ido Hany ta yi tana sauraron kalaman sa wad'an da lokaci guda suka ja ra ayin ta ta saki murmushi ta ce "Amma meyasa kake sona bayan baka sanni ba you don't know even my name?"


D'an murmushi ya yi ya ce "Abinda ya ja hankali na a gare ki nutsuwar ki hankalin ki da Kuma kyawawan halayen ki kina da qualities d'in da duk namijin da ya ganki zai ji kin kwanta masa a zuciyar sa tabbas kin cancanci a so ki I really love you Please I beg you to accept my request please," ya fad'a tare da tsugunnawa a gaban ta irin a taimaka masa d'in nan.




Rik'e k'ugu ta yi tare da juya idanunta a zuciyar ta take fad'in uhm uhm fa Hany karki yiwa kanki ki rasa wannan santalelan saurayin gashi kyakkyawa dogo fari ga iya kalamai sannan ga hankali da nutsuwa k'ara kallon sa ta yi sannan ta ce "Meye sunan ka," da sauri ya ce "Sunana Abdul-Aleem amma zaki iya kirana sweetheart," ihu da tafi wajen ya d'auka banda iPhones ba abinda ke tashi a wajen ana yi musu video bayan yan gidan televisions dake nasu.



Alim ya ce "Amma ya sunan sarauniyar tawa?" D'an murmushi ta yi ta ce Sai ka tashi sannan zan sanar maka mak'e kafad'a ya yi ya ce "No bana so na tashi a nan har sai kinyi accepting d'ina a matsayin masoyin ki," dariya ta yi ta ce "Ban tab'a had'uwa da saurayin da naji zuciya ta ta aminta da shi lokaci guda ba sama da Kai a wannan lokacin bazan iya dakatar da kaina ba wajen fad'a maka Ina sonka ba yanzu ne na k'ara tabbatarwa gami da gasgata cewar zab'i mafi girma da nayi a rayuwata shine dana zab'e ka sannan Kuma na amince da irin soyayyar da ka ke yi mani Alim bana tunanin yanzu da Kuma nan gaba wani zai bayyana daka iya sauya akalar zuciyata daga son da nake maka nayi dace nayi sa'a da bayyanar ka a rayuwata Ina son ka sannan sunana Haneefa amma zaka iya kirana da matar ka insha Allah," mik'ewa Alim ya yi tare da yin wani juyi ya d'aga hany sama yana juyi da ita a wajen.



Su Ummi na gefe sai dariya suke yi hakama sauran jama'ar wajen abun ya burge su sai tafi ake musu.




Saurin k'arasawa wajen Hanfa ta yi ta karb'i abun maganar ta ce "mun gode kwarai da gaske da wannan nishad'antar damu da ku kayi sannan ku b'ace mana da gani wannan lokaci ne na cin abinci dan ni na matsu," duka wajen aka kama dariya.




Daga haka aka fara gudanar da dinner kowa sai abinda yake so sannan yake ci yayin da Fauwaz ya dage sai ciyar da amaryar sa yake yi shi da Umar yayinda Maleek da Sabeeha ke zaune suna fira abinsu suna dariya ruwa kawai da lemo suke sha da haka aka kammala cin abinci sannan Ummi ta je ta gabatar musu da gift d'in su wasu rings ne guda biyu ta umarci Maleek da ya sawa Sabeeha haka kuwa akayi ya d'auki ring d'in da sai kyalli yake yi ya zira mata a yatsar ta ana yi musu tafi sannan itama ta d'auka tasa masa nan ma akayi tafi tare da hotuna sannan aka tashi kowa ya shiga motar sa zuwa gida.




'yan uku kuwa mota d'aya suka shiga da Doctor domin a gida zasu kwana saboda gobe d'aurin aure.
[10/25, 8:48 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️






RUBUTAWA DAGA
HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ)





SADAUKARWA GA
MY DAUGHTER SABEEHA
BILKISU Z.YA'U (🅱️K)
AISHA MAGAJI DABO (AMA)


GODIYA TA MUSAMMAN A GARE KU
HAFSAT YAHYA (NAMECY)
SISTER MARIYA
Nagode sosai da kulawar ku a gareni Allah yabar zumunci ya barmu tare sannan wannan page d'in na sadaukar da shi a gareku masoyan kwarai🥰

Page 25


Suna zuwa gida d'akin su suka nufa a gajiye wanka suka yi sannan suka shirya cikin kayan baccin su iri d'aya kamar yadda suka saba sai dai kowaccen su a zuciyar ta tunani take yi yanzu shikenan daga yau bazasu k'ara kwana tare ba duk sai suka dinga jin ba dad'i Dija ce ta shiga d'akin ita da Rinaz da kallo suka bi 'yan uku ganinsu duk jikin su a sanyaye.



Dija ta ce "Beb's ya akayi ne nagan ku haka what wrong?" Ta fad'a tana zama gefen Sabreen dake kwance ruf da ciki ta zabga uban tagumi kamar wacce aka yiwa mutuwa Sabeeha kuwa tana zaune akan gado daga gefe ta had'a kai da gwiwa yayin da Sameeha ke zaune tsakiyar su ta tank'washe k'afa ta yi tagumi.



Rinaz ce ta ce "Wai lafiya ku ke kuwa meke faruwa?" Ta fad'a fuskar ta d'auke da damuwa sai lokacin Sabreen ta yi juyi ta kalle su ta ce "Hmm sisters ku bari kawai gobe ne auren nan ko?"



"Eh fa da wata matsalar ce?" Dija ta tambaya tana kallon Sameeha da har k'walla ta taru a kyawawan idanunta "Wallahi ni duk sai nake jin ba dad'i shikenan daga yau mun dena kwana tare da su dear zamu raba gida?" Sabreen ta fad'a tana goge hawayen

Please Login or Register in order to submit comment