Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba kowane zai iya abinda ta yi ba.



Daddy kuwa kansa ya dafe da yake juya masa ta bakin Maleek tabbas da a tsaye yake dole sai ya fad'i domin maganar ta girgiza shi sosai maganar ta tashi hankalin sa fiye da tunanin mai tunani idanunsa sun kad'a sunyi jajir tsabar b'acin rai ya kalli Uncle ya ce "Why Yaya meyasa zaka aikata hakan shin tsanar da Kai mana ne ya Kai har haka kome yanzu meye ribar abinda ka aikata yanzu kaji dad'i kenan da case d'in yake a hannun d'anka?" Share hawaye Uncle ya yi ya ce "Nayi nadama tabbas na aikata kuskure babba na biyewa zuciya ta da nayi amma ku gafarceni san abin duniya ne ya jefani a wannan halin amma Wallahi bansan cewar miyagun kwayoyi ake Shirin shigo dasu k'asar nan ba,"



Da mamaki Maleek ke kallon Uncle sannan ya ce "Kamar ya kenan?"



Uncle ya share hawayen sa ya ce "Alhaji sammani mijin mahaifiya ta shi ya kirani har gida yace tunda an koreni daga wajen aiki na zuba hannun jari a kasuwancin sa sanin bazai cutar dani ba yasa ba tare da nayi bincike ba nasa kud'ina akan cewar za a dinga shigo da kaya daga k'asar waje a dinga siyarwa sannan zamu dinga raba ribar nayi farin ciki sosai na yi masa godiya," tun daga lokacin sai dai kawai na dinga ganin alert a wannan lokacin n kuma ya kirani yake sanar dani cewar sunyi meeting tare da abokan kasuwancin mu kasancewar ni basu tab'a yin meeting d'in su dani ba yake sanar dani akwai kayan da za a shigo dasu Kuma akwai riba sosai a kayan sai dai akwai matsala wajen shigo da kayan saboda idanun Nigerian army na kan kayan saboda haka tunda Kai d'a ne a wajena na sanar da Kai ka bayar da izinin wucewa da kayan ni Kuma na sanar da shi bazan iya rok'ar alfarma a wajen ka ba hakan ne yasa ya kawo shawarar a zuba maka wannan maganin amma Wallahi bansan kwayoyi aka safara ba da makamai ko ranar da ka same mu a can ranar dai ya sanar dani cewar kaya sun iso amma dai nazo domin a ranar za a yankewa matar ka hukunci ita kuma na goyi bayan kashe ta ne ba dan komai ba sai domin farin cikin daughter amma nayi dana sanin abinda na aikata dan Allah ku yafe mun,"


D'an shiru Maleek ya yi sannan ya mik'e tsaye ya kalli Uncle ya ce "Uncle kenan Alhaji sammani da kake ganinsa ba mutumin kirki bane Nigerian army na da tarihin sa ya dad'e Yana aikata laifuka marigayiya Hajiya Hauwa'u ita ce mata ta biyar da ya aura Kuma kowaccen su ya bayar da ita ne wa k'ungiyar asiri ciki kuwa harda mahaifiyar ka da ya bada jinin ta nasan ba kasan da hakan ba ko?"




Rud'ani firgici nadama da dana sanine suka saukarwa Uncle a lokaci guda jikin sa har rawa yake yi idanunsa sunyi jajir shi kansa Daddy ya girgiza da jin wannan lamarin Maleek kuwa ko a jikin sa bai Kuma damu da yanayin Uncle d'in ba ya ce "Abu na gaba Alhaji Hamisu kwangila da kake gani d'ansa Arfat ya taka muhimmiyar rawa wajen tarwatsa rayuwar 'yarka d'aya tilo shi ya fara raba ta da budurcin ta dukkan wasu kud'ad'e da kake bata shi take kaiwa sannan duk wata kadara tata daka sani gida ko fili duk ta siyar ta Kuma bashi kud'in ita kanta batasan nasan da hakan ba sarai mahaifin Arfat yasan da wannan abun amma bai yi k'ok'arin hana yaron shi ba duk da cewar suna da dukiya a tak'aice dai Uncle kana zaune da mak'iyan ka ne baka sani ba Ni Kuma a daidai wannan lokacin zan yanke wani hukunci game da rayuwata domin na dad'e da Dena kallon Nasreen a matsayin matata saboda haka na yanke duk wata igiyar aurena dake kanta dama nayi Mata d'aya saboda haka na sake ta saki biyu,"




Uncle kuwa tashin hankalin da ya shiga baya misaltuwa sai kawai gani aka yi ya yanke jiki ya fad'i a wajen.
[10/25, 8:58 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️



RUBUTAWA DAGA
HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ)




SADAUKARWA GA
MY DAUGHTER SABEEHA
BILKISU Z.YA'U (🅱️K)
AISHA MAGAJI DABO (AMA)





🇸🇦 ZAMAN AMANA WRITERS
(Gidan zaman lafiya da amana Insha Allah)🤜🤛




Page 38

Da sauri Daddy da Ummi Nasreen da Doctor suka yi wajen Uncle dake kwance tare da Umman Nasreen da shigar ta part d'in kenan.



Maleek kam ko motsawa bai yi ba haka ma su Fauwaz yunk'urawa Sabeeha ta yi zata je wajen Maleek ya yi saurin rik'e ta tare da rungume ta a jikin sa yana girgiza Mata kai hawaye ne suka zubo mata domin Uncle ya bata matuk'ar tausayi k'ara mak'ale Maleek ta yi tana kuka k'asa k'asa.



Ruwa Daddy ya zubawa Uncle take ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya ya tashi zaune sai kawai ya fashe da kuka idanunsa akan Daddy da shima nasa idanun suka yi jajir ya ce "Yaya kana lafiya dai ko?" Daddy ya tambaya hankalin sa a tashe Uncle kuwa hawayen sa ne suka k'aru sai yanzu ya k'ara tabbatar da cewa Daddy masoyin sa ne na gaske duba da abubuwan da ya yi masa kuma Daddyn ya sani amma shi Sam hakan bai d'aga masa hankali sosai ba kamar lafiyar d'an uwan nasa bayan Yana da damar rama fiye da abinda Uncle d'in ya yi masa sai dai shi zuciyar sa kyakkyawa ce ta gaske.


Uncle baisan sanda ya rungume Daddy ba yana kuka ya ce "Dan girman Allah Hamza ka yafe mun nasan na aika maka laifuka da dama naso na cutar da rayuwar ka kai da iyalan ka amma Dan Allah ka yafemun kafin a yanke mun hukuncina Wanda nasan na kisa ne," a razane Daddy ya kalli yayan nasa sannan ya juya yana kallon Maleek da har lokacin rarrashin Sabeen sa yake yi.



K'asa k'asa cikin muryar Kuka ta ce "Please My ka taimaki Uncle ka duba nadamar da ya yi ka duba shima cikin tashin hankali yake I beg you please save his life," shiru kawai Maleek ya yi Yana sauraron inda take kukan ya ce "Zanyi yadda ki ke so amma idan kin daina kukan," shirun ta yi tana sakin ajiyar zuciya.



Daddy kuwa gaba d'aya ya zama speechless ya rasa abin cewa sai kallon Maleek kawai yake yi Umman Nasreen kuwa kwanciya ta yi flat ita da Nasreen suna rok'on Maleek akan ya ceci Uncle Ummi da Doctor ma suka sa baki ga Sabeen sa ma.



Shiru ya yi na d'an lokaci ya kalli Uncle tabbas nadamar sa ta gaskiya ce ya ji a ransa shima yana son taimakon Uncle ko dan soyayyar da mahaifin sa ke masa ko dan nadamar da ya yi ko dan iyalan sa baya ga haka ma akwai k'amshin gaskiyar cewar Uncle ba Mai laifi bane.


Ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Shikenan za ayi bincike," daga fad'in hakan ya yi ficewar sa yabar falon.




Yana fita mota ya shiga Kai tsaye NDA ya nufa tare da sojojin sa ya je suka zauna meeting ya yi musu bayani akan abinda ke faruwa sosai suka jinjinawa k'ok'arin Maleek anan ake bayanin cewar dukkan masu laifin da aka kama Nigerian Army da kanta zata yanke musu hukunci amma sai bayan anyi bincike game da Uncle bayan sun gama tattaunawa akan hakan sannan suka tashi suka nufi gidan gonar Alhaji sammani.




Sunyi motoci sun Kai hamsin jiniya kuwa ta cika garin na KD suna zuwa basu tsaya wata wata ba suka zubawa gidan fetur suka k'one shi k'urmus suka bar wajen.



A gida kuwa bayan tafiyar Maleek Daddy ya d'ago Uncle bayan ya gama neman yafiyar su Ummi har ma da Sabeeha suka yafe masa suka nufi upstairs Umman Nasreen ma ta nemi yafiya tare da Nasreen d'in kanta ba su yi wani tunani ba suka yafe musu suna ta godiya.


Doctor kuwa sallama ta yi musu ta tafi har mota 'yan ukun ta suka rakata ta tafi sannan suka koma ciki Sabeeha kuwa bedroom d'in Ummi ta tafi ta kwanta tana kwanciya bacci ya d'auke ta.



Sabreen da Sameeha kuwa kitchen suka shiga suka fara yin girki Fauwaz kuwa ya koma office haka ma Umar.

Sai Yamma sannan Sabeeha ta farka daga baccin da take yi mik'a tayi tare da yin salati ta kalli agogon dake d'akin zare ido ta yi ta tashi da sauri ta fad'a toilet ta yi wanka tare da alwala ta fito ta kuwa samu an kawo mata kayan ta a gurguje ta shirya cikin wata black d'in atamfa mai touches d'in light blue bata yi kwalliya ba ta zura hijjab ta yi salolin dake kanta sannan ta gyara d'akin Ummin tsaf ta yafa light blue veil sai k'amshi take yi ta fita zuwa down stairs falon ya gauraye da k'amshin girki da air freshener ga Ac na aikin ta fararen kwayayen dake falon sun haska falon sosai.


A hankali ta taka zuwa falon ta samu Ummi da su Sabreen da Sameeha Ummi ta ce "Daughter kin tashi zonan kusa dani," wajen Ummi ta zauna tana amsa sannun da su Sabreen ke yi mata ta kalli Ummi ta ce "Ummi yunwa nake ji," da sauri Sameeha ta tashi ta had'o mata abinci da ruwa da drinks ta kai mata.



Kallon ruwan ta yi ya gaji da yin sanyi take ta tuna Maleek ya hana ta shan Abu mai sanyi a zuciyar ta tace tunda baya nan gara nasha abuna tunda inaso da wannan tunanin ta fara kai lomar abincin bakin ta Maleek ne ya yi sallama a falon yana amsa waya da alama ya d'an jima da dawowa saboda ya canja wanka cikin wasu complete ash color d'in k'ananan kaya ya yi kyau k'amshin sa ya cika falon d'an tsayawa ya yi Yana kallon Sabeeha dake ta kai loma ba ruwan ta d'an murmushi ya yi da ya bayyana dimples d'insa ya shafa tulin kwantacciyar sumar kansa ya ce "Ok Daddy gani nan," ya fad'a tare da nufar upstairs.



Da sallama ya shiga falon Daddy ya amsa masa sallamar kallo d'aya Maleek ya yiwa mahaifin nasa ya ga har ya d'an rame kusa da Daddy ya zauna ya gaishe shi amsawa Daddy ya yi tare da shafa kan Maleek d'in ya ce "Son hankalina yak'i kwanciya akan case d'in Yaya yanzu ya binciken naku ya kasance?"


D'an juya idanu Maleek ya yi ba tare da damuwa ba ya ce "Daddy sai dai fa kayi hak'uri domin Uncle dai da hannunsa dumu dumu a wannan harka dan haka ma ku fara yafar juna," salati Daddy ya yi cikin matuk'ar damuwa.



Tashi Maleek ya yi daga kusa da Daddy yana dariya ya ce "Dama so nake naga yadda zaka yi Daddy munyi bincike mun gane Uncle na da gaskiya bai da laifi," ajiyar zuciya Daddy ya sauke yana hararar Maleek tare da d'aukar pillows d'in kujera ya fara jifan Maleek yana cewa "Marar kunya sai ka bar aikin soja tunda mai daku yake marasa tausayi," da sauri Maleek ya nufi k'ofar fita yana dariya ya ce "Kwantar da hankalin ka Dad ka kusa tashi daga mahaifin ga MG Abdul-maleek zuwa mahaifin Marshall Abdul-maleek Hamza mai dala domin girma za a k'aramun," ya fad'a tare da ficewa.



Murmushi Daddy ya yi Allah ya sani har zuciyar sa yana matuk'a k'aunar Maleek saboda yaron ya yi tako Ina ga biyayya ga kyautatawa ga taimako ga son nasa komai lalacewar sa ga misali kan Uncle duk tsana da muzgunawar da Uncle ya yi masa amma bai damu ba sai ma taimakon sa da ya yi lallai wannan miji da matar 'yan aljanna ne da izinin ubangiji Daddy ya ayyana a ransa.


Maleek kuwa down stairs ya sauka Sabeeha na ganin sa ta yi saurin d'auke ruwan ta b'oye a bayan ta su Sabreen nayi mata dariya kallon su ya yi sannan ya juya idanunsa kan Sabeeha ya zauna gefen ta itama shi take kallo d'aga mata gira ya yi tayi saurin girgiza Kai alamun babu komai ya ce "Sure?"


Noding kanta ta yi ta ce "Yeah,"


"Hmm! Ok zanci abincin nima," kallon plate d'in ta yi sannan ta kalle shi ta ce "Wannan fa nawa ne ni kad'ai nake so na cinye shi," d'an zare ido ya yi yana k'ara kallon abincin da ko rabin sa bata ci ba amma tana zancen duka zata cinye ya gyad'a kai ya ce "Uhmm! Lallai na jinjinawa rowar ki baby yanzu duka za ki cinye?"


"Eh fa," ta bashi amsa tare da cigaba da Kai loma "Amma shi wannan hannun fa da kike b'oyewa a bayan ki fa ko yana ciwo ne?" Girgiza kai ta yi da sauri ta ce "A'a a'a My a haka yake so ya zauna tun d'azu kafin kazo nake dawo dashi daidai amma yana cakud'awa baya abinda za ayi kawai kyale shi za a yi idan ya gaji sai ya dawo da kansa," dariya ta bashi ma ya jinjina kai yana kallon ta tana murmushi.




Itama murmushin take to amma na yak'e sake kallon hannun ya yi ganin yadda take motsa shi tana wani k'ifk'ifta idanunta kamar babyn roba d'age girar sa d'aya yayi Yana kallon ta yana kallon hannun nata yana kallon fuskar ta sannan ya mayar da kallon sa kan k'aramun center table d'in dake gabanta hollandia yogurt ne kawai a kai yayin da plate d'in abincin ke kan cinyar ta.


"Allah dai yasa kar My ya gane,"


"Sabee na kince wani Abu ne?" Da sauri ta ce "A'a bakomai," juya idanunsa ya yi dariya na cinsa Sarai ya ji abinda ta fad'a ya mik'e tsaye tare da rik'e k'ugu ya ce "Sabee na meyasa kuma kike cin abinci ba ruwa kusa," k'asa ta kalla tana juya idanun ta sai Kuma ta kalle shi ta yi murmushi ta ce "Dama ai zan sha...," Tari ta fara tana wani rik'e duk a wayon ta na son ganin ya d'an matsa daga gurin ya je d'auko mata ruwa kafin ya dawo ita kuma ta d'an kora mai sanyin.


Sarai yasan akwai abinda take b'oyewa domin ita bata cin abinci ba ruwa a kusa ganin bai ko motsa ba daga inda yake sai ma tsayawa kallon ta da ya yi ya d'age gira d'aya cak ta tsaya da tarin ta ce "My tari fa nake ka samo mun ruwa na sha," d'an zare mata ido ya yi ganin tarin nata ya tsaya sai Kuma ta cigaba da tarin.



Wannan karon kam sai da ya murmusa har fararen jerarrun hak'oran sa suka fito ya ce "Ayyah Hubbyna sannu wannan tarin naki amma latest ne ko domin naga kamar ana controlling d'in sa da remote," ya fad'a tare da kama kafad'un ta da hannayen sa duka ya mik'ar da ita tsaya har lokacin hannunta na bayan ta tana rik'e da gorar ruwa.



Ya kalli su Sameeha da suke guntse dariyar su ya ce "Sabreen dear d'aukowa Baby ruwa," tashi Sabreen ta yi ta nufi fridge d'in dake daining zata d'auko ruwa da kallo Sabeeha ta bita har zata bud'e ya ce "But not cool one,"



"Toh," Sabreen ta amsa tare da d'auko mara sanyi ta nufe su Sabeeha kuwa sai juya idanu take irin na marasa gaskiyar nan hannu Maleek yasa ta bayan ta ya rik'o hannunta da ta rik'e ruwan ya karb'a yana murmushi ya ce "Hubbyna Shan ruwan sanyi na da illa ga babyn mu," ya fad'a tare da ajiye ruwan saman center table ya karb'i na hannun Sabreen ya tsiyaya a cup ya Kai Mata baki kwab'e fuska ta yi zata yi masa kuka sannan ta kawar da kai gefe ita a dole baza ta sha ba.



"Haba mana baby na please ki sha ruwan nan," mak'e kafad'a ta yi juya idanunsa ya yi ya ce "Shikenan bari na tafi da shi ni," ya fad'a tare da Kai hannu zai d'auke Mai sanyin ta yi saurin rik'e hannun nasa ta ce "Tofah shi nake so nasha," kallon ta ya yi har ranta take son shan ruwan ya ce "Ok amma kad'an zaki sha sannan da kaina zan zuba miki kin yadda?"



"Eh eh na yadda ta fad'a da sauri," gyad'a Kai ya yi ya zuba Mai sanyin rabin cup ya Kai bakin ta da sauri ta rik'e cup d'in tare da had'awa da hannun sa ta shanye ruwan tas har da sauke ajiyar zuciya.



Murmushi ya yi ya ajiye cup d'in ya kalli Rolex watch d'in hannun sa ya ce "Bari naje masallaci," ya fad'a tare da d'aukar ragowar ruwan sanyin ya fice.


Ummi kuwa tana kallon su tana dariya k'asa-k'asa.
[10/25, 8:58 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️



RUBUTAWA DAGA
HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ)




SADAUKARWA GA
MY DAUGHTER SABEEHA
BILKISU Z.YA'U (🅱️K)
AISHA MAGAJI DABO (AMA)





🇸🇦 ZAMAN AMANA WRITERS
(Gidan zaman lafiya da amana Insha Allah)🤜🤛




Page 39


Bayan fitar Maleek ta zauna sai tura baki take yi tana hararar su Sabreen dake yi mata dariya kamar an tsikare ta ta mik'e ta nufi kitchen bata dad'e ba sai ga ta da abinci a hannun ta har da ruwa mai sanyi ta fito da kallo su Ummi suka bita k'ofar fita ta yi "Ina Kuma za ki dear?" Sabreen da Sameeha suka fad'a a tare kallon su ta yi ta ce "Yanzu zan dawo," tana fad'a ta fice daga falon.


Tana fita ta fara kalle kalle Salman ta hango shi da Adam gurin su ta nufa suna ganin ta suka Sara Mata d'an murmushi ta yi ta ce "Salman ko zaka kaini wajen da masu laifin nan suke," ba musu ya ce "Ok muje," daga haka ya yi gaba tana binsa a baya har wani b'angare a gidan d'akin da suke ya b'ude mata a d'an tsorace ta shiga d'akin gaban ta sai da ya fad'i da ta ga inda aka sauya musu halitta da duka d'auke kanta gefe ta yi tana kallon tsohuwa Sailuba dake shimfid'e a gefe ko motsin kirki bata iyawa saboda dukan da ta sha su kuma ganin Sabeeha da kular abinci ne yasa su tsura mata idanu saboda mahaukaciyar yunwar da suke ji.



Kai tsaye wajen tsohuwa Sailuba Sabeeha ta nufa a hankali ta tsugunna a gaban ta duk da kuwa tsoran ta da Sabeehan ke ji ta ce "Ga abinci," ai kafin Sabeeha ta gama fad'a har tsohuwa Sailuba ta wafce kular ta bud'e ta fara ci tab'e baki kawai Sabeeha tayi tare da ajiye ruwan hannun ta ta mik'e zata tafi "Nagode 'yannan kin yi mun alkhairi," waigawa Sabeeha ta yi ta kalle ta ta ce. "Karki damu nayi Miki hakan ne dan Allah sannan da Kuma darajar Rashida," tana gama fad'in hakan ta fita daga d'akin.


Tana fita su Alhaji sammani suka k'wace abincin suka cinye suna dannawa tsohuwa Sailuba zagi.


"MG Ina so ka saki mahaifina ni Kuma ko nawa ne zan biya," wata muguwar harara Maleek ya narkawa mai yi masa maganar sannan ya gyara tsaiwar sa ya ce "Arfat kenan to ba Kai ba ba Kuma mahaifin ka ba duk duniya babu Wanda ya isa ya sani abu domin baku da kud'in da zaku nuna mun Kai kanka kasan gidan su kazo saboda haka tun kafin hukuncina ya biyo ta kanka kabar nan," ganin yadda Maleek d'in ya canja masa fuska ne zuwa had'e rai yasa shi fadin "Shikenan sai anjima," daga haka ya shige motar sa ya tafi.



Tsaki kawai Maleek ya ja tare da juyawa domin shiga part d'in Ummi sai ya hangi Sabeeha da sauri ya k'arasa wajen ta ya ce "Sabee na daga Ina haka Kuma?" Shiru ta yi tana kallon sa shima kallon nata yake yi domin jin abinda zata fad'a d'an murmushi ta yi ta ce "Dama..dama na kaiwa waccan matar abinci ne," girgiza Kai kawai ya yi yayi gaba ta bishi a baya zuwa cikin part d'in Ummi.




Da daddare Umar da Fauwaz suka d'ebi matan su suka tafi gida.


Washe gari kuwa aka sojojin k'asar Nigeria suka yankewa su Alhaji sammani hukuncin kisa inda kowannen su aka harbe shi ya mutu.



A gajiye Maleek ya shiga part d'in Ummi ya zauna akan kujera Sabeeha ce Ke saukowa stairs wajen sa ta k'arasa bayan ta d'auko masa ruwa mai sanyi da cup ta tsiyaya a cup ta mik'a masa tare da fad'in "Sannu da dawowa My," ya ce "Yawwa Sabee Ummi fa?" D'an juya idanu ta yi ta ce "Ummi tana office," jinjina Kai ya yi ya ce "Zo muje ki rakani part d'in mu nayi wanka mana," mak'e kafad'a ta yi ta ce "Uhm uhm nikam bazan bika ba," mik'ewa ya yi tare da d'aukar ta cak ya nufi k'ofar fita yana cewa "Aikuwa yarinya baki isaba ladan ne bakya so ki samu," ita dai Sabeeha sai zillewa take yi domin tsoron had'uwar su take ji saboda an kwana biyu ba a gamu ba.




Ko ta kan mota bai bi ba a k'afaya nufi part d'in Yana rik'e da ita kamar jaririya duk inda suka gifta idanun ma'aikatan gidan na kan su suna kallon su cikin burgewa bai ajiye ta ba sai da suka shiga bedroom d'insu sannan ya ajiye ta akan gado ya fara cire Mata kayan jikin ta ta ce "Allah fa My ni nayi wanka na," bai ko damu ba ya ce "Na sani wani nake so ki k'ara yi," bata sake magana ba har ya cire Mata kayan ya d'auke ta zuwa toilet.




Sun dad'e sosai a ciki sannan suka fito d'aure da towels Sabeeha sai tura baki gaba take yi shi Kuma yana you mata dariya "Dama nasan ba wani wanka da zaka Bari ayi ai,"


"To yarinya ko iya haka ai kin samu lada," ya fad'a tare da jawota jikinsa ya zare towel d'in jikin ta ya ce "Yanzu Kuma ladan da Zaki samu yafi na d'azu," ya fad'a tare da kwantar da ita saman gadon ya fara aika mata da wani irin kissing Mai tsayawa a rai tun tana basarwa har itama ta biye masa suka fara bawa junan su farin ciki.




Sun dad'e suna aikin abu d'aya abinka da an dad'e ba a gamu ba sannan suka sake yin wanka suka shirya cikin k'ananun kaya Maleek riga da wando farare Sabeeha Kuma pink d'in doguwar riga sai k'amshi suke zabgawa hannun su rik'e da juna suka fita dga part d'in.




Suna zuwa part d'in Ummi suka samu ta dawo nan fa suka zauna zaman fira a nan Maleek ke sanarwa da Ummi cewa gobe zasu tafi dubai shi da Sabeen sa Ummi tayi musu fatan alkhairi tun daren ranar suka had'a kayan su tsaf washe gari 'yan uwa da abokan arzik'i suka yi musu rakiya airport tare da zugar sojoji suka hau jirgi sai Dubai.



A gajiye suka k'arasa gida kamar wad'an da suka je a k'asa wanka suka yi suka ci abinci sannan suka kwanta baccin gajiya rungume da juna abinsu.



Zuwan su Dubai ba k'aramun kwanciyar hankali suka samu ba ga wata kulawa da suke bawa juna more especially ma Maleek da yake ganin Sabeen sa ba ita kad'ai bace hakan ne yasa shi zage damtse wajen ninka kulawar sa a kanta kullum sai sun fita yawo abin su yau suna shopping gobe suna shan icream ko cinema jibi suna restaurant.



Babyn su kuwa kamar zasu saye Dubai Mall gaba d'ayan ta saboda siyayyar da suka yi masa duk wani Abu na buk'atar jariri da wasan sa sun siya sun ajiye kullum suna kan hanyar siyayyar baby a b'angre guda Kuma su Ummi da Doctor ma ba a barsu baya ba wajen siyayyar harma da Daddy da Abba da suke murna sun kusa samun jika ko ince jikoki domin Sabreen da Sameeha ma suna da shigar ciki.




Rinaz da take India ma kullum cikin yi musu waya take ballantana Sameeha da Sabreen su ji labari haka ma Zainabu itama tana Kira harma da mutanen Abuja su hanfa abun mamaki kuwa Kira harda su Nasreen domin ta yiwa kanta karatun ta nitsu daga ita har iyayen ta dan Uncle ma yabi Daddy Landon a can Daddy yasa baki aka mayar da Uncle bakin aikin sa yadda ya cigaba da aikin sa cikin mutunci da amana.



Haka rayuwar ta cigaba da kasance musu cikin farin ciki a kowanne bangare a haka har cikin Sabeeha ya shiga watan haihuwa lokacin ne Kuma Ummi ta fara damun Maleek da waya akan cewar lallai ya d'auki Sabeeha su koma Nigeria saboda ta haihu a gida.


Yanzu ma zaune suke a falo Sabeeha na kwance jikin Maleek sai sauke masa shagwab'a take

Please Login or Register in order to submit comment