Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

take so aikuwa ta kama Zainabu da duka sai ihu take yi.



Dakyar Abba da Sameeha suka raba fad'an ya yinda Sabreen ke gefe tana kallon su dan bata so aka raba ba so tayi Sabeeha ta yiwa Zainabu jinajina duk abinda zai faru ya faru.



Zainabu kuwa fita ta yi tana kuka kamar wacce Uwar ta ta mutu tana zuwa zauren gidan su ta k'ara volume d'in kukan ta.



Lantana matar Kawu Bala tana jiyo kukan Zainabu ta mik'e tana karkad'e zani ta d'urma ashar ta ce "Wane d'an shegiyar ne ya tab'a mun 'yata Wallahi yau sai an hau sama dani," Zainabu ta ce "Lantana kinga 'yan uku ko daga zuwa gidan su suka hauni da duka har ma da Uban su," mayafi Lantana ta d'auka tana cewa "Muje gidan yau zanga uban da ya tsaya musu har suka dokar mun 'ya," haka tasa Zainabu a gaba suna tafe tana masifa.



A hanya suka ci karo da Kawu Bala shima yana jin abinda Zainabu ta fad'a ya bisu shima Yana balbala kalar tasa masifar.


Suna zuwa suka samu 'yan uku zaune a kan tabarma kawai suka rufe su da duka su Sabeeha kawai ji suka yi an rufe su da duka tako ina gashi Abba ya fita baya nan tab'arya Zainabu ta d'auka ta nufi Sameeha dan duk a tunaninta Sabeeha ce Aikuwa ta rafka mata a goshi.



Wata k'ara Sameeha ta saki ta fad'i sumammiya hankali tashe Sabeeha da Sabreen suka yi kanta suna kuka jijjiga ta Sabeeha ta fara yi tana cewa "Sameeha dear please ki tashi karki mutu ki bar mu a wannan halin please," ganin da su Kawu Bala suka yi Sameeha bata yin ko motsi aikuwa suka fice a tsorace.



Sabeeha da Sabreen kuwa sai kuka suke yi suka d'ebo ruwa suka zuba mata ajiyar zuciya Mai nauyi ta sauke sai dai har lokacin jini sai zuba yake yi daga goshin ta a rikice Sabeeha ta fita ta nemo mai machine suka kai Sameeha chemist treating d'in wajen aka yi mata tare da magunguna sannan suka tafi gida.



Ko da suka koma gida ruwan wanka suka d'ora mata ta ta yi wanka ta kwanta sannan suka dafa taliya da manja suka ci Saneeha tasha magani ta kwanta saboda ji take yi kanta kamar zai tsage domin ba k'aramun ciwo yake mata ba.

Da Abba ya dawo hankalin sa ba k'aramun tashi ya yi ba ganin kan Sameeha nannad'e da Bandage ko da su Sabeeha suka fad'a masa abinda ya faru hak'uri kawai ya iya basu.



Kawu Bala sai da ya yi kwana biyu bai je gidan ba a b'angaren su Sabeeha kuwa ba k'aramun dad'in hakan suka ji ba sai dai duk da haka hankalin su ba a kwance yake ba saboda ciwon kan Sameeha kullum k'aruwa yake yi wataran har kuka suke tasa ta a gaba su yi tayi saboda gani suke yi kamar mutuwa zata yi ta barsu shi kansa Abba hankalin sa ba a kwance yake ba.

Wata rana da yamma Sabeeha ta fita zuwa shagon shazali ta siyo maggi suka ci karo da Zainabu itama an aike ta shagon kallon banza Zainabu ta yi mata ta ce "Ina mara kunyar gidan ku ai nasan yanzu ta shiga taitayin ta banzaye Karuwai ashe gado ku ka yi ashe haka uwar ku ma ta tafi yawon karuwanci sai dai ita nata yawon yayi riba tunda gashi har yanzu bata dawo ba tun kuna yara," wani irin juyawa kan Sabeeha ya fara yi juyawa kawai ta yi ta nufi gida tana jin kanta ya yi mata wani mugun nauyi.



Da gudu ta k'arasa shiga gidan Abba da Sabreen ne zaune a kan tabarma sai Sameeha dake gefe a kwance da sauri ta k'arasa ta zauna gaban Abba hawaye na fita a idanunta ta ce "Abba Dan Allah kaji tausayin mu ka fad'a mana ina maman mu take Abba ashe dama maman mu na raye bata mutu ba," Sabreen a rikice ta ce "Sabeeha dear waye ya fad'a miki maman mu na raye?" Cikin kuka ta ce "Yanzu Zainabu ta fad'amun wai maman mu yawon karuwanci ta tafi ta barmu Abba meyasa meyasa mama zata yi mana haka?" Dukan su kuka suke yi har Abba Wanda aka tab'o masa inda ke masa ciwo ya ce "Ku gafarce ni yarana maman ku na raye Amma ba yawon karuwanci ta tafi ba hakan ba halin Maryam bane," share hawaye Abba ya yi ya cigaba da cewa "Tun ina yaro mahaifana suka rasu daga ni sai Yaya Bala mu kad'ai iyayen mu suka haifa sai dai tun muna yara Yaya Bala ya d'auki tsanar duniya ya d'ora mun saboda a cewar sa iyayen mu sunfi sona kuma bakomai ne yaja hakan ba sai dan nafi jin maganar su nafi yi musu biyayya shi kuwa babu Wanda ya isa ya sa shi ballantana ya hana shi tunda iyayen mu suka rasu Kuma na rasa gata domin Yaya Bala baya duba maraicin mu haka zai tara abokan sa suyi mun duka haka rayuwata ta cigaba da kasancewa daga baya da naga rayuwa na yi mun wuya saina fara neman aiki saboda mu bamu yi makaranta ba Kuma iyayen mu 'yan gudun hijarane bamu san kowa a garin nan ba haka nayi ta bin shaguna ina neman aiki har na had'u da malam Haruna Wanda yanzu ya rasu Allah sarki mutumin kirki shine ya d'auke ni a matsayin yaron shagonsa ina zama idan mun tashi ya sallame ni Ni Kuma idan ya bani bana kashewa duka nake yin tari sannan duk sanda kaya ya k'are mana muke shiga cikin kaduna muyo sarri a haka har muka saba da Wanda muke zuwa sari wajen sa a birni har ya tambayi Malam Haruna ni d'ansa ne malam Haruna bai b'oye masa komai ba ya fad'a masa ni maraya ne mutumin ya tausaya mun sosai sai kawai ya xe da malam Haruna dan Allah a bashi ni na zama yaron sa koda malam Haruna ya tambayeni nace na yadda saboda mutumin Yana da kirki sosai haka na koma kaduna da zama sannan idan aka tashi Yana bani kud'i da yawa hakan ne yasa na koma makarantar islamiyya,"



Shiru Abba ya yi sannan ya cigaba da cewa "haka na cigaba da zama a wajen Malam Usman har na girma a lokacin ne kuma cuta ta kama malam Usman har ya rasu bayan ya mallaka mun shagon kyauta saboda ya sanar dani shi ba d'an kaduna bane sannan bai da kowa nayi kukan rashin sa haka na cigaba da zama da shi har na kai shekara talatin da biyu a lokacin ne na had'u da Maryam kyakkyawa ce sosai sannan iyayen ta masu kud'i ne kuma hakan bai sa ta kasance mai girman Kai ba tana da mutunci bata da wulak'anta talakawa ko kad'an kusan kullum tana zuwa shagona siyayya ba Dan komai ba sai dan jinin mu ya had'u da ita abu kamar wasa na fara jin soyayyar ta a zuciyata tun ina b'oyewa har sai da na fad'a mata ga mamakina sai na ga ta kamu da matuk'ar farin ciki ashe itama ta dad'e tana sona sai dai lokacin da iyayen ta suka ji ba irin wulak'ancin da bangani ba saboda sun tsane ni kasancewa ta ba mai kud'i ba har duka mahaifinta yasa aka yi mun akan na rabu da ita dan bazai bani auren tilon 'yar sa ba Amma kamar k'ara sonta nake yi haka itama a nata b'angaren ta zab'i zama dani iyayen ta suka ce to indai ta nace sai ni babu su ba ita tace ta yadda haka aka d'aura auren mu na tafi da ita garin mu dama Ina da gadon wannan gidan a ciki muka zauna lokacin Kuma Yaya Bala ya yi aure ya auri Lantana zama muke Ni da Maryam zaman lafiya sai dai Kawu Bala yana d'ora idanunsa akan Maryam ya ji ya tsane ta ba dan komai ba sai dan ita ta kasance mai ilimi domin a k'asar waje ta yi karatu gata kyakkyawa sab'anin matar sa masifaffiya ce sannan ba ilimin boko bana Arabic kamar yadda shima yayan ya kasance hakan ne yasa suke mata hassada k'iyayyar da Yaya ke mun saita shafi Maryam ba irin wulak'ancin da ba ayi mata ba amma ta shanye Dan tana da hak'uri da kawaici a haka har matar Yaya Bala ta haifi d'anta na fari Faruk lokacin ne Kuma aka farke shagona dana dawo da shi nan k'auyen aka kwashe min komai na ciki da Kuma cinikin dake shagon daga lokacin na koma ba cin yau babu na gobe Maryam kuwa iyayen ta suka watsar da ita har kaduna ta je ta nemi gafarar ta suka yafe mata lokacin tana d'auke da cikin ku haka muka cigaba da rayuwa saboda iyayen ta sun bani wani jarin a haka har aka haife ku kyakkyawa da ku sannan kuna kama da Maryam sai dai ita ta fiku haske sosai haka muka cigaba da rainon ku inda muka sa muku sunana mahaifiyar Maryam wato Rukayya ke kenan Sabeeha sai Sadiya sunan mahaifiya ta wato Sabreen Sameeha Kuma sunan kakar Maryam Hajara kuna da shekara uku wata rana na fita shago ina dawowa na tarar Maryam bata nan har dare bata dawo ba hankalina ya tashi sosai a haka har akayi sati d'aya kawai saina shirya naje kaduna Amma da naje sai na samu labarin mutuwar iyayen Maryam da suka yi hatsarin jikin sama sannan an tabbatar mun Maryam ta je garin sai dai tunda iyayen ta suka rasu ta siyar da gidan tabar unguwar ba neman da banyi mata ba Amma ban ganta ba haka na hak'ura na dawo sai dai ina dawowa na tarar an Kuma farke shagona an sace komai sannan ku kuma naje na tarar matar Yaya ta yi muku duka harta fasawa Sabeeha baki haka na d'auke ku zuwa gida na cigaba da kula da ku na koma wajen Malam Haruna sai dai shima lokacin Yana kwance ba lafiya 'ya'yan sa ke zama a shagon haka nai ta dako ina ciyar da ku har kuka kawo wannan lokacin akwai wata rana da akayi bak'i a k'auyen nan anan Sadam ya ga Sabeeha ya ce Yana rik'o ni sam ban yadda dashi ba saboda Sam bai da isasshiyar tarbiyya Amma Yaya Bala yayi caraf yace ya bashi ke ya saku a makaranta haka yake aiko driver Yana Kai ku Yana d'auko ku inda naji dad'i Yaya bai nuna baya so ba saboda yana tsoron Sadam haka ya cigaba da d'awainiya da ku komai ya siyo Miki sai kik'i k'arb'a kice sai ya kawowa 'yan uwanki tun daga ranar komai zai siyo miki guda uku yake siyowa wannan ne labarin mu Amma Wallahi Maryam ba yawon banza ta tafi ba sai dai bansani ba ko tana raye ba ko ta mutu sannan bansan meyasa ta tafi ta barmu ba," kuka sosai su Sabeeha ke yi gwanin tausayi har shesshek'a suke yi dakyar Abba ya yi k'arfin halin rarrashin su.



Tun daga lokacin su Sabeeha su ka fara addu'ar Allah ya bayyana musu maman su.



B'angaren Maleek kuwa tun washe garin da aka Kai Nasreen ya dena shiga harkar ta har kallo bata ishe shi ba idan ta gaishe shi zai amsa daga haka ba ruwan sa da ita.



A haka har aka yi sati d'aya ranar yana part d'in Ummi kasancewar ranar week end ne Ummi bata fita office ba da kanta ta yi masa girki fira su Ummin ke yi ita da su Fauwaz shi dai Maleek bai ce Komai ba.



Ummi ta ce "Rinaz gobe ki shirya kije gidan Doctor Maryam Dan ta damu kije Wai kwana biyu bakya zuwan mata," Rinaz ta ce "Nima Ummi ai nayi missing d'in ta Allah sarki mamana Wallahi Ummi ina son Mama sosai tana da kirki sosai," Fauwaz ya ce "Gaskiya dai akwai kirki nima tana burgeni," Murmushi Ummi ta yi ta ce "Ku ma kenan Ni kaina ina son Doctor Maryam k'awa ce ta gari ko a asibiti kowa yabon halin ta yake,"


"Son," Ummi ta kira shi kallon ta Maleek ya yi sannan ya ce "Na'am Ummi,"


"Ka ga daga yau fa ba k'ara yi maka girki zanyi ba," zare ido ya yi ya ce "Why Ummi?"

"Saboda gobe matar ka zata fara yi maka girki," langab'ar da Kai ya yi ya ce "Allah Ummi ba ta iya ba," dariya Ummi ta yi ta ce "Ta ya kasan bata iya ba bayan ba tab'a cin abincin ta kayi kaji ba?" Ya ce "Ai shiyasa nace bata iya ba ban fa tab'a gani ta yi ba," Rinaz ta ce "Wallahi kuwa Ummi bata iya ba akwai sanda na tab'a ci Kai abin kamar ayi amai ko a ido," pillown kujera Ummi ta jeri Rinaz da shi ta ce "Kinga Mamana ki kiyaye ni," tura baki Rinaz ta yi ta ce "Allah Ummi dagaske," shi dai shiru ya yi bai Kuma magana ba haka ma Fauwaz da ko maganar Nasreen baya so ayi.


Washe gari kuwa 'yan aiki ne suka yiwa Nasrin girki kamar gaske tasa a ka jera mata komai a daining a waya ta kira Maleek ta sanar masa an gama abinci yace Yana zuwa.


Dama lokacin Yana waccan part d'in nasa wanka ya yi ya shirya cikin black trouser pencil tare da white T-shirt sannan ya d'ora bottles one a sama tare da black tunber loon takalmi a kafarsa sai zabga k'amshi yake yi kan nan yasha had'adden aski sai shek'i yake yi yana fitowa sojojin sa suka bud'e masa k'ofa aka jashi zuwa d'ayan part d'in da Nasreen ke ciki duk da ba nisa Amma abin ku da Mai mulki da gata sai a mota yake zuwa suna zuwa soldier's suka bud'e musu gate suka shiga aka bud'e masa k'ofa ya fita.



Da Sallama ya shiga falon Nasrin na zaune ta hakimce a kujera tasha kyau ba laifi cikin doguwar rigar material ga 'yan aiki zagaye da ita.



Tunda ya shigo take binsa da ido domin ba k'aramun kyau ya yi ba tafiya yake yi cikin k'asaita ji take yi kamar ta je ta rungume shi a jikin ta sai dai ba fuska.




A hankali ta tashi ta nufi inda yake ta ce "Sannu da zuwa ya Maleek," ya ce "Yawwa," daga haka suka nufi daining yana jin haushin kallon da 'yan aikin ke binsa da shi sannan ga haushin Nasreen da yake ji ita sam ba ruwanta bata cewa 'yan aikin su basu guri indai yaje part d'in ko magana zata fad'a masa bata cewa su bar wajen.


Kujera ta ja masa ya zauna sannan ta fara sarving d'insa abinci kallon abincin yake Yana yatsina fuska domin ko a ido bai da kyan gani sai dai da gani tasha uban curry shinkafar Wai nan a dole anyi jallop sai dai naman da akasa kamar zai yi magana zama tayi tana wani fari da ido ita a dole ta yiwa miji girki.



Kad'an ya d'iba a spoon ya kai bakinsa da sauri ya fesar Yana aikawa Farida harara domin 'yan aikin Ummi ma sunfi nasu iyawa sau dubu balle shi da ya saba cin na Ummi.



Sink d'in dake daining d'in ya je ya kuskure bakin sa sannan ya koma ya zauna ya zuba ruwa yana sha Yana hararar Nasrin.



Ta ce "Ya Maleek lafiya maiya faru?" Sai da ya yatsina fuska sannan ya ce "Who cook for me?" Ta ce "Maid's," ya ce "Maid's Ni kika bawa 'yan aiki suka ma girki to bari kiji daga yau ban yadda wata a cikin su ta yi mun girki ba dan haka tashi ki je ki dafo mun wani," Yana fad'ar haka ya nufi cikin falon ya kalli 'yan aikin ya ce "Kubar mun nan," da gudu suka fice shi Kuma ya zauna Yana kallon diamond watch d'in hannunsa sannan ya kalli Nasreen ya ce "Ki wuce ina jiran ki," wucewa ta yi tana k'unk'uni shi Kuma ya yi k'wafa Yana danna wayar sa.




Ta dad'e sosai a kitchen d'in kace wani wahalallen girki take yi shi Kuma Yana sane yasa ta dan so yake ya gwada ta ya gani ta iya ko bata iya ba sai da ta yi wajen awa biyu sannan ta fito hannunta rik'e da plate ashe duk dad'ewar da tayi jallop d'in taliya take girkawa.



Har zata wuce daining ya ce "No need kawo mun nan," ya fad'a yana nuna mata center table ajiyewa ta yi zata zauna ya ce "Kawo mun ruwa," tashi ta yi ta kawo masa ruwa da cup har da lemo sai lokacin ya kalli abinci a zuciyar sa ya ce duk dai d'aya.



A tsorace ya Kai abincin bakin sa Yana addu'ar Allah yasa kar ya yi amai ai da gudu ya tashi daga wajen yaje ya zubar ya fara aikin kuskure baki kamar Wanda yaci d'anyen nama idanunsa sunyi jajur.



Komawa ya yi ya kalle ta yace "D'auke abincin ki," d'auka ta yi tabar wajen ta Kai kitchen sannan ta dawo saboda ji ya yi taliyar kanta bata dahu ba ga uban ya ji gashi an cika maggi ga curry an zabga har k'anin maggi taliyar ke yi ya ce "Zauna," ta zauna ya ce "Ba ki iya girki ba?" Ta ce "Uhm ni ban tab'a yi ba," jinjina kai ya yi ya ce "Good ki shirya gobe Rinaz zata zo ta koya miki," zata yi magana ya ce "Karki kuskura Wallahi," shiru ta yi shi Kuma ya fice.



Kamar zai yi kuka ya je yana bawa Ummi labari itama Ummi ta tausaya masa tashi ta yi da kanta ta girka masa tana tunanin ya zama dole ta samowa Maleek wacce ta iya girki dan bazata barshi ya dinga zama da yunwa ba gashi ya ce Rinaz ma da kad'an nata ya fi na 'yan aikin.



Washe gari Nasreen ta je koyawa Nasreen girki sai dai ita Nasreen mugun son girma ne da ita Wai lallai sai dai Rinaz ta je kitchen ta yi girki sannan ta kaiwa Nasreen d'in taci sannan Kuma ta fad'a mata yadda ta yi ta girka da kuma abubuwan da tasa aikuwa Rinaz ta yi tsalle ta dire ta ce wallahi bazata yi ba sai dai su shiga kitchen d'in tare a yi a gabanta ta gani aikuwa nan Nasreen ta fara zage-zage.



Ganin haka Rinaz ta d'auki mayafinta tabar gidan.



Ko da Rinaz ta fad'awa Maleek jinjina kai ya yi ya ce "kyale ta tayima kanta idan ma ta iya kanta idan ma akasin haka kanta," tun daga ranar bai sake magana akan girkin ba haka ma Nasreen Rinaz ma tafiyar ta gidan k'awar Ummi doctor Maryam ta yi.

Kwana biyu a tsakani Maleek ya shirya tare da sojojin sa suka tafi duba wata masana'anta a wani k'auye sanye yake cikin uniform d'in su na sojoji ya yi kyau sosai motoci suka shiga suka d'auki hanya.


Sabeeha da Sabreen ne zaune a tsakar gida sun sa Sameeha a gaba sai kuka suke yi ganin yadda take jin jiki saboda kanta dake matuk'ar yi mata ciwo duk ta rame Abba ne ya yi Sallama da sauri Sabeeha ta tare shi ta ce "Abba an samo mai motar?" Ya ce "Eh yana waje ku yake jira ku taso mu tafi," Sabreen ta ce "A'a Abba ka zauna a gida kaima baka da lafiya Ni da Sabeeha dear mun isa," Sabeeha ta ce "Eh Abba ka zauna," haka ya zauna su Kuma suka kama Sameeha zuwa mota suka tafi gashi tunda ranar da su Kawu Bala suka dake su basu k'ara zuwa gidan ba.



Tunda suka hau titi Sabeeha ke lure da wasu garada machine biyu suna binsu bata damu ba sannan bata gayawa Sabreen ba har suka je wani k'aramun asibiti dake garin dake gaba da nasu shima k'auye ne garin sai dai yafi nasu samun ci gba.



Emergency room aka Kai Sameeha likita ya fara dubata yayin da su Sabeeha ke waje suna jiran fitowar likita sai gab da magriba sannan likita ya fito da sauri da takarda a hannunsa ya mik'awa Sabeeha ya ce "Ki sauri yanzu ki fita wajen asibiti ki siyo wannan maganin dan bamuda shi a nan," Sabeeha ta ce "To doctor," ya ce "Ki hanzar ta dan yanzu ake buk'atar sa da gaggawa," ta ce "Toh," ta kalli Sabreen ta ce "Sabreen dear ki zauna a nan bari naje na dawo," tana fad'ar haka ta fice da sauri ga hadari ya had'o sosai a garin tana fita harabar asibitin ta ga wad'an nan na machine d'in da suka biyo su tun daga k'auye bata damu da kallon da suke mata ba ta k'ara sauri burin ta kawai ta je ta siyo maganin ta koma.



Sai dai abinda ta lura da shi shine suma binta suke yi k'ara sauri ta yi har tana had'awa da d'an gudu.



Tafiya motocin MG ke yi bana wasa ba jiniya kawai ke tashi shi kuwa yana bayan wata benz Army green sai kallon Rolex watch d'in hannunsa yake yi domin ya matsu su isa gida sai dai Yana kallon agogon ya ga time d'in sallar magrib ya yi a hankali kamar mai koyon magana ya ce "Salman idan an samu masallaci gaba mu tsaya time d'in sallah ya kusa," Salman dake zaune a gaban mota ya ce "Ok," motocin gaba ya sanarwa umarnin ogan nasu aikuwa basu dad'e suna tafiya ba suka tarar da masallaci.



Waigawa Salman ya yi ya ce "An samu masallaci sai dai a k'auye ne Kuma masallacin ba wani Mai kyau bane," kad'an Maleek ya murmusa har dimples d'in sa suka lotsa sannan ya ce "Salman kenan ibada ai ba sai a waje Mai kyau ba kuma suma masu yi a ciki ai mutanene kamar ni kuma nasan babu najasa a wajen domin na tabbata baza su yi sallah a wajen da yake da najasa ba dan haka muje kawai," Yana gama fad'in haka bai jira an bud'e masa k'ofa ba ya bud'e ya fice.



Salman kuwa k'imar Maleek ce ta k'aru a idanunsa domin shi mutum ne mai son jama'a ba ya kyankyamun talakawa sam balle kuma wulak'anci shi kowa nasa ne.



Sabeeha kuwa ganin sun biyo ta ne yasa ta d'iba da gudu suma suka bita gudu take yi sosai suma haka d'aya a cikin su ya ce "Mu tabbatar mu kama ta saboda biyan mu Rashida ta yi sannan bayan ita mu nemo ragowar," jin haka yasa Sabeeha k'ara gudu har ta fita titi gashi tunda ta fito bata ga jama'a ba ko d'aya.



A can nesa ta hangi wasu Manya Manyan sababbun motoci sunyi guda goma Sha biyar da Kuma sojoji a tsaitsaye da bindigu da gudu ta d'iba ta yi wajen daidai lokacin Maleek ya gama alwala ya mik'e kenan ta wuce ta gaban sojojin kamar walk'iya ta rungume shi ta baya tsam tana b'uya a bayan sa wani irin shock Maleek ya ji a jikin sa k'ok'arin juyawa yake yi ya ga waye ya rik'e shi haka Amma ba dama saboda yadda ta k'ank'ame shi cikin daddad'ar muryar ta ta ce "please help me zasu kamani Kuma Sameeha dear na buk'atar magani yanzu," sojojin sa ne suka yo wajen sa a zafafe domin zuwa su hukunta yarinyar da ta tab'a musu ogan su da sauri ya d'aga musu hannu suka tsaya sannan ya kalli 'yan daban da suka biyo ta sun tsaya cirko cirko suna ganin kallon da yake musu suka fara ja da baya Maleek ya kalli sojojin sa ya ce "Yanzu nake buk'atar ku zo mun da su," sai lokacin Sabeeha ta sassauta rik'on da ta yi masa amma idanunta a runtse suke waigawa ya yi a hankali Yana kallon ta yadda ta rintse idanune yaso bashi dariya.


Wai gawa wajen da Sojojin sa suke ya yi ya ga suk basa nan sun tafi bin umarnin sa ajiyar zuciya kad'an ya sauke tare da kallon agogon sa sannan a hankali ya juya wajen yarinyar sai dai Yana juyawa ya ga wayam ba kowa gefe da gefen sa ya kalla nan ma ya ga ba kowa a zuciyar sa ya ce "To Ina kuma ta yi?"




Ita kuwa Sabeeha kunyar rungume shi da ta yi ne yasa ta zanzare bai saniba ta gudu chemist d'in taje ta siya maganin sannan ta nufi asibitin tana mamakin dama Rashida 'yar daba ce da wannan tunanin ta k'arasa asibitin.



Da gudu ta k'arasa Emergency ta

Please Login or Register in order to submit comment