Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka yiwa mummy sallama bayan ta cika su da abin arzik'i su turaruka kayan make up da sark'ok'i da agoguna masu tsadar gaske suna ta godiya sannan suka tafi.




Direct gidan Ummi Umar ya Kai su da sallama suka shiga falon Fauwaz suka samu kwance akan kujera yana waya yana cewa "Kai haba ki kwantar da hankalin ki zan zo insha Allah," ai tuni Sabreen ta had'e girar sama da ta k'asa sai ka rantse bata tab'a dariya ba tunda take.



A zafafe ta nufi inda Fauwaz ke kwance ta fisge wayar ta kara a kunne muryar budurwar ta ji tana cewa "Please karka k'i zuwa I'm waiting for you,"




"To munafuka bazai zo ba Wallahi indai Sabreen na raye sai dai idan mutuwa nayi ke yanzu ko kunya bakya ji kinsa mijin wata a gaba kina cewa yazo wajen ki to Wallahi ki kiyayeni marar aji kawai," fisge wayar Fauwaz ya yi ya kashe ya ce "Haba my Love wannan fa friend d'ita ce tare muka yi school da ita a Landon," hararar sa Sabreen ta yi sannan ta zauna a inda ya tashi ta zabga tagumi sai hawaye.


Ummi dake kallon su ta saman bene ta yi murmushi ta koma d'aki abinta.



Hankali tashe Fauwaz ya zauna gefen Sabreen yasa hannunsa ya cire mata tagumin harara ta zabga masa sannan ta cigaba da kukan ta ya ce "Please dear calm down," cikin muryar kuka ta ce "Ank'i ai calm down d'in kuma wallahi Allah ya isa tsakanina da ita iya muryar ka da taji," ta fad'a tana sakin wani kukan shi dariya ma ta bashi ya dake ya ce "Please mana ki fahimce ni," murgud'a Baki ta yi.




Sabeeha kuwa dariya ta yi ta girgiza Kai sannan ta haye stairs.



Su Sameeha kuwa tsayawa suka yi ganin drama tashi Sabreen ta yi zata bar falon tashi shima Fauwaz ya yi ya janyo mata hannu abinka da mara k'arfi tafiya gaba d'aya ta yi zata fad'i yayi saurin rik'o abar sa ta fad'a a jikin sa.



Ai tuni su Sameeha suka zanzare sukabar falon Sabreen kuwa ba k'aramun tsorata ta yi ba ta fara k'ok'arin janye jikin ta amma Fauwaz ya hanata ta ce "Ni kawai ka cikani na tafi," ya ce "Please don't be upset with me try to understand me dear," ta ce "To ni cikani," sakin ta ya yi ta d'anja baya sannan ta kwasa da gudu ta yi stairs tana cewa "Ank'i a tsaya d'in," zama kan kujera Fauwaz ya yi ya dafe Kai ya ce "Tofah meerah kin jawo min ruwa ya zanyi da rigimar Sabreen,"





Sabreen kuwa da gudu ta shiga d'akin Rinaz a nan ta same su dariya Sameeha ta yi ta ce "Dear wannan gudun fa?"



"Bakomai," Sabreen ta fad'a tana zama Sameeha ta ce "Amma sister ya kamata ki tsaya ki saurari abinda zai fad'a miki," shiru Sabreen ta yi ba magana Rinaz ta ce "Ya Fauwaz na falon?" Gyad'a kai Sabreen ta yi ficewa Rinaz ta yi.





A falo ta samu Fauwaz a zaune da kallo ya bita har ta k'arasa kusa da shi ta zauna kallo d'aya ya yi mata yasan tana da damuwa ya ce "K'anwa ya aka yi ne?" Hawaye ta share ta ce "Ya Fauwaz kaji wai Daddy India zai turani karatu kuma ni wallahi bana so na tafi nabar 'yan uku sai dai mu tafi tare," zare ido Fauwaz ya yi ya ce "K'anwa kenan maganar ku tafi tare babu ita domin kwanan nan zamu yi wuff da su amma ki gayawa Ummi ta yi masa magana may be ya janye,"





"Na fad'a mata tace zata yi masa magana amma kana ganin zai hak'ura kasan halin dad indai magana akan karatu ne Kuma fa next week yace zan tafi," jinjina Kai Fauwaz ya yi ya share mata hawaye ya ce "Ki kwantar da hankalin ki insha Allah zai barki kiyi a nan kinji?" Noding kanta ta yi sannan ta tashi ta nufi stairs.


Haka rayuwa ta cigaba da tafiya satin su d'aya a gidan Ummi suka koma gidan Mama inda a sati d'ayan nan Sabreen bata bari suna had'uwa da Fauwaz ko wayar sa dena d'agawa ta yi duk ya damu ya fad'awa Ummi ita Kuma ta ce ba ruwan ta sunfi kusa.



Sabeeha kuwa tana lissafe da ranar da Maleek ya ce Mata zai dawo ya wuce yana sati na biyu amma bai yi mata maganar zai dawo ba itama kuma bata yi masa ba saboda tasan yanayin aikin nasu.



Kawu Bala ne zaune a tsakar gidan sa ya zabga uban tagumi kamar ko yaushe Lantana na gefe itama duk ta fita hayyacin ta saboda yunwa Zainabu na gefe a kwance kan tabarma haihuwa ko yau ko gobe kallon ta Kawu ya yi ya kalli Lantana ya ce "Lantana mun cuci kan mu ki duba halin da muka jefa kanmu a ciki nayi nadamar abinda na yiwa d'an uwana da iyalan sa ki duba abinda zamu ci ma babu duk wani abu namu na amfani duk mun siyar gidan nan kad'ai ya rage mun bansan me Kuma zai faru ba duk sanda Maryam ta taka k'afar ta a garin nan ba nayi nadama Wallahi," ya fad'a yana share hawaye.





Lantana ta ce "Tabbas mun tafka babban kuskure a rayuwar mu mun aikata laifi babba banga amfanin hassada ba a rayuwata nima nayi dana sani gashi Sadam tunda ya koro yarinyar nan har yau bai ko lek'o ganin lafiyar ta ba tir da halin mu," Zainabu na gefe sai hawaye take sharewa domin zuwa yanzu tasan meye rayuwa.


Motoci ne wajen guda goma suka yi parking a gidan su Maleek guards ne suka bud'ewa Uncle mota ya fito fuskar sa a had'e can wata motar aka bud'ewa Daddy mota ya fito fuskar sa fal farin ciki domin zai ga farin cikin sa kallon sa Uncle ya yi ya ja tsaki ya wuce fuuu zuwa part d'in Hajiya Asiya Daddy ma ya nufi part d'in Ummi.



Da sallama Daddy ya shiga falon Ummi dake saukowa stairs ta tsaya tana kallon sa domin bai sanar da ita da zuwan sa ba murmushi Daddy ya yi tare da bud'ewa Ummi hannu a hankali ta taka har inda yake ta fad'a jikin sa ya rungume ta a tare suka saki ajiyar zuciya domin sun dad'e rabon su da juna a hankali Ummi ta ce "Sannu da dawowa," d'ago fuskar ta ya yi ya kalle ta sannan ya ce "Yawwa Aysha Ina zuwa haka?" Murmushi ta yi ta ce "Hospital amma na fasa," ta fad'a tana jan hannun Daddy zuwa upstairs ruwan wanka ta had'a masa sannan ta sauko k'asa ta nufi kitchen ta fara yi masa simple food bata bar kitchen d'in ba sai da ta gama ta jera komai a daining sannan ta koma bedroom d'in ta wanka ta sake yi ta shirya cikin maroon less ta gaji da yin kyau sai k'amshi take yi ta juya ta kalli Daddy da ya tsaya kallon ta ta ce "Mu je kaci abinci," tare suka je daining d'in Ummi tayi sarving d'insa suka fara cin abincin.



Suna gamawa suka koma falo suka zauna Fauwaz ne ya fito daga part d'in sa ganin mahaifin nasu ya k'arasa falon ya ce "Ina kwana Daddy ka dawo lafiya?" Daddy ya ce "Lafiya lau Abbana Ina zuwa haka?" Kallon agogon sa ya yi ya ce "Daddy zani office ne," murmushi Daddy ya yi cikin son yaron nasa ya ce "To a dawo lafiya," cikin jin dad'in addu'ar Fauwaz ya ce "Ameen Daddy Ummi na tafi," itama ta yi masa addu'a sannan ya fita.



Kallon Ummi ya yi ya ce "Abbana kenan ya zama cikakken mutum saura aure," murmushi Ummi ta yi ta ce "Aikuwa dai amma wannan zuwa naka haka dafatan dai lafiya?" Ajiyar zuciya Daddy ya yi ya ce "To nima bana ce ba Aysha ina tsaka da aiki Yaya ya kirani yana ta yi mun fad'a ni gaba d'aya ban fahimci akan meye ba sannan ya ce lallai na shirya yau muzo gida shine dalili," gaban Ummi ne ya fad'i domin tasan dole akan Maleek ne bata so a karo na ba adadi Uncle ya rusawa yaron ta farin cikin sa.




"Aysha lafiya kuwa?" Girgiza Kai Ummi ta yi cikin murmushi ta ce "Bakomai muje ka huta nasan ka gaji," stairs suka nufa Daddy ya ce "Banga Rinaz ba tana Ina?" Ummi ta ce "Tana gidan Maryam," gyad'a kai Daddy ya yi.




Uncle kuwa yana shiga falon ya tsaya turus jin muryar Nasreen na cewa "Wallahi Umma kin gama dani ashe Dan ki kashe mun aure ne ki ka shirya min wannan k'aryar kika had'ani da yaron k'awar ki dake wata k'asar can tare da matar sa harma da yaran sa hud'u yana yaron shago mummuna da shi ashe biyan sa ki ka yi ya yaudare ni ni kika rabani da mijina Wanda ya fisa komai," shiru Hajiya Asiya ta yi ba magana Uncle ya k'arasa falon Nasreen na ganinsa ta fad'a jikin sa ta saki kuka ta ce "Daddy Umma bata sona ni kawai ka mayar dani gidan mijina ta biya wani ya yaudare ni nima Kuma na biya shi ya fad'amun gaskiya," shafa bayan ta Uncle ya yi ya ce "ki kwantar da hankalin ki nima abinda ya dawo dani kenan na mayar dake d'akin ki kinji?" Noding kanta ta yi tana jin wani farin ciki a ranta.




Sabeeha ce kwance akan gado a d'akin Doctor waya take yi ta ce "Amma sweetheart tahowa zaka yi yanzu meyasa hakan?" Daga can Maleek dake sauka stairs ya ce "My choice Ina tunanin akwai wata damuwar ce tun jiya Uncle ke kirana akan lallai yau nazo gida na sanar da shi akwai abinda nake yi a nan mai muhimmanci bazan samu damar zuwa ba shine yanzu Daddy ya kirani yana ta yi mun fad'a tare da bani umarnin yanzu na taho bansan me Uncle ya sanar da shi ba shiyasa nasa aka shirya mun flight d'ina yanzu zan taho amma ki kwantar da hankalin ki," Maleek ya fad'a tare da shiga mota.



Sabeeha kuwa tunda aka ambaci Uncle gaban ta ya fad'i dakewa kawai ta yi ta ce "Tom Allah ya kawo ka lafiya," ya amsa da "Ameen," sannan ya katse kiran.


Rinaz dake tsaye a bakin k'ofa ta kalli Sabeeha ta ce "Dear lafiya naga kamar kina cikin damuwa?" Kallon Rinaz ta yi ta ce "Bakomai kawai dai Daddy ya dawo tare da Uncle," shiru Rinaz ta yi domin tasan zuwan Uncle ba alkhairi bane gashi har da Daddy Kuma suna neman Ya Maleek kallon Sabeeha ta yi ta ce "Gaskiya Dear akwai wata matsalar amma ki kwantar da hankalin ki bari nazo naje gidan duk yadda ake ciki zan sanar miki," Sabeeha ta ce "Toh saina jiki," tafiya Rinaz ta yi.




Daddy kuwa yana gama Kiran Maleek ya kalli Ummi ya ce "Aysha duk yadda aka yi zuwan nan akan Maleek ne tunda kullum shike yawo mana matsala shine ma tunda gashi Yaya ya kirani akan na Kira shi lallai ya dawo Mai ya aikata?" Tab'e baki Ummi ta yi ta ce "Ba abinda ya aikata wanda yake ba daidai ba mu dai jira muji," Ummi na fad'in haka tabar d'akin.




Rinaz kuwa tana zuwa gida direct d'akin Ummi ta nufa a zaune ta samu Ummi ta k'arasa ta zauna ta ce "Ummi lafiya Uncle ya zo tare da Daddy a wannan ranar tunda ba ranar zuwan su bace kuma meyasa zasu ce Yaya yazo?" Numfashi Ummi ta sauke ta ce "Mamana kema kinsani bazai wuce akan Nasreen ba so suke su hargitsawa yarona farin cikin sa su burin su kullum su ganshi a damuwa," Ummi ta fad'a kamar zata yi kuka Rinaz ta ce "Ummi mu taya Yaya da addu'a kawai insha Allah abun su kansu zai koma," sun dad'e suna tattaunawa akan lamarin sannan Ummi ta yi alwala ta tayar da sallah Rinaz ma ta wuce d'akin ta ta yi wanka tayi alwala.


A sanyaye Sabeeha ta shiga d'akin su ta yi wanka Sabreen dake kwance ta kalle ta ta ce "Lafiya kuwa sister?"



"Eh lafiya," Sabeeha ta fad'a tare da nufar wadrobe ta d'auko kaya ta saka ta tayar da sallah kyale ta kawai Sabreen ta yi amma tasan tana da damuwa.


Ummi da Daddy da Rinaz na zaune a falo Uncle ya shiga falon Nasreen a bayan sa tare da Hajiya Asiya ko sallama basu yi ba suka samu waje suka zauna Ummi ta kalli uncle ta ce "Yaya Ina wuni anzo lafiya," banza Uncle ya yi da ita Ummi bata damu ba ta kalli Hajiya Asiya ta ce "Asiya Ina wuni?" Tsaki Hajiya Asiya ta ja Ummi kuwa ta ja bakin ta ta yi shiru Rinaz kuwa ganin da Daddy a wajen ta gaishe da Uncle amma ko kallon ta bai yi ba bare ya amsa shiru falon ya d'auka


Tsayuwar motoci suka ji a k'ofar part d'in Maleek ne ya yi sallama a falon Ummi Daddy ne da Rinaz kad'ai suka amsa Nasreen kuwa da kallo ta bi shi kamar ta had'iye shi saboda tsabar kyan da ta ga ya k'ara shi kuwa waje ya samu ya zauna sannan ya ce "Daddy Ina wuni ka dawo lafiya?" A ciki-ciki Daddy ya ce "Lafiya," saboda haushin Maleek yake ji saboda yana basa matsala shi da yayan sa.




Maleek kuwa kallon Ummi ya yi abun tausayi saboda bai ji dad'in yadda Daddy ya amsa masa gaisuwa ba ya ce "Ummina Ina wuni?" Ta ce "Lafiya lau son ka iso lafiya?" Ya ce "Lafiya lau Ummina," Rinaz ta gaishe shi ya amsa.




Saboda iyayi Nasreen ta ce "Ina wuni ya Maleek ka dawo lafiya?" Banza ya yi mata Uncle ya ce "Au baza ka amsa ba ana gaishe ka?" Shiru Maleek ya yi kamar bada shi ake magana ba sai ma cewa ya yi "Uncle Ina wuni," Uncle bai ko amsa ba ya fara balbala fad'a "To bari kaji daka amsa gaisuwar daughter da karka amsa dole ne ka mayar da ita wato saboda bamu isa da kai ba shine zamu aura ma yarinya ka sake ta har saki biyu saboda baka da tarbiyya?"




"Saki fa?" Daddy ya maimaita yana kallon Maleek Uncle ya ce "Eh saki har biyu saboda shi mahaukaci ne kuma sakin ma akan budurwa," shiru Maleek ya yi kansa a k'asa idanunsa sunyi jajir saboda b'acin rai ga zagi ana k'are masa.



Daddy shima ransa a b'ace ya ce "Saki Abdul-maleek ka saki 'yar uwar ka har saki biyu to akan wane dalili," kafin Maleek ya yi magana Uncle ya yi caraf ya ce "Ba shi da wani dalili wanda ya wuce a kan budurwar da yake so wannan ne dalili idan Kuma ni baka yadda dani ba nayi k'arya to ka cigaba da tambayar sa," Uncle ya fad'a duk Dan kar aba Maleek damar magana saboda yasan duk abinda Nasreen da mahaifiyar ta suka aikata.




Daddy kuwa jin abinda Uncle ya fad'ane yasa shi yin shiru Ummi ta ce "Son bai sake ta ba dalili ba..," d'aga mata hannu Uncle ya yi ya ce "To masu d'a kare shi Zaki yi kenan ai dama naji ance budurwar tasa 'yar gidan aminiyar ki ce dole ki so a saki Nasreen domin ya aure ta domin naji labarin a gaban ki aka yi sakin amma baki tsawatar masa ba kece ma ki kasa ya yi sakin," kallon Ummi Daddy ya yi girgiza masa Kai Ummi ta yi alamun ba bata da hannu domin jin Uncle na neman had'a mata sharri wajen mijin ta.




Sai lokacin Maleek ya d'aga Kai ya kalli Daddy domin baya son abinda zai had'a tsakanin Ummin sa da Daddy ya ce "Ba ruwan Ummina dan ra'ayin kaina na sake ta domin bana so na cigaba da zama da ita,"





"Ato Hamisu ka dai ji da bakin ka ko ya sake ta ne dan ya tozar ta mu," Fauwaz ne ya yi sallama a falon waje ya samu kusa da Maleek ya zauna baice komai ba.



Ucle ya ce "To baka isa ba tunda ba Kai ka haifemu ba yanzu sai ka mayar da ita Kuma babu saki tsakanin ka da ita Kuma wannan yarinyar dole ne ka rabu da ita," a razane Maleek ya kalli Uncle idanunsa kamar an watsa masa jajjagaggen attaruhu Uncle ya ce "Kalle ni dakyau yarinya tun yanzu tasa ka saki 'yar uwar ka ai bata arzik'i bace saboda haka ba kai ba ita Kuma yanzu yanzu ka mayar da daughter,"




Zumbur Fauwaz ya mik'e tsaye ya ce "Saboda me Yaya zai mayar da Nasreen bayan ba k'aunar sa take yi ba mahaukaciya ce ita dabba wacce taso ta ga bayan...," Kasa k'arasa maganar Fauwaz ya yi saboda marin da Daddy ya zabga masa ya ce "Ashe dama baka da hankali bansani ba idan ka Kuma magana anan saina b'ata maka rai Kuma lallai ka fito da mata kayi aure kabar gidan nan tunda baka da amfani a gidan kai kuma umarni ne wannan ba shawara ba yanzu ka mayar da matar ka," Daddy ya fad'a ransa a b'ace.



Hannu Maleek yasa ya rik'o na Fauwaz ya zaunar da shi zama Fauwaz ya yi dafe da kunci domin Daddy bai tab'a sa hannu ya daki d'ansa ba sai ranar Rinaz dake gefe sai hawaye take yi Ummi ma hawaye ta goge idanunta na kan Maleek domin ganin yanayin sa ya canja sosai jikin sa har rawa yake yi sannan ga gumi Yana yi duk da Ac dake falon shiru kawai ta yi.




"Kai muke jira," Daddy ya fad'a cikin had'e fuska yana kallon Maleek.




A hankali Maleek ya bud'e baki murya na rawa ya ce "Na mayar da ita," ya fad'a hawaye na zuba a idanunsa sannan ya ce "Daddy bazan yi saki ba tare da wani dalili ba amma na mayar da ita duk abinda ta yi mun Allah yana ganin ta amma Daddy Ina so na k'ara aure," kafin Daddy ya yi magana Uncle ya yi caraf ya ce "Baza ka k'ara auren ba saboda yarinyar bata da tarbiyya tun tana waje tasa ka saki matar ka ina ga ta shigo sannan saboda ba son daughter ka ke ba ita ke son ka idan ka auri waccan baza ka yiwa daughter adalci ba saboda haka baza ka yi auren ba," Daddy jin bayanin Uncle ya ce "Haka ne baza ka yi adalci ba saboda haka karna k'ara jin batun aure a bakin ka," zuwa yanzu kukan Ummi Mai sauti take yi domin tausayin yaron ta.




Maleek kuwa lokaci guda zuciyar sa ta yi wani irin bugawa da sauri ya mik'e tsaye ya yi hanyar fita sai dai kafin ya fita sai ji suka yi timm ya fad'i a wajen.




Da gudu Ummi Fauwaz Rinaz Daddy dama Nasreen suka yi wajen sa suna Kiran sunan sa amma ko motsawa bai yi ba.




A rikice Ummi ta ce "Fauwaz mu kai shi asibiti," da gudu Fauwaz ya fita ya Kira Salman suka kama Maleek zuwa mota Ummi da Daddy suka bisu a baya Rinaz ma zata bisu Daddy ya ce ta zauna a gida su kuma suka tafi.





Uncle kuwa tab'e baki ya yi ya fice shi da Hajiya Asiya.



Rinaz kuwa Kuka ta saki ta kwanta taita kuka



Sabeeha kuwa hankalin ta kasa kwanciya ya yi ko abinci kasa ci ta yi duk ta damu jiran Kiran Rinaz kawai take yi gashi har yanzu magrib shiru sannan Maleek ma shiru bai kirata ba kasa hak'uri ta yi ta Kira wayar Rinaz.





Rinaz dake kwance zazzab'i ya rufe ta ta d'auki wayar ta ce "Hello," Sabeeha ta ce "Please Dear maike faruwa?" Hawaye ne ya fito daga idanun Rinaz ta ce "ki hau WhatsApp yanzu,"




"Bani da WhatsApp lafiya ki ke kuwa?" Sabeeha ta tambaya a rikice jin muryar Rinaz wani iri Rinaz ta ce "Ki karb'i ta Sabreen zan tura miki sak'o yanzu," Sabeeha ta ce "Ok turamun," Sabeeha ta fad'a tare da kashe wayar ta nufi down stairs da sauri.




A zaune ta samu Mama da Abba da su Sameeha a falo ta kalli Sabreen ta ce "Sabreen dear bani wayar ki," mik'a mata Sabreen ta yi ta karb'a tare da komawa d'aki da kallo suka bita ganin ta kamar a d'an hargitse sai dai ba Wanda ya kawo komai a ransa.




Tana shiga d'aki ta kunna da ta kasancewar ba chart da mutane sosai Sabreen ke yi ba dan da nan message d'in Rinaz ya shigo jiki na rawa Sabeeha ta bud'e recording ne Rinaz ta tura mata wanda ta yi shi tun shigar su Uncle part d'in Ummi.




Zama ta yi gefen gado tana sauraro tass take jin abinda ke faruwa da maganar Uncle da ta Daddy duk abinda aka tattauna tana ji wasu hawaye ne masu zafi suka zubo mata jin abinda Uncle ke fad'i a kanta Wai bata da tarbiyya tausayin kanta da Maleek ne ya kamata kuka Mai sauti ta fara tana yinsa kamar ranta zai fita bata ji k'arar fad'uwar Maleek ba sai dai ji da ta yi hankali take su Ummi na Kiran sunan sa daga nan recording d'in ya k'are.





Hankali tashe ta tashi zaune gaban ta na fad'uwa jiki na rawa ta d'auki wayar ganin da voice a k'asa ta yi saurin bud'ewa ta kara a kunnen ta.





Muryar Rinaz na kuka ta ji tana cewa "Sabeeha Yaya yanke jiki ya yi ya fad'i tun lokacin har yanzu suna asibiti tare da su Ummi tun lokacin likitoci suke a kansa amma har yanzu bai farfad'o ba," Sabeeha na jin haka ta mik'e zumbur gaban ta na fad'uwa idanunta kuwa sai ambaliyar hawaye suke yi.



Kamar mahaukaciya ta fara magana a fili "Ya fad'i likitoci na kansa ko dai ya mutu ne Rinaz ta b'oye mun A'a bai mutu ba to meyasa bai tashi ba har yanzu?" Wata zuciyar ce ta bata amsa da kin manta yana da ciwon zuciya ko dai ya tashi ne.



Ai da gudu Sabeeha ta nufi down stairs yana kuka ko kallon inda su Mama suke bata yi ba ta yi hanyar fita ganin ta a hakane suma ya razana su da sauri Sameeha ta rik'o ta ta ce "sister Ina Zaki je lafiya kuwa?" Tana kuka ta ce "Cikani Sameeha ki cikani naje naga halin da yake ciki," wajen Mama da Abba suka yi ganin yadda Sabeeha ta koma kamar mai aljanu Sabreen ta ce "Dear lafiya?" Cikin kuka Sabeeha ta ce "Sister mutuwa zanyi kinsan me Rinaz ta fad'a mun kuwa?" Jin haka Sabreen ta nufi stairs domin d'auko wayar ta ta kira Rinaz ta ji meke faruwa.




Doctor ta rik'o hannun Sabeeha ta ce "Lafiya maiya faru Ina Zaki?" Abba ma ya ce "Aminiya ta maiya faru ne?" Kuka ta fashe da shi ta ce "Mama na shiga uku," tana fad'ar haka ta fad'a jikin Mama a sume.




A rikice suka fara Kiran sunanta Amma ko motsi bata yi ba.
[10/25, 8:43 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️




RUBUTAWA DAGA
HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ)





SADAUKARWA GA
MY DAUGHTER SABEEHA
BILKISU Z.YA'U (🅱️K)
AISHA MAGAJI DABO (AMA)





Page 17


Da sallama Kawu Bala ya shiga gidan sa ransa fess domin so yake idan ya je d'aurin auren yarinyar malam saleh ya bawa abinci mamaki.




Lantana ya k'walawa kira ta fito tana hura hanci tab'e baki Kawu ya yi ya ce "Je ki ki d'auko mun wannan kayan nawa babbar riga zani d'aurin aure," hanyar zaure Lantana ta nufa Kawu ya ce "Baki ji me nace bane kayana nace ki kawo mun fa," ba tare da ta waiga ba ta je har sharar da ta zuba kayan ta d'ebo su ta je ta zubar a gaban Kawu Bala.




Ba tare da ya kalli Kayan ba ya ce "Wai ni kuwa Lantana baki samu tab'in hankali ba taya Ina yi miki maganar kayana zaki d'ebo mun bola?" Kyalkyalewa da dariya Lantana ta yi ta ce "Kalli dai dakyau Bala kayan naka ne ai," saurin kallon gaban sa Kawu ya yi aikuwa idanunsa suka yi masa tozali da kayan sa da Lantana ta yiwa gutsi-gutsi.





Saurin mik'ewa Kawu ya yi ya nuna Lantana ya ce "Me nake gani haka?"



"Kayan ka mana ai nasan bayan su baka da komai shiyasa na huce haushin marin da kayi min a kansu Kuma wallahi kad'an ka gani daga aikin Lantana," jinjina kai Kawu ya yi zuciyar sa fal takaici da jin haushin abinda ta yi masa ya ce "Eh lallai ne naga aikin ki Lantana yanzu kuma zaki ga

Please Login or Register in order to submit comment