Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka yi jajir tsabar b'acin rai direct wajen Nasreen da tayi mutuwar tsaye ya yi ya d'aga hannu ya zabga wasu zafafan maruka guda biyu Wanda yasa ta ganin stars ya Kuma d'aga hannu da niyyar k'ara mata Ummi ta ce "Rabu da ita duk abinda suka yi dan kansu amma duk sanda ku ka cutar mun da yaro bazan tab'a yafe muku ba," Ummi ta fad'a tana share hawaye.



Hanyar fita Fauwaz ya yi rai b'ace domin yaso anbar sa ya sauyawa Nasreen kamanni bai dad'e da fita ba ya dawo tare da yo wurgi da Fati a tsakiyar falon harta buge da centre table fuska ba alamar rahama Fauwaz ya ce "Dan uban ki me aka baki kisawa yayana a abinci," Fati na kuka ta ce "Dan Allah kuyi hak'uri cewa suka yi idan na aikata hakan zasu bani kud'ad'e sannan idan ban aikata hakan ba zasu koreni nabar gidan nan,"





"Aikuwa gidan nan dole kibar sa tunda bana ubanki bane," Rinaz ta wurgawa Fati wani matsiyacin kallo ta ce "Zaki tashi kibar mana gida ko sai nasa an canjawa fuskar ki kamanni?" Da gudu Fati ta tashi.




Wata k'aramar k'walba ce ta fad'o daga gefen zanin Fati d'auka Fauwaz ya yi ya gani tabbas poison ne quick action ma kuwa.


Mik'ewa tsaye Maleek ya yi ya kalli Nasreen da tayi tsilli-tsilli da idanuwa ya ce "Bayan yadda da auren ki da nayi bayan bana son ki wanne laifin na aikata muku da ku ke son ganin nabar duniyar?" Shiru Nasreen ta yi wata uwar tsawa Maleek ya daka mata wacce tasa kowa na falon razana.




Nasreen kuwa wacce aka yi tsawar domin ta tuni ta kai k'asa ta ce "Dan Allah kayi hak'uri ganin irin soyayyar da kake yiwa Sabeeha ne wacce ni ko kwatar ta bansamu daga gare ka bane yasa nace gara kawai mu rasa gaba d'aya saboda ina son ka bazan juri ganin wata a matsayin matar ka ba Kuma Umma ce ta ce akwai wani yaron k'awar ta dake sona ya fika dukiya da kyau shiyasa amma dan Allah kayi hak'uri," kallon da ya watsa mata ne yasa ta shiga hankalin ta ya ce "Allah kuwa ya tsinewa so idan har haka yake ki sani na da ki ke gani na wuce duk inda ki ke tunani tabbas nasan akwai abinda aka zuba a cikin abincin tun lokacin da kika zo part d'ina har kina mun magana akan breakfast abinda bakya yi amma dan kina mahaukaciya kiyi tunanin ni bazan zargi akwai abinda kike k'ullawa ba tun shigowa ta falon nan naga tashin hankali a idanun Sabeeha baya ga haka kuma a d'azu nasan sanda ta je k'ofar part d'ina Wanda nasan haka kawai baza ta je ba idan har bani na Kira ta ba ki sani ni bazan cigaba da zama dake a matsayin matata ba ba dan ina tsoron karki sake tunanin cutar dani ba kin dad'e baki cutar dani ba na tsallake mutuwa daga wajen mak'iyana da dama wad'an da suka fi ki had'ari kallo d'aya na yiwa abincin nasan anyi poisoning d'in sa da wani k'aramun poison saboda haka na sake ki saki biyu domin bana tunanin sake kallon ki a matsayin matata," kuka Nasreen tasa ta ce "Dan Allah kayi hak'uri," wata uwar harara Maleek ya wurga mata ya ce "Wallahi karki kuskura idan kuwa ba haka ba saina yi miki dukan da saina sauyawa fuskar ki kamanni da iyayen ki ma baza su iya gane ki ba,"




Juyawa Ummi ta yi ta haura stairs tana hawaye.



Maleek kuwa hanyar fita ya yi Fauwaz ya kalli Nasreen ya ce "Ni dama na dad'e da tsanar ki ban tab'a kallon ki a matsayin 'yar uwa ta ba saboda ko isasshiyar tarbiyya baki da ita zaki tashi kibar mana falo ko saina yi mummunan duka sannan ki sanar da uwar taki cewar plan d'in ku bai yi aiki ba," Rinaz ta ce "Dalla can malama tashi ki fita me ki ke jira sannan itama uwar taki ki sanar da ita nan gaba ko ciwon Kai yayana ya sake yi sai kun gane naku wasa ne," da gudu Nasreen tabar falon domin ganin kallon da Fauwaz ke mata tsab zai iya yi mata mummunan dukan da ya ambata.
[10/25, 8:43 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️




RUBUTAWA DAGA
HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ)







SADAUKARWA GA
MY DAUGHTER SABEEHA
BILKISU Z.YA'U (🅱️K)
AISHA MAGAJI DABO (AMA)





Page 18


Haka Lantana da Zainabu suka tafi gida ko wannen su zuciyar sa ba dad'i ko da suka je gidan ko kallon arzik'i basu samu daga Kawu Bala ba.




Da gudu Sabeeha ta shiga d'akin su ta kalli Sabreen dake gaban mirrow ta ce "Haba Sabreen dear please kiyi sauri time na tafiya fa," tana rufe baki wayar ta ta fara ringing d'auka ta yi tare da karawa a kunne ta ce "Sorry Sweetheart gani nan tahowa fa," shiru ta yi tana sauraron abinda Maleek ke ce mata sannan ta ce "A'a ba sai kazo ba gani nan," daga haka ta katse Kiran sannan ta yi hanyar fita daga d'akin Sabreen na biye da ita sun sha kyau ba k'arya.







Suna sauka down stairs suka samu Mama zaune tana danna laptop Sabeeha ta ce "Mama mun tafi sai mun dawo," d'aga musu hannu ta yi ta ce "Ok bye take care," suka ce "Ok," daga haka suka fice a wajen mota suka samu Sameeha da Rinaz na jiran su sannan suka shige driver ya jasu zuwa gidan Ummi.




Suna shiga gidan suka samu motocin sojojin Maleek a jere a k'ofar part d'in Ummi suna fitowa daga mota daidai lokacin Ummi ke fitowa daga part d'in ta tana rik'e da hannun Maleek ya sha kyau har ya gaji cikin maroon trouser da white T-shirt sai shirt bottles one a sama maroon da maroon p-cap sai wani farin takalmi sai k'amshi yake zabgawa.





Tunda suka fito idanunsa yake akan Sabeeha haka itama kallon sa take yi kamar basu tab'a ganin juna ba ido d'aya ya kanne mata ita Kuma ta aika masa da murmushi Ummi ta ce "yammata na saukar yaushe?" Sameeha ta ce "Yanzu Ummi," har k'asa suka gaishe ta sannan suka gaida Maleek ya amsa cikin fara'a.



Kallon agogon hannunsa Maleek ya yi sannan ya kalli Ummi ya ce "Ummi lokaci na tafiya ni zan wuce," murmushi Ummi ta yi sannan ta manna masa kiss a goshin sa ta ce "Allah ya kiyaye ya bada sa'a son," rungume Ummi ya yi ya ce "Ameen sweet mom," kallon su su Sabeeha ke yi cikin birgewa har ya saki Ummi ya juya ya ce "Auu Ummina bari kiji wata magana," saitin kunnen ta ya rad'a mata "Ummi Ina dawowa fa za ayi maganar auren mu da Sabee na," murmushi Ummi ta yi shi Kuma kai tsaye ya nufi inda Sabeeha ke tsaye tana kallon sa a gaban ta ya tsaya ya ce "Muje ko my Queen," tare suka jera zuwa motar sa inda take zagaye da sojoji a k'ame kamar gumaka.





Tura baki Rinaz ta yi ta ce "To Yaya mu fa?" D'an waigawa ya yi ya ce "Ooh ku idan kunga dama ku kwana nan," dariya Sabeeha ke yi k'asa-k'asa tana yi musu gwalo Sabreen kuwa k'wafa ta yi tana cije baki.




Bud'e musu mota aka yi suka shiga su Rinaz ma suka shiga wata motar suka bi bayan tasu motar sai Airport.




Suna zuwa bayan an tsayar da motocin Maleek ya waiga ya kalle ta itama kallon sa take yi ya ce "Kin shirya?"




"Dame kenan?" Ta tambaye shi murmushi ya yi ya ce "Da auren mu mana da zarar na dawo," d'an juya idanu ta yi ta ce "Eh na shirya fa," ya ce "Good girl,"




"Yawwa ya Maleek wai yaushe zaka dawo," shiru ya yi kamar mai yin tunani sannan ya ce "Ba dad'ewa zan dawo six months kawai zanyi," zare ido Sabeeha ta yi ta ce "Six months fa ni dai gaskiya ban yadda ba," ta fad'a cike da shagwab'a.



'yar dariya ya yi ya ce "To naji yanzu kwana nawa ki ka bani?" Shiru ta yi tana tunani sannan ta ce "Sweetheart ka dai ga k'asar nan ba tamu bace karka je ka zaunar musu a gari su zo suna yi maka gori saboda haka karka dad'e kayi kwana kad'an ka dawo," dariya Maleek ya yi ya girgiza Kai ya ce "Ok na fahimta baby nima bazan so su yi mun gori ba ai one week ya yi ba?" Ta ce "Yawwa ya yi,"






Kallon agogon sa ya yi ya ce "Ni zan wuce sai munyi waya ki kulamun da kanki sosai," ta ce "Toh Allah ya kiyaye," ya ce "Ameen," bud'e murfin motar ya yi zai fita itama ta bud'e tana cewa "Bari na raka ka mana," ya yi saurin cewa "No baby nan wajen da mutane bana so a kallar mun ke," ya kalli driver ya ce "Adam ka mayar mun da ita gida," cikin girmamawa Adam ya ce "Ok sir," daga haka Maleek ya juya suka tafi.





Su Sabeeha ma direct gidan Doctor Maryam suka nufa bayan Adam ya yi parking motar ya fito ya bud'e mata motar tare da Sara mata tana fitowa ta ga su Rinaz su ma suna fitowa daga mota amma ko waccen su fuska a had'e dariya Sabeeha ke k'unshewa Sabreen da ta zo wucewa ta gaban ta ta ce "Zaki sani yaseen," daga haka suka wuce suka barta sai dariya take yi sai da ta gama dariyar sannan ta bisu a baya.





Da sallama ta shiga falon Mama ce ta amsa banda su Sabreen da kowacce ta d'auke kai murmushi Sabeeha ta yi Doctor Maryam ta ce "Ni kam me yake faruwa ne ku ke ta had'e fuska tunda ku ka shigo?" Tashi Sameeha ta yi ta nufi fridge ta zubo ruwa a cup ta juyo tana fad'in "Hmm Mama ai yau mu muka ga love," Sabreen ta d'ora da cewa "Dube ni fa Mama yadda na d'auki kwalliya duk domin zani Airport amma kinsan me Sabeeha sister da ya MG suka yi mana kuwa?" Girgiza Kai Mama ta yi tana murmushi.





Sabreen ta ce "Hmm Wai fa Mama muna tsaye muna jiran ya MG ya shiga mota mu tafi amma Sabeeha dear kad'ai ya yiwa magana suka tafi mota tare mu aka barmu," Sabreen ta girgiza kai irin na takaicin nan sannan ta ce "Har fa zanyi magana Rinaz habibty ta rigani cewa ya MG mu fa kawai sai cewa ya yi ai ya zata nan zamu kwana hmm Mama bakina k'in rufuwa ya yi,"




Rinaz ta ce "Ni Mama abinda yafi tafasani Wai Sabeeha sister ke yi mana dariya har da gwalo,"




"Wallahi kuwa habibty nima ta kunnani kuma Mama wai da muka je airport d'in kawai suka yi zaman su a mota ko me suke cewa oho Mama na tak'aice miki zance ni dai banga amfanin zuwan mu ba Dan ko a dawo lafiya bamu samu damar cewa Ya MG ba Mama Anya aka yi bikin Sabeeha sister zata ga 'yan k'afafuna a gidan ta kuwa?" Dariya Mama kawai ke yi Sabeeha dake bakin k'ofar falo kuwa sai da ta gama sauraron Sabreen sannan ta nufi cikin falon ta zauna ta ce "Mama kinsan me muke tattaunawa da shi kuwa?"


Girgiza Kai Mama ta yi Sabeeha ba kunya ta yi tsalle ta ce "Wallahi Mama cewa ya yi yana dawowa za a yi maganar auren mu," ihu falon ya d'auka Sabreen ta rungume Sabeeha ta ce "Wayyo dad'i kice mun kusa warwasawa ai dear da bikin ki akwai kodumo," Rinaz ta ce "Ya kamata mu fito da anko mai kyawun gaske," Sameeha ta ce "Wanne color ne zai fi kyau," Sabreen ta ce "Pich ya yi," Rinaz ta ce "A'a sea green yafi," Sameeha ta ce "No sai dai red zai fi ko light blue," tab'e baki Sabeeha ta yi ta ce da Sabreen "Kinga malama cikani Karki karyamun wani gurin," sakin ta Sabreen ta yi tana hararar ta.



Wucewa stairs Sabeeha ta yi tana dariya Mama ma dariya ta yi ta mik'e tana cewa "Ummi's girls Allah ya shirye ku," ta fad'a tare da shigewa bedroom d'in ta.



Maleek kuwa jirgin su yana landing motocin sojojin sa na nan suka zo d'aukar sa jiniya kad'ai ke tashi ana bud'e masa mota ya shige sojojin suka ja motocin da gudun gaske zuwa gidan
Maleek.



Suna zuwa aka bud'e masa mota ya fita kallon su ya yi sun kai su ashirin ya ce "Ku biyo ni ciki," yana fad'ar haka ya yi gaba suna binsa a baya had'adden falon suka shiga su suka tsaya a falon shi kuma ya haura stairs.




Wanka ya yi ya shirya sannan ya sauko down stairs suna nan a tsaye yadda ya barsu zama ya yi kan sofa sannan ya ce "Ku zauna," cikin bin umarnin sa suka zazzauna kallon Salman dake gefe a zaune ya yi sannan ya fara magana "Salman Ina son cikin sirri ba tare da sanin da motsin ku ba a Dubai ku je kuzo mun da Ahmad," Salman ya ce "Ok sir," daga haka suka fita domin cika umarnin ogan nasu.


Kallon agogon hannun sa ya yi sannan ya kalli daining an jera masa komai tashi ya yi ya nufi daining d'in ya zauna ya fara cin abincin kamar mai cin magani sai yamutsa fuska yake ture plate d'in ya yi tare da jan tsaki daddad'an abincin Sabeeha ya tuna domin ji ya yi wannan ba wani teste duk da da yana jin dad'in abincin wata zuciyar ta ce aika saba dana Sabeeha ne shiyasa kaji wannan ba dad'i.




D'aukar wayar sa ya yi ya Kira Sabeeha lokacin da yake Kira Sabeeha na wanka har Kiran ya katse sake Kira ya yi lokacin fitowar ta kenan k'arasawa inda wayar take ta yi ta d'aga ko ba a fad'a mata ba tasan Maleek ne domin ganin number d'in bata Nigeria bace a hankali ta ce "Hello sweetheart," ajiyar zuciya ya sauke sannan murya can k'asa ya ce "Baby kina lafiya?" Ta ce "lafiya but just missing you," murmushi ya yi ya ce "Same here," ya fad'a tare da mik'ewa daga kan kujerar daining d'in ya koma falon ya zauna ya ce "Nayi missing girkin ki naci abincin Juliet but ba dad'i," kamar tana gaban sa ta had'e fuska ta ce "Waye Juliet?"




Sai da ya tab'e baki sannan ya ce "Wata mai yi min abinci ce," hmm kawai Sabeeha tace domin wani kishi ne ya tokare mata k'irji.




Maleek ya gane hakan ya ce "Karki damu baby ni sam ban ma tab'a ganinta ba iya kacina kawai naci abincin ta," cikin shagwab'a ta ce "To ita wannan Surayya d'in fa ai ita kana ganin ta," d'an zare ido ya yi cikin mamakin a Ina tasan Surayya ya ce "Ina ki kasan batun Surayya?"




"Ni dai kawai ka fad'a mun," dariya ya yi ya ce "Baby rigima ai Surayya ba tasan nazo ba kuma ai ina da ke ba abinda zai had'a ni da ita ki kwantar da hankalin ki kinji?" Noding kanta ta yi kamar yana ganinta.




Su Salman ne suka shiga falon cikin wata iriyar shiga bak'ak'en riguna ne a jikin ta sai army green d'in wanduna sarawa Maleek suka yi jinjina musu kai kawai ya yi sannan ya ce da Sabeeha "Sabee na I will call you back later," ta ce "Ok bye," daga haka ya yi hanging up na wayar ya ajiye saman center table ya kalli Salman ya ce "Ina Ahmad?" Bud'e k'ofar falon Salman ya yi Ahmad ya shiga cikin shiga irin tasu Salman.



Sarawa Maleek Ahmad ya yi "Zauna," Maleek ya fad'a yana nuna masa sofa zama Ahmad ya yi ragowar Sojojin suka juya domin barin falon Maleek ya ce "No ku zauna ya yi bayani kuna ji," komawa suka yi suka zazzauna.




Kallon Ahmad ya yi ya ce "Meke tafiya?" Ahmad ya cire farin glass d'in idan sa ya ce "A bincinken da nayi akan safarar miyagun kwayoyi da makaman da za ayi a zaman su na k'arshe da suka yi suna shiri ne akan zasu shigar da kayan ne nan da 2 months sakamakon shugaban su da ya yi tafiya zuwa Egypt saboda haka suka bar maganar har sai ya dawo but sir gaskiya mutanen suna da had'ari na gaske akwai gang guda da suka shirya domin su shigar da kayan suna yin shiri sosai," jinjina kai Maleek ya yi sannan ya ce "Ba sunan ko da mutum d'aya daka samu a cikin su?"




"Gaskiya har yanzu ba wani bayani game da hakan amma zan cigaba da bincika hakan," cewar Ahmad kallon sojojin Maleek ya yi ya ce "kunji dai abinda ke tafiya saboda haka ku kasance cikin shiri," suka amsa da "Ok sir," tashi Maleek ya yi ya nufi stairs su kuma suka fita daga falon.




Tunda Maleek ya je Dubai baya samun zama domin shima bincike yake fita da kansa sai dai kullum da dare sai sunyi waya da Sabeeha.


B'angaren su Kawu Bala kuwa rayuwa ta yi musu zafi zuwa yanzu sun fara nadamar abinda suka aikata domin ruwan sha wuya yake yi musu duk sun fita daga hayyacin su musamman Zainabu da take da tsohon ciki idan ka ganta kamar almajira.




Kawu Bala ne ke tafiya yana tangad'i saboda yunwar da ta addabi cikin sa kayan jikin sa duk a yage kamar mahaukaci ya yi bak'i ya rame da ya gaji da tafiyar ne ya samu waje ya zauna a hankali hawaye ke malalowa a idanun sa duk Wanda ya gansa sai ya tausaya masa domin ko ka sanshi ba daga kallo d'aya zaka gane shi ba domin hatta kamannin sa sun sauya a hankali ya fara magana "Habu kana Ina Dan Allah ka dawo ka gafarceni tun kafin mutuwa ta riskeni na zalince ka Kai da matar ka harma da 'yan uku," kuka ya fashe da shi duk Wanda yazo wucewa sai ya kalli Kawu Bala cikin tausayawa.



Doctor Maryam ce zaune a falon ta ita da Abba tana taya shi lissafin wasu kud'ad'e domin yanzu Abba ya zama babban d'an kasuwa super market ne da shi manya manya wad'an da akasan da su kullum dukiya k'aruwa take yi Sameeha ce ta yi sallama a falon suka amsa Abba ya ce "K'araso mana aminiya ta," k'arasawa ta yi ta zauna akan carpet ta yi k'asa da kanta ta yi shiru.



Murmushi Doctor ta yi ta ce "Ya aka yi ne uhm?" A hankali ta ce "Mama dama uhm momyn Ya Umar ce tace tana so naje ta ganni shine nace bari na sanar muku zamu je tare da su Sabeeha dear," murmushi Doctor ta yi ta ce "To shikenan ba damuwa sai kun dawo," ta ce "To Mama," sannan ta tashi ta fita.




Kitchen ta nufa Sabeeha ta samu tana yin abincin rana tare da su Halima ta ce "Dear ku shirya da yamma zamu je gaida mommyn Ya Umar na sanarwa Mama," Sabeeha ta ce "Ok ba damuwa," Sallama suka ji a falo da gudu suka fita domin jin muryar Ummi.





Aikuwa ita ce rungume ta suka yi suna murnar ganin ta karb'ar jakar hannun ta Sameeha ta yi suka k'arasa cikin falon suna yi mata sannu da zuwa zama Ummi ta yi suka tsugunna har k'asa suka gaishe ta ta amsa cikin fara'a domin yaran kullum k'ara shiga ranta suke yi saboda ladabin su shiyasa take jin dad'i domin zasu zama surukan ta.




Sabreen ce ke saukowa daga stairs itama da gudu ta k'arasa ta ce "Laa Ummi sannu da zuwa," Ummi ta ce "Yawwa daughter," bayan ta gaishe ta ne ta ce "Bari na Kira Mama," Sabreen ta tafi domin Kiran doctor Sabeeha Kuma ta nufi fridge ta kawowa Ummi ruwa da lemo.


Doctor ce ta fito tare da Sabreen sai da Ummi da Doctor suka rungume juna sannan suka zauna Ummi ta ce "Kwana biyu naji yarana shiru shiyasa daga hospital na taho nan domin na gansu gaba d'aya gidan babu dad'i duk sun tafi sun barni," Mama ta yi dariya ta ce "Haka nima na gama fad'a musu jiya sai Sabeeha ta ce ai yau zasu je," Ummi ta ce "Wallahi kuwa da naji dad'i," Rinaz ce ke saukowa daga stairs da alama daga bacci take yi sai dai kallo d'aya zaka yi mata kasan ranta a b'ace yake.




Da kallo suka bita da gudu ta k'arasa falon ta fad'a jikin Ummi ta saki kuka hankali tashe 'yan uku suka fara tambayar ta lafiya Doctor ta ce "Daughter lafiya maiya faru?" Cikin kuka ta ce "Mama Daddy wai na shirya next week zan tafi India karatu Ummi ni wallahi ki fad'a masa bazan je ba," Doctor ta ce "To meye damuwar daughter ko karatun ne baki so?" Girgiza Kai ta yi ta ce "A'a Mama ni bana so na tafi nabar 'yan uku ne,"




Sameeha mai saurin ku ka har ta fara hawaye su Sabeeha ma sunji ba dad'i sai dai ba yadda suka iya Ummi ta shafa bayan ta ta ce "Shikenan ya isa mamana zanyi magana da shi," sai lokacin Rinaz ta ji sanyi a ranta sannan ta zauna anata fira banda ita domin gaba d'aya jikin ta ya yi sanyi haka ma 'yan uku.



Sai da suka ci abinci sannan Ummi ta tafi har mota suka raka Ummi sannan suka koma cikin gidan jikin su a sanyaye domin jin batun tafiyar Rinaz India.




Da yamma suka shirya cikin shigar su ta alfarma sun sha kyau ba k'arya musamman Sameeha da suka nutsu wajen shirya ta wani milk less mai flowers coffee color riga da skirt suka yi mata simple make up tasa mayafi coffee color haka ma jaka da takalmin k'afar ta sai zabga k'amshi suke yi sallama suka yiwa Doctor sannan suka fita inda umar kw jiran su a waje.


Suna fita suka shiga mota suka tafi tun daga nesa suke kallon gidan domin ya had'u ba k'arya horn ya yi gate man ya bud'e musu gate suka shiga parking ya yi sannan ya fita da kansa ya bud'ewa Sameeha mota ta fita su Sabeeha ma suka fita suka nufi cikin gidan Umar na gaba suna binsa a baya.




Da sallama suka shiga babban falon gidan da ya gaji da had'uwa Umar yana k'wala kiran "Mummy! Mummy!!" Saukowa stairs mommy ke yi ta ce "Ka fa kiyayeni Faruk irin wannan Kira haka," dariya Umar ya yi ya ce "Mummy gamu munzo," ya fad'a yana nuna mata su Sameeha.



Cikin fara'a Mummy ta ce "Sannun ku da zuwa," tun kafin su yi magana Umar ya ce "Yawwa," hararar sa Mummy ta yi ta ce "Da Kai nake," sannan ta kalli su Sabeeha ta ce Ku K'araso yarana.





Har k'asa suka gaisheta sannan suka zauna Umar na zaune a gefen Mummy bakin sa yak'i rufuwa Sameeha kuwa sarkin 'yan kunya kanta na k'asa ta kasa had'a ido da Mummy Mai aiki Mummy ta kira take aka cika musu gaba da abinci kala kala da lemuka.




Sannan mummy ta kalli Rinaz ta ce "Daughter ya Ummin ki fa?" A hankali ta ce "Tana lafiya tana gaida ki," ta ce "Masha Allah Ina amsawa," Lemo Rinaz ta zuzzuba musu a cups ta d'auka tana sha haka ma Sabreen.




"Amma dai 'yan uku ne ko?" Umar ya ce "Eh Ummi ga Sabeeha wacce Maleek zai aura wannan Sabreen ita kuma ta Fauwaz then ga sarauniya ta masoyiya ta matata da yardar Mai sama Sameeha," ya fad'a yana nuna Sameeha da ta yi k'asa da kai saboda duk ya bata kunya.



Mummy ta ce "Masha Allah kace duk yarana ne anan zo nan kinji d'iyata," a hankali Sameeha ta tashi ta k'arasa ta zauna k'asan carpet mummy ta ce "Sameeha," a hankali Sameeha ta d'aga kanta ta kalli maman Umar.




A hankali Mummy ta ce "Masha Allah,Allah ya yi muku albarka Allah ya kaimu lokacin bikin ku yarinyata da gani kina da nutsuwa gaskiya naji dad'i sosai na Kuma yi murnar kasancewar ki suruka a gareni domin kullum addu'ata Allah ya had'a faruk da mata ta gari sai gashi Allah ya amshi addu'a ta amma fa sai kinyi hak'uri da wannan fitinannen," k'asa da Kai Sameeha ta yi tana murmushi tura baki Umar ya yi ya ce "Kai mummy so ki ke ta rainani Kuma ai bata manta ba Ummi ta ce ta rik'e ni gam domin karta rasani," dariya kowa na falon ya yi har da Mummy.



Sun d'an jima a gidan sannan

Please Login or Register in order to submit comment