Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce "Nasreen ya ki ka ga aikin mijina abun Sona aina fad'a Miki ba shi kika d'auka wawiya kawai," Tana fad'ar haka suka haura stairs.



Kayan jikin ta ta cire sannan ta d'aura towel suka shiga toilet Fauwaz da kansa ya yi Mata wanka sannan ya shirya ta suka fita mota suka shiga zuwa part d'in Maleek da sallama suka shiga d'akin.



Suka samu Umar da Sameeha a d'akin Sameeha na ganin Sabreen ta mik'e da sauri ta nufi Sabreen tare da fad'in "Sabreen dear Mai ya faru dake haka?" Gaba d'aya mutanen wajen suka bi su da kallo har Maleek dake kwance sai da ya kalli wajen Ummi ta ce "Sabreen Kuma?"



Sameeha ta ce "Eh Ummi Sabreen dear ce,"
[10/25, 8:58 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️



RUBUTAWA DAGA
HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ)


SADAUKARWA GA
MY DAUGHTER SABEEHA
BILKISU Z.YA'U (🅱️K)
AISHA MAGAJI DABO (AMA)




Page 35


"Dear Mai ya faru dake haka?" Gaba d'aya kasa magana Sabreen ta yi Ummi ta ce "Sameeha wannan fa Sabeeha ce," kafin Sameeha ta yi magana Fauwaz ya ce "Eh fa may be dan ta gan mu tare ne ta yi tunanin ko My love ce," kallon Sabreen d'in Sameeha ta yi domin duk duniya babu mai fad'a mata 'yan uwan ta tasan Sabreen haka ma Sabeeha amma ita Ina Sabeeha dear take da ake Kiran Sabreen da sunan ta Kuma meye dalilin da yasa Sabreen take amsa sunan Sabeehan haka ta dinga tunane tunane a zuciyar ta.


"Kai dear su abun Kuma har da k'in gane ni ai Sabreen dear na gidan ta bata jin dad'i ne," Sabreen ta fad'a tare da kashewa Sameeha ido ba tare da kowa ya lura ba.




Sameeha ta ce "Sorry dear na bangane ki da wuri ba," Ummi ta yi dariya ta ce "Daughter wato har kin fara manta Sabeeha ko?"



"Ai kyale ta kawai Ummi nima zan rama," Sabreen ta fad'a tana dariya Maleek kuwa idanunsa ya mayar ya lumshe.



Umar kuwa bayan ya duba Maleek ya gane cewa desire tablets yasha amma abin tambayar shine waye ya ba shi bayan ga halin da yake ciki bai yi tunanin fad'awa ko da Ummi abinda ke faruwa ba ya dai yi masa allura tare da magani sannan ya kalli Sabreen ya ce "Sabeeha zan d'an ganki yanzu," ya fad'a tare da barin d'akin bin bayan sa Sabreen ta yi a falo ta same shi a zaune zama ta yi ta ce "Ya Umar gani,"


"Dama so nake na sanar miki cewar ki dinga kula da abincin da MG zai dinga ci saboda a bincike na naga desire tablets aka zuba masa a abinci ya kamata kisa idanu akan Nasreen sosai domin babu shakka ita tasa masa," jinjina Kai Sabreen ta yi domin wani tausayin Maleek ne ya rufe ta saboda bai yi dacen mata ba sannan mai son sa tsakani da Allah bata nan ba asan halin da take ciki ba.



Tashi Umar ya yi ya fita daga part d'in gaba d'aya domin shima mugun tausayin Maleek yake ji.




Komawa cikin d'akin ta yi babu Wanda ya tambaye ta yadda suka yi da Umar itama bata fad'a ba Sameeha ta tashi ta kalli Sabreen ta ce "Dear yunwa nake ji muje ki bani abinci," ta fad'a tana fita daga d'akin.



Sarai Sabreen tasan ba wata yunwa da Sameeha ke ji kawai so take yi su keb'e akan batun Sabeeha bin bayan ta Sabreen ta yi suka nufi d'ayan part d'in a falo suka ya da zango.


"Dear kiyi mun bayanin abinda ke faruwa Ina Sabeeha dear take?" Hawaye ne ya zubowa Sabreen ta ce "Bansani ba dear bansan inda Sabeehan mu take ba,"


"Kamar ya kenan Sabreen sister me ki ke nufi da ba a ga Sabeeha dear ba?" Sameeha ta fad'a itama tana hawaye.



Tas Sabreen ta kwashe abinda Sabeeha ta fad'a musu ita da Fauwaz ta sanarwa Sameeha.


Zuwa lokacin kuka sosai Sameeha take yi mai sauti cikin kukan take fad'in "Why why Sabreen sister meyasa ke da Sabreen sister zaku b'oye mun wannan d'in Sabreen akan meyasa zaku bar Sabeeha dear ta tafi bakwa tunanin samun matsala ga rayuwar ta ko cikin dake jikin ta kinsan munanan mafarkan da nake yi akan ta kuwa?" Sosai k'arar kukan Sabreen ya k'aru ta rungume Sameeha suka cigaba da kuka babu Mai rarrashin wani a cikin su.


Cikin kuka Sameeha ke fad'in "Sabreen dear yanzu shikenan ba wani labari akan Sabeeha dear ki duba fa halin da Ya MG ke ciki shin idan har wani Abu ya faru da Sabeeha wane hali ki ke tunanin zai shiga mu ma ya rayuwar mu zata kasance babu rabin jikin mu?" Ta Kuma sakin kuka.



Daidai lokacin wayar Sabreen ta fara ringing ganin number d'in Sabeeha yasa ta saurin d'agawa tasa a handsfree ta ce "Hello dear,"



Daga can Sabeeha dake rakub'e murya a wahalce ta ce "Dear kuka ki ke yi Mai ya faru dake?" Wani kukan ne ya Kuma kufcewa Sabreen saboda tausayin 'yar uwar ta domin ko da sau d'aya mutum yasan muryar Sabeeha ya ji ta a yanzu yasan tana cikin mawuyacin hali yasan a wahalce take amma bata damu da halin da take ciki ba sai ma tambayar Sabreen d'in da take yi meyasa take kuka Sameeha ma jin muryar Sabeeha na fita dakyar ne yasa ta sakin nata kukan.



"Dan Allah kar ku k'ara tayar mun da hankali meya faru ku ke yin kuka Sabreen dear maiyasa zaki fad'awa Sameeha?" Ta k'arasa maganar a wahalce.



"Meyasa Sabeeha dear akan me zaki tafi a lokacin da muke buk'atar ki a lokacin da Ya MG yafi buk'atar kulawar ki?" Hawaye ne suka zubowa Sabeeha ta ce "Ya My d'in yake yanzu?"



"Da sauk'i dear ki fad'a mana inda kike muzo mu ma please," Sabreen ta fad'a kamar tana gaban su ta fara girgiza kai domin ko mak'iyin ta baza ta so ya shiga irin halin da take ciki ta ce "A'a dear kawai ku cigaba da tayani da addu'a ita kad'ai nake buk'ata a halin da nake ciki yanzu," ta fad'a tari na sark'e ta a tare suka ce "Maiya faru dear Mai ya same ki?" Kafin ta yi magana suka ji k'arar mari "fass tass!!,"



"Ke!! Ke da uban waye kike magana Kuma dame kike maganar Zaki bani ko saina gana Miki azabar da tunda kike baki tab'a fuskantar ta ba?" Tsohuwar ta fad'a tare da buga kan Sabeeha a bango hakan yasa ta saki wata razananniyar k'ara ta fad'i sumammiya.



A tare Sabreen da Sameeha suka sa hannun su a baki domin hana kukan dake niyyar kufce musu fitowa suna kallon wayar Kiran ne ya katse.



Kuka sosai Sabreen da Sameeha ke yi kamar ransu zai fita Sameeha kuwa da gudu ta yi hanyar fita daga falon tana fita wajen part d'in taci karo da Umar jikin sa kawai ta fad'a tana sakin kuka a rud'e yake tambayar ta meya same ta amma ko magana ta kasa hakan ne yasa ya bud'e gaban mota ta shiga shima ya shiga ya ja motar suka bar gidan gaba d'aya.



Suna zuwa ya fara rarrashin ta tare da tambayar ta meyasa take kuka amma ta kasa fad'a masa haka ya hak'ura da jin dalilin kukan sai rarrashin ta da ya cigaba da yi har tayi shiru sai dai zazzzab'i ya rufe ta.




Sabreen ma a haka Fauwaz ya same ta tana kuka fuskar ta duk ta kumbura idanunta sunyi jajir da ya tambaye ta bata b'oye masa ba ta fad'a masa abinda ke faruwa shima hankalin sa ya tashi sosai amma haka ya dake ya rarrashi Sabreen amma itama zazzab'i ne ya rufe ta.


B'angaren Sabeeha kuwa tsohuwar ce ta d'ebo ruwa cikin bokiti ta juyewa Sabeeha a jikin ta a razane Sabeeha ta tashi zaune gaba d'aya ta fita hayyacin ta ko gane ta idan Wanda ya santa bazai iya ba kamar dai wata mahaukaciya.



"Dan kutmar ubanki zaki bani abinda ki ke magana da shi ko saina sauyawa fuskar ki kamanni?" Shiru Sabeeha ta yi domin bata jin zata iya bada wayar nan.



Duka sosai matar ta yiwa Sabeeha duk ta ji mata ciwo a jiki amma Sabeeha bata ba da wayar ba hakan yasa matar ta zaunar da Sabeeha kan kujera ta d'aure ta tamau d'auri na mugun ta dan har k'ara sai da Sabeeha ta saki sannan ta mannewa Sabeeha baki yadda baza ta iya magana ba sannan ta ce "Na ga ta bakin da zaki iya magana shegiya aljana," ita kuwa hawaye kawai take yi domin jin jikin ta take yi kamar wacce aka yiwa wanka da markad'add'en attaruhu.


A gaban ta matar ta d'auki waya tayi Kira kamar tana gaban ogan nasu ta tsugunna ta ce "Allah ya biya oga dama wannan yarinyar ce na kamata tana yin magana a d'aki to yanzu dai ga ta na d'add'aure ta ba irin dukan da banyi Mata ba amma tak'i bani wayar,"


"To abinda za ayi gobe dukan mu gang zamu zo nan domin kawai yarinyar nan kashe ta kawai zamu yi," tsohuwar ta ce "To,to ku iso lafiya," daga haka mutumin ya kashe kiran.



Tass Sabeeha ta ji abinda mutumin ke fad'a tashi matar ta yi ta fice daga d'akin.


Washe gari da safe Fauwaz ne ya shiga falon part d'in Maleek ya samu Ummi zaune ita da Doctor ya gaida Doctor sannan ya kalli Ummi hankalin sa a tashe ya ce "Ummi Daddy fa yazo gashi nan shigowa nan," kafin Ummi ta yi magana Daddy ya shiga falon cikin wata blue suit ya yi kyau har ya gaji kullum kamar k'ara masa kyau ake yi da gayu sai k'amshi yake yi mik'ewa kawai Ummi ta yi tana kallon sa har gaban ta ya k'arasa dakyar Ummi ta iya cewa "Sannu da dawowa,"


"Yawwa Aysha yadai naga kamar baki farin ciki da dawowa ta ba ko dai da wani Abu ne?" Ya fad'a yana shafa kwantaccen sajen sa Doctor ce ta gaishe shi ya amsa cikin fara'a.



Sabreen ce ta fito daga cikin d'akin da kallo Doctor ta bita har zata tambaye ta me take yi cikin bedroom d'in Maleek sai Kuma ta yi shiru ganin da mutane a wajen.




Har k'asa Sabreen ta gaida Daddy ya amsa cikin fara'a "Ina son fa?" Daddy ya tambaya yana kallon Ummi.



"Yana ciki baya da lafiya ne," Ummi ta fad'a domin yanzu baza ta iya b'oyewa Daddy cutar d'an nasu ba.


"Subhanallah me yake damun sa bari na ganshi," Daddy ya fad'a tare da nufar d'akin Kai tsaye su Ummi suka bi bayan sa.



D'akin ya shiga da Sallama ganin Maleek d'in kwance baya motsi sannan bai amsa sallamar sa ba sai kallon mahaifin nasa kawai da yake yi yasa Daddy k'arasawa da sauri ya ce "Innalillahi Son what wrong with you," gaba d'aya Daddy ya gama rikicewa yama rasa abin yi ya kalli Ummi ya girgiza Kai "Yanzu Aysha Son yana cikin wannan halin amma you can't even tell bayan muna waya dake and you Fauwaz you can't even give me a call Nagode muku sosai mu shirya mu tafi asibiti kawai," girgiza Kai Maleek ya fara daidai lokacin Salman ya shiga d'akin da sauri bai lura da Daddy ba Maleek ya kalla ya ce "Boss labari na samu yanzu daga Ahmad cewar an samu nasarar shigo da kayan nan Nigeria ta wata hanyar da mu bamu San da ita ba yanzu haka suna k'asar nan a wani waje da mu ba musan ina bane yanzu haka sojojin daka tura nayi musu waya cewar su dawo gida," jiniyar dawowar sojojin ce ta cika gidan gaba d'aya Maleek ya shiga tashin hankali jin abinda Salman ke fad'a duk ya ma rasa abinyi.


Nasreen ce tayi dariya ta kalli kalli Jamila ta ce "Da alama gidan nan yau akwai labari domin nasan zuwa yanzu burin Daddy na na gab da cika bari naje naga wainar da ake toyawa," ta fad'a tare da barin falon gaba d'aya direct part d'in Maleek ta same shi cike da mutane domin lokacin Sameeha da Umar ma sunje guri ta samu ta k'ace tana wani kad'a k'afa ita ga 'yar iska.


Kowa idanunsa na kan Maleek dake kwance ya lumshe idanu kowa tausaya masa yake yi Daddy kuwa guri ya samu ya zauna Sam ya rasa tunanin da zai yi kallon Maleek kawai yake yi idanunsa sunyi jajir yanzu d'ansa da ya fi k'auna ne a wannan halin amma ba Wanda ya fad'a mishi.



B'angaren Sabeeha kuwa ko rintsawa bata yi ba har safiya gashi igiyar da aka d'aure ta sai ci mata jiki take yi tana cikin wannan halin kawai ta jiyo wata murya a falon gidan kamar tasan muryar tana fad'in "Goggo! Goggo ta!!"



Motsin bud'e k'ofa Sabeeha ta ji aikuwa ana bud'e k'ofa tabi wacce ta bud'e k'ofar da idanu tabbas Rashida ce da suka yi aiki da ita a gidan Yallab'ai khamis.



Sam Rashida bata gane Sabeeha ba domin a tunanin ta ko mahaukaciya ce da sauri Rashida ta k'arasa ta ce "Na shiga uku Ashe har yanzu Goggo bata bar wannan halin nata ba wannan Kuma a Ina ta same ta?" K'ok'arin yin magana Sabeeha ke yi amma ba dama ganin hakan ne yasa Rashida d'ayewa Sabeeha abinda aka rufe mata baki da shi.



"Rashida ni ce Sabeeha sun kamoni ne dan Allah ki taimake ni," cike da mamaki Rashida ke kallon Sabeeha ba tare da ta yadda ba ta ce "Kina nufin Sabeeha 'yan uku dana sani?"


"Eh eh ni ce kar tazo please ki taimake ni," Sabeeha ta fad'a tana hawaye Rashida ta ce "Ni yanzu wanne taimako zanyi miki Sabeeha duka gidan nan a zagaye yake goggo ta kama mu har da ni zata had'a,"



"Rashida kwance mun hannuna," ba musu Rashida ta kwance ta duk a tsorace suke jiki na rawa Sabeeha ta d'auko wayar ta da Sabreen ta bata jiki na rawa ta fara rubuta number d'in Maleek ta fara Kira amma ba a d'aga ba a fili ta ce "Please My ka d'aga wayar," Kira na biyun ma ya katse ta sake Kira tana hawaye.




Maleek dake kwance bai kalli inda wayar take ba ma saboda tunda ya kwanta cuta yana ji ana Kiran sa baya iya d'agawa Kira ne ya sake shigowa wayar a karo na hud'u Salman dake kusa da wayar a tsaye ya tura wayar kusa da Maleek domin ya ga mai kira.


A hankali ya Kai duban sa kan screen d'in wayar kawai ya ga ansa "Sabee na," zare ido ya yi sannan ya Kai duban sa inda Sabreen da Sameeha ke zaune.



Abun mamaki kawai sai gani suka yi Maleek ya tashi zaune zumbur ya d'auki wayar cikin cool and sweet voice d'in sa ya ce "Sabee na," duka mutanen wajen sun shiga rud'ani da al'ajabin abinda ya faru na tashin Maleek.



Daga can Sabeeha cikin muryar Kuka ta ce "My kazo please,"


A rud'e ya ce "Kina Ina ne ina ki ka tafi?"


"Bansan ina bane amma mutanen da ka ke nema duk suna hanyar zuwa inda nake bari na bayar a fad'a ma address," Sabeeha ta fad'a tare da mik'awa Rashida wayar.



Kwatancen wajen ta yiwa Maleek jinjina Kai ya yi sannan ya mik'e tsaye ya kalli Fauwaz ya nuna masa Nasreen ya ce "Karka barta ta fita ko Ina," daga haka ya fice da sauri Salman ya bisa a baya.


Suna fita ya kalli sojojin sa ya ce "Ku shiga motar muje," bud'e masa motar aka yi ya shiga suka ja motar da gudun tsiya.
[10/25, 8:58 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️



RUBUTAWA DAGA
HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ)





SADAUKARWA GA
MY DAUGHTER SABEEHA
BILKISU Z.YA'U (🅱️K)
AISHA MAGAJI DABO (AMA)




Page 36


Gaba d'aya hankalin Maleek a matuk'ar tashe yake gaba d'aya wannan lamarin yasa shi a duhu.



Sabeeha kuwa suna gama waya da Maleek ta kashe wayar duka ta b'oye sannan ta kalli Rashida ta ce "Rashida ga matar nan ta taho ki k'ulle ni kar ta zo ta tarar kin kwance d'aurin," k'ulle Sabeehan ta yi.



Daidai lokacin tsohuwar ta shiga d'akin da kallo tabi Rashida ta ce "Ke kuma me ki ke yi a nan?"


Murmushi kad'an Rashida ta yi ta ce "Dama neman ki nake yi shiyasa na shigo nan amma gwaggo me wannan baiwar Allah tayi miki ki ka canja mata kamanni haka?" Rashida ta fad'a idanunta na kawo k'walla.



"Au dama kin Santa kenan ko me?" Saurin girgiza kai Rashida ta yi ta ce "Amma gwaggo wannan zalinci ne fa ku...," D'aga mata hannu tsohuwar ta yi ta ce "Rashida wallahi idan kina shiga harkar sana'a ta zanci kutmar ubanki,"



Jan baki Rashida ta yi tayi shiru k'arar motoci kawai suka fara ji a wajen gidan suna ta parking iya k'arar motocin ya isa ya sanar da kai cewar motocin masu yawa ne.



Jiki na rawa Tsohuwar ta k'arasa gaban window ta lek'a da sauri ta dawo ta kalli Rashida ta ce "Maza ki shige wani gurin ki b'oye domin idan har Oga ya ganki a nan sai dai wata ba ke ba ke ba ma ke kad'ai ba har ni zai had'a domin baison asan da wannan gidan," tana gama fad'ar hakan ta fara kwance Sabeeha da gaban ta banda fad'uwa ba abinda yake yi.


Tana gama kwance ta ta damk'i gashin kan Sabeeha da hakan yasa ta sakin k'ara saboda azabar da taji a kan nata amma tsohuwar bata damu ba haka ta ja Sabeeha har babban falon gidan.



Turus Sabeeha ta tsaya tana kallon Uncle dake zaune ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya a k'alla sun kai su ashirin a wajen magidan ta ne sai masu gadin su manya manya kallo d'aya zaka yi musu ta tsorata saboda tsabar girman su gasu bak'ak'e wuluk da su idanun Sabeeha ne ya Kai kan wani babban mutum Wanda ke zaune a tsakiyar mutanen tunanin Sabeeha ne ya katse lokacin da taji wannan matar ta yi wurgi da ita a tsakiyar falon har ta bugu da center table Wanda hakan yasa ta sake buge goshin ta take jini ya b'alle a goshin ta wata azaba ce ta ratsa jikin ta ga wani jiri da take ji tana daga kwancen Mai da idanunta ta yi ta rufe ruf.



"My son wannan yarinyar ce ta hana jika ta sakewa a gidan mijin ta?" Cikin girmamawa Uncle ya ce "Eh father," wata mahaukaciyar dariya oga ya yi sannan ya ce "Zan sa a keta mata mutuncin ta sannan na kashe ta kafin shi kansa MG ya biyo bayan ta domin jikata na riga nayi Mata miji," jinjina Kai Uncle ya yi.



Wani a cikin su ya ce "Boss amma ya batun kayan mu dake cikin gidan nan," kallon sa Oga ya yi ya ce "Wannan ba damuwa bane a yau idan mun kammala kashe wad'an nan biyun zamu fita dasu sannan mu aiwatar da aikin mu," daga fad'ar hakan Oga ya juya ya kalli tsohuwar dake tsaye ya ce "Ke Sailuba a yanzu ba sai anjima ba Ina so ki fito mun da jikarki da ke cikin gidan nan," take jikin wannan tsohuwa mai suna Sailuba ya fara rawa sanin duk Wanda ya Musa maganar Oga sunan sa gawa yasa ta juya jiki na rawa ta shiga d'akin da Rashida ta b'uya ta fito da ita har falon take wasu cikin wannan dabar suka fara lashe baki ciki kuwa har da Uncle domin shi ma lamba d'aya ne wajen neman mata.




Dariya Oga ya yi ya ce "Sailuba kin karya mun dokata ta cewar bana so wani yasan da wannan gidan domin sirrina ne amma ke ki ka karya mun ita sannan sarai kinsan hukuncin Wanda ya bijirewa umarnina saboda haka kema shekaru ashirin da muka d'auka kina aiki a k'ark'ashina hakan bazai sa na kyale ki ba tabbas kina yi mun aiki yadda nake so hakan ne ma yasa zan baki zab'i cikin biyu ki zab'i d'aya," tuni tsohuwa Sailuba ta zube a wajen domin tasan kashin ta ya bushe rok'o take akan ya yi hak'uri amma ko kulata ba Wanda ya yi Rashida kuwa kuka sosai take yi jin abinda Oga ya fad'a.




"Ki zab'a ko na sadu da jikar ki sannan na kashe ta ko Kuma ke na shek'e ki," a razane Tsohuwa Sailuba ta kalli Oga idanunta fal da nadamar aiki da Oga sannan ta kalli Rashida dake kuka tabbas tana son Rashida domin ita ta raini Rashida tun daga yaye sakamakon rasuwar iyayen Rashida amma Kuma ai itama tana son rayuwar ta sai kawai ta ce "Na bayar da Rashida," bud'e da ido Rashida ke kallon tsohuwar sai dai ta kasa fad'ar komai.



Wata dariyar basawa Oga ya yi sannan ya kalli inda Sabeeha ke kwance jini ya wanke mata fuska ya kalli wani k'ato cikin yaran sa ya ce "D'auke mun wannan abun daga nan kaje na baka ita kayi amfani da ita domin ni tayi mun k'azan ta da yawa duk da tafi waccan sura mai kyau," ya fad'a yana nuna Sabeeha dake kwance tana d'ibar azaba.



Maleek kuwa suna isowa wajen daga nesa suka hangi gidan dan haka ya kalli Salman a matuk'ar rud'e ya ce "Park here," take Salman ya yi parking da sauri Maleek ya bud'e mota ya fita tare da zaro bindigar sa daga aljihun motar sa har biyu ya soke su a jikin sa sannan ya yi gaba sojojin sa na binsa a baya.



Sabeeha kuwa jin abinda Oga ya fad'a ba k'aramun tayar mata da hankali ya yi ba saurin bud'e idanunta ta yi sai kawai ta ga wannan k'aton mutum a gaban ta k'ok'arin tashi take yi amma ta kasa hannu yasa ya rik'o na Sabeeha ya mik'ar da ita tsaye sannan ya fara janta zuwa wani d'aki tana tirjewa domin akan ta aikata abinda ake nufi da ita gara gawar ta.



Maleek kuwa zagaye gidan suka yi kamar karare haka suka dinga karya k'asusuwan yaran su Uncle murd'e musu wuya kawai zaratan sojojin ke yi ba tare da sun sha wahala ba.


Maleek kuwa idan ka ganshi zaka yi tunanin ba shi kad'ai ke aikin ba saboda kamar yana murd'e wuyan kaza haka ya dinga murd'e wuyan 'yan daban ko mai k'arfin su yana yin jifa da su kamar karare.


A zuciye ya nufi k'ofar falon yasa k'afa ya yi mata duka d'aya ta karye ta fad'i da k'arfin gaske Wanda hakan ya ja hankalin mutanen wajen inda yake.



Idanunsa ne ya sauka kan wannan k'aton mutumin dake jan Sabeeha tana tirjewa Sabeeha kuwa kallon inda Maleek yake ta yi cikin kuka ta ce "My ka taimake ni," a razane Maleek ke kallon ta cikin wani mugun yanayi domin shi Sam bai gane wannan sabeen sa bace saboda gaba d'aya kamanin ta sun sauya ga jini ya wanke mata fuska.



Marin da mutumin ya yiwa Sabeeha ne yasa ta fad'uwa a wajen a sume bata numfashi.



A wani mugun harzuk'e Maleek ya nufi wajen da Sabeeha take kwance kawai wani k'aton mutum ya sha gaban sa tare da kawowa Maleek wani mugun punch a fuska saura k'iris naushin ya sauka a fuskar Maleek ya yi saurin sa tafin hannunsa ya tare dukan sannan ya murd'e hannun ji kake "k'aras b'as k'as," ya karya hannun sannan duk girman mutumin ya d'aga shi sama ya yi jifa da shi a kan k'aton center table d'in dake falon take wata k'ara ta cika falon.




Daidai lokacin sojojin Maleek suka shiga falon tare da zagaye falon tare da saita ragowar mutanen falon da bindigogi take yaran suka zubar da makaman su da da sun saita Maleek da su suna jiran umarni su sakar masa harbi tako ina.

Maleek kuwa duk da ya ga mutumin baya motsi sai da yasa hannun sa ya jawo shi ya rik'e d'aya hannun nasa ya karya.



Kallo d'aya zaka yiwa Maleek kasan cewa ransa idan ya yi trillion ya b'aci saboda jan da idanunsa suka yi jijiyoyin damtsen sa da goshin sa sun tashi.



Kai tsaye wajen Sabeeha ya nufa da gudu ya tsugunna a gaban ta yana kallon ta wasu zafafan hawaye suka zubo masa janta jikin sa ya yi ya rungume a hankali ya fara Kiran sunanta "Sabeeha Sabee na please open your eyes Maleek is here your husband is with you please baby," wani irin jan numfashi Sabeeha ta yi Sam Maleek bai damu da daud'a da Kuma k'arnin jinin da Sabeeha ke yi ba ya rungume ta tsam a jikin sa.


Sannan ya kalli fuskar ta da tayi bak'ik'irin tsabar datti gashin kanta duk ya hargitse kamar na mahaukaciya ya ce "Open your eyes dear," a hankali Sabeeha ta bud'e idanunta da take jin sunyi mata mugun nauyi

Please Login or Register in order to submit comment