Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na Bala," ya fad'a yana d'aukar wani itace dake gefe.



Kamar wasa Lantana ta ji saukar itaccen a goshin ta wani uban ihu ta saki dan lokaci d'aya ta ji kanta ya yi mata mugun nauyi da gudu ta nufi d'aki sai dai kafin ta rufe har Kawu Bala ya shige yana shiga yasa sakata a k'ofar ya fara jibgar ta.




Ihu Lantana ke zabgawa tana cewa "Na tuba wallahi na tuba bazan k'araba shikenan zai kashe ni wayyo Allah hancina," haka lanatana tai ta ihu tana neman taimako amma Kawu bai dena nad'arta ba fad'i ya ke yi "Yau ai banga mai ceton ki ba a gidan nan dan Wallahi sai nayi Miki mummunan duka shegiya mai bak'in hali,"



Nasreen ce kwance saman gadon ta sai kuka take yi a fili ta ce "Wallahi Allah ya isa Umma da kika rabani da mijina," ta fad'a tana k'ara fashewa da wani sabon kukan sannan ta d'auki wayar ta ta kira wayar Uncle yana d'agawa ba tare da ta gaishe shi ba ta fashe da kuka har cewa ta shiga uku.




A rikice Uncle ya ce "Daughter lafiya maiya faru?" Cikin kuka ta ce "Daddy ya Maleek ya sakeni,"



"What!?" Daddy ya tambaya tare da cewa "Ki kwantar da hankalin ki ki dena kuka next week zan zo k'asar zanji dalilin da yasa hakan dan uban sa tunda shi ba a isa da shi ba yaro sai rashin tarbiyya to zamu dawo tare da uban nasa naji ko shine yasa shi ya sakar mun ke," ya fad'a tare da katse Kiran.



B'angaren Lantana kuwa sai da Kawu Bala ya gaji dan kansa sannan ya kyale ta ya fito daga d'akin ya fice yana masifa.




Lantana kuwa da dafa bango ta fito daga d'akin ga wani jiri dake d'ibar ta mayafin ta ta zara dake kan igiya ta fita tana tangad'i ko da ta fita bata ga Kawu Bala ba ta zari hanya ta tari mai machine ta fad'a masa inda zai Kai ta tana suna zuwa ta nuna masa wani gida mai koren fenti ya tsaya.





Sauka ta yi a hankali sannan ta kalli mai machine d'in irin d'an yau d'in nan ne Kuma daga ganinsa yana shaye shaye ga gashin nan an tsayar da shi a tsakiyar kai yayi buzu-buzu Lantana ta ce "D'ana yi hak'uri bari na shiga cikin gidan nan na karb'o maka kud'in ka," kallon banza ya yi Mata ya ce "Bangane d'anki ba Kinga malama bana son rainin hankali kawai ki ba mutum kud'in sa ya ware," a zuciyar ta Lantana ta ce "Na shiga uku ni Lantana gashi bani da ko sisi bari naje na samo masa kud'in sa idan ba haka ba tsaf na lura wannan zai d'ora wani dukan kan na Bala,"



"Kinga iya muna jira fa haba kinsan Baki da kud'i har da wani hawa babur," shiru Lantana ta yi ta juya tare da nufar k'ofar gidan.



Sadam ne ya fito daga gidan fuu kamar an jefo sa ajiyar zuciya Lantana ta sauke domin ba k'aramun jin dad'in ganin sa ta yi ba yana zuwa ko kallon Lantana bai yi ba ya kalli mai machine d'in ya ce "Kai yane zaka juya ne?" Mai acab'ar ya ce "Gaskiyar ka fad'a,"





Sadam ya ce "To muje," mai acab'a ya ce "To ke iya jira nake yi fa dan ba kwana nazo yi a nan ba ki bani kud'ina mana ke dan fa kece wallahi da tuni na bazar dake a nan," ya fad'a cikin wata k'atuwar murya Lantana ta kalli Sadam cikin bada umarni ta ce "Kai Sadam bawa wannan yaron kud'in sa,"





Wani kallon banza Sadam ya yi mata kamar ya ga kashi ya ce "A matsayin ki nawa a wajena zan baki kud'i kinga malama ki ba shi kud'in sa kawai ni wallahi mutane suna bani mamaki ace baka da kud'in kaza kace sai kayi haba," ya fad'a yana jan wani dogon tsaki.




Cikin gidan Lantana ta nufa tana fad'a a zuciyar ta shikenan komai ya lalace asirin da muka yiwa Sadam ma ya lalace.




Da sallama ta shiga gidan turus ta tsaya ganin Zainabu zaune ta rafka uban tagumi tana hawaye ga ciki duk ta rame ta k'anjale tayi bak'i har Lantana ta je ta d'auki naira hamsin d'in dake gabanta ta fice bata saniba sai da ta dawo sannan ta zauna gefen Zainabu tare da dafe goshin ta da ya yi wata uwar kumbura gashi har jini yake yi.





Dafata Lantana ta yi ta ce "Zainabu ta lafiya Mai ya faru?" Firgigit Zainabu ta yi tare da kallon Lantana tana ganin ita ce ta rushe da kuka ta fad'a jikin ta ta ce "Na shiga uku Lantana Dan Allah ki tafi dani gida Wallahi kashe ni zai yi idan ki ka barni a nan," a rud'e lantana ta ce "Zainabu baki da lafiya ne ki ka zama haka kamar mai ciwon k'anjamau?,"





"Lantana ni dai ki tafi dani kullum dukana yake yi baya bani isasshen abinci gashi baya barina fita Lantana asirin jikin sa ya barsa cewa yake yi uban meyasa aka aura masa ni ai shi bani ya ke so ba Sabeeha yake so sannan an kore shi daga wajen aikin su yanzu abincin da zamu ci ma gagarar mu yake yi," hawayen tausayin Zainabu ne ya fito daga idanun Lantana ta ce "Mu dai kam munga ta kanmu yanzu haka ma Bala ne ya yi min duka na taho nan gashi yunwa nake ji Zainabu bani abinci naci,"




Girgiza Kai Zainabu ta yi ta ce "Lantana kenan ai ko ruwan sha bamu da shi a gidan nan wannan hamsin d'in da ki ke gani ita ya bani na nemi abinda zanci na k'oshi," ta fad'a tana kallon gaban ta inda ta ajiye hamsin d'in ta ga wayam dube-dube ta fara yi ganin babu hamsin d'in inda ta ajiye ta.


Lantana ta ce "Ai hamsin d'in ita na d'auka na biya Mai acab'a da ita," Zainabu ta mik'e tana karkad'e daddaud'an zanin ta ta ce "Lantana tashi mu tafi," mik'ewa Lantana ta yi ta ce "Shawarata Zainabu ki zauna a gidan mijin ki domin idan ki ka bini sai kin dawo domin Bala yanzu banda talauci ba abinda yake fama da shi gara ma a nan kina samun hamsin d'in amma a can garin k'waki na ashirin babu me baki," kuka Zainabu ta fashe da shi tana rik'e wuyan hijabin ta da ya yage ta ce "Wallahi baki isa ba lantana saina biki," ta fad'a tana nufar k'ofar fita turus ta tsaya ganin Sadam a k'ofar take jikin ta ya fara rawa kamar ta ga mala'ikan mutuwa.




K'ok'arin bud'e baki take yi ta bashi hak'uri ya ce "Saurin me ki ke yi to ki tattara ki bi uwar ki," yana fad'in haka ya juya ya fice.






Kuyi hak'uri da wannan bani da caji ne amma insha Allahu zuwa dare zaku jini😂
[10/25, 8:43 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️




RUBUTAWA DAGA
HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ)





SADAUKARWA GA
MY DAUGHTER SABEEHA
BILKISU Z.YA'U (🅱️K)
AISHA MAGAJI DABO (AMA)




Page 19


A matuk'ar rud'e Sameeha ta nufi fridge ta d'auko ruwa suka yayyafa mata a hankali ta sauke ajiyar zuciya sai dai ko idanunta tak'i bud'ewa haka ta kwanta shiru a jikin Doctor.




Sabreen ce ta sauko daga stairs idanunta taf hawaye domin tana zuwa d'aukar wayar ta samu Sabeeha bata fita daga cikin app na WhatsApp ba da suke yi da Rinaz kunna voice d'in tayi ta ji duk abinda ke faruwa.





Tana zubar da hawaye ta k'arasa da gudu ganin su Mama duk a wajen Sabeeha domin ita bata san ma Sabeehan suma ta yi ba tana zuwa ta fad'a jikin Sabeeha ta fashe da kuka.



Abba kuwa gaba d'aya ya gama rud'ewa ya yi domin shi dai kam bai tab'a ganin yaran nasa cikin irin wannan yanayin ba shi yama rasa abin yi kallon Sameeha ya yi ya ga yadda ta had'a Kai da gwiwa itama tana nata kukan Doctor kuwa tagumi ta yi domin itama bata cikin nutsuwar ta ballantana su.



Abba ne ya ce "Haba aminaina me yake faruwa ne haka gaba d'aya hankalin mu yak'i kwanciya ku fad'a mana menene silar damuwar ku ne?" Dakyar Sabreen ta iya d'aga Kai ta kalli Doctor da idanunta da suka yi jajir ta mik'a mata wayar ta ba tare da tace komai ba.




Karb'a Doctor ta yi ta kalli screen d'in wayar ta yi Rinaz habibty ta ga ansa daga k'asa kuma sak'on k'arshe na Rinaz ta kalla ba tare da wani tunani ba ta kunna tare da k'ara volume yadda Abba zai ji suka fara sauraro shiru falon ya d'auka sai sheshshek'ar kukan Sabreen da Sameeha domin gaba d'aya ji ta yi kanta ya yi mata wani mugun nauyi sai hawaye kad'ai ke fita a idanunta.




A tare Abba da Doctor suka kalli Sabeeha cikin tausayawa sannan Doctor a hankali ta janye Sabeeha a jikin ta ta mik'e ta ja hannun Abba suka koma cikin falon suka zauna suna cigaba da sauraron abinda ke faruwa har k'arshe.




A hankali Sabeeha ta yunk'ura ta mik'e ta nufi inda doctor take a gaban ta ta tsugunna ta rik'o hannun ta cikin zubar da hawaye ta ce "Mamana dan Allah ki barni naje na ganshi please Mama,"




"Meyasa ki kayi sanadin raba shi da matar sa Rukayya?" A razane Sabeeha ta d'aga Kai ta kalli Doctor a hankali ta fara girgiza mata kai sai lokacin sabeeha ta tuna ashe fa duk abinda ya faru basu gayawa Mama ba.




Tsawa Doctor ta daka mata wacce tasa ta razana "Ba dake nake magana ba meye dalilin ki na shiga tsakanin miji da mata shin ina ruwan ki da matar sa kin kuwa san halin mahaifin ta gashi dai kinji da kunnuwan ki yadda yake zayyana wasu halaye wad'an da yarinyata bata da su amma yake danganta ki da su meyasa Sabeeha akan me zaki shiga lamarin nan?" Sabeeha gaba d'aya ta kasa magana tunanin ta Ina ma zata fara tayi.




Saneeha ce ta k'arasa gaban Doctor ganin yadda ta d'auki zafi zata yi magana Doctor ta yi Mata wata uwar tsawa da ta k'ara firgita 'yan uku ta ce "Matsa mun a nan Sadiya tun kafin raina ya b'aci a kanki bake nake tambaya ba,"



Sameeha wajen Abba ta nufa ta rik'e hannayen sa tana hawaye ta ce "Abba ka saurare ni wallahi Sabeeha dear bata da laifi," Sabeeha kuwa gaba d'aya tunanin ta baya tare da ita damuwar ta kawai shine tasan halin da Maleek ke ciki a hankali ta tashi domin ficewa daga falon.




Wani wawan mari Doctor ta zabga mata cikin d'aga muryar da basu tab'a ji ta yi ba ta ce "Kina hauka ne kin raba aure sannan ki ke k'ok'arin zuwa wajen?" Jin k'arar marin ne yasa Sabreen yin wajen Doctor da gudu ta rungume ta ta fashe da kuka ta ce "Please Mama ki dena dukan Sabeeha dear wallahi Mama a zuciyata nake jin zafin hakan,"




Sameeha kuwa cak ta tsaya da maganar da ta yi niyyar fad'a domin a tare ita da Sabeeha suka dafe kuncin su Abba kuwa rintse idanu kawai ya yi domin baya so yasa baki a maganar.



A hankali Sabeeha ta ja baya ta sulale a k'asa jikin kujera ta had'a kanta da gwiwa ta cigaba da kuka.



A hankali Abba ya mik'e ya nufi wajen Doctor da ta ture Sabreen daga jikin ta tana aika mata da harara jan Doctor jikin sa ya yi ya rungume a hankali ya ce "Maryam ki samu nutsuwa kinji wannan Sam ba hanyar da ta dace ki nunawa aminiyata kuskuren ta bane," a hankali Doctor ta yi ajiyar zuciya ta ce "Na nuna musu kuskuren su dai domin nasan duk tare suka yi komai ai ka fini sanin halin su," d'an girgiza Kai Abba ya yi ya ce "Please mana Doctor ki fahimce ni ni nasan ba haka kawai aminaina suka yi hakan ba ki duba aminiyata halin da take ciki tana cikin damuwar da tafi tamu lokacin da nake neman auren ki shin kin tuna wahalar da muka sha kafin mu mallaki juna?kina ganin wannan ce hanyar da ya kamata mu bi wajen taimako yarinyar mu?" A hankali Doctor ta girgiza kai.



Ajiyar zuciya Abba ya sauke sannan ya ja hannun Doctor suka zauna a kujera ya ce "Aminaina kuzo nan," Sabreen da Sameeha ce suka zauna gaban su Sabeeha kuwa har lokacin tana gefe ko d'aga Kai ta kasa damuwar ta d'aya Maleek.




Abba ya kalli su Sameeha ya ce "Aminaina k'arya ba halin ku bace ku fad'a mana asalin abinda ya faru," basu b'oye komai ba suka fad'awa su Abba duk abinda ya faru tun lokacin had'uwar Sabeeha da Nasreen a part d'in Ummi har zuwa sakin da Maleek ya yiwa Nasreen duka.



A d'an tsorace Doctor ta kalli su Sameeha jin abinda Nasreen taso aikatawa mijin ta Wanda take so to Ina ga 'yar ta da zata je a matsayin kishiya duk da tasan Aysha Mai kular mata da Sabeeha ne fiye da yadda ita kanta zata kula da ita amma abun da kamar wuya auren Sabeeha da Maleek ya yuwu duk da ta lura soyayyar sa tayi nisan da dakatuwar ta zai zama babban abu wanda bazai yuwu ba.




Kallon Sabeeha dake zaune tana kuka Doctor ta yi cikin tausaya mata tabbas yarinyar ta bata da laifi domin duk ta yi hakan ne domin ceton rai da Kuma kare 'yan uwan ta da take jin baza ta bari wani Abu ya same su ba a kansu tak'i yadda da soyayyar Maleek duk domin su zauna lafiya lallai Sabeeha ta musamman ce.



Muryar Abba ta ji ya ce "Kinji ko Maryam yarana basa abu kai tsaye dukan su Allah ya basu fahimta da Kuma sanin daidai suna son junan su fiye da tunanin ki su kan sadaukar da farin cikin su domin farin cikin d'ayan su tun suna yara haka suke Kuma Allah ya kare mana su domin rashin mahaifiyar su hakan bai sa sun rasa tarbiyya ba," a hankali hawaye ya zubo daga idanun Doctor take ta ji abinda ta yi bata kyauta ba a hankali ta tashi ta nufi inda Sabeeha ke zaune ta dafa ta da sauri Sabeeha ta d'aga kai ta kalli mahaifiyar tata da idanunta da saika rantse dama can a haka suke saboda jan da suka yi.


A hankali hawaye suka gangaro daga idanun Doctor ta bud'e baki ta ce "Yarinya ta kiyi hak'u...," Saurin rufe mata baki Sabeeha ta yi tana girgiza mata kai sannan ta fad'a jikin ta ta rungume ta Doctor ma rungume ta tayi a jikin ta cikin matuk'ar so 'yar tata ta ce "Allah ya yi muku albarka 'yan uku na," a tare suka amsa da "Ameen,"




A hankali Sabeeha ta d'aga Kai ta kalli Doctor ta ce "Mamana uhm," sai Kuma ta yi shiru ajiyar zuciya kad'an Doctor ta sauke sannan ta kalli agogon hannun ta ta ce "Sabeeha dare fa k'arfe tara fa," langab'ar da kai Sabeeha ta yi k'walla taf idanunta.



Tausayi taba mahaifiyar tasu ta ce "Shikenan kuje ku Kira driver a waya ya fito ya Kai ku and kar kuyi dare okay?" Noding Kai Sabeeha ta yi sannan ta yi saurin tashi mayafin kanta kawai ta gyara suka yi waje.



Driver suka Kira yazo suka bar gidan a hanya Rinaz ta Kira Fauwaz shi ya sanar da su cewar suna asibitin su Ummi direct can suka nufa ko gama daidai ta parking driver bai yi ba Sabeeha ta fice sai sauri take yi domin burin ta bai wuce ta ga halin da sahibin nata ke ciki ba su Sabreen na biye da ita.




Guards tare da sojojin da suka gani ne suka tabbatar musu da Maleek na wajen a k'ofar shiga Sabeeha ta kalli Salman da idanun sa suka yi jajir domin b'acin rai domin duk Fauwaz ya sanar da shi abinda ke faruwa jijiyoyin jikin sa duk sun fito rud'u_rud'u kallo d'aya zaka yi masa kasan a tunzure yake ran maza ya b'aci amma ganin halin da Sabeeha ke ciki ne yasa ya bita da idanu cikin kallon tausayi.




Tana shiga ta hangi Ummi Daddy da Kuma Fauwaz a k'ofar ICU ko wanne ya kasa zaune bare tsaye Nasreen kuwa Uncle takanas ya aika driver yazo ya d'auke ta zuwa gida.



Sabeeha na k'arasawa direct gurin Ummi ta wuce ta rungume ta a hankali ta saki kuka ta ce "Ummi wane hali ya Maleek ke ciki?" Shafa bayan ta Ummi ta yi cike da k'arfin hali ta d'ago ta daga jikin ta ta ce "Daughter ki kwantar da hankalin ki insha Allah Son zai samu sauk'i kinji?" Noding Kai kawai Sabeeha ta yi tana share hawaye da bayan hannun ta.




Sai da ta ji su Sabreen na yin gaisuwa ne sannan ta waiga ta ga suna gaida Daddy a hankali ta zame ta tsugunna k'asa ta gaida Daddy ya amsa musu ba yabo ba fallasa domin shima zuwa lokacin hankalin sa a tashe yake ganin har lokacin ko likita d'aya bai fito ba sai dai sai kallon Sabeeha yake yi ganin a yanayin da ta zo asibitin hakan ya lurar da shi damuwar da yarinyar ta yi da d'an sa sharewa kawai ya yi ya kalli tsadadden agogon hannun sa.




A hankali su Sabeeha suka zauna a kujerun dake wajen Fauwaz kuwa ko magana ya kasa banda dafe kansa da ya yi domin saran da kan ke yi masa.




Sabeeha kuwa ji take yi kamar ta tashi ta lek'a ta ga halin da yake ciki ta glass d'in dake k'ofar d'akin amma gaba d'aya ta kasa domin jin nauyin Daddy da take ji domin yana da matuk'ar kwarjini a hankali ta d'aga kai ta k'ara kallon Daddy shi baya kama da Maleek kama yake yi da Fauwaz da Kuma Rinaz fari ne shima sosai Sam bai da jikin tsufa sai kace bai haifi Maleek ba ma.




Kasa daurewa ta yi ta mik'e ta ta nufi jikin k'ofar ta lek'a gaban ta ne ya yi matuk'ar fad'uwa ba k'aramar razana ta yi ba ganin Maleek kwance kamar gawa ko Ina nasa baya motsi fuskar sa ta yi wani mugun haske oxgyen ne a hancin sa sai wasu wayoyi da aka sassa masa a k'irjin sa ga wasu allurori da taga sai yi masa ake yi manya manya amma har lokacin ko yatsan sa bai motsa ba da sauri ta ja baya hannun ta rufe a bakin ta domin kar kukan da ya taho mata ya kufce jin ta yi ta buge mutum ta baya ne yasa ta waigawa ta ga Sabreen ce rungume Sabreen d'in ta yi murya a sanyaye cikin kuka ta ce "Sabreen dear baya motsi wallahi baya motsi," Fauwaz ne ya tashi zuwa inda suke cikin k'arfin hali ya ce "Sabeeha kiyi hak'uri tun sanda muka kawo shi har yanzu a haka yake babu wani canji sannan har yanzu babu wani bayani,"




"Haba Abbana haka ya kamata ka sanar da su domin kwantar musu da hankali Kinga yarinya ki kwantar da hankalin ki Son zai samu lafiya," Daddy dake daga gefen su ya fad'a hannunsa duka sanye cikin aljihu shima a cikin damuwar yake amma wannan ai yarinya ce k'arama ba haka ya kamata ace anyi mata magana ba Daddy ke fad'i a zuciyar sa tare da d'an hararar Fauwaz da ya yi saurin yin k'asa da kai.




Sabeeha kuwa hararar da Daddy ya yi ne ya k'ara tuna Mata da Maleek Daddy ya ce "Ki kwantar da hankali okay?" A hankali Sabeeha ta yi noding kanta.




Sun Kai wajen mintuna talatin a wajen sannan likita guda d'aya ya fito a tare suka yi wajen sa tun kafin su yi magana ya kalli Daddy da Ummi ya ce "Yallab'ai Doctor muje office," girgiza kai Daddy ya yi ya ce "No Doctor why not ka fad'a mana a nan I hope there's no big problem?" Likita ya ce "I can said that cuz har yanzu ba wani bam_bamci a gaskiya Yallab'ai yana cikin wani hali domin zuciyar sa tana gab da ta yi buga Wanda hakan na nufin we can lose him cigaba d'aya aka samu daga d'azu zuwa yanzu dogon suma ya yi Wanda ciwon sa da ya tashi ne ya ja hakan a yanzu zuciyar sa ta fara bugawa amma yadda take beating is too fast gaskiya Yallab'ai Ina ga MG na buk'atar special care ba Ina nufin nan bamu da halin kulawa da shi ba Doctor u already known all about MG kamata ya yi a fitar da shi waje a can zai fi samun kulawar da ta dace da shi domin sun fimu k'wararrun likitoci a wannan fannin that's all,"

Daddy ya ce "Ok no problem ina ga gobe zamu je kawai amma bari na Kira friend d'ina a waya babban likita ne a wannan fannin domin shi yake duba son lokacin yana school a dubai," daga haka Daddy ya zaro wayar sa daga aljihu ya ciro wayar sa ya yi kira tana fara ringing aka d'aga daga can Doctor ya ce "The most architecture person in the world," dariya Daddy ya yi ya ce "Ka fara ba Doctor Kamal where are you now hope you are in Dubai now?" Daga can Doctor ya ce "i dey Egypt now any problem?"




"Yeah Son is in unconcious now we need you urgently," daga can Doctor yace "Subhanallah jikin son ne ya tashi ya ilahi naje duba governor na can ne sai next week zan dawo,"




Daddy ya ce "Ok no problem zamu jira dawowar ka sai mu shigo," Doctor Kamal ya ce "Ok worry don't I will do my possible best to scz the days," Daddy ya ce "Thank you friend,"



Dariya Doctor ya yi ya ce "The architecture amma ka bani wayar likitan dake kula da shi akwai shawarwarin da zan basu domin kula da shi kafin na dawo insha Allah," Daddy ya ce "Ok zan bashi wayar ka," daga haka suka yi sallama.




Doctor ya ce da Daddy "Yallab'ai wai dama Doctor Kamal is your friend amma ka kawo MG wajen mu?"




"Doctor yanzu ai ga amfanin kawo son gurin ku domin Kamal baya Dubai zuwa next week zai dawo zan baka wayar sa zaku yi magana," cikin jin dad'i doctor ya ce "to to ngd," bashi number d'in Daddy ya yi ya wuce office.



Bayan tafiyar Doctor Daddy ya kalli agogon sa sannan ya kalli Ummi ya nuna mata su Sabeeha da ido Ummi ta ce "Daughter dare ya yi ya kamata kuje gida zuwa gobe sai ku dawo ko?" Noding kanta Sabeeha ta yi sannan suka tashi.



Daddy ya ce "Abbana kuje a kai su gida," Sabreen ta ce "Daddy da driver muke," Daddy ya ce "Ok ku gaida Mamar ku," suka ce "To," suna fita Fauwaz ya bisu.



Sun bud'e mota zasu shiga Fauwaz ya k'arasa wajen kallon jikin su duk a sanyaye yake ya ce "Please ku kwantar da hankalin ku anything will be right," ba Wanda ya iya magana a cikin su domin yanayin da Maleek d'in ke ciki ya wuce a kwantar da hankali.




Sabreen ce tayi k'arfin halin yin murmushi ta ce "Ok bakomai sai da safe idan mun dawo," jinjina kai ya yi sannan ya juya ciki su kuma suka shiga mota suka tafi.



Fauwaz na komawa ya samu Ummi da Daddy sun zauna gefen Ummi ya zauna ya ce "Ummi naga kun zauna ke da Daddy dare fa ya fara kuje gida ku huta zan zauna a nan d'in," a tare suka kalle shi Daddy ya ce "No Ummin ku ta tafi ni zan zauna," Ummi ma girgiza kai tayi.



Fauwaz ya ce "Daddy Ummi kuyi hak'uri kuje gida Daddy yau fa ka dawo daga tafiya," shiru Daddy ya yi "Ummi please kuje tare," Fauwaz ya fad'a yana kallon su.



Mik'ewa Ummi ta yi ta ce "Shikenan gobe da safe zamu dawo," tashi Daddy ya yi suka tafi har wajen mota Fauwaz ya raka su sannan ya juya wajen da Salman ke tsaye ya k'arasa ya ce "Ya Salman mu k'arasa ciki," binsa Salman ya yi zuwa ciki.




Sabeeha kuwa suna zuwa gida suka samu Abba da Doctor a zaune a falo da alamu dawowar su suke jira sai dai da kallo su Doctor suka bisu ganin su duk jikin su a sanyaye guri suka samu suka zauna babu me yin magana a cikin su Abba ya ce "Ya jikin Abdul-maleek d'in?" Sameeha ce ta ce "To da sauk'i dai za a ce Abba amma har yanzu

Please Login or Register in order to submit comment