Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ya zubo mata.



Sameeha kuwa tuni ta fara kuka domin itama tunanin ta kenan tashi Sabreen ta yi zaune ta rungume Sameeha suka cigaba da kuka kamar wad'an da aka yiwa mutuwa su Dija sai aikin rarrashi suke yi.




Tashi Sabeeha ta yi tabar d'akin idanunta sunyi ja sosai da alama itama tana cikin yanayin da 'yan uwan ta ke ciki domin itama tana jin ba dad'i a zuciyar ta.



Falo ta koma ta zauna ta d'ora uban tagumi wayarta dake gefen ta ce ta fara ringing ganin me Kiran ne yasa ta yi picking ta kara a kunnen ta ba tare da ta ce komai ba.



"Baby," Maleek ya fad'a cikin in his sweet and cool voice d'in sa lumshe idanu Sabeeha ta yi sannan a hankali ta ce "Uhm," ya ce "Lafiya kuwa," kamar tana gaban sa ta girgiza kai alamun a'a.




Kamar yasan me tayi ya ce "Ok fad'amun meye damuwar kinji sweetheart na?" Ai kamar jira take yi ta saka masa kuka har da shesshek'a tashi zaune ya yi daga kwancen da yake tare da shafa tulin sumar kansa ya ce "Ya salam please baby kibar kukan nan ki fad'a mun mene damuwar,"





Bata bar kukan ba sai ma k'ara volume da tayi cikin kukan ta fara magana kukan da kana jinsa kasan na tsantsar shagwab'a ne ta ce "To ba shikenan ba zamu rabu da su Sameeha dear ba shikenan na dena ganin su kullum," ajiyar zuciya ya sauke sannan ya yi k'asa da murya cikin sigar rarrashi ya ce "is okay wannan ne ya saki kuka uhm?" Gyad'a kai ta yi a hankali ta ce "Eh,"



Murmushi ya yi a zuciyar sa yana fad'in na bani ni Abdul yanzu tun yau baby ta fara kuka lallai zanyi fama da rigimar ta a fili kuma ya ce "Shikenan yi shiru abinki kullum fa zan dinga kai ki wajen su ammafa idan kinyi shiru,"




Da sauri ta share hawayen fuskar ta ta ce "Nayi shiru,"


"Yawwa that's my baby to yi dariya naji," dariyar kuwa ta yi kamar ba ita ta gama kuka ba sannan suka d'ora da firar su.



Washe gari tun safe jiniya ke tashi a garin kasancewar rana ce ta musamman ga babban soja wato MG Abdul-maleek dan haka tun safe manyan sojoji ke dira a garin Kaduna daga wannan jiniya sai waccan jiniya Maleek kuwa tun safe suke zirga_zirgar tarbar bak'i shi da su Umar.





Daddy ma a nasa b'angaren haka take domin shima sai amsar bak'i yake su Ummi ma haka sai hidima suke yi.




Yan uku kuwa haka suka tashi sukuku Doctor na lure da su sai dai bata ce musu komai ba tana ta fama da bak'i.




K'arfe Sha d'aya da rabi aka d'aura auren Rukayya Abubakar da Abdul-maleek Hamza mai Dala sannan aka d'aura na Umar Aliyu da amaryar sa Sadiya Abubakar sannan na Muhammad Hamza mai dala da Hajara Abubakar akan sadaki dubu d'ari-d'ari.



D'aurin auren ya samu halattar manyan manyan sojoji ma'aikata da 'yan siyasa dama sauran jama'ar gari angwaye kuwa duk Wanda ka kalla a cikin su fuskar sa fal farin ciki gashi sunyi kyau sosai cikin ankon farar shaddar da suka yi.



Reception aka yi bayan d'aurin auren a wani babban hall sai hotuna ake yi duk inda ka kalla masu d'aukar hotona ne da marok'a Maleek kuwa tare da Salman suka tafi mayar da sojojin da suka zo zuwa masaukin su.



Daga can gida suka wuce direct part d'in sa Maleek ya nufa can ya samu su Umar sun baje a falo suna ganinsa Muhsin ya mik'e yana gyara babbar rigar jikin sa ya ce "Yawwa guy dama kai muke jira mu wuce zuwa part d'in sweet momma," Maleek baice komai ba sai juya da ya yi ya nufi k'ofa suka bi bayan sa zuwa part d'in Ummi.



Suna gama parking suka nufi cikin falon suna shiga aikuwa falon ya d'auki gud'a nan suka fara gaggaisa da mutane.




Can Maleek ya hango Ummi zaune kan kujera sai kallon sa take yi tana murmushi kallo d'aya zaka yi Mata kasan tana cikin tsantsar farin ciki tasha kwalliya sosai cikin light blue shadda hannu da wuyan ta sun sha adon gold ba k'aramun kyau tayi ba ba zaka tab'a cewa ta haifi d'a kamar Maleek ba hak'orin makkah na bakinta sai walwali yake yi.


Takawa Maleek ya yi har gabanta ya tsugunna akan lallausan carpet d'in dake falon ya ce "Ina wuni Ummina," murmushi ta yi ta shafa sumar kansa kasancewar ya cire hular dake kansa ya rik'e a hannu ta ce "Lafiya lau Son an d'aura aure Allah ya sanya alkhairi," kallon mutanen dake falon ya yi domin kunyar su ya ke yi kifa kansa ya yi a jikin Ummi sannan ya ce "Ameen Ummina," gud'a Aisa ta rangad'a mik'ewa Ummi ta yi ta d'ago shi daga tsugunnen da yake ta rungume shi ta ce "Allah ya yi maka albarka," ta fad'a tare da k'arbar hular shi dake hannun sa tasa masa ya ce "Ameen Sweet mother,"



"Son d'ina," Aisa ta fad'a waigawa wajen ta ya yi ya ce "Na'am sweet momma na," ya fad'a tare da rungume ta ta ce "Allah ya sanya alkhairi ya yi muku albarka ya kawo zuri'a d'ayyi ba," kafin ya amsa Umar ya rigashi.



"Yawwa ku haura sama Hajiya na nan," Ummi ta fad'a ya ce "To," saman ya haura yabar su Umar suna gaisawa da su Ummi.


Da sallama ya shiga d'akin Ummi Hajiya dake zaune tana cin farfesun kaji ta amsa sallamar fara ce tas bata tsufa ba sosai dagargar take idanunta sanye da farin glass k'arasawa wajen ta ya yi ya zauna gefen ta ya ce "Hajiyata Ina yini?" Harara ta aika masa tare da kawar da kai murmushi ya yi ya ce "Haba Hajiyata laifin kuma menayi?" Ya fad'a yana langab'ar da kai tare da d'ora kansa a kafad'ar ta.



"Kai ni d'agani kazo ka wani danne mutane kuma dana sani ma da banzo ba ko da yake ma ai ba dan kai nazo ba dan Fauwaz nazo saboda shi kad'ai ke ziyarta ta amma kai har manta kamannin ka nake," Maleek da ya k'ura mata ido yana kallon ta ya yi murmushi ya ce "To amma dai kinsan bana k'asar ko hadda wani kin manta kamata to yanzu ya akayi ki ka ganeni jikin ki Kuma ki rik'e abinki ni da zan hau wanda yafi naki," dariya su Umar dake zama suka yi Hajiya kuwa rik'e hab'a ta yi ta ce "Tabdijan ni kuwa yaushe ka zamo mara kunya haka a lallai gara da Hamza ya yi maka aure ko da yake ai dama kana da wata matar sannan ko ka turo ta ta gaishe ni ko?" Tsuru ya tsaya yana kallon Hajiya domin shi Sam ya manta yana da wata Nasreen banda yanzu da aka tuna masa tab'e baki ya yi ya yatsina fuska baice komai ba.



"To 'yan miskilancin ne zasu tashi kenan ai kai da wannan bansan wa ku ka yo ba," ta fad'a tana dungurewa Muhsin kai shi Kuma ya harare ta salati Hajiya ta saka ta ce "Yanzu Muhsin ni ka ke harara to ai dukana ya kamata kayi wannan matar ka ta shige su da Kai," shiru Muhsin ya yi mata dan shi yafi Maleek miskilanci.



Mik'ewa Maleek ya yi "Ni ku taso mu tafi gidan Mama domin so nake naje na ga baby na before anjima a kawomun abata,"



"Ah lallai Audul ka k'aro rashin mutunci Allah sarki yarinya zata yi hak'uri da fitina da uban miskilancin ka" dariya ya yi ya nufi k'ofa yana fad'in "Waye ya gayamiki ai ita ta daban ce baza ayi mata ba," ya fad'a tare da ficewa yabar Hajiya na masifar ita ya raina kenan.


Direct gidan Doctor suka nufa Hanfa da Ashraf suka samu a compound d'in gidan suna fira ita tayi musu jagora har cikin babban falon dasu Doctor ke ciki itama ta yi kyau sosai cikin shaddar ta irin ta Ummi domin anko suka yi Lantana tunda suka shiga take rangad'a gud'a su kuma suka zube suna kwasar gaisuwa.




Rinaz ta kalli su Sabeeha da suka yi mugun kyau cikin wani farin less Mai blue flowers sun sha kwalliya ta ce "Beb's da alama su Yaya sun iso ya kamata mu fita domin yin pictures," tashi suka yi suka nufi down stairs.



Tunda suka fara sauka kallo ya koma kansu kallon Sabeeha Maleek ke you babu ko k'iftawa wani farin ciki yake ji mara misaltuwa a zuciyar sa idan har ya tuna yanzu fa ta zama matar sa mallakin sa ga wani mugun kyau da tayi masa itama a nata b'angaren haka take domin ba k'aramun kyau ya yi mata ba kallon juna suke yi ba tare da d'ayan su ya d'auke idon sa ba.



Gud'ar da aka rangad'a ne yasa yin k'asa da kansa saboda tunawa da yayi a gidan surukai yake sannan ya mik'e ya fita bayan sun fitane su Sabeeha ma suka fita suka fara hotuna bayan sun gama har mota Sabeeha ta raka Maleek sannan ta koma cikin gida.




Da misalin k'arfe biyu Doctor ta shiga d'akin su 'yan uku suna tare da k'awayen su ta ce "Yammatan Abba ku shirya Aysha ta yi mun waya zata turo a d'auke ku saboda lokacin walima ya kusa," suka ce "To," sannan suka tashi suka sake yin wanka suka zauna aka fara yi musu kwalliya.



Doctor kuwa d'akin Abba ta shiga ta same shi yana amsa zama ta yi gefen sa jikin ta duk a sanyaye katse wayar Abba ya yi ya kalle ta ya ce "Doctor na lafiya kuwa?"



"Wallahi Abban su ji nake yi babu dad'in rabuwa da su," murmushi Abba yayi ya ce "Nima Ina cikin irin yanayin da ki ke ciki Doctor amma wannan ne gatan da zamu yi musu saboda haka muyi ta musu addu'a Allah ya zaunar da su a gidan mazajen su lafiya tare da yara na gari," Doctor ta ce "Ameen ya rabbi,"




Shiryawa 'yan uku suka yi cikin wani tsadadden material purple mai adon farin flowers a jiki sunsha kwalliya sosai alkyabba suka d'ora saman kayan sunyi kyau sosai motocin da Ummi ta turo musu suka shiga tare da 'yan uwan Doctor wad'an da zasu walimar da Kuma k'awayen su da suka sha kyau cikin atamfar anko.



Suna zuwa su Ummi suka tare su cikin farin ciki a cikin gidan daga wani b'angare za ayi walimar gurin ya tsaru sosai ansa runfuna da kujeru har wajen zaman su su Ummi suka yi musu rakiya yayinda kansu ke k'asa suna tafiya a hankali sai tashin k'amshi suke yi.



Ba b'ata lokaci babban malamin da aka gayyato ya fara da walima da nasihohi ga amare dama sauran jama'ar da suka halacci wajen jikin amare duk ya yi sanyi domin wa'azi da Kuma nasihar malam ta shige su sosai.




K'arfe biyar aka tashi daga Walimar Ummi tasa aka mayar da 'yan uku gida domin fara shirin Kai kowaccen su d'akin ta.



Maleek kuwa hotel d'in da Abokan aikin sa suke ya tafi sukai ta fira da dariya da Kuma wasu tsare-tsaren wani soja ne ya shiga d'akin da sauri ya mik'awa Maleek waya ya ce a cewar Ahmad daga Dubai yana kira.





KUYI HAK'URI DA WANNAN BA YAWA.
[10/25, 8:50 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️





RUBUTAWA DAGA
HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ)



SADAUKARWA GA
MY DAUGHTER SABEEHA
BILKISU Z.YA'U (🅱️K)
AISHA MAGAJI DABO (AMA)






Page 26



Shiru d'akin ya d'auka mik'a hannu Maleek ya yi ya karb'i wayar yana tunanin lafiya kuwa da yasa Ahmad bai kira tasa wayar ba kara wayar ya yi a kunnensa.



"Barka da wannan lokacin sir," gyad'a kai kawai Maleek ya yi Ahmad ya cigaba "Sir gaskiya akwai matsala,"



"Meye matsalar yanzu?" Maleek ya fad'a yana gyara zaman sa.



"Gaskiya a yanzu akwai wata matsala mutanen yanzu suna yawan yin meeting sannan shi ogan su yana gab da dawowa suna yawan yin waya da shi a meeting d'in sannan duk maganar da suke yi cikin wani yare suke yi da bansan wanne yare bane domin yaren iya nasu ne sannan abinda nake tunani suna shirye shirye ne akan kayan da zasu shigo da su," Maleek da ya gama sauraron Ahmad ya ce "Ahmad ka cigaba dasa ido a lamuran su sannan abu d'aya dana fuskanta shine akwai Wanda ke kai musu information akan plan d'in mu hakan ne yasa suka canja yare wannan kuma zansa a kula da lamarin,"



"Ok sir an d'aura aure Allah yasa alkhairi ya bada zaman lafiya,"



"Ameen Ahmad," daga haka ya katse kiran zuciyar sa fal tunani ajiye wayar ya yi sannan ya mik'e ya nufi k'ofar fita daga d'akin ba tare da ya yiwa kowa magana ba.




'yan uku kuwa tunda Ummi ta shiga d'akin su tace su tashi su yi wanka su shirya dare nayi suka fara kuka dakyar suka yi wankan sai dai tunda suka yi wankan ko mai basu shafa ba suka zauna suna ta aikin kuka su Rinaz na rarrashin su daga baya itama Rinaz ta fara nata kukan Dija kuwa tagumi ta zabga ta kalle su ta ce "Yanzu Beb's meye amfanin kukan da ku ke yi look at you beb ke da zaki rarrashe su kema kin fara stop it please aure fa ba mutuwa bane sannan kuna gari d'aya fa zaku dinga ganin juna,"



"Beb's munzo duniya tare komai tare muke yi bama tab'a rabuwa da juna kullum a tare muke kwana muna jin motsin juna hatta kayan mu iri d'aya muke sawa komai namu iri d'aya ne muyi kuka tare mu yi dariya tare duk inda zamu tare duk wannan shak'uwar ace rana d'aya zamu rabu rabu da juna ya zaki ganmu?" Sabreen ta fad'a tana k'ara sakin wani kukan Wanda tasa su Sabeeha k'ara nasu volume d'in.




Wata k'awar Doctor ce ta shiga d'akin ta same su suna ta kukan sai da suka bata tausayi zama ta yi tana rarrashin su amma basu yi shiru ba dakyar dai ta samu suka shafa mai ba batun kwalliya wani tsadadden less suka sa pich color takalman su da jakar su da mayafi duk dark pink sai k'amshi suke yi sunyi kyau sosai sai dai idanunsu sunyi ja Kuma har lokacin basu dena kukan ba jansu ta yi zuwa down stairs.



Falon Abba ta kaisu inda Abba da Doctor ke zaune tsugunnawa suka yi a k'asan carpet d'in kansu a k'asa suna zubar da hawaye.




Gyara zama Abba ya yi cikin yin k'asa da muryar sa ya ce "Aminaina," basu iya amsawa ba sai gyad'a kai da suka yi shima Abba ji yake ba dad'i haka ya dinga yi musu nasiha mai ratsa jiki yana Kuma jaddada musu su yiwa mazajen su biyayya ba abinda kake ji sai shesshek'ar kukan su.



Doctor ta ce "Aure ibada ne tabbas nasan baku da matsala sannan na haifi yara masu biyayya da tsafta da girmama na gaba da su Rukayya Sadiya Hajara ku girmama mazajen ku ku zauna da su lafiya ku nuna musu ku masu tarbiyya ne ku nuna musu kunsan ya kamata dukda zaman tare zomu zauna ne zo mu sab'a amma Dan Allah ku kula sannan ku yi ta addu'a ku rik'e sirrin mazajen ku Allah ya baku zaman lafiya tare da zuri'a d'ayyi ba," basu iya amsawa ba sai kukan da suke yi mai sauti.



"Rukayya kina da abokiyar zama saboda haka Yaya ce a gare ki girmamata dan Allah karki zamo silar fitina a gidan auren ki duk abinda zai faru kiyi hak'uri ku zauna lafiya Allah ya yi muku albarka," suna kukan suka amsa da "Ameen Abba,"



"Ku shigo mana," Ummi ta fad'a tare da ajiye wayar k'arasawa wajen ta 'yan uku suka yi suka rungume ta suna kuma sakin wani kukan itama dauriya kawai take yi saboda yadda suke kukan har zuciyar ta take jinsa daga nan suka tafi gurin Abba shima suka rungume shi suna kuka shafa bayan su Abba ke yi yana rarrashin su.




Wasu daga cikin k'awayen Doctor ne da danginta da lantana suka shigo domin motocin d'aukar amare sun iso 'yan uku kuwa k'ank'ame Abba suka yi suka k'i sakinsa sai kuka suke yi.





Doctor ta ce "Kuyi hak'uri ku tafi ana jiran ku zaku fara zuwa gidan Aysha ne," har lokacin basu saki Abba ba domin shak'uwar da suka yi da shi basu yi da Doctor ba.




Tsawar da Doctor ta yi musu ne yasa suka saki Abba suna kuka Jan hannunsu aka yi aka tafi dasu suna kukan rabuwa suna fita daga d'akin Doctor ta fad'a jikin Abba tana kuka ajiyar zuciya Abba ya sauke ya ce "Maryama kiyi hak'uri kinji dole za aji ba dad'i kukan ya isa haka please," shiru Doctor tayi jikin Abba tana sauke ajiyar zuciya.




'Yan uku kam har a mota basu bar kuka ba har suka je gidan Ummi bayan motocin da suka kawo su wajen guda ashirin sunyi parking sannan aka fara shiga falon Ummi.




Tarba ta mutunci su Ummi suka yi musu Lantana da Zainabu kuwa sakin idanu suka yi suna kallon aljannar duniya wato duk had'uwar gidan Doctor ga Wanda yafi nata nesa ba kusa ba su ai irin wannan gidajen a televisions suke ganinsa Zainabu kuwa kallon Ummi take yi a zuciyar ta tace ashe ba iya gidan ne na k'asar waje ba su kansu indiyawa ne da haka suka zazzauna Ummi kuwa gata ga 'yan ukun ta a zaune sai farin ciki take yi.



An d'an tab'a fira sannan Ummi taja 'yan uku taja hannun 'yan uku zuwa cikin d'akin ta wani ruwan wanka tayi musu ruwan yasha wasu kayan k'amshi ta ce su yi wanka kowacce ta yi wankan duk sunyi wani irin mai Ummi ta basu ta ce su shafa kamar turare tsabar k'amshin sa sai da suka gama Ummi ta d'auko wani yadi shi ba code net ba ba less ba mai k'ananun zane kamar material kowacce best color d'in ta Ummi tasa aka d'in ka mata dogayen riguna ne fitet gownt tare da mayafi bayan sunsa ta feshe su da wani turaruka masu dad'in k'amshi.



Sannan Ummi ta fara yi musu tata nasihar sannan ta k'ara da cewa karsu d'auke ta a matsayin suruka su d'auke ta a matsayin uwa karsu dinga b'oye mata wata damuwar komai k'ank'antar ta Hajiya ce ta shiga d'akin tana fad'in "Ina kishiyoyin nawa?" Ummi ta yi dariya ta ce "Gasu nan," zama ta yi gefen Ummi.




A hankali suka gaishe ta ta ce "Lafiya k'alau ya kamata dai naga fuskar wad'an da zasu k'wace mun mazaje," a hankali suka yaye fuskar su Hajiya kuwa sakin baki ta yi tana kallon su domin ganin tsananin kamar su ta ce "Masha Allah Ina ta Audul ne?" Ummi na dariya na nuna mata Sabeeha "A lallai Masha Allah amma fa sai kinyi hak'uri da wannan yaron dan naga kansa rawa yake yi," k'asa Sabeeha ta yi da kanta bata ce komai ba.




Waya Ummi ta d'auka ta yi Kira ta ce "Haba me kuke jira ne dare fa ya fara," daga can Maleek dake d'aura agogo a hannun sa ya ce "Ummi gamu nan," daga haka ya katse kiran.



Turare ya fesa a jikin sa harya gaji da yin kyau kallon Umar ya yi dake gefe sai murmushi yake yi shi kad'ai ya ce "Umar muje nifa kwana biyun nan na lura cutar murmushi Kai kad'ai ba tare da wani dalili ba ta kamata sai kace wani k'wark'war," dariya Umar ya yi ya ce "MG banson iskanci fa duk wanda yake da Mata kamar Sameeha ai bashi ba fushi ko k'unci shiyasa kake ganina always in smile," ya fad'a yana k'ara washe baki kallon sama da k'asa Maleek ya yi masa ya girgiza Kai ya ce "Na tausayama," daga haka ya fice.




Mota suka hau zuwa part d'in Ummi cikin falon suka shiga da Sallama daidai lokacin Fauwaz ya fito daga part d'insa ya sha kyau ba k'arya take falon ya rud'e da gud'ar ganin angwayen gaggaisawa suka yi da mutanen wajen sannan suka wuce zuwa stairs.



Da sallama suka shiga d'akin Ummi amsawa ta yi sannan suka k'arasa cikin d'akin idanunsu nakan 'yan uku dake zaune kansu a k'asa d'ayan gefen Ummi Maleek ya zauna idanunsa na kan Sabeeha da tasha kyau cikin doguwar riga maroon color wacce tayi mata kyau jin kamar ana kallon ta ta d'aga kanta Aikuwa suka had'a ido shima shaddar jikin sa maroon ce Kuma suma Ummi ce ta yi musu.




Tana kallon sa hawaye ne suka ciko idanunta ta yi saurin yin k'asa da idanunta wata k'aramar ajiyar zuciya ya sauke sannan ya mik'e ya k'arasa gabanta ya tsugunna a gabanta wani k'amshi ne ya daki hancinta itama a nata b'angaren haka lumshe ido yayi ya bud'e su a kanta a hankali ya kai hannunsa ya d'ago fuskar ta yana kallon idanunta da suka yi jajir ga Kuma wata k'wallar a cikin su girgiza mata kai ya yi a hankali ta lumshe idanunta take hawayen ciki suka zubo hanky ya zaro a aljihun sa ya fara goge mata yana magana k'asa k'asa "Please kukan ya isa haka karki rashin lafiya uhm kibar kuka okay?" A hankali ta gyad'a kanta a hankali ya jawota zai rungume ta Hajiya ta yi gyaran murya.




D'an waigawa ya yi ya kalle ta yana mata kallon tambaya ita Kuma ta harare shi tab'e baki ya yi ya yatsina fuska ya ce "Sannu fa Hajiya," yana fad'ar haka ya rungume Sabeeha yana yi Mata a magana a kunnenta a hankali "Please Baby ki dena," ita dai ajiyar zuciya kawai take saukewa a jikin sa ga kunyar rungume tan da yayi.




Ummi kuwa kallon su tayi tana murmushi tabbas tasan Maleek na son Sabeeha kamar yadda itama ke son sa ta tabbata zasu ba juna kulawar da ta dace ta ce "Son lokaci na k'urewa ku dai ba saina ce muku komai ba illa iyaka ga amanar yarana nan na damk'a ta a hannunku nasan baza ku cutar mun da su ba sannan nasan yarana masu biyayya ne saboda haka ku Kuma kuyi musu adalci ku kula da su," suka amsa da "Toh Ummi,"




"Ina ga yanzu ya kamata Fauwaz Kai da Umar zaku wuce da matan ku sannan akwai dangi da zasu raka su saboda haka kuje lokaci na k'urewa saboda kowa ya koma gida da wuri," da sauri Fauwaz ya ce "To Ummi," ya fad'a tare da mik'ewa Umar ma bakinsa dai har lokacin yak'i rufuwa sai jefawa Sameeha wani kallo yake yi.




Su Sabeeha kuwa ba k'aramun tashin hankali suka shiga ba jin abinda Ummi ta ce a tare zuciyoyin su ke bugawa dagaske dai rabuwar zasu yi ai tuni kamar ansa remote control an kunna su suka fara kuka a tare har Sabeeha da har lokacin tana jikin Maleek.



Sabreen da Sameeha kuwa rungume juna suka yi suna kuka Ummi kanta ta tausaya musu tashi kawai ta yi tabar d'akin domin tausayin su saboda bazata manta lokacin da za a kawosu gidan ba da Sabeeha ta ce indai ba tare da 'yan uwanta ba ta fasa aikin da kuma farkon zuwan su gidan da suka ce a d'aki d'aya zasu zauna amma yau ga ranar da zasu raba gida ka ga kuwa kuka dole.



Tana fita Fauwaz ya k'arasa wajen su ya janye Sabreen da ta rik'e Sameeha ya ce "Sorry my love zo muje," ya nufi k'ofa rik'e da hannunta.



Umar ma rik'e hannun Sameeha dake hawaye yayi suka nufi k'ofa yana mata magana k'asa-k'asa juyawa Sameeha ta yi tana kallon Sabeeha.



Wasu hawayen ne suka Kuma zubowa Sabeeha cikin kuka da kuma muryar ta da ta dashe ta ce "Please My zan raka su," k'ara rungume ta ya cigaba da kukan ta yi shi kuma ya waiga ya kalli Umar alamun su wuce kawai fita suka yi.



Nan aka tafi raka su Sabreen da Sameeha gidajen su Wanda fad'in had'uwa da tsarin gidajen b'ata lokaci ne tsarin gidajen irin na k'asar turai ne ku dai yi imagine yadda gidajen wad'an nan 'yan gatan 'yan bokon masu ji da kud'i zai kasance haka dangi suka tafi ana yaba gidajen da Kuma dukiyar da aka narkar wajen zuba furnitures d'in gidan da kayan kitchen domin gidan Sameeha da Sabreen bedroom uku uku ne Wanda kowannen su yasha furnitures nagani na fad'a falon kuwa guda hud'u hud'u kamar sun had'a baki ga garden da su swimming pool abun dai gwanin sha'awa.



Sabeeha kuwa tana jikin Maleek sai sauke ajiyar zuciya take yi tashi Hajiya ta yi tayi hanyar fita tana cewa "Kai dai

Please Login or Register in order to submit comment