Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kaimu wajen cin abinci mafi kusa," ya ce "To ba damuwa ku shigo," trolleys d'insu suka d'auka suka shiga ya jasu suna tafe suna fira kasancewar Mai napep d'in akwai surutu sai mamakin kamar su yake yi su Kuma suna amsa masa sama-sama saboda yunwar dake damun su.


Ya ce "Yawwa 'yan uku ga wani wajen cin abinci gaban mu kad'an sai dai na hajiyoyi ne domin wajen akwai tsadar abinci sai dai sun iya girki," Sabeeha ta ce "Bakomai mu tsaya a nan d'in," suna k'arasawa ya tsaya suka biya shi kud'in sa suka shige wajen janye da trolleys d'in su Sameeha na rik'e da magen Sabeeha wacce suke kira da pretty.



Motoci ne da yawa a harabar wajen suna shiga kuwa kallo ya dawo kansu saboda ganinsu janye da trolleys su kuwa basu damu da kallon da ake yi musu ba saboda damuwar su bata wuce cikin su ya d'auka ba guri suka samu can nesa da mutane suka zauna saboda ba sabawa da cin abinci suka yi cikin mutane ba.


Waiter ce ta je wajen ta ce "Me za a kawo muku?" Kallon Sameeha Sabeeha ta yi ta ce "Sameeha dear me za a kawo miki?" Sameeha ta ce "Jallop rice please with mirinda," Sabreen Kuma ta ce "Nima jallop rice amma da hollandia Mai sanyi," Sabeeha ta ce "Ni kuma fried rice with coslow sai maltina," juyawa waiter d'in ta yi ta tafi ba dad'ewa ta dawo ita da 'yar uwar ta d'ayar ta ce "Wow identical triple," murmushi kawai Sabeeha ta yi ta ce "Sunana Aysha," Sabreen ta ce "Nice name I'm Sabreen and here is my sister's Sabeeha and Sameeha," Aysha ta ce "Nice names nice to meet you," cikin gajiya da surutun ta Sabeeha ta ce "Nice to meet you too," tana fad'ar haka suka fara cin abincin.



Aysha ganin sun fara cin abinci ta tafi tana waigen su hakan ne ya janyo hankalin yawancin mutanen kansu sai kallon su ake yi saboda ganin su su uku iri d'aya.


Su kuwa sai cin abincin su suke yi Sabeeha ta ce "Kusan wani abu?" Sabreen ta ce "Meya faru?" Dariya Sabeeha ta yi ta ce "Da alama wata zata daku a wajen nan," Sameeha ta ce "Wato Sabeeha dear kin fara ko ni na rasa irin ki yanzu sai ki fad'i magana kuma sai ta tabbata wai to meyasa hakan?" Murmushi Sabeeha ta yi ta ce "Bansani ba nima amma Ni kaina Ina mamakin kaina haka kawai zanji wai abu kaza zai faru kuma ya faru wani bana ganin alamun abun zai faru amma wani lokacin kuma ina ganin alamun faruwar hakan kamar dai yanzu ku kalli waccan guy d'in Mai siffar 'yan daba magana yake yiwa waccan siririn abokin nasa tare da nuna masa waccan budurwar mai shan ice cream kuma alamu sun nuna magana yake cikin fushi har k'wafa yake yi," ta fad'a tana nunawa su Sabreen mutum da Kuma yarinyar.



Tunani suke yi anya Sabeeha bata da aljanu kuwa domin tunda suka taso take hakan sai dai ta dad'e hakan bai faru ba sai yau ko dan basa shiga mutanene oho basu gama tunani ba suka ga guy d'in ya shiga wajen direct ya yi wajen budurwar itama tana ganinsa ta mik'e tana zare ido Yana zuwa bai jira wata-wata ba ya fara zabgawa budurwar mari ita kuma tana zaginsa har mutane sun fara taruwa.



Mik'ewa Sabreen ta yi ta ce "Lallai ma waccan guy d'in d'an iska ne bari naje tsabar baisan darajar mata ba shine zai wani kama Marin ta?" Rik'e ta Sabeeha ta yi ta ce "Karki je babu ruwan ki domin ita ce bata da gaskiya," a tare su Sabreen suka had'a baki wajen cewa "Ta ya kika sani?" Dariya Sabeeha ta yi ta ce "Da kan ku ya kamata ku gane hakan ku duba lokacin da guy d'in ya shigo nan a firgice ta mik'e tsaye Kinga da alamau akwai abinda ya had'asu sannan ki duba mulki irin na mace da shine ya yi mata laifi baza ku ga ta tsure haka ba," aikuwa nan suka ji yo guy d'in na cewa "Ke dan kin raina mun hankali saboda bana kula ki shine zaki je har gurin mom d'ina kice kina d'auke da cikina to Wallahi kotu ce zata raba mu," duk mutanen dake wajen domin raba fad'an suka tafi jin maganar ta fi k'arfin su.



Sabreen ma zama ta yi tana cewa "Ahhab ai gara da yaci uban shegiya," Sabeeha kuwa waiter ta yafito da hannu zuwa waiter d'in ta yi Sabeeha ta ce "How much your money?" Ta ce "Six thousands eight hundred," bud'e jaka Sabeeha ta yi ta fito da kud'in ta biya.



Aysha ce ta k'arasa wajen ta ce "Sai tafiya?" Sabeeha ta ce "Eh,"


"A wanne unguwa ku ke ku bani address d'in ku wataran nazo," Sabeeha ta ce "Mu ba 'yan gari bane Kuma bamu san kowa nan ba yanzu ma zamu je mu nemi masauki ne," jinjina kai Aysha ta yi ta ce "Zan iya taimakon ku?" Sameeha ta ce "Haba Aysha waye yak'i taimako," Aysha ta ce "Kun ga rayuwar garin nan Yana da tsada mai zai hana ku zauna a nan ku dinga aiki," Sabreen ta yi caraf ta ce "Eh Kuma Sabeeha dear ta iya girki sosai," ta fad'a tana nuna Sabeeha.



Aysha ta ce "Ok ba damuwa bari naje wajen madam naji," tana fad'ar haka ta juya ta shige wani d'aki da alama Office ne.



Tana shiga ta samu ogar tasu a zaune kan kujera da glass fari manne a fuskar ta durk'usawa Aysha ta yi ta ce "Madam dama wasu bak'i ne a garin nan suka zo nan cin abinci sunce mun basu da masauki shine nayi musu tayin aikin mu tunda naji kina neman ma'aikata shine nazo na sanar Miki sannan d'aya a cikin su ta iya girki sosai," jinjina kai madam ta yi ta ce "Zo mun dasu," fita Aysha ta yi suka koma tare.



Kallon su Madam ta yi bayan sun gaisa ta ce "Amma 'yan uku ne ko?" Suka amsa mata da "Eh," ta ce "Masha Allah meye sunan ku?" Nan suka fad'a mata sunayen su ta jinjina kai sannan ta ce"Zan d'auke ku aiki sai dai naji ance akwai wacce ta iya girki sosai a cikin ku Kuma akwai wata Hajiya da ta bani cigiyar wacce ta iya girki sosai saboda yaron ta da duk Mai aikin da aka tura masa idan ya ci girkin ta sai yace bata iya ba bansani ba idan na turaki zai ji dad'in girkin ki ba domin idan na turaki mutum goma kenan dana tura musu ya ce abincin su ba dad'i wad'an da anan har santin girkin su ake yi Amma yanzu zaki yi anan muci muji kafin ki je can su Kuma 'yan uwanki zasu zauna anan tare da mu," a tare su Sabeeha suka kalli juna domin tunda suka tashi ko ina tare suke zuwa Sabeeha ta ce "To nagode amma gaskiya madam kiyi hak'uri bazan iya rabuwa da su Sameeha ba kawai zan zauna anan tare da su," Madam ta ce "No karki damu zan sanar da Hajiya idan ta yadda sai ku tafi dukan ku amma yanzu je ki Aysha ta raka ki kitchen white rice with fish soup nake so ki girka," gyad'a kai Sabeeha ta yi sannan ta tashi tabi bayan Aysha.



Kitchen suka tafi Aysha na tsaye na taya ta fira ita kuma tana girkin ta cikin k'arewa har ta gama sannan ta zuba a plate ta zuba miyar a k'aramun bowl sannan ta zuba salat d'in da tayiwa k'ananan yanka a gefen shinkafar yasha kayan had'i ta ajiye cokali a gefe ta d'auka suka tafi.



Fira ta samu su Sabreen nayi da Madam suna dariya saman table d'in Sabeeha ta ajiye abincin ta ce "Gashi na gama," Madam ta yi dariya ta ce "Iya saurin gamawar da ki kayi na yaba," murmushi Sabeeha ta yi.



Jan plate d'in gaban ta madam ta yi tai Bismillah ta kai one spoon bakin ta lumshe ido ta yi tana jinjina kai har wani kad'a kai take yi ta ce "Wow gaskiya kin iya girki ba dan kar nayi k'arya ba sai nace ban tab'a cin abinci Mai dad'in naki ba," gaba d'aya mutanen wajen suka sa dariya.



Aysha ta ce "Madam ba d'and'ane ne?" Madam ta ce "Kai Anya kuwa ko da yake zo kici one spoon kawai," k'arasawa Aysha ta yi ta ci cokali d'aya ta ce "Wallahi madam ban tab'a cin abinci Mai dad'in wannan ba gaskiya Sabeeha zanzo ki koyamin," dariya su Sabeeha ke yi ga mamakin su kuwa daga lauma d'ayan nan Madam bata k'ara bari Aysha ta ci ba.



D'aukar wayar ta ta yi ta kira Ummi tasa wayar a handsfree tana d'agawa bayan sun gaisa Madam ta ce "Yawwa Hajiya ansamu mai girkin sannan Wallahi ta iya girki sosai," daga can Ummi ta ce "Masha Allah Fulani yadda ki ke fad'an nan ta iya girki Allah yasa son ya so girkin ta," madam ta ce "Gaskiya Hajiya da wuya girkin ta yak'i burge shi saboda ta iya sosai na yaba sosai da girkin ta sai dai ba ita kad'ai bace 'yan uku ne Kuma tace idan ba tare da 'yan uwan ta zasu zo ba bazata ba da alama ba k'aramar shak'uwa ce tsakanin su ba," Ummi ta yi dariya ta ce "Banda abin Fulani ina ke Ina raba 'yan uku Wanda suka taso tare abinda za 'ayi gobe zan aiko driver ya d'auko su kawai," Fulani ta ce "To hajiya," daga haka suka yi Sallama.
[10/25, 7:37 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️


RUBUTAWA DAGA
HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ)




SADAUKARWA GA
MY DAUGHTER SABEEHA
BILKISU Z.YA'U (🅱️K)
AISHA MAGAJI DABO (AMA)




Page 6

Bayan Fulani ta ajiye waya ta kalli su Sabeeha ta ce "kun dai ji yadda muka yi da Hajiya da kunnen ku ni dai abinda nake so da ku shine ku tsaya kuyi abinda ya Kai ku babu ruwan ku da harkar da ba taku ba duk abinda aka saku kuyi sannan ku dage da tsafta duk da dama da ganin ku ba sai an fad'a ba kuna da tsafta sai dai ina so ku ninka wacce ku ke yi yanzu idan kunje can saboda Hajiya macece mai son gayu tana tsafta sosai sannan tana son duk wani mai tsafta bata da matsala da kowa na tabbata zata kula da ku sosai kamar yadda zata kula da 'ya'yan cikin ta ke dai Sabeeha abinda nake so dake shine ki dage sosai wajen yin aikin ki yadda ta kamata saboda ta d'auke ki ne saboda yaron ta shine babban d'anta Kuma babban soja ne kamar yadda na fad'a muku na kai 'yan aiki gidan da dama amma sai yace basu iya girki ba hatta k'anwar sa bai cin girkin ta sai dai idan mahaifiyar sa ce ta girka masa har mata ce da shi amma bai cin girkin ta domin Sam ita bama ta iya abincin ba kasancewar ta 'yar hutu," kallon juna su Sabeeha suka yi Fulani ta ce "kuna mamakin ta ya nasan matar sa bata iya girki ba ko?" Sabeeha ta ce "A'a saboda da ta iya ai baza a nemi Mai yi masa ba," jinjina kai Fulani ta yi ta ce "Good girl kin fad'i gaskiya sannan abinda nake so daku shine gidan wani irin gida ne dole sai kunyi hak'uri sannan duk masu aikin gidan suna da uniform Kuma nasan idan ku ka je za a baku zancen kud'in albashi Kuma baku da matsalar sa saboda suna da kud'i sosai haka kawai ma kyauta suke yi balle anyi musu aiki dan haka ku kula sosai," suka ce "Insha Allahu," suna tunanin lallai wannan gidan daga ji sun fi Yallab'ai Kamis kud'i.



Fulani ta ce "Aysha ki kaisu su d'akin ku su yi wanka su huta kafin gobe dan nasan da safe driver zai zo d'aukar su," Aysha ta ce "To," sannan suka fice.



Har d'akin ta kaisu suka ajiye kayan su sannan suka yi wanka suka yi sallah bayan sun idar ne suka yi shiru suna tunanin gidan da zasu aiki Sabreen ta ce "Wallahi daga jin gidan bana wasa bane Sabeeha dear Dan Allah ki nutsu gobe ki yi masa girki Mai matuk'ar dad'i wanda baki tab'a mai dad'in sa ba," hararar wasa Sabeeha ta yiwa Sabreen ta ce "Allah ya shirye ki," Sameeha ta ce "Ni dai fatana Allah yasa 'yan gidan basu da wulak'anci saboda bana son wannan karon mu sake guduwa," ita dai Sabeeha bata ce komai ba ta yi shiru tana sauraron su haka sukai ta fira abinsu sai tsakar dare suka yi bacci Aysha na jin kamar ta bisu goben.


Washe gari bayan sunyi Sallah basu koma bacci ba suka yi aika ce aikace sai wajen k'arfe goma sannan Madam ta je wajen ta shiga d'akin da suke ta ce "Ya kamata ku shirya yanzu," suka amsa da "toh," wanka sukayi sannan suka fara tunanin kayan da zasu sa saboda ce musu da akayi Hajiya na son mai tsafta.


Sameeha ta d'ago wata amfar su iri d'aya ta ce "Kun ga musa wannan mana," kallon kayan suka yi Sabreen ta ce "A'a gaskiya gara musa wad'an nan rigunan,"ta fad'a tana nuna wasu dark pink d'in dogayen rigunan su.



Sameeha ta ce "Sabeeha dear ke wanne ne zab'in ki?" Girgiza kai Sabeeha ta yi ta ce "Karku damu duk Wanda ya yi muku shi zamu sa," Sameeha ta ce "To mu sa rigunan kawai," dogunayen rigun nan suka sa har turare suka fesa duk da su basa kwalliya amma sunyi kyau sosai kamar ka sace su ka gudu sai shek'i suke yi.


D'akin Fulani ta shiga ta ce "To driver yazo ku fito," trolleys d'in su suka d'auka suka nufi waje Aysha ta karb'i trolley d'in Sabeeha ita Kuma ta d'auki pretty d'in ta suka fita wajen.


Tsayawa kallon motar da tazo d'aukar su suka yi saboda motar ta yi kyau bak'ar BMW ce sannan tinted windows ne da ita sai shek'i take yi driver cikin uniform d'insu na drivers fari.



Trolleys d'insu yasa a boot gaisawa suka yi da Fulani su Sabeeha ma suka gaishe shi ya ce "Lafiya lau 'yan uku," Dan ko ba a fad'a ba kana ganinsu ka ga 'yan uku.



Fulani ta ce "To Allah ya kiyaye baku da waya ko?" Suka ce "Eh," ta ce "Karku damu zamu dinga gaisawa a wayar Hajiya Allah ya kiyaye," gaban mota Sabeeha ta shiga su Sameeha a baya driver ya ja mota suna d'agawa su Aysha da Fulani hannu.



Suna tafe driver mai Suna Alasan yana jansu da fira aikuwa nan sukai ta fira abinsu kamar sunsan juna ya ce "Wannan magen ki ce?" Gyad'a kai Sabeeha ta yi sai lokacin ta yi tunanin kar dai akwai Wanda bai son mage a gidan take sai ta ji jikin ta ya yi sanyi domin ba k'aramun so takewa pretty ba.



Tunanin ta ne ya katse ganin layin da suka shiga nan suka fara raba idanu suna kallon ikon Allah domin ko a mafarki basu tab'a tunanin zasu gansu a irin wannan gidan ba suna zuwa gate sojojin dake gate d'in suka bud'e musu suka wuce ba tare da wani bincike ba domin ansan motar ta gidan ce nan su Sabeeha suka dinga kalle kalle ganin ko ina sojojine birjik kamar a barrack sannan ko ina a gidan shuke shuken fulawoyi ne kala kala da suka k'awata gidan sai da suka yi tafiya mai d'an Nisa suka isa wani gate d'in ana bud'e musu suka hango wani had'adden gini duk glass ne a jikin ginin ga sojoji ta ko ina parking lot Kuma cike da motoci na gani na fad'a ga wasu parts d'in a gidan sannan ga 'yan aiki mata da maza ko wannen su cikin uniform maza coffee mata blue d'in riga da skirt har da hijabi k'arami.



Tunanin su ne ya tsaya lokacin da suka tsaya gaban part d'in Ummi a hankali suka fita suna k'arewa gidan kallo.


Alasan ya ce "Nan zaku shiga bari a shigar muku da kayan ku," Hadiza ce da Yasira suka fito daga part d'in Alasan ya ce "Yawwa Hadiza ku shigar musu da kayan su bak'in Hajiya ne," d'aukar kayan su Hadiza suka yi suna yi musu Sannu da zuwa basu tab'a tunanin 'yan aiki bane saboda basu yi kama da 'yan aiki ba.



Bin bayan su Hadiza suka yi har zuwa cikin falon nan suka k'ara tabbatar da cewar masu gidan manya ne na gaske ta b'angaren kud'i gani suke yi kamar a mafarki can suka hangi Ummi zaune tasha gayu cikin wani less ash Mai matuk'ar kyau falon banda k'amshi ba abinda yake yi k'arasawa suka yi lokacin suka ji Ummi na cewa "Eh gasu sun k'araso ok sai anjima," Ummi ta katse kiran tare da kallon su Sabeeha ta yi murmushi ta ce "Sannun ku da zuwa ku k'araso mana," a k'asan carpet suka zauna suka ce "Hajiya Ina wuni?" Cikin fara'a Ummi ta ce "Lafiya qlau," sannan ta kalli su Hadiza ta ce "kuje," tafiya suka yi suna cewa "Wallahi 'yan uku ne ikon Allah kama sak ba banbanci,"



Ummi ta ce "Sannun ku da hanya 'yan uku," haka kawai Ummi ta ji son yaran har cikin ranta murmushi kawai suka yi Ummi ta ce "meye sunayen ku?" Sabreen ta ce "ni sunana Sabreen," Sameeha ta ce"Ni Kuma Sameeha," "Ni Kuma Sabeeha," cewar Sabeeha Ummi ta ce "Masha Allah," Zainab ta fito daga kitchen ta cika gaban su Sabeeha da abinci da drinks.



Ummi ta ce "Wacece ta iya girkin a cikin ku?" Sabeeha da ta zuba lemo a cup zata sha ta ce "Ni ce Hajiya," Ummi ta ce "A'a ni bana son Hajiya ku kirani Ummi ku d'auke ni kamar mahaifiyar ku," suka ce "Toh Ummi,"



"Sabeeha ke ce daga yau zaki dinga yiwa yarona girki tun daga safe har dare gobe zaki fara sannan ku Kuma zaku dinga yi mun abinda ba a rasa ba saboda ina da masu yi mun komai sannan muna da uniform da 'yan aikin gidan nan ke sawa amma ku banda ku saboda ina jinku kamar 'ya'yana sannan naga kayan ku iri d'aya ku ke amfani da shi sannan za a dinga biyan ku dubu d'ari duk wata," a razane suka kalli Ummi jin nannauyan kud'in da za a dinga basu duk wata ba tare da sunyi wani nannauyan aiki ba dan ko a gidan Yallab'ai da suke aiki kamar bayi dubu goma ne a wata.


Ummi ta ce "Ko kud'in sunyi muku kad'an sai a k'ara muku," da sauri har suna had'a baki suka ce "A'a wallahi Ummi mungode Allah ya saka da alkhairi," ta ce "Ba damuwa ai hakk'in ku ne," Sabeeha ta ce "Ummi dama wannan magen ba matsala bansaniba ko wani baya so a nan gidan," Ummi ta ce "A'a ki bar abar ki," wani sanyi suka ji a ransu.


Rinaz ce ke saukowa daga stairs da alama daga bacci ta tashi riga da wando ne a jikin ta kusa da Ummi ta zauna sai lokacin ta lura da su Sabeeha zare ido ta yi tana kallon ikon Allah kasa yin shiru ta yi ta ce "Oh my God Ummi Kinga kama kamar mutum d'aya?" Dariya Ummi ta yi ta ce "Allah ya shirye ki to ga k'awaye Nan nayi miki," Nasreen ta ce "Na karb'a Wallahi Ummi," Nan ta tambaye su sunayen su suka fad'a mata itama ta fad'a musu sannan Ummi ta ce "Yanzu kuje d'akin ki su huta zuwa gobe zansa a gyara musu dakunan su," kallon juna suka yi Sabreen ta ce "Ummi idan da hali dan Allah a barmu a dak'i d'aya dukan mu," Ummi ta ce "To ba damuwa kuje ku huta," bin bayan Rinaz suka yi suka haura stairs suna kallon aljannar duniya.


D'akin Rinaz d'in suka shiga wayyo kyau komai na d'akin pink ne gwanin sha'awa Rinaz ta ce "feel free ku d'auka a gidan ku ku ke kunaji dai Ummi ta had'a mu k'awance," murmushi suka yi zama suka yi Nan Rinaz taita yi musu surutu domin so take su saki jiki da ita.



A haka har lokacin sallar azahar ya yi suka yi alwala suka yi sallah sannan Sabeeha ta haye saman gadon Rinaz ta kwanta bacci ne ya d'auke ta yayin da tabar su Sabreen na fira.



Maleek ne kwance saman gadon sa 3Quater ne a jikin sa black da white t-shirt ruf da ciki ya kwanta yana danna laptop d'in sa sai dai gaba d'aya hankalin sa baya kan aikin da yake yi gaba d'aya tunanin sa yana wajen yarinyar hannunsa ya zura cikin lallausar sumar sa ya hargitsa tare da rufe laptop d'in ya lumshe idanunsa yana jin wani iri a jikinsa ji yake tun yanzu son yarinyar na neman yi masa illa gashi yasa an bincika masa k'auyen da ya ga yarinyar amma ba bu labarin ta.


Saurin bud'e idanunsa ya yi jin an kwanta masa a jiki Nasreen ce sai wani narke masa a jiki take yi a hankali ya janye ta a jikin sa sannan a hankali ya ce "Please Nasreen ki kyaleni sanin kanki ne na hanaki hawar mun jiki," tura baki ta yi ta tashi ta fice fuu da kallo ya bita har ta fita ya koma ya kwanta.


Sai bayan la'asar Sabeeha ta tashi daga baccin da take yi ta samu su Sabreen basa d'akin kayan ta ta gani akan gadon tashi ta yi ta fad'a toilet ta yi wanka ko da fito Mai kawai ta shafa tasa riga da skirt na atamfa tayi sallah ta gyara d'akin tsaf sannan ta fita falon dake saman basa nan down stairs ta sauka anan ta samu Ummi na zaune tana shan fruits Fauwaz na gefen ta yana danna waya wajen ta k'arasa ta ce "Sannu da hutawa Ummi," kallon ta Ummi ta yi ta ce "Yawwa yarinyata," ta kalli Fauwaz ta ce "Ina wuni?" Sai lokacin ya d'aga Kai ya kalle ta domin Fauwaz halin sa daban yake yana da d'an girman Kai da miskilanci a hankali ya ce "Lafiya lau Ummi Wai ita ce d'ayar?" Ummi ta ce "Eh ita ce," a zuciyar sa ya ce Masha Allah.



"Ummi ina su Sabreen fa?" Ummi ta ce "sun fita zaga gida su da Rinaz," jinjina kai ta yi sannan ta tashi ta nufi inda take tunanin kitchen ne aikuwa kitchen ne Wanda ya gaji da had'uwa yasha kaya sosai ko fridge sun Kai biyar su Hadiza ta samu zasu d'ora abinci gaisawa suka yi sannan ta fara taya su aikin tana yi suna fira kad'an-kad'an zobon da ta ga zasu had'a tace a bar mata ta had'a aikuwa suka bar mata can cikin kitchen d'in ta shige kasancewar kitchen d'in ciki da falo ne.



Ta d'ora zob'on a saman wuta sannan ta d'an daka ginger tasa a ciki sai da ya tafasa sosai sannan ta sauke shi ta tace shi a wata roba Mai kyau sannan ta d'auko water melon a fridge ta yanka ta cire b'awon ta yankata k'anana ta cire k'wallayen ta zuba a blander sannan ta d'auki cucumber ta feraye itama ta yankata ta had'a da water melon d'in ta yi blanding d'insu ta tace ta zuba cikin zob'on sannan ta zuba tiara mai watermelon sannan tasa kayan k'amshi da color sannan ta samu wani jug a cikin d'in ta juye a ciki tasa a fridge sannan ta cigaba da ta ya su Hadiza aiki har suka gama suka jera komai a daining.



Ko da su Sabreen suka dawo a falon suka zauna suna ta fira abinsu.


Da daddare suka hallara a daining su Sabeeha duk suna jinsu daban a hakan ma sai da Ummi ta nuna musu fushin ta sannan suka zauna zasu ci abinci tare sai dai sun kasa sakewa zob'on Ummi da Fauwaz suka zuba suka sha Fauwaz ya ce "Wow Ummi amma ya yi dad'i sosai," itama Ummi ya yi mata dad'i sosai ta kalli Sabeeha ta ce "Ke kika had'a ko?" Noding kanta ta yi Ummi ta ce "Ko da naji ni nasan basu Hadiza bane suka had'a," Rinaz ta ce "Wayyo dad'i Wallahi Ummi," dariya suka yi mata a haka suka gama cin abincin sannan suka kwashe komai suka haye stairs dan zuwa su yi sallah.



Tunda suka yi sallah suka zauna zaman fira.


Maleek ne zaune a falonsa

Please Login or Register in order to submit comment