Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tafi masallaci.



Daddy kuwa motocin su gama parking guards d'in su suka bud'e musu k'ofa suka fito manyan mutanene sannan kana kallon su kaga ya da k'ani saboda kamar da suke yi.



Sannan Daddy ya wuce part d'insa haka ma Uncle ya wuce part d'insa.



Da daddare Maleek na zaune a falon sa yana kallon news Nasreen ta shiga falon sai wani karairaya take yi tana iyayi kallo d'aya ya yi mata ya d'auke Kai domin tsoro ma ta bashi tayi wani fau kamar aljana dama fara ce ita sai Kuma ta k'ara da mai sai dai bata wani kyau ga ta da k'ananun idanu kamar 'yar China.




K'arasawa ta yi ta zauna a gefen sa ta ce "Sannu da hutawa husby," bai kalle ta ba ya ce "Kece da sannu ba Maleek ba," basarwa ta yi ta ce "yawwa Ya Maleek dama cewa nayi mai zai hana na zauna a nan part d'in ni bana son waccan part d'in," kallon banza ya you mata sannan ya ce "koh?" Wayar sa ce ta yi ringing d'auka ya yi ya ce "Ok gani nan zuwa," yana fad'ar haka ya yi hanyar fita ta ce "Yaya Maleek ina Kuma zaka muna magana?" Ba tare da ya juya ba ya ce "Kiran da ya fi naki muhimmanci zani Kuma a can zaki zauna kya iya fitar mun a part," Yana fad'ar haka yasa Kai ya fice itama ranta a b'ace ta fita.
[10/25, 7:34 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️



RUBUTAWA DAGA
HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ)





SADAUKARWA GA
MY DAUGHTER SABEEHA
BILKISU Z.YA'U (🅱️K)
AISHA MAGAJI DABO (AMA)


Page 3


Yana fita Kai tsaye part d'in Uncle ya shiga da sallama a bakin sa amsawa sukayi suna zaune akan kujera k'arsawa ya yi ya zauna k'asan carpet ya ce "Daddy uncle sannun ku da hutawa da fatan Kun dawo lafiya?" Daddyn say ya ce "Lafiya lau Son," Uncle baban Nasreen kallon banza ya yi masa ba tare da ya amsa ba shima Maleek bai sa akan sa ba ya kalli mahaifin sa ya ce "Daddy gani,"



"Son dafatan ka sanar da auren ka ga abokan ka da Kuma wajen aikin ka ko Dan naji har yanzu banji wata sanarwa daga radio ko jarida ko gidan televisions ba," ya ce "Daddy gaskiya ban sanar ba," kafin Daddy ya yi magana Uncle ya fara zazzaga masifa "Ai dama Kai baka da tarbiyya baka daraja iyayen ka wato kai ba a isa da Kai ba ko to wallahi ka kiyayeni wawan yaro kawai wato saboda tsanar da ka yiwa daughter ne yasa baza ka sanar da auren ba kenan?" Shiru Maleek ya yi zuciyar sa na tafasa dan ji yake kamar ya shak'e Uncle ya kaisa har lahira Amma ba dama saboda wan mahaifinsa ne.



Kallo d'aya zaka yi masa kasan Yana cikin b'acin rai saboda idanunsa sunyi jajur kamar Wanda aka watsawa barkono a idanun jijiyoyin dantsen sa duk sun tashi dan a lokacin duk Wanda ya damk'a sai dai wani ba shi ba.



Daddy dai ko uffan be ce ba mik'ewa Maleek ya yi yayi hanyar waje Uncle na cewa "Ka gani ko Hamza ka ga rashin tarbiyyar ko ina magana Amma saboda ya rainani ya tashi zai fita wato ga mahaukaci na magana," har lokacin Daddy bai yi magana ba dan yasan idan har Maleek ya tsaya a wajen zai iya aikata abinda ba a tab'a tunani ba domin yana da zuciya sosai.



Haka Maleek ya fita yabar Daddy Sai Masifa yake yi Daddy dai bai ce komai ba shiru ya yi Yana sauraron yadda yayan sa ke k'arewa d'ansa zagi da tsine masa a gaban sa.



Maleek kuwa ko da ya fita part d'in sa ya wuce ya kwanta saman lallausan gadon sa sai sauke ajiyar zuciya yake yi kamar Wanda ya yi kuka ya k'oshi da abun ya dame shi ya tashi ya yi ta sallah ya yi karatun Qur'an sannan ya ji zuciyar sa ta yi sanyi.


Washe gari aka d'aura auren Fatima Aminu mai dala da MG Abdul-maleek Hamza mai dala akan sadaki dubu d'ari biyu d'aurin auren ya samu halartar abokan Daddy da Uncle daga k'asashe daban daban sai dai ango ba tawagar sa dan bai yi gayyata ba.




Ana gama d'aurin auren ya nufi gida part d'in sa ya nufa ya watsa ruwa ya kwanta bayan ya ba sojojin sa umarnin kar su bar kowa ya shiga inda yake.



A firgice su Sabeeha suka tashi daga baccin da suke yi sakamakon bugun da akewa k'ofar d'akin su gaba d'aya sun gama tsorata especially ma Sameeha Dan har ta fara hawaye ta b'oye a bayan Sabreen da itama jikin ta rawa yake yi Sabeeha kuwa tsaki ta ja tare da nufar k'ofar ta bud'e.



Farida ce ta shiga d'akin tare da cin kwalar Sabeeha ta ce "Ke har wacece ke da zaki aure mun miji to wallahi yau sai kin bar gidan nan tunda bana uban ki bane," yatsina fuska Sabeeha ta yi ta ce "Wanne mijin naki ki ke magana Wai?" Dak'uwa Farida ta yi mata ta ce "Dan uwar ki miji nawa gareni to wallahi daga ke har 'yan uwanki sai kun bar gidan nan shegu aljanu," k'arfi Sabeeha tasa ta fisge rigar ta ta ce "Dalla can malama cikani muje wajen mijin naki shine yace Miki akwai alak'a tsakanina da shi to bari kiji ko maza sun k'are bazan auri wannan wawan ba kawai dama danna had'a ku ne Kuma ko yanzu alhamdulillahi burina ya cika," Sabreen da Sameeha sakar ido suka yi suna kallon ikon Allah basu tab'a tunanin k'arfin halin Sabeeha ya kai haka ba.


Juyawa Farida ta yi ta fita tana cewa "Gara da ki ka tonawa kanki asiri," tana fita Sabeeha ta kyalkyale da dariya ta ce "Sabreen dear Sameeha sister ya ku ka ga wannan," to ku biyo ni ku ga wani salon ta d'auki hijabi ta d'ora saman hijabin jikin ta ta fita suma binta suka yi suma.



Falo suka fita suka samu Kamis zaune kan kujera Farida kuma na tsaye a kansa sai zabga masifa take yi kamar zata tsaga gidan saboda d'aga murya "To Wallahi sai dai idan ka sake ni ka rasa wacce zaka aura sai waccan yarinyar wacce ba son Allah da annabi take ma ba so take kawai ta ga ta rabamu," Sabeeha na zuwa falon ta fashe da kukan munafurci har da k'ak'alo hawayen k'arya tuni Kamis ya rikice ya yi wajen ta kamar zai rungume ta ya ce "Subhanallah maiya faru?" Cikin kukan k'arya Sabeeha ta ce "Ni kawai bar maka gidan ka zanyi saboda bazan iya da masifar matar ka ba yanzu fa zuwa ta yi ta hauni da duka ina cikin bacci ni kawai tafiya zamu yi bazan iya ba tun yanzu ta fara dukana ina ga munyi aure?" A fusace Kamis ya kalli Farida ya nuna ta da yatsa ya ce "Wallahi Farida ki kiyayeni idan ba haka akan yarinyar nan yanzu zan sake ki ki tafi," zazzaga masifa yake yi kamar Wanda aka yiwa asiri ita kanta Farida mamaki take yi.



Sabeeha ta ce "A'a my love ka kyale ta kawai indai nice na hak'ura amma ka ja mata kunne ba ruwan ta dani," aikuwa nan ya fara bugawa Farida warning har ma 'yan aikin gidan akan duk abinda Sabeeha ta ce ayi ayi shi ba b'ata lokaci sannan ya sallami kowa.



Su Sabeeha ma suka koma d'aki suna tik'ar rawa ko a jikin su wannan karon har da Sameeha a rawar.


Tun daga ranar ko aiki denawa suka yi a gidan Farida kuwa makirci kala kala tana shansa wajen Sabeeha wataran har duka Kamis kewa Farida akan Sabeeha.


B'angaren amarya Nasreen kuwa a ranar da aka d'aura aure aka Kai ta part d'in ta dake gidan yasha kaya gida guda ne harda gate a gidan upstairs ne ya sha kyau har ya gaji ga sojoji ta ko ina a gidan sai dai har aka kaita bata ga ango ba yana can yana bacci abinsa.



Amarya kuwa har k'arfe sha d'aya ba ango ba labarin sa har k'awayen ta duk sun watse amma babu shi wayar ta ta d'auka ta kira Uncle tana kuka kamar wacce aka yiwa mutuwa yana d'agawa ta sake fashewa da kuka daga can uncle a rikice ya ce "Mamana ya akayi ne mai ya faru?" Cikin kuka ta ce "Daddy ka ga fa har yanzu ya Maleek bai zo ba," Uncle ya ce "kwantar da hankalin ki ina zuwa yanzu zaki ga ya zo," bai jira cewar ta ba ya kashe wayar ya fara neman layinkan MG amma duk a rufe shi kuwa rufe wayoyin sa yayi saboda kar ma a neme sa.



K'wafa Uncle ya yi sannan Kai tsaye ya nufi part d'in Ummi babu ko sallama ya shiga falon sai hura hanci yake yi Fauwaz ne zaune yana charting yana cin fruits ko kallon inda Uncle d'in yake bai yi ba sai ma rera wak'a da yake yi ta joeboy "oh my baby I'm getting jealous already,"


"Kai Fauwaz!!" Uncle ya daka masa tsawa kallon sa Fauwaz ya yi yana yamutsa fuska alamun tsawar ta dame shi sannan ya ce "Na'am," jinjina kai Uncle ya yi ya ce "Dan uwar ka baka ganni bane da bazaka gaishe ni ba ko da yake ba ta kai nake yi ba uban ka nake nema kira mun shi," mik'ewa Fauwaz ya yi ba tare da ya kalli inda Uncle yake ba ya bud'e wata k'ofa ya shige da alama d'akin sa ne.



Sakin ido Uncle ya yi yana kallon ikon Allah lallai wannan yaron ya zama dole na koya masa hankali Yana nan tsaye Rinaz ta sauko daga stairs hannun ta rik'e da glass cup sarai ta ga Uncle amma ta nuna kamar ba mutum a falon ta nufi kitchen ta ajiye cup d'in hannunta ta fito.



Har zata fara hawa stairs ta ji Uncle ya ce "To 'yar gidan marasa tarbiyya baki iya gaisuwa ba?" Sai lokacin Rinaz ta kalle shi ta ce "Sannu Uncle tarbiyya Kuma ai babu ita a nan tunda ni goyon Nasreen ce," tana fad'ar haka ta tafi ta barshi Yana danna ashar.



A falon sama ta had'u da Ummi k'ofar d'akin ta ta bud'e zata shiga Ummi ta ce "Mamana ke da waye naji kamar kina magana da wani a down stairs?" Murza ido Rinaz ta yi ta ce "Eh to naga wani kamar Uncle sai dai idanuna basu tantance ba saboda daga bacci na tashi," tana fad'ar haka ta shige d'aki tasa key.



Girgiza kai Ummi ta yi saboda sarai tasan Uncle d'in ne sai dai tasan halin su Rinaz rashin kunya suke masa sab'anin Maleek da ya kasance mai girmama shi sai dai shi uncle d'in baya gani su Kuma su Rinaz ganin irin rashin mutuncin da Uncle d'in kewa yayan nasu ne harma da Ummi yasa su Kuma basa ragawa Uncle duk da basa yi a gaban Maleek saboda sun san tsab zai iya zane su.



K'asan Ummi ta sauka ta ce "Laa Yaya kaine sannu da zuwa ai bansan da shigowar ka ba," tsaki ya ja ya ce "Ai dama baza ki saniba tunda kin fini iko da k'anina tun d'azu na shigo amma kin hana shi fitowa sai yara mara tarbiyya da ki ka haifa," k'asa Ummi ta yi da kanta bata ce komai ba domin idan da sabo ta saba da halin wan mijin nata.




Daddy ne ya sauko yana cewa "Sannu da zuwa yaya ai bamusan ka shigo ba," harara ya aikawa Daddy ya ce "ta ya zakasan na shigo bayan gimbiyar ka uwar mata ta hanaka fitowa," girgiza kai Daddy ya yi ya ce "A'a Wallahi yaya ba laifin Aysha," d'aga masa hannu Uncle ya yi ya ce "Ba abinda ya kawoni kenan ba nazo ne akan waccan d'an naku ni zai rainawa hankali na d'auki 'yata na ba shi amma kamar an kai masa abu mara amfani to wallahi duk inda yake ku kira shi ya tafi wajen amaryar sa," Yana fad'ar haka ya kad'a babbar rigar sa ya fice da kallo suka bi shi har ya fita.


Daddy ya kalli Ummi ya ce "Aysha kinga halin d'an ki ko Sam baya gudun b'acin ranmu da nashi gaba d'aya ki kalli abinda ya ja to yanzu ki kira shi ya tafi wajen matar sa," shima Yana fad'ar haka yabar falon.



Ajiyar zuciya Ummi ta sauke sannan ta d'auki wayar ta ta kira wayar Maleek lokacin kunna wayar kenan wayar Ummi ya shiga d'agawa ya yi ya ce "Hello Ummina," ta ce "Son ina ka shiga ne yau fa kwana wajen biyar ban ganka ba?" Ya ce "lafiya qalau nake Ummi," ta ce "Masha Allah amma dan Allah son ka dena jamun magana yanzu Yaya yabar nan wai baka je wajen amaryar ka ba dan Allah ka tafi yanzu," daga can ya sauke numfashi ya ce "To Ummi bari naje," ta ce "Yawwa d'ana Allah ya yi maka albarka," ya ce "Ameen Ummina goodnight I love you," ta ce "I love you more," daga haka ya ajiye wayar ya tashi ya fad'a bathroom ya yi wanka.



Yana fitowa ya zura jallabiyya tare da fesa turare ya d'auki wayoyin sa ya fice daga d'akin.



Yana fita motar sa ya hau ya nufi gidan ko da ya yi parking aka bud'e masa k'ofa ya fita ya shiga falon ya nemi waje ya zauna a falon ya jingina a kujera ji yake dama bai dawo k'asar ba gaba d'aya bai da wani kwanciyar hankali ya dad'e yana tunani sannan ya mik'e ya haye stairs.


Tura k'ofar d'akin ya yi ya shiga da sauri Nasreen ta kalli k'ofar idanunta sunyi jajir saboda kukan da tasha sai kuma ta ba shi tausayi Dan ko ba komai 'yar uwar sa ce bai kamata ya barta tana kuka haka ba ai laifin mahaifin ta bai kamata ya shafe ta ba tunda ita mai son shi ce halin ta ne kawai bai so.



Bai gama tunanin da yake ba Nasreen ta tashi da gudu ta rungume shi tana kuka bai shiru ya yi yana jin yadda take kuka sannan a hankali ya janye ta daga jikin sa ya zaunar da ita gefen gado Yana kallon ta sannan ya ce "Kukan na meye?" Ba k'aramun dad'i ta ji ba saboda kulata da ya yi ta ce "Tun d'azu nake jiran ka baka zo ba," d'an tab'e baki ya yi ya tashi tsaye ya ce "Kinci abinci?" Girgiza kai tayi ya juya ya je kitchen ya ebo mata snacks da kaza da drinks ya Kai mata ya ce "Ki daina zama da yunwa," noding kanta ta yi sannan ta fara ci sai da ta gama ci ta koma ta kwanta ya ce "Wait kinyi sallah ma kuwa?" Shiru ta yi dan rabon ta da Sallah tun kafin a fara bikin su shirun da ta yi ne ya tabbatar masa da bata yi ba ya ce "Please tashi ki yi kar asa mun gida ya kama da wuta," ya fad'a kamar ba shi ya fad'i maganar ba.



Tashi ta yi tai wanka lokacin da ta fito bata same shi a d'akin ba sallar ta yi sannan ta fita zuwa falo can ta same shi ya rufe ido kamar mai yin bacci ta zauna gefen sa ta ce "Ya Maleek," a hankali ya bud'e ido ya kalle ta ta ce "Nayi sallar," ya ce "Good," daga haka bai Kuma cewa komai ba ta ce "Ya Maleek muje mu kwanta," bece komai ya mik'e yana gaba tana binsa a baya har d'akin ta kwanciya ya yi ya ce "Bismillah kwanta," ya fad'a yana nuna mata gefen sa hayewa ta yi ta kwanta.


Maleek ya kasance mutum mai hak'uri da Kuma tausayi hakan ne yasa yake mata hakan sannan zai yi k'ok'ari wajen sauke duk wani nauyi nata da ya hau kansa yana cikin wannan tunanin ya ji ta rungume shi ta baya ji ya yi kamar namiji ne ya tab'a shi saboda bai da wani feeling a kanta.


Juyawa wajen ta ya yi Yana kallon ta itama kyakkyawar fuskar sa ta tsurawa ido kamar zata had'iye shi a hankali ya lumshe idanunsa mai d'auke da zara-zaran eye lashes bai ankara ba ya ji ta had'e bakinsa da nata ta fara kissing da sauri ya bud'e idanunsa Yana kallon yadda take tsotse masa baki kamar mayya.



Tun baya biye mata har ta bashi tausayi ganin yadda ta fita hayyacin ta ya fara k'ok'arin faranta mata sai dai abinda ya ji ne ya sa shi saurin tashi ya shige toilet wanka ya yi ya fito ya nemi gefen gadon ya zauna ba tare da ya kalle ta ba.



Ita kuwa a nata b'angaren Addu'a yake Allah yasa bai gane ita ba virgin bace bata gama tunanin ba ta ji ya ce "Ya akayi hakan ta faru?" Kuka ta fara yi tsawar da ya daka mata ne yasa ta yi shiru ya ce "Tambayar ki nake yi!!" Cikin kuka ta ce "Dan Allah Yaya kayi hak'uri dama Arfat ne ya gama sanina," jinjina kai Maleek ya yi ya ce "D'an gidan waye?" Tana hawaye ta ce "D'an gidan Alhaji Hamisu kwangila," a d'an razane Maleek ya kalle ta ya ce "Tabbas baki da hankali Nasreen ke yanzu har iskancin ki ya Kai Nan ko da yake ba laifin ki bane na Uncle ne Amma kisani daga yau karki kuskura kice zaki k'ara tab'ani stupid kawai," kuka kawai take yi tana bashi hak'uri ya ce "kukan da kike ba abinda zai amfana Miki ni dai bazan tona Miki asiri ba saboda bani da riba amma idan kin tona kanki I don't care," yana fad'ar haka ya tashi yabar mata d'akin sai aikin kuka take yi.



Sabeeha ce zaune a d'akin su ita da 'yan uwan ta wata 'yar aiki ta shiga hannunta rik'e da envelope har k'asa ta tsugunna ta ba Sabeeha ta ce "Ranki ya dad'e gashi inji Yallab'ai ya ce a kawo muku salary d'in ku ne," karb'a ta yi ta ji da nauyi ko ba a fad'a ba tasan kud'in sunfi k'arfin iya na salary d'in su.


'yar aikin na fita ta kalli su Sameeha ta ce "Sabreen dear ku fara had'a mana kaya yau ba sai gobe ba zamu bar gidan nan," aikuwa suka fara had'a kayan su.


Da daddare suka d'auki trolleys d'in su suka fito suna tafe suna sand'a a falo suka hangi Farida zaune ta zabga uban tagumi sai kuka take yi fuskar ta ta kumbura tsabar dukan da take sha gun Kamis ko kula dasu bata yi ba har suka fice bata sani ba.


Turus suka tsaya ganin Mai gadi a bakin k'ofa da Kuma Mai bawa flowarers ruwa Sameeha ta ce "Sabeeha dear yanzu ya zamuyi?"



Jan hannun Sameeha ta yi a hankali suka bi ta baya kasancewar katangar bayan babu wani tsayi suka d'ane suka haure suna haurawa suka fara gudu har sai da suka fita titi kasancewar ba wani dare ne ya yi ba suka samu mota suka shiga sai k'auyen su.
[10/25, 7:35 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️


RUBUTAWA DAGA
HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ)




SADAUKARWA GA
MY DAUGHTER SABEEHA
BILKISU Z.YA'U (🅱️K)
AISHA MAGAJI DABO (AMA)




Page 4

Ba su suka je k'auyen su ba sai tsakar dare tafiya suke a tsorace saboda dare ne Kuma garin su duk daji da haka suka k'arasa gidan su da ko k'ofa babu Kai tsaye suka shiga gidan da sallama amma gidan tsitt kamar babu kowa cikin sa.



Kad'an suka hango haske a d'akin Abban su d'akin suka nufa Sameeha ta bubbuga k'ofar d'akin daga ciki Abban su ya ce "Waye?" Sabeeha ta ce "Mune Abba, jin muryar 'ya'yan sa ne yasa ya bud'e k'ofar Yana bud'e musu k'ofa suka rungume shi suna murnar ganinsa shima tsabar farin cikin ganin su har hawaye ya yi.


Sannan suka zauna Abba ya ce "Aminaina k'ara goduwa ku ka yi?" Sabeeha ta ce "Eh mana mun gaji," Sameeha ta ce "Eh Wallahi Abba mutanen gidan basu da mutunci kullum wulak'anci ake yi mana," Sabreen ta cigaba da cewa "Kuma fa Abba wataran ma har dukan mu suke yi," kallon tausayi Abba ya yi musu sannan ya ce "Aminaina rayuwa fa dole sai kunyi hak'uri da ita yanzu dawowar nan da ku ka yi Allah kad'ai ne yasan abinda zai faru idan yaya ya sani kunsan bata d'aga muku k'afa har dukan kunsan yi muku shi yake yi," shiru suka yi saboda sarai suma sunsan halin wan mahaifin nasu.



Sabeeha ta ce "Abba kaci abinci kuwa?" Girgiza kai ya yi ya ce "Yarinyar Abba ai yau ba ranar abinci bace Ni Kuma babu lafiyar da zan fita na nema," tausayin mahaifin nasu ne ya kama su suka bud'e trolleys d'in su suka fito da snacks da lemo suka ci dama suma suna jin yunwar sai da suka k'oshi Abba ya ce "Yanzu ku kwanta a nan tunda d'akin ku ba a gyare yake ba gobe sai ku gyara," suka ce "Toh Abba,"



Kwanciya suka yi dama kafin su baro gidan Kamis sai da suka yi sallah haka suka yi bacci cikin farin ciki haka ma Abba shima bacci ya yi cikin farin cikin dawowar 'yan ukun sa.


Washe gari tun asuba da suka tashi basu koma bacci ba suka fita k'aton tsakar gidan su suka fara gyara shi sai da suka fara gyara d'akin su mai d'auke da k'atuwar katifa da ledar tsakar d'aki da labulaje masu kyau haka ma bedsheet d'in Mai kyau ne har da rishow a d'akin Wanda duk abinda ke d'akin Sadam ne ya shiya musu dan ma wasu abubuwan Kawu Bala Yana k'wacewa shi da matar sa.



Tsaf suka gama gyara d'akin sannan suka tsafta ce ko ina a gidan tsakar gidan su ya yi fess duk da ba suminti bane amma ya yi kyau.

Suna gamawa suka yi wanka suka shirya cikin 'yan kati riga da skirt dama 'yan uku akwai tsafta Sabeeha da Sabreen suka d'auki Hijabi sannan Sabeeha ta kalli Sameeha ta ce "Sameeha dear na ga akwai kananzir a cikin rishow d'in mu ki d'ora mana ruwan shayi bari muje shagon shazali mu siyo kayan had'awa," Sameeha ta ce "To sai kun dawo," suka fita.



Tunda suka fita ake kallon su kowa da abinda yake cewa domin d'auka ya yi 'yan uku sun tafi yawon karuwanci Kai tsaye shagon suka je suka siyi kayan shayi suka tafi gida ba tare da sun lura da kallon da mutanen k'auyeb ke yi musu ba saboda su dama ko k'awaye ba su da su rayuwar su kawai suke yi su uku abinsu.



Da sallama suka shiga gidan Abba da Sameeha suka amsa musu k'arasawa wajen Abba dake zaune kan tabarma k'ark'ashin bishiya suka yi suka gaishe shi tare da yi masa ya jiki ya amsa cikin fara'a sannan suka je suka had'awa Abba tea d'in suka Kai masa ya ce "Allah ya yi muku albarka," suka ce "Ameen Abba," sannan suma kowacce ta had'a nata suka sha bayan sun gama suna zaune wajen Abba suna fira kawai sai tsintar kawu Bala suka yi a kansu sai huci yake yi da alama a zuciye yake.



Gaishe shi suka yi ya musu kallon banza sanna cikin masifa ya ce "Wato Dan uwar ku shine ku ka sake gudowa to bari kuji na fad'a muku nan da sati d'aya zan aurar da ku shegu 'yan iska," shiru suka yi har Abba ba Wanda ya ce uffan.



Mtswww ya ja tsaki sannan ya ce "Ina kud'in da ku ka zo da su ku bani nan," Sabeeha ce ta yi k'arfin halin cewa "Mu bamu zo da kud'i ba,"

"Dalla can rufe mun baki dama ai ke kinfi kowa rashin kunya to wallahi bari kuji kafin naje na dawo ku fito mun da su idan ba haka ba na lahira sai ya fi ku jin dad'i," Yana gama fad'in haka ya fice yana masifa.

Bai dad'e da fita ba 'yar sa Zainabu ta shiga tasha kwalliyar irin tasu ta k'auyawa ko kallon Abba bata yi ba balle ta gaishe shi ta ce "Karuwai ashe yawon iskan cin babu riba kenan tunda har gashi an dawo Wallahi anji kunya Uban ma da yake kamar mai hankali Amma ya kasa hana ku," tashi Sabeeha ta yi ta je gaban Zainabu ta ce "Au Wai kina nufin naki uban bai gaya Miki inda muka tafi ba to ai shine kawalin mu," Zainabu ta ce "Ki ka zageni?"


"An zage ki d'in ki yi abinda zaki yi," duka Zainabu ta kaiwa Sabeeha dama haka Sabeehan

Please Login or Register in order to submit comment