Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dawowar sa kenan daga masallaci ya yi wanka amma yana zaune ya zurfafa a aikin nasa ji yake kamar a daren nan ya tafi k'auyen ya duba da kansa wani Abu ya tsaya masa a k'irji yak'i tafiya.



Wayar sa ce ta katse masa tunani hannu yakai ya d'auka ya kara a kunne daga can Ummi ta ce "Son kazo yanzu zamu yi magana," a hankali ya ce "To Ummi," ta ce "Lafiya kuwa na jika haka?"

"Ummi sai dai nazo," yana fad'ar haka ya kashe Kiran ya mik'e ya fita daga part d'in mota ya hau har part d'in Ummi.


Da sallama ya shiga falon ya zauna kusa da Ummi ya ce "Gani Ummi," ya fad'a yana kallon yadda Ummi ke ta faman sha zob'o ta ce "Yawwa dama magana ne akan Mai yima girki," take ya had'e rai baice komai ba Ummi ta cigaba da cewa "Yarinya ce mai hankali sannan da alama ta iya girki bari na kira ma ita ka ganta," girgiza kai ya yi yace "No Ummi kyaleta kawai dai ki samun zan Sha abinda ki ke sha," matsawa kusa dashi ta yi ta Kai masa cup d'in bakinsa ya sha lumshe ido ya yi saboda ba k'aramun dad'i ya yi masa ba k'ok'arin janye cup d'in daga bakin sa Ummi ta yi amma ya rik'e hannunta gam Yana girgiza kai kamar k'aramun yaron da uwar sa zata janye masa abincinsa.



Sai da ya shanye tass sannan ya ce "Ummi wannan abun ya yi dad'i waye ya yi?" Hararar wasa ta yi masa ta ce "Mai girkin ka mana," jinjina kai ya yi ya ce "Da alama ta iya ko da yake bari gobe naji kar naje wannan abun kawai ta iya," ya fad'a ko a jikinsa Ummi ta ce "Wai ni kuwa Mai yake damun ka?" Langab'ar da Kai ya yi ya ce "Ummi Wallahi Ina sonta kullum tunaninta nake yi har mafarkin ta nake yi na rasa yadda zanyi Ummi Wallahi Ina sonta a Ina zan ganta," ajiyar zuciya Ummi ta sauke cikin tausayin d'an nata ta ce "karka damu yarona insha Allahu zaka same ta okay? Gyad'a kai ya yi yana jin sabon tunanin yarinyar dako sunanta bai saniba na zuwar masa haka sukai ta fira da Ummi sannan ya yi mata sallama ya tafi.


Washe gari tunda safe da su Sabeeha suka tashi basu koma bacci ba gyaran gidan suka fara suka gyara ko ina fess sannan suka yi wanka suka shirya cikin dogayen riguna na material red sunyi kyau sannan Sabeeha ta nufi kitchen ta fara tunanin mai zata girka masa ne domin bata saniba ko wanne kalar abinci yafi so ba.



Wata zuciyar ta ce Kinga gidan ba abinci kala d'aya suke yi ba ki yi masa biyu dole idan wani bai yi masa ba wani zai yi masa.



Feraye doya tayi ta yi doya da kwai da tasha attaruhu da kayan had'i sannan ta yi kunun gyad'ar da yasha madara ta zuba a plask sannan Kuma ta yi wata k'warya-k'wayar white rice da miyar hanta sannan ta dafa ruwan tea da ya sha kayan k'amshi sannan ta yi chips.



Tana gamawa ta Kai komai daining sannan ta je ta gyara kitchen d'in sannan ta fita falo lokacin har su Ummi sun fito saboda Ummi zata fita office har k'asa ta tsugunna ta gaida Ummi ta amsa cikin fara'a tare da yi mata Sannu da aiki.



Ummi ta ce "Ai daga jin k'amshin girkin ki nasan son zai yaba bari na kira shi yazo ya yi breakfast d'in," ranar kam breakfast d'insu daban dan d'akin Rinaz suka tafi Ummi bata hanasu ba saboda ganin jiya basu wani sake ba.



Suna tafiya Maleek ya yi sallama a falon yasha kyau cikin shadda light blue ya yi kyau sosai kamar a sace shi a gudu gaida Ammi ya yi su Rinaz suka gaida shi sannan suka tafi daining tare da Rinaz da Fauwaz.


Tunda Rinaz ta bud'e warmers d'in wani daddad'an k'amshin girkin ya daki hancinsa har sai da ya lumshe ido aikuwa ana zuba masa ya ja plate d'in gaban sa ya fara cin doyar lumshe ido ya yi ya bud'e ya ga su Ummi na kallon sa domin jin Mai zai ce.



Bai yi magana ba ya yi sipping kunun gyad'ar nan ma ya ji dad'i kallon Ummi ya yi ya ce "Ummi ta iya girki sosai ba Dan kar nayi k'arya ba sai nace ta fiki iyawa," Rinaz ta ce "Eh Wallahi Yaya Sabeeha ta iya girki," a zuciyar sa ya maimaita sunan domin ya yi masa dad'i sosai.


Ranar kuwa ya ci abinci sosai Ummi ta ce "Bari a kirama ita ku gaisa," ya ce "A'a Ummi ki rabu da ita," ta ce "Shikenan ni bari na tafi office Rinaz ku kula sosai sannan an gyarawa 'yan uku d'akin su zasu iya komawa," ta ce "Tom Ummi," Maleek ya ce "Ummi ni fa yau binki office zanyi," ta ce "To taho mu tafi," tashi ya yi ya bita suka fita.



Da kansa ya ja Ummin tasa yayinda soldier's d'insa suka sa motar su a tsakiya jiniya kawai ke tashi.

A haka suka k'arasa tafkeken asibitin suka nufi office yayinda sojojin sa ke biye da su suka tsaya k'ofar office d'in su Kuma suka shiga kujera ya samu ya zauna ya tafi sana'ar tasa wato tunanin Sabeeha yayin da Ummi ke aikin ta.



Tare suka koma gida da Ummi ya wuce part d'in sa ya yi wanka ya d'an kwanta sai dare sannan ya nufi part d'in Ummi ya ci Abinci Wanda ji ya yi yama fi na safiyar dad'i har santi ya ringa yi Ummi na masa dariya.



A k'auye kuwa Kawu bai je gidan ba sai ana gobe d'aurin aure amma sai ya ga wayam ba kowa sai Abba Nan ya tambaye shi 'yan uku Abba ya ce shima baisan inda suka tafi ba aikuwa ranar Abba ya ga ruwan bala'i domin daga yaran har shi sun sha zagi shi dai Abba shiru ya yi baice komai ba har Kawu ya gama masifar sa ya kad'a riga ya tafi bai dad'e da tafiya ba aka je aka kwashi akwatin Dauda Dana faruk ya yinda aka bar na Sadam domin Kawu so yake idan sadam d'in ya je su rarrashe shi ya auri Zainabu sai dai tunda suka gayamasa buk'atar su ya ce shi Sam bai yadda ba hakan yasa Lantana ta je wajen boka aka yi mata asiri har Sadam ya dawo duk duniya Zainabu kawai yake so ya ce shi a satin a d'aura musu aure amma kawu yak'i amincewa wai sai nan da wata d'aya zuwa lokacin sun shirya haka sadam ya hak'ura.
[10/25, 7:37 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️


RUBUTAWA DAGA
HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ)




SADAUKARWA GA
MY DAUGHTER SABEEHA
BILKISU Z.YA'U (🅱️K)
AISHA MAGAJI DABO (AMA)



Page 7

Sabeeha ce a kitchen tana girkin dare ya yinda tabaro Sabreen da Sameeha a d'akin su kasancewar su ba wani aiki da suke yi a gidan gashi Sabeeha ta ce bata so su bita su hanata aikin ta yadda ta kamata.



Falo ta fita lokacin Shigar Nasreen falon kenan zama ta yi sannan ta aikawa da Sabeeha wani banzan kallo ta ce "Ke zonan," Sabeeha a zuciyar ta ta ce wannan fa daga Ina tab'e baki Sabeeha ta yi ta k'arasa gaban Farida ta ce "Gani," harara Nasreen ta aika mata ta ce "Baki iya gaisuwa bane?" Banza Sabeeha ta yi kamar bata ji me Nasreen ta fad'a ba.



Jinjina kai Nasreen ta yi ta ce "Dan uwar ki ba magana nake miki ba?" Sai lokacin Sabeeha ta yi mata wani kallon karki k'ara sannan ta yi k'wafa kawai.



Cikin fushi Nasreen ta ce "Ke!! Kece mai yiwa mijina girki?" Sai lokacin Sabeeha ta ce "Waye mijin naki?" D'an cije baki Nasreen ta yi ta ce "Ya Maleek,"



Shiru Sabeeha ta yi kamar mai tunani sannan ta ce "Waye Maleek a gidan nan?" Bata ankara ba ta ji an zabga mata mari dafe wajen Sabeeha ta yi domin jin bak'on abu a fuskar ta tuni ta ji wani bak'in ciki a zuciyar ta saboda a rayuwar ta ta tsani a mare ta aikuwa tana d'aga kanta itama ta tsinkawa Nasreen mari.



A idon su Sabreen komai ya faru da sauri suka k'arasa Sameeha ta ce "Subhanallah Sabeeha dear Mai ya faru?" Ko kallon su bata yi ba ta yi wucewar ta kitchen tabar suna bawa Nasreen hak'uri ita Kuma tana cewa "To Wallahi yau sai kunbar gidan nan tunda bana Uban ku bane Kuma sai kinyi regretting marina da kikayi banza ye kawai daga ke har wad'an da suka kawo ki gidan nan," Rinaz dake gefe ta ce "Ke Wallahi karki kuskura ki zagar mun mahaifiya idan ba haka ba sai kin gane kuren ki Wallahi an gaya Miki kowa irin ki ne da baisan darajar iyayensa ba?" K'wafa Nasreen ta yi ta fita.



Sabreen ta ce "Rinaz waccan d'in wacece?" K'wafa Rinaz ta yi ta ce "Matar Yaya ce," zare ido suka yi suna kallon ta ganin yadda ta yiwa matar yayan nata ita kuwa ko a jikin ta ta haye stairs su Kuma suka nufi kitchen suka samu Sabeeha sai aikin ta take yi amma lokaci zuwa lokaci ta yi k'wafa.



Kallon su Sabreen ta yi ta ce "Meye ku ke ta wani kallona ku yi tambayar ku mana," aikuwa har suna had'a baki wajen tambayar ta Mai ya had'a ta da Nasreen bata b'oye musu komai ba ta fad'a musu ta ce "Kuma wallahi sai tasan ta taroni fad'a," Sameeha ta ce "Sabeeha dear Dan Allah karki fara kinga ba dad'ewa a gidan nan muka yi ba kar a fara haka damu Kuma matar fa Wanda kika zo gidan nan domin sa ce,"

"To sai me dan matar sa ce to ko shine ya yi mun ba rabuwa zanyi da shi ba balle wata matar sa danni bazan d'auki iskan ci ba Wallahi,"



Nasreen kuwa tana fita direct part d'in Maleek ta nufa yana zaune akan kujera Yana waya da Umar ta shiga falon tana kuka ta zauna gefen sa tana sharar hawaye kallon ta ya yi sannan ya ce "Umar Ina zuwa," daga haka ya katse kiran ya ce "Lafiya maiya faru?" Cikin kuka ta ce "Ya Maleek part d'in Ummi naje shine na samu wata Wai ita mai yi ma girki dan kawai na tambaye ta ita ce mai yima girki da ka fad'a mun shikenan Nasreen ta fara yimun gori wai ban iya girki ba ita kuma yarinyar hadda marina," ya ce "What mari fa ki ka ce?" Matsawa kusa da shi ta yi tana nuna masa wajen aikuwa ya ga shatin yatsun Sabeeha domin ba k'aramun mari tasha ba.



Take ran Maleek ya b'aci akan me wata can 'yar aiki ta zo har gida Kuma harta marar masa mata jinjina kai ya yi ya ce "Shikenan kwantar da hankalin ki zan d'auki mataki a kansu," wayar sa ya d'auka ya kira number d'in Rinaz tana d'agawa ya ce "Ku zo yanzu Ina son ganin ku ke da wacce ta mari Nasreen," Yana fad'in haka ya katse kiran bin wayar da kallo Rinaz ta yi sannan ta sauka down stairs ta samu Sabeeha na jera abinci a daining ta ce "Mata Sabeeha zo muje," Sabeeha kuwa warware mayafin blue black d'in doguwar rigar jikin ta ta yi ta yafa shi sannan ta ce "Muje," Sabreen ta ce "Au abin ba gayyata?" Rinaz ta ce "No ku zauna nasan yanzu Ummi zata dawo," suka "Ok," su Kuma suka fita.



Suna tafiya Sabeeha ta ce "Nasan k'ara aka kaimu ko?" Dariya Rinaz ta yi ta ce "Eh mana yaya ke neman mu," Daram gaban Sabeeha ya fad'i amma ta dake bata ce komai ba.



Sojoji suka tarar a bakin k'ofar sai dai basu hanasu shiga ba Rinaz na gaba Sabeeha na binta a baya a kwance suka same shi idanunsa a lumshe hoton fuskar yarinyar kawai yake gani sanye yake cikin red t-shirt da red 3Quater gefe Kuma Nasreen ce zaune idanunta sun yi jajir ko kallon ta basu yi ba Rinaz ta ce "Yaya gamu," ba tare da ya bud'e idanunsa ba ya ce "Ku zauna a nan," Zaman suka yi Sabeeha ta b'uya a bayan Rinaz domin kallo d'aya ta yi wa Maleek ta ji gaban ta na fad'uwa take ta ji tsoron sa ya kamata gashi kamar aljani saboda kyau ga jajayen kayan sunyi masa kyau sosai ga wani k'amshi da ya daki hancin ta Wanda bazata tab'a manta shi ba.



Tashi zaune ya yi fuskar sa a matuk'ar had'e ya kalli Rinaz ya fara balbale ta da fad'a "Dama baki da hankali bansani ba ashe bakya amfani da ilimin ki to tsaya ke iya abincin ki kayi da har zaki dinga yi mata gori akan bata iya abinci ba," Rinaz ta bud'e baki da niyyar yin magana ya ce "Wallahi karki kuskura kice zaki yi mun magana a nan to ita mai marin na ta sai tabar gidan nan na hak'ura da cin girkin nata," magana yake you hankali yana yatsina.



Sannan ya ce "A yau kuma a yanzu subar gidan nan saboda bazan lamunci wulak'anci ba domin ita matata ce," ku tashi kubar nan Rinaz na hawaye ta ce "Dan Allah Yaya kayi hak'uri Wallahi ba laifin Sabeeha bane," kallon da ya watsawa Rinaz d'in ne yasa ta yin shiru Sabeeha kuwa a zuciyar ta ta ce Lallai ne mai mata mu ai bamu da mai kare mu amma ko ba komai ka ji me ya had'a mu da ita.



Ai take ran Sabeeha ya b'aci ta mik'e ba juya ta yi hanyar fita daga falon tana tunanin ai yanzu yanzu zasu bar gidan dama ai ba yanzu aka saba korar su a gidan aiki ba akwai gidan ma da ranar da aka kaisu suka barsa ballantana wannan sunyi sati d'aya.



Tana fita part d'in Ummi ta nufa tana shiga su Sabreen suka tare ta suna tambayar ta maiya faru ta ce "Ku had'a kayan ku yanzu mu tafi," Sameeha ta ce "What ina zamu je?" Tsawa Sabeeha ta daka musu ta ce "Mu tafi nace!!," Ba b'ata lokaci suka had'a nasu ya nasu suka fita daidai lokacin Rinaz zata shiga part d'in domin gudu ma ta yi Dan kar su tafi ganinsu janye da akwatunan su ta ce "Dan Allah karku tafi ku zauna," Sabeeha ta ce "Kiyi hak'uri Rinaz amma dole mu tafi saboda yace lallai a yau mubar gidan nan," Rinaz ta share hawaye ta ce "Naji amma ina ne gidan ku?" Sabeeha ta ce "Mu ba a garin nan muke ba zamu koma garin mu ne dama k'addara ce ta rabo mu da mahaifin mu mahaifiyar mu dama tun muna yara aka nemeta aka rasa yanzu ma mun baro gidane saboda auren dolen da Kawu zai yi mana munzo ne domin idan komai ya lafa mu koma wajen mahaifin mu da yanzu bamu san halin da yake ciki ba iya haka mun gode da taimakon ku idan Ummi ta dawo kice mata mun tafi," kuka Rinaz ta fashe da shi ta ce "Dan Allah kuyi hak'uri yanzu idan Kun tafi Ina zaku," Sameeha Mai saurin yin kuka tuni ta fara ta ce "mu ma bamu saniba," k'arasawa gaban su ta yi ta ce "Akwai wata k'awata iyayen ta suna k'asar waje ita Kuma tana gidan auntyn ta Dan Allah kuje can kunga yanzu dare ya fara gobe sai ku tafi zan sa a kaiku can zanyi mata waya," girgiza kai Sabeeha ta yi ta ce "A'a Rinaz kar mu sake jawo Miki wata matsalar," daga haka ta ja trolley d'in ta dakyar Rinaz ta lallab'a su suka yadda tasa driver ta ce ya kai su gidan su dija.



Sai da suka tafi sannan ta kira dija a waya ta sanar mata sannan ta shiga gidan ta zauna a kan kujera ta saka kuka domin wani tausayin 'yan uku ne ya kamata ga wata shak'uwa da suka yi kamar sun shekara biyar tare tana wannan halin falon ya d'auka Fauwaz is open the door.


Yana shiga ya samu Rinaz sai kuka take yi ya k'arasa da sauri ya ce "Rinaz lafiya me aka yi Miki?" Wani kukan ta fashe da shi ta ce "Bro yaya ne ya kori 'yan uku," a razane ya kalle ta ya ce "Ya kore su fa kika ce?" Ta gyad'a kai.



Shiru Fauwaz ya yi Yana jin ba dad'i har cikin zuciyar sa basu ji shigowar Ummi ba kawai sai ji suka yi ta ce "Lafiya kuwa mamana?" Rungume Ummi Rinaz ta yi ta ce "Ummi yaya ya kori su Sabeeha," take gaban Ummi ya fad'i domin ji tayi kamar an raba ta da wani abu nata Mai matuk'ar muhimmanci ta ce "What! Yanzu Ina suka tafi," shiru Rinaz ta yi zama Ummi ta yi tare da zaro wayar ta daga hand bag d'in ta ta kira wayar Maleek yana d'agawa ta ce "Yanzu kazo Ina son ganinka," tana fad'ar haka ta katse kiran.




Tashi ya yi ya tafi Kiran Ummin tunda ya shiga falon Ummi ke binsa da wani irin kallo gefen ta ya zauna ya ce "Ummi gani," ta ce "Meyasa ka kori su Sabeeha?" Fad'a musu abinda Nasreen ta fad'a masa ya yi.


Ummi ta kalli Rinaz ta ce "Meya faru mamana nasan ba haka abin yake ba haka kawai Sabeeha bazata mari Nasreen ba," Rinaz na hawaye ta ce "Ummi Nasreen ce ta shigo bakya nan sai Sabeeha shine tace mata Wai dan uwar ta bata iya gaisuwa ba sai Sabeeha ta yi shiru shine Nasreen ta ce Wai ita ce mai yiwa mijin ta girki shine Sabeeha ta ce Waye mijin nata kusan ita bama ta tab'a ganin Yaya ba shine fa Nasreen ta mare ta ku duba lamarin ba fa abinda akayi mata shine itama Sabeeha ta rama shine muka rabasu shine Nasreen tace sai su sabeeha sunbar gidan nan shine ta ce musu banzaye dasu da Wanda ya kawosu Ni Kuma nace karta sake tasa Ummi ciki shikenan fa tace ta fad'awa yaya k'arya da gaskiya," dafe Kai Maleek ya yi a hankali ya furta ya "Ya ilahi," Yana jin dama bai kore ta ba ya fara jin Mai ya had'asu sai dai shatin yatsun da ya gani a fuskar Nasreen ne ya tunzura shi.


Ummi ta ce "Son ka ga irin ta ko Wallahi yaran nan babu ruwan su suna da girmama na gaba da su basu da raini," Fauwaz ya ce "Wallahi kuwa Ummi ni kaina suna burgeni," Ummi ta kalli Rinaz da har lokacin kuka take ta ce "Yanzu Ina suke?" Nan ta basu labarin abinda Sabeeha ta fad'a mata dangane da rayuwar su.




Ummi har hawaye ta yi gaba d'aya tausayin su ya kama su Maleek kuwa tunda Rinaz ta fara magana yake kallon ta saboda ya tausaya musu jin za ayi musu auren dole a zuciyar sa yace kamar dai ni da Uncle ya yi mun amma nasu daban ne domin ko uwar da zata rarrashe su bata kusa.



A hankali ya ce "Ummi dan Allah kuyi hak'uri duk bansan da haka ba amma insha Allah zansa a nemo su Ina son hoton su," Ummi ta ce "Mamana akwai hoton su?" D'aukar wayar ta ta yi ta ce "Eh akwai video d'in da nayiwa Sabeeha tana yin girki," ta fad'a tana mik'awa Maleek wayar.



Karb'a ya yi ya Kai idanunsa kan wayar saurin mik'ewa ya yi Yana k'urawa wayar ido gani yake ko dai gizo idanunsa ke masa murza idon ya yi Yana kallon ta tana girki tana murmushi saurin juyawa ya yi da sauri yabar falon da kallo su Ummi suka bishi har ya fice.




Yana fita ya k'walawa Salman kira yana zuwa ya ce "Ku kawo motoci," motocin aka kawo aka bud'e masa ya shiga sannan suka bar gidan sai jiniya ke tashi wajen mota ashirin suka fita neman 'yan uku.



Ya yinda Maleek ta lumshe idanunsa hoton fuskar ta kawai yake gani yana jin meyasa ya aikata hakan ashe dama ita ce a gidan su take masa daddad'an girki bai saniba bud'e idanunsa ya yi Yana k'ara kallon videon sannan ya nunawa Salman ya ce "ita zamu nemo,"



Nan suka fara zagaye garin kaduna suna duba inda zasu hango su Sabeeha amma shiru babu su ba alamun su.



Basu suka koma gida ba sai dare a gajiye Maleek ya shiga falon Ummi domin tunanin ta da yake yi ne ya saukar masa da wani irin ciwon kai Wanda bai tab'a tunaninsa ba domin Maleek yana d'aya daga cikin masu barin abu a rai abu kad'an sai ya hana shi sukuni.



Yana shiga falon Rinaz ta mik'e da sauri ta ce "Yaya an same su?" Girgiza Kai ya yi sannan ya zauna kusa da Ummi gaba d'aya ya rasa nutsuwar sa ganin halin da ya shiga Ummi ta ce "Son lafiya kuwa?" Kallon Ummi ya yi da idanuwan sa da suka yi jajir ya ce "Ummi bamu same ta ba Ummi ita ce ita ce Wacce zuciya ta take so ita ce Wacce tunanin ta ya hanani sakewa," ya fad'a kamar zai yi kuka.



Ummi ta ce "Ita ce wa?" Ya ce "Ummi ita ce Wacce nagani waccan lokacin a waccan k'auyen yanzu a Ina zan ganta sonta ya yi mun kamun da ban tab'a tunani ba," cikin Mamaki da tausayin d'an nata ta shafa kansa ta ce "Nasan kana sonta tunda har ka iya furtamun domin nafi kowa sanin yarona idan har ya furta Yana son abu to ba k'aramun so yake wa abun ba dan haka ka kwantar da hankalin ka har zuwa lokacin da za a gansu," noding kansa ya yi yana jin idan ba a ganta ba zai shiga wani hali.



Har Rinaz ta bud'e baki da niyyar fad'in inda suke sai Kuma ta yi shiru a zuciyar ta tana fad'in ashe dama ita Yaya ke matuk'ar so aikuwa sai na wana shi kafin yasan inda suke.



Karb'ar wayar ta ta yi ta haye stairs ta kira dija a waya daga can Dija ta ce "Beb yane nagode da kyautar k'awaye masu shiga rai," dariya Rinaz ta yi ta ce "Ya suke to?" Dija ta ce "Normal ga Sabeeha a nan Sabreen da Sameeha na tare da aunty a kitchen," jinjina kai Rinaz ta yi ta ce "Yawwa ba Sabeeha wayar," karb'a Sabeeha ta yi ta ce "Hello Rinaz dear," Rinaz ta ce "Yes kina jina ba Ummi ta dawo taji mai Yaya ya yi sannan bata ji dad'i ba haka ma yaya Fauwaz amma kinsan me sharri Nasreen ta yi mana wajen yaya sannan na fad'a masa abinda ya faru yanzu haka baki ga damuwar da ya shiga ba bai dad'e da dawowa daga neman ku ba amma ban sanar da kowa nasan inda ku ke ba Dan haka ku zauna a nan har saina wana Yaya," murmushi Sabeeha ta yi ta ce "To ba damuwa ya Ummi fa?" Rinaz ta ce "Tana lafiya sai dai tana cikin damuwar rashin ku," murmushi Sabeeha ta yi tabbas tasan Ummi Mai k'aunar su ce.


Da haka suka yi sallama Rinaz kuwa ba ta fad'a wa Sabeeha komai akan budurwar da yake so ba saboda tasan zuciyar Sabeeha cike take da haushin Maleek idan ta fad'a mata ma ba lallai su koma gidan domin zata iya tunanin dan yana sonta ne shiyasa ya matsu su koma sannan Kuma ba ta da tabbacin Sabeeha ya gani a k'auyen may be Sabreen ce ko Sameeha domin tasan Yaya Maleek bai tab'a ganin ko d'aya a cikin su ba.




Ranar Ummi da Fauwaz basu rintsa ba balle Kuma oga Maleek domin tunda ya yi wanka ya yi sallah ya kwanta saman gadon sa ya fad'a tunanin yanzu idan ba a ganta ba ya zai yi haka ya yi ta tunani gashi Nasreen ta dame shi da kira Amma ya k'i d'agawa domin wani mugun haushin ta yake ji domin duk ita ta ja komai ranar dai inda ya ga rana haka ya ga dare ko da Asuba da ya yi Sallah bai iya yin baccin ba addu'a kawai yake yi Allah ya bayyana ta sai dai zuwa lokacin shima ya fara karaya akan idan ma ta dawo dakyar ta so shi saboda yasan cewar yanzu haka haushin sa take ji.



Yana zaune har gari ya yi haske wanka kawai ya yi suka k'ara fita neman su ba tare da ya ko

Please Login or Register in order to submit comment