Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kafin ta sauka take jiyo hayaniyar su.




Tana fara sauka duk suka juya suna kallon ta Sabreen Kalli su Hanfa da tun zuwan su da Rinaz suke tambayar amaryar Maleek ta ce "To ga amaryar Yaya MG can saukowa," da gudu Haneefa ta je ta rungume Sabeeha ta ce "Nice to meet you sweetheart," kallon ta Sabeeha ta yi ta ce "Nice to meet you too," sannan ta kalli Hanfa da ta tsaya tana kallon ta tabbas wannan ita ce na gansu a asibiti tare da wacce ta rungumi Ya maleek kenan wannan ce Sabeeha ta fad'a a zuciyar ta tana kallon Haneefa.




Bata gama tunani ba Hanfa ta rungume ta ta ce "Gaskiya naji dad'in had'uwa dake sis hany Kinga wata kama a tsakanin su kamar mutum d'aya?" Haneefa ta ce "I see sis Hanfa I'm very surprised kamar ma ta b'aci," d'an murmushi Sabeeha ta yi sannan ta ce "Mu k'arasa," suka koma cikin falon suka zauna.




Hanfa ta ce "Ya MG yace kinyi fushi muna baki hak'uri a madadin sa," murmushin yak'e ta yi ta ce "No bakomai," Haneefa ta ce "Ni sunana Haneefa wannan Hanfa mu yaran Aisa ne k'anwar Ummin Ya MG," jinjina kai Sabeeha ta yi a zuciyar ta kuwa ta ce na jinjinawa surutun ku.



Rinaz ta ce "Sabeeha dear ki taya mu zab'a mana wannene ya dace da Kamu da Kuma dinner?" Kallon kayan Sabeeha ta yi sunyi matuk'ar kyau sai walwali suke yi daga gani kaya ne masu tsada materials ne d'aya pich color d'aya kuma dark green sai walwalin silver color d'in zaiba suke yi.



Sabeeha ta ce "Pich d'in na kamu green Kuma na dinner duk da silver head ya yi?" Dija ta ce "That's my Sabee abinda nake fad'awa babes d'in nan kenan Kinga wannan milk d'in less d'in ranar dinner d'in su Ummi da suka had'a tare da Maman ya Umar then wannan dark blue material d'in kuma ranar d'aurin aure bayan munsa wannan atamfar a lokacin walima da yamma tunda already dama wannan shaddar da safe zamu sa lokacin d'aurin aure," tafi wajen ya d'auka jin tsarin Dija ya yi Sabeeha kuwa shiru ta yi tana jin ikon Allah anko wajen kala biyar sannan ko wanne d'aya a ciki ya haura 20k kallon Zainabu dake can gefe ta yi ta yi tsuro tausayi ta bata amma ta basar.





Doctor ce ta yi sallama a falon suka amsa suna yi Mata sannu da zuwa Hanfa da Haneefa kuwa har da zuwa su rungume ta domin su haka suke sun saba suka gaishe ta ta amsa cikin fara'a sannan ta wuce bedroom d'in ta.





Haka aka cigaba da gudanar da hidimar bikin 'yan uku kullum su Rinaz suna gidan su Sabeeha suna shiri Sabeeha kuwa fushi ta yi da Maleek ko wayar sa bata d'agawa hakan ya damu Maleek amma ya basar a zuciyarsa yana fad'in Zaki zo hannu ne yarinya saura k'iris.


Ummi tare da Aisa mamar su Hanfa da momyn Umar da maman Salman ne suka shirya suka tafi Dubai Landon domin had'o lefen 'yan uku.




Aikuwa lefe suka had'o nagani na fad'a lokacin da suka dawo suka samu gida cike da dangi da 'yan uwa haka ma gidan Doctor gidan a cike yake da K'awayen Doctor duk da ba babbar k'awar ta wato Ummi kasancewar itama tana can da nata bak'in sannan 'ya'yan Kawu Bashir ma sunzo da yaran su 'yammatan duk suna wajen 'yan uku.





Ana saura kwana biyu a fara biki ranar Aisa da Umman Salman tare da wasu daga cikin dangin Ummi suka tafi kai lefen 'yan uku tarba mai kyau su Doctor suka yi musu a babban falon gidan akwatuna aka fara shigarwa cikin falon tun ana k'irgawa har aka dena domin yawan su akwatunan kala biyu ne maroon guda ashirin da hud'u haka ma pink d'in ashirin da hud'u abu sai Wanda ya gani ana haka masu Kawu lefen Sameeha ma suka isa da akwatunan su suma ashirin da hud'u su Kuma kalar coffee haba nan fa aka rasa Wanda za a gani domin kaya ne na gani na fad'a masu matuk'ar tsadar gaske ga sark'ok'in cikin akwatunan daga na gold saina diamond hakama agogunan ciki Kai Abu ba a cewa komai haka 'yan kai lefen suka tafi suna tambayar amare domin suna san ganin su sunji ance 'yan uku ne Doctor ke sanar musu ai suna Salon suka ce bakomai zasu had'u idan aka fara shagalin bikin haka suka tafi suna yaba halin karamci na Doctor.




Haka ma su Doctor suke yaba dangin Ummi da su Umar da Kuma yaba kayan abinda basu saniba duka akwatunan 72 Ummi ce tayi musu da duk wani Abu da aka gani a ciki duk Ummi ce ta siya a cewar ta ai lefe ita ya kama domin zata aurar da yaranta wad'an da daga su bata da wasu wad'anda zata had'awa sai dai ita a kawo mata idan bikin Rinaz ya tashi sannan tana matuk'ar ji da yaran nata maza sannan tana son 'yan ukun ta domin 'ya'ya ne a wajen ta Dan haka dole ne ta had'a musu kaya na gani na fad'a domin su yan gata ne sannan kuma gasu surukan ta dan haka ba sisin su Maleek duk ita ta fitar da kud'in abu d'aya tasan Maleek ya yi shine ya bada car keys guda uku da Kuma sababbin wayoyi iPhone 12 pro max guda uku an saka a kowacce akwatu.





Lokacin da su Doctor suka ga car keys mamaki ne ya cika su su gani suke yi abin Kuma yayi yawa har da motoci abinda basu sani ba shine motocin ma suna waje da su ake tafe.




'yan uku suna shiga gidan idanun su ya sauka akan motocin da suke ta kyalli suna sauka direct wajen motocin suka nufa Sabreen ta shafa farar ta ce "Wayyo Allah amma fa motar nan ta ware da tunanina Dan Allah kalli Sameeha dear," dariya Sabeeha ta yi ta ce "To da tayi kyan ai ba taki bace ni Kinga wannan maroon d'in ce tayi gabas da hankalina," dariya suka shek'e da ita Aysha ta ce "A lallai ne ai dama best color naki ne maroon," Sameeha ta ce "Nima ai ga best color na nan ta fad'a tana shafa bak'ar motar," Rinaz ta ce "Kunga kubar wannan abun mu shiga ciki," Hanfa ta ce "Gaskiya nabi zab'in ki anty," Haneefa kuwa ta kalli Sabeeha ta ce "Ni kuwa na dangwalawa zab'in ki sweetheart," Sabeeha ta ce "Nagode," Dariya Dija ta yi har da rik'e ciki ta ce "Na jinjinawa shashancin ku Wallahi especially you 'yan uku babes ya daga ganin motar mutane may be bak'i Mama ta yi su Sabeeha dear har da godiya," Dariya suka kwashe da ita suka shige falon.





Suna shiga falon ya d'auki gud'a su Lantana ne gaba wajen rangad'a gud'a Doctor ce ta lek'o da waya a kunnen ta ta ce "Aminan Abba kuzo nan," d'akin suka nufa yayin da su Rinaz kayan lefen suka yi gabas da tunanin su sai kalla suke yi.




Suna shiga lokacin Ummi ke cewa "Haba Aysha kayan sunyi yawa," daga can Ummi ta yi magana amma basa ji Mama ta ce "To shikenan sai anjima," ta katse wayar ta kalle su ta ce "Yanzu ba sai anjima ba maganin da na baku d'azu kuje ku shanye tun kafin ranku ya b'aci aina duba naga baku sha ba," tuni kowacce ta had'e rai sai kumbure kumbure suke yi suka juya zasu fita.



Doctor ta ce "Baku jiba ga lefe can ankawo yanzu muka yi waya da Aysha ta sanar mun ke Sabreen maroon ne naki mayyar Maroon ke kuma Sabreen pink d'in ne naki Sameeha ke Kuma cofee d'in sannan haka ma motocin dake waje Aysha ta sanar mun kowacce da tata basai nayi muku bayani ba kowacce tasan tata domin kowacce tasan zab'in ta," ihu suka saki suka rungume Doctor suna murna.




Doctor ta ce "Kai ni ku cikani Karki yar da ni saura kuma ku fita kuna wannan shashancin cikin mutane Wai ma dama kunsan za a sa muku car keys a lefe?" A tare suka girgiza kai Sabreen ta ce "Ni dai nasan lokacin da muke gidan Ummi mun tab'a fita da my one naga wata farar mota nace ta burgeni har ya tambaye ni inason farar mota ne nace eh," Sameeha ta ce "ni dai tambaya ta ya Umar ya yi Wai meyasa nafi cewa yayi kyau idan yasa bak'ak'en kaya shine nace masa ai shine best color d'ina black and coffee," jinjina kai Doctor ta yi ta kalli Sabeeha ta ce "kefa shugabar 'yan rigima?" Tura baki Sabeeha ta yi ta ce "To nidai bansani ba," doctor ta ce "To kuje," fita suka yi suna ji kamar su je a kalli lefen da su amma ba dama suka wuce zuwa d'akin su.




Rinaz ce ta shiga d'akin ta ce "ga phones d'in ku ku rik'e a wajen ku saboda kar a fasa muku," cikin murna suka k'arbi wayoyin Sabreen ta ce "Rinaz Habibty ashe motors d'in wajen namu ne," Rinaz ta ce "Ai kune baku saniba amma Ina jin sanda Yaya ya yi yawa yace a kawo masa motoci guda uku ya fad'i colors d'in wayoyin Kuma yace duk farare" Sameeha ta ce "Allah ya saka masa da alkhairi," Sabreen ta ce "Wayyo dad'i Allah yabar mana ya MG ya saka masa da alkahiri ya biya masa buk'atun sa," suka amsa da "Ameen,"



A b'angaren Maleek yasha godiya wajen Fauwaz da Umar sannan suka had'u suka yiwa Ummi godiya.




Da daddare su Sabeeha na kwance a d'akin su ta mik'e Sabreen ta ce "Dear sai Ina kuma?" Sabeeha ta ce "Ina zuwa," ta zira hijab d'inta ta fice.



Direct part d'in su Lantana ta wuce da sallama ta shiga falon Zainabu dake kallo ta amsa sallamar tana kallon Sabeeha domin bata gane wacece a cikin su ba tab'e baki Sabeeha ta yi ta ce "Ke wannan kallon fa?" Take Zainabu ta gane Sabeeha ce saboda ita ce take ce ke.



Ta ce "Barka da dare anty," murmushi Sabeeha ta yi ta ce "Yawwa Zainab dama magana nazo muyi dake," ta ce "To anty zauna mana," zama Sabeeha ta yi gefen ta ta ce "Zainab," ta amsa "Na'am,"




Sabeeha ta ce "Kina son Sadam?" Kallon ta Zainabu ta yi ta ce "Amm...," D'aga mata hannu ta yi ta ce "Just answer my question kina son Sadam?" A hankali Zainabu ta ce "Eh anty," jinjina kai Sabeeha ta yi ta ce "Ya matsayin auren ku yake?"



"Cewa tayi na tafi gida," kallon ta Sabeeha ta yi kamar mai yin nazari ta ce "Kina nufin ba sakin ki yayi ba," gyad'a kai Zainabu ta yi.


Ajiyar zuciya Sabeeha ta yi ta ce "To dama ranar nan da ki ka ganmu da my ya yi mun maganar ki sai nake bashi labari shine yace zai yi wani Abu akai Kinga dai ni yanzu aure zanyi Kuma akwai shirin da muke yi ni da shi domin gyara rayuwar ki amma fa sai kinyi hak'uri kin Kuma kawar da kanki da Kuma soyayyar da kike wa Sadam Kinga aike kina son shi sab'anin shi da auren ki kawai ya yi ba don Yana sonki ba sai dan saboda anbi ta wata hanyar Zainab zaman ki haka bai kamata ba shiyasa nake so mu shirya plan d'in Sadam zai so ki fiye da yadda ki ke son sa k koma d'akin ki ko dan Habibi domin yanzu ko aure ki ka sake yi babu lallai ki samu Wanda zai kula da Habibi sama da mahaifin sa amma kamar yadda na fad'a Miki sai fa kin cire soyayyar da kike masa a lokacin ungo wannan wayar na baki ita da ita zamu dinga yin magana dake," karb'a Zainabu ta yi tana hawayen farin ciki ta ce "Nagode anty Allah ya saka da alkhairi,"




Sabeeha ta ce "Babu komai Zainab ai ke kanwata ce duk abinda nayi miki ban fad'i ba ko lokacin da ku ka dawo gidan nan bawai na tsane ki bane har ga zuciya ta tun lokacin na yafe miki abu d'aya ne yasa nake yi miki haka Zainab saboda yadda ki ke gatsa sunan mahaifiyar ki wanda hakan bai dace ba mu kina Kiran mu da aunty amma Kuma mahaifiyar ki ki gatsa sunan ta karfa ki manta itace silar zuwan ki duniya ko kin girmama ta baki biyata ba ke fa yanzu uwa ce baza ki so Habibi ya tashi yana gatsa sunan ki ba Zainab karki zama d'aya daga cikin yara marasa d'a'a da tarbiyya ki zama 'ya ta gari wacce iyayen ta zasu yi alfahari da ita kinji?" A hankali tana hawaye ta ce "To anty insha Allah na dena,"




Sabeeha ta ce "Yawwa Nagode da kika fahimce ni Ina Habibi ko ya yi bacci ne?" Ta ce "Eh ya yi bacci," Lantana da ke jiyo su a d'aki ta fito ta zauna Lantana ta ce "Barka da fitowa Umma," cikin mamaki da jin dad'i ta ce "Yawwa," gaishe ta Sabeeha ta yi ta amsa cikin fara'a ta ce "mun gode Sabeeha Allah ya biya ki da gidan aljanna tabbas ku na daban ne kuna kyakkyawar zuciya Kuma wankakkiya fes saboda duk abinda muka yi muku a baya baku d'auke shi a komai ba Kun rungume mu baku kyamace mu ba mungode," ta fad'a tana share hawaye Sabeeha ta ce "Bakomai inna ai Zainab kanwata ce,"





Kawu dake k'ofar shigowa tun farkon shigar Sabeeha tas yaji maganar da suka tattauna da Zainabu ya shiga da Sallama amsawa suka yi ya samu waje ya zauna Sabeeha ta gaishe shi ya amsa cikin fara'a ya ce "Yarinya ta Allah yayi miki albarka yasa aljanna makomar ki tabbas 'yan uku ku na daban ne a baya har karuwai na Kira ku nayi Shirin yi muku auren dole sannan bayan haka Kuma na kashe miki naki auren amma yau kece ke son 'yata ta yi zaman farin ciki a gidan auren ta sannan ki ke nuna mata hanyar da zata sada ta da aljanna Allah ya raba ki da naki iyayen lafiya ya yi miki albarka," ta ce "Ameen Kawu," tashi Kawu ya yi ya nufi d'akin sa yana share hawaye da babbar rigar sa.




Tashi Sabeeha ta yi ta ce "Inna na tafi sai da safe," daga haka ta fice.





Tana shiga falon su Sameeha ta rungume ta tana murna ta ce "Dear zo kiga kayan da Abba ya siya mana na fitar biki," janta Sameeha ta yi har tsakiyar falon inda kayan suke akwatuna ne guda hud'u manya manya kusa da Sabreen ta zauna ta d'auki wani less maroon mai adon flowers silver color ta ce "Wow Abba angode Allah ya saka da alkhairi ya k'ara bud'i," ya ce "Ameen aminiya," Sabreen ta ce "Abba dama haka ka iya zab'e?"





Cikin farin ciki Abba ya ce "Ai doctor ce ta tayani zab'ar muku su domin Wad'an da ke mun oder nasa suka nemo mun su domin ku kad'ai 'yan ukuna gashi nan kowacce d'aya d'ayar Kuma ta Doctor," godiya suka dinga yi domin kayan kana ganin su kasan kud'i mai suna kud'i akasa aka siya lesses ne masu kyau da atamfofi da takalma masu tsadar gaske da sark'ok'i na gaske ga materials abin ba a cewa komai.





Doctor ta ce "Abban 'yan uku mu k'arasa waccan falon ka ga lefen kuma ku taso domin nasan ko ban gayyace ku ba sai kunzo," tashi suka yi suka je domin ganin kayan yayinda bak'i ke can b'angaren bak'i saboda Abba ya sake da iyalan sa abinku da 'yan boko wayayyu.




Bubbud'ewa suke suna santin kayan.




Wani takalmi Sabreen ta gwada ta mik'e tana kwatanta yadda zata yi tafiya idan tasa dariya sosai Abba ke yi shi da Doctor haka suka dinga sa iyayen nasu dariya Abba kansa yasan zasu yi missing yaran nasu shi da Doctor.





Gajiya suka yi da ganin kayan suka tashi ba dan sun gama gani ba sai dan gajiyar da suka yi dan ko rabin rabi basu yi ba haka suka tafi domin su kwanta.



ana i gobe Kamu Daddy ya Kira Maleek falon sa gaishe shi Maleek ya yi ya amsa sannan ya ce "Son dama dalilin Kiran ka magana ce akan Nasreen d'azu muka yi magana da Yaya domin yanzu ma ta koma d'akin ta," Maleek ya ce "To Daddy,"






Daddy ya ce "Yawwa Son Allah ya yi maka albarka," ya amsa da "Ameen," sannan yabar falon.






'yan uku ne kwance a d'akin su cikin kayan baccin su iri d'aya Sameeha na amsa waya Sabreen na chart Sabeeha kuwa na kallo a laptop sun sha kyau ba k'arya k'afa da hannun su ya d'au kyau da jan lalle da bak'in da akayi musu kansu yasha gyara d'an gaske fatar su sai fitar da shek'i take yi juyi Sabeeha ta yi tayi k'wafa Sabreen ta ce "Dear lafiya kuwa?" K'aramun tsaki ta ja ta ce "Sabreen bansan me Ya Maleek ke nufi dani ba wallahi,"





"Me ya yi miki?" Sabreen ta tambaya furzar da numfashi Sabeeha ta yi ta ce "Ranar da muka je fa hospital ni da Zainab ne muka ganshi,' nan ta basu labarin abinda ya faru kaff Sameeha da ta gama waya tana sauraron ta ta ce "Amma dear ai laifin ki ne meyasa zaki k'i picking calls d'insa bayan kin gano relationship d'insa dasu Hanfa?" Tab'e baki Sabeeha ta yi ta ce "I don't know am only know that Ina matuk'ar kishin sa sannan shi kuma sai bai sake Kira ba," Sabreen ta ce "Ki kwantar da hankalin ki sis ai saura k'iris wai maye ya yi amarya," dariya Sameeha ta yi ta ce "Aikam dai," haka dai suka dinga fira abinsu.
[10/25, 8:48 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️




RUBUTAWA DAGA
HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ)





SADAUKARWA GA
MY DAUGHTER SABEEHA
BILKISU Z.YA'U (🅱️K)
AISHA MAGAJI DABO (AMA)




Page 24


Washe gari suka tashi da shirin yin Kamu hidima ake yi sosai a gidajen guda biyu hakan ne yasa 'yan uku suka had'a abubuwan da zasu yi amfani da shi suka tafi gidan Auntyn Dija.



Fauwaz ne ya shiga falon Ummi tare da Ahmad Ashraf da Abdul_alim sai Usman duk 'ya'yan yayyen Ummi ne maza sa'annin Fauwaz nan dangi suka dinga ga ango ga ango washe baki kawai Fauwaz ke yi abinsa.



Hanfa ce gaban Aisa k'anwar Ummi wato mahaifiyar su tana buga k'afa cikin shagwab'a ta ce "Please Momcy munsan hanya fa ko sis hany?" Haneefa dake zaune gefen Momcy ta ce "Eh Momcy mun iya fa ta fad'a kamar zata yi kuka," Ashraf dake bayan ta kuma shi zai aure ta cak ya d'aga ta ya ajiye ta gefe ya ce "sweet momma karki yadda da wannan yarinyar wai ma akan me ki ke rigimar?" Tura baki Hanfa ta yi tana hararar sa.




Haneefa kuwa wajen Fauwaz ta yi ta rik'e hannunsa ta ce "Please bro kasa baki Momcy ta bamu key d'in motar munfa san hanya,"




"Ke kuwa Hany Ina zaku kuma?" Fauwaz ya fad'a yana kallon Momcy ta ce "To gidan su amare zamu fa," Momcy ta ce "To kwata_kwata yaushe suka san gidan da zasu je su kad'ai?" Alim ya ce "Kai babe's ba inda zaku Sweet momma karki basu," Haneefa ta ce "Hmm zaka sani wlh," d'aga kafad'a Alim ya yi ya ce "Indai ba fasa aurena Zaki yi ba ai shikenan gashi bama wannan ba My hany nasan ku fa bakwa driving a hankali," Fauwaz ya ce "Shikenan amma ai su my heart basa gidan Mama suna gidan su Dija bari nasa Alasan ya kai ku," Jan hannunsa Hanfa ta yi ta ce "To muje kuma babu ni ba wani ehe," ta fad'a tana kallon Ashraf Haneefa ma ta bisu Alim ya ce "My fav inzo na raka ki?" Harara Hany ta zabga masa ta ce "Baza ni da kai ba kuma baram-baram," daga haka suka fice.





"Wallahi MG wani mahaukacin farin ciki nake ji a zuciyata Wai zan mallaki Sameeha,"



"Allah koh?" Cewar MG dake juya wayar sa yana so ya Kira Sabeeha ga Kuma mugun son ganinta da yake yi.



Umar ya ce "Wallahi fa gashi yau wajen kwana biyu bangan ta ba saboda suna busy amma fa yau zan ganta domin na sanarwa da Mummy sai dai a kama mu dukan mu," tab'e baki MG ya yi ya ce "Dama ana kama maza ne?"




"Oho idan ma ba ayi sai a fara ta kanmu," dariya falon ya d'auka Arif yayan Alim ya ce "Gaskiya ne babban ango," Umar ya kalli Aiman yayan Ashraf ya ce "Aiman ya kace," cikin dariya Aiman ya ce "Banga laifin ka ba kuwa,"




D'ayan mai Suna Muhseen yayan su Hanfa Wanda magana ma bata dame shi ba shiru ya yi yana jin su baice komai ba Maleek ya kalli Umar ya ce "Mu kam baza ka ja mana raini ba," suka kwashe da dariya haka suka dinga fira abinsu.





B'angaren 'yan uku kuwa duk zaune suke a wani falo suna fira wayar Sabreen tayi k'ara tana d'agawa ta ce "Angon saura k'iris," daga can Fauwaz ya ce "Haka yake saura k'iris ki zama tawa su Hanfa sunzo nan kuwa?" Ta ce "No basu K'araso ba," ya ce "Aha to suna hanya,"





"Ok to sai sunzo," Sabreen ta fad'a tare da kashe wayar.





Da yamma aka fara shirin zuwa wajen Kamu make up sosai su Dija suka d'auka sannan suka shirya cikin ankon su sunyi kyau ba k'arya zaune suke a falon suna jiran fitowar 'yan uku domin sun dad'e a cikin d'aki make overs d'in da Doctor ta d'auko suna gyara su.



Sun dad'e sosai sannan aka bud'e k'ofar d'akin wani k'amshi ne ya hure falon gaba d'aya Wayyo kuzo ku ga kyau iya kyau wajen 'Yan uku kamar ka sace su ka gudu sunyi kyau sosai cikin shigar dark blue d'in dogayen rigunan code net da suka yi fuskar su tasha make up sosai Nan fa aka fara ruwan hotuna su Dija sai yaba kyan da suka yi suke.





Da haka suka fita suka shiga motocin da aka kawo musu domin zuwa kamu.




Hall d'in da aka kama ya yi kyau iya kyau yasha decoration ko Ina ka kalla kaskon turaren wuta ne da aka zuba turaren ciki gurin sai tashin k'amshi yake yi ga 'yan uwa duk sun hallara ba b'ata lokaci aka fara gudanar da shagali.





A b'angaren su MG kuwa hana Umar zuwa yayi dan dole ya hak'ura.



Haka aka gudanar da Kamu Wanda ya k'ayatar aka tashi bayan daga nan kowa ya koma gida abinsa.


Washe gari da daddare kuwa aka fara shirin party k'awayen amarya sunyi kyau cikin ankon su dark green Mai adon silver hakama head d'in da suka d'aura silver color amare kuwa wedding gown suka sa farare sunyi kyau sosai ba k'arya sai ka rantse mutum d'aya ce saboda tsanin kama.



Hotuna suke yi sosai wayar Rinaz ta fara ringing d'agawa ta yi daga can Fauwaz ya ce "Beb ku fito fa muna waje time na tafiya," ta ce "Ok," kallon su Sabeeha ta yi ta ce "Dear muje suna jira," dukan su suka yi hanyar fita yayinda amare ke tafiya a hankali a haka suka fita har compound d'in gidan nan suka ga motoci reras.



Fauwaz ne ya fito daga bayan wata bak'ar mota yasha kyau sosai cikin farar shadda sai k'amshi yake zabgawa ya kalli Rinaz ya ce "Matar Yaya ga motor d'in da zata shiga can," ya fad'a nuna wata farar Bugatti Hanfa ce ta rik'e hannun Sabeeha har zuwa wajen motar ta bud'e mata back seat a hankali ta shiga motar wani k'amshi ta ji ya daki hancin ta tabbas tasan shine dan haka bata waiga inda yake ba ma ta jingina da jikin kujerar ta lumshe idanunta.




Maleek kam a hankali ya saki wata ajiyar zuciya tare da gyara zaman sa yana k'arewa fuskar ta kallo yana jin wani farin ciki mara misaltuwa a zuciyar sa a jikin ta ta ji kallon ta ake yi lokaci guda ta bud'e idanunta suka had'a ido murgud'a masa baki ta yi tare da d'auke idanunta ta k'ara matsawa can jikin murfin motar.



Murmushi yayi mai sauti wanda yasa dimples d'insa suka lotsa jin sautin murmushin sa ne yasa ta kalli b'angaren da yake sai da gabanta ya fad'i saboda ganin tsanin kyan da ya yi sanye yake cikin farar gizner shadda d'inkin riga da wando da babbar riga ya matuk'ar yin kyau kamar kwana biyun

Please Login or Register in order to submit comment