Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sanar dani hakan dan haka kada ki bari ku dinga had'a idanu da shi sannan baza ki samu damuwa ba saboda yanzu ko magana baya iyawa," gyad'a Kai kawai Sabreen ke yi.


"Yanzu muje part d'in Ummi," cewar Sabeeha ta fad'a tare da rik'e hannun Sabreen suka nufi k'ofar fita.



Nasreen dake lab'e tsahon lokaci ta nufi d'akin ta tana wata shegiyar dariya Jamila ta samu a d'akin ta kalle ta ta ce "Jamila kinsan wani Abu?" Girgiza kai Jamila ta yi ta ce "A'a ranki ya dad'e sai kin fad'a," wata dariyar Nasreen ta yi sannan ta fad'awa Jamila komai ta d'ora da cewa "Kinga yanzu na samu damar gyarawa itama Sabreen zama lallai Sabeeha ta burgeni da ta tsara hakan sannan abinda bata saniba shine idan ta tafi baza ta tab'a dawowa ba sai dai gawar ta," suka shek'e da dariya Jamila ta ce "Meye Shirin ki na gaba ranki ya dad'e?"


"Shirina na gaba shine bana so Umma tasan cewar Sabreen na gidan nan ita da Kawu daga sannan ni Kuma zan koyawa Sabreen hankali daga lokacin da aka kawo gawar Sabeeha su Aysha da Hamza da shi kansa Maleek zasu gane cewar Sabreen ce zaune a matsayin Sabeeha sannan kafin nan sai nasan yadda nayi har Maleek ya yiwa Sabreen ciki Kinga daga nan zaman lafiya ya k'are daga nan Kuma shi kansa Maleek Daddy zai sa a kashe shi har da ma iyayen sa da kowansa Kinga shikenan mu Kuma mu gaje abinda suka mallaka daga nan Daddy ya warke har mu kanmu babu mu ba talauci," ta fad'a tare da tafawa ita da Jamila suka tuntsira dariya.




Sabeeha kuwa ta k'ofar kitchen ta shiga falon Sabreen Kuma ta k'ofar shiga Fauwaz suka samu jikin Maleek yana kuka kamar k'aramun yaro domin bai kawo abin ya Kai haka tsamari ba haka ma Sabreen kukan take yi.


A hankali Sabeeha ta k'arasa falon inda suke kusa da Maleek ta zauna tana kallonsa shima ita yake kallo hawaye ne ya gangaro mata girgiza mata kai ya yi sai tayi saurin goge hawayen ta Ummi dake gefe abubuwa sun dame ta ta ce "Bari na Kira Daddyn ku na sanar masa," a tare Sabeeha Sabreen da Fauwaz suka kalle ta.


Fauwaz ne ya yi saurin cewa "A'a Ummi karki sanar masa domin d'azu muka yi waya da Daddy ya sanar mun cewar akwai aikin da yake yi mai muhimmanci da ya tafi gabatarwa a london idan ki ka sanar masa hankalin sa zai tashi sosai mu bi komai a Sannu," jinjina Kai Ummi ta yi yayin da Sabeeha ta saki b'oyayyar ajiyar zuciya.


"Amma dai na sanarwa Maryam," ta fad'a tare da d'aukar waya ta sanarwa Doctor abinda ke faruwa hankalin Doctor ya tashi sosai Dan ko iya yanayin muryar Ummi da ta ji ya isa ya tashi hankalin ta ba shiri ta nufo gidan.



Ko da tazo itama sai da ta yi kukan tausayin halin da Maleek ke ciki itama cewa ta yi su je asibiti amma da Ummi ta yi mata bayani kan yanayin aikin su Maleek sai itama ta yi shiru da maganar.



Suna Nan zaune har dare Sabeeha ta kalli Ummi ta ce "Ummi mai zai hana mu koma can part d'in sa saboda nan ba wani sirri," Doctor ta ce "Haka ne Aysha can ya kamata su koma," Ummi ma ta yi na'am da hakan.


Dad'a matsawa kusa da shi Sabeeha ta yi alamun tana son fad'a masa wani abu fahimtar da Maleek ya yi ne yasa ya zubawa bakin ta idanu a hankali ta ce "Zaka yi wanka?" Gyad'a Kai ya yi kallon Ummi Sabeeha ta yi ta ce "Ummi wanka yake so," Ummi ta ce "To bari Salman ya dawo," tana rufe baki Salman ya yi sallama tare da wheelchair ba b'ata lokaci suka d'ora Maleek a Kai tsaye part d'in Fauwaz suka nufa saboda nan ne a down stairs Sabeeha ce ta yi masa wankan dakyar ta iya sannan ta tura shi zuwa cikin bedroom d'in Fauwaz ta shafa masa mai sannan tasa masa wata riga fara tas tare da farin 3quater ta taje masa kansa ta fesa masa turare ya yi kyau sosai.


Maleek kuwa zuciyar sa fal tausayin Sabeeha ganin harta fara hidima da shi gashi bashi da bakin yi mata godiya ganin ya kafeta da idanu yasa ta sakar masa murmushi ta tura shi zuwa cikin falon.



Suna fita waje suka fita akasa Maleek a mota sannan aka nufi part d'insa dake cikin gidan ba Wanda Nasreen ke ciki ba suna zuwa dama d'akunan dake down stairs a gyare suke d'aya a ciki aka shiga da maleek aka kwantar da shi saman k'aton gadon Sabeeha na gefen sa a zaune.


Mama ta yi musu Sallama Salman ya kaita gida.



Har lokacin suna d'akin Nasreen ta shigo d'akin da gudu har haki take yi tana zuwa ta fad'a jikin Maleek ta saka kuka kamar gaske ta ce "Shikenan na shiga uku na lalace Ya Maleek Mai ya same ka dama baka da lafiya yanzu Ina zansa kaina?" Ta fad'a tana cigaba da ihu kamar sabon kamu Sabeeha dake gefe duk ta gama k'ulewa ga wata muguwar tsanar Nasreen dake zuciyar ta ta kalle ta ta ce "Kinga Dan Allah kiyi mana shiru ai My bashi da mak'iyiyar da ta wuce ki dalla malama d'aga mun jikin miji idan ba haka ba Wallahi sai kin gane bani da wani mutunci," Gaba d'aya mutanen wajen kallon su ya koma wajen Sabeeha hatta ma Nasreen d'in jin abinda Sabeeha ta fad'a.


Sabeeha kuwa ba ma tasan maganar ta fito daga bakin ta ba sai kawai ta mik'e ta fice daga d'akin ashe tana fita sai Nasreen ta kalli Ummi ta ce "Ummi Ina so na dawo nan part d'in nima saboda kula da shi idan ranar girkina yazo," ba tare da wata damuwa ba Ummi ta ce "Bakomai ai kema mijin ki ne ki dawo," ta ce "To Bari naje na shirya," ta fad'a tare da fita a falo ta samu Sabeeha tana kuka kallon ta ta yi tare da yin dariya ta fice.



Cikin d'akin ta koma sannan ta kalli Fauwaz ta kanne masa ido ganin har sha biyu ta yi ya kalli Ummi ya ce "Ummi ya kamata kije ki kwanta Kinga dare ya yi?" Ummi ta ce "To ku ma ya kamata ku tafi dare ya fara"



Fauwaz ya ce "To Ummi bari na Kai ki," tashi Ummi ta yi ta kalli Maleek da har ya yi bacci ta k'arasa wajen sa sumbace shi a goshi sannan ta fita tana ji kamar ta kwana a wajen sa sai dai ba dama ganin da matan sa har biyu a part d'in.


Suna fita Sabeeha ta kalli Sabreen ta ce "Dear muje can part d'in sai ya Fauwaz ya same mu a can," tashi Sabreen ta yi suka nufi d'ayan part d'in suna shiga suka samu Nasreen zaune a falo tana cin kaza tana korawa a falo ko kallo bata ishe su ba suka haura stairs wanka Sabeeha ta fad'a tana fitowa ko mai bata shafa ba ta zura wata black d'in doguwar riga ta yi parking gashin ta kallon ta kawai Sabreen ke yi ga cikin ta har ya tasa take tausayin Sabeeha ya kama Sabreen ta ce "Sister ki zauna ni su tafi dani Kinga bake kad'ai bace kar su cutar dake tare da yaron ki," shafa cikin Sabeeha ta yi hawaye cike a idanunta sai Kuma ta d'an yi murmushi ta ce "Insha Allah ba abinda zai faru dear," daga haka ta zira hijabi abinta ta kalli Sabreen ta ce "Sister kiyi wanka," ba musu ta shiga toilet ta yi wanka ta fito tasa wata doguwar rigar Sabeeha blue sannan suka fita falo suna zama Fauwaz ya yi sallama suka amsa sannan ya zauna ya ce "Sister kina ganin abun nan zai yuwu kuwa?" Gyad'a kai Sabeeha ta yi ta ce "Eh abinda kawai zan fad'a shine ka dinga kula da Sabreen saboda Nasreen," gyad'a Kai Fauwaz ya yi sannan suka tashi suka fita daga part d'in zuwa part d'in Maleek ko shiga Fauwaz bai yi ba ya ce "Zai wuce gida," rungume shi Sabreen ta yi ya shafa bayan ta ya ce "Sai na dawo gobe My love take care," noding kanta Sabreen ta yi sannan ya shiga mota ya tafi su Kuma suka shige part d'in.


D'akin da Maleek yake suka shiga sun dad'e a d'akin a zaune sannan Sabeeha ta kalli agogon hannunta ta ga d'aya saura sai ta tashi ta kwanta jikin Maleek wani kuka ne ya kufce mata ta dad'e tana kukan sannan ta mik'e suka rungume juna da Sabreen suna kuka sun dad'e suna aikin abu d'aya sannan Sabeeha yi jarumtar cewa "Dear ni zan tafi ki kula sosai," gyad'a Kai Sabreen ta yi sannan ta mik'awa Sabeeha k'aramar wayar ta ta ce "Sister kije da wannan akwai kati sosai a ciki ki kasance tare da ita Dan Allah ki dinga Kiran mu ko hankalin mu zai kwanta," karb'a Sabeeha ta yi ta ce "To Nagode na tafi," ta yi hanyar fita tana waigen Maleek.



Tana fita Sabreen ta zauna ta saka kukan tausayin 'yar uwar ta.




Sabeeha ma tana tafiya tana sharar k'walla d'akin ta ta shiga ta kwanta sai dai ta kasa bacci.



Sabreen ma kwanciya tayi saman kujerar dake d'akin.


Duk cikin su ba Wanda bacci ya d'auka daga Maleek har Sabreen da Fauwaz da Ummi da Salman ballantana Sabeeha da sai juyi take yi.




Misalin k'arfe biyu da rabi Sabeeha dake yin Sallah ta ji an bud'e k'ofar d'akin ta bata damu ba domin dama tasan zasu zo tana sallar suka shigo cikin bak'ak'en kaya manya ne sosai su hud'u sun rufe fuskokin su ganin tana yin Sallah sai suka tsaya jiran ta tana yin sallama d'aya a cikin su ya zaro bindiga ya nuna Sabeeha da ita sai lokacin ta ji wani tsoro ya kamata ta ce "Su waye ku?"


"Zaki san ko mu su waye taso mu tafi kawai ko yanzu mu fasa kanki da wannan bindigar," da sauri jiki na rawa ta mik'e domin iya muryar mutumin abun tsoro ce haka suka tasa Sabeeha a gaba har mota ta shiga suka ja motar da gudu suka bar gidan.
[10/25, 8:56 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️


RUBUTAWA DAGA
HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ)




SADAUKARWA GA
MY DAUGHTER SABEEHA
BILKISU Z. YA'U (🅱️K)
AISHA MAGAJI DABO (AMA)




Page 32


Tunda suka hau titi suke zabga gudu Sabeeha kuwa wasu hawaye ne suka zubo Mata a idanunta domin rashin sanin abinda zai faru ga rayuwar ta tabbas taji dai Uncle yana zancen za a d'auke ta sannan tasan basu d'auke ta dan komai ba sai dan su raba ta da ranta shikenan yanzu hakan na nufin ta rabu da mijin ta da take matuk'ar k'auna shikenan ta rabu da iyayen ta shikenan yanzu ta rabu da 'yan uwan ta da suke matuk'ar son ta sannan a hankali ta shafa cikin ta wasu zafafan hawayen suka sake zubo mata saboda tunawa da babyn dake cikin ta da ta yi tabbas aka kashe ta Maleek ya yi asarar Babyn sa.



Ajiyar zuciya ta sauke sai Kuma tunanin ta ya koma kan tunanin meyasa Uncle yake son kashe Mata miji wata zuciyar tace shin kin manta labarin da Maleek ya Baki akan rayuwar sa ta baya take ta bawa zuciyar ta amsa akan cewar tsanar da Uncle kewa Daddy da Ummi ne har ya shafi Maleek tana cikin tunanin ta ga an yanki wata hanya a cikin daji sai da aka yi nisa sannan ta ga wani gida guda d'aya tak a dajin da alama ma gidan gona ne bud'e musu gate aka yi suka shiga suka yi parking sannan suka bud'e motar suka fita suka ce Sabeeha ma ta fito ta fito wani mugun tsoro ne ya kama ta ganin gaba d'aya gidan a zagaye yake da wasu manyan murd'a_murd'an mutane masu tsayi da k'iba bak'ak'e k'irin da su cikin bak'aken kaya har da bindigu a hannun su.



"Kee! wuce muje" wani a cikin Wanda suka zo tare ya dakawa Sabeeha tsawar da sai da ta firgita ta fara tafiya cikin gidan suka shiga bakowa a gidan sai wata mata tsohuwa a zaune tana shan taba da mamaki Sabeeha ke kallon ta ganin tsohuwar mace irin wannan da shan sigari sannan kanta ba kitso wacce tsohuwar a k'alla zata yi shekara 65.




Tashi matar ta yi ta k'arasa gaban Sabeeha sannan ta d'aga hannu ta zabgawa Sabeeha mari har biyu ta ce "Uban waye yace miki ana kallo na haka?" Saurin k'asa da Kai Sabeeha ta yi hawaye na bin fuskar ta domin Marin ya shige ta ba k'arya damk'ar gashin kanta da matar ta yi ne yasa ta sakin k'ara amma duk da haka matar bata sake ta ba ta fara janta har zuwa wani d'aki ta turata fad'uwa Sabeeha ta yi kanta ya buge da tiles take wajen ya fara jini rintse idanunta ta yi tana jin wata azaba na ratsa ko Ina na jikin ta ga wani sanyi da yake ratsa ta da baya-baya ta ja sannan ta jingina jikin wata kujera dake d'akin wacce duk fad'in d'akin ita kad'ai ce a ciki curewa waje d'aya ta yi ta kifa kanta da gwiwa tana kuka a hankali.


Matar dake bakin k'ofa ta ce "Kee!! Kiyi mana shiru a nan idan kuwa ba haka ba na lahira sai ya fi ki jin dad'i," wayar matar da ta fara ringing ne yasa ta d'aga cikin ladabi ta ce "Allah ya ja da ran Yallab'ai," sannan ta ce "Eh an kawo ta to Yallab'ai zan ganar da ita azaba kamar yadda ka buk'ata shikenan angama," daga haka ta katse wayar ta ja k'ofar d'akin ta rufe da key Sabeeha kuwa addu'a kawai take jerawa cikin ranta.


A gida kuwa asuba a idanun Sabreen ta yi saurin tashi ta yi ta shige toilet ta d'auro alwala ta yi sallah ta dad'e tana addu'ar Allah ya kare mata 'yar uwar ta sannan ta tashi ta fice daga d'akin duk Maleek na kallon ta direct part d'in su Sabeeha ta nufa tana sauri har tana yin tuntub'e tana shiga falon ta tarar ba kowa cikin bedroom d'in Sabeeha ta shiga sai ta ga wayam sannan bata ji motsin ta a toilet ba hakan ya tabbatar mata kenan mutanen sun tafi da Sabeeha zama ta yi gefen gadon ta saka kuka tana tunanin shikenan yanzu an tafi da 'yar uwar ta yanzu basu San a halin da take ciki ba shin tana raye ne ma ko sun kashe ta suna nan garin ko ma sunbar k'asar da ita oho shin ko tana raye zasu sake ganinta ko kuwa shikenan sun rabu kenan da saurin Sabreen ta fara girgiza Kai kamar wata tab'abb'iya a fili ta furta "Bazai yuwu ba ba abinda zai faru dake Sabeeha dear zaki dawo gare mu zamu yi rayuwar farin ciki," ta k'arashe maganar cikin kuka.




Ta dad'e tana kukan sannan ta tuna Maleek fa ya farka sannan fito Yana kallon ta ba tare da tace masa komai ba karfa ya gane ba ita bace Sabeeha da sauri ta mik'e ta nufi hanyar fita tana sauka down stairs sai ta ga Nasreen a tsaye kallon tsaf ta yi mata sannan ta ce "yammata ya jikin mijin ki?" Banza Sabreen ta yi Mata ta yi hanyar fita shan gabanta Nasreen ta yi ta ce "Ya Ban gama magana dake ba za ki wani tafi?" Nan ma Sabreen ta kasa cewa komai.



"Ke ko Wai rashin maganar mijin ki ne ya dawo kan ki Kuma fa Ina ganin daga wannan cutar zaku wayi gari ku ga sai gawar sa," wani mugun kallo Sabreen ta watsa mata sannan cikin harzuk'a ta ce "Wallahi karki kuskura ki ce zaki shiga sabga ta domin hakan bazai miki kyau ba idan Kuma Kinga zaki gwada ki cigaba ni kuma zan nuna miki tawa haukar tafi taki stupid kawai," Sabreen na fad'ar haka ta fice tabar Nasreen a tsaye sake da baki.



A fili ta ce "Stupid," sai kuma ta kyalkyale da dariya ta ce "A sannu zan nuna miki karawa da Nasreen ba abune mai sauk'i ba Sabreen," tana fad'ar haka ta haye stairs abinta.

Da sallama a bakin ta ta shiga d'akin kallon ta kawai Maleek ya yi a hankali ta k'arasa wajen sa ta tsaya ta kasa furta ko da kalmar a ce shi kuwa d'auke kansa ya yi sai Kuma kanta a k'asa ta ce "To yanzu ta ya zata iya yin sallah?" Shiru ba magana daidai lokacin Ummi da Fauwaz suka yi sallama a hankali Sabreen ta sauke ajiyar zuciya tare da amsa musu sallamar suka shiga suka zauna gaishe su ta yi yayin da idon Fauwaz ke a kanta baya ko k'iftawa ganin idanunta sunyi jajir alamar ta yi kuka.

Suna had'a ido ta ce "Dama za shi toilet ne," tashi Fauwaz ya yi ya nufi wajen Maleek ya kalle shi murya a raunane ya ce "Sannu Yaya," lumshe masa ido kawai Maleek ya yi Ummi ma wajen sa ta nufa ta zauna gefen sa ta shafa lallausar sumar kansa ta ce "Sannu kaji Son Allah ya baka lafiya," jinjina kai ya yi a zuciyar sa kuwa ya amsa da Ameen Ummina.


Salman ne ya shiga d'akin Umar na binsa a baya ganin halin da Maleek d'in ke ciki ya k'arasa da sauri yana salati kamar k'aramun yaro haka Umar ya saka kuka domin shi Salman ya yi masa bayanin anahin abinda ke faruwa.


Ummi ke rarrashin sa dakyar ya yi shiru Maleek kuwa da kallo yabi Umar ganin irin kukan da yake yi ya gane tabbas Salman ya sanar da shi abinda ke faruwa girgiza masa Kai kawai Maleek ya yi.


Har da Umar suka sa shi a wheelchair sannan Umar ya tura shi zuwa toilet ya cire masa rigar jikin sa sannan ya d'aura masa towel a k'ugunsa sannan ya zare masa boxer d'in jikin sa ya fara masa brush sannan ya yi masa wanka sannan ya rufa masa wani towel d'in a jikin sa ya tura shi domin fita daga bathroom d'in.



Jin motsin za a bud'e k'ofar yasa Sabreen saurin cewa "Ummi Bari naje nayi masa breakfast," kafin Ummi tayi magana har ta fice daga d'akin.


Kitchen ta shiga ta fara had'a breakfast har ma dasu Ummi da Fauwaz da tasan babu abinda yaci gamawa ta yi tas sannan ta jera a babban tray ta nufi d'akin da sallama ta shiga da sauri Fauwaz ya k'arba yana yi Mata Sannu.



Zama tayi gefen gadon lokacin har an shirya Maleek cikin bak'aken k'ananan kaya ya yi kyau sosai abincin Ummi ta zuba a plate ta mik'awa Sabreen ta ce "Ungo Daughter bawa Son," ta mik'a hannu zata karb'a sai Fauwaz ya yi wuff ya karb'a ya ce "A'a Ummi bani ni zan ba shi," Ummi bata kawo komai a ranta ba Fauwaz kuwa gefen Maleek ya koma ya fara bashi abincin.


"Daughter kema ya kamata ki ci abincin," Ummi ta fad'a tana kallon Sabreen da dama yunwa take ji rabon ta da abinci tun jiya da rana a hankali ta ce "To Ummi," zuba abincin ta yi a plate tana ci kamar wata mara gaskiya.



Kallon ta Maleek ke yi a zuciyar sa Kuma mamaki yake yi yaushe Sabee ta fara cin chips saboda tunda ta samu ciki ta dena cin chips ko k'amshin sa amai yake sata amma yanzu gashi tana ci sannan Kuma yanzu bata so suna had'a ido sannan wannan ba d'and'anon girkin ta bane mai ya ja hakan wata zuciyar tace may be rashin lafiyar ka ne ya ja Mata wannan canjin.



Kallon spoon d'in chips da Fauwaz ya kai bakin sa ya yi ya girgiza Kai alamun ya k'oshi sannan ya ba shi ruwa ya sha.



"Ya Fauwaz Kai baka ci abincin ba ko kaci wani Abu ne?" Sabreen ta fad'a tana kallon sa girgiza Kai ya yi ya ce "A'a sister bara dai naci yanzu," ya fad'a tare da fara cin ragowar da ya bawa Maleek.



Tashi Umar ya yi ya kalli Fauwaz ya ce "Fauwaz Ina Sabreen ne?" Daram gaban Sabreen da Fauwaz ya fad'i.


"Amm Ya Umar tana gida," Umar ya ce "Dama Meeha ce ke son ganinta ka sanar da ita sai na biya ta gidan muje saboda bata da lafiya ne," Fauwaz da har ya fara zufa ya ce "Ai da...ma ita ma bata da la..fiya ne shiyasa," ya k'arasa maganar cikin in Ina jinjina Kai Umar ya yi ya ce "Ok ba damuwa zan sanar mata bari naje zan dawo anjima insha Allah," Ummi ta ce "To ka yi Mata Sannu Allah ya bata lafiya," ya amsa da "Ameen," tare da ficewa.



"Mai yake samun Daughter d'in?" Ummi ta fad'a tana kallon Fauwaz d'an ajiyar zuciya Fauwaz ya yi ya ce "Ummi tun jiya da muka koma gida tace mun kanta na yin ciwo daga baya Kuma sai zazzab'i ya kama ta," Ummi ta ce "Ayyah Allah ya bata lafiya Kira mun ita a waya nayi mata sannu," da Sauri Sabreen dake kallon sa ta fara girgiza kai fara lalubar k'aryar da zai yi Fauwaz ya fara Sabreen ta yi saurin cewa "Laaa Ummi ai jiya nan Sabreen ta manta wayar ta," Fauwaz ya ce "Au dama nan ta manta wayar ai mun d'auka fad'uwa ta yi kinji ashe ma tana nan amma Ina komawa zan fad'a mata kina yi mata sannu,"

Mik'ewa Sabreen ta yi ta fice tana fita hanyar part d'in su Sabeeha ta yi domin zuwa tayi wanka tana shiga bedroom d'in ta cire rigar jikin ta ta d'aura towel ta shige wanka tana fitowa ta nufi mirrow ta zauna.



Mik'ewa Fauwaz ya yi ya ce "Ummi bara na d'an shiga ciki na dawo," gyad'a Kai kawai Ummi ta yi sannan ta kalli Maleek cikin tausayin sa ta ce "Son muje asibiti ko?" Girgiza mata kai ya yi saboda ya fahimci abinda tace masa.

Fauwaz kuwa direct part d'in su Sabeeha ya shiga Kai tsaye ya shige bedroom ya hangi Sabreen ta mik'e tsaye domin ko Mai ta kasa shafawa ta baya ta ji an rungume ta a tare suka saki ajiyar zuciya sannan Fauwaz ya ce "Nayi missing d'in ki My love," waigawa ta yi ta kalle shi sai Kuma tasa kuka.




Rikicewa Fauwaz ya yi ya ce "Subhanallah meya faru?" Cikin kuka sannan ta rungume shi tsam ta ce "My heart Sabeeha dear bamu San halin da take ciki ba sun tafi da ita me zasu yi mata tana da ciki fa,"



Sai lokacin Fauwaz ya tuna da cewar fa Sabeeha na da ciki amma suka yarda tasa kanta a had'ari ya ce "Ya Salam Allah ubangiji ya kare ta daga dukkanin sharri," Sabreen ta ce "Ameen amma meyasa kazo nan karfa wani ya ganka," ya ce "Ba Wanda ya ganni ni gurin matata nazo," shiru kawai Sabreen ta yi a jikin sa su n dad'e sannan ta shirya ita ta fara fita sai da ta dad'e sannan shima yabi bayan ta.


Nasreen ce ta zauna gefen gadon ta ta kyalkyale da dariya a fili ta ce "Wannan ma wata hanyar ce da zan tarwatsa duk wani Shirin ku domin tunda Fauwaz mayen Sabreen ne zai cigaba da biyo ta nan part d'in dan Haka sai nayi musu video na nunawa Maleek da uwar su daga lokacin kuwa asirin su zai tonu,"




Da sallama Umar ya shiga bedroom d'in Sameeha tana kwance cikin blanket gefen gadon ya zauna jikin sa a sanyaye a hankali ta ya ye bargon sannan ta matsa kusa da shi ta shige jikin sa ta ce "Hubby me yake faruwa ne Dan Allah ka kaini naga Sabeeha dear saboda tun jiya nake yin munanan mafarkai a kanta Dan Allah ka kaini na ganta ko tana lafiya," ajiyar zuciya Umar ya yi sannan ya shafa kanta zuwa bayan ta ya ce "Ki kwantar da hankalin ki Meeha Sabeeha na lafiya yanzu ma daga can nake Sabreen ce Kawai Fauwaz ya ce mun bata jin dad'i zan Kai ki wajen Sabeehan amma sai kinji sauk'i kinji?" Noding kanta ta yi amma har lokacin hawaye take yi domin a mafarki ta gani cewar Sabeehan su na cikin wani hali sai wata zuciyar ta ce Wannan ba komai bane illa rashin lafiyar Sabreen da mafarki ya hargitsa Miki komai ya danganta hakan da Sabeeha sai Kuma ta ji hankalin ta ya d'an

Please Login or Register in order to submit comment