Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

iyayen su sannan a meyere suke sannan su da mahaifin su kad'ai ne a gidan su,"



"Mamar su fa?" Maleek ya tambaya yana kallon Salman.



Salman ya ce "Gaskiya nemar ta aka yi aka rasa ba asan inda take ba kuma tun suna 'yan 3years," tsayawa da abinda yake yi Maleek ya yi yana kallon Salman sannan ya ce "Ina da abubuwa da yawa amma jibi zamu je k'auyen," Salman ya ce "Angama," daga haka Maleek ya tashi suka nufi gida.
[10/25, 7:42 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️





RUBUTAWA DAGA
HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ)







SADAUKARWA GA
MY DAUGHTER SABEEHA
BILKISU Z.YA'U (🅱️K)
AISHA MAGAJI DABO (AMA)




Page 12


Sabeeha kuwa sai yamma sannan ta yiwa Abban su sallama ta tafi bayan ta ba shi kud'i mai yawan gaske da Ummi ta bata a bashi sannan taje gidan zuwaira mai abinci ta k'ara mata wasu kud'ad'en.




Abba kuwa sai godiya yake yi yana sa mata albarka haka ta tafi tana jin ba dad'i haka ma Abba ji ya yi kamar kada ta tafi domin ya ji dad'in zuwan ta sosai ranar ya ji shi cikin farin ciki.




Sai dare sannan ta isa Kaduna mai keke napep ta samu ta shiga zuwa gida.




Maleek ne tsaye a compound d'in gidan sai kai da komawa yake yi sannan lokaci zuwa lokaci yana kallon agogon hannunsa ji yake yi kamar ya bita k'auyen meyasa zata yi dare haka?



Salman ne ya k'arasa wajen sa ya ce "Ranka ya dad'e da alama fa ta iso sai dai tana gate d'in farko domin bincike," k'aramun tsaki Maleek ya ja sannan ya ce "Kira mun Adam a waya," Kiran sa Salman ya yi sannan ya mik'awa Maleek wayar.



Maleek ya ce "Adam ka barsu su shigo kasan dai abinda ya dace," Adam jin muryar boss d'in su jiki na rawa ya ce "Ok sir," katse wayar Maleek ya yi.




Adam jiki na rawa ya hau mota har wajen Sabeeha ya bud'e mata ta shiga ya ja motar.


Sarai tasan wannan umarnin Maleek ne dan haka sai zuba ido take yi ta ga ta inda zata ganshi amma babu shi sai k'amshin turaren sa da ya cika wajen Adam na tsayar da motar ta bud'e ta fice tunanin fal zuciyar ta domin zuciyar ta fad'a mata take yi Maleek ya hak'ura da ita tunda gashi ko son ganin ta baya yi.




Abinda bata saniba kuwa Maleek baya son su had'u ne saboda ya tabbata idan ya ganta sabuwar soyayyar ta ce zata k'aru a ransa sai dai baya buk'atar hakan tunda har ita bata son shi.




Da sallama ta shiga falon su Sabreen da gudu suka rungume ta suna yi Mata sannu da zuwa har k'asa ta tsugunna ta gaida Ummi cikin fara'a ta amsa tare da tambayar ta hanya da kuma Abban su tace "Lafiya lau Ummi yace na gaida ki," Ummi ta ce "Masha Allah Ina amsawa yanzu kije ki watsa ruwa kici abinci ki huta," ta ce "To Ummi," ta fad'a tare da mik'ewa ta nufi d'akin su.


Bin bayan ta su Sameeha suka yi tana shiga d'akin ta cire hijabin jikinta ta ajiye gefen gado sannan ta cire bak'ar doguwar rigar jikin ta ta d'aura towel.




Su Sabreen ne suka shiga d'akin har suna had'a baki wajen cewa "Abba yana lafiya dai ko?" Murmushi ta yi ta ce "Lafiya k'alau yake yace yana gaishe ku," a tare suka sauke ajiyar zuciya Sameeha ta ce "Ya b'angaren su Kawu fa?" Kallo mai kamar harara Sabeeha ta yi mata sannan ta ja tsaki ta ce "Oho bansani ba amma dai ya aurawa Sadam Zainabu," tsalle Sabreen ta buga ta ce "Wayyo dad'i gaskiya kan Kawu naja irin wannan had'i haka dama yana da wata macen sai ya aurawa Dauda," dariya Sameeha ta yi ta ce "Allah ya shirye ki ai Dauda yana nan yana jiran ki 'yammata," wata uwar harara Sabreen ta makawa Sameeha ta ce "Ya ishe ki malama," juyawa Sabeeha ta yi ta shige toilet tana dariya ganin yadda Sabreen ta yi kicin-kicin da fuska.



Itama Sabreen juyawa ta yi ta nufi k'ofa tana cewa "Kuma yaseen ki ka yi wasa sai na fad'awa ya Fauwaz domin yasan zaman da zai yi dake," da sauri Sameeha ta rik'o hannun ta ta ce "Haba sister mie kinsan fa ni dake ba fad'a tsakanin mu Dan Allah karki fad'a masa harna fara jin kunyar sa tun kafin ki gaya masa ai Sabreen sister sai ya Fauwaz Wallahi ke da shi ba rabuwa wallahi ke da shi ba rabuwa bazar kowa bazar kowa da bazar sa ke kike taka rawa da bazar sa ke ki ke taka rawa," aikuwa Sabreen ta fara taka rawa domin wak'ar Sameeha ta faranta mata sosai.




Dariya Sameeha ta yi ta fice tabar Sabreen ta tik'ar rawa ita kad'ai.


Washe gari Ummi na zaune a falo tana yin waya aka bud'e k'ofar falon aka shiga falon da sallama kallon wajen Ummi ta yi mamaki ne k'arara ya bayyana akan fuskar Ummi domin ganin Umman Nasreen a part d'in ta domin rabon ta da part d'in an dad'e kuma idan har an ganta a b'angaren to ba alkhairi ne ya Kai ta ba, katse wayar ta yi tare da amsa sallamar.



K'arasawa cikin falon Umman Nasreen ta yi ta zauna gefen Ummi ta ce "Aysha Ina wuni," ta fad'a tana washe baki kamar gaske Ummi ta ce "Lafiya k'alau ya yara?"




Umman Nasreen ta ce "Wallahi lafiya k'alau ya su Abdul-maleek?" Nan ma da kallon mamaki Ummi ta bita domin wannan tambayar tafi komai bata mamaki domin tana da tabbacin duk duniya ba wanda Asiya ta tsana kamar Maleek amma yau ita ce ke tambayar lafiyar sa abinda bata tab'a ba kenan tun kuwa Maleek d'in na jariri.




Kawar da tunanin Ummi ta yi ta ce "Yana lafiya,"




"Masha Allah," cewar Umman Nasreen sannan ta cigaba da cewa "Aysha dama zuwa nayi na k'ara baki hak'uri akan abubuwan da suka faru a baya nayi nadama Dan Allah kiyi hak'uri," cikin farin ciki Ummi ta ce "Haba Asiya komai ya wuce," Ummi ta fad'a zuciyar ta fal farin ciki domin dama bata da burin da ya wuce su had'a kansu ba ma tun yanzu ba dan dai kawai ita Umman Nasreen ta nuna ba hakan a ranta ne.


Rinaz da Sameeha tare da Sabreen ne suka yi sallama a falon gaishe da Umman Nasreen suka yi suka wuce banda Rinaz da ta d'auke kai kamar bata ganta ba duk da hararar da Ummi ke aika mata suka haura stairs.



Umman Nasreen ta ce "Aysha wad'an nan tagwayen fa?" Murmushi Ummi ta yi ta ce "Ai 'yan uku ne," nan Ummi ta bata kad'an daga cikin labarin su Umman Nasreen ta ce "Allah sarki ko zaki bani aron d'aya ta dinga zuwa tana yi mun aiki dama Huwaila taje unguwa?" D'an jim Ummi ta yi tana tunani sai kuma ta yi tunanin kar ta hana Umman Nasreen ta yi tunanin wani abu sai kawai ta ce "Shikenan sai Sameeha ta dinga zuwa tana yi miki," Umman Nasreen ta ce "To bakomai nagode," murmushi Ummi ta yi ta ce "Bakomai wallahi," daga haka Umman Nasreen ta yiwa Ummi sallama ta tafi.



Bayan tafiyar ta ne Ummi ta kira Sameeha ta fad'a mata cewar zata dinga zuwa part d'in Umman Nasreen tana ta ya su wasu ayyukan kafin Huwaila ta dawo duk da akwai wasu 'yan aikin Sameeha ta ce "To Ummi,"




Da daddare Sameeha ta samu su Sabeeha a d'aki ta fad'a musu cewar ita fa zata fara zuwa part d'in su Nasreen domin yiwa Umman su Nasreen aiki a d'an razane Sabeeha ta kalle ta saboda tasan dole akwai abinda Nasreen da mahaifiyar ta ke k'ullawa a kansu amma sai bata nunawa su Sameeha ba ta ce "Allah ya kaimu amma sun fad'a miki sanda zaki fara zuwa?" Sameeha ta ce "A'a," Sabreen ta ce "Kai nifa ba abinda Umman Nasreen d'in nan tayi mun amma duk na tsane ta Wallahi," Sabeeha dai bata ce komai ba.



Washe gari da wuri Maleek ya shirya domin zuwa k'auyen su Sabeeha k'arfe 9 ya fito daga part d'in sa ya matuk'ar yin kyau cikin light blue shadda kansa da bak'ar hula yayi kyau iya kyau kullum kamar k'ara masa kyau ake yi wayar sa ya zaro k'irar iPhone 12 pro max ya yi kira.



Sabeeha na kitchen tana k'arasa had'a breakfast Rinaz ta lek'o ta saman bene ta ce "Ummi Yaya yace na fad'a miki zai je unguwa ya k'ira wayan ki bai samu ba," Ummi ta ce "Ooh ni son mai part d'ina ya yi masa da bai son zuwa Allah ya dawo mun da shi lafiya," Rinaz ta ce "Ameen,"




Sabeeha na jin haka ta fice ta k'ofar baya dake kitchen d'in da gudu domin bala'in son ganin sa take yi rabon da ta gansa har ta manta sai dai tana fita lokacin an bud'e masa mota zai shiga bata ga fuskar sa ba sai bayan sa ta hango Salman ya bud'e masa k'ofa ya shiga an rufe sun ja motocin da gudu.



Had'adden k'amshin sa ne ya daki hancin ta da ya sata lumshe ido wanda hakan yaba hawayen da ya taru a idanunta damar zubowa a ranta tace shikenan na rasa shi na tabbata yanzu ba soyayya ta a zuciyar sa haka ta juya ta koma direct d'akin su ta wuce ta sha kukan ta ba tare da kowa ya saniba.



Tana cikin kukan ne bacci ya d'auke ta ta dad'e tana baccin sannan ta farka Sabreen ce ta shiga d'akin tasha kyau sosai cikin riga da skirt na less maroon mai adon flowers silver color ta kalli Sabeeha ta ce "Sabeeha dear kin tashi dama zamu fita ne da my love," jinjina Kai Sabeeha ta yi sannan a hankali ta ce "Sai Kun dawo," kallon ta Sabreen ta tsaya yi sannan ta ce "Dear mai yake damun ki?" Girgiza Kai Sabeeha ta yi ta ce "No bakomai," Sabreen ta ce "Kinsan nasan ki nasan yanayin ki Dan Allah ki dena saka komai a ranki idan har kina son farin cikin mu," Murmushi Sabeeha ta yi ta ce "Bakomai fa kawai kaina ke mun ciwo,"




Sabreen ta ce "To ki sha magani ni na tafi," Sabeeha ta ce "Ok," fita Sabreen ta yi zuwa falo ta samu Fauwaz zaune ya ci ado ba k'arya ta ce "My love muje ko," tashi ya yi ya ce "Ok let's go my heart Ummi sai mun dawo," hararar su Ummi ta yi ta ce "To marasa kunya," dariya suka yi dukan su har Sameeha dake zaune kan kujera tana buga game a wayar Rinaz.



Wayar Ummi ce ta fara ringing ta d'aga tana gama wayar ta mik'e ta kalli Sameeha ta ce "Daughter d'auko mun d'aya a cikin key's d'in motana a bed side drower zani hospital ne Ina da patient," Mik'ewa Sameeha ta yi ta ce "To Ummi," ta nufi stairs bata dad'e ba ta dawo sannan ta d'auki hand bag d'in Ummi ta ce "Ummi muje na raka ki motor," Ummi ta ce "To muje," har mota Sameeha ta raka ta sannan ta koma direct stairs ta nufa d'akin Rinaz.




Tana haurawa stairs Sabeeha ta fito daga kitchen daidai lokacin d'aya daga cikin 'yan aikin Umman Nasreen ta yi sallama.




Amsawa Sabeeha ta yi sannan 'yar aikin ta ce "Dama Hajiya ce ta aikoni ta ce gashi a bawa Sameeha lokutan da zata dinga zuwa aiki ne," tab'e baki Sabeeha ta yi sannan ta karb'a ita Kuma 'yar aikin ta fice.





B'angaren su Maleek kuwa suna zuwa k'auyen sojojin sa suka diddiro daga motocin su suka nufi motar da yake ciki suka zagaye ta Salman ne ya bud'e masa mota ya fito.




Gani ya yi 'yan garin sun taru suna kallon sa har da masu lek'e ta katanga sai dai ana cewa kett zasu gudu saboda kallo d'aya zaka yi musu kasan a matuk'ar tsora ce suke.



Kallon Salman ya yi ya ce "Kayi mun sallama dame gidan," zauren gidan Salman ya shiga ya yi sallama Abba dake zaune bisa tabarma ya amsa sallamar sannan ya ce "Bismillah shigo,"



Shiga suka yi da Sallama Abba ya amsa tare da nuna musu tabarmar da yake zaune ya ce "Ku K'araso ga guri," zama suka yi sannan suka gaida shi ya amsa cikin fara'a sannan ya ce "Sai dai bangane ku ba?" Maleek ya ce "Abba ni sunana MG Abdul-maleek Hamza mai dala wannan Kuma Salman," a tsorace Abba ya ce "Lafiya dai ko?" Domin Abba yasan MG a radio k'arara mamakin ganinsa a gidan sa ya bayyana a fuskar Abba.




Maleek ya ce "Lafiya lau Abba yaran ka 'yan uku a gidan mu suke ai," nan Maleek ya ba shi labarin tsananin soyayyar da yake yiwa Sabeeha da kuma k'in amincewar da ta yi sannan ya cigaba da cewa "Nayi bincike ne nagane a nan suke Kuma kaine mahaifin su sai dai Abba mamar su fa?"



Kallon tausayawa Abba ya yiwa Maleek domin ba k'aramun so Maleek ke yiwa Sabeeha ba sannan Abba ba tare da tunanin komai ba ya bawa Maleek labarin auren sa da mamar su Sabeeha har zuwa b'atan ta domin haka kawai yaji ya yadda da Maleek ba ma haka ba duk Wanda yasan MG yasan yana da halaye masu kyau ga taimako.



Jinjina Kai Maleek ya yi sannan ya ce "Abba ko zan samu hoton ta a wajen ka?" Shiru Abba ya yi kamar mai tunani sannan ya ce "Eh akwai bari na d'auko ma," tashi Abba ya yi ya shiga d'aki.




Kawu Bala na zaune a k'asan wata bishiya kan tabarma labari ya same shi cewar ga sojoji can da bindigu a gidan k'anin sa take Kawu ya rikice ya ce "Tabdijan wacce masifa Habu ya kirawa kansa to Dan Allah karku ce ni yayan sa ne bari ma na tashi nabar nan shi kad'ai ya Kira masifar sa dan haka a kansa zata k'are," yana fad'ar haka ya kad'e babbar rigar sa ya mik'e ya zura takalman sa ya nufi bayan gari da sauri har yana had'awa da gudu.



Fitowa Abba ya yi hannun sa rik'e da hoto ya k'arasa ya zauna sannan ya mik'awa Maleek hoton ya ce "Wannan shine hoton Maryam tare da k'awar ta,"



Karb'a Maleek ya yi ya kalli hoton a hankali ya ce "Ummina kuma?" Ya fad'a yana kallon hoton Ummin sa ce tare da doctor Maryam.


Abba ya kalle shi ya ce "Kana nufin kai yaron Aysha ne?" Gyad'a kai Maleek ya yi ya ce "Eh tabbas wannan Ummina ce tare da Doctor Maryam," a zuciyar sa kuwa yana mamakin dama k'awancen Ummin sa da Doctor Maryam ya dad'e haka.



Abba ya ce "Yanzu Ina Maryam take tana lafiya dai ko?" Gyad'a kai Maleek ya yi ya ce "Abba ka kwantar da hankalin ka tana lafiya Kuma nayi maka alk'awarin had'a ka da ita dama yaran ku gaba d'aya," wani farin ciki ne ya mamaye zuciyar Abba domin tun b'atan Maryam bai k'ara jin labarin ta ba sai yau domin da yana ko kwanton shin tana raye ko ta mutu amma da ya ji tana lafiya hakan ba k'aramun faranta ran Abba ya yi ba.



Nan Abba ya fara zubawa Maleek Addu'a Yana sa masa albarka Maleek dai da "Ameen," kawai yake amsawa sannan ya mik'e ya ce "Abba sai ka ji daga gare ni," Abba ya ce "To Abdul ka gaida mun da Aysha sosai," murmushi Maleek ya yi ya ce "To Abba," daga haka ya ajiyewa Abba mak'udan kud'in da baisan adadin su ba ya fice Abba na yi masa godiya.



Suna fita suka samu k'ofar gidan cike famm da jama'a har da wad'an da suka zo daga makwaftan garin jin labarin MG Abdul-maleek yazo sai dai ko wannen su a tsorace yake.




Ana bud'e masa mota ya shige yana mamakin to meyasa Doctor Maryam bata neman mijin ta ballantana mijin ta shin meye dalilin ta kuma bayan suna raye ba mutuwa suka yi ba dole ne ya je wajen doctor Maryam ya ji daga gare ta har ma da Ummin sa da wannan tunanin suka tafi.
[10/25, 7:42 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️




RUBUTAWA DAGA
HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ)






SADAUKARWA GA
MY DAUGHTER SABEEHA
BILKISU Z.YA'U (🅱️K)
AISHA MAGAJI DABO (AMA)





Page 13


Su Sabreen da Fauwaz kuwa yawon su suka sha sannan ya wuce wajen sai da wayoyi iPhone 11 + ya siya guda uku sannan ya biya kud'in suka nufi gida.




Suna zuwa a falo suka ya da zango wayoyin Fauwaz ya mik'a mata ya ce "Wannan naku ne tare da su Sameeha," wani uban tsalle Sabreen ta buga ta ce "Wow dagaske My love," bata jira amsar sa ba ta fara k'wala kiran "Sabeeha dear Sameeha sister ku fito," yadda ta kira su ne yasa su fitowa da sauri.





Rungume Sabeeha ta yi ta ce "Dear kalla my love ya siya mana waya," ta fad'a tana mik'a musu wayar karb'a suka yi suna yi masa godiya.



Rinaz ce ta fito itama tana taya su murna wayoyin irin ta ta ne itama ta taya su yiwa Fauwaz godiya.




Maleek kuwa sai dare suka koma gida saboda ya biya NDA a masallacin dake gidan suka tsaya suka yi sallah sannan ya k'arasa part d'insa wanka ya yi ya kwanta gaba d'aya shi kansa a d'aure yake akan lamarin Doctor Maryam meyasa zata bar yaranta mata kamar haka ko waiwayen su bata yi ko meye dalilin ta nayi hakan?



Ganin babu Mai basa amsa ne yasa shi barin tunanin amma gobe zaije har hospital zai je ya sameta akan maganar.




Sabeeha tare da su Sameeha ne a d'aki ta d'auko takarda ta mik'awa Sameeha ta ce "Dear gashi d'azu aka aiko miki takarda ce mai d'auke da lokutan da zaki dinga zuwa aiki part d'in Umman Nasreen," karb'a Sameeha ta yi tana dubawa.



Sabeeha ta ce "Amma please sister sai kin kula sosai ko da yake nasan ke baki da shiga sabgar da ba taki ba da dai wannan ce," ta fad'a tana nuna Sabreen.



Dariya Sabreen ta yi ta ce "Ai wallahi a hakan ma Umman Nasreen sai ta ga iskanci," dariya suka yi dukan su Sabeeha ta ce "Kinga Sameeha dear rabu da wannan marar aikin yin ke dai baccin wuri ne ya kamace ke saboda kinsan gobe ne zaki fara fita," Sameeha ta ce "Wallahi kuwa dear gaskiyar ki dan idan na biyewa Sabreen sister sai mu kwana nan bata dena zuba ba," ta fad'a tana kwanciya.



Washe gari da wuri Sabeeha ta tashi ta shiga kitchen ta had'a breakfast sannan ta nufi d'akin su a k'ofa suka yi kacib'us da Sameeha.




"Dear daga Ina haka da safiyar nan," Sameeha ta tambaya tana kallon Sabeeha wacce kallo d'aya zaka yi Mata kasan a gajiye take Sabeeha ta ce "Daga kitchen mana kinga ki je aikin ki kada kiyi latti," tana fad'ar haka ta shige cikin d'akin Sameeha Kuma ta fice zuwa part d'in Umman Nasreen.



Tun kafin Sameeha ta shiga falon ta fara jiyo muryar Umman Nasreen na narka zagi daram dam gaban Sameeha ya fad'i dakewa ta yi ta shiga falon da sallama ko amsa mata sallamar ba a yi ba sai marin wata 'yar aiki da Umman Nasreen ke yi.




K'arasawa wajen Sameeha ta yi ta tsugunna ta ce "Hajiya ina kwana?" Wata uwar harara Umman Nasreen ta aikawa Sameeha sannan ta ce "Wannan Kuma wani salon iskancin ne sau nawa Kuma zaki gaishe ni ko ni sa'ar wasan kice?" Girgiza kai Sameeha ta yi tana tunanin to yaushe tazo part d'in ma da har ta gaishe ta.



Bud'e baki Sameeha ta yi a hankali ta ce "Yi hak'uri Hajiya yanzu wanne aikin zanyi?" Cikin masifa Umman Nasreen ta ce "Bayan aikin da ki ka gama yi yanzu amma tunda neman aikin ki ke yi jeki ki gyaramun store yanzu," mik'ewa ta yi sannan ta ce "To Ina ne kitchen d'in?" Wani uban zagi Umman Nasreen ta yiwa Sameeha ta ce "To uwar ki ma ta yi kad'an ta raina mun hankali balle ke yanzu ki yi wanke-wanke kibar kitchen d'in amma yanzu ki zo kina tambaya ta kitchen zaki wuce ko sai nayi ball dake?" Saurin matsawa Sameeha ta yi ta nufi inda take tunanin kitchen ne zuciyar ta fal tunanin anya kuwa Umman Nasreen bata ci Kai ba kuwa.




Tana shiga ta ga kitchen d'in ne kuwa zama ta yi kan wata kujera ta zabga tagumi hawaye ne ya fito daga idanunta ita dai duk inda zata aiki sai ta fuskanci wannan matsalar.


Share hawayen ta ta yi ta fara aikin da aka sata kamar ance ta kalli window ta hangi Sabreen tana yarfe hannu da alamu ta yi aikin ruwa take maganar Sabreen ta jiya da daddare ta fad'o mata da take cewa a hakan ma sai Umman Nasreen ta ga iskanci.



Murmushi Sameeha ta yi sannan ta cigaba da aikin ta har ta gama sannan ta fito daga kitchen d'in ta samu Umman Nasreen zaune akan kujera ta ce "Hajiya na gama," kallon banza Hajiya Asiya ta watsa mata sannan ta ce "B'ace mun da gani," juyawa Sameeha ta yi da sauri tabar falon.


Maleek ne ya fito tsaf cikin Shirin sa na zuwa hospital wajen Doctor Maryam Sabeeha na kitchen Hadiza ta shiga kitchen d'in hannun ta rik'e da breakfast d'in Maleek da ta tafi kai masa ajiyewa ta yi kallon ta Sabeeha ta yi ta ce "Lafiya ki ka dawo da breakfast d'in?" Hadiza ta ce "Cewa ya yi a dawo da shi ya k'oshi," shiru Sabeeha ta yi tana jin zuciyar ta ba dad'i tunani take yi ba dai har girkin nata ya dena ci ba?


Ummi ta jiyo tana cewa "Son na lura da kai kwana biyu sam baka son cin abinci ballantana ka sha drugs d'in ka," muryar Maleek ta jiyo yana cewa "Sorry Ummina Ina da abubuwa da yawa yanzu fita zanyi," da gudu Sabeeha ta nufi k'ofar barin kitchen d'in zuwa falo sai dai kafin ta fita Maleek ya fice.




Yana fita mota ya shiga sai hospital wajen Doctor Maryam jiniya ke tashi a garin Kaduna a duk inda motocin MG suka gifta.




Suna zuwa asibitin sojojin sa suka zagaye motar da yake ciki Salman ne ya bud'e masa k'ofa ya fito sannan suka nufi cikin asibitin direct office d'in Doctor Maryam suka nufa knocking Salman ya yi daga ciki Doctor Maryam ta ce "Yes come in," tura k'ofar suka yi suka shiga da Sallama.




Cikin fara'a Doctor Maryam ta amsa musu sallamar tare da cewa "m
"Maraba da yaron Ummi ku zauna," zama suka yi tare da gaishe ta ta amsa cikin murmushi sannan ta ce "Yaron Ummi yau Ina Ummin fa fatan tana lafiya?" K'asa Maleek ya yi da kansa yana sosa kai ya ce "Tana lafiya tana gida," Doctor Maryam ta ce "Masha Allah," ta fad'a tana gyara zaman farin glass d'in dake idanta.




Maleek ya ce "Mama dama wata magana ke tafe dani," ajiye biron hannunta Doctor ta yi ta ce "Tom Ina jinka,"





"Mama ko kinsan wani malam Abubakar a k'auyen meyere?" Maleek ya fad'a yana kallon ta hawaye ne ya zubo daga idanun Doctor Maryam sannan kamar an tsikare ta ta mik'e tsaye tana kallon Maleek ta ce "Wallahi nasan shi yana ina? Wanne hali yake ciki Ina yarana?" Ganin duk ta rud'e ne Maleek ya ce "Mama ki kwantar da hankalin ki please zauna," komawa ta yi ta zauna ta ce "Son please yana ina?" Ajiyar zuciya Maleek ya sauke ya ce "Come down Mama yana nan lafiya amma Mama meyasa duk tsawon lokacin nan baki neme sa ba?" Share hawaye ta yi ta ce "Bansani ba amma duk lokacin da nayi niyyar zuwa na duba lafiyar su sai wani abun ya d'auke mun hankali na rasa meyasa hakan ke faruwa dani bansan wanne hali yake ciki ba bansan halin da yarana ke ciki ba bazan iya jurewa ba yanzu zan tafi naje na ga halin da suke ciki," Maleek ya ce "A'a Mama ki kwantar da hankalin ki nayi miki alk'awarin had'a ki da mijin ki da kuma yaran ki duka," Nan dai Maleek ya yi ta kwantar mata da hankali har ta hak'ura.





Sabeeha na zaune a d'akin su Sameeha ta shiga d'akin ta zauna sannan ta kalli Sabeeha ta ce "Sabeeha sister kinsan me?" Girgiza Kai Sabeeha ta yi.




"Kinsan Sabreen sister ita taje ta yi mun aiki kafin naje a part d'in Umman Nasreen," nan dai ta bawa Sabeeha labari dariya Sabeeha ta yi ta ce "Kyale ta karki nuna mata kinsani ki

Please Login or Register in order to submit comment