Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

DABO (RUHAZ)




SADAUKARWA GA
MY DAUGHTER SABEEHA
BILKISU Z.YA'U (🅱️K)
AISHA MAGAJI DABO (AMA)





Page 2


Maleek na fita daga part d'in na Ummi ya nufa a garden ya hangi Nasrin zaune kan wata kujera sai zabgawa wata 'yar aiki mari take yi kamar wata uwar ta tsaki ya ja kamar Nasrin tasan Yana tsaye a wajen ta waiga suna had'a ido ta tashi da gudu ta nufe shi rungume shi tayi niyyar yi ya tsayar da ita ya ce "Meye haka?" Ya fad'a a d'an tsawa ce had'e fuska ta yi ta ce "Haba ya Maleek murnar ganin ka ce fa sannan kasan wani Abu kuwa jiya Daddy yazo sannan anyi maganar auren mu," kallon banza Maleek ya yi mata ya ce "Bangane me ki ke son fad'a ba kinga idan ma kina wasa ne ki dena nifa ban tab'a cewa ina sonki ba kinga maganar aure it is impossible thing,"


"Haba MG bangane auren mu bazai yiwu ba Amma aini ina sonka Kuma wallahi ko baka sona sai ka aureni," wani murmushi Maleek ya yi ya ce "Idan kin gama zaki iya barin nan wajen if not Wallahi saina buge ki stupid kawai," da gudu ta yi part d'in Umma tana kuka shi Kuma ya ja tsaki ya tafi.



Bud'e masa k'ofar falon sojan sa ya yi ya shige ya samu su Ummi zaune a falo suna kallo zama ya yi ba tare da ya yi magana ba Ummi ta ce "Muje kaci abinci son," duka daining suka nufa suka fara cin abinci sai dai shi Sam ba wani cin abincin yake ba tashi ya yi kawai yabar daining d'in ya koma falo ya zauna fuskar sa babu alamun wasa.



Ba Wanda ya yi masa magana har suka gama cin abincin sannan suka koma falon dukansu shafa kansa Ummi ta yi ta ce "My son meye matsalar?" Kallon ta ya yi ya ce "Ummi dagaske ne maganar da Nasreen ta fad'amun wai za ayi mana aure ni da ita?" Jiki a sanyaye Ummi ta ce "Hak'uri zaka yi son kasan halin yayan Daddyn ku Sam bashi da hak'uri jiya haka yazo nan ya dinga fad'ar maganganu har Daddyn ku ya kira dole ya baro Landon yazo aka yi maganar auren yanzu haka one month aka sa bikin shiyasa mahaifin ku ya kira ka ya ce lallai ka dawo a yau," cije leb'e MG ya yi sannan ya ce "Yanzu Ummi ina Daddy yake?"



"Ya koma Landon yau da safe," jinjina kai Maleek ya yi sannan ya ce "Ummi Sam bansan meyasa Uncle yake son ganina a cikin damuwa ba sannan ni fa ba sonta nake ba," Ummi ta ce "nasani son amma kayi hak'uri wata rana sai labari," gyad'a kai ya yi ya mik'e ya fice.



Part d'in sa ya koma ya kwanta bacci ne ya d'auke shi.



Nasreen Kuma da kuka ta shiga falon ta fad'a jikin Umma a rikice Umman ta ce "Lafiya Nasreen mai ya faru?" Cikin kuka ta ce "Umma Wai kinji baya sona," tsaki Umman ta ja ta ce "kyale banza duk da baya sonki aure ke da shi babu fashi ya yi duk abinda ya ga dama amma sai ya aure ki Kuma mun kwashe dukiyar d'an iska," Nan dai Umma tai ta rarrashin ta.



B'angaren 'yan uku kuwa Sabeeha ce a kitchen tana yin girki Rashida ta shiga sai wani shan k'amshi take tana yatsina ko kallo bata ishi Sabeeha ba fridge ta bud'e ta d'auki ruwa ta juya zata fita Sabeeha ta ce "Rashida baki ji ba," waigawa Rashida ta yi ta ce "Lafiya kuwa?" K'arasawa gaban ta Sabeeha ta yi ta ce "Akwai maganar da nake son fad'a miki amma sirri ce bana so wani yaji,"



"Ina jinki," cewar Rashida murmushin mugunta Sabeeha ta yi sannan ta ce "Wai kuwa kinsan yallab'ai yana mutuwar sonki kuwa?" Zare ido Rashida ta yi kamar gaske ta ce "nidin Kuma?" Gyad'a kai Sabeeha ta yi ta ce "sosai ma domin jiya naji yana waya Yana sanarwa da abokin sa shi duk duniya ke yake so," tsalle Rashida ta yi ta ce "Nagodewa Allah dama Wallahi ina mutuwar son shi kamar raina amma dan Allah ki tayani rufe sirrina bana so Farida ta sani dan gaskiya ina tsoron hukuncin da zata yanke mun," tsaki Sabeeha ta yi ta ce "karki damu ni nan zan taimake ki karki damu tunda ai shima Yana son ki kinji?" Gyad'a kai Rashida ta yi cike da gamsuwa sannan ta ce "Amma aike d'in bangane ki ba a cikin 'yan ukun?" Tab'e baki Sabeeha ta yi ta ce "Manta kawai ni dai burina na taimake ki dan haka karki damu kanki wajen sanin wacece ni cikin 'yan uku," tana gama fad'in haka ta juya ta cigaba da abinda take yi Rashida Kuma ta fita zuciyar ta fal farin ciki.


Haka Sabeeha tai ta jan Rashida tana zugata akan cewar Yallab'ai na mahaukacin sonta ya yinda shi baima san wainar da ake toyawa ba.



Zaune Yallab'ai yake shida wani gabjejen abokinsa suna fira yallab'ai ya kalli abokin sa cikin k'atuwar muryar sa ya ce "Gaskiya Habibu ina mutuwar son yarinyar nan dake yi mana girki a cikin gidan mu saboda gata doguwa kyakkyawa ga iya girki dan tunda nake a rayuwata ban tab'a cin girki mai dad'in na ta ba," jinjina kai Habibu ya yi ya ce "Yanzu kana nufin auren ta zaka yi ko me?" Gyad'a kai Yallab'ai ya yi ya ce "Sosai ma kuwa kawai abinda nake so da kai shine kai nake son aikawa wajen ta," Habibu ya ce "Haba dai ai gara kaje da kanka ka gaya mata," girgiza kai Yallab'ai Kamis ya yi ya ce "A'a gaskiya kamar ni da matsayina naje wajen ta bayan 'yar aikina ce," Habibu ya ce "Shikenan yanzu yaushe zan same ta d'in?"


"Ka bari zanyi ma magana kawai," Habibu ya ce "To Shikenan an gama," haka firar ta su ta tashi.



Sabeeha ce ita da Rashida a kitchen suna fira idan ka kalle su zaka d'auka k'awaye ne domin fira suke suna dariya kamar gaske Rashida ta ce "Yanzu kina ganin anjima ya yi daidai dana fad'a masa abinda ke zuciya ta?" Gyad'a kai Sabeeha ta yi ta ce "Sosai ma kuwa d'azu ya kirani yake ce mun Wai Yana son ki ya lura kwana biyu munfi kusa ni da ke shiyasa ya fad'a mun sannan anjima Yana neman ki a falon Farida," d'an zare ido Rashida ta yi ta ce "Amma kina ganin ba matsala?"


"Bawani matsala gani nake yi ya yi hakan ne dan ba k'aramun so yake Miki ba kuma son naki ne yasa yace kije har falon Farida dan da alama so yake ya nunawa Farida kalar son da yake Miki," wani wawan tsalle Rashida ta yi ta ce "Wayyo dad'i Amma nagode sosai," cikin murmushi Sabeeha ta ce "Karki damu," haka suka gama hirar su Sabeeha ta tafi tabar Rashida a kitchen domin dama kawai fira ce ta kai su kitchen d'in.



Da yamma Yallab'ai Kamis da Farida na zaune a falon Farida suna yin fira sai Sabeeha ta shiga falon d'auke da tray a hannunta da fruits a ciki har k'asa ta tsugunna ta gaishe su Yallab'ai Kamis ne kawai ya amsa yayin da Farida ta galla mata harara dan ita bata son ganin wacce ta fita kyau musamman idan mijin ta na wajen.



Sabeeha kuwa tana ajiyewa ta mik'e ta fita tana fita ta kalli Rashida dake tsaye tasha kwalliya ta ce "Yace ki shiga," cikin farin ciki Rashida tasa kai cikin falon ya yinda Sabeeha ta mak'ale tana lek'e tana dariyar mugunta.



Da sallama Rashida ta shiga sai wani yanga take tana lankw'asa jiki da kallon Mamaki suka bita ba tare da wani tunani ba Rashida ta k'arasa ta zauna d'ayan gefen Yallab'ai Kamis ta ce "Barka da hutawa masoyina a gaskiya naji dad'in cewar da kayi kana sona dama Kuma na dad'e ina mahaukacin sonka dama damuwata ka ce baka sona Amma tunda ka furta hakan da bakin ka cewar kana sona naji dad'i sosai sannan ina so asa bikin babu yawa saboda bana so abin ya yi nisa nafi so asa nan kusa domin na baka kulawar da ta dace ba irin ta wawiyar matar ka ba," duk abinda take da kallo suka bita sai da ta kai k'arshe sannan Yallab'ai ya mik'e ransa a matuk'ar b'ace saboda ba wacce ma bata kwanta masa a rai cikin 'yan aikin gidan ba kamar Rashida dan dai kawai Farida na sonta ne yasa bai kad'a keyar ta gidan su ba.



Ya ware zabgegen hannunsa ya zabgawa Rashida Marin da sai da ta fad'o daga kujera tana ganin stars bata gama wartsakewa ba ya Kuma k'ara mata wani Marin ya yi ball da ita har sai da ta buge da jikin kujera goshin ta ya fashe kuka ta fashe da shi tana ihu.



Cikin k'atuwar muryar sa ya ce "Ke dan uwar ki ni sa'an ki ne da zaki zo kice kina sona shegiya munafuka so kike ki had'ani da sarauniya ta ko?" Farida ma cikin b'acin rai ta mik'e ta ce "Dama duk abinda ki ke yi dan ki aure mun mijine aikuwa Wallahi yau sai kinci uban ki a gidan nan sannan daga yau sai kinbar gidan nan munafuka kawai," duka suka rufe Rashida da shi sai ihu take yi gashi babu Mai ceto.



Sabeeha tana daga waje har rik'e ciki take yi saboda dariya sannan ta nufi d'akin su da gudu tana k'wala Kiran "Sabreen sister Sameeha dear kuzo ku yi kallo," da gudu suka fito suka bita ragowar 'yan aikin gidan jin ihun da 'yan uku ke yi suma suka fito suka nufi falon su ma.



Kowa tsayawa ya yi Yana kallon yadda Farida ke yawo Rashida daga bene sunyi mata jinajina sai ihu take yi tana bada hak'uri Amma ko sauraron ta basa yi har tsakiyar falon suka jawo ta suka yi wurgi da ita zabgegiyar dorinar hukunci Yallab'ai ya karb'a ya fara zabga mata sai ihu take yi har sai da ta kasa motsi sannan ya kyale ta ya koma gefe ya zauna.



Sabeeha kuwa har lokacin dariya take yi harda rik'e ciki wani farin ciki take yi Sabreen ma sai taya ta dariyar take yi Sameeha kuwa tun tana dariyar har ta koma kuka tsabar tausayin Rashida galala su Sabeeha suke kallon yadda take hawaye sannan suka cigaba da dariyar su.



Farida ta ce "Dan uban ki ki dena yi mana ihu a falo ki tashi ki bar mana gida ko insa a fitar dake daga cikin gidan nan," mik'ewa Rashida ta yi dakyar tana tafiya har wani layi take yi suna had'a ido da 'yan uku Sabeeha ta kashe mata ido d'aya.



Juyawa Rashida ta yi ta fita daga gidan ya yinda kowa ya watse.



Da murna su Sabeeha suka shiga d'akin su sai taka rawa suke yi ita da Sabreen ya yinda Sameeha ta zauna gefen gado tana kallon su.



Sabreen ta d'ebo shoky tana cewa "Sabeeha dear saura Kuma Farida itama ta gane kuren ta," Sabeeha rawa take yi kamar wata macijiya ta ce "Ai yanzu aka fara wasan," Sameeha ta ce "Ni dai please Sabeeha sister ki dena abun nan," ko kallon ta basu yi ba suka cigaba da rawar su sai da suka yi Mai isar su sannan ko wacce ta tafi wajen aikin ta.


Zaune Maleek yake a falon sa wasu takaddu yake dubawa wani soja ya shiga falon ya Sara masa sannan ya ce "Ranka ya dad'e kana da bak'o," sai da ya ajiye takardar hannun sa sannan ya kalli sojan ya ce "waye?" Cikin ladabi sojan ya ce "Umar ne ranka ya dad'e," cikin Mamaki Maleek ke kallon sojan sannan ya ce "Ok ya shigo mana," sanna ya cigaba da abinda yake yi.



Umar ne ya shiga falon ya k'arasa gaban Maleek ya Sara masa hararar sa MG yayi sannan ya ce "Yau Kuma me ka ke ji da sai an nema maka izinin ganina?" Zama gefen sa Umar ya yi ya ce "Wallahi Maleek baka da kirki yanzu ka shigo gari Amma ba labari yanzu ma fa sai da na je wajen Ummi ne Rinaz ke fad'amun ka dawo shiyasa ma yanzu nace a nema mun izini kar nazo a harbe ni tunda haushina ake ji," kad'an Maleek ya yi murmushin gefen baki sannan ya kalli Umar idanun sa sunyi jajur ya ce "Umar kasan auren dole?" Dariya Umar ya yi ya ce "Yeah I know it but for what reason ka tambaye ni?" Tab'e baki Maleek ya yi ya ce "To shi za ayi mun," Ware ido Umar ya yi ya ce "Kai haba dai amma you are joking?" Mtswww Maleek ya ja tsaki ya ce "Umar I'm not joking I'm serious Wai ko ka manta halin Uncle ne yanzu haka fa bikin bai fi 3 weeks ba," jinjina kai Umar ya yi tare da cewa "Kenan mu fara shiri?" Tsaki Maleek ya ja ya tashi ya fice.



Bin bayan sa Umar ya yi dan yasan haushi ya ji da sauri ya tarar da Maleek dake tafiya shi da Salman ya ce "Sorry MG amma dai ba Nasreen ba ce ko?" Ba tare da Maleek ya kalle shi ba ya ce "Ita mana," daga haka ya wuce ya yafi part d'in Ummi.



Salman ya kalli Umar ya ce "Amma Umar abinda ake yiwa MG Sam ba a kyauta masa Dan ma dai mai biyayya ne shiyasa," Umar ya dafa kafad'ar Salman ya ce "Captain Nima abin na damuna Wallahi Amma kawai mu taya shi da addu'a kawai," haka suka cigaba da tattaunawa akan matsalar dake faruwa a gidan.



Da Sallama Maleek ya shiga falon Ummin sa ya zauna akan kujera ya jingina a jikin kujerar Yana tunanin damuwar da yake ciki ji yayi falon ya d'auka da "Fauwaz is open the door," har lokacin bai ko bud'e idanunsa ba.



Fauwaz ne ya shiga falon kunnen sa manne da ear piece yana rera wak'ar fire boy ta like I do har wani kad'a kai yake yi Yana bin wak'ar "e-sure for you baby I'm going no where your love is true I know you always be there no one can take my place bad energy stay fa...," Tsawar da Maleek ya yi masa ne yasa shi saurin cire ear piece d'in jikin sa har d'an rawa yake yi dan tsoro.



"Zo nan," Maleek ya ce Yana k'ara had'e fuska kamar bai tab'a dariya ba k'arasawa Fauwaz ya yi ya zauna k'asan carpet Dan yau ya ga ba wasa kallon sa Maleek ya yi ya ce "Kai Wai meyasa baka jin magana ka shigo waje babu ko sallama," Fauwaz ya ce "Sorry ya Maleek bazan sake ba," d'aga kafad'a Maleek ya yi ya ce "Is left for you," Rinaz ce ta k'arasa falon tana yiwa Fauwaz dariya k'asa k'asa.



Hararar ta Fauwaz ya yi sannan ya cije baki ya kalli Maleek ya ce "Yaya kasan kuwa me Rinaz ta yi da baka nan?" Duk da yana cikin damuwa sai da ya girgiza kai domin yana so ya ji halin da k'annen nasa ke ciki domin rayuwar yanzu sai a hankali musamman shi da ya san baya rasa mak'iya.



Fauwaz ya ce "Last week fa Rinaz ta fita unguwa tun around 5:00pm bata dawo ba sai wajen 10 Wai ta tafi birthday party d'in friend d'in ta," jinjina kai Maleek ya yi tare da kallon Rinaz da ta yi tsilli tsilli da ido ya ce "Haka ne?" Cikin rawar murya ta ce "Sorry ya...," Tsawa ya daka mata ya ce "Don't sorry me I just ask you haka ne!" Noding kanta ta yi sannan ta ce "Kuma wallahi yaya shima fa bro kullum sai cikin dare yake dawowa kuma kullum sai Ummi ta yi masa fad'a," Girgiza kai Maleek ya yi Yana binsu da ido sannan ya ce "Ok yanzu nagane wato duk ranar da bana nan duk abinda kuka ga dama shi kuke aikawata ko?" A tare suka girgiza kai kwafa ya yi ya ce "You really know bazan ce ku dena ba dan Allah ku cigaba da duk abinda ku ka ga dama," yana gama fad'in hakan ya ce "Kun isheni da zama da anan," da sauri suka bar wajen suna hararar juna.



Falon ne ya d'auka da "Ummi is open the door," k'ofar Nabil ya kalla sannan ya mik'e ya nufi inda take rungume ta ya yi ta yi masa kiss a for head d'insa ya ce "Sannu da dawowa Ummi," ya fad'a tare da karb'ar hand bag d'inta suka k'arasa falon ta zauna a gajiye tare da cire farin glass d'in dake idanun ta.



Ya ce "Ummi Sannu shiyasa nace ki hak'ura da aikin nan Ni Sam banga amfanin hakan ba," hararar wasa ta yi masa ta ce "Yanzu kai taimakon al'umma ne bai da amfani bayan kaima abinda ka ke yi kenan," murmusawa ya yi ya ce "Amma Ummi ai ni daban zuwa yanzu kamata ya yi ki zauna ki huta a gida zuwa asibitin ya isa haka," banza ta yi da shi ta k'wala Kiran "Hadiza," wata budurwa ce ta fito daga kitchen d'auke da wani had'adden tray mai d'auke da ruwa da drinks da glass cups ta ajiye akan center table ta ce "Sannu da dawowa Ummi," cikin fara'a Ummi ta ce "Yawwa Hadiza da fatan komai lafiya," Hadiza tana satar kallon Maleek ta ce "Lafiya lau Ummi,"



"Ok kun gama girki ne?" Cikin ladabi ta ce "Eh mun gama," gyad'a kai Ummi ta yi ta ce "Me ku ka girka?" Murya na rawa Hadiza ta ce "fried rice with coslow and papper chicken then white rice with fish soup and fruits salad an...," Tsakin da Maleek ya ja ne ya hanata k'arasa fad'in abinda zata fad'a dan mugun tsoron sa take ji gashi da kwarjini.


Kallon sa Ummi ta yi ta ce "Son me za a kawo ma?" Kallar tausayi ya yi ya ce "Ummi fa ni naki nake so dukan su ba abinda suka iya," girgiza kai Ummi ta yi ta ce "Ni yanzu Son na gaji amma ka fad'i wacce kake so ta yi ma girki cikin Hadiza,Salma,Halima,Yasira,Zainab,Hajara ko fati?" Kamar zai yi kuka ya ce "Ummi duka basu iya ba,"



D'aukar waya Ummi ta yi kira ana d'agawa ta yi sallama suka gaisa sannan ta ce "Yawwa Fulani ina so ki samo mun 'yan aiki wad'an da suka iya girki," tana gama fad'in haka ta kashe wayar tana yiwa MG hararar wasa ta ce "Wallahi na gaji da rigimar ka," tana gama fad'in haka ta yi stairs shi Kuma ya kalli Hadiza ya ce "kina jiran meye ne?" Da sauri tabar wajen har tana tuntub'e.




Sabeeha ce kwance a d'akin su da yamma wata 'yar aiki ta yi sallama ta ce "Kece Sabeeha?" Gyad'a kai Sabeeha ta yi.



"Ki zo inji Yallab'ai," ba tare da tsoro ba ta ce "Gani nan," ta tashi sanye da dogon hijabin ta ta fita a hanya suka had'u da Sabreen dake komawa d'aki.



"Sabeeha dear ina zaki?" Tab'e baki Sabeeha ta yi ta ce "Wai Kamis ke kirana," zare ido Sabreen ta yi ta ce "Dafatan dai lafiya?"


"Nima bansani ba amma kije yanzu zan dawo," tana fad'in haka ta tafi Sabreen ta bita da kallo Dan gani take yi kamar za ace laifi Sabeehan ta yi.



A falo ta samu Yallab'ai shi da Habibu tana zuwa Kamis yabar wajen Yana binta da wani irin kallo ita kuma tana hararar sa.



Habibu ya ce "k'araso mana 'yan mata," k'arasawa ta yi ta zauna k'asan carpet ta ce "Gani," Nan fa Habibu ya zayyane mata dalilin kiran ta wani murmushin mugunta Sabeeha ta yi ta ce "Kace masa na amince zan aure shi," shi kansa Habibu ya yi mamakin saurin amsawar da ta yi Amma ya fuske ya ce "To ba damuwa mun gode," sannan ya d'auko kud'i wajen dubu hamsin ya bata karb'a ta yi har da godiya ta tafi.




Ko da Kamis ya ji yadda suka yi ba k'aramun dad'i ya ji ba Dan ranar har kyauta ya yiwa 'yan aikin gidan abinda bai tab'a ba su kansu mamaki suke yi.



Nan fa kusan kullum sai ya aika an kira ta sunyi fira ba tare da Farida ta saniba.



A haka aka yi sati d'aya Sabeeha da Kamis suna kwasar soyayya kamar gaske.



Yau ma firar suka gama ta nufi d'akin su tana farin ciki da sallama ta shiga d'akin Sabreen ta tare ta tana cewa "Ka ga ta Yallab'ai," dariya suka yi harda tafawa ta ce "Mu zauna Sabreen dear akwai labari," zama suka yi ta ce "kinsan mene yau nace da Kamis ya sanar da matar sa yana sona Kuma aurena zai yi," Sameeha ta ce "Shikenan mun shiga uku yanzu Sabeeha dear abinda ki ka jawo mana kenan," Sabreen ma a tsorace ta ce "Amma sister kina ganin hakan bazai jawo mana matsala ba?" Sabeeha ko a jikin ta ta tab'e baki ta ce "Manta ba abinda zai faru ba dai saura kwana hud'u ayi salary ba ranar zamu bar gidan nan sannan zuwa lokacin ku zuba ido ku ga abinda zai faru,"



"Son gobe nake so na tafi Dubai ni da Asiya da karimatu Amma ba dad'ewa zamu yi ba bai fi muyi 3 to 4 days ba," Maleek dake gefe yasha kyau cikin jajayen k'ananun kaya ya ce "Me zaku yi a can?" Ummi ta ce "ka manta bikin ka bai ma kai 2 weeks ba zamu je had'o lefe mana," take ya had'e rai kamar bai tab'a dariya ba.



"Haba yaron Ummi dan Allah ka saki ranka kasan auren nan ba fashi kayi hak'uri ayi a gama lafiya ka cigaba da yiwa mahaifin ka biyayya kaji?" Noding kansa ya yi cikin damuwa sannan ya ce "To Ammi maganar abinci fa?" Dariya ta yi ta ce "Yadda ka ke damuwa da maganar abinci da haka ka ke cinsa da kafi haka girma to ban da rigima irin taka Kai da zaka yi aure ai matar ka ce zata dinga girka ma," shiru kawai ya yi ba magana.



Washe gari Ummi da Maman Umar da Umman Salman suka tafi Dubai had'o lefen auren Maleeek.



B'angaren amarya Nasreen kuwa shiri suke yi ita da friends d'in ta sai shirya events take yi bata damu da yadda Maleek baya ko kiranta ta waya ba hidimar ta kawai take yi tana cin uwar kud'i kamar central bank a gidan yake sai rawar Kai take yi zata auri kyakkyawan jarumin namiji Mai dukiya ya yinda friends d'inta kowa burin sa ya ga MG Maleek.



Shi kuwa a nasa b'angaren ko a jikinsa har mantawa yake yi Wai aure zai yi idan ba zancen aka yi masa ba.


Kwanan su Ummi hud'u a Dubai suka koma tare da kayan lefe akwatuna ashirin da hud'u Maleek da kansa tare da sojojinsa da Kuma Salman da Umar suka je suka tari iyayen nasu.



Ko da suka koma gida ana nunawa Maleek kayan ko kallon basu ishe shi ba daga k'arshe ma tashi ya yi yabar wajen su Umar suka bi bayansa Dan suma jinin su bai had'u da amaryar ba Dan bata da kirki kwata kwata ga wulak'anci da girman kai da rashin girmama na gaba da ita.



A haka akai ta shagali ya yinda Rinaz itama Sam bata son Nasreen Dan tunda aka fara Shirin bikin bata wunin gidan.



Ballantana Fauwaz da ko kallo Nasreen bata ishe shi ba Dan da Yana da hali yayan sa bazai aure ta ba dan Sam bata da kamun Kai.




A b'angaren uwar amarya Umma shiri take yi sosai na aurar da tilon 'yar ta.



A haka aka fara gabatar da events ba tare da ango ya lek'a ko nan da can ba amarya ma bata damu ba domin gayyar maza abokan ta ta yi suka dinga shek'e ayar su duk abinda ke faruwa Maleek Yana sane sai dai shi ko a jikin sa.


Wuni yake yi a part d'in sa dan ko part d'in Ummi baya zuwa saboda yasan cike yake da bak'i kullum Yana tare da Umar da Salman idan ba a fad'a ma ba bazaka ce bikin sa ake yi ba dan uzurin gaban sa kawai yake yi.


A gobe d'aurin aure Daddy da Uncle suka dira a Nigeria.


Maleek ya fito kenan cikin Shirin masallaci kasancewar juma'a ce ya ga motocin su Daddy na shigowa gidan kallo d'aya ya yiwa motocin ya d'auke Kai ya kalli Salman ya ce "Salman muje ko?" Mota suka shiga suka

Please Login or Register in order to submit comment