Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

miki gida," mak'e kafad'a ta yi "Ni banso kawai matar ka ta biyani,"



"Toh shikenan amma Baby Wanda ya mutu fa baya dawowa fa ji mana ba sai kun kawo mana ba Queen d'in tawa ta dena ra'ayi" ya fad'a yana kallon ma aikatan wajen sannan ya bud'e mota yasa 'yar rigimar sa ya zagaya ya shiga suka nufi gida ranar dai kwana Sabeeha ta yi kuka Maleek na aikin rarrashi.



B'angaren Sadam kuwa zaune yake yana jiran fitowar Zainabu zuwa part d'in Doctor domin wannan karon yace sai ya yi Mata magana duk abinda zai faru ya faru domin ya lura indai ya ganta sau d'aya a rana baya sake ganinta gashi hak'urin sa ya k'are.




Yana cikin tunanin ne sai gata ta fito cikin doguwar rigar material red tayi kyau kam da sauri ya nufi wajen ta yana cewa "Zainabu! Zainabu!" Tsayawa ta yi cak sannan ta juya ta kalle shi sannan ta keb'e baki ta ce "Me kace?"


"Zainabu ki saurareni Wallahi nayi nadama,"


"Mtsww waye kuma Zainabu ni Zainab nake," daga haka ta cigaba da tafiya sake shan gaban ta ya yi ya durk'usa a gabanta ya ce "Zainabu ki tausaya mun Wallahi nayi nadama nasan kece matata please ki tausayamun Wallahi Ina sonki Ina son yarona yana Ina?" Banza ta yi masa zata tafi ya rik'o k'aramun veil d'in kanta a fusace ta waiga ta zabga masa mari ta ce "Kai har wani d'a gare ka ka ga ka fita a rayuwa ta ni bansan ka ba haba," daga haka tayi shigewar ta ta barsa a wajen a tsugunne.




Dafa shi malam Musa ya yi ya ce "Na fad'a maka Zainab d'in mu ba Zainabun ka bace gashi ka jawa kanka mari yi hak'uri ka taso tunda ta ce ba ita bace ka kyale ta," tashi kawai Sadam ya yi suka je suka zauna shida gate man.



Zainabu kuwa tana shiga falon zama ta yi ta fashe da kuka tabbas taji tausayin sa sai dai idan ta tuna abinda ya yi Mata sai taji tana jin haushin sa duk da kuwa soyayyar da take masa sai da ta ci kukan ta sannan ta fita zuwa part d'in su kunnuwan ta suka jiye Mata Sadam na fad'in "Musa bazan iya zama a gidan nan Ina kallon Mai kama da matata ba kawai zan tafi neman matata wacce nake k'auna idan har ban same ta a k'auye ba to bazan dawo nan ba a k'auyen ma bazan zauna ba zan shiga duniya Musa na aikatawa Zainab kuskure Amma nayi nadama ta haifar mun yaro amma banko tab'a ganinsa ba nayi nadama," wuce su tayi tana jin ba dad'i a ranta tana shiga part d'in su ta Kira Sabeeha ta kora mata jawabin abinda ke faruwa Sabeeha ta ce "Manta kawai ba abinda zai faru insha Allah kinji," Nan dai ta kwantar mata da hankali sannan suka yi sallama.




Bayan kwana biyu Sabeeha ta tashi da wani zazzafan zazzab'i ba b'ata lokaci Maleek ya d'auke ta suka je wajen Ummi ta dubata ba b'ata lokaci aka yi gwaje_gwaje inda Ummi ta tabbatar musu da Sabeeha na da ciki na sati hud'u babu ko kunya gaban Ummi suka rungume juna suna murnar samun cikin ita Kuma Ummi nayi musu dariya.



Haka Maleek ya ninka kulawar sa akan Sabeeha ita Kuma tana ajiye masa rigima iri_iri ta ce Bata cin wannan sai wancan shi Kuma yana biye mata zancen ciki kuwa ba Wanda bai ji shi ba Nasreen kuwa tunda Maleek ya yi Mata mummunan duka take mugun jin tsoron sa ko zaman falo ya gagare ta kullum tana d'aki sai dai suna nan suna k'ulla makircin su ita da Jamila.




Bayan one week Maleek da Sabeeha suka shirya domin zuwa gidan Doctor sunyi kyau sosai ba k'arya cikin shadda light blue shadda kamar ka sace su ka gudu Sabeeha tayi using da pich color d'in takalmi da jaka da mayafi sai k'amshi suke yi.


Mota aka bud'e musu suka shiga suka d'auki hanya jiniya kawai ke tashin a garin har k'ofar part d'in Doctor suka yi parking suka shiga Sabreen suka hanga akan daining tana cin aminci sai Sameeha a gefen Mama.




Sameeha na jin sallamar su ta k'arasa da gudu suka rungume juna da Sabeeha suna murnar ganin juna haka ma Sabreen sai da suka gama murna suka gaida Maleek sannan Sabeeha ta k'arasa gurin Doctor da gudu ta fad'a jikin ta tana cewa "I really miss you Mamana,"


"Ku dai bakwa girma Wallahi ni d'agani," kwab'e fuska tayi ta kalli Sabreen ta ce "Wai sister haka Kuma Mama tayi muku," dungure Mata kai Doctor ta yi ta ce "Ku fa kiyayeni," tura baki ta yi ta koma can kusa da Maleek ta koma tana tura baki su Sabreen na Mata dariya Aikuwa sai tasa kuka su abin ma mamaki ya basu duk da sun santa da saurin kuka amma abin bai kai haka ba.



Rarrashin ta Maleek ya fara ya ma manta a inda yake sai rungume ta yake yi Mama kuwa kunya ma suka bata.



"Yarinya da anyi magana sai kuka kamar wata jaririya," Doctor ta fad'a cikin fad'a.


"Dan Allah Mama kiyi hak'uri saboda ba ita kad'ai bane shiyasa,' ihun murna falon ya d'auka Domin ba Dan Maleek ba da rawa zasu taka a wajen.



Doctor Kuwa girgiza Kai kawai ta yi tana murmushi ranar dai wunin gida Mama suka yi sannan suka koma gida.


Sadam ne zaune ya zabga uban tagumi a wajen malam Musa sai Kuma kamar an tsikare shi ya mik'e "Ina Kuma zaka irin wannan irin zumbur haka ko kashi kake ji," harara Sadam ya aika masa ya ce "Ka ga Ni ka kyale ni kayana zan d'auko yanzu ba sai anjima ba zanbar gidan nan," yana fad'ar haka ya fara tafiya.




Daga d'aki Zainabu ta fito ta kalli Lantana dake zaune ta ce "Umma Habib fa ya fito a d'aki Yana Ina?"


"Ke yanzu Banda ke shashasha ce Zainabu yaro ya fito sai yanzu Zaki biyo bayan sa bayan kinsan k'ofar fita a bud'e take," Zainabu ta ce "Wallahi Umma na d'auka yana ta wajen ki ne amma bari na duba shi," tana fad'ar haka ta yi hanyar fita da sauri tana neman Habibi kasancewar rarrafe yake yi.



Tana fita ta hange shi yana rarrafawa compound d'in gidan d'an girgiza Kai ta yi ta nufi wajen sa da sauri ta d'auke shi tana fad'in "Kai kuwa yaro ka fito waje haka," waigawar da zata yi suka yi ido hud'u da Sadam dake bayan ta Yana kallon ta tare da yaron hannun ta da ko ba a fad'a masa ba yasan d'ansa ne saboda kamar da ya ga yaron nayi da shi.



Sharewa ta yi zata tafi ya yi saurin cewa "Zainab ki saurareni Dan Allah karki yi k'ok'arin raba miji da matar sa da Kuma d'ansu please," bata ce komai ba ta juya ta shige.




Ya dad'e a tsaye yana tunani sannan ya nufi wajen gate ya zauna ya kalli Malam Musa ya ce "Waye yace maka Zainab d'in ku ba Zainabu ta bace to itace matata domin yanzu na ganta da yarona a hannunta," tab'e baki Malam Musa ya yi shi lallai bai yadda ba.



Aikuwa ranar Sadam ya ga Kawu ya shigo gidan nan ya tare shi Yana yi masa kuka Yana rok'an sa hakan ne yasa Kawu ya jashi har falon su ya Kira Abba a waya har da Doctor suka zauna aka yi sasanci sannan Abba ya yiwa Sadam kyautar gidan da zasu zauna sai godiya yake yi shi da Zainabun sa Nan da sati d'aya zata koma.


Bayan wata abubuwa sun faru ciki har da komawar Zainabu gidan Sadam inda suke shan soyayya.



Sabeeha ce Zaune a falon su lokacin Maleek baya nan saboda yanzu baya samun zama saboda yawan meeting da suke yi yau ma tun safe ya fita zaune kawai Sabeeha take amma gaba d'aya bata jin dad'in jikin ta ga yawan fad'uwar gaban da take yi a 'yan kwanakin kawai tana daurewa ne jin zaman ita kad'ai ya dame ta ne yasa ta tashi ta zura hijabin ta ta fita zuwa part d'in Ummi.




Har zata hau Mota da yanzu ta iya sai Kuma ta fasa ta tafi da k'afa wata bak'ar mota ta gani ta yi parking a k'ofar part d'in Umman Nasreen haka kawai taji hankalin ta bai kwanta da motar ba can sai Uncle ya fito daga motar da sauri kamar zai kifa ya shige cikin part d'in.




Mamaki ne k'arara a fuskar Sabeeha to meyake faruwa da Uncle haka ta fad'a cikin zuciyar ta sannan Kai tsaye nufi sashen gaban ta na fad'uwa a daidai window d'in cikin falon ta lab'e.


"Eh daughter ta yi wannan aikin tun jiya da daddare sannan idan har ya taka maganin to zuwa yanzu ya fara jin sauyi a jikinsa domin 3 hours maganin ya fara aiki sannan sai matar sa kamar yadda ka fad'a a daren yau za a d'auke ta," Uncle ya fad'a sannan Kuma ya kyalkyale da dariya ya ce "To dama Baba me aka yi aka yi uban Abdul-maleek ma ballantana shi Maleek d'in ai kawai kasa a ranka munyi aikin mu mun gama," ya fad'a yana fashewa da wata muguwar dariya.



Zare ido Sabeeha ta yi tasa hannunta ta toshe bakin ta saboda kukan da ya taho mata a hankali take ja baya a zuciyar ta ta ce wanne magani suka sawa sweetheart me yake nufi da maganar sa da wani mugun gudu tayi part d'in Ummi tana shiga ta fad'a jikin Ummi tasa wani kuka Mai ban tausayi.




A rikice Ummi ke tambayar ta maiya faru amma ba amsa sai kukan da take yi kamar mak'ogoron ta zai fashe.



Maleek da fitowar sa kenan daga meeting cikin kakin sojojin sa ya yi kyau har ya gaji sai dai wani iri yake ji a jikin sa kamar anyi masa duka gashi kamar ana tsotse masa jinin jikin sa a haka ya k'arasa gaban motar sa Salman ya bud'e masa ya shiga ya zauna wayar sa ce ta fara ringing d'agawa ya yi.



"Yallab'ai akwai matsala dafatan dai baka shiga motar ka ba saboda ansa mata magani a ciki Wanda idan ka taka shi shikenan zaka kamu da cutar mutuwar b'arin jiki ba abinda zaka ji ko anyi maka magana sannan baza ka yi magana ba Yallab'ai wallahi akwai matsala domin idan ka kwanta shikenan zasu samu damar shigo da kayansu Nigeria sunyi shiri sosai," katse Kiran kawai Maleek ya yi ya lumshe idanunsa sannan ya bud'e idanunsa ya kalli inda k'afafun sa suke tsirawa gurin ido ya yi sai lokacin ya lura da wani garin magani bak'kk'irin a inda k'afar sa ke Kai gaban sa ya yi muguwar fad'uwa bai iya cewa komai ba har suka isa gida ya kalli Salman ya ce "Salman yi parking k'ofar part d'in Ummi," ana yin parking ya fito daga motar.



Ya tsaya ya kalli duk sojojin sa da suka zagaye shi sannan cikin muryar sa mai dad'i ba tare da wani tsoro ba ya ce "Na samu labarin shigo da makamai k'asar nan kwanan nan abinda nake so daku a yanzu kuje jaji da NDA ku had'a duka runguna ta ku rabu duk wata hanya da ku kasan zasu iya biyowa Salman Kai kuma zaka zauna a tare dani su Kuma dukan su zasu tafi yanzu wish you all the best," har Salman zai yi magana ya d'aga masa hannu su Kuma sojojin suka shiga shiga motocin su suka bar gidan.



Waigawa Maleek ya yi ya kalli Salman "Sir me yake faruwa ne haka?" Hawaye ne suka fito daga idanun Maleek abun ya matuk'ar tsorata Salman.


Bayanin abinda ke faruwa Maleek ya yiwa Salman sannan ya ce "Salman na fad'a maka hakane saboda yaddar da nayi maka sannan na damk'a amanar family na a hannunka kar wani abu ya same su sannan kar wani yasan da wannan maganar sannan ko bayan na kwanta kar Wanda ya yi k'ok'arin nema mun magani domin hakan bazai yi amfani ba," kuka sosai Salman yasa kamar ba soja ba sannan ya rungume Maleek shi kuwa Maleek yana yin da yake ji a jikinsa ya fara fin k'arfin sa a hankali yana jan k'afa ya shiga falon Ummi.


Da gudu Sabeeha ta je ta rungume shi ta fashe da kuka a hankali kamar ana Shak'e shi ya ce "Baby meya faru?" Kasa magana ta yi jin yadda muryar sa ke fita.



Kafin kace me ya sulale k'asa a wajen baya yin motsi da gudu Ummi ta k'arasa wajen tana Kiran sunansa Sabeeha kuwa jikin sa ta fad'a tana fashewa da kuka.
[10/25, 8:55 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️


RUBUTAWA DAGA
HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ)



SADAUKARWA GA
MY DAUGHTER SABEEHA
BILKISU Z.YA'U (🅱️K)
AISHA MAGAJI DABO (AMA)



Page 31


Iya rud'u rikici da tashin hankali Ummi da Sabeehs sun shige shi ganin yadda Maleek ke kwance kamar gawa Salman dake bakin k'ofa ne ya jiyo kukan su kai tsaye ya shiga falon shima ganin halin da Maleek d'in ke ciki ya tashi hankalin sa sosai.



Da sauri ya k'arasa wajen yana salati suka d'auke shi suka kwantar da shi saman kujera har lokacin kuka suke yi "Salman meya faru da son haka dama ya sanar maka baida lafiya ne ko ya sanar maka wani abun na damun sa," Ummi ta fad'a tana sharar hawaye.


Shiru Salman ya yi Sabeeha kuwa tana so ta sanarwa da Ummi wayar da taji Uncle nayi sai dai bata da kwarin gwiwar hakan domin sanarwa Ummi na nufin ninkuwar tashin hankalin ta ne Maleek kuwa hakan zai k'ara masa damuwa.


"Ummi bakomai dama muna Shirin yin wata tafiya ne tare da Yallab'ai to shiyasa yace ayi masa wata allura wacce tana da had'arin da idan jinin mutum bai da k'arfi takan kwantar da mutum cutar paralyse ta tsawon lokaci sannan ta hana magana da kuma ji nayi tunanin hana Yallab'ai amma bai saurare ni ba tun a hanya yake sanar dani Yana jin yanayin jikin sa na sauya masa," ya fad'a hawaye na zuba a idanunsa.




Sai lokacin Maleek ya bud'e idanunsa sai dai ya yi k'ok'arin d'aga hannun sa hakan ya faskara kallon Sabeeha da Ummi kawai yake yi ganin yadda suke zubar da hawaye ji ya yi kamar ruwan zafi a zuciyar sa k'ok'arin bud'e bakin sa yake yi domin rarrashin su sai kawai ya ji kamar an d'ora masa wani k'aton dutse a bakin wasu zafafan hawaye ne suka zubo a idanunsa kansa kad'ai yake iya juyawa duk su Ummi basu lura a halin da yake ciki ba gaba d'aya zubawa Salman ido suka yi cikin tashin hankali "Ya sunan allurar Ina so nasani," Ummi ta tambaya jikin ta har rawa yake yi.



Da sauri Salman ya kalli Ummi domin ya ma manta cewar Ummi likita ce har ya yi mata wannan k'aryar kallon Maleek ya yi suna had'a ido Maleek d'in ya lumshe idanunsa ya bud'e ya gane me yake nufi sai ya ce "Ummi bansani ba," domin Maleek na fuskantar me suke fad'a idan ya kalli bakin su kallon ban yadda da Kai ba Sabeeha ke yi masa sannan ta kalli Maleek ganin idanunsa a bud'e ta ce "My dagaske ne abinda Salman yake fad'a," a hankali ya gyad'a kansa wani sabon kukan Sabeeha tasa ta ce "Yanzu baza ka iya tashi ba kenan jikin ka bazai motsa ba?" Ta fad'a tana kwantar da kanta saman jikin sa.



Ummi kuwa gaba d'aya ta rasa tunanin da zata yi ta ce "Salman mu tafi asibiti kawai zanyi bincike," Nan ma da sauri ya kalli Maleek da ido Maleek ya fad'a masa kar ya bari aje.




"A'a Ummi kar muyi hakan saboda aikin da yake tunkaro mu,"


"Haba Salman akan me zamu zauna da shi a gida yana cikin wannan yanayin?" Sabeeha ta fad'a idanunta sun kumbura tsabar kukan da tasha Dan ajiyar zuciya Salman ya sauke ya ce "Ba Ina nufin kwata kwata kar a Kai MG asibiti bane amma Kai shi a yanzu Yana nufin duniya zatasan halin da yake ciki Wanda hakan zai dakatar mana da aikin mu na tsayar da shigo da makamai k'asar mu ba kuma idan har labari ya Kai musu hankalin su zai karkata ga tunanin ta yadda zasu bi MG asibitin su kashe shi yayin da a gefe kuma zasu shigo da kayan," shiru suka yi Ummi kuma kuka ta saka tare da rungumar Maleek ta ce "Ya Allah ga bawan ka Allah Ina rok'on ka da ka bawa yarona lafiya ka kare mun shi daga sharrin masu sharri," suka amsa da "Ameen,"



Maleek kuwa hawaye ne kwance a idanun sa domin ganin hawayen Ummi na tayar masa da hankali hakan ne yasa shi d'an yin murmushi yana girgiza mata Kai.


"Ummi bai ci abinci ba kafin fitar sa," Sabeeha ta fad'a tana kallon Ummi da sauri jiki na rawa Ummi ta tashi ta nufi kitchen sai gata da tray da abinci a center table ta ajiye sannan dakyar suka zaunar da Maleek tare da jingina shi a jikin kujerar Ummi da kanta take bashi abincin.


Tashi Sabeeha ta yi ta nufi stairs da kallo Maleek ya bita so yake ya yi Mata magana amma ba dama domin yasan tana shiga d'akin zata cigaba da kukan ne kawai.


Tana shiga d'akin Ummi ta fara Kai da komawa a d'akin hawaye na bin fuskar ta gaba d'aya kanta ya kulle tama rasa abinda zata yi wayar ta ta d'auka ta Kira wayar Sabreen ana d'agawa daga can Sabreen ta ce "Hello dear," cikin dashashiyar muryar ta ta ce "Sabreen Ya Fauwaz na gida?"


"Eh yana nan amma lafiya kuwa naji muryar ki haka?" Sabreen ta tambaya "Ni dai Dan Allah kuzo tare yanzu gida ina jiran zuwan ku," daga haka ta katse Kiran ta zauna ta d'ora da kukan ta.


Tafi minti talatin a zaune a wajen sannan ta sauka down stairs ta shige kitchen sannan ta fice ta k'ofar baya zuwa part d'in su tana shiga ta samu Nasreen da Jamila zaune suna fira abinsu ko ta kansu bata bi ba ta haura stairs a falon ta zauna abubuwa da dama nayi Mata yawo a kwakwalwar ta.



Batasan shigowar su Sabreen ba sai da ta ji an dafata ta sannan ta yi saurin kallon Sabreen idanunta cike da k'wallah Sabreen kanta ta tsorata da ganin yanayin da 'yar uwar ta ta ke ciki ta ce "Subhanallah dear meya faru ne? Da wata matsalar ce?" Rungume Sabreen kawai Sabeeha ta yi ta saka kuka ta ce "Dear mun shiga Uku,"



Da sauri Fauwaz da shigar sa kenan ya k'arasa da sauri ya ce "Me yake faruwa ne?" Ganin Sabeeha da ya yi a jikin Sabreen.



Kome Kuma Sabeeha ta tuna sai tayi saurin tashi zaune ta share hawayen ta ta kalli Fauwaz sannan ta kalli Sabreen ta ce "Akwai matsala sister muna cikin wani hali ina buk'atar taimakon ku Dan Allah," gaba d'ayan su basu fuskanci me Sabeehan ke nufi ba Fauwaz ya ce "Sister ki nutsu ki yi mana bayanin abinda ke faruwa ko tsakanin ki da Yaya ne?" Girgiza Kai tayi sannan ta ce "Ya Fauwaz maganar da zan fad'a yanzu ta zama sirri a tsakanin mu dan Allah wato abinda ke faruwa da safe My ya shiga wanka wayar sa na hannu na sai kawai naji shigowar text sai kawai na duba rubutu ne ansa MG ka shirya rasa matar ka a yau da daddare abun ya tayar mun da hankali ina gani sai nayi sauri na goge text d'in sai dai abun ya dame ni a raina sosai My yaso ya fuskanci cewar ina cikin damuwa sannan nima nayi tunanin sanar da shi abinda ke faruwa amma ganin yana sauri yasa banyi masa maganar ba har ya tafi ni kuma nasa a raina cewar yana dawowa zan sanar da shi abinda ke faruwa,"


"Yanzu Ina shi Yayan ni Bari naje na sanar da shi," Fauwaz ya fad'a tare da niyyar nufar hanyar fita.



"A'a ya Fauwaz sanar dashi yanzu akwai matsala saboda shi ma Yana cikin wani yanayi," Sabeeha ta fad'a tare da sanar da su rashin lafiyar Maleek d'in daga ita har Sabreen da Fauwaz hawayen suke yi idanun Fauwaz har sunyi jajir zuwa fuskar sa Sabreen rungume Sabeeha ta yi ta ce "Yanzu dear wanne taimakon ki ke so a gare mu?"


"Dan Allah sister Ina so ki zauna a nan gidan sannan a matsayina ni kuma su zo su tafi dani?"



"Kamar ya?" Sabreen da Fauwaz suka fad'a a tare.



"Ku fahimce ni yanzu My yana cikin mawuyacin hali idan har na sanar da shi wannan hankalin sa zai fi haka tashi sannan kunsan cewar Yana da ciwon zuciya gashi kamar yadda na sanar muku ba a so asan da wannan rashin lafiyar tasa a gari hakan kan iya jawo masa matsalar da rayuwar sa zata kasance a cikin had'ari Ummi damuwa zata yi Mata yawa ga tunanin rashin sanin halin da nake ciki ga Kuma rashin lafiyar sa so nake kawai ni su yi mun duk abinda su ga dama idan ma kashe ni zasu yi su aikata hakan amma ku ku zauna lafiya,"




Kuka Sabreen ta fashe da shi ta ce "A'a hakan bazai yuwu ba ni nan zanje a madadin ki kinji?" Girgiza kai Sabeeha ta yi ta ce "A'a dear ni ya kamata naje,"



"Dukan ku ba Wanda zai je bari na Kira Daddy na fad'a masa a d'auki mataki a Kai," Fauwaz ya fad'a tare da k'ok'arin ciro wayar sa a aljihun sa "A'a Ya Fauwaz fad'awa Daddy halin da ake ciki na nufin My da Ummi kenan su San halin da ake ciki bana son ciwon My ya tashi sannan bari na fad'a muku gaskiya na fuskanci idan ba haka nayi ba baza ku fahimce ni ba wannan cutar da My yake yi sune silar jefa shi a ciki asiri suka yi masa sannan sun tabbatar a text d'in da suka yi masa cewar ba malamin da ya isa ya karya wannan asirin idan har basu suka warware shi da kansu ba wanda zuwana ne kad'ai zai sa su warware asirin ni d'in Kuma suna buk'ata tane kawai domin su rik'eni a wajen su su hana My dakatar da shigo da makamai da hodar cocaine Nigeria ni Kuma Ina so naje ne domin sun tabbatar mun da cewar suna d'auka ta zasu warware asirin jikin sa Kuma kunga yana samun lafiya zai samu damar k'wato ni da Kuma dakatar da k'udirun su ni dai ku taimake ni," Zama Fauwaz ya yi tare da dafe kansa da yaji yana sara masa.



"Na amince dear amma Ina tsoron su cutar mana dake Wallahi baza mu iya jura ba," Sabreen ta fad'a tana hawaye mik'ewa Fauwaz ya yi tsaye ya ce "Na fahimci komai sister duk wannan Yaya bai saniba sannan baisan sanadin ciwon sa ba hakan ne yasa akace allurar sojoji aka yi masa domin kwantar da hankalin mu ko?" Gyad'a Kai Sabeeha ta yi.


"Shikenan Nima na amince da hukuncin ki sai dai ina tsoron abinda zai je ya dawo," cikin jin dad'i ta ce "Insha Allah ba abinda zai faru kawai ku tayani da addu'a,"



Fauwaz kuwa Sabreen ya kalla sannan ya juya ya ce "Bari naje na ga Yaya," ya fad'a tare da fita daga d'akin.




Sabeeha Kuma ta kalli Sabreen da har lokacin hawayen ta bai tsaya ba tasa hannu ta goge mata ta ce "Haba dear ki bar kukan haka mana ki zama jaruma na zab'i na fad'a Miki ne saboda nasan kinfi Sameeha dear jarumta ko da wasa karki sanar da kowa wannan lamarin ko da Mama ce da kuma dear saboda gudun halin da zasu shiga," gyad'a Kai kawai Sabreen ta yi ta ce "Ta ya zan iya zama a matsayin ki a tunanin ki Ya MG bazai gane ba?"


"Eh bazai gane ba idan har kin bi hanyoyin da zan sanar dake,"



"Wanne hanyoyi ne?" Sabreen ta tambaya "Bari na fayyace Miki komai Kinga dai My bashi da lafiya nasan ba ta yadda za'ayi ya yi tunanin yin wata mu'amullar aure sannan zansa a yanzu a dawo da shi nan part d'in saboda a can za a iya samun matsala sannan karki kuskura ki Kira shi da Yaya domin hakan na iya sawa ya gane cewar ke d'in bani bace sannan abu Mai muhimmanci da ya kamata ki sani shine My yana gane Ni a cikin ku idan har ya kalli cikin idanuna da kansa ya

Please Login or Register in order to submit comment