Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta kalle shi hawaye na zuba a idanunta ta Kai hannunta da ya gama b'aci da jini ta shafa sajen sa a hankali cikin muryar azaba ta ce "Na godewa Allah ka samu sauk'i My," daga haka ta sake rufe idanun ta ba numfashi dad'a hugging d'in ta Maleek ya yi wani azababben son ta na k'aruwa a zuciyar sa.



Cak ya d'aga ta ya nufi kujera ya kwantar da ita sannan ya yi wata iriyar juyawa tare da zaro bindigun sa biyu ba abinda ka ke ji sai k'arar harbi idanunsa a rufe yake harbin sai da ya gama sannan ya yi jifa da bindigun.



Mutanen dake falon duka rintse idanunsu suka yi jin yadda MG ke harbi idanunsa a rufe sai dai ga mamakin su suna bud'e ido gaba d'aya 'yan daban dake falon da a k'alla sun Kai talatin gaba d'aya ya harb'e su gaba d'ayan su sun zama gawa.

A hankali ya k'arasa gaban Uncle ya yi masa kallon Sama da k'asa hawaye taf idanun sa ya ce "Why Uncle meyasa zaka aikata haka meyasa zaka yi hakan akan me zaka jefa mu a irin wannan halin Uncle meka rasa a rayuwar ka da ka zab'i kashe bayin Allah tare da cutar da su meyasa Uncle," Maleek ya fad'a yana fashewa da kuka kamar k'aramun yaro cikin k'aramun lokaci Kuma ya kalli gefe guda tare da share hawayen sa da babban yatsan sa ya kalli Uncle ya ce "Ka da ka tab'a tunanin zan tausayawa Wanda yake cutar da al'umma," daga haka ya bar gaban Uncle ya koma kan Oga kwata kwatan su ya tsaya a gaban sa ido cikin ido Maleek ya kalle shi ya yi murmushin gefen baki ya ce "Alhaji sammani miji ga mahaifiyar Uncle marigayiya Hajiya Hauwa'u ashe dama kaine the most criminal person da Nigerian army bamu sanka ba a gaskiya na tausaya maka da case d'inka yazo hannun MG Abdul-maleek Hamza mai dala domin kashin ka ya bushe tabbas naji dad'i da granny baza ta kawo wannan lokacin da idanunta zai gane mata mutuwar mijin ta da d'anta ba Ina tabbatar muku wasan ku yazo k'arshe," daga haka ya matsa gaban wani mutum.





Sai da Maleek ya k'are masa kallo ya ce "Alhaji Hamisu kwangila uba ga Arfat yaro d'aya daka mallaka a duniya sannan Kuma minister ashe da hannun ka wajen rusa mana k'asa hmm ku jira result d'in ku," haka Maleek ya gama yi musu zayyana kaf d'in su sannan ya juya musu baya tare da zura duka hannayen sa a aljihu idanunsa akan Sabeeha ya ce "Sabeeha yarinya Mai hankali da nutsuwa sannan Kuma mata ga MG Abdul-maleek yarinyar da nake so Kuma nake matuk'ar k'auna kamar rayuwata Kai fiye ma da rayuwata yarinyar da nake so na riritata na gatata ta na ji da ita kamar 'yar tsanar zinare amma hakan ya gagara saboda ku d'in nan," ya fad'a tare da nuna su sannan ya jinjina Kai kamar Yana yiwa yaran sa fad'a ya ce "A bisa hakan nake yi muku albishir da cewar dukan ku zaku karb'i results d'in ku tun a nan duniya kafin ku had'u da ubangijin mu," daga haka ya kalli sojojin sa cikin bada umarni ya ce "Salman dukan su ku sasu a motor zuwa gida," daga haka ya nufi inda Sabeeha take ya d'auke ta ya yi hanyar fita har ya Kai k'ofa ya waiga ya kalli Tsohuwa Sailuba ya ce "Har da wannan," daga haka ya fice ya nufi motor ya bud'e ya shiga aka rufe akaja motar zuwa gida.
[10/25, 8:58 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️



RUBUTAWA DAGA
HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ)





SADAUKARWA GA
MY DAUGHTER SABEEHA
BILKISU Z.YAU (🅱️K)
AISHA MAGAJI DABO (AMA)




Page 37


Tunda suka d'auki hanya zubawa fuskar Sabeeha ido kawai Maleek ya yi cikin tausayin ta a hankali ya shafa gashin kanta da ya yi uban dirty kamar an shekara uku ba a wanke shi ba.



Suna shiga gate d'in gidan sojojin sa suka k'arasa gaban motar sa da gudu Salman ne ya bud'e masa motar tare da Sara masa fita daga motar Maleek ya yi d'auke da Sabeeha a hannun sa "Salman aje dasu waccan b'angaren ka tabbatar jikin su ya fad'a musu," Maleek ya fad'a tare da fara tafiya.



"Amma sir Uncle fa har da shi?" Wani banzan kallo Maleek ya aikawa Salman wanda bai tab'a yi masa makamancin sa ba ya ce "Shi Uncle d'in shi waye shi to har da shi nake nufi," yana fad'ar haka ya shige part d'in Ummi.


Da sallama ya shiga ya same su kowa cirko cirko a tsaye Daddy ne kawai a zaune da glass cup a hannun sa Yana shan ruwa amma ragowar mutanen falon kowa kansa a kulle yake da abinda ya faru.


Ganin shigar Maleek ne yasa kowa binsa da idanu ganin wata a hannun sa domin duk ciki ba Wanda ya gane Sabeeha ce direct kujera ya nufa ya kwantar da ita yana kallon ta.



A tare Sabreen da Sameeha suka nufi wajen domin dole sunsan wannan 'yar uwar su ce suna kallon ta wani tashin hankali ya ziyar ce su saboda ganin halin da Sabeehan su ke ciki.


Sameeha kuwa fad'uwa tayi sumammiya a wajen Sabreen kuwa da sauri ta waiga ta rungume Fauwaz dake bayan ta ta fashe da wani irin kuka ta ce "Na shiga uku my heart duba fa ka gani yanzu da gaske wannan Sabeeha dear ce?" Shima kansa Fauwaz hankalin sa a tashe yake.



Umar kuwa da sauri ya nufi inda Sameeha ke kwance ya d'auke ta zuwa b'angaren Fauwaz ya kwantar da ita a saman gado ya shafa mata ruwa da kuka ta farfad'o tana Kiran sunan Sabeeha dakyar Umar ya shawo kanta tayi shiru sannan ya ja hannunta suka koma falon.



Ummi kuwa k'arasawa wajen da Sabeeha ke kwance ta yi tana kallon ta itama take hawayen tausayin Sabeeha ya wanke mata fuska mik'ewa Maleek ya yi ya dafe goshin sa take hawaye ya zubo masa hankali a tashe Daddy ya k'arasa wajen sa fad'awa jikin Daddy Maleek ya yi ya saka masa kuka kamar k'aramun yaro shi kansa Daddy dauriya kawai yake yi domin duk wanda ya ga halin da Sabeeha ke ciki sai ya tausaya mata cikin dauriya Daddy ya ce "Be strong Son insha Allah Daughter zata samu lafiya okay?"



Maleek kam ko magana ya kasa sai gyad'a kai kawai da yake yi hawaye wasu na bin wasu a hankali Daddy ke buga bayan sa alamun rarrashi sannan ya kalli Umar ya ce "Umar zaka iya treating daughter a nan ko sai munje hospital?"



"Daddy Ina ganin muje hospital kawai," a hankali Maleek ya zare jikin sa daga na Daddy ya share hawayen sa ya k'arasa inda Sabeeha ke kwance ya d'auke ta cak ya yi hanyar fita da ita Umar Daddy Ummi na biye da shi.



Har mota suka k'arasa Umar ne ya shiga driver seat Daddy Kuma front seat yayin da Ummi ta shiga back seat Maleek kuwa motar sa aka bud'e masa ya shiga suka nufi hospital.

Direct office d'in Ummi suka shiga da Sabeeha Ya kwantar da ita saman gadon dake d'akin Ummi da Umar ne a kan Sabeeha suna treating d'in ta har lokacin a sume take ja baya Maleek ya yi ya jingina da k'ofar d'akin yana share hawaye daga k'arshe ma ya fita daga office d'in gaba d'aya.

A zuciye ya fita daga office d'in Ummi ko bari a yi driving d'in sa k'in yadda ya yi ya fad'a mota ya jata da wani masifaffen gudu kamar mai Shirin tashi sama zuciyar sa banda tafasa ba abinda yake yi ikon Allah ne kad'ai ya kaisa gida lafiya.




Ko gama sai ta parking bai yi ba ya fice daga motar ya shige part d'in Ummi a zuciye gaba d'aya da kallo mutanen falon suka bi shi.



Direct wajen da Nasreen take a rakub'e Maleek ya yi gaba d'aya ta gama jik'ewa da zufa da Kuma fitsarin da ta yi domin tasan yau gashin ta ya bushe kallo d'aya zaka yiwa Maleek ka fahimci zuciyar sa a kusa take.


Nasreen na ganin ya yo ta wajen ta tashi da gudu domin samun wajen b'uya sai dai kafin ta yi wani yunk'uri Maleek ya d'amk'i hannun ta ya yi wurgi da ita a jikin bango wata razananniyar k'ara Nasreen ta saki saboda wata azaba da ta ratsa bayan ta zuwa k'eyar ta Sam Maleek bai damu ba ya k'arasa inda take ya fara ball da ita tana ihu da neman ceto amma tsakanin Fauwaz Sabreen da Sameeha ba Wanda ya yi k'ok'arin taimakon ta.



Sosai Maleek ke ball da Nasreen tana ihu shak'ar da Maleek ya yiwa Nasreen ce tasa Fauwaz yin wajen da sauri ya rik'e hannun Maleek d'in ya ce "Please Yaya ka sake ta haka zata iya mutuwa fa," saboda duk Wanda aka yiwa wannan shak'ar mutuwa ce k'arshen sa Nasreen kuwa har numfashin ta ya fara guduwa idanunta sun firfito shi kansa Maleek yasan shak'ar mutuwa ya yi mata Sameeha da Sabreen su ma abin ya tsorata su yanzu rintse idanu Sabreen ta yi Sameeha kuwa k'ara ta saki ganin MG na niyyar yin kisa.


Wurgi da ita gefe ya yi ba dan komai ba sai dan ganin hankalin Sabreen da Sameeha ya tashi huci kawai yake yi Nasreen kuwa suma ta yi ko ta kanta bai bi ba ya fice zuwa part d'in sa wanka ya yi ya fito a gurguje ya shirya cikin wata farar shadda d'inkin zamani sumar kansa sai shek'i take yi yana zabga k'amshi sai dai fuskar sa babu annuri a tamke take kamar bai tab'a dariya ba.


Car key d'insa ya d'auka tare da wayoyin sa ya fita direct asibiti ya nufa har lokacin Sabeeha bata farfad'o ba guri ya samu ya zauna ya zuba mata idanu Yana kallon ta har magrib ta yi tashi ya yi shi da dad suka tafi masallacin dake cikin asibitin suka yi sallah a hanyar komawar su ne Fauwaz ya yiwa Maleek waya akan cewar suna so su je asibitin ya ce "Ok kuzo d'in but wannan abar ka kulle min ita a part d'in ka," ko ba a fad'a ba Fauwaz yasan Nasreen ake nufi sai ya ce "Okay," ya yi hanging up.



Ba su dad'e da komawa d'akin ba sai ga Fauwaz da Sabreen da Kuma Sameeha su ma zama suka yi suna kallon 'yar uwar tasu hankalin su a tashe kowa tausayin ta fal zuciyar sa a haka har dare ya fara Maleek ya kalli Fauwaz ya ce "Ina ga kuje gida dare ya yi Ummi kema da Dad kuje gida," Sabreen ta girgiza Kai ta ce "Zan zauna a nan," Sameeha ta ce "Nima haka," Ummi da Daddy ne kawai suka tafi Amma Fauwaz Sabreen da Sameeha har ma da Umar a asibitin suka kwana.



Wasa wasa Sabeeha sai da ta kwana biyu bata farfad'o ba a safiyar kwana na biyun Maleek ya nufi gida domin yin wanka domin wankan kawai yake iyawa sai sallah amma batun abinci kuwa babu shi bacci ma baya yi kwana yake a zaune.



Yana zuwa part d'insa ya wuce ya yi wanka ya shirya cikin k'ananun kaya jajaye ya yi kyau har ya gaji ya d'ora red p-cap sai dai fuskar sa a had'e take sosai asibitin ya koma.



Da sallama ya shiga d'akin daidai lokacin Sabeeha ta motsa tare da bud'e idanunta da sauri ya k'arasa wajen gadon ya zauna gefen ta fuskar sa d'auke da farin ciki ya ce "Sabee na," idanunta ta sauke a kansa baisan hawaye yake ba sai da ta girgiza masa kai tare da nuna masa su Sabreen da idanunta sannan ya share hawayen ya rungume ta sosai a jikin sa.


Su Ummi ma da sauri suka k'arasa wajen su suna hamdala su Sabreen kuwa har da hawayen farin ciki ita dai Sabeeha da idanu kawai take binsu ita kanta tasan tayi missing d'in su over kamar ranar ta fara ganinsu haka take binsu da idanu tare da k'ara kwanciya jikin Maleek.


Kallon Ummi ta yi ta ce "Ummi zanyi wanka," Ummi da kanta ta had'a mata ruwan wanka ta tashi a hankali ta nufi toilet d'in ta dad'e a toilet d'in tana gurzar jikin ta kanta kuwa tayi masa wanki yakai goma take ta dawo Sabeehan ta ta da towel ta d'aura ta fito ta samu d'akin ba kowa sai Maleek kad'ai.



Yana ganin fitowar ta ya k'arasa wajen ta da sauri ya d'auke ta cak ya k'arasa da ita gefen gadon ya zaunar da ita ta tsane jikin ta da kansa ya shafa mata mai me matuk'ar k'amshi sannan ya gyara mata kanta ya d'aure mata shi sannan ya bata wata doguwar riga red tasa ta yafa mayafin rigar ya feshe ta da turare a hankali ya Kai hannunsa saman cikin ta da ya d'an fito lumshe ido ta yi sannan ta bud'e su a saman kyakkyawar fuskar sa ya ce "I really miss you my wife,"


A hankali ta ce "Miss you more," sumbata ya bata a check d'in ta sannan ya zauna tare da zaunar da ita akan cinyar sa ya bata abinci ta ci ya bata magani tasha sannan ya ce "Yanzu me yake miki ciwo," girgiza Kai ta yi cikin sassanyar muryar ta ta ce "Bakomai sai gajiya kawai," ta fad'a tare da kwanciya kan gadon su Ummi ne suka shiga d'akin.


Gaishe su Sabeeha ta yi suka amsa tare da tambayar ta jikin ta ta ce "Da sauk'i," kowa da kalar tambayar da yake son yi sai dai ba wajen da ya dace ayi tambayar bane sai kawai kowa ya yi shiru abinsa.



Sameeha da Sabreen kuwa rungume 'yar uwar tasu suka yi suna murnar ganin ta samu sauk'i "Ummina zamu iya tafiya gida ai ko?" Maleek ya fad'a yana kallon Ummi.



"Eh zamu iya tafiya," Ummi ta fad'a tare da mik'ewa ta fara dialing number d'in Doctor bayan sun gaisa Ummi ta ce "Maryam yarinya ta bata da lafiya fa ya kamata kizo ki dubata," daga can Doctor ta ce "Tom Insha Allah zanzo,"



"To sai kinzo," Ummi ta fad'a tare da katse wayar suka had'a koman su suka fita wajen asibitin.



Maleek da kansa ya bud'e mata gaban motar sa ta shiga ya zagaya ya shiga yayinda Sabreen da Sameeha ke back seat motar baya Kuma Fauwaz ke driving sai Umar a front seat Ummi da Daddy na back seat haka suka nufi gida bayan sunyi parking direct part d'in Ummi suka nufa a falo suka zazzauna.



Basu dad'e ba da zama Mama ta yi sallama a falon Sabeeha ce a gaba wajen rungume Doctor tana murnar ganinta bayan ta zauna ne aka gaggaisa sannan falon ya d'auki shiru daga Ummi har Daddy suna so su ji wata magana gamsashiya daga bakin Maleek.




Maleek ya yi gyaran murya tare da cire p-cap d'in sa ya ajiye sannan ya kalli Fauwaz ya ce "Fauwaz zo da wannan yarinyar," tashi Fauwaz ya yi ya bud'e part d'insa ya fito da Nasreen tana fitowa suka had'a ido da Maleek da gudu ta juya zata koma cikin d'akin domin yanzu mugun tsoron Maleek d'in take dan gara taita zama a part d'in Fauwaz baci ba sha da ta gauraya da shi.




Tsawa dodon nata ya daka mata ya ce "Zonan!" A d'ard'ar ta nufi cikin falon tana raba idanu kowa a falon da kallo ya bita kallo d'aya zaka yi Mata kasan bata da gaskiya saboda raba idanu da take tana sosa k'eya tana k'asa da idanu.



Guri ta samu can nesa da Maleek d'in ta zauna mik'ewa Maleek ya yi ai tana ganin ya mik'e ta saki ihu ta tashi da gudu ta b'uya bayan Ummi tayi mata wani mugun rik'o shi dariya ma ta bashi domin ba wajen ta zashi ba Ummi kuwa ta ce "Kinga cikani karki karyani," Maleek kuwa ficewa ya yi direct inda yasa akai su Uncle ya nufa.



Yana shiga wajen sojojin dake wajen suka Sara masa kallon su Uncle ya yi duk sun gama galabaita tsabar wuya har sun cire manyan rigunan jikin su murmushin gefen baki ya yi ya kalli Uncle ya ce "Uncle zan ganka yanzu," ai har da gudu Uncle ya had'a wajen zuwa gurin Maleek ya rik'e hannun sa tamau ya ce "Gani Dan Allah kace su kyale mu haka ka duba matsayina a wajen ka," kawar da Kai gefe Maleek ya yi tabbas Uncle uba ne a gurin sa sannan yana son sa sai dai Uncle d'in ya kasance mai laifi Maleek har zuciyar sa yake jin ba dad'i amma ya basar ya ce "Uncle d'an sake ni mana,"




Da sauri Uncle ya ce "To to to Wallahi na sake ka," wani tausayin Uncle d'in ne ya dirar masa a zuciya jiki a sanyaye ya ce "Muje," ya fad'a tare da yin gaba Uncle na binsa a baya har falon Ummi.


Tunda suka shiga Maleek ya samu waje ya zauna sai lokacin idanun Sabeeha ya sauka akan Uncle ai da azamar gaske Sabeeha ta fad'a jikin Maleek ta k'ank'ame shi domin wani mugun tsoron Uncle d'in take ji shafa bayan ta Maleek ya yi saitin kunnen ta ya ce "Ki kwantar da hankalin ki Sabee na ba abinda zai miki okay?" K'ara mak'alk'ale shi Sabeeha ta yi har da rintse idanu.



Daddy kuwa ganin yadda yayan nasa ya koma ne duk fuskar sa a kumbure yasa shi mik'ewa da sauri ya ce "Yaya lafiya Mai ya same ka?" Uncle kuwa sai kallon Maleek yake yi cikin jin tsoran sa Daddy ma Maleek d'in ya kalla ya ce "Son just tell me what happens?" Ajiyar zuciya Maleek ya sauke ya ce "Daddy ka zauna domin maganar da zan fad'a yanzu bata tsaiwa bace domin zaka iya fad'uwa," babu musu Daddy ya koma ya zauna sai dai har lokacin idanunsa na kan d'an uwan sa d'aya tilo da bai da kamar sa Yana so ya ji Mai ya faru da shi.



Maleek ya fara magana da cewa "Daddy iya sanina tun ina yaro Uncle baya k'auna ta bai tab'a Sona ba duk da matsayin sa na uba a gare ni baya son cigaba na baya son farin cikina Wanda k'iyayyar da yake maka ne ta shafeni Daddy ka fini sanin halin d'an uwanka domin tare ku ka rayu a iya sanina Uncle baya sona ne saboda kawai nazo a matsayin d'an ka sannan na kasance namiji Kai Kuma baya sonka ne saboda a komai kaine gaba da shi a ko da yaushe ina addu'ar Allah ya ganar da shi gaskiya amma Uncle bai tab'a tunanin cewa abinda yake yi ba daidai bane kullum burin sa shine ya ganni a matsala ya aura mun 'yar sa ta dole bana sonta amma nayi muku biyayya domin faranta ranku Daddy a ta kowacce hanya Uncle so yake ya ga bayan mu ba dan komai ba sai dan dukiya," d'an shiru Maleek ya yi yana bin mutanen falon da kallo sannan ya sauke idanun sa akan Nasreen dake rakub'e a bayan kujera.




Ya ce "Daddy Uncle ya shirya kashe ni sannan ya had'a da Sabeeha,"




"What?" Daddy ya fad'a da k'arfi idanunsa akan Uncle da ya yi k'asa da Kai gyad'a Kai Maleek ya yi ya ce "Hakane Daddy domin da kunnena naji yana fad'awa Nasreen a waya cewar ta tabbatar tasa mun maganin da ya aiko mata cikin motata maganin da idan na taka shi shikenan zan kwanta paralyse Wanda bazan warke ba har sai sanda suka so sannan idan na kwanta cutar zasu samu damar rabani da numfashina sannan Ku ma su kashe ku domin su mallake duk abinda muka mallaka Daddy Uncle ya zubar mana da mutunci Uncle safarar miyagun kwayoyi yake yi da makamai Wai dasa hannun Uncle wajen kashe al'umma da jefa su cikin mawuyacin hali Daddy bansani ba shin daidai na aikata ba ko laifi dana kama uba a gareni matsayin mai laifi," Daddy hawaye ne zafafa suka zubo masa a idanunsa kowa dake falon kansa a kulle yake shin mamaki zasu yi ko kuma al'ajabin abinda yake faruwa zasu yi.


Wata ajiyar zuciya Maleek ya sauke ya ce "A lokacin da naji wayar Nasreen da mahaifin ta sam banyi mamakin jin hakan ba a daren idanuna na kanta har lokacin da ta je har cikin motata ta zuba maganin bayan ta gama ni Kuma a daren nasa aka kawomun irin motar sak aka ajiye nasa aka fitar da d'ayar saboda ba damar na hau wata daban domin zasu gane ba ita nahau ba ni Kuma Ina so suji a ransu aikin su ya yi hakan ne yasa nasa aka kawo mun wata motar washe gari Ina gani Nasreen na lek'en fitata ta window bayan zuwana meeting na fito na yanke shawarar yin pretending domin na nuna musu cewar aikin su ya tafi daidai Wanda na tabbata hakan ba k'aramun dad'i ya yi musu ba Sabee na kad'ai nayi niyyar fad'awa gaskiyar abinda ke faruwa sai dai abu d'aya daya tsaya mun a zuciya shine ta ya Sabee na ta je gare su tabbas lokacin da nake kwance na gane Sabreen ce zaune a matsayin Sabee na abun ya d'aure min kai matuk'a Umar kad'ai yasan abinda ke faruwa shi kad'ai ke d'awainiya wajen nemo inda Sabeeha take amma ba labari ni kuma ba damar na tambaya domin idan har wani ya gane cewar na samu sauk'i na tabbata maganar zata kai wajen Uncle na damu sosai da rashin ganin Sabee na hankalina ya tashi sosai sai dai dole nasan Sabreen tasan wani game da hakan ita da Fauwaz,"


Sabreen ta ce "Eh Ya MG Sabeeha dear ta sanar damu cewar wayar ka na hannunta aka yi maka text akan cewar za azo a d'auke ta a daren ranar daka kwanta ciwo kuma har sai an d'auke ta ne sannan za a warware asirin dake jikin ka hakan ne yasa na zauna matsayin Sabeeha dear kafin ta dawo sai daga baya Kuma muka gane munyi kuskuren barin Sabeeha dear da muka yi ta tafi saboda duk lokacin da muke waya da ita muna jinta cikin mawuyacin hali ranar da Sameeha dear tazo ta Kira mu ranar hankalin mu ya tashi sosai saboda jin wata mata ta buga ta da bango tana dukan ta," Sabreen ta fad'a tana hawaye.




Sabeeha dake mak'ale jikin Maleek sai lokacin ta d'aga kanta ta kalli Maleek ta ce "Ka gafarceni My lokacin da ka fita meeting na fito zuwa wajen Ummi naji Uncle nayin waya yana magana akan zuba mata magani da akayi a motor Wanda zaka kwanta ciwo sannan Ni Kuma a daren ranar zai turo a sace ni sannan a kashe ni sannan kaima a kashe ka har ma da su Ummi hankalina ya tashi sosai na nufi wajen Ummi domin fad'a Mata abinda ke faruwa sai dai ganin dawowar ka ba lafiya ya hanani sanar mata saboda gudun kar hankalin ta yafi haka tashi sannan ga Kuma halin da My yake ciki hakan ne yasa na yanke hukunci gara kawai na Bari su tafi dani ba tare da Ummi ko my sun saniba saboda gudun afkawar su a damuwa My ga rashin lafiya Ummi Kuma ga rashin lafiyar sa ga Kuma sace ni hakan ne yasa na fad'awa Sabreen dear haka ita da ya Fauwaz na b'oye musu ainahin gaskiyar saboda gudun karsu shiga halin rashina sannan nasa Sabreen zama a madadina saboda kada kuyi tunanin bana nan sun azabtar dani sun so su cutar da rayuwa sunso su rabani da farin cikina ranar da suka shirya kasheni a ranar Allah ya turomun Rashida ita ta kwance ni daga d'aurin da suka yi mun harna Kira ka domin ba dan ita ba nasan shikenan zai sun aiwatar da abinda suka yi niyya a kaina sannan naji ana maganar shigo da kaya k'asar nan," ta fad'a tana kallon sa jawota jikin sa ya yi ya rungume ta yana jin sonta na ratsa duk wata jijiya dake jikin sa da jinin jikin sa tabbas Sabeeha macece ta gari a gare shi ita ta daban ce saboda ta yarda ta rasa rayuwar ta domin farin cikin ahalin ta.



Doctor kuwa share hawaye ta yi a zuciyar ta kuwa tana yabawa 'yar tata haka ma Ummi hawayen take yi na tausayin Sabeeha ga Kuma wata sabuwar soyayyar ta da ta dad'u a idon Ummi su Sabreen ma da su Umar sai da suka ji ta burge su domin

Please Login or Register in order to submit comment