Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

barta ta cigaba da taya ki dama ita ce mara aikin yi ai," Sameeha ta ce "Wallahi kuwa amma fa naji tsoron Umman Nasreen saboda zagin da tayi mun," Sabeeha ta ce "Ki kyale ta wannan ita da mahaliccin ta," daga haka ta mik'e tabar d'akin.



Maleek kuwa ya dad'e a asibitin suna magana da Doctor Maryam sannan ya yi mata sallama suna fitowa daga office d'in aka kira shi a waya daga wajen aikin su dan haka direct NDA ya wuce daga can kuma JAJI barrack ya wuce bashi ya koma gida ba sai yamma wanka kawai ya yi ya kwanta domin hutawa saboda ya gaji da yawa domin zuwa ya yi ya had'a tawagar sa da zasu tura domin aiwatar da aikin tsayar da shigo da cocaine cikin k'asar nan dan haka bai samu damar ganawa da Ummi ba kamar yadda yaso domin ya yi waya da Rinaz ta kuma tabbatar masa dukan su suna falo shi kuwa bai son zuwa ya ga Sabeeha beside ma ga gajiyar dake damun sa.



Washe gari Maleek ya nufi part d'in Ummi bai samu kowa a falo ba ya haura stairs ya tura k'ofar falon dake saman a can ya hangi Ummi zaune saman kujera gama wayar ta kenan da Daddy.



K'arasawa Maleek ya yi ya zauna gefen Ummi ya ce "Sannu da hutawa Ummina," shafa kansa Ummi ta yi ta ce "Yawwa son," d'an gyara zaman sa ya yi sannan ya ce "Ummi Wai dama k'awancen ki da Doctor Maryam ya dad'e haka?" Murmushi Ummi ta yi ta ce "Eh mana ai tare muka yi karatu da ita a malesia lokacin da muka dawo hutu ne ni ban koma ba nayi aure ita Kuma ta koma har lokacin da na haife ka tana can kuma dalilin da yasa baka santa ba a lokacin saboda baka k'asar kana Dubai," gyad'a kai Maleek ya yi sannan ya ce "Ummi ashe dama tana da miji a k'auyen meyere?" Nan fa Maleek ya bata labarin zuwan sa wajen Abba dama zuwa wajen Doctor Maryam da ya yi.



Farin cikin Ummi kasa b'oyuwa ya yi domin kuwa har hawayen farin ciki ta yi ta ce "Yanzu son kana nufin su Sabeeha yaran Maryam ne?" Noding kansa Maleek ya yi sannan ya ce "Ummi ni mamakina meyasa duk tsawon lokacin nan bata je k'auyen ba bata damu da ta duba lafiyar mijin ta da yaran ta ba wanda tun suna 3 years rabon ta da su?"



"Son kenan Maryam mutuniyar kirki ce kowa yana yaba halin ta ko sanda muna malesia kamar yadda na fad'a ma tare muka yi karatu da ita sai dai ni muna zuwa hutu ban koma ba nayi aure ita Kuma ta koma har ta gama lokacin Kuma na haife ka lokacin kana Dubai sanda ta dawo ne iyayen ta suka ce ta fito da mijin aure amma ita Sam a maneman ta bata samu Wanda take so ba har iyayen ta suka fara tunanin ko aljanu ne suka aure ta domin lokacin kai ka gama primary school d'in ka kwatsam ta bani labarin ta had'u da wanda take so naji dad'in hakan sosai domin nima lokacin burina shine ta yi aure sai dai sam iyayen ta suka nuna basa son Abubakar saboda ita kad'ai iyayen ta suka haifa sannan suna da dukiya hakan ne yasa su basa so 'yar su ta auri talaka nasan Abubakar sosai saboda wasu lokutan har nan gidan suke zuwa su yi fira saboda basu da damar yin fira a gidan su Maryam saboda tsananin mahaifin ta akan Abubakar," shiru Ummi ta yi sannan ta cigaba da cewa "Har duka mahaifin Maryam yasa aka yiwa Abubakar akan ya rabu da Maryam amma hakan baisa ya ji a ransa zai rabu da Maryam ba daga k'arshe ma iyayen Maryam suka ce idan har ta nace sai ta auri Abubakar to basu ba ita haka ta amince aka yi auren su ya tafi da ita meyere sai daga baya ta samu daidaitawa da iyayen ta sai dai ta fuskanci matsaloli sosai daga matar yayan Abubakar Bala dama shi kansa balan kullum musguna mata suke yi sai dai Maryam macece mai hak'uri bata nunawa a hakan ta samu cikin 'yan uku harta haife su kwatsam watarana Maryam ta dawo gida ba a cikin hayyacin ta ba abun kamar shafar aljanu hakan ne yasa k'anin mahaifin ta Kawu Bashir tsayawa tsayin daka wajen nema mata magani harta samu sauk'i sai dai idan aka tambaye ta mijin ta da yaran ta bazata ce komai ba abu kamar wasa Maryam bata maganar su ni da kaina naje k'auyen sau da yawa amma sai dai Bala ya ce mun shima rabon sa da Abubakar ya manta har na gaji na dena zuwa," ajiyar zuciya Maleek ya yi ya ce "Ummi duk abinda yake faruwa da alamu akwai hannun wan mahaifin su amma bincike ne zai tabbatar da hakan," Nan suka cigaba da tattaunawa akan lamarin.



Hankali a matuk'ar tashe Sabeeha ta shiga d'akin su ta fad'a saman gadon su ta saka kuka a hankali ta fara magana "Meyasa zata aikata hakan shin wanne irin laifi muka aikata mata?" Jin za a bud'e k'ofar d'akin ne yasa ta daidai ta nutsuwar ta Sameeha ce ta shiga d'akin ta zauna ta ce "Sabeeha dear kinsan yau ma Sabreen sister ita taje ta yi aiki a madadina," murmushin da iyakar sa fuskar ta Sabeeha ta yi ta ce "Kyale ta idan ta gaji zata dena dan kanta," Sabreen ce ta shiga d'akin tana rik'e da pretty a hannunta ta kalli Sabeeha ta ce "Sabeeha dear da alama fa pretty bata da lafiya gaba d'aya tak'i taci abinci bari mu kaita asibiti ni da my one,"



"Ayyah sorry pretty," Sameeha ta fad'a sannan ta kalli Sabreen ta ce "Sister nagode da aiki fa," kallon rashin fahimta Sabreen ta yi mata Sabeeha ta yi saurin cewa "Sabreen dear please ku tafi Kinga pretty sai kuka take yi," juyawa Sabreen ta yi ta fita tana cewa "sai mun dawo," ta fice.


K'ara matsawa kusa da Sabeeha Sameeha ta yi ta ce "please dear duba mun forehead d'ina kiga naji ciwo," Sabeeha ta ce "Mai ya same ki a wajen?" D'an tura baki Sameeha ta yi ta ce "Munyi karo da wani ne?"


"Wanene," cewar Sabeeha "Nima bansan shi ba amma ya tambaye ni ko nice Sabeeha nace mishi a'a," Sameeha ta fad'a tana shafa goshin ta Sabeeha ta ce "Ayyah sorry dear,"




Sabreen na fita falon daidai lokacin Maleek ke saukowa stairs gaishe shi suka yi ita da Fauwaz ya amsa da "Lafiya," ya fad'a yana kallon pretty sannan ya ce "Wannan magen fa?" Sabreen ta ce "zamu kaita asibiti ne ni da my one bata da lafiya ta Sabeeha dear ce," baice komai ba Fauwaz ya ce "My heart mu tafi ko," hararar sa Maleek ya yi a zuciyar sa ya ce na jinjinawa rashin kunyar ku daga haka ya fice.




Part d'insa ya nufa yana shiga falon ya tsaya yana kallon Umar dake kwance saman kujera sai murmushi yake saki shi kad'ai aikuwa ya kyalkyale da dariya har da rik'e ciki domin duk Wanda ya ga Umar sai ya dara.



K'arasawa Maleek ya yi ya ce "Lafiya kake kuwa," wani Murmushin Umar ya yi ya ce "MG wallahi nayi matar aure a gidan nan kana kallon ta kasan hankali nutsuwa tarbiyya sun samu a wajen ta,"




"Wacece," Maleek ya tambaya yana zama gefen Umar.



"Gaskiya bansani ba amma suna kama da Sabeeha na tambaye ta ko ita ce ta ce A'a," shiru Maleek ya yi ya ce "Idan kuwa ba Sabeeha bace to kuwa Sameeha ce," Umar ya ce "Wallahi ina son ta please ka taimaka mun ta wannan b'angaren,"



D'an hararar sa Maleek ya yi ya ce "To bud'e zuciyar ta zanyi nasa mata sonka idan har dagaske kake to kaje da kanka ka same ta," ya fad'a yana nufar stairs Umar ya ce "Amma dai kasan ban tab'a yaudarar d'iyar kowa ba ko?" Maleek ya ce "Ta ya zan sani bayan ban dad'e da dawowa k'asar ba," yana fad'ar haka ya shige bedroom d'in sa.
[10/25, 7:43 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️





RUBUTAWA DAGA
HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ)





SADAUKARWA GA
MY DAUGHTER SABEEHA
BILKISU Z.YA'U (🅱️K)
AISHA MAGAJI DABO (AMA)





Page 14


Bayan kwana biyu Sabeeha ce kwance akan gado tana buga game a wayar ta sai pretty dake gefen ta a kwance.




Tashi zaune ta yi ta tankwashe k'afar ta sannan ta ajiye wayar tana shafa jikin pretty.



Da gudu su Rinaz suka shiga d'akin suka fad'a kan gadon suna ihu saurin sa hannuwanta Sabeeha ta yi ta toshe kunnuwan ta sannan ta ce "Lafiya ku ke kuwa?"




"Dear jibi birthday d'in ku fa," cewar Rinaz itama Sabeeha ihun murna ta saki ta fara tsalle akan gadon Sameeha ta ce "Wayyo harna matsu ranar tayi akwai shagali," Sabreen da ta kwaso shoky ta ce "Ke dai bari sister ai akwai kodumo," Rinaz ta kalli Sabeeha ta ce "Ummi ta ce mu Kira ki ne fa," tsayawa da rawar da take yi tayi sannan ta ce "Muje to,"




Tare suka fita falon Rinaz ta ce "Ummi Ina Kuma yayan ya tafi?" Ummi ta ce "Cewa ya yi zai fita may be akwai inda zashi ko da wata matsala ce?" Girgiza kai Rinaz ta yi ta ce "Naso dai yana nan zamu yi tsare-tsaren celebrating d'in," tana rufe baki wayar ta tayi k'ara alamar shigowar sak'o.



Tana dubawa ta buga tsalle ta ce "Wow Ummi yayane ya turo mana 2 million muje shopping," murmushi Ummi ta yi ta ce "Ya kyauta kuwa sannan dalilin kiran ku shine ina ga zaku Kai birthday party d'in ku gidan Doctor Maryam saboda ranar ina da bak'i," Rinaz ta ce "To Ummi bari muje gidan Maman," Ummi ta ce "No ba sai kunje ba zansa ayi komai,"



Umar ne ya shiga falon sai tura baki yake yi kusa da Ummi ya zauna sai cika yake yana batsewa shafa kansa Ummi ta yi ta ce "Son lafiya?"



Tura baki ya yi ya ce "Ummi ni da Maleek ne tun shekaran jiya nake masa magana akan yarinyar da nake so ya taimakamun amma sai yace wai bud'e zuciyar ta zai yi yasa mata sona naje da kaina idan kuma bata sona na hak'ura tunda ba a so dole," Dariya Rinaz da Sabreen ke yi har ma da Ummi.




Sabeeha kuwa gaban ta ne ya yi mummunar fad'uwa jin abinda Umar ya fad'a kenan hakan yana nufin itama ya hak'ura da ita kenan take ta ji wasu hawaye na neman zubo mata saurin mayar da shi ta yi.



Ummi ta ce "Manta da Son kasan halin sa ni nan zan taimaka maka fad'a min wacece yarinyar," matsawa kusa da Ummi Umar ya k'ara yi ya ce "Zo kiji Ummi," rad'a ya yi mata yana kallon Sameeha.




Murmushi Ummi ta yi sannan ta ce "Kai ku bamu guri," tashi suka yi dukan su Ummi ta ce "No banda ke Sameeha zauna," komawa Sameeha ta yi tana kallon Umar sarai ta gane shi shine wanda suka yi karo.




Kallon ta Ummi ta yi ta ce "Daughter kina da saurayi kuwa?" Kallon ta Umar ya tsaya yi dan jin me zata ce.



Girgiza Kai ta yi ta ce "A'a Ummi," saurin sauke ajiyar zuciya Umar ya yi ya ce "Yawwa Ummi kinji bata da shi," hararar wasa Ummi ta yi masa ta ce "Babu ruwan ka a maganar mu if not zan fasa taimakon," jan bakin sa ya yi yayi shiru Dan kar Ummi ta fasa.




Mayar da kallon ta Ummi tayi kan Sameeha ta ce "Daughter tunda baki da saurayi to ni nayi miki yaro ne mai hankali da sanin ya kamata sannan zai baki kulawa sosai dan haka ki rik'e shi gam haka zalika nasan shima zai rik'e ki sosai da kulawa domin samun irin ki a yanzu abu ne mai wuya," ajiyar zuciya Ummi ta yi sannan ta cigaba da cewa "Idan ya yi miki laifi ki fad'a mun dan bazan lamunci rabuwa a soyayyar dana had'a ba sannan daughter karfa ki yi tunanin ba wai shi yace Yana son ki ba A'a da kansa ya ganki yake sonki," d'an tsayawa Ummi ta yi sannan ta ce "Kaga ni bakina ya gaji da magana ka cigaba da kanka," tana fad'ar haka ta mik'e hannun ta rik'e da wayar ta ta nufi stairs.



Kallon Sameeha ya yi sannan ya ce "Kin dai ji abinda Ummi tace ki rik'e ni gam domin idan ki ka rasani baza ki tab'a samun sumulmulin saurayi kamata ba," dariya maganar tasa ta bawa Sameeha sai ta ce "Idan nace bana yi fa karfa ka manta ban amsawa Ummi cewar ina sonka ba," d'an zare ido Umar ya yi ya ce "A'a Dan Allah karki ce haka Kuma ai nasan baza ki k'ibin zab'in Ummi ba," ya fad'a yana yin kalar tausayi.



Murmushi Sameeha ta yi domin dariya Umar ke ba ta Yana da barkwanci d'aga ido ta yi ta kalle shi ya langab'ar da kai ya ce "Ki tausaya mun Kinga ni maraya ne," dariya Sameeha ta yi ta ce "Bayan lokacin da ka bugeni a kai ko hak'uri baka bani ba," ta fad'a tana tura baki.



"Ayyah lokacin k'ararrawar zuciya ta kad'awa take yi a kanki dan tun lokacin ki ka tafi da imanin Umar," k'ara tura baki Sameeha ta yi ta ce "To bani hak'uri," Saurin saukowa daga kujera Umar ya yi ya ce "Wannan shi yafi komai sauk'i," rik'e kunnuwan sa ya yi ya ce "Kiyi hak'uri zuciyar Umar,"





Su Sabeeha dake lek'e ta saman bene Sabeeha ta ce "Ah lallai Sameeha dear irin wannan kwasar love haka," Sabreen ta buga tsalle ta ce "Shegiya Sameeha dear ashe dama haka ta iya love gaskiya za a kwashi love da ruwa ruwansa yaseen wayyo Allah," Sabeeha ta ce "Dear ku kalla gashi sun dace sosai gaskiya na taya ta murna sosai samun miji irin ya Umar abu ne mai wuya,"




Sai lokacin Rinaz ta ce "Gaskiya kam hakane sai dai wata ta samu Wanda ya fi shi amma tace bata yi," Sabreen ta ce "Wallahi kuwa Rinaz habibty," shiru Sabeeha ta yi domin tasan gaskiya suka fad'a a zuciyar ta ta ce hmm baza ku gane ba 'yammata.




Diamond watch d'in hannun ta Rinaz ta kalla sannan ta ce "Sister's time na tafiya fa ya kamata mu tafi shopping yanzu," down stairs suka nufa suka samu Sameeha da Umar sai fira suke abinsu suna dariya.



Suna zuwa Rinaz ta ce "Sameeha dear ki taso mu tafi time na tafiya," kallon ta Umar ya yi ya ce "Ina zaku kuma?" Sabreen ta yi caraf ta ce "Zamu je shopping ne jibi ne birthday d'in mu," hararar ta Sabeeha ta yi kamar ita aka tambaya.



Umar ya ce "Amma abin ba gayyata?" Sabreen ta ce "Karka damu ai indai Sameeha sister na wajen to kaima kana nan," hanyar fita Sabeeha ta yi a zuciyar ta ta ce na jinjinawa surutun ki Sabreen.




Kallon Sabeeha Umar ya yi ya ce "Ita ce Sabeehan Maleek ko?" Rinaz ta ce "Eh ita ce," Mik'ewa Umar ya yi ya ce "To muje nayi muku rakiya zuwa shopping d'in," suka fita a waje suka samu Sabeeha ta tsirawa k'ofar part d'in Maleek idanu domin burin ta bai wuce ganinsa ba.




Mota suka shiga su uku a back seat Sameeha a front seat.



Suna zuwa suka fara jidar kaya mayafai leases jakunkuna sarka agogo dogayen riguna kayan make up da sauran kayayyaki suna gamawa Umar ya biya kud'in sannan suka nufi gida.




Godiya suka yi masa sannan suka shige gida suka barshi tare da Sameeha suka yi sallama sannan ya tafi yana jin wata zazzafar soyayyar Sameeha a zuciyar sa.



Ko da suka shiga gida Ummi suka nunawa kayayyakin itama ta yaba kyansu domin kayane masu matuk'ar tsada ga kyau ta ce "An godewa son," daga haka suka tafi d'akin su.



Washe gari suka fita zuwa saloon bayan an gama musu suka ce da Alasan ya kaisu gidan abincin Hajiya fulani.



Da gudu Aysha ta rungume su Sabeeha tana murnar ganin su suma haka Office d'in Hajiya Fulani suka shiga suka gaishe ta ta amsa cikin fara'a suka ce dama sunzo su fad'awa Aysha birthday celebration d'in su ne da za a yi gobe.



Fulani ta ce "Masha Allah,Allah ya k'aro shekaru masu albarka," suka amsa da "Ameen," sun jima suna fira sannan suka yiwa Fulani sallama suka fita.




Rakiya wajen motor Aysha ta yi musu Rinaz ta kalle ta ta ce "Please goben kizo da wuri banda African time," Aysha ta ce "To ba damuwa sai goben," suka yi sallama suka tafi.


Daga nan gidan su Dija suka wuce da sallama suka shiga k'aton falon Dija dake zaune ta tare su cikin farin ciki suka rungume juna sannan suka zauna.




Sabreen ta ce "Ina Aunty fa?" Dija ta ce "Tana bedroom d'in ta," Rinaz ta ce "Beb me zaki kawo mana ne yunwa nake ji," Dija ta ce "Meye na tambayana bayan kinsan hanyar kitchen," tashi Rinaz ta yi ta shiga kitchen ta d'ebo snacks da lemuka ta kawo musu suka fara ci.




Aunty ce ta sauko daga stairs tana cewa "Muryar suwa nake ji kamar 'yan uku?" Suka ce "Mune aunty," suka gaishe ta ta amsa cikin fara'a sannan suka cigaba da firar yadda birthday celebration d'in zai kasance.




Sai yamma sannan suka yi musu Sallama suka tafi gida daidai lokacin da suka shiga gidan lokacin motocin Maleek ke fita bin motar da Maleek ke ciki Sabeeha ta yi da kallo duk da tinted windows ne ji take kamar ta tsayar da su dan kawai ta ganshi.




"Su waye a motar can?" Maleek ya fad'a yana kallon Salman.



"Sir Ina ga su Rinaz ne domin naji d'azu tana cema Alasan zai kai su saloon," shiru Maleek ya yi baice komai ba.




Washe gari tunda Wuri Sabeeha ta tashi ta gama had'a breakfast tana zaune gefen gado Rinaz ta shiga d'akin cikin wasu pink d'in sleeping dress da earpiece a kunnen ta da alama waya take amsawa.




Zama ta yi gefen Sabeeha tare da fad'in "Wow sweetheart da gaske to Allah ya dawo da Kai lafiya," daga haka ta katse Kiran Sabeeha ta ce "Man d'in ne?" Dariya Rinaz ta yi ta ce "Shine kam," sannan ta ce "Ina Sameeha dear ne?"




"Tana part d'in Umman Nasreen," cewar Sabeeha kallon Sabreen dake sharar bacci Rinaz ta yi ta ce "Ah lallai dole kiyi bacci jiya fa har 12 suna tare da ya Fauwaz," Sabeeha ta ce "Aikuwa dai bari na yi wanka," tana fad'ar haka ta cire kayan jikin ta ta d'aura towel ta shige wanka.




Tana fitowa ta samu Rinaz ma ta yi kwanciyar ta gefen Sabreen tana bacci.



Sameeha ce ta shiga d'akin da Sallama kana kallon ta kasan ta gaji zama ta yi tare da fad'in "Wash!" Sabeeha ta ce "Sorry dear,"




"Dear dama haka Sabreen ke shan aiki yau da bata je ba Baki ga aikin da nasha ba," Sameeha ta fad'a tare da nufar inda Sabreen ke kwance ta bata light kiss a goshin ta ta ce "Nagode dear," Murmushi Sabeeha ta yi ta ce "Nikam yunwa nake ji zan fita naci abinci," towel Sameeha ta zara ta ce "Nima Bari nayi wanka na biyo ki nima yunwa nake ji," daga haka ta shige toilet Sabeeha kuma ta k'arasa Shirin ta ta fice.



Kitchen ta shiga ta had'a tea d'in ta mai kauri sannan ta d'ebi chips a plate ta nufi falo ta zauna taci ta k'oshi sannan ta Kai kayan kitchen ta fito can gefen falon wajen wasu set d'in kujeru ta je ta kwanta sai bacci.




Da yamma suka fara Shirin su takanas Ummi tasa aka d'auko musu make over ta shek'e musu fuskokin su sunyi kyau har sun gaji dogayen rigunan dark blue d'in material suka sa duka su hud'un anyi musu d'aurin da red abu kamar ka sace su ka gudu musamman su Sabeeha dan baza ka iya banbance su ba sun zama su uku iri d'aya.



Falo suka fita Ummi ta kalle su ta ce "Masha Allah yarana kunyi kyau," suka had'a baki wajen cewa "Thank you Ummi," sannan suka zazzauna.




Wayar ta Sabreen ta d'auka tare da dialing number d'in Fauwaz yana d'agawa ta ce "Hello my one kana ta Ina ne haka?" Daga can ya ce "Sorry cwt gani nan fitowa," Daga haka ya katse Kiran.




K'ofar part d'in Fauwaz d'in aka bud'e ya shigo ya yi matuk'ar kyau cikin k'ananun kaya sai k'amshi yake zabgawa domin Fauwaz akwai kyau da d'aukar wanka tunda ya shiga falon yake kallon su shi a dole yana so ya gano Sabreen a cikin su.



Zama ya yi a kujerar da take facing Wacce suke kai yana kallon su d'aya bayan d'aya sannan ya kalli Ummi ya ce "Nikam Ummi Ina Sabreen cikin su?" Dariya falon ya d'auka Sabreen ta ce "Ashe dama my one baza ka iya gane ni ba?" Ya ce "No zan iya mana baby amma idan bakwa tare kamar haka," k'ofar falon aka bud'e aka shiga Dija ce tasha kyau cikin doguwar riga da murna suka tare ta ita kuwa sai yaba kyan da suka yi take yi.


Suna zaune nan Umar ya shiga falon yasha wanka cikin dark blue d'in k'ananan kaya ya yi kyau ba k'arya yana shiga yabi su Sabeeha da ido domin sunyi kyau har zai yi magana Ummi ta ce "Son ya kamata ku tafi time na k'urewa," kallon Rolex watch d'in hannunsa ya yi ya ce "Ummi daga wajen Maleek nake akan yazo mu tafi sai ya ce Kawai muje zai zo daga baya," Ummi ta ce "Shikenan kuje kawai," hanyar fita suka yi Sabeeha ta ce "To Ummi kefa sai yaushe?"




"Karku damu zamu zo tare da son," cewar Ummi su Kuma suka fita.



A waje suka ci karo da Aysha da ta dad'e da zuwa amma tun a gate d'in farko aka tare ta dan bincike sai da Salman ya yi magana sannan aka barta ta shiga itama ta yi kyau ba k'arya cikin doguwar riga pich color.




Ba b'ata lokaci suka shiga mota suka tafi mota biyu suka yi.



B'angaren Kawu Bala da Abba kuwa sai da labari ya samu Kawu Bala cewar sojojin da suka zo gidan Abba sun tafi sannan ya nufi gidan a zaune ya samu Abban kan tabarma kallo d'aya zaka yi masa kasan yana cikin farin ciki.



Kawu Bala ya ce "Kai habu na samu labarin sojoji sunzo gidan ka hala cikin yaran ka ne d'aya ta jawo maka masifa ko?" Cikin farin ciki Abba ya kalli yayan nasa ya ce "A'a yaya yau na samu labarin inda Maryam take Abba anga Maryam d'inta," daram dam gaban Kawu Bala ya fad'i maimakon ya yi farin ciki da ganin matar k'aninsa da aka yi sai ma wata uwar zufa da ya had'a yasa Kai ya fice kawai.




Tafiya kawu Bala yake kamar zai kifa tsabar sauri tun daga zaure yake k'wala kiran "Lantana! lantana!!"



"Haba malam wanne irin kira ne wannan kamar naci bashi lafiya dai ko?" Yarce gumi Kawu ya yi sannan ya ce "Ina fa lafiya Lantana Maryam zata dawo yanzu Habu ke fad'a mun ya samu labarin ta," take itama Lantana ta rud'e ta ce "Shikenan mun shiga uku malam bamu ga ta zama ba mu tafi wajen bokanya kawai," gyalen ta ta yayi ba akan igiyar shanya suka fice suna zuba uban sauri.


Har titi suka fita suka hau mota tafiyar da suka yi ba wata mai nisa bace sannan aka ajiye su suka hau machine sai da suka yi tafiya mai nisa sannan suka sauka suka fara tafiyar k'afa wani daji suka nufa mai sauk'in bishiyu sai da suka yi tafiya mai nisan gaske sannan suka isa wata bukka.




Tun kafin su k'arasa wajen bukkar wata murya mai ban tsoro ta ce "Ku dakata dama sai da na fad'a muku idan har ku ka yi kuskuren k'in barbad'a wannan maganin na kwana d'aya a k'ofar gidan to tabbas zata dawo kuma sannan kamar yadda ku ka hana Habu yin arziki zai yi arziki sannan ku kuma zaku d'and'ana talauci mai zafi ku je ku tafi ku jira dawowar ta domin tabbas zata dawo ba abinda zamu iya," take jikin su Kawu ya mutu suka juya a sanyaye suka nufi gida.





Tun a hanya Kawu Bala ke fad'a "Wallahi Lantana ke dai ba mutuniyar arzik'i bace akan meyasa baki barbad'a maganin na kwana d'aya ba?" Lantana ta share

Please Login or Register in order to submit comment