Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tafi," wata 'yar aiki Maleek ya ga ta fito daga kitchen nan ya fara balbala masifa akan sunbar waje da dirty irin haka duk ranar da suka Kuma a bakin aikin su zubewa ta yi tana bashi hak'uri bai damu ba ya ja hannun Sabeeha taku d'aya ta yi tasa masa kukan shagwab'a a rud'e ya ce "Baby da wata matsalacce?" Bubbuga k'afa ta fara yi ta ce "Toba k'afana ke yi mun zafi ba ni bazan iya tafiya ba sai dai ka goyani," kallon ta ya tsaya yi yasan ba wani k'afar ta dake zafi tsabar rigimace kawai irin na ta ya ce "Wannan ai shi yafi komai sauk'i," ya durk'usa ta haye suka nufi stairs.




Nasreen dake lab'e kuwa wani bak'in ciki ne ya turnik'e ta a fili ta ce "Ai Wallahi gara ma duk ku mutu a huta," wata 'yar aiki dake bayan ta ta ce "Hajiya su mutu Kuma?" Da sauri Nasreen ta juya ta kalli Jamila dake tsaye domin batasan a fili ta yi maganar ba ganin Jamila ce Kuma ta aminta da ita sai ta ce "Eh Jamila so nake su mutu kinsan Ina son Ya Maleek ai ko?"




"Eh sosai ma kuwa ranki ya dad'e," Jamila ta fad'a tana russunawa "To amma shi baya sona yafi son waccan aljanar saboda haka sai naga bayan su," Jamila irin jahilan k'auyen nan ce ba wata babba bace Amma ta girmi Nasreen 'ya'yan ta biyu suna wajen mahaifiyar ta ta ce "Ai ranki ya dad'e nima lokacin da nake da aure haka babban yarana ya auro wata ya nuna Mata so fiye dani sai kawai nabi dare na kashe shi kowa ma ya rasa," dariya Nasreen ta yi ta ce "Gaskiya za aje dake Jamila dan haka zan had'a kai dake," Jamila ta ce "Baki da matsala domin har yanzu ba Wanda yasan ni na kashe mijina an d'auka b'arayi ne," Nan suka cigaba da firar su.




Maleek kuwa suna shiga d'aki ya ajiye ta saman gado sannan suka shige wanka bayan sun fito ko kaya basu tsaya sawa ba suka shige blanket suka fara farantawa juna rai.


A haka aka yi sati d'aya kullum da irin tsokana da neman fad'an da Nasreen zata yi amma basa kula ta domin sun Mai da ita mahaukaciya Maleek kam baisan kulata ne domin idan yace zai biye mata sai ya karyata ya zubar.



Maleek ne zaune a d'ayan part d'insa shi da Salman ya kalli Salman ya ce "Salman a yau nake so kuje ku yi abinda nasa ku kuje," Salman ya ce "Ok boss," Yana fad'ar haka ya fice.




Mota biyu na sojoji suka yi suka nufi k'auye suna zuwa nesa da gidan sadam suka yi parking suna cikin mota basu fito ba wani mak'ocin Sadam ya fito daga gidan sa Horn Salman ya danna masa kallon wajen mutumin ya yi aka Kuma yi masa horn wajen motar ya nufa Yana jin d'ard'ar sai da ya kusa da motar sannan ya tsaya ya nannad'e hannun rigar sa da k'afar wandon sa a zuciyar sa yana fad'in saboda ko abun gudu zai kama sai inda maina ya k'are.




Yana k'arasawa wajen Salman ya sauke glass ganinsa da kayan sojojine yasa mutumin k'ara rud'ewa Salman ya bashi hannu suka gaisa sannan Salman ya ce "Sunanka fa?" Mutumin ya ce "Sunana Sunusi," jinjina Kai Salman ya yi ya ce "Dama munzo nan ne domin mu nemi mai yi mana aiki mutum d'aya kamar yadda ka gani mu sojojine sannan aikin ba wamu za ayi shi ba ogan mu ne yake so a samu Mai yiwa mahaifiyar sa aiki," jinjina Kai sunusi ya yi ya ce "Kai amma naso ni ne zani aikin nan amma ba dama domin a gidana da iyalaina da mahaifiya ta Kuma nine komai nasu bazai yuwu na barsu ba,"




"Ka ga malam sunusi ba lallai fa sai Kai ba," Salman ya fad'a domin ai dama aikin su ba a kansa bane.



Sunusi ya ce "Shikenan amma akwai wani Mai suna sadam aikin yi yake nema ido rufe ko wanne iri ne saboda duk garin nan da ba Wanda ya Kai shi kud'i yanzu Kuma yafi kowa talauci sannan kum...,"




Salman ya ce "Is enough Kira mana shi," juyawa sunusi ya yi a zuciyar sa yace is enote d'in yake nufi oho da ganinsa dai d'an gayu ne sallama ya rangad'a k'ofar gidan Sadam daga ciki Salman ya amsa ya fito duk ya canja kamanni kamar ba shi ba bayan sun gaisa Sunusi yayi masa bayanin abinda ke faruwa cikin jin dad'i Sadam ya fara yiwa sunusi godiya shi kuwa sunusi sai wani hura hanci yake yi Wai shi a lallai ya yiwa wani hanyar arzik'i.




Wajen motar suka nufa ba tare da b'ata lokaci ba Sadam ya ce "Sunusi ya fad'a mun komai na amince muje kawai," bud'e masa akayi ya shiga yana d'agawa sunusi hannu.
[10/25, 8:52 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️



RUBUTAWA DAGA
HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ)




SADAUKARWA GA
MY DAUGHTER SABEEHA
BILKISU Z.YA'U (🅱️K)
AISHA MAGAJI DABO (AMA)





Page 29


Sabeeha ce zaune a falon ta tana yin waya bayani take yi Mata akan plan d'in su ita da Maleek akan daidai ta auren Sadam da Zainabu Doctor ta ji dad'in hakan da haka suka gama wayar tana ajiye wayar Maleek ya fito daga bedroom d'in ta da waya mak'ale a kunnensa shima da alamar yake.




Hanyar fita ya nufa "Am Sweetheart," tsayawa ya yi tare da katse wayar k'arasawa ta yi ta shagwab'e fuska ta ce "Ina Kuma zaka?" Shafa kyakkyawar fuskar ta ya yi ya ce "Zani waje ne yanzu zan dawo," gyad'a kai ta yi ta koma cikin falon shi Kuma ya fita a falo ya samu Nasreen da Jamila suna magana suna ganinsa suka yi shiru bai damu ba ya fice abinsa.




Yana fita Salman tare da sauran sojojin sa suka sara masa ya ce "Salman ya ake ciki?"



"Boss yana cikin motor," gyad'a kai Maleek ya yi tare da shafa sajen sa ya ce "Yanzu abinda za ayi Salman kuje dashi gidan Mama tasan komai," Salman ya ce "Angama boss," hararar sa Maleek ya yi ya ce "Boss or friend," dariya Salman ya yi ya ce "Dukan su," murmushi kawai Maleek ya yi ya juya cikin gidan.




Nan ma yana shiga kamar d'azu su Nasreen suna ganinsa suka yi gum sharewa ya yi har ya fara taka stairs sai Kuma ya tsaya tare da waigawa ya kalli Jamila da jikin ta har ya fara rawa ya ce "Ke Dan uwar ki tashi kibar gidan nan idan na sake ganin ki sai kin gane naki wasa ne," jiki na rawa ta mik'e ta yi waje har tana had'awa da tuntub'e.




"Haba ya male..," Maleek ya yi saurin d'aga mata hannu ya ce "Karki kuskura wallahi Nasreen kice mun wani Abu a nan if not you see what happens stupid," yana fad'in haka ya k'arasa hayewa stairs d'in.




Tsaki Nasreen ta ja ta ce "Wallahi zaku gane kuren ku da Kai da 'yar gold d'in taka mtswww,"



Salman kuwa suna gama parking daidai lokacin Mama na fitowa daga part d'in ta zuwa part d'in Kawu Bala k'arasawa suka yi wajen ta tare da Sadam gaishe ta suka yi ta amsa cikin fara'a Sadam kuwa tuni ya zube Yana kwasar gaisuwa amsawa Mama ta yi tana k'arewa sadam d'in kallo sannan ta kalli Salman ta ce "Zaku iya tafiya," ya amsa da "Toh," sannan suka shiga mota suka tafi.




Kiran Faisal a waya Mama ta yi akan tana son ganinsa ba b'ata lokaci sai gashi ya gaishe ta ta amsa ta ce "Am Faisal kuje da wannan ya yi wanka sannan kazo ka amsar masa abinci wajen Halima then ga wannan kaje botique ka siyo mas kaya," ta fad'a tare da bud'e jakar ta ta deb'o kud'i masu yawa ta bashi ya ce "Tom madam," Sadam kuwa godiya ya fara kamar ya ari baki Mama ta ce "No bakomai komai nayi maka ai bazan iya biyan ka abinda kayi mun ba aikin ka shine bawa flowers ruwa," ya ce "To ranki ya dad'e," daga haka ta wuce zuwa part d'in su Lantana Sadam Kuma yabi bayan Faisal yana tunanin to shi me ya yiwa Doctor da tace komai tayi masa baza ta iya biyan sa abinda ya yi mata ba.





Doctor kuwa itama tafiya take tana tunani tare da k'udurar niyyar kyautatawa Sadam saboda abinda ya yi Mata babba ne ya d'auki d'awainiyar 'yan ukun ta duk da ba wai haka kawai ya yi ba Dan yana son Sabeeha ne amma duk da haka taji dad'i domin ba don ya d'auki d'awainiyar su ba Kuma basu da kud'in yiwa kansu hidima zasu iya fad'awa wata hanyar gashi kuma ya yi abinda baza a iya biyan sa ba domin ba dan shi ba tasan yaran ta basu yi karatu ba haka zasu taso with empty brains amma ta sanadin sa sunyi primary da secondary sai Kuma cigaba da wannan tunanin ta k'arasa part d'in Kawu.




Da sallama ta shiga Zainabu dake zaune ta ce "Sannu da Zuwa Mama,"



"Yawwa Zainab ya Habib?" Zainabu da ta kashe d'auri cikin doguwar rigar atamfa ta ce "Yana nan lafiya bacci yake yi," gyad'a kai Mama ta yi.




Lantana ce ta fito daga kitchen domin ta jiyo muryar Mama ta zauna suka gaisa Mama ta sake yi musu bayani akan zuwan Sadam d'in Zainabu kuwa jin Sadam na gidan ba k'aramun dad'i taji ba.




Wayar Doctor ce ta fara ringing tana dubawa ta ga Sabeeha ce tayi picking daga can Sabeeha dake kwance jikin Maleek ta ce "Mamana Sadam ya iso ko?" Doctor ta ce "Eh ya iso,"



"To Mama Ina Zainab?" Sabeeha ta tambaya tare da tsotsar lips d'in Maleek "Gata," Mama ta fad'a tare da mik'awa Zainabu wayar karb'a ta yi ta ce "Hello Aunty," daga can Sabeeha ta ce "Zainab kina jina,"




"Eh," Zainabu ta fad'a tare da barin falon zuwa bedroom d'inta.



"Abinda nake so dake shine kamar yadda na fad'a Miki a baya sai fa kin matsar da soyayyar da kike wa Sadam gefe idan har kina so ki samu taki soyayyar ki dinga kwalliya kina ado kinji ko?" Zainabu ta ce "To aunty zanyi yadda ki kace," Sabeeha ta ce "Wannan shine ke dai macece ba saina tsaya koya Miki komai ba sai anjima,"



"To Nagode Aunty," Zainabu ta fad'a ba tare da tasan Sabeeha ta ma kashe kiran ba saboda wasan da suke yi da Maleek ne yafi k'arfin ta.


Kwanan Sadam biyu a gidan amma har ya fara dawowa hayyacin sa yaci mai kyau yasha mai kyau Wanda ko a da baicin kamar sa domin ko da ruwan pure water yake sha amma gidan Doctor har gate man ruwan jarka yake sha ga kaya masu tsada da Mama tasa aka jido masa da takalma sannan tun washe gari ya fara aikin sa na ba flowers ruwa.




Yanzu ma gama aikin sa kenan ya zauna kusa da Malam Musa gate man suna fira sai kawai ya hango wata ta fito kamar Zainabu da sauri ya mik'e tsaye ya ce "Zainabu!," Gate man ya ce "Ka santa ne?" Sadam kuwa ya ma kasa magana.




Zainabu kuwa fitowar ta daga part d'in su kenan zata je part d'in Mama tasha kyau cikin riga da skirt na shadda ta yi kyau ba laifi domin ta waye ta yi fresh abinta ta iya kwalliya yanzu ma Tasha kwalliya ta yi d'aurin ta da malha tana taunar chewing gum kunnen ta mak'ale da earphone.




D'an kallon wajen ta yi ta ga Sadam ya saki baki da hanci da idanu Yana kallon ta itama tsayawa kallon sa ta yi ko me ta tuna Kuma sai ta tab'e baki tare da jan tsaki tayi gaba abinta yayin da Sadam ya bita dana mujiya.




Ganin ta b'acewa ganinsa yasa ya koma dab'ar ya zauna ya kalli Musa ya ce "Malam Musa wannan ba Zainabu ta bace?" Kallon baka da hankali Malam Musa ya yi masa ya ce "Bangane Zainabun ka ba kwata-kwata yaushe ne kazo nan gidan da zaka kirata taka ko da yake bansani ba amma wannan dai sunanta Zainab Kuma 'yar gidan nan ce," shiru Sadam ya yi sannan ya ce "Wannan ma sunanta Zainab d'in ce ni Zainabun da nake magana matata ce tsautsayi ya rabamu Amma dakyar idan wannan ita ce domin ita tawa ramammiya ce Wannan ta fita k'iba sannan tawa bak'ace sosai Amma wannan baza a kirata fara ba sannan baza a Kira ta bak'a ba Kai gaba d'aya ma wannan tafi tawa komai da wayewa da komai nifa tawa 'yar k'auye ce Kai nasan kamace kawai," dariya malam Musa ke kyalkyalawa kamar wani mahaukaci sabon kamu Dan har wani kwanciya yake akan bencin da suke zaune sannan ya ce "Kai Sadam banda ma kai bagashare ne yaushe sifofin daka zayyano na Zainabun ka za a had'a shi dana wannan Zainab d'in mu?" Tsaki kawai Sadam ya ja baice komai ba shi a lallai an ciwa Zainabun sa mutunci.




Zainabu kuwa can wajen Mama ta zauna suka yi ta fira har sai da ta ji an Kira sallar azhar sannan ta yiwa Mama Sallama ta tafi domin tasan lokacin Sadam ya tafi Masallaci domin wannan Shirin Sabeeha ne domin ta ce sau d'aya tak a rana zata dinga bari tana had'uwa da Sadam.



Shi kuwa Sadam tunda ya ga shigewar Zainabu shigewar part d'in Doctor ya zauna ya zubawa k'ofar ido domin ganin fitowar ta amma shiru Kiran sallar da akayi ne yasa ya tafi masallaci yanzu ma Yana dawowa ya Kuma samun waje ya zauna shi lallai yana jiran fitowar ta amma har dare shiru sallah kad'ai ke tashin sa ga wata uwar yunwa yana ji tun d'azu Faisal yace an kai masa abinci amma yak'i zuwa yaci.





Duk abinda ke faruwa Zainabu na gani ta window dariya ita ya bata ma har ta gaji ta kwanta bacci Sadam kuwa sai da ya fara gyangyad'i sannan ya hak'ura ya tafi b'angaren su.




Washe gari da yamma ma yana cikin bawa flowers ruwa ya kuma ganinta ta fito daga part d'in su zuwa part d'in Doctor taci kwalliya cikin black d'in doguwar riga sai k'amshi take yi abinta tiyon hannunsa ya fad'i k'asa da ido ya bita ji yake kamar ya yi mata sai dai yana shakkar hakan har Zainabu ta wuce yana kallon ta ajiyar zuciya ya sauke.



Malam Musa dake bayan sa ya kyalkyale da dariya ya ce "Zainab d'in mu ba Zainabun ka bace," tsaki Sadam ya ja sannan ya gama aikin sa ya samu waje ya zauna Yana aikin kallon k'ofar part d'in Doctor ko Zainabu zata fito amma shiru kake ji.



Zainabu kuwa wajen su Halima ta je suka fara fira kasancewar Doctor ta tafi hospital aiki ta taya su sai da aka shiga sallar magrib sannan tabar part d'in lokacin Doctor ta dawo.


Sadam kuwa Yana dawowa ya cigaba da aikin jiran fitowar ta amma ranar ma shiru sai Malam Musa ya Kai ya kawo ya kalle shi ya kyalkyale da dariya ya ce "Zainab d'in mu ce ba Zainabun ka ba," shi dai Sadam shiru Dan shi baisan yana son Zainabu har haka ba sai yanzu da ya ga Mai kama da ita dan har yanzu bai tab'a had'uwa da Kawu Bala ba da Lantana ba bare Kuma Abba da yanzu baya samun zama.




Ranar ma har dare shiru damun sa da malam Musa ya yi ne da "Zainab d'in muce ba Zainabun ka ba," yasa ya tafi flat d'in su zuciyar sa fal tunani.

A haka har akayi sati kullum sai Sadam ya ga Zainabu sau d'aya cikin kwalliya da k'amshi ga wani aji da take ja masa ko kallon sa bata yi shi kuwa idon sa na kanta gashi ko Habibi bata fita da shi Yana cikin gida wajen Lantana haka zai ta zama Yana jiran ta amma shiru ita kuwa suna shiga sallah take guduwa part d'in su abun ya damu Sadam gashi ba rashin ci da sha da sutura amma har ya rame saboda damuwa har ya fara tunanin komawa k'auye neman Zainabun sa domin yanzu mugun sonta yake yi gashi wannan Zainab d'in kullum sau d'aya yake ganinta sannan shakkar yi Mata magana yake balle ya tambaye ta ko fuska ma bai gani ba sai dai kullum malam Musa ya dame shi da "Zainab d'in muce ba Zainabun ka ba,"


"Na bani ni Sabeeha yanzu Ina pretty take yau fa tunda na tashi banganta ba," Sabeeha ta fad'a tare da rik'e k'ugu cigaba da pretty ta yi tun daga bedroom har toilet da falo da kitchen da store tana Kiran ta amma shiru domin da tana nan tana jin an Kira sunanta zata je da gudu idon Sabeeha har ya fara tara k'wallah k'aramun veil d'inta red ta d'auka ta yafa saman kanta bak'ak'en riga da wando ne a jikin ta tayi kyau sosai ga kanta yasha gyara sosai sai k'amshi take ta yi k'iba ga wani haske da tayi down stairs ta nufa tana k'wala Kiran "Pretty my pretty," Amma shiru.




Cikin falon ta k'arasa turus ta tsaya hango pretty da tayi kwance a gefe ga jini duk jikin ta a gefe Kuma Nasreen ce tsaye da wuk'a a hannunta wuk'ar duk jini domin yanzu ta k'una bata tsoron k'auri domin duk neman fitinar ta basa kulata hakan ne yasa yau ta tab'o pretty wacce tasan Sabeeha na sonta sosai.




Wasu zafafan hawaye ne suka zubowa Sabeeha a ido da gudu ta k'arasa wajen pretty ta d'auka tana jijjigata amma Ina pretty rai yayi halin sa kuka sosai Sabeeha ke yi.




Daidai lokacin Maleek ya yi sallama jin muryar sa yasa Sabeeha ta tashi tayi wajen sa da gudu ta rungume ta fashe masa da kuka gaba d'aya ta gama mak'alk'ale shi a rikice ya ce "Ya Salam baby what happened me yake faruwa?" Ta kasa magana sai kukan da take yi rik'e fuskar ta ya yi da duka hannayen sa ya ce "Please ki fad'amun meya faru," cikin kuka muryar ta har sark'ewa take yi ta ce "P...ree..tty," ta fad'a tare da nuna masa inda gawar pretty take.



Da sauri ya k'arasa wajen kallo d'aya ya yiwa magen yasan ta mutu Kuma yankata aka yi da wuk'a take idanunsa ya yi jajir domin shima Yana son magen akwai ta da shiga rai.




Nasreen Ba tasan ta aikata kuskure ba sai da ta ga yadda fuskar Maleek ta koma take jikin ta ya fara rawa.



Cikin d'aga murya Maleek ya ce "Waye!! Waye ya aikata hakan?".
[10/25, 8:55 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️


RUBUTAWA DAGA
HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ)


SADAUKARWA GA
MY DAUGHTER SABEEHA
BILKISU Z.YA'U (🅱️K)
AISHA MAGAJI DABO (AMA)



Page 30

Wuk'ar dake hannun Nasreen ce tsabar tsoro ta fad'i k'asa wajen Maleek ya kalla ganin yadda jikin Nasreen d'in ke rawa ga kuma wuk'ar da ta yar duk jini ya tabbatar masa da Nasreen d'in ce ta kashe Pretty.


Gudurin ta ya nufa a zafafe ya d'aga hannu ya zabga Mata maruka har biyu k'asa ta durk'ushe tana kuka kamar cristiano Ronaldo ke buga k'wallo haka Maleek yayi ball da Nasreen har sai da ta Kai wajen stairs case wata razananniyar k'ara ta saki wacce tasa Sabeeha dake durk'ushe tana kuka rintse idanunta Hawaye suna zuba daga idanunta ba k'akkautawa.



Wajen Nasreen Maleek ya nufa ya jata k'i zuwa sama Yana cewa "Wallahi karki kuskura ki cikamun kunnen mata da ihu," har cikin d'akin ta ya shiga da ita yasa key ya d'auki belt ya fara dukan ta iya k'arfin sa Aikuwa Banda ihu ba abinda Nasreen ke yi taji dukan jarumin soja ihu take yi iya k'arfinta kamar zata fasa mak'ogaron ta.




Ihun ta yasa duka 'yan aikin ta fitowa su yi cirko_cirko a falo ba damar zuwa ceto sai da ya yi Mata lilis ya fito kai tsaye falon ya koma har lokacin Sabeeha na durk'ushe a gaban gawar pretty tana kuka k'arasawa wajen ya yi ya d'ago ta ya rungume ta ita rungume shi tayi sosai tana k'ara sakin wani kukan domin ba k'aramun so take yiwa pretty ba ga Kuma sabon da suka yi da ita shafa bayan ta Maleek ke yi a hankali cikin k'asa da murya ya ce "Sorry please baby kukan ya isa haka," maimakon ta yi shiru sai ma k'ara volume da tayi.



Kallon 'yan aikin dake zagaye da su ya yi ya ce "Me ku ke jira ku gyara wajen," ya fad'a tare da jan hannun Sabeeha su nufi stairs shima kansa Maleek farar shaddar sa ta b'aci da jini Sabeeha kuwa waigen pretty da Jamila ke niyyar d'auke ta a wajen wasu zafafan hawaye ne suka Kuma zubo mata.



Suna shiga falon ta zauna aka kujera tare da kifa kanta jikin hannun kujerar ta cigaba da kukan ta tausayin ta duk ya cika Maleek bedroom ya wuce domin tsaftace jikin sa.



Wayar Sabeeha ce ta fara ringing ganin Mai kiran ne yasa ta d'aga wayar Sameeha ta ce "Dear kin shiga Ina na nake ta Kiran wayar ki Baki yi picking ba?" Kuka kawai Sabeeha tasa rikicewa Sameeha ta yi ta ce "Me ya faru dear?" Nan ma shiru ba magana sai kuka da Sabeeha ke yi tambayar duniya Sameeha ta yi Mata amma tak'i magana sai gajiya Sameeha ta yi ta katse kiran.



Tana nan zaune har Maleek ya fito yana cewa "Wallahi Umar Nasreen ce ta kashe mata magen ta," daga can Umar ya ce "Kai amma wannan anyi 'yar iska Wallahi shegiya Kai kamar murhun giya ai da Meeha ta kira 'yar gidan ka taji tana kuka ka ganta itama sai kukan take yi shiyasa ba shiri na Kira naji ko lafiya amma Nasreen an yi shegiya ice ko dai kaci uwar ta?" D'an murmusawa Maleek ya yi ya ce "uhm uhm fa,"



"Mtsww Amma Wallahi MG ka kwafsa ai da ni ne da tuni ta kwashi kashin ta a hannu," wannan karon dariya Maleek ya yi ya katse Kiran.



Daga can Sameeha ta ce "Please me yake faruwa Hubby?" Ajiyar zuciya ya yi ya ce "Wai Nasreen ce ta kashewa sister d'in mu Mage," ware ido Sameeha ta yi hawaye na zubo Mata ta ce "Kenan ta kashe preetty?"



"Pretty," Umar ya maimata sannan ya ce "May be ita ce kam," kuka sosai ya ga Sameeha tasa nan yaita aikin rarrashi dakyar ta yi shiru.



Maleek kuwa k'arasawa wajen ta ya yi ya durk'usa a gaban ta ya ce "Please baby kibar kukan haka kinji," bata d'aga Kai ta kalle shi ba sannan bata bar kukan ba dafe kansa ya yi ya ce "Ya Salam meyasa Nasreen zata yi mun haka ne dama batasan kwanakin nan rigima kike ji ba mtsww," d'an dafata ya yi ya ce "Sorry taso muje na siya Miki wata," sai lokacin ta d'aga Kai ta kalle shi ya ce "Yes let's go," ya fad'a tare da rik'o hannunta ta mik'e suka shiga d'aki tasa hijabi yana rik'e da hannunta suka fita.


Mota ya bud'e Mata ta shiga sannan ya shiga har zai ja Salman ya ce "Sir bai kamata ka fita kai d'aya ba," ba tare da damuwa ba ya ce "No karku damu yanzu zamu dawo," daga haka ya ja motar suka bar gidan.




Nasreen kuwa da taimakon Jamila ta farfad'o daga suman da ta yi ta taimaka mata tayi wanka ta gasa jiki tasha magani sai dai zazzafi ya rufe ta kwanciya ta yi har lokacin kuka take yi abinka da 'yar gata ita fa ko mari Sabeeha ce ta fara Marin ta a rayuwar ta.


Maleek kuwa yana yin parking suka shiga gurin parking ya yi sannan yana rik'e da hannun ta suka shiga gurin ma'aikatan wajen kallon su ya yi ya ce "Na kawo ta ne ta zab'a wacce ranta yake so," suka amsa da "To ranka ya dad'e," fara zagaya wajen suka yi Sabeeha sai zuba jajayen idanunta take yi tana kallon kyawawan magunan wajen wad'anda suka fi pretty kyau sai dai ita lallai sai irin ta ganin babu aikuwa ba kunya ta zama ta kama kuka har da shura k'afafu.



Ware ido Maleek ya yi yana kallon ta domin yayi mamakin wannan aikin da take yi wannan wacce iriyar rigima ce ya fad'a a ransa sannan ya d'auke ta cak ya fara tafiya yana fad'in "Baby wannan wacce iriyar rigima ce haka?"



"Ni kawai kace matar ka ta biyani pretty ta kuma na ga Wanda ya bani yace na kula masa da ita sosai," ta fad'a tana k'ok'arin sauka ya ce "Ya isa ai na zab'a miki mai kyau zasu kawo

Please Login or Register in order to submit comment