Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi breakfast ba ranar ma haka suka wuni neman su Sabeeha amma basu ba labarin su domin Ummi har Fulani ta kira ta tambaya Amma aka ce basu je ba.



Haka ranar ma Maleek ya komawa Ummi kamar zai yi mata kuka dakyar ta rarrashe shi amma duk yadda taso ya ci Abinci k'in ci ya yi ranar ma haka ya kwana bacin abinci ga rashin bacci.



Sabeeha ce kwance da daddare haka kawai taji bacci ya k'auracewa idanunta sai juyi take yi Sabreen ta yi juyi ta ce "Sabeeha dear lafiya kuwa? A hankali ta ce "Bansaniba dear banjin bacci ne kawai amma kina ganin mu koma gidan nan kuwa?" Sabreen ta ce "Eh mu koma mana idan bamu koma ba Ina zamu je?" Sameeha dake jinsu ta ce "Nima ji nake kamar kar mu koma saboda kar suyi tunanin saboda dukiyar su zamu koma," Sabeeha ta ce "Nima abinda nake tunani kenan sannan Wallahi yayan Rinaz bai da kirki akan Matar sa ita Kuma da gani makira ce tunda har ta nuna bata son mu nasan kad'an muka fara gani a cikin makircin ta Ni nasan tabbas akwai abinda zai faru gaba," Sabreen ta ce "Haka ne Kuma dear yanzu meye mafita?" Sabeeha ta ce "Kawai gobe mubar gidan nan," haka suka tsayar da shawarar gobe zasu bar gidan gara ko k'auye ne su koma abinda basu saniba shine duk firar su Dija na jinsu sannan sun burge ta ta wani b'angaren sai dai bata ji dad'in tafiyar da suka ce zasu yi ba domin har ta saba da au gasu da shiga rai sannan tasan indai ta b'angaren su Ummi ne basu da matsala sai dai Nasreen domin bata da kirki ko kad'an.



Washe gari da wani zazzafan zazzab'i Maleek ya tashi domin tun daren jiya ya rufe shi gashi yak'i ya sanarwa kowa Yana kwance lullub'e da blanket fuskar sa ta yi jajir da kyar ya iya tashi ya yi sallah ya yi wanka ya koma ya kwanta gashi bai ci komai ba balle ayi maganar magani hatta soldier's d'insa dake tsaron sa basu san baida lafiya ba gashi har lokacin Nasreen bata dena Kiran sa ba.



Kasa jurewa Nasreen ta yi ta shirya ta nufi part d'in nasa tura k'ofar d'akin nasa ta yi ta shiga can ta hango shi duk'un k'une a blanket da sauri ta k'arasa ta ce "Ya Maleek baka da lafiya ne?" Saurin runtse idanunsa ya yi domin baya son ganinta domin ita ce silar faruwar komai ganin yayi mata banza ne yasa ta zari wayar sa d'aya dake bedside drower ta lalubi number d'in Ummi ta kira lokacin Ummi zata tafi office ta kalli Rinaz ta ce "Mamana zan tafi office daga nan zan je na bayar da cigiyar su Sabeeha na damu da rashin ganinsu gari ko garin su bamu saniba gashi son ya damu sosai," jinjina kai Rinaz ta yi.



Wayar Ummi ce ta d'auki k'ara ta d'auka sai Kuma ta ce "Subhanallah gani nan zuwa," tana fad'ar haka ta nufi k'ofa hankalin ta a tashe domin sanin kanta ne Maleek Yana da ciwon zuciya Wanda tun yana yaro yake da shi Kuma bai fiya tashi ba sai ya shiga damuwa.



Ganin Ummi ta fita hankalin ta a tashe yasa Rinaz binta da gudu tana tambayar ta lafiya ba abinda Ummi ta iya furtawa mota kawai suka shiga zuwa part d'in Maleek.



Da sauri suka shiga d'akin suka same sa kwance a cikin blanket da sauri Ummi ta k'arasa ta ce "Son," sai lokacin ya bud'e idanun sa da suka yi jajir ya kalli Ummi ba tare da yace komai ba dafa goshin sa ta yi taji zafi zau ta ce "Son tashi mu tafi hospital," janye masa blanket d'in ta yi ya mik'e duk da bai da lafiya jarumtar sa na nan domin mik'ewa ya yi tsaf Ummi ta rik'e hannunsa suka fita Rinaz na biye da su ita da Nasreen.



Suna fita Ummi ta bada umarnin a kawo motoci ba tare da b'ata lokaci ba aka jera motoci suka shiga sojojin suka ja motar suka bar gidan Rinaz na gaban mota Ummi na back seat Maleek ya d'ora kansa a kafad'ar ta Yana tunanin wane hali yarinyar sa take ciki.




A haka suka k'arasa asibitin suka yi parking aka bud'e musu k'ofa Ummi ta fita hannun ta rik'e da na Maleek direct office d'in ta suka nufa su Salman na biye da su har sai da suka shiga office d'in sannan suka tsaya daga waje domin tsaron ogan nasu yayinda su Ummi suka shige ciki tare da su Nasreen.



Suna shiga Ummi ta zaunar da shi kan kujerar ta ta fara yi masa gwaje gwaje nan ta gane zazzab'i ke damunsa wanda tunanin da yake yi ne ya kawo masa shi d'akin dake office d'in ta ja shi tasa masa drip sannan ta zauna gefen gadon yayin da Rinaz ke gefe a tsaye Nasreen Kuma zaune kan wata hadadd"iyar kujera ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya sun dad'e a haka kawai suna kallon sa Ummi ko ba a fad'a mata ba tasan akan Sabeeha ne itama Rinaz tunanin da take yi kenan Nasreen Kuma tunani take yi Mai ya kawowa Maleek wannan zazzab'in cikin k'ank'anin lokaci.



Ummi ta kalli Rinaz ta ce "Rinaz ku je da Salman ki had'o abinci ki kawo mun," Rinaz ta ce "To Ummi," ta fad'a tare da juyawa da niyyar fita wayar ta ta fara ringing tana dubawa ta ga Dija ce ta ji dad'in Kiran dama so take ta kira ta domin ta aika a dawo da su Sabeeha sai dai tana d'agawa ta ji Dija na cewa "Beb akwai matsala fa jiya da dare naji su Sabeeha na shawarar barin gidan mu domin baza su dawo gidan ku ba domin gudun abinda zai je ya dawo gashi yanzu sun fita ba yadda banyi da su ba sun k'i zama," a rud'e Rinaz ta ce "Kina nufin su Sabeeha sunbar gidan ku to Ina suka tafi?" Dija ta ce "Nasan baza su wuce tasha ba domin gida suka ce zasu koma," Rinaz ta ce "Bari naje tashar," Maleek na jin haka ya yi saurin tashi zaune ya fisge drip d'in da aka sa masa ya mik'e ya yi hanyar waje tare da cewa Rinaz "muje," bin bayan sa ta yi suka fita daga office ya ce "Salman muje," bin bayan sa soldier's d'insa suka yi.



Ummi kuwa kasa magana ma ta yi tana kallon ikon Allah mara lafiya da tafiya neman Sabeeha lallai ba k'aramun so yake mata ba.



Nasreen kuwa wani bak'in ciki ne ya mamaye mata zuciya ganin Wai ya tafi tasha neman su Sabeeha lallai dole ne ta d'au mataki a kansu.
[10/25, 7:37 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️




RUBUTAWA DAGA
HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ)





SADAUKARWA GA
MY DAUGHTER SABEEHA
BILKISU Z.YA'U (🅱️K)
AISHA MAGAJI DABO (AMA)




Page 8


Maleek yana fita aka bud'e masa mota ya shige yana jin wani farin ciki a zuciyar sa gudu sosai soldier's d'insa ke zabgawa a hanyar ga jiniya na tashi duk inda suka wuce sai an kalle su.




Rinaz na gaban motar da Maleek ke ciki a hankali ta juya ta kalle shi suna had'a ido ya zabga mata harara ya ce "Wallahi zaki gane kurenki wato dasa hannunki a rashin lafiya ta ko?" Ya yi k'wafa ta ce "Sorry Yaya ita ce fa tace baza ta koma ba Kuma ai kaine baka tsaya kaji meya had'a mu ba," ya ce "Hmm baza ki gane baki da wayo ba sai idan bamu ga yarinyar nan ba," ya fad'a Yana k'ara aika mata harara ita kuwa Rinaz shiru ta yi tana addu'ar Allah yasa ma a gansu d'in.


Shi kuwa Maleek lokaci zuwa lokaci yake kallon agogon hannunsa domin gani yake duk wasu mintunan dake wucewa suna nufin tafiyar su Sabeeha.




Kai tsaye ya ce a shiga har cikin tashar aikuwa suka shiga cikin tashar Nan fa kallo ya koma kan motocin sa domin ko ba a fad'a ba ansan shine a ciki kowa mamaki yake yi to me ya kawo MG Maleek tasha yake yi ya yinda shi kuwa MG bai damu da kallon da akewa motocin sa ba.



Cewa ya yi su yi parking aikuwa suna yi bai jira an bud'e masa k'ofa ba ya bud'e ya fita Rinaz ma ta fita haka ma sauran soldier's d'insa suka fito suka tsaya a bayan sa kowannen su rik'e da bingiga.



Kai tsaye ya nufi inda motocin tashar suke yayinda mutanen dake tashar kowa yabar abinda yake yi ya tafi kallon MG Maleek wasu sun sanshi a TV wasu a jarida domin ba Wanda ya tab'a ganinsa a araha haka wani ma sai dai ya ga wucewar motocin sa amma yau gashi har cikin tasha.



Mata kuwa har ma da mazan sai nuna shi suke yi domin ganin tsananin kyawunsa sanye yake cikin army green d'in trouser da farar t-shirt sai Kuma army green shirt a sama takalmin k'afar sa ma army green ne sumar kansa sai shek'i take yi gashi ta sha wani had'adden aski sai k'amshi ke tashi Nan fa matasan suka fara "Allah ya kare mana MG," hannu kawai ya d'aga musu yana sakin murmushi Wanda ya k'ara faranta ran masoyan nasa domin Yana da masoya sosai saboda bai da girman kai Yana da son al'umma.



Sabreen ta kalli Sameeha dake kusa da ita ta ce"Sameeha dear kalli fa gab'a d'aya 'yan cikin tashar nan sun taru waje d'aya lafiya kuwa?" Sameeha ta ce "Nima dai abinda na gani kenan gashi Kuma Sabeeha dear har yanzu bata dawo ba,"


Sabeeha kuwa cikin wani shago ta je siyo ibon sweet ta dawo ta ga gaba d'aya tashar ta wani rikice kowa ka kalla fuskar sa tabb farin ciki a fili ta tab'e baki sannan ta nufi wajen mutanen tana fad'i a zuciyar ta Kai nima bari naje na ga Mai ake kallo haka da a bani labari gara na bayar.



Lokacin da ta nufi wajen Maleek ya fara tafiya shi da Rinaz domin duba ta aikuwa mutanen gaban su na matsawa domin basa hanya ya wuce ita Kuma na k'ara kutsa kanta aikuwa sai tsintar ta ta yi gaban su cak ya tsaya yana binta da ido kamar bai tab'a ganin ta ba sai ranar Sabeeha kuwa kallo d'aya ta yi masa ta kauda fuskar ta ba Wai dan ta gaji da kallon sa ba a'a kawai dan tana d'an jin haushin sa ne ga kuma wani hamshak'in kyau da ta ga ya k'ara.



Rinaz kuwa da gudu ta k'arasa wajen Sabeeha ta rungume ta tana murnar ganin ta ita kuwa Sabeeha murmushin yak'e ta yi tana satar kallon Maleek Wanda ya kafeta da idanuwa Rinaz ta ce "Yanzu Sabeeha dear da tafiya zaku yi ku barni?" Kad'an Sabeeha ta yi dariyar da iyakar ta fuskar ta saboda ita har ga Allah taso sun tafi.



"Sameeha dear muje mu gani me yake wakana a can wajen muma," cewar Sabreen ta bud'e k'ofar motar ta fice itama Sameeha ta fita suka nufi wajen mutanen.



Suna zuwa suka tarar da Sabeeha tare da Rinaz su Sam basu kula da Maleek ba da yake gefe a tsaye ya hard'e hannayen sa a k'irji yana kallon Sabeeha.


Rinaz ta ce da Sabeeha "Ina su Sabreen fa?" Sai lokacin ta hangi su Sabreen suna tsaye ai da sauri suka k'arasa suka rungume juna da Rinaz suna farin ciki sai lokacin idanun Maleek ya sauka a kan su Sabreen da Sameeha zare ido ya yi cikin Mamaki Yana kallon su sannan ya kalli Sabeeha ya sake kallon su ya kalli Sabeeha shi a dole yana son ya nemo banbancin su amma ba bambamci a zuciyar sa ya ce "Tofah MG kana ruwa yanzu wacce nagani that time," su Sabreen ma sai lokacin suka kula da Maleek kallon sa suka tsaya yi kamar guma ka gani suke yi kamar a mafarki ne suke kallon wannan balaraben yadda ya tsaya kallon su su d'in ma haka suka tsaya kallon sa shi Yana mamakin kamar su su ukun su Kuma suna mamakin kyansa.




Su kansu mutanen tashar tsayawa kallon 'yan uku suka yi ganin tsananin kamar dake tsakanin su juyawa kawai Maleek ya yi ya nufi motar sa ana bud'e masa ya shiga ya yinda Rinaz da su Sabeeha suka shiga motar dake bayan tasa suka bar tashar.


Kai tsaye gida suka nufa Rinaz ta kira Ummi a waya ta ce "Ummi mun wuce gida tare da Yaya da kuma su sabeeha," cikin jin dad'i Ummi ta ce "To shikenan sai na dawo," daga haka suka ajiye wayar.



Kallon Sabreen Rinaz ta yi ta ce "Ke kuwa lafiya kike irin wannan sakin baki haka?" Sabreen ta ce "Hmm ke idan ana sallah ba a magana wato Rinaz dama akwai irin yayan ki a Nigeria Wallahi ni ko a tv banga Mai kyansa ba tabdijan yaseen na d'auka a mafarki ne ba dan da mutane ba sai na tab'a shi nagani shin dagaske ne ko mafarki," dariya suka shek'e da ita ban da Sabeeha da ta yi kicin kicin da fuska Sameeha ta ce "Wallahi Nima dai haka Sabreen ban tab'a ganin Mai kyan sa ba," Jinjina kai Rinaz ta yi domin ita kanta tasan yayan nata ya gaji da had'uwa a wani gefen Kuma tana tunanin kenan indai Sameeha da Sabreen basu tab'a ganin ya Maleek ba kenan hakan na nufin Sabeeha ce Wacce suka had'u wancan lokacin.



A haka suka k'arasa har gida suna gani aka bud'e masa mota ya fita ya nufi part d'in Ummi su ma fita suka yi zuwa part d'in Ummin.


Suna shiga suka same shi zaune a falo ya jingina da jikin kujera ya lumshe idanunsa mai d'auke da zara-zaran eyelashes hannunsa d'aya akan lallausar sumar sa har lokacin bai dena mamakin kamar da ke tsakanin su ba.



Har zasu wuce suka ji muryar sa mai dad'in sauraro ta ce "Kuzo nan," ba musu suka juya suka nufi wajen sa suka zauna k'asan carpet suna kallon sa a hankali ya bud'e idanunsa ya kallesu a zuciyar sa ya ce "Ikon Allah," a fili Kuma ya gyara zaman sa tare da gyaran murya ya ce "Da farko dai kuyi hak'uri akan abinda ya faru," ai Sabreen ba ta jira ya k'arasa fad'a ba da sauri ta ce "Bakomai Wallahi komai ya wuce," harara Sabeeha ta zabga mata duk Yana kallon ta Sameeha ta ce "Wallahi kuwa komai ya wuce dama misunderstanding aka samu," Sabeeha kuwa tab'e baki ta yi bata ce komai ba shi kuwa ita yake kallo domin jin abinda zata ce amma shiru a zuciyar sa ya ce to kodai ita ne wacce ke yin girki kallon Rinaz ya yi ya ce "Yunwa nake ji wacece ke dafa mun abincin?" Rinaz ta ce "Sabeeha kinji Yaya na jin yunwa ki dafa masa abinci," ta fad'a tana kallon Sabeeha shima ita ya kalla ba tare da ta ce komi ba ta mik'e ta nufi kitchen shi Kuma yana binta da ido har ta shige kitchen d'in haka kawai ya ji zuciyar sa tafi karkata akan ita ya gani waccan lokacin.



Ya kalli su Sabreen ya ce "Sunayen ku fa?" Sabreen ta ce "Ni Sabreen ga Kuma Sameeha," ta fad'a tana nuna Sameeha kallon Sameehan ya yi sannan ya jinjina kai sannan ya tashi ya kalli Rinaz ya ce "Idan ta gama ta kai mun part d'ina," yana fad'ar haka ya juya yabar falon.



Ko da ya koma part d'insa zama ya yi kan kujera ya lumshe idanunsa Yana tunanin shin wacece sahibar tasa ne a cikin su shi dai zuciyar sa tafi karkata ga Mai yi masa girki sai dai ba shi da tabbacin ita ce saboda duk irin su d'aya saurin bud'e idanunsa ya yi domin tunawa da wani Abu da ya yi tunawa ya yi lokacin da ya ganta ta kira wani suna da ta fad'a mayar da idanunsa ya yi ya lumshe fuskar ta ya gani sannan ya ji muryar ta ta ce "Please help me zasu kamani kuma Sameeha dear na buk'atar magani yanzu," a hankali ya bud'e idanunsa sannan a fili ya ce "Kenan ba Sameeha ce na gani ba a cikin Sabreen da Sabeeha ne naga d'aya," bud'e k'ofar falon nasa aka yi aka shiga a hankali ya Kai duban sa wajen ya ga Umar tsaye kamar gunki Yana sara masa harara ya aikawa Umar d'in sannan ya ce "Ka fara ba?" Dariya Umar d'in ya yi sannan ya k'arasa ya zauna ya ce "MG yane?"

"Kamar ya fa?" Maleek ya tambaya Umar ya ce "Nifa aure nake so gaskiya dan harna fad'awa mommy," dariya Maleek ya yi har da rik'e ciki sannan ya ce "Kai amma dai anyi d'an iska yanzu Kai ko kunya baka ji?" D'aga kafad'a Umar ya yi ya ce "Wallahi ni banji kunya ba Kai dan kaga kana da taka matar Kai nifa har yanzu bani da budurwa," jinjina Kai Maleek ya yi ya ce "Lallai sannu babban ango ba budurwa ake zancen aure lallai na jinjinawa iskancin ka,"


"Ni yanzu MG mata nake nema Mai hankali a Ina zan samu?" Sai da Maleek ya harare shi sannan ya ce "Tofah shi Maleek ta ya zai sani bayan sanin kanka ne ba shiga harkar su nake ba," ya fad'a yana danna wayar sa.



Nasreen ce ta shiga falon ta tsaya gaban Maleek ta rik'e k'ugu bai d'aga Kai ya kalle ta ba balle Umar da ya gyara zaman sa ya kama yin chart hakan ne ya k'ara k'ular da ita ta ce "Gurin ka fa nazo," har lokacin ba Wanda ya kalle ta cikin k'ulewa ta ce "Ya Maleek," sai lokacin ya kalle ta bata jira ya amsa ba ta ce "Wallahi bazai yiwu ba su Sabeehan ya kuke da su da har zaka tafi neman su ko Kuma akwai wacce kake so cikin su ne?" Mik'ewa ya yi tsaye tare da cire rigar sa shirt d'in dake sama sannan ya ce "Wow gaskiya kina ja yanzu har kin gano ina son d'aya cikin su kin fad'i gaskiya sannan ki tayani da addu'a Allah yasa tana Sona kamar yadda nake sonta," Yana fad'ar haka ya nufi stairs ta ce "To kuwa Wallahi bazai yiwu ba Kuma baka siyi zaman lafiya ba domin zan iya jure komai daga gareka amma Wallahi banda kishiya zanga shegiyar da zata aurar mun miji cikin su," bai ko waiga ba ta nufi stairs d'in itama sai lokacin ya ce "Kinsan Allah idan kika zo kina mun hayaniya a nan zanyi miki dukan da bakya tunani," yana fad'ar haka ya shige d'akin.




Fuuu ta fice cikin jin haushi Umar kuwa dariya ya kyalkyale da ita yana tafa hannu ya ce "D'an iska MG ashe wata zaka k'aro?" Banza Maleek ya yi da shi ya shige wanka abinsa.




Sabeeha kuwa girki tayi masa kamar yadda ya buk'ata tana gamawa ta fice ta k'ofar kitchen d'in zuwa d'akin su ta yi wanka ta shirya ta koma tana shiga falon Rinaz ta ce "Na manta Sabeeha dear Yaya ya ce ki kai masa abincin part d'insa," bata ce komai ba ta je ta zuba komai a basket ta nufi part d'in nasa tana cewa a zuciyar ta Allah yasa ba wani cin mutuncin za ayi mun ba tana zuwa ta ga soldier's wajen biyar a k'ofar sai Kuma taja ta tsaya dan tsoron su take yi sai Kuma ta gyara nutsuwar ta ta nufe su ta ce "Dan Allah Yana ciki dama zan Kai masa abincin sa ne," basu ce mata komai ba d'aya ya shiga falon ya samu Umar zaune a falon ya ce "Oga fa dama wata ce tazo Wai za a kawo masa abinci ne," Umar ya ce "Ok ta shigo mana," juyawa sojan ya yi ya fita sannan ya kalli Sabeeha ya ce "Shiga," Kai tsaye ta shiga had'adden falon da sallama a bakin ta Umar ya amsa tare da binta da kallo k'asa ta yi ta kanta.



Daidai lokacin Maleek ke saukowa stairs yasha kyau cikin wasu k'ananan kaya dark blue sai k'amshi yake yi tun daga nesa ya k'ure ta da ido Yana kallon ta yana k'arasawa ya zauna k'amshin da ya daki hancin ta ne yasa ta lumshe ido sannan ta ce "Ga abincin," ya ce "Ok zuba mun," babu musu ta zuba masa ta ajiye kan center table d'in dake gaban sa sannan ta ajiye jug d'in d'in zob'on da ta had'a masa da glass cup domin dama Ummi ta fad'a mata yaji dad'in zob'on ta dinga yi masa tana gamawa ta mik'e zata tafi ya ce "dawo ki zauna," tura baki tayi dan ita har ga Allah a takure take shi kuwa yadda yadda ta tura bakin sai ya bashi dariya dan ganinta ya yi kamar 'yar baby zama tayi har da tank'washe k'afa tana kallon sa.


Shi kuwa abincin sa ya d'auka yana ci a hankali Umar kuwa tunda ya kyalla ido ya ga zob'o ya fara gyara baki dan Yana son sa aikuwa ya zuba ya fara sha.



Kallon sa kawai Sabeeha ke yi yadda yake cin abincin a nutse yana yi yana kallon ta sannan ya ajiye spoon d'in ya fara shan zob'on da ya yi masa dad'i sosai a zuciyar ta ta ce kai ba dai har ya k'oshi ba sai ji ta yi ya ce "Yes na k'oshi," ashe a fili tayi maganar k'asa tayi da kanta dan kunya ta ji sai da ya gama shan zob'on sa sannan ya daidai ta nutsuwar sa a kanta ya ce "Na tambaye ki mana?" Gyad'a kai ta yi ya ce "3 weeks back I think it's Thursday around 6:35pm kina ina wannan lokacin?" Shiru Sabeeha ta yi tana tunanin tambayar tasa inda ta dosa ta tuna tabbas wannan ranar suna asibiti tare da Sameeha Kuma a wannan lokacin ta fita siyan magani Kuma lokacin 'yan daban Rashida suka bita har ta rungume wani soja zare ido tayi domin wata zuciyar ta ce tace tabbas wannan ne sojan duk da banga fuskar sa ba Amma ai na ji k'amshin turaren sa irin na wannan ne sannan motocin waccan lokacin na sojojin sa irin na sojojin wannan ne tabbas ma shine tunda har ya yi mun maganar tunda idan ba shi bane ta ya yasan naje waccan k'auyen sannan har ma da lokacin tabbas shine.




Maleek kuwa tsayawa kallon ta ya yi yadda ta zurfafa a tunanani har wani tallafe kumatun ta take yi a nata b'angaren kuwa ji ta yi kamar lokacin ta rungume shi dan wata kunya ce ta rufe ta sai Kuma wata zuciyar yace ai baisan ke bace ko bake bace kawai ki zabga masa k'arya aikuwa ta gyara zaman ta ta ce "Dama waccan lokacin muna asibiti ne tare da Sameeha dear," ya ce "Kina nufin baki fita ko ina ba?" Gyad'a kanta ta yi ta ce "Ni kam ba inda naje," ajiyar zuciya ya d'an sauke ya ce "Ok shikenan zaki iya tafiya," zumbur ta mik'e dan dama ta matsu tabar wajen ta d'ebi kayan da yaci abinci ta fice da sauri da kallo ya bita har ta fita.




Sannan a zuciyar sa ya ce may be d'ayar ce zan tambaye ta itama kuwa Umar ne ya katse masa tunani da cewa "Kai wannan tambayoyin fa ko dai ka Santa ne?"


"Ni kuwa nasan ta domin tun 3 weeks ago na tab'a ganinta a wani k'auye," nan ya labartawa Umar komai sannan ya ce "Abinda ban saniba ashe triple's ne hmm na shiga rud'u Umar dukan su fa iri d'aya suke ba different na rasa ta yadda zan gano tawa a ciki amma na cire Sameeha ciki domin time d'in itane a hospital kaga kenan ita bata fita ba hakan na nufin cikin su biyu ne kenan tunda ita wannan tace ba ita bace dole zai kasance d'ayar ce to tunanin da nake yi kar waccan ma tace ba ita bace Kuma fa dole hakan zai iya kasancewa waccan d'in ma tace ba ita bace sai dai I don't know why zuciyata tafi believing cewa wannan ce saboda yadda ta tafi dogon tunani ka ga da ita ce kai tsaye zata ce Ita ce amma sai ta tafi wani tunanin daban ba sai dai bansan mai take tunani ba amma soon zan gane shin ita d'in ce ko a'a," yana gama fad'in haka ya d'auki zob'on yana sha Umar kuwa sakin baki ya yi

Please Login or Register in order to submit comment