Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce "To yanzu fad'a mun kana farin ciki da amsa soyayyar ka da daughter ta yi?" Shiru ya yi ya kalli had'adden p.o.p celling d'in falon alamar tunani sannan ya kalli Ummi ya ce "Eh Ummina I'm very happy har na matsu ranar auren ta yi," dungure masa kai Ummi ta yi ta ce "Marar kunya a gaban nawa," rik'o hannun Ummin ya yi yayi masa kiss yana dariya itama Ummin tana dariya ya ce "To Ummi bayan ma Sabeehan ta yi tafiyar ta gidan Mama," Ummi ta ce "To ai tace zata dinga zuwa yima abinci," murmushi ya yi.



Sai da suka d'an yi fira sannan ya yiwa Ummi sallama ya koma part d'insa ya yi sallah ya kwanta bacci zuciyar sa fal farin ciki.




Da daddare Sabeeha na kwance akan gadon su wayar ta ta fara ringing d'aukar wayar ta yi tana kallon ta cikin mamaki domin ita har mantawa take yi tana da waya tunda ba Kiran ta ake yi ba d'agawa ta yi tare da yin sallama daga can had'add'iyar muryar Maleek ta amsa mata sallamar zare ido ta yi kamar yana gaban ta ta ce "Ya Maleek are you amma a Ina ka samu number nah?" Murmushi ya yi ya ce "A radio," had'e fuska Sabeeha ta yi cikin shagwab'a ta ce "Yanzu number d'in nawa ake raba ta radio?" Dariya Maleek ya yi ya ce "Sorry wasa nake yi amma kinsan number d'in ki bazai yi mun wuya ba beside ma kinyi mun text da ita that time," ta ce "Ooh hakane fa na manta,"



Sameeha ce ta shiga d'akin tasha kyau cikin doguwar rigar shadda pich color ta ce "Sabeeha dear naje wajen ya Umar," Sabeeha ta ce "Ok my regard to him," Sameeha ta ce "Ok tare da ficewa," Sabeeha ta ce "Hello ya Maleek," daga can ya ce "Hi Sabee na," dariya ta yi ta ce "Yawwa wai ka fasa yin tafiyar ne?" Ta fad'a tana rungumar pillow.



Zumbur Maleek ya tashi zaune daga kwancen da yake yasa hannunsa cikin sumar kansa sannan ya dafe goshi ya ce "Ayyah nikam Sam na manta da batun tafiya and zuwana Dubai yana da muhimmanci sosai amma Ina tunanin next week zanje," ta ce "Allah ya kaimu," ya amsa da "Ameen," sannan ya ce "Sabee na ya batun abinci fa Ummi ta ce Wai kince zaki na zuwa kina yi mun," ta ce "Eh mana," ya ce "Shikenan wataran ma zan dinga zuwa naci a nan,"




"Da gaske wai?" Sabeeha ta tambaya ya ce "Sosai fa," nan suka cigaba da fira abinsu sannan suka yi sallama.



Washe gari da Sabeeha ta tashi daga bacci wanka ta yi ta shirya cikin riga da skirt na wata red d'in atamfa ta yi kyau sosai kamar ka sace ta ka gudu sai k'amshi take yi abinta d'akin Mama ta nufa ta je ta gaishe su ita da Abba sannan ta yi musu Sallama ta fita driver ya kaita gidan su Maleek.




Tana shiga ta samu Ummi na saukowa stairs har k'asa ta tsugunna ta gaishe da Ummi cikin murmushi Ummi ta amsa ta ce "Daughter kenan sannu da k'ok'ari har kin fito?" Ta ce "Eh Ummi office zaki fita ne?" Ummi ta ce "Eh zan fita office ne ina da patient ki shiga su Hadiza na ciki sai na dawo," ta ce "To Ummi sai kin dawo," Ummi ta fita ita kuma ta nufi kitchen ta had'awa Maleek breakfast ta bawa Hadiza ta kai part d'insa ita Kuma ta koma gidan Mama.



Da sallama ta shiga falon ta samu ba kowa kitchen ta wuce kitchen inda take jiyo hayaniyar su Rinaz da sallama ta shiga kitchen d'in suka amsa mata kallon fuskar Sabreen ta yi ta kyalkyale da dariya ganin yadda fuskar tata ta yi kaca-kaca da flour ita a lallai tana yin cake.



Su Rinaz ma dariyar suke yi Sabeeha ta ce "Sannu dear da aiki," Sabreen ta ce "Yawwa sister wallahi kuwa girki da wuya," jinjina kai Sabeeha ta yi ta ce "Aikuwa idan ma zaki zage ki zage domin ba zamu Kai ki ki dinga yiwa ya Fauwaz jagwalgwalo ba," Dariya Rinaz ta yi ta ce "Wallahi kuwa fad'a mata habibty dan tsab zamu k'aro mata wata," ai tuni Sabreen ta yi kicin-kicin da fuska dan ita ba dai kishi ba ta ce "Aikuwa Wallahi baku isa ba ko ban iya ba haka zai ci kuma zaku yi yadda cake d'ina zai yi wuta bari ma na Kira my one d'in," ta fad'a tana dialing number d'in Fauwaz Rinaz ta ce "Aikuwa sai dai kici kwab'ar ki ke d'aya banda Rinaz," ta fad'a tana dariya.





Sabeeha ta kalli Rinaz ta ce "Sameeha dear fa?" Rinaz ta ce "Suna tare da ya Umar a wancan falon," jinjina Kai Sabeeha ta yi.




Fauwaz na d'aga wayar Sabreen bata jira ya ce komai ba ta ce "My love Wai kaji zaka yi mun kishiya," zare ido Fauwaz ya yi kamar Sabreen na gaban sa ya ce "Inji waye?"



"Inji su Sabeeha dear mana Rinaz habibty har da cewa Wai jagwalgwalo na iya baza su ci cake d'ina ba," kasancewar wayar a handsfree take ya ce "Ke Rinaz ki kiyayeni rabu da su baby gani nan shigowa gidan," daga haka ya katse Kiran su Sabeeha Kuma suka fita suna dariya.


Suna zama babu dad'ewa Fauwaz ya yi sallama a falon yasha gayu cikin wasu k'ananan kaya masu matuk'ar kyau kalar fari da blue sai k'amshi yake yi ga wasu sark'ok'i a wuyan sa sai walwali suke yi kana kallon su kasan masu tsada ne sosai ya yi kyau dama Kuma Fauwaz akwai kyau.




Gaishe shi su Sabeeha suka yi ya amsa cikin fara'a da gudu Sabreen ta fito daga kitchen jin shigowar sa waigawa Fauwaz ya yi ya kalle ta dariya ce ta sub'uce masa ganin yadda fuskar ta tasha kwalliyar flour su Sabeeha na taya shi dariyar.




Tura baki Sabreen ta yi tare da juyawa ta shige ta koma kitchen d'in binta Fauwaz ya yi yana cewa "Baby baby," Amma bata ko waiga ba sai da suka shiga kitchen d'in sannan ta tsaya dakyar ya rarrashe ta ta sauko ya taya ta suna yi tana yi masa surutu shi kuwa sai biye mata yake yi.



A haka suka gama suka fito daga kitchen d'in Fauwaz sai goge fuska da hanky yake yi shi a lallai ya yi aiki sannan ya kalli Sabreen ya ce "My love bari naje na dawo," ta ce "Ok my heart sai ka dawo," daga haka ya fice itama ta haura sama domin yin wanka.



Can Fauwaz ya dawo ya canjo wani wankan ya yi kyau abinsa zama ya yi suka sha fira da Sabreen suna cin cake d'in abinsu.



Bayan tafiyar Fauwaz Mama da Abba suka dawo daga asibiti dan tun fitar Sabeeha suka tafi.




Kitchen su Sabeeha suka shiga tare da 'yan aikin Mama suka shirya abinci mai rai da lafiya sai da suka yi wanka suka yi sallah sannan suka nufi daining suka ci abinci bayan sun gama sannan suka koma falo suka zauna suna fira Sabreen ta zubo cake d'in ta a plate tana ci kallon cake d'in Sabeeha ta yi gwanin sha'awa ta ce "Sabreen dear d'an sammun mana," hararar ta Sabreen ta yi ta ce "Gaskiya bazan iya ba," had'iye yawu Rinaz ta yi ta ce "Ni fa dear," Sabreen ta ce "Rinaz habibty sai dai kiyi hak'uri amma zan cinye kwab'a ta ni kad'ai babu mai ci sai Sameeha dear," ta fad'a tana ajiye plate d'in kan center table ta d'auki d'aya ta nufi bakin Sameeha ta ce "Yawwa sweetheart bud'e bakin," Sabeeha ganin Sabreen ta juyawa plate d'in baya ta yi wuff ta d'auki d'aya ta mik'e.



Sabreen ta ce "Sabeeha dear ni kawai ki bani abina," k'in bata Sabeeha ta yi nan suka fara zagaye falon Sabeeha ta ce "Mama kina jinta ko?" Sabreen ta ce "Abba kace ta bani," dariya su maman ke yi musu da su Rinaz Sabeeha ta nufi stairs da gudu ta shige d'akin su tasa key.



Sabreen ta koma falo sai tura baki take ta tarar Rinaz ma ta d'auka tana ci bin Rinaz d'in ta yi tana cewa "Ni dai gaskiya kizo ki bani abina," ficewa Rinaz ta yi da gudu itama tura baki Sabreen ta yi ta ce "Mama kina dai ganin su ko?" Dariya Mama ta yi sannan ta k'wala kiran "Halima!halima," daga kitchen Halima ta amsa sannan ta fito da sauri ta ce "Mama gani,"




"Halima Ina so yanzu ke da su abasiyya ku yi mana yanzu cake a gidan nan," Halima ta ce "To Mama," ta fad'a tare da komawa kitchen d'in Mama Kuma ta kalli Sabreen ta ce "Gashi nan za a yi muku wani shikenan ko?" Gyad'a kai Sabreen ta yi Mama da Abba Kuma suka nufi d'aki.




Sabeeha kuwa wayar ta ce ta fara ringing d'agawa ta yi tare da fad'awa kan gado ta ce "Washh,"



"Lafiya kuwa Sabee na?" Maleek ya tambaya cikin shagwab'a ta ce "To ba Sabreen dear bace ta biyo ni da gudu ba,"



"Lalala me ki ka yi mata haka?" Ya tambaya cikin kulawa k'ara shagwab'e fuska ta yi ta ce "Wai fa dan na d'aukar mata cake," murmushi ya yi ya ce "To banda abun Sabee na meyasa ki ka d'aukar mata abinta?"



"To shikenan na ma fasa ci," Maleek ya ce "A'a wasa nake miki ci ki kyale ta," ci ta fara yi sannan ta ce "Ya Maleek zaka ci?" Girgiza Kai ya yi ya ce "No kici da nawa," ta ce "To," nan suka cigaba da fira suna dariya.


Haka rayuwa ta cigaba Sabeeha da Maleek na soyayya cikin bawa juna kulawa da soyayya ta musamman har gidan yake zuwa ya ci girkin ta ya tafi wataran yasa mata rigimar ta bashi a baki.




B'angaren Kawu Bala kuwa a zaune yake abun duniya ya yi masa zafi saboda tun kafin Maryam ta d'ora k'afar ta a k'auyen amma talauci yasa shi a gaba tun ranar da sojojin Maleek ma suka zo suka tafi da Abba labari ya Kai masa cewa ya yi shi ina ruwan sa wata k'ila cikin yaran sa ne wata ta jawo masa masifa dan haka ba ruwan sa shima ya ji da masifar dake tunkaro shi.




Tashi ya yi ya nufi gida tun daga zaure yake k'wala kiran "Lantana! Lantana," fitowa daga d'aki lantana ta yi da d'ankwali a hannu ga kannan ya yi datti ko tsagar kitson kan ba a gani ta ce "Wai Bala lafiya ka ke mun irin wannan Kira kamar na cima bashi ko wata tsiyar zaka bani," kusan Wanda talauci ke ci abu kad'an ke tunzura shi aikuwa ya fara masifa "Wallahi Lantana ki fita daga idanuna na rufe idan ba haka ba wallahi saina mangare ki," dariyar rainin hankali Lantana ta yi ta ce "Ah lallai ne Bala ka mangare ni kaji,"



"Wallahi Lantana ki fita a idanuna na rufe idan ba haka ba sai kinga bala'i na," ta ce "Dan Allah Bala naga bala'i da wallahi yau sai kasan ka tab'o lantana Wallahi sai nayi maka abinda baza ka tab'a mantawa dani ba," jinjina kai Kawu Bala ya yi ya ce "Lantana karki fasa nace lantana idan kin fasa Allah ya tsinewa dangin ku shegiya mai farar k'afa," aikuwa nan lantana ta fara sababi tana zage-zage aikuwa Kawu Bala ya zabga mata mari.




Dafe kunci ta yi ta ce "Bala nika mara?"


"An mare ki d'in ki rama mana," Kawu ya fad'a yana nufar hanyar fita Lantana ta ce "Bazan rama ba amma Wallahi sai nayi ma abinda baka tab'a tunani ba matsiyaci kawai wallahi Bala da kai gara garin kwaki na ashirin," ficewa Kawu Bala ya yi yana k'wafa.




Bayan fitar Kawu lantana ta yi k'wafa ta ce "Zaka ga me zanyi," ta cije baki sannan ta tsaya tunanin me zata yiwa Kawu Bala can ta shige d'aki sai gata ta fito da kayan sawar Kawu Bala da almakashi ta zauna ta yayyanka su gutsi-gutsi ta kai shara ta watsar ta ce "Ka dawo naga uban da zaka yi,"





Kawu Bala kuwa yana fita k'ark'ashin wata bishiya ya je ya zauna yana sababi shi kad'ai malam saleh ne yazo wucewa ya ce "Malam Bala kaine zaune a nan?" Kawu ya ce "Eh wallahi ni ne malam saleh ina zuwa haka ka ke sauri?" Malam Saleh ya washe baki ya ce "Wallahi aski zani kasan yau ake auren yar wajena ta inna da k'arfe uku dafatan zaka zo," Kawu Bala ya ce "Zan zo," daga haka Malam Saleh ya wuce.


Kawu Bala a zuciyar sa ya ce "Ai ko dan naje na cika cikina naje wallahi," kallon kayan jikin sa ya yi farin jadi ne amma duk ya zama milk saboda datti hammatar duk ta yage haka ma gwiwoyin duk sun ya ge.




A hankali ya ce "Na tuna akwai kayana na shiga jama'a basu fi wanki aahirin ba bari na tashi naje na fara shiri," daga haka Kawu Bala ya tashi ya nufi gida.
[10/25, 7:43 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️




RUBUTAWA DAGA
HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ)




SADAUKARWA GA
MY DAUGHTER SABEEHA
BILKISU Z.YA'U (🅱️K)
AISHA MAGAJI DABO (AMA)





Page 15


Bud'e k'ofar aka yi Salman ne ya shigo tare da mutum biyu a bayan sa.


Zare ido Sabeeha ta yi gani take yi kamar a mafarki haka ma Sameeha da ta sake murza idanunta ko sune suke yi mata gizo Sabreen kuwa ko motsi ta kasa domin gani take yi kamar mafarki take yi.




Can dai Sabreen ta yi k'arfin halin mik'ewa tsaye ta ce "Abba kaine?" Gyad'a kai Abba ya yi da gudu Sabreen ta yi wajen sa ta rungume shi tana murnar ganinsa gashi ya canja kamar ba shi ba.




Daga bayan Sabreen suka ji Sameeha ta ce "Abba wacece wannan?" Ta fad'a tana kallon Doctor Maryam da zuwa lokacin harta fara hawayen farin ciki tana mamakin girman 'yan ukun ta.




Abba ya ce "Maman ku ce Allah ya dawo mana da ita ta sanadin Abdul-maleek," rungume Doctor Maryam Sabreen da Sameeha suka yi suna murnar ganinta tare da hawayen farin ciki haka ma Doctor hawayen take yi.



Sabeeha kuwa har lokacin bata motsa ba ta tsaya kallon ikon Allah haka ma Rinaz da take tunanin dama maman ta ce Mahaifiyar su Sabeeha haka ma su Umar suka tsaya kallon su.



Sabreen ta ce "Mama dama kina raye ashe dama zamu ganki?" Share hawaye Doctor ta yi ta ce "Ku gafarceni yarana ba laifina bane a ko wanne lokaci kuna raina ku gafarce ni," Sameeha dake rungume jikin Doctor ta ce "Mama baki yi mana komai ba mun yafe miki," Sabreen kuwa sai gyad'a kai take yi.




Doctor ta kalli Maleek dake tsaye ta ce "Abdul-maleek nagode sosai domin ta sanadin ka na samu farin cikin dana fidda rai da samun sa Allah ya saka mata da mafificin alkhairi Allah ya faranta maka kamar yadda ka faranta mana Allah ya cigaba da kare mana Kai a duk inda kake," a hankali ya amsa da "Ameen Mama," su Sabreen ma suka amsa da "Ameen," domin wani girma da mutuncin Maleek ne ya k'aru a idanun su sosai suka k'ara ganin mutuncin sa godiya suka yi masa sai kawai ya yi musu murmushi.



Kallon inda Sabeeha take Doctor Maryam ta yi a hankali ta nufi wajen ta ta tsaya a gaban ta ta ce "Nasan na aikata muku ba daidai ba yarinya ta amma ki gafarceni banyi hakan da son raina ba nasan ban cancanci yafiya a wajen ku ba," fad'awa jikin Doctor Sabeeha ta yi ta saka kuka ta ce "A'a Mama mu baki aikata mana komai ba mun yafe miki," Sabeeha ta fad'a tana hawaye itama doctor Maryam hawayen take yi.




A hankali Sabeeha ta waiga inda Maleek yake amma sai ta ga wayam baya nan wani sabon hawayen ne ya zubo mata domin wata sabuwar soyayyar sa ce taji ta d'arsu a zuciyar ta duk da cewa da tayi bata son sa ta k'ona masa zuciya ta hana shi farin ciki har cuta sai da ya yi amma shi hakan bai sa ya tsane ta ba sai ma nema mata nata farin cikin da ya yi tabbas Maleek na daban ne zuciyar sa kyakkywar zuciya ce take ta ji mutuncin sa da soyayyar sa sun k'aru a zuciyar ta.




Ummi ce ta k'arasa wajen su wacce zuwan ta kenan rungume ta Doctor Maryam ta yi ta ce "Nagode Aysha nagode da kulawar da kika bawa 'yan uku Allah ya saka da alkhairi," Ummi ta ce "Haba Maryam ai tsakanina dake ba godiya nima ai 'ya'yana ne," rungume Ummi su Sabeeha suka yi cikin farin ciki daga nan aka cigaba da gudanar da celebration aka yanka cakes aka ci aka sha su Sabeeha sai godiya suke wa Ummi bisa k'ok'arin ta.




Anan suke jin ai duk abinda suka gani a birthday d'insu duk Maleek ne ya yi musu nan ma Maleek ya k'ara samun rank a zuciyar 'yan uku.





Bayan an gama ne suka koma falo Doctor Maryam ta basu labarin abinda ya faru tun auren su da Abba da kuma barin su da ta yi bayan Ummi tasa driver ya kai Aysha da Dija gida.



Tausayin Mahaifiyar tasu ne ya kama su har ma da Abban su.




Tashi Ummi ta yi ta ce "Nikam bari na tafi," a tare Rinaz da 'yan uku suka tashi kallon su Ummi ta yi ta ce "Ina kuma zaku?" Sabeeha ta ce "Ummi binki zamu yi," girgiza Kai Ummi ta yi ta ce "A'a ban yadda da hakan ba ku zauna tare da Mamar ku kunji?" Doctor Maryam ta ce "Aysha ku je mana," Ummi ta ce "Ai da nan da can duk d'aya ne kuma zasu je duk sanda suke so sai dai banda yau domin Ina so ku samu zama," ta kalli su Sabeeha ta ce "Ku zauna," zama suka yi.




Doctor kuwa taji dad'in abinda su Sabeeha suka yi saboda ganinta da suka yi hakan baisa sunji sunfi buk'atar ta fiye da wacce ta rik'e su na wani lokaci ba duk da kuwa dad'ewar da suka yi ba tare da ita ba.



Rakiya suka yiwa Ummi har mota sannan suka koma cikin gidan tare da Rinaz domin tace duk inda 'yan uku suke to tana nan.




Wanka suka yi da sallah sannan suka fita falo suka ci abinci su sabeeha suka gyara wajen sannan suka koma falo suka fara fira suna dariya gwanin sha'awa sai dai banda Sabeeha da duk hankalin ta ya yi wajen Maleek tunani take yi gobe waye zai had'a masa breakfast.




Doctor ta kalli Abba ta ce "Ni kuwa Abban 'yan uku bangane rigimammiya ta ba a cikin su," Rinaz dake kwance cinyar Doctor Maryam ta ce "Mama wacece?" Doctor ta ce "Kullum fa sai ta hanamun bacci da kukan ta haka zata yi ta kuka har sai ta tashi 'yan uwan ta," Abba ya kalli Sabeeha ya ce "To aminiyata kinji fa," dariya falon ya d'auka su Sabreen sai tsokanar ta suke yi suna ce mata "Rigimammiyar Mama," ita kuwa sai hararar su take yi sannan ta tashi ta haye stairs.




Wani had'adden d'aki ta shiga komai na d'akin pink ne d'akin ya had'u ba k'arya zama ta yi gefen gadon ta fad'a tunanin Maleek.



Su Sameeha ne suka shiga d'akin Sabreen ta d'auko kyautar da Maleek ya yi musu ta bud'e a tare ita da su Sameeha suka ce "Woww amma fa ya yi kyau," kallo itama Sabeeha ta yi wata siririyar sark'ar diamond ce sai kyalli da walwali take yi tayi kyau over haka ma d'an kunnen ya yi kyau.





Sameeha ta ce "Gaskiya ya yi kyau sosai nima bari na duba nawa," bud'ewa ta yi sak irin ta Sabreen ba banbanci Rinaz ta ce "Sabeeha sister ke ina naki kyautan," bed side drower ta nuna mata.




D'aukowa Rinaz ta yi ta nufi su Sabreen suka bud'e k'amshin da ya daki hancin Sabeeha ne yasa ta lumshe idanunta sai dai lokaci guda ta bud'e su jin ihun da su Rinaz suka saki suna fad'in "Wallahi ya yi kyau sosai dear zo ki gani," sark'a ce irin tasu Sabreen sai dai ita da wani ring mai d'aukar hankali na diamond da Kuma wani diamond watch harma da wani fashion designer d'in abun hannu ga wani tsadadden turare Mai dad'in k'amshi.




"Wow," kawai Sabeeha ta iya furtawa domin ganin key d'in mota su Sabreen kuwa ihun murna suka saki tare da ficewa da gudu suka nufi falo domin nunawa Abba da Doctor Maryam.




Sabeeha kuwa kwanciyar ta ta yi sai lokacin idanunta ya Kai kan wata farar takarda dake wajen d'auka ta yi ta bud'e take idanunta suka yi mata tozali da wani kyakkyawan rubutu mai kyan gaske Wanda bata tab'a ganin mai yanayin sa ba ma tsabar kyau da tsaruwa fara karantawa ta yi cikin nutsuwa.





"Assalamu Alaiki sarauniyar kyawawa Ina fatan kina lafiya hak'ika naso wannan sarauniyar kyan ta kasance mallakina sai dai hakan ba mai yuwuwa bane saboda wannan sarauniyar da zuciya ta ta makance a k'aunar ta ya kasance ni bana d'aya daga cikin tsarin ta Ina addu'ar Allah yasa hakan shine mafi alkhairi ga k'aramar kyautata nan a gareki karki yi tunanin nayi miki ne domin ki soni a'a nayi miki ne a matsayin wacce zuciyata taso kasancewa tare da ita sai dai hakan bai samu ba Sabeeha na hak'ura dake kuma ba Wai dan bani sonki ba sai dan kawai na baki dama ki zab'i wanda ki ke son yin rayuwa da shi fatana shine ki kasance cikin farin ciki a k'arshe ina yi miki fatan alkhairi Allah ya zab'a Miki mafi alkhairi na barki lafiya," tun kafin ta gama karantawa hawaye ya wanke mata fuska.





Kifa kanta jikin pillows ta yi ta saka kuka mai ban tausayi a hankali ta fara magana "Why Maleek meyasa zaka yi mun haka wallahi Ina sonka please karka rabu dani," ta fad'a tana k'ara sakin wani sabon kukan.



Shiga d'akin su Sabreen suka yi tare da su Abba da Doctor domin su taya ta murna sai suka tsaya turus domin ganin yadda Sabeeha ta kifa kanta jikin pillows sai kuka take yi kamar wacce aka yiwa mutuwa.



A hankali Doctor Maryam ta k'arasa gefen ta ta zauna tare da dafa kafad'ar ta d'aga jajayen idanuwan ta Sabeeha ta yi tana ganin Doctor ce ta fad'a jikin ta ta cigaba da rera kukan ta.



Shafa bayan ta Doctor ke yi tare da gashin ta ta ce "Meya faru ne?" Shiru ba magana sai kuka.




Sabreen da Sameeha ma harsun fara nasu kukan matsawa gaban Sabeeha Sabreen ta yi tana kuka ta ce "Please dear ki fad'a mana meye yake damunki bamu tab'a ganin ki cikin irin wannan yanayin ba dan Allah kiyi hak'uri hakan na cutar damu," jin muryar Sabreen na kuka ne yasa Sabeeha rage volume d'in kukan ta.




Sameeha itama tana hawaye ta ce "Sister damuwar ki tamu ce bazamu iya jurar ganinki a irin wannan yanayin ba please kiyi hak'uri," shiru Sabeeha ta yi sai ajiyar zuciyar da take saukewa domin a duniya idan akwai abinda ta tsana to damuwar su Sameeha ce.



Abba ne ya k'arasa tare da rik'o hannun Sabeeha ya ce "Zo nan kinji aminiyata zo muje ki fad'a mun meye damuwar," ya fad'a tare da janta suka bar d'akin binsu Doctor Maryam ta yi zuwa falo.




Zama Abba ya yi tare da zaunar da Sabeeha kusa da shi Doctor Maryam kuwa fridge ta nufa ta zubo ruwa a cikin wani glass cup mai matuk'ar kyau ta k'arasa inda suke ta mik'awa Sabeeha karb'a ta yi ta sha sannan ta ajiye cup d'in akan center table a hankali take sauke ajiyar zuciya.




Abba ya ce "Aminiya ta muna jinki ki fad'a mana meye damuwar ki domin ba wanda ya kamata ki fad'awa damuwar ki fiye da mu kinji?" Gyad'a kai ta yi sannan ta fara basu labarin had'uwar su tunta farko da Maleek da kuma cewar da ta yi bata son sa da Kuma dalilin ta sannan ta d'ora da basu labarin letter d'in da ta gama karantawa yanzu.





Bayan hannun ta tasa tana goge hawayen da ya b'ata mata fuska jinjina kai Abba ya yi sannan ya ce "Gaskiya ne aminiya ta ni shaida ne akan son da Abdul-maleek ke miki domin bai ko ji kunya ta ba ya bani labari kamar yadda ki ka fad'a yanzu aminiya ta Abdul-maleek ya cancanci ya samu soyayya a duk inda ya je neman ta domin duk wata

Please Login or Register in order to submit comment