Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kwanta.



Sabeeha kuwa tunda asuba ta yi ta fara buga k'ofar d'akin da take ciki wannan tsohuwar ta bud'e tana aikawa da Sabeeha wani mugun kallo.



"Dan Allah baba ki taimake ni ki bud'e ni nayo alwala nayi sallah," tas fas ka ke ji matar ta wanke fuskar Sabeeha da maruka sannan cikin d'aga murya ta ce "Uban waye ya sanar dake Zaki yi sallah a nan gidan da har Zaki tashe ni Ina bacci to kinyi na farko Kuma da k'arshe," ta fad'a tare dasa k'afar ta ta daki cikin Sabeeha.



Baya Sabeeha ta yi ta fad'i dafe da cikin ta tare da sakin wani ihu saboda wani abu da taji ya mugun tsira mata a cikin ta saka kuka tana murk'usu su matar Kuma ta ja tsaki ta ja k'ofar d'akin ta rufe ta bar wajen.
[10/25, 8:56 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️


RUBUTAWA DAGA
HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ)




SADAUKARWA GA
MY DAUGHTER SABEEHA
BILKISU Z. YA'U (🅱️K)
AISHA MAGAJI DABO A
(AMA)



Page 33

Sosai cikin Sabeeha ya fara ciwo mararta na murd'a mata gaba d'aya ta fita hayyacin ta daga nan bata sake sanin inda kanta yake ba.



Ruwan da aka kwara Mata a jiki ne yasa ta farfad'o daga sumar da tayi k'ok'arin tashi zaune take yi amma ta kasa tsohuwar ta gani a kanta a tsaye tana aika mata da wani mugun kallo.



Dakyar ta iya tashi zaune tana rintse idanu kallon banza tsohuwar ta yi mata sannan ta ce "Tashi yanzu muje ki d'ora mana girki," kallon ta Sabeeha ta yi a zuciyar ta ta ce girki Kuma sai ta fara k'ok'arin tashi tsaye dakyar ta iya tashi tsaye tana dafa bango matar ta juya ta yi hanyar fita Sabeeha na binta a baya har zuwa kitchen suna shiga matar ta ce Yanzu muke buk'atar kiyi mana girki ga kayan nan daga haka matar ta fice daga kitchen d'in.



Zama Sabeeha ta yi dafe da cikin ta dake yi mata ciwo tana kallon shinkafar da aka nuna mata a k'alla tayi kwano uku.


Tunawa tayi da wayar da Sabreen ta bata ta yi da sauri ta lalubo wayar ta fara neman layin Sabreen.




Sabreen dake zaune kan kujera tana facing Maleek wayar ta ta fara ringing kallon wayar ta yi tana ganin number d'in ta gane ta da sauri jikin ta har rawa yake yi ta ce "Hello dear," k'asa_k'asa cikin muryar wahala ta ce "Sabreen dear Ina My ya jikin sa?" Maleek kamar yasani sai kallon Sabreen yake yi ba ya ko k'iftawa.


Hawaye ne ya zubowa Sabreen saboda jin muryar Sabeeha kamar tana cikin wahala a hakan ma batasan saita muryar Sabeeha ta yi ba.



"Dear lafiya ki ke kuwa Mai yake faruwa ne Sameeha dear yaushe Zaki zo sannan ya yanayin abun yake har yanzu mu ba muji wani sakamako ba," take Sabeeha ta gane cewar Sabreen na cikin mutane sannan ta fahimci inda tambayar ta dosa a hankali cikin muryar azaba ta ce "Dear kina tare da My ne?" A hankali Sabreen ta ce "Eh,"



"Shikenan sai na k'ara Kiran ki ki kwantar da hankalin ki zandawo very soon," daga haka ta kashe wayar gaba d'aya ta b'oye sannan ta kalli wata k'ofa ta bud'e sai ta ga ashe toilet ne da sauri ta shiga a gurguje tayi alwala ta fito ta kalli inda take tunanin nan ne alk'ibla ta tada sallah tana idar ta fara k'ok'arin had'a itace a cikin k'aton murhun dake kitchen d'in haka ta cigaba da aikin tana dafe cikin ta dake mata tsananin ciwo idanunta Kuma yana zubar da hawaye ga hayakin itacen a haka ta k'ok'ar ta ta d'ora k'atuwar tukunyar a haka dakyar ta dafa jallop d'in shinkafar sannan ta bubbuga k'ofar kitchen d'in matar ta bud'e tare da ture Sabeeha ta shige cikin kitchen d'in ta bud'e tukunyar iya k'amshin da taji ne ya tabbatar mata da girkin bana wasa bane wajen dad'i.




Kallon Sabeeha ta yi ta ce "Wuce mu tafi," fita ta yi matar na binta har d'akin da take ciki ta tura ta ciki ta kulle malala Sabeeha ta kwanta saman tiles d'in d'akin ga cikin ta da yake ciwo ga yunwar dake damun ta domin rabon ta da abinci tun jiya da safe gashi goshinta da ta buge a jiyan shi ya haifar Mata da wani ciwon kai ta dad'e sosai a kwance sannan tsohuwar ta bud'e k'ofa ta shiga har gaban Sabeeha ta k'arasa ta ajiye mata wani k'aramun kwano da abincin da bai fi loma biyar ba sannan ta juya ta fice.


Abincin Sabeeha ta kalla ta fashe da kukan tausayin kanta ta dad'e tana kukan sannan bacci ya d'auke ta a wajen domin tunda ta samu cikin yawan bacci ne da ita.



Dukan da taji ta ko Ina shi ya tashe ta daga baccin a mugun firgice tana kallon matar cikin d'aga murya matar ta ce "Waye ya Baki izinin yin bacci tashi yanzu muje ki d'ora abincin dare," gaban Sabeeha ne ya fad'i jin abinda matar ta fad'a sai dai bata da damar musawa sai kawai ta tashi tana tafiya a hankali saboda yanayin da jikin ke ciki ga gajiyar dake damunta.




Har kitchen din matar ta rakata sannan ta kulle ta a ciki da sauri Sabeeha ta shiga toilet d'in da ta shiga d'azu tayi alwala ta yi sallar Azahar da la'asar da bata yi ba sannan ta d'ora girkin wannan karon Mai da yaji ta yi musu sannan aka mayar da ita d'aki aka kulle.



Ko abincin ba a Kai Mata ba haka taci Wanda aka Kai Mata da rana saboda yunwar da take ji ga hannunta sai rad'ad'i yake yi saboda dakan yajin da ta yi haka taci abincin tana kuka tare da tuna gida.



Haka rayuwar Sabeeha ta cigaba da tafiya kullum ita take yin girkin gashi wata sabuwar muguntar da ake mata kullum da daddare sai matar nan ta yi mata duka a cikin sati d'aya gaba d'aya Sabeeha ta fita daga hayyacin ta ta yi duhu sosai saboda rashin wanka ga k'aurin da jikinta yake yi saboda girki ga kanta duk a hannunta saboda dake dake ga babu isashshiyar k'oshi gashin kanta duk yayi datti idan ka ganta sai ka tausaya mata sosai.




A b'angaren Sabreen kuwa abubuwa sun dame ta sosai ga rashin Sabeeha gashi har yanzu Maleek babu wani canji a wani b'angaren Kuma ga matsalar Nasreen kullum sai sunyi cacar baki jin dad'in ta d'aya da ko da yaushe Umar da Fauwaz da Ummi na part d'in dan haka ba ita ke kai Maleek toilet ba ba ita ke yi masa wanka da Shirin sa ba.




A b'angaren Maleek kuwa gaba d'aya ya gama gamsuwa da cewar wannan ba Sabeen sa bace saboda kulawar da Sabeen sa ke bashi baza a tab'a had'a ta da ta sabeen sa ba abubuwa da yawa sun dame shi a ransa dan dai ba yadda zai yi ne kullum ko da idanunsa biyu zaka ganshi idanunsa a rufe ya fad'a duniyar tunani.



Sabreen ce ta fito daga kitchen da tray a hannunta ta nufi d'akin su tana shiga Nasreen da Jamila dake lab'e suka tuntsire da dariya harda tafawa "Ai Jamila Ina fad'a miki ba paralysed ba kome waccan d'an iskan ke yi yau sai ya tashi ya sadu da yarinyar can kuwa ba haka ba ciwon mara ne ajalin sa yau," Jamila ta shek'e da dariya ta ce "Aikin ki na kyau ranki ya dad'e," daga haka suka juya suka bar part d'in.



Sabreen kuwa da sallama ta shiga d'akin Fauwaz ya tare ta tare da karb'ar tray d'in hannunta ya ajiye sannan da kansa ya zuba abincin a plate yasa cokali sannan ya zauna gefen gado kusa da Maleek inda yake zaune akan wheelchair ya fara bashi abincin har sai da ya k'oshi Sabreen ta kalle shi ta ce "Abincin fa?"




Girgiza Kai ya yi ya ce "Na k'oshi sister," bata ce komai ba ta mik'e ta fita daga d'akin ta nufi part d'in su Sabeeha kayan jikin ta cire ta d'aura towel sannan ta fad'a toilet domin yin wanka ta dad'e tana wankan sannan ta fito.



Fauwaz ta gani zaune a gefen gado yana ganin ta ya mik'e da sauri ya nufe ta jikin sa na rawa ya rungume ta a d'an tsorace ta ce "My heart lafiya kuwa ka bari mana," k'ara k'ank'ame ta ya yi ya ce "Bazan iya ba my love bazan iya jure rashin ki a kusa dani ba kullum ina cikin buk'atar ki yanzu na kasa jurewa ne please help me," kallon tausayi ta yi masa tasan tabbas ya yi hak'urin rashin ta sannan ya yi kewar ta kamar yadda ita tayi kewar sa sai kawai ta zame towel d'in jikin ta suka fara sarrafa juna.


Sun dad'e sosai suna aikin abu d'aya sannan suka yi wanka suka shirya Fauwaz shi ya fara fita sannan ta bi bayan sa daga baya.



Tun kafin ta sauka down stairs take jiyo shewar Nasreen ko kallon ta Sabreen bata yi ba tayi hanyar fita sai dai har tasa k'afar ta waje ta ji Nasreen na fad'in "A yau sai na tonawa maciya amana biyu asiri ashe haka ake cin amanar Maleek ba a sani ba saboda a ganshi a kwance sannan ya auri jarababbiyar mata saboda haka vedion nan har a social media saina d'ora shi," daram dam gaban Sabreen ya fad'i ta yi saurin juyawa ta nufi inda Nasreen take.



A tsaye kan Nasreen ta tsaya tare da lek'a wayar Nasreen d'in tabbas video d'in ta ne ita da Fauwaz d'azu da suna tare wani k'ululun bak'in ciki ne ya taso mata a zuciyar ta tana fad'in wannan wacce iriyar masifa ce a d'auki Mata a mijin ta a waya a lokacin da suke saduwa da junansu wannan ai haukane da jahilci.


A harzuk'e Sabreen ta fisge wayar sannan ta dage ta bugata da k'asa ta tarwatse sannan ta kai hannu zata d'auki memoryn take hannun ta Nasreen ta yi da k'arfin gaske domin idan har Sabreen ta d'auke memoryn tabbas ta rasa hujjar ta domin ta rasa video d'in kenan har abada.


Sosai Sabreen ta ji zafin taka ta da Nasreen ta yi dan haka da k'arfi tasa d'aya hannun ta tankad'a ta baya har sai da ta fad'i sannan ta d'auke memory card d'in tasa shi a baki ta taune shi tas sai da ya lank'washe ya k'arye sannan ta fito da shi tayi jifa da shi k'asa sannan ta kalli Nasreen ta ce "Wannan shine kashedi na k'arshe da zan yi Miki akan cewar ki fita a sabga ta idan kuwa ba haka ba sai na nuna miki wacece Sabreen," a harzuk'e Nasreen ta kaiwa Sabreen mari.



Rik'e hannun Sabreen ta yi ta ce "Wannan shine kuskure na farko da zaki fara aikatawa a rayuwar ki ni da ki ke gani nafi k'arfin mari daga wulak'antaccen hannu irin naki," daga haka ta yi jifa da hannun Nasreen ta juya zata bar falon.


Wani k'aton kuttun fulawa na k'asa dake gefe Nasreen ta d'auka tabi bayan Sabreen da shi.



Sam Sabreen bata ji tahowar Nasreen ba sai ji kawai ta yi an buga mata abu a kanta k'ara ta saki ta fad'i a wajen sumammiya ba numfashi.



Jifa da abun Nasreen ta yi a tsorace ganin Sabreen kwance babu numfashi ga jini na zuba a kanta a hankali Nasreen ta ce "Na shiga uku Allah dai yasa Sabreen bata mutu ba domin idan ta mutu na tabbata Fauwaz Kashe ni zai yi,"



Fauwaz da ya dad'e da komawa wajen Maleek ya ji shiru ba Sabreen ba alamar ta gashi Kuma tunda ya shiga d'akin ya lura da Maleek d'in bai da lafiya bayan rashin lafiyar dake damunsa domin sai rintse ido yake yi yana cije lips sannan yana d'an juya kansa maganar duniya Fauwaz ya yi masa amma yak'i kula shi daga k'arshe ma ya lumshe idanunsa domin shi baisan ta Ina zai fara yiwa Fauwaz bayanin abinda ke damun sa ba ko da yana baki balle babu bakin magana sannan ko da akwai baya tunanin zai iya fad'awa kowa abinda ke damunsa indai ba matar sa.




Gashi kuma baida lafiyar da zai iya biyawa kansa buk'ata hawaye masu zafi ne suka gangaro masa daga idanunsa.



A rikice Fauwaz ya ce "Subhanallah Yaya me yake faruwa ne meke damun ka?" Shiru ba magana domin idanun Maleek a rufe suke ma balle ya kalli bakin Fauwaz ya fahimci abinda yake fad'a Wanda ko da ya gani babu bakin magana.




Fauwaz kuwa duk ya rud'e ga halin da yayan sa ke ciki a wani b'angaren Kuma har yanzu Sabreen shiru bata dawo ba.


Gaba d'aya hankalin sa a tashe yake tunanin sa yak'i ba shi daidai akan k'in shigowar Sabreen da sauri ya mik'e ya yi hanyar fita direct part d'in su Sabeeha ya nufa domin dubo Sabreen.
[10/25, 8:57 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️



RUBUTAWA DAGA
HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ)



SADAUKARWA GA
MY DAUGHTER SABEEHA
BILKISU Z.YA'U (🅱️K)
AISHA MAGAJI DABO (AMA)





Page 34

Babu ko sallama ya shiga falon ya samu Nasreen a zaune a kan kujera ta had'a uban gumi duk da kuwa AC dake falon kallo d'aya yayi Mata ya haura stairs kai tsaye.



Yana shiga falon ya fara Kiran ta "My love! My love!" Amma shiru hakan yasa ya fara nemanta amma bai ganta ba nan fa hankalin sa ya k'ara tashi down stairs ya dawo har zai fita sai Kuma ya kalli Nasreen fuska a matuk'ar sannan a had'e ya ce "Kee! Kingan ta?"



"Wafa?" Ta tambaya, ba tare da wani tunani ba kansa tsaye ya ce "Matata mana," duk da tana cikin tashin hankali sai ta ce "Dama tazo gidan nan ne?" Wani banzan mahaukacin kallo Fauwaz ya aika mata sannan cikin had'e fuska da kumbura murya ya fara fad'in "Dalla can malama karki raina mun hankali ina matata nace?" Jikin ta har ya fara rawa ta ce "Wallahi bangan ta ba," tsaki Fauwaz ya ja ya ce "Iskancin banza," ya fad'a tare da ficewa daga part d'in gaba d'aya.


Sai da ya fita Kuma ya fara tunanin shin ina Sabreen zata je a wannan lokacin wata zuciyar ta ce ko tana part d'in Ummi ne Kai tsaye ya nufi can d'in domin dubata da sallama ya shiga falon da yake tsaf-tsaf sai tashin k'amshi yake yi Ummi dake saukowa stairs ta amsa masa sallamar sannan ta ce "Ina Shirin zuwa can wajen ku sai ga ka lafiya dai ko?" Ya ce "A'a Ummi Sabreen tazo nan kuwa?" Kallon tambaya Ummi ta yi masa sannan ta ce "Sabreen tazo nan ne dama?" Da sauri ya ja bakin sa ya yi shiru sannan ya ce "Sorry Ummi Sister zance matar Yaya,"



"Bata shigo ba lafiya dai ko?" Dakyar ya iya k'ark'aro murmushi ya ce "Eh Ummi bari naje," bai jira cewar ta ba ya fice abinsa da kallo Ummi ta bi shi tabbas tasan akwai abinda ke faruwa tunda ta ga yanayin Fauwaz haka sai kawai tabi bayan sa.




Yana shiga d'akin da Maleek yake da sauri ya k'arasa ganin yadda Maleek d'in ya had'a uban gumi sai cije pink lips d'insa yake yi da suka k'ara pink tsabar wuya "Yaya mai yake damunka ne haka?" Maleek kam ba bakin magana sai bud'e idanunsa da ya yi da suka zama jajir tsabar wahala ya kalli Fauwaz baice komai ba Ummi ce ta yi sallama a d'akin itama da sauri ta k'arasa ta ce "Subhanallah Son lafiya kuwa?" Itama ta yi tata tambayar duk da tasan babu bakin amsa mata sai kallon ta itama da Maleek d'in ke yi ja da baya Fauwaz ya yi ya zauna akan kujera ya lumshe idanu.



Zama Ummi ta yi gefen gadon da Maleek ke kwance tana cigaba da tambayar sa abinda ya faru ta ce "Kanka ke ciwo?" Ya girgiza mata kai "Ciki?" Ta tambaya gyad'a mata Kai ya yi a hankali ta kai hannunta kan cikin sa wajen tsakiya ta ce "Nan?" Ya girgiza kai wajen marar sa ta Kai hannun ta ce "Nan ne?" Gyad'a mata Kai ya yi yana rintse idanu.

Ummi ta ce "Bari na Kira Doctor yazo ya duba ka," Nan ma ya girgiza kai Ummi ta ce "Shikenan bari na kira Umar shi yazo ya duba ka," Nan dai shiru ba magana.




Number d'in Umar Ummi ta kira Yana d'agawa ta sanar da shi tana son ganinsa ya ce "To Ummi,"


Tana ajiye wayar sai Ummi ta kalli Fauwaz ta ce "Wai Ina Daughter d'in?" Da sauri ya bud'e idanunsa ya kalli Ummi sannan ya ce "Bari na duba ta," daga haka ya tashi ya bar d'akin ba dan yasan inda zai je duba Sabreen d'in ba.



Bayan fitar Fauwaz da sauri Nasreen ta mik'e ta fara safa da marwa a falon domin jan Sabreen ta yi ta kaita wani d'aki ta kulle sannan tasa Jamila ta gyara wajen da jini ya b'ata.



Sabreen kuwa dake kwance a k'asan tiles sanyin da tiles d'in ya d'auka ne yasa ta farfad'owa ta motsa hannunta sannan ta bud'e idanunta k'ok'arin mik'ewa take yi amma ta kasa saboda mugun sarawar da kanta keyi mata ji take yi kamar buhun sumunti aka d'ora mata akan nata idanunta sunyi jajir tsabar wahala dakyar ta iya mik'ewa tsaye tana dafa bango sannan ta nufi k'ofa sai ta jita a rufe bubbugawa ta fara yi Nasreen dake falon jin ana bubbuga k'ofar ne yasa ta jin wani farin ciki ta nufi k'ofar da sauri ta bud'e.




Dakyar Sabreen ta d'aga idanu ta kalle ta sannan cikin muryar wahala ta ce "Wannan d'in ba shi ki ka ci wallahi sai kin gane kuren ki," tana fad'ar haka ta nufi hanyar fita tana dafe bango.




Dakyar ta iya Kai kanta part d'in Maleek tana bud'e k'ofar Fauwaz ta hanga kwance a kujera ya lumshe idanunsa tunani ne fal zuciyar sa akan Ina Sabreen ta tafi.


Ita kuwa tafiya take yi ga wani jiri na d'ibar ta domin har lokacin jinin bai tsaya ba Sam Fauwaz bai ji tahowar ta ba sai ji kawai ya yi ta fad'a jikin sa a sume.



Da sauri ya bud'e idanunsa yana kallon ta hankali a matuk'ar tashe ya ce "My love meya same ki haka?" Jin ba amsa sannan kamar bata numfashi yasa shi kwantar da ita a kan kujerar ya nufi fridge ya d'auko ruwa sannan ya shafa mata a fuska wata ajiyar zuciya ta saki sannan ta bud'e idanunta a kansa a hankali ta ce "My heart," kafin ya yi magana Ummi ta fito jin motsi a falon da ta yi da sauri ta k'arasa ganin halin da Sabreen d'in ke ciki ta ce "Subhanallah Daughter meya same ki haka ya kamata muje asibiti yanzu tana buk'atar taimakon gaggawa," Fauwaz da duk ya gama rud'ewa ya ce "A'a Ummi zamu je tare da ita ke kin zauna wajen Yaya shima yana buk'atar wani kusa da shi bari muje wajen Mama," tabbas maganar Fauwaz haka take sai kawai Ummi ta ce "Ok kuje to," ta fad'a tare da juyawa cikin d'akin ganin haka sai kawai Fauwaz ya d'auki Sabreen cak ya nufi hanyar waje da ita.




A mota ya sata sannan ya ja motar zuwa asibiti yana driving yana kallon ta so kawai yake ya ji meya faru da ita haka sai ya ce "My heart garin ya hakan ta faru?" Rintse idanu ta yi sannan a hankali tana juya kanta da take jin ya yi mata nauyi ta ce "Nasreen ce,"



"Whatt!!?" Fauwaz ya fad'a tare da jan burki babu shiri Allah yaso ma babu motar dake binsu a baya da sai sun ja accident ta ce "Mu tafi My love kaina ciwo yake mun," Jan motar ya yi suka cigaba da tafiya bai k'ara cewa komai ba sai k'wafa kawai yake ja yana jijjina kai domin bazai tab'a bari hakan ya tafi a banza ba.



Har suka je asibitin bai ce komai ba direct cikin office d'in Mama ya nufa Yana shiga Doctor ta tashi da sauri ta ce "Subhanallah meya faru da ita haka shigo da ita ciki," Mama ta fad'a tare da shigewa wani d'aki dake cikin office d'in ta Fauwaz na biye da ita akan gadon dake d'akin ya kwantar da Sabreen sannan ya ce "Mama a toilet na same ta a kwance Ina ga fad'uwa ta yi," jinjina Kai kawai Doctor ta yi ba Dan ta yadda da hakan ba domin yanayin ciwon baya nuna alamun fad'uwa ta yi treating d'in ta kawai ta fara yi Fauwaz na zaune a gefe.





Yana zaune har aka gama Sabreen d'in ma ta samu bacci ya mik'e ya kalli Doctor ya ce "Mama Bari naje gida na kawo mata abinda zata ci," girgiza Kai Doctor ta yi ta ce "A'a bari na Kira Halima ta kawo kawai," ta fad'a tare da d'aukar wayar ta kan table ta kira Halima ta ce yanzu Faisal ya kawo ta hospital ta taho da abinci Halima ta amsa da "Toh Mama," daga haka Doctor ta ajiye wayar ta zauna tana tunanin to garin ya ya Sabreen ta ji irin wannan ciwon haka.



Fauwaz ya mik'e ya kalli rigar jikin sa da ta gama b'aci da jini ya ce "Mama Bari naje na canja kaya," ta ce "To sai ka dawo," fita kawai ya yi domin damuwar sa ba akan ya canja kayan bane illa ya je ya ci uwar Nasreen kawai.



Mota ya shiga a matuk'ar fusace yake driving har ya je gidan direct a can part d'in ya yi parking sannan ko tsayawa kulle k'ofar bai yi ba ya shige cikin falon.


Nasreen dake daining area tana zuba abinci a plate ba tasan shigar Fauwaz sai kawai ji ta yi anyi ball da ita ta bugi fridge d'in dake wajen abinci muka ya k'ife Mata a jiki wata k'ara ta saki Fauwaz ya zare belt ya fara dukan ta baji ba gani sai ihu take yi bai kyale ta ba sai da ya ga ko motsi bata iyawa sannan ya kyale ta ya ce "Kuma Wallahi akan matata sai naci uwar ki Wallahi shegiya dak'ik'iya Kuma wallahi kallon banza ya sake had'aki da Sabreen ba ke ba Uwar ki da ubanki ma sun shiga uku," Yana fad'ar haka ya juya ya fice yabar banza a wajen da k'aton k'ulu a gaban goshi.



Yana fita mota ya shiga zuwa part d'in Ummi ya yi wanka ya canja kaya sannan ya nufi asibitin.



Umar ne ya fito daga bedroom Sameeha na biye da shi ya kalle ta ya ce "Meeha kiyi hak'uri mana ki k'ara jin sauk'i sai muje," bubbuga k'afa ta fara yi cikin tsantsar shagwab'a ta ce "Uhm uhm nidai sai na bika naji sauk'i fa," ya girgiza Kai ya ce "Ban yadda ba," k'arasawa wajen sa ta yi ta shige jikin sa ta rungume shi sosai ta hana shi tafiya ya ce "Meeha rigima to ki cikani na tafi mana Kinga Ummi na jirana," ta ce "Uhm uhm ni sai ka je dani,"


"Is okay d'auko hijabin ki mu tafi to," cikin farin ciki ta sake shi ta nufi bedroom har zata shiga sai ta tsaya ta waiga ta kalle shi ta ce "Hubby kar fa ka gudu ka barni," murmushi ya yi ya ce "Bazan tafi ba," ta ce "Promise?" Ya ce "Yes I promise dear," juyawa ta yi cikin bedroom d'in ta milk d'in hijab ta d'ora saman cofee shadda dake jikin ta ta d'auki hand bag d'in ta da takalmi ta fito ya rik'e hannunta suka bar gidan.


Da sallama Fauwaz ya shiga office d'in Doctor ya samu Sabreen zaune suna fira da Mama da sauri ya k'arasa ya zauna gefen ta ya ce "Sannu My love," ta ce "Yawwa My heart ka dawo?" Ya ce "Eh na dawo,"




"Yanzu zaku iya tafiya ai tunda ta ji sauk'i," Mama ta fad'a tana had'a takardun gaban ta Fauwaz ya ce "To Mama My love taso mu tafi ko saina d'auke ki ne?" Tashi ta yi tana dariya ta ce "A'a zan iya," ta fad'a suna nufar hanyar fita Doctor kuwa da kallo ta bisu tana girgiza kai.


Mota suka shiga suka nufi gidan Ummi har k'ofar part d'in su Sabeeha ya yi parking suka shiga tare hannun su rik'e da na juna a falon suka samu Nasreen zaune a saman kujera sai kuka take yi Jamila na gasa mata jiki kallon ta Sabreen ta yi sannan ta kalli Fauwaz da sauri ya kawar da fuska irin baisan zancen ba Sabreen kuwa tunda ta ga haka tasan aikin sa ne sai kawai ta kyalkyale da dariya ta

Please Login or Register in order to submit comment