Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Audul baka da kunya," baice mata komai ba sai tab'e baki da ya yi ta fita.




Sabeeha kuwa bacci ne ya d'auke ta a jikin sa jin yadda take sauke numfashi ne yasa ya gane bacci take yi a hankali ya d'ago fuskar ta yana kallon kyakkyawar fuskar ta data jik'ata da hawaye share Mata ya yi yana murmushi sannan ya mik'e da ita a hannun sa ya kwantar da ita kan gadon Ummi ya fita daga d'akin zuwa down stairs.




Yana sauka Ummi ta ce "Son Ina kuma zaka Ina Daughter?" Kallon agogon hannunsa ya yi sannan ya kalli Ummi ya ce "Ummi bacci ta yi yanzu zan dawo bak'i ne ke kirana ba dad'ewa zanyi ba," yana fad'ar haka ya fice.



Hotel d'in da Abokan aikin sa suke ya je a nan suke sanar da shi gobe zasu wuce amma kafin nan suna so su gabatar da parate domin taya shi murna bai musa ba ya ce Allah ya kaimu da haka yayi musu Sallama ya nufi gida.




A part d'in Ummi ya tsaya a falo ya samu su Ummi ya ce "Ummi wai bata tashi ba?" Kafin Ummi ta yi magana Aisa ta ce "Eh saboda haka ka kyale ta kawai ta kwana a nan," zare ido ya yi sannan ya langab'ar da kai ya ce "A ji tausayina mana sweet momma," dariya ta yi ta ce "Wasa nake yi," murmushin da ya bayyana dimples d'insa ya yi sannan ya nufi stairs.




Tura k'ofar d'akin ya yi ya shiga har lokacin baccin ta take yi domin dama tunda aka fara shagalin bikin su bata samun hutu hayewa gadon ya yi ya zauna yana k'are Mata kallo wato ita komai kyau yake yi mata hatta bacci ma a hankali ya kai hannunsa ya shafa fuskar ta mik'a ta d'anyi sannan ta bud'e idanunta masu d'aukar hankali ta sauke su a kansa daidai lokacin Ummi ta bud'e k'ofa ta shiga d'akin hararar wasa ta yi masa ta ce "Wato sai da ka tashe ta ko son," d'an tura baki ya yi ya ce "To fa Ummi tafiya zamu yi," girgiza Kai kawai Ummi ta yi.




Sabeeha kuwa tashi zaune ta yi Ummi na fita ya sauka daga gadon ya mik'ar da ita tsaye ya gyara mata zaman mayafin kanta yayin da d'ankwalin ke rik'e da a hannunsa ya rik'e hannun ta suka nufi waje.




Sun fara sauka stairs rigar ta ta tad'iye ta ta tafi luu zata fad'i yayi saurin rik'o abar sa ta fad'a jikin sa a tare suka saki ajiyar zuciya yayinda mutanen falon hankalin su ya yi wajen su kallon rigar ya yi har jan k'asa take yi furzar da iska ya yi daga bakin sa ya d'an juya idanunsa cikin k'asa da murya ya ce "Kinga wannan rigar zata kayar mun da ke ko?" Ai kafin ta yi magana cak ya d'auke ta ya fara sauka stairs.



"My please ka sauke ni da mutane fa," ta fad'a cikin dashashshiyar muryar ta sannan hawaye na taruwa a idanunta ganin yawan mutanen dake wajen shi kuwa ko a jikin sa baice komai ba.




Hanfa da Haneefa kuwa tuni suka fara aikin nasu wato d'aukar hoto Ummi kuwa girgiza kai kawai ta yi Sabeeha kuwa ganin ya nufi cikin falon da ita yasa tayi saurin b'oye fuskar ta a k'irjinsa ya kalli su Hanfa ya ce "Ku bakwa gajiya ko," daga haka ya yi hanyar fita Aisa ta ce "To Son masu rakiyar fa?" Bai waiga ba ya ce "No sweet momma mun yafe," gud'a wata cikin su ta rangad'a shi kuwa ya fice.




Sojojin sa suna tsaitsaye bai ko kalle su ba ya zagaya gaban motar Salman ya bud'e masa ya zaunar da ita a ciki sannan ya zagaya ya shiga ya ja motar zuwa part d'insa inda Nasreen ke ciki.


Tafiya yake yi a hankali ya d'an kalli Sabeeha ya ce "Baby yadai," kallon sa ta yi sannan ta yi masa harara ta ce "Meyasa zaka d'auke ni gaban su Ummi Kuma Hajiya ma na nan harda mama Aisa ma," ta fad'a tana marairaice fuska.




D'age gira ya yi yana kallon ta sannan ya ce "Manta kawai Baby kina ganin kayan jikin ki zasu yar dake beside ma mene danna d'auki baby na Kuma matata ni ba ruwana da suna nan saboda i can't hide your love infront of koma waye," murmushi ta yi kawai bata ce komai ba.



Har suka k'arasa aka bud'e masa gate ya shiga ya yi parking sannan ya fita ya zagaya ya bud'e inda take ya bud'e ya d'auke ta kamar 'yar baby ya nufi cikin gidan da ya gaji da had'uwa Sabeeha ma kallon gidan take yi saboda ko da wasa bata tab'a zuwa part d'in ba.



Suna shiga cikin falon suka samu Nasreen kwance akan kujera 'yan aiki na zagaye da ita suna mata tausa wata arniyar riga ce a jikin ta iyakar ta gwiwa gata wata shara shara jin sallamar Maleek ne ya sata tashi zaune da sauri domin rabon da ta ganshi ta manta sai dai ganin ya d'auko Sabeeha ne yasa ta had'e fuska ba Kuma ta amsa sallamar ba.



Kallo d'aya ya yi Mata ya d'auke kai domin wani fauu da ta yi kamar a gudu sai k'ananun idanu a wajen banda ma tana da dogon hanci da ana kaita china ba mai gane ita ba 'yar china bace.



Stairs ya nufa da yayinda 'yan aikin suka bisu da kallon birgewa itama kanta Nasreen ta ga sun mugun dacewa amma ganin yadda 'yan aikin suke kallon su kamar sun samu TV yasa ta daka musu tsawa cikin masifa ta ce "Uwar ku ku ke kallo ku b'ace mun da gani tun kafin raina yafi haka b'aci," da sauri suka bar falon suka barta sai huci take yi.



Maleek kuwa yana shiga falo cikin bedroom ya wuce ya zaunar da ita a kan gado ya ce "Baby bari naje nayi wanka," ya fad'a tare da sakar mata kiss a forhead d'in ta ya fita lumshe ido ta yi tana jin farin ciki a ranta.




Yana fita itama ta tashi ta cire kayan jikin ta ta d'aura towel ta nufi gaban mirrow ta ta had'e gashin kanta waje d'aya ta samu wani k'arfe dogo ta soke shi sannan ta nufi toilet d'in da fad'in had'uwar sa b'ata lokaci ne ta watsa ruwa ta fito ta nufi mirrow ta shafa mai sama sama mai k'amshin gaske gashi taji garin akwai sanyi sosai iska sai kad'awa take yi.




Wata sleeping dress tasa ruwan hoda doguwar riga ce mai wani d'an siririn hannu ta d'ora ta samanta wata falmaran mai igiya bata tsaya d'aure igiyar ba ta zira dogon hijabi har k'asa brown color mai haske sallolin da ake binta ta yi tana nan zaune Maleek ya shiga d'akin cikin wasu kayan bacci farare da kallo ya bita domin ba k'aramun kyau hijabin ya yi mata ba gashi hijabin kalar fatar ta zama ya yi gefen gadon har tayi addu'a suka shafa tare ta kalle shi ya ce "Kin idar ba?" Gyad'a kai ta yi.




"Ok taso muje," mik'ewa ya yi ya rik'e hannunta suka fita down stairs a inda suka bar Nasreen a nan suka same ta tana cin jallop rice yatsina fuska yayi saboda da ganin abincin ba dad'i zai yi ba sai uban curry zama ya yi ya zaunar da Sabeeha gefen sa.




Ya kalle ta ya ce "Ke!," Kallon sa ta yi ta ce "Yes," wani haushi ya kama shi wato shi take wani cewa yes ya share ya ce "Kamar yadda ki ka sani nayi aure sannan ga Baby nan a wannan gidan bana son tashin hankali wannan shine kawai abinda nazo na sanar miki kinsan bazan d'auki iskanci ba kija girman ki," yana fad'ar haka ya mik'e rik'e da hannun Sabeeha zasu koma d'aki.



"Banji kayi maganar kwana ba?" Harara ya aika mata ya ce "Ashe ki manta da magana dake a ranar da aka kawo ki gidan nan ko?" Wani haushi ya kama Nasreen ta ce "Ban manta ba Kuma hakan da kake k'ok'arin yi ba adalci bane kawai ka raba mana kwana ehe,"




Daga bayan sa k'asa k'asa Sabeeha ta ce "Please My do as he said tana da gaskiya," ajiyar zuciya ya sauke ya kalli Nasreen ya had'e fuska ya ce "Bayan mun gama cin amarci kowacce kwana biyu ne kwananta," yana fad'ar haka ya juya yaja hannun Sabeeha suka yi d'aki.



Nasreen kuwa tsaki ta ja ta ce "Aikuwa Wallahi sai yarinyar nan taci uwar ta a gidan nan wato ita zaka bawa kanka amma Wallahi Allah ya isa ko da yake Arfat ne babban shege Kuma wallahi saina nuna muku real color na," ta fad'a tare da shigewa d'akin ta.



Maleek kuwa suna shiga d'aki ya ce "Ina zuwa," falo ya fita ya shiga kitchen ya sai gashi da lemuka da su fresh milk da kaza ya ce "Zo baby kici nasan baki ci komai ba," ba musu ta zauna da kansa ya bata taci ta k'oshi tasha fresh milk ta kalle shi ta ce "Kaifa?" Girgiza kai ya yi ya ce "No baby na k'oshi," d'aukar kayan ta yi ta Kai kitchen Wanda ya gaji da tsaruwa ta fito.




Tana shiga d'akin ta zauna lokacin Maleek ya shiga toilet yin alwala yana fitowa ya ce "Baby zo muyi sallah," ta ce "To Ina zuwa," toilet ta shiga ta yi brush sannan ta fito ta samu ya shimfid'a prayer mat a saman lallausan carpet d'in d'akin ya jasu Sallah raka'a biyu suka yi addu'a sannan ya dafa kanta yayi Mata addu'a ya yi Mata tambayoyi sannan suka hau gado domin yin bacci bayan sun kashe k'wan d'akin.




Nan fa suka tsunduma wata duniyar ta daban domin Maleek hanata sakat ya yi abinka da farin shiga tab'o can tsotsi can ita kuwa sai nok'ewa take yi daga baya kuwa da ta tsumu da salon sa ta fara biye masa sai da aka zo ganawa da babbar fada sannan ido ya raina fata domin ta wahala ba k'adan ba duk da tana da dauriya amma sai da tayi masa kuka yayinda shi kuwa gaba d'aya tayi gabas da hankalin sa sai addu'a yake shek'a mata.



A b'angaren su Umar kuwa Sameeha zazzab'i ne ya rufe ta magani Umar ya bata sannan suka kwanta tana manne a jikin sa har bacci ya kwashe su.





Sabreen kuwa tun a mota take zuba suna zuwa gidan bayan mutane sun tafi Fauwaz ya jata d'akin sa suka yi wanka sannan suka ciyar da juna suka yi sallah sannan tun a wajen suka fara kashe juna da romance sannan suka haura zuwa bed tofah masu rawar Kai biyu sun had'u aikuwa sai durzar juna suke yi daga k'arshe wiwi Sabreen ta fara kuka tana cewa Wallahi ta hak'ura ita ya kyale ta Fauwaz kuwa baima San me take yi ba domin ya shiga babbar fada.



NI KUWA NACE ASUBA TA GARI SABEEHA DA SABREEN.
[10/25, 8:51 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️



RUBUTAWA DAGA
HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ)





SADAUKARWA GA
MY DAUGHTER SABEEHA
BILKISU Z.YA'U (🅱️K)
AISHA MAGAJI DABO (AMA)



Page 27


Washe gari tun asuba zazzab'i ya rufe Sabeeha tana kwance ga azabar da k'asan ta ke mata kamar an yayyanka mata da reza sai hawaye take yi tana kwance jikin Maleek da tunda yayi mata wanka shima ya yi ya kasa matsawa ko ina ko sallah ranar a gida ya yi sai sannu yake jera Mata.




Tashi ya yi ya shiga kitchen domin sama mata abinda zata ci sai dai shi sam bai wani iya girki ba dakyar dai ya dafa ruwan tea ya soya dankali da kwai ya nufi d'akin ya zauna gefen gadon tare da shafa sumar kanta ya ce "Baby taso kici abinci kinji?" Girgiza kai tayi har da hawayen ta ganin dagaske fa ba cin abinci zata yi ba yasa ya fara k'ok'arin cire rigar jikin sa yana cewa "Tunda baza kici ba bari na k'ara yi," a firgice ta girgiza masa kai ta ce "Wallahi zanci," murmushi ya yi ya ce "Yawwa baby na," d'aukar ta ya yi cak ya d'ora ta a cinyar sa ya d'auko tea d'in da ya had'a yana bata tana sipping a hankali sai da ta ce ya isa sannan ya kyale ta.






Dankalin ya d'ebo da fork ya kai bakin ta sai ta shagwab'e fuska ta ce "Uhm uhm da zafi fa," ta fad'a tana k'ifk'ifta idanunta da har lokacin da k'walla a cikin su.



Sarai yasan rigimar ta ce sai ya fara hura mata abincin kamar yadda akewa yara yana bata sai dai bata ci da yawa ba ta ce ita ta k'oshi sannan ya rabu da ita ya zaunar da ita ya d'auke kayan ya kai kitchen yana dawowa tabi shi da idanu gira d'aya ya d'aga mata "Da wani abune Baby?" Noding kanta tayi ta ce "Ina so nayi brush ne," d'aukar ta ya yi ya kaita toilet tayi brush d'in ya dawo da ita cikin d'akin.



Lokaci ya kalla sannan ya d'auki wayar sa ya kira wayar Rinaz Hanfa ce ta d'aga wayar ta ce "Hello Yaya good morning,"



"Morning," ya fad'a a tak'aice "To Ina sweetheart tana lafiya?" Kallon Sabeeha ya yi sannan ya ce "Hanfa ina Ummi?"




"Yaya Sweet momma fa ta tafi hospital," Hanfa ta fad'a cikin jin mamakin maganar Hanfa ya ce "Ok ba matsala," ya katse wayar ya fita daga d'akin.



Sai da ya jima da fita sannan ya koma cikin d'akin cikin wata blue light d'in shadda sai kyalli take yi ya yi kyau sosai kallon sa Sabeeha kansa ba hula sai tulin sumar kansa dake shek'i fuskar sa fayau gwanin sha'awa bakinsa ya k'ara pink ga girar sa data kusa had'ewa ta yi bak'i sosai kamar gashin kansa haka ma zara-zaran gashi idanunsa.



Kashe mata ido d'aya ya yi ita Kuma ta yi k'asa da kanta murmushin sa mai tsada wanda ke bayyana dimples d'insa ya yi mata sannan ya nufi drower ya ciro wani dogon Hijabi coffee color ya zira mata saman milk d'in doguwar jikin ta yasa mata takalmin ta cak ya d'auke ta ya yi hanyar fita da ita.


Kallon sa ta yi ta ce "Ina zamu je?"


"Hospital kinga baki jin dad'i sosai," ya fad'a tare da bud'e k'ofar falon ya fita.



Nasreen dake zaune a falon tana jinsu su dai basu san da halittar ta a wajen ba tsaki ta ja tana jin wani Abu ya tokare mata k'irji sai kawai ta kama kuka tana jin kamar ta kashe Sabeeha ta huta.


A mota ya sata ya zagaya ya shiga yaja motar yabar gidan gaba d'aya a hanya Sabeeha ta kasa yin shiru ta ce "Amma wanne asibitin zamu je?"


"Na su Ummi mana," ya fad'a hankalin sa na kan titi "Ni dai gaskiya kar muje nan me zaka cewa Ummin to?" Ta fad'a tana marairaice fuska dariya ya yi ya ce "Ce mata zanyi Ummi mota ce zata shiga ma ajiyar ta ma'ana garaje Kinga ai gurin already nata ne so sai wani gini yaso bata matsala lokacin da take k'ok'arin shiga d'akin ta sai kawai wannan motar ta rusa ginin shine muka zo a duba mana wajen da fatan ba matsala," ya k'arasa maganar tare da yin murmushi.




Shiru Sabeeha ta yi tana tunanin maganar sa ta ce "Mota ta rusa gini kuma shine zamu a dub...," Zare ido ta yi tana kallon sa saboda ta gano abinda yake nufi ta ce "Please My kar muje wajen Ummi Wallahi kunya nake ji," ta fad'a k'walla na zubowa a idanunta.



"Ok shikenan sai muje wajen Mama ai," kuka kawai tasa masa girgiza Kai ya yi ya ce "Nabani Baby me ya faru kuma?"




"Haba Dan Allah baby saboda mune sarakan rashin kunya kawai sai muje wajen su mu fad'a musu wannan abun?" Ta fad'a cikin kuka.




"To sai me kinga nifa su kad'ai zan iya fad'awa wannan sirrin bedside ma nifa ko mace 'yar uwarki bazan je wajen ta ta duba ki fa Aha garama kiji," ganin dagaske yake maganar yasa ta cigaba da kukan ta har suka k'arasa asibitin ai a nan ta tabbatar dagaske yake.




Zagayawa ya yi ya bud'e b'angaren da yake zai d'auke ta ta zare ido ta ce "Please ka barni zanje da kaina," had'e fuska ya yi ya ce "To naji fito kiyi tafiyar mugani," a hankali ta zura k'afafun ta waje ta fito tana rintse idanu hannun ta ya rik'e suka fara tafiya sai dai sai runtse idanu take yi k'walla ya cika idanunta.





Ganin haka yasa Maleek d'aukar ta yana cewa "Kin fiya rigima baby kina irin wannan tafiyar ai sai kija hankalin mutane wajen mu idan Kuma na d'auki matata ina ruwan wani dani," luf kawai tayi a jikin sa domin ita kad'ai tasan me take ji.


Ai kuwa duk inda suka gifta sai an kalle su shi kuwa ko a jikinsa har suka k'arasa k'ofar office d'in Ummi ya murd'a handle d'in ya shiga rintse idanu kawai Sabeeha ta yi saboda wata kunya da ta saukar mata.




Da sallama ya shiga office d'in Ummi ce tare da Doctor ne a zaune suna yiwa juna ya gajiyar taro suna d'an tattaunawa ganin Maleek d'auke da Sabeeha ne yasa su sakin baki suna kallon su wucewa ya yi da ita kan doguwar kujerar dake cikin office d'in sannan ya k'arasa gaban su ya gaishe su suka amsa.




Kallon juna Ummi da Mama suka yi sannan suka mayar da kallon su kan Maleek Ummi ta ce "Son lafiya kuwa me yake damun Daughter d'in?" D'an k'asa ya yi da kansa sannan ya kalli Ummi yana d'an sosa kai bai yi magana ba.



"Uhm hum Kai muke sauraro," a hankali ya tashi ya zagaya kujerar da Ummi ke zaune ya kai bakin sa saitin kunnen ta ya ce "Ummi a d'an dubana wajen ko fa tafiya ta kasa," hararar sa Ummi ta yi sannan ta tashi da sauri ta k'arasa wajen Sabeeha da har lokacin ta kasa bud'e idanunta saboda kunya ta zauna gefen ta.




Tashi Doctor ta yi ta kalli Ummi ta ce "Aysha ni na tafi office," bata jira cewar Ummi ba ta fice jin muryar maman su yasa ta kuma jin wata kunyar ta kuma kamata dariya Ummi ta yi ta ce "To ai Maryam d'in ta fita bud'e idanunki Ummin ki ce fa," a hankali ta bud'e idanunta masu d'aukar hankali eyelashes d'inta duk sun jik'e da hawaye ta kalli Maleek sannan ta kalli Ummi tana hawaye.





D'an rungume ta Ummi ta yi ta ce "Sorry kinji yarinya ta Son ne ko?" Gyad'a kai Sabeeha ta yi.


"To yi hak'uri kyale shi ko ya fita?" Nan ma gyad'a kai Sabeeha ta yi Ummi ta kalle shi ya k'urawa Sabeeha ido ta ce "To daughter ta ce ka fita saboda haka ayi waje,"



"Ni koh baby?" Ya fad'a yana nuna kansa a hankali ta ce "Eh," ta fad'a tana maida kanta k'irjin Ummi.



Tashi ya yi yana cewa "Idan fa na tafi bazan dawo ba," tashi Ummi ta yi ta ja hannun sa ta tura shi waje ta rufe k'ofar sannan ta dawo wajen Sabeeha ta kwantar da ita ta fara dubata.



Gaskiya kam ba laifi ta ji jiki dan yaji mata ciwo d'inki kad'an Ummi ta yi mata tare da allurai tana yi mata sannu suna nan Maleek ya yi knocking Ummi ce ta bud'e masa k'ofa ya shiga sai hararar wasa yake aikawa Sabeeha.



"Yawwa Son ina ga kawai mu tafi zuwa gida," ya ce "Toh," k'arasawa ya yi gaban Sabeeha ya d'auke ta ya yi hanyar fita Ummi na biye da su a baya har wajen mota ta bud'e masa gaban motar ya zaunar da Sabeeha sannan ya zagaya ya shiga Ummi ta ce "Yawwa kuje bari zan taho a tawa motar," gaba suka yi ta bisu a baya.



Suna zuwa a k'ofar part d'in Ummi ya yi parking Ummi nayin parking ta k'arasa ta ce "Son muje ciki akwai magungunan da ya kamata tasha," cikin falon suka shiga yana d'auke da Sabeeha direct d'akin Ummi ya kaita sannan ya koma falon inda su Aisa suke.



"Ai dama tunda naga Audul na rawar kai nasan sai yayi ba daidai ba," Hajiya ta fad'a tana hararar Maleek yatsina fuska ya yi ya ce "To ke Ina ruwanki sannan ni a dena b'ata mun suna nikam ba sunana Audul ba Abdul nake ehe idan baki iyawa kice Maleek,"




"Rabu da Hajiya Son zonan kusa dani ka zauna bari na kawoma abinci nasan baka samu kayi break fast ba," ta fad'a tare da mik'ewa ta nufi kitchen ta had'o masa breakfast a tray ta janyo k'aramun center table ta ajiye masa a kai ta zauna gefen sa.




Side hug yayi mata ya manna mata kiss a check d'inta ya ce "Thank you sweet momma na," ya fara cin abincin yana kallon Hajiya da ta saki baki tana kallon su.





Ummi ce ta shiga falon bata kalle su ba ta wuce kitchen ta had'awa Sabeeha breakfast ta nufi stairs tana shiga daidai lokacin Sabeeha ta fito daga wankan da Ummi ta had'a mata ruwa tasa ta yi a hankali take takawa ta zauna gefen gadon ta shafa mai dasu humra Ummi ta bata wata had'add'iyar tsadaddiyar atamfa d'inkin doguwar riga up shoulder tasa atamfar ta yi Mata kyau fara ce da blue Ummi da kanta ta gyara mata gashinta ta kitse mata shi ta gefe kan bata sa mata ribbom ba saboda kar ya dame ta ta fesa mata turaruka sannan Ummi da kanta ta bata abincin taci sannan tasha magunguna ta ta d'auki abubuwan abincin ta fita.



Ummi na fita su Rinaz suka shiga d'akin ita da su hany "Sannu dear ashe kin maguzu," Rinaz ta fad'a cikin sigar tsokana "Sannu Sweetheart kunsha aiki ke da Yaya," hany ta fad'a Sabeeha kuwa da harara kawai take binsu.





Ummi ce ta shiga d'akin ta ce "Ku Kuma ya akayi ku ka zo ku ka samun yarinya a gaba?" Ta fad'a tana kallon Sabeeha da take kallon Ummin idanunta taf k'walla.


"Kunga ga hanya nan bana son takura oya kuyi waje then kuje part d'insu ku gyara musu tas kunji ba?"




"To Ummi ba mu car key d'in ki," Hanfa ta fad'a mik'a mata Ummi ta yi suka fita.



"Kwanta ki huta kinji daughter," Ummi ta fad'a sai da ta ga Sabeehan ta kwanta sannan ta fita tare da ja Mata k'ofar d'akin.





B'angaren su Sabreen kuwa itama ta gurzu ba laifi bayan sunyi wanka sai shagwab'a Sabreen ke sauke masa dan ko abincin da Ummi ta aika musu cewa ta yi ita baza ta ci ba sai dai ya girka mata wani ba yadda ya iya haka ya shiga kitchen ya girka mata dan mugun ji yake da ita motsi kad'an ya ce mata sannu.




Su Sameeha kuwa da safe sumul ta tashi zazzab'in ya sake ta hakan yasa suna gama breakfast Umar ya fara shishshige mata duk sai ta gama tsorata sai tattab'e ta yake yi kamar zata yi kuka ta ce "Ni dai ka barni ko na fad'a ka da Ummi," cikin zare ido ya ce "Kice mata me bayan tasan ke d'in mallakina ce," ya fad'a yana d'aga mata gira d'aya tura baki Sameeha ta yi ta ce "Toba dama ta ce idan kayi mun ba daidai ba na gayamata ba?"



"To amma nima ai tace ki girmamani sannan kiyi mun biyayya ko ba a sanar dake hakan ba bugu da k'ari kuma Ummi tace ki rik'e ni gam saboda haka kawai ba mutunci a bani hakk'ina," shiru Sameeha ta yi tabbas maganar sa gaskiya ce sai ta marairaice fuska irin a tausaya mata d'in nan ta ce "To shikenan naji amma ka bari sai da daddare ka ga yanzu ban gama samun sauk'i ba," sarai yasan taji sauk'i garau amma sai ya basar ya ce "To shikenan naji na kuma yadda," daga haka suka cigaba da fira.




Sabeeha kuwa bacci tayi sai azahar sannan tayi juyi ta bud'e idanunta daidai lokacin Maleek ya shiga d'akin tsayawa kallon ta ya yi domin ta yi kyau sosai cikin atamfar itama kallon sa take yi ya canja wanka cikin wata farar shadda yayi kyau sosai ba aiki a kayan sai wasu bak'ak'en bottles da aka har wajen aljihun sannan rigar iyakar ta cinya sai dogon hannu da ya sawa Link's bak'ak'e kansa ba hula sai k'amshi yake yi gashi kansa ya zubo har goshin s.




Shi kuwa gashin ta da aka kitse mata shi a gefe shi ya tafi da shi domin ba k'aramun kyau ta yi

Please Login or Register in order to submit comment