Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

samu Sabreen a tsaye Sabreen d'in na ganinta ta tare ta ta ce "Sabeeha dear a Ina ki ka tsaya haka?"


"Akwai abinda ya tsayar dani sister ina zuwa," bakin k'ofar d'akin ta tsaya ta k'wank'wasa likitan ya fita ya amsa ya juya ya koma ita Kuma ta koma kusa da Sabreen ta zauna tana sauke ajiyar zuciya.



Kad'an Sabreen ta kalle ta ta ce "Sis wannan daddad'an k'amshin turaren fa da kike yi?" Kad'an Sabeeha ta yi dariya tare da tuna aika aikar da ta yiwa Wanda bata san waye ba.



Cikin dariya ta bawa Sabreen labarin abinda ya faru sannan ta ce "Sister da gani babba ne a sojojin ma ke Kinga matsu tsaron sa da bindigogin su kuwa hmm ai Wallahi na d'auka zan sha harbi," dariya Sabreen ta yi ta ce "Dear dama haka Rashida ta koma ni Wallahi tsoro nake ji kar su dawo Kinga fa abinda Rashida ta aikata to ko me su Yallab'ai zasu yi Kuma oho," Sabeeha ta ce "Dalla can rabu da su," Nan sukai ta fira.



Maleek kuwa Yana tsaye a wajen bai motsa ko ina ba.



'yan garin kuwa tsoro ne ya kama su ganin babban soja kamar Maleek tsaye a k'ofar masallacin su domin da yawa a cikin su masu karanta jarida sunsan sa addu'a suke yi Allah yasa ba laifi suka aikata ba Kuma ga motoci nan birjik a wajen.



Duk cikin su an rasa mai k'arfin halin zuwa wajen da yake ballantana su yi tunanin shiga masallacin su yi Sallah.



Maleek kuwa agogon hannunsa ya kalla ya ga k'arfe bakwai saura kad'an tsaki ya ja Yana tunanin anya kuwa masallacin nan ana yin sallah cikin sa gashi har yanzu sojojin sa basu dawo ba bai gama tunanin ba sai gasu sun dawo tare da 'yan daban har gaban sa suka gurfanar da su k'are musu kallo ya yi.



Sannan ya juya ya ga mutane a bayan sa Kuma alamun su ya nuna a tsorace suke kallon sa ya mayar kan sojojin jin nasa wad'an da ba musulmai ba ya ce "Michel,jamsyn,Monday daniel,mesharck stay with them," sannan ya k'arasa gaban mutanen ya yi murmushi ya ce "Muje mu yi sallah lokaci yana k'urewa," sai lokacin mutanen suka saki jikin su suka shiga masallacin suna mamakin lallai wannan yaron ya basu mamaki duk muk'a munsa Amma a wannan masallacin zaiyi sallah.



Liman kuwa gani yake yi idan ya ja sallah Maleek zaice bai iyaba Dan haka yak'i jan Sallar Maleek ganin time na k'urewa kawai ya je ya ja su sallar cikin had'add'iyar muryar sa da Kuma k'ira'arsa Mai matuk'ar dad'i su kansu jama'ar k'auyen kowa mamaki yake yi wannan Kuma waye haka kamar sheikh sudais.


Sabreen ta tab'a Sabeeha ta ce "Wayyo sister kinji wata murya na jan sallah Wallahi tunda nake ban tab'a jin murya mai dad'in ta ba kinji a hankali yake yi ga muryar tasa mai shiga k'wak'walwa nasan a kaf garin nan baza a samu mai wanna muryar ba sai dai ko bak'o," kallon Sabreen kawai Sabeeha ke yi kamar za ta yi dariya ta ce "Allah ya shirye ki Sabreen ni tashi muje muyi alwala," fita suka yi suka yo alwala sannan suka yi sallah.




Maleek kuwa bayan ya idar da sallar tare da kwararo addu'oi ya tashi ya fita har mota 'yan k'auyen suka yi masa rakiya ya shiga sannan ya kalli Salman ya ce "Me wad'an can abubuwan suka ce?" Salman ya ce "Wai biyan su aka yi su kamo yarinyar," jinjina kai Maleek ya yi ya ce "Good a kaini wajen Wanda ya turo su," ba b'ata lokaci aka sanarwa da motocin gaba Wanda 'yan daban ke cikin d'aya daga ciki.



Sai da suka yi tafiya Mai nisa sannan suka isa inda gidan su Rashida yake ko fita daga motar Maleek bai yi ba ya ce "Salman jeka kayi masa warning idan yak'i ku nuna masa kuskuren sa," abinda Maleek bai saniba ai ba Wanda ya isa ya ga wannan zugar sojojin da bindigu bai tsure ba.



Fita Salman ya yi d'aya daga cikin Wanda Rashida ta aika d'aya ya kirata a waya ba b'ata lokaci ta fita sai dai ganinsu tare da sojoji sai da ta fara fitsari a wando Maleek kuwa mamaki yake yi mace ce ma wai da wannan karf'in halin shi kansa Salman ya yi mamaki amma ya dake ya koma yanayin sa na jaruma sojoji ya buga mata warning wanda Rashida har kuka take tana basu hak'uri sannan Salman ya tafi ya bata waje ya koma mota suka kama hanya bayan sun sauke mata 'yan daban ta.




Gudu suke yi sosai a hanya yayinda Maleek ya lumshe idanunsa ya jingina da kujera ga mamakin sa tunda ya lumshe ido hoton fuskar ta kawai yake hangowa saurin bud'e idanunsa ya yi Yana mamakin kansa basarwa ya yi ya sake rufe idanunsa sai dai nan ma ya sake hango fuskar ta tsaki ya ja sannan ya bud'e idanunsa ya d'auki wayar sa dake ringing.



Ya d'aga tare da yin sallama daga can Ummi ta amsa ta ce "Son ya hanya?" Ya ce "lafiya lau Ummina," ta ce "Masha Allah dama Kiran ka nayi naji lafiyar ka," cikin son mahaifiyar tasa ya ce "Ina lafiya Ummina mun kusa sauka insha Allah," ta ce "Tom Allah ya tsare hanya," ya amsa da "Ameen," daga haka ya katse kiran sai da dare sosai sannan suka Kai gida.


Rashida kuwa ta yi da ta sani yakai sau million gani take yi kamar zasu iya dawowa.



Su Sabeeha kuwa sai da suka kwana bakwai a asibiti sannan aka yi discharging d'in su.



Jikin Sameeha ya yi sauk'i sosai domin dama rashin samun kulawar da bata dace bane yasa ta ciwon kan tafiya suke yi su uku suna fira abinsu suna dariya inda Sabreen ke ba Sameeha labarin abinda Rashida ta so aikawata Sameeha ta ce "Tabdijan lallai ma Rashida ni tsorona kar su Kuma dawowa," daga bayan su suka ji wasu samari na cewa "Wallahi yau sati d'aya kenan da MG Abdul-maleek ya zo garin nan Kuma shi ya ja sallah a wancan masallacin," d'aya ya ce "Anya kuwa da gaske MG Abdul ne domin abun da mamaki Mai matsayi kamar sa mai ji da kyau ilimi kud'i da Kuma muk'ami ya rasa inda zai tsaya ya yi sallah sai a garin nan domin ko a saudia yaso ya yi sallah zai je ya yi ya dawo," waccan ya Kuma cewa "Abokina kenan MG ba kamar sauran jama'a bane Wanda na tabbata ko D.P.O na garin nan ba zai yi sallah a can masallacin ba amma MG ba bu ruwan sa kowa nasa ne ballantana ya nuna k'yama kai fak'at ma bari na nuna maka hotan sa," nan ya nunawa abokin sa hoton Maleek.


"Kai gaskiya ina yin sojan nan sosai ko dan taimakon sa ga talakawa," Sabreen ta kalli Sabeeha ta ce "Wallahi Sabeeha dear shine Wanda ki ka bani labari bari naje na gansa," saurin rik'o ta Sabeeha ta yi ta ce "Ke meye haka so ki ke su rainaki zo mu tafi," ta ja hannun Sabreen suka yi gaba Sabreen ta ce "Tunda kin hanani na gansa bani labari ya kamannin sa yake?"



Sabeeha ta ce "Wow," ta yi gaba tana kallon wata k'aramar mage da ta d'auki hankalin ta fara ce magen sai bak'i-bak'i kad'an a jikin ta nufar magen ta yi tana cewa "Wow pretty," d'aukar magen ta yi tana shafa jikin ta.



Da kallo su Sameeha suka bita da shi Dan duk a tunanin su da Sabeeha ta ce wow labarin kyawun MG zata fara zayyana musu ashe mage take cewa wow d'in.

Wani mata shine ya k'arasa wajen Sabeeha ya ce "Mage tace," mik'a masa Sabeeha ta yi tana jin dama ya bar mata ya ce "Dama zan bayar da ita ne ko kina so?" Da sauri ta ce "Eh Wallahi ina so ta shiga raina," ya ce "Tom na baki amma ki kula da ita sosai," ta ce "Tom zan kula da ita nagode," tana fad'ar haka ta waiga wajen su Sabreen ta ce "Ku zo mu tafi mana," k'arasawa wajen ta suka yi suna kallon magen su ma ta yi musu kyau.


Sabreen ta ce "Ban manta ba fa dear ya sojan yake?" Tsaki Sabeeha ta ja ta ce "Ni fa bansani ba abinda nasani kawai dogo ne sannan yana dadda'an k'amshi kamar yadda ki ka ji k'amshin ranar domin ni banga fuskar sa ba ko kad'an kawai dai nasan babban mutum ne saboda yawan sojojin dake tsaron sa wajen mota ashirin sai dai ni ana bani mamaki ki kalla yadda wad'an can samarin ke firar sa Kai shiyasa fa duk inda d'an k'auye yake sai ya nuna k'auyen ci nasan yanzu ya ma manta ya zo nan amma kalli tsahon sati d'aya kenan Amma ba a dena firar sa ba," tana fad'ar haka ta yi gaba abinta abinda Sabeeha bata saniba shine ko a birni ma rububin ganinsa ake yi.



B'angaren su Yallab'ai Kamis kuwa tunda aka nemi su Sabeeha aka rasa ya kwanta rashin lafiya saboda shi dagaske sonta yake yi har sai da ya kwanta a asibiti gashi baisan garin su ba Rashida ce kawai tasani Kuma itama bata gidan gashi Farida tak'i fad'a masa garin su Rashida bare su je su tambaye ta haka yai ta jinya har ya ji sauk'i ya warware amma son Sabeeha na nan a ransa.



Maleek kuwa tun daga ranar kullum tuna ta yake yi ko bacci yake yi mafarkin ta yake yi gaba d'aya ya canja sai ya zauna kawai Yana tunanin ta shi kansa har mamakin kansa yake yi domin bai tab'a jin hakan akan wata mace ba sai ita.



Yau ma zaune yake a falon sa ya zurfafa a tunanin ta kamar kullum ya tashi kawai ya fita zuwa part d'in Ummi.



Yana shiga ya samu waje ya zauna yana danna wayar sa Ummi ce ta sauko daga stairs gefen sa ta zauna ta shafa kansa ta ce "Son," ya ce "Na'am Sannu da fitowa Ummi," ta ce "Yawwa ni kuwa kwana biyu mai yake damunka ne naga kamar kullum cikin tunani kake ko Kai da matarka ne?" Girgiza kai ya yi ya ce "A'a Ummi ba da ita bane," sannan ya bawa Ummi labarin komai.



Murmushi ta yi ta ce "Son kenan you're fall in love with her right?" Shiru ya yi yana tunanin jin soyayya kenan to indai kuwa haka ne to kuwa ya fad'a son ta Ummi ce ta katse shi da cewa "Har naji ina sonta me sunanta?" Kallar tausayi ya yi ya ce "I don't know Ummi Anya kuwa ba aljana bace Ina juyawa fa na ga bata nan," dariya Ummi ta yi saboda wani lokacin idan Maleek ya yi wani abun kamar yaro ta ce "Son kenan mutum ce mana saboda kasan wad'an da suka biyo ta baza su biyo aljana ba ko suma aljanun ne?" Dariya ya yi ya ce "A'a mutane ne fa,"


"Nima dai abinda nagani kenan amma son yanzu idan kasan gidan su Mai zai faru?" Shiru ya yi alamun tunani sannan ya ce "Uhmm kawai Auren ta zanyi," kallon sa Ummi ta yi tana jin farin cikin hakan domin ko ba komai tasan idan ya k'ara aure da Kuma wacce yake so hankalin sa zai fi kwanciya sai dai tana tsoron abinda zai je ya dawo.


Falon ne ya d'auka Rinaz is open the door da gudu Rinaz ta shiga falon ta yiwa Ummi side hug ta ce "Ummina na dawo Kuma fa tare muke da Mama," kafin Ummi ta yi magana Doctor Maryam ta shiga falon tasha gayu cikin doguwar rigar shadda maroon ta yi kyau sosai hannun ta rik'e da hand bag da key d'in mota sai k'amshi take yi.


Tashi Ummi ta yi tana murnar ganinta sai da suka d'an rungumi juna sannan suka k'arasa falon cikin girmamawa Maleek ya gaida doctor Maryam ta amsa cikin fara'a sau biyu kenan suka tab'a ganin juna amma doctor Maryam ta ji yaron k'awar ta ta ya shiga ranta saboda biyayyar sa da Kuma girmama manya.


Suna gaisawa ya mik'e ya ce "Ummi bari naje," Ummi ta ce "To ka fa binciko mun inda yarinyata take," ya yi murmushin da ya bayyana dimples d'insa ya ce "Toh Ummi," ya fice Doctor Maryam ta ce "Wacce yarinya Kuma?" Ummi ta ce "Wata yarinya ya had'u da ita yake so," murmushi Doctor Maryam ta yi ta ce "Masha Allah yarinya ta yi dacen miji kam," Rinaz kuwa murna take yi domin idan abun ya tabbata ba k'aramun budiri zata had'a ba.



Maleek kuwa yana fita ya ga Nasreen cikin motar ta ta figo ta da gudu kallo d'aya ya yiwa motar ya d'auke Kai yana yiwa Salman magana.


Gurin ta k'arasa ta ce "Ya Maleek," waigawa ya yi ya kalle ta tasha kwalliya cikin wata doguwar riga Mai k'aramun mayafi ta wani d'aura shi a ka sai kace ba matar aure ba yatsina fuska kawai ya yi ta ce "Dama bikin friend d'ita ce ko zamu je tare?" Kallon Mamaki ya yi mata domin bai ma san zata fitan ba ya ce "No jeki abinki," ta juya ta tafi tana wani karairaya shi kuwa ko kula da abinda take ma bai yi ba dan hankalin sa na gun Salman Yana fad'in "Ina so ku bincika mun garin ina so nasan komai a kanta," Salman ya ce "angama ranka ya dad'e," shi Kuma ya wuce part d'insa Salman kuwa mota ya shiga tare da wasu sojoji suka bar gidan.
[10/25, 7:35 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️



RUBUTAWA DAGA
HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ)




SADAUKARWA GA
MY DAUGHTER SABEEHA
BILKISU Z.YA'U (🅱️K)
AISHA MAGAJI DABO (AMA)



Page 5

Sabeeha kuwa mota suka samu suka tafi gida suna sauka a bakin titi suka tafi a k'afa har zuwa k'auyen su hango mota suka yi a k'ofar gidan su Sabeeha ta da fa goshi ta ce "Na shiga uku waccan mayen ya zo kenan?" Sameeha ta ce "Anya ba wani abu Kawu ke k'ullawa ba?" Zare ido Sabreen ta yi ta ce "Kai kunga fa mai gari can har ma da d'ansa waccan Mai k'aton Kai lallai akwai abinda kawu ke k'ullawa," tunawa da wani Abu da Sabeeha ta yi ne yasa ta ja da baya su ka ce "Meya faru?" Sabeeha ta ce "Kun manta da maganar kawu ne da ya ce nan da sati d'aya zai yi mana aure?" Ai take dukan su suka tsure Sabreen ta ce "Anya kuwa ma je gida kuwa dear Dan Wallahi aka aura mun Dauda mutuwa zanyi," Sameeha ta dafe k'irji ta ce "Wallahi da na auri faruk gara na mutu banyi aure ba," Sabeeha ta ce "Ku kwantar da hankalin ku ba Wanda zamu aura cikin su ku zo ku ji wata magana," rad'a tayi musu aikuwa suka shek'e da dariya suka nufi gidan kamar basu da wata damuwa.



Da sallama suka shiga gidan turus suka tsaya ganin akwatuna da cofee guda shida sai bak'ake guda biyu.



K'arfin hali Sabeeha ta yi ta k'arasa tana kallon Sadam dake zaune kan tabarma sai wani hura hanci yake yi yana wani karkad'e jiki da hanky shi lallai ga d'an gayu gashi bak'i k'irin da shi da jajayen idanu gefen sa kuma Kawu ne shi da D'ansa faruk wanda Sam shi ba halinsa d'aya da Kawu ba kawai dai Sameeha bata son shi da aure ne amma shi ba ruwan sa da takura musu.



Daga d'aya gefen Kuma Mai gari ne tare da Dauda d'ansa daga can Kuma Abba ne ya yi jugum kamar Wanda aka yiwa mutuwa yana kallon ikon Allah Wai a matsayin sa na mahaifi sai dai kawai ya ga an kawo kayan lefen 'ya'yan sa ba tare da ko izinin zance ba Wanda ya zo ya nema wajensa.



Sabeeha na k'arasawa ta d'urk'usa ta gaishe su tana washe bakin da iyakar sa bakinta amsawa suka yi banda Kawu Bala da ya aika mata harara bata damu ba ta mik'e sannan ta kalli su Sabreen da suka yi mutuwar tsaye ta kanne musu ido d'aya take suma suka baje hak'ora suka k'arasa suka kwashi gaisuwa.



Kawu ya ce "Naji dad'i da ku ka zo domin ayi komai a gaban ku wad'an nan akwatunan da ku ka gani naku ne," ya nuna guda shida ya ce "wannan sune naki ki godewa Allah ki samu mai dukiya," ya fad'a yana nuna Sabeeha sannan ya ce "ku Kuma ko wacce d'ai d'ai," Mai makon ya ga sun had'e rai ko su tubure kawai sai ya ga suna ta washe baki Sabeeha ta ce "Wayyo murna yau nice da kayan aure har haka amma naji dad'i yanzu yaushe ne auren?" Shi kansa Abba mamakin su yake yi Sabreen ta ce "Nima murna nake yi," Kawu Bala kuwa had'e rai ya yi domin ba haka yaso ba domin shi burinsa ya k'untata musu amma sai ya ga sai rawar Kai suke yi ya ce "Jibi ne d'aurin auren," Sabeeha ta ce "Dan Allah Kawu a k'ara mana ko kwana biyu ne saboda mu shirya," har Kawu zai yi magana Sadam ya ce "A k'ara musu," Kawu ya ce "Shikenan nan da kwana hud'u za a d'aura auren," ana haka Lantana da Zainabu suka shiga gidan kayan suka fara bud'ewa suna kallo sai da suka gama sannan suka kalli su Sabeeha suka yi dariya suka ce "Amaren kwana hud'u," ga mamakin su suka ji 'yan uku sunce "Na'am," had'e rai Lantana ta yi bata Kuma magana ba.



Kud'i Sadam ya zaro sun Kai dubu goma ya ajiyewa Sabeeha a gaba ya ce "Ga wannan kiyi amfani dasu a shagalin biki gobe zan dawo," Sabeeha ta yi far da ido ta ce "To sai ka dawo my love," ya fita yana dashare baki.


Haka ma Dauda ya ajiyewa Sabreen dubu biyar tai ta godiya har da raka shi zaure sannan ta dawo Sameeha ma Faruk ya bata tana ta fara'a wanda faruk bai tab'a ganin ta yi ba.



Ta tafi raka shi sai da ta raka shi waje har zata koma cikin gida ya ce "Sameeha," tsayawa ta yi ya k'arasa har inda take ya ce "ki yi hak'uri nasan bakya sona nayi duk yadda zanyi Baba ya janye maganar auren nan amma yak'i," ta ce "Ya faruk kenan karka damu da kanmu zamu d'au mataki," jinjina kai ya yi ya ce "Nasan kuna hak'uri da Baba amma ku cigaba da hak'uri wata rana sai labari amma yanzu me ku ka yanke yi?" Kasancewar sun yadda da shi Sameeha ta fad'a masa ya ce "Hakan yayi yanzu bari na baku number ta duk sanda ku ke buk'atar taimakona ku samu waya ku kirani domin ni gobe zan koma makaranta," number d'insa ya bata sannan ya tafi.


Dama shi ba mazaunin k'auyen bane karatu yake yi a birni.



Komawa cikin gidan Sameeha ta yi tana shiga ta samu su Kawu sun mik'e suka fice suna fita Zainabu ta sa kuka ta ce "Baba sai da nace karka bari Waccan ta Auri Sadam ni zai aura amma kak'i yadda wallahi Kuma ni shi nake so," Kawu Bala ya ce "Haba 'yar lelena ki kwantar da hankalin ki zaki aure shi domin na riga na gama shirya hakan so nake yi sai anyi auren sannan zan k'ulla mata tugun da sai ya sake ta daga nan kuma saina ba shi auren ki Kuma Kinga munci riba biyu saboda ko ba komai kin auri Mai kud'i ita Kuma mun mayar da ita bazawara," Lantana ta ce "Gaskiya Malam kana da basira Wallahi aida na d'auka haka zaka zuba ido ta Auri mai kud'i 'yar mu kuwa ko oho," Kawu ya ce "Kema kinsan hakan bazai yuwu ba kawai yanzu lallama shi nake yi saboda yanzu naga ya gama makancewa akan waccan d'in," Haka suka yi ta kitsa yadda zasu mayar da Sabeeha bazawara.

Su kuwa bayan su Kawu sun tafi su Sabeeha suka bubbud'e kayan suka gani suna dariyar da su kad'ai suka san ma'anar ta Abba kuwa kallon su kawai yake yi ba tare da ya ce musu komai ba suma Kuma basu ce komai ba suka had'a kud'aden da aka basu suka had'a da kud'in salary d'insu da aka basu Wanda ko rabi basu tab'a ba ga kuma dubu hamsin d'in da Habibu abokin kamis ya bata.



Shigar da akwatunan d'aki suka yi sannan suka d'ora girki suka ci suka k'oshi.



Da daddare suka samu Abban su a d'aki ya yi jugum zama suka yi a gaban sa Abba ya ce "Aminaina yadda ku ka nuna farin cikin kawu lefen ku hakan ya nuna kuna son auren ko?" Sabeeha ta ce "A'a Abba dama mun yanke wata shawara ne," ya ce "Ta me?" Sabreen ta ce "Abba gaskiya ba ma son auren nan shiyasa muka yanke shawarar mubar garin har sai komai ya nitsa," Sabeeha ta ce "Eh Abba dan wallahi na tsani Sadam," Sabreen ta ce "Ai gara ke Sabeeha Wallahi," hararar wasa Sabeeha ta yi mata ta ce "Ai Wallahi da na auri Sadam gara na auri Kamis," Sameeha ta ce "Ai ni kuwa bani da case domin ya Faruk ya hak'ura," Abba ya ce "Ni yanzu damuwata ina zaku je?" Sabeeha ta ce "Abba ka kwantar da hankalin ka zamu kula da kanmu," ya ce "Na yadda daku sai dai Dan Allah karku wuce Kaduna saboda tafi kowacce state kusa damu sannan ku rik'e mutuncin ku kula da kanku," Suka ce "To Abba insha Allah,"



"To yanzu yaushe zaku tafi?" Sameeha ta ce "Zuwa jibi Abba," ya ce "Allah ya kaimu Allah ya yi muku albarka," suka amsa da "Ameen Abba,"




Washe gari da yamma suka shirya duka su Uku suka fita Kai tsaye gidan wata Mai abinci a unguwar su bayan sun gaisa suka bata dubu ashirin suka ce ta ajiye a wajen ta kullum ta dinga aikawa da Abban su abinci tunda da safe tana yi tayi da rana da daddare ma tayi.


Rok'on ta suka yi akan karta fad'awa Kawu matar ta ce "Kar ku damu zan b'oye muku sirrin ku ko dan mahaifiyar ku saboda mutuniyar kirki ce," godiya suka yi mata sannan suka tafi.


Suna fita kuwa tasha suka je suka samu mai wata mota golf suka yi magana akan gobe da asubar fari zai je ya d'auke su ya kaisu har kaduna domin basa so wani ya ga sanda zasu bar garin balle a kaiwa Kawu Bala munafunci.



Sai yamma lik'is suka koma gida girki suka yi sannan suka shiga d'akin su suka harhad'a kayansu tass suka ajiye.




Tun dare suka yi wanka suka ajiye kayan da zasu sa ranar raba dare suka yi suna fira da Abban su sannan suka sanar da shi duk abinda suka yi da suka fita yai ta sa musu albarka sannan suka tafi d'akin su suka kwanta.


Da asuba kuwa suna yin sallah suka zira dogayen rigunan su blue iri d'aya sannan suka fita waje suka samu mai motar zuwan sa kenan trolleys d'in su suka d'auka suka fita da su akasa a mota sannan suka shiga gidan d'akin Abban su suka nufa yana zaune akan sallaya yana addu'a gefen sa suka zauna suka shafa tare sannan cikin tausayin yaran nasa ya ce "Kun gama shiryawa mai motar ya zo?" Suka ce "Eh Abba," Nan ya fara yi musu Nasiha kuka kawai suke yi domin gani suke yi idan suka tafi bazasu dawo ba shima Abban hawaye yake yi ya ce "Ku tashi kuje Allah ya yi muku albarka ku yi ta addu'a nima zan taya ku Allah ya karemun ku ya d'aukaka ku," suna kuka suka ce "Ameen Abba," sannan suka rungume shi suna kuka har wajen ya raka su sannan ya ce "Ku tafi kar wani ya ganku Allah ya kiyaye," suka amsa da "Ameen," sannan Suka shiga mota Sabeeha na gaba da magen ta a hannunta Sameeha da Sabreen na bayan mota.


Haka suka tafi suna d'agawa Abba hannu kowaccen su na sharar hawaye.



Lokacin da suka isa Kaduna karfe Goma na safe tunda driver ya ajiye su suka rasa inda zasu yi ga yunwa na damunsu magen Sabeeha ma kukan yunwa take yi kifi ta siya mata ta bata taci ta k'oshi Sameeha ta ce "Sabeeha dear nifa yunwa nake ji," Sabreen ta ce "Nima haka wallahi," tashi Sabeeha ta yi ta tari Mai keke napep ya ce "Ina za a kaiku?" Sabeeha ta ce "Wallahi yayana mu ba 'yan gari bane dan Allah so muke ka

Please Login or Register in order to submit comment