Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba a hankali ya taka wajen ta ya haye gadon daf da ita yana kallon ta ya ce "Sannu baby kin tashi?" Gyad'a kanta ta yi kamar an tsikare ta ta ce "Wai My d'azu da Ummi ta kore ka a asibiti ina kaje?" Hararar wasa ya yi mata saboda tuna masa da tayi ya ce "Waya naje nayi da budurwata a mota," take had'e fuska har k'walla na had'ar mata a fararen idanunta ta kawar da kanta gefe "Baby," ya Kira ta amma bata kalle shi ba sai ma hawayen da ya zubo mata.



Ummi ce ta shiga d'akin kallon Sabeeha ta yi sannan ta kalli Maleek cikin had'e fuska ta ce "Zuwa kayi ka dame ta ko oya fitar mun a nan," tura baki ya yi k'asa-k'asa ya yi magana yadda Sabeeha ce Kawai zata ji shi ya ce "Ki ka bari Ummi ta sake korata wayar zanje na sake yi da Surayya," daram gaban Sabeeha ya fad'i ta kalli Ummi ta ce "Ummi ki kyale shi kawai,"



"Ok kaci darajar daughter," Ummi ta fad'a tare da barin d'akin tana fita Sabeeha tasa bayan hannunta tana goge hawayen da ya b'ata mata fuska.



Cikin k'asa da muryar cikin sigar rarrashi yasa hannun sa ya juyo da fuskar ta suna facing juna ya ce "Is okay ya isa uhm ni wasa nake yi miki da kika sa aka koreni wajen Mama na tafi muka yi fira," ajiyar zuciya ta sauke shi kuma ya rungume ta a k'irjin sa yana jin wutar sonta na k'ara ruruwa a zuciyar sa ita kuwa luf ta yi a jikin sa domin tana jin dad'in d'umin jikin sa a hankali ya ce "Ya jikin naki?"



"Ya warke fa yanzu ba inda ke mun ciwo," ta fad'a tana zagaya hannunta a bayan sa murmushi ya yi tare da bata kiss a goshin ta ya ce "Masha Allah kenan yanzu zamu iya k'ara yi?" Ya fad'a yana kallon cikin idanunta.




Harara ta aika masa ta ce "Idan kashe ni kake son yi ba to ni ban warke ba," ta fad'a tana jamewa ta d'ora kanta a cinyar sa dariya ya yi tare da yin wasa da gashin ta.




Wayar sa ce ta fara ringing cikin wani sauti mai dad'in gaske d'aukar wayar ya yi ba tare da ya yi magana ba can ya ce "Okay ba damuwa gani nan zuwa," daga haka ya katse kiran.



"My Ina zaka?" Juya idanu ya yi ya ce "Zani wani waje amma yanzu zan dawo ki shirya saboda za ayi wani taro yanzu saboda mu kingane?" Gyad'a kai ta yi sannan ya manna mata kiss ya fita da ido ta bishi tana jin soyayyar sa na ratsa ta.



Yana fita compound d'in gidan ya samu su Salman sai gyara wurin da za ayi taron suke yi suna ganinsa suka taso d'aga musu hannu ya yi kamar baya son magana ya ce "Ku cigaba da aikin ku zani ni d'aya," yana fad'ar haka ya fad'a mota ya jata yabar gidan.





Hotel d'in yaje suka d'anyi tsare-tsare sannan ya koma gida part d'in Ummi ya shiga ya tarar sai hidima ake yi Ummi ya hanga ta nufi stairs wajen ta ya nufa ya ce "Ummi ga wannan kayan su Baby zata sa," kallon kayan ta yi na sojoji ne ta karb'a ta ce "Amma ai kasan bata da lafiya ko ba lallai ta iya zuwa,"



"No Ummi tace ta warke fa zata iya zuwa,"



"Shikenan bari naje amma fa idan tace bazata iya ba bazata fito ba," Ummi ta fad'a tare da haurawa stairs shi kuma ya juya ya fita.


Ummi na shiga d'akin ta samu Sabeeha ta fito daga wanka sai dai har lokacin tafiyar ta bata dawo daidai ba k'arasawa ciki Ummi ta yi ta ajiye kayan saman gado ta ce "Idan kin shirya wannan kayan Zaki sa saboda taron da za ayi," kallon kayan Sabeeha ta yi ta ce "Toh,"




"Zaki iya ai ko?" Ummi ta tambaya gyad'a kai kawai Sabeeha ta yi "To Bari na aika a d'auko mai make up tayi miki," Ummi na fad'ar haka ta fita.



Zama gefen gadon ta yi wayar Ummi dake ringing Sabeeha ta kalla Daughter ta gani rubuce a screen d'in d'auka ta yi tare da sallama "Sabeeha dear," Sabreen ta fad'a cikin farin ciki "Na'am sweetheart," Sabeeha ta fad'a tana murmushi.




"Lafiya kike kuwa naji muryar ki haka ko da yake dama haka ya kamata naji ki kasancewar ki sabuwar amarya saboda ehem kinsan kuwa hmm bari dai nayi shiru," Sabeeha da tunda ta fara magana take murmushi ta ce "Allah ya shirye ki amma dai zaku zo?"



"Eh muna nan muna shiri yanzu muka gama magana da Sameeha dear ma itama shirin suke yi," Sabeeha ta ce "Ok sai kun shigo daga haka ta katse Kiran," har zata ajiye wayar sai kuma ta Kira Doctor.




"Hello Aysha," Doctor ta fad'a "Ni ce Mama Ina wuni?" Sabeeha ta fad'a Doctor ta ce "Lafiya lau 'yar rigimata ya jikin?" Cikin jin kunya ta ce "Da sauk'i Mama amma ai zaku zo ko?"



"Me ake yi?" Doctor ta tambaya "Taro zasu yi ne Ummi please kizo Ummi tace zaku zo ai," shiru Doctor ta yi ko shine taron da Ummi ke fad'a Mata a asibiti sai ta ce "To shikenan zamu zo,"



"To sai kun zo," tana fad'ar haka ta katse Kiran Ummi ce ta shigo tare da me make up ba b'ata lokaci aka fara ranga'awa Sabeeha Kwalliya yayinda take jiyo jiniya na cika gidan.



Lokaci kad'an aka gama tsantsara mata kwalliya Mai masifar kyau eyelashes ne kawai tace kar asa mata itama mai kwalliyar bata yi tunanin sa mata ba saboda tana da gashin ido sosai wani ma sai yace eyelashes d'in tasa irin dogayen nan taje mata shi da mascara kawai akayi.



Kayan sojojin tasa wad'an da suka yi Mata matuk'ar kyau gasu cif daidai jikin ta tana gama sawa make over d'in a zuciyar ta ta ce Masha Allah, Allah yayi halitta a nan ga kyau ga sura.



Tana gama sa kayan ta koma ta zauna make over d'in ta fara gyara mata gashinta inda yasha mayuka sai kyalli yake yi aka d'aure mata wani a tsakiyar kanta cikin milk and army green d'in ribboms aka sake shi har gadon bayan ta sannan aka zubo mata da wani ta gaban goshin ta aka lank'wasa shi aka had'e dana bayan sannan aka sa mata wata hula army green mai kyau mai wasu kunnuwa biyu a gaba yayinda tsakiyar kan yake a bud'e domin band ce hular gashin gaban goshinta ya kwanta luf luf a gwanin sha'awa.




Sannan tasa wani hill d'in takalmi army green wayyo ba k'aramun mugun kyau tayi ba kamar ka sace ta ka gudu kayan zuwa kwalliyar sunyi mata azababben kyau kamar 'yar baby turaruka ta fesa masu dad'in k'amshi ita kanta tsayawa kallon Sabeeha ta yi ta ce "Masha Allah kinyi kyau," Sabeeha ta ce "Nagode," sannan ta juya ta kalli mirror itama tsayawa kallon kanta ta yi saboda tunda aka fara shagalin bikin su zata iya cewa bata yi kyau ba kamar yau ba hatta d'an kunnen ta army green ne da agogon ta.




Ummi ce ta shiga d'akin tasha kwalliya cikin wani less milk tayi kyau tana ganin Sabeeha ta ce "Masha Allah daughter na kinyi kyau sosai," murmushi Sabeeha ta yi ta ce "Nagode Ummina,"



Kallon make over d'in Ummi ta yi ta ce "Nawa ne kud'in ki," ta ce "Dubu d'ari ne hajiya," Ummi ta ce "Gaskiya yadda kika fito mun da daughter na haka zan biyaki dubu d'ari biyar," nan ta fara godiya sannan Ummi ta fita daga d'akin.



Ummi na fita ba dad'ewa Maleek ya shiga d'akin cikin uniform d'insa na sojoji da a kullum yasa su kamar k'ara masa kyau ake yi yasha kyau gashin kansa sai walwali yake yi ga askin dake kansa da k'ara masa kyau sosai sai tashin k'amshi yake yi.



Sallamar sa ce tasa Sabeeha waigawa ta kalle shi sai da numfashin sa ya d'auke na wasu seconds saboda tsabar kyan da ya ga ta yi a zuciyar sa sai hamdala yake yi da ya same ta matsayin abokiyar rayuwa itama kallon sa take yi yadda ya yi kyakkyawan kyau.



Make over dake zaune kallon Maleek ta yi a zuciyar ta ta ce haba dama wannan falleliyar ai sai wannan had'adden guy d'in gaskiya sunyi matching gaskiya za a ga yara a nan wai kallon da Maleek ya yi Mata ne yasa ta mik'e ta fita tana waigen su.





A hankali ya k'arasa gaban ta ya mik'ar da ita Yana kallon cikin idanunta sannan ya rungume ta a tare suka saki ajiyar zuciya.



"Kinyi kyau sosai Baby," murmushi ta yi sannan ta d'aga kanta tana kallon fuskar sa kasancewar ya fita tsayi ta ce "Kai ma kayi kyau My," murmushin ya yi dimples d'insa suka lotsa hannu ta Kai ta tab'a wajen ta ce "Bani d'aya My," dariya ya yi ya ce "Ai wannan ma naki ne amma zan bawa yaro ko yarinyar da zamu haifa," dariya tayi wayar sa ya zaro ya fara rangad'a musu hotuna.




Suna rungume da juna Ummi ta fito ta ce "Son ku fito time na tafiya mutane sun taru fa," jan hannun Sabeeha ya yi suka fita.




Tunda suka fara sauka stairs idanun mutane ya yi kansu iPhones kawai ke tashi a wajen ana yi musu hotuna kowa na fad'in sun dace a haka suka k'arasa sauka.



Aisa ta k'arasa gaban su ta rungume Sabeeha ta ce "Masha Allah Daughter kinyi kyau," ta ce "Nagode Momma," su Hany Hanfa da Rinaz sai hotuna suke musu har su Ashraf Alim da su Muhsin da Aiman da suka shiga falon sai pictures suke musu domin sun burge kowa.




Daidai lokacin Sabreen da Fauwaz suka shiga falon sunyi kyau ash shadda Fauwaz yasa Sabreen kuwa Ash less tasa Mai adon silver sunyi kyau ba k'arya daga bayan su Kuma Umar da Sameeha ne suma sunyi anko Umar cikin bak'ar shadda yayi kyau Sameeha Kuma bak'in less sunyi kyau sosai Sabeeha na ganin su ta cika da farin ciki.




Rungume ta Sabreen ta yi ta kalli fuskar ta ta ce "Wayyo dear Kinga yadda ki ka yi mugun kyau Wallahi kin had'u ba k'arya," dariya Sabeeha ta yi ta ce "Thank you dear," sannan ta rungume Sameeha ta ce "I miss you sis,"



"Same here dear kinyi kyau," Sabeeha ta ce "Thanks," sannan suka gaisa da su Fauwaz nan aka cigaba da hotuna su Dija ma sunje cikin ankon su dark blue material irin na jikin su Rinaz.





Su Mama da Lantana da Zainabu tare da sauran dangi sunje Mama kuwa anko suka yi da Ummi Aikuwa sunsha pics 'yan uku kuwa sai murnar ganin juna da Doctor suke.




Da haka mutane kowa ya fita wajen taron banda su Maleek sai can sannan suka fita suna fita sojojin da suka yi layuka biyu sai hanyar da suka bayar a tsakiya suka sarawa su Maleek da Sabeeha ga masu video da hotuna na aikin su domin tunda aka fara bikin kullum sai sunje.



Maleek rik'e da hannun Sabeeha suka fara tafiya akan carpet d'in dake shimfid'e a wajen kalar army green a hankali Sabeeha ke tafiya saboda har lokacin tafiyar ta bata dawo daidai ba Wanda a zahiri tafiyar ta bada style.



Yana rik'e da hannunta suka k'arasa gaban wani dogon table inda manyan sojojin da suka dira a yau suke zaune cikin uniform a tare Maleek da Sabeeha suka sara musu gurin ya d'auki tafi sannan suka k'arasa wajen da Daddy tare da Abba ke zaune da Kuma Kawu Uncle kuwa yabar k'asar ma.



Sabeeha kuwa cikin mamaki take kallon Abban su dama har da shi ko da yake ai taron bana yara bane bayan sun gaishe su suka tafi wajen da aka tana da domin su suka zauna.




Table d'in yasha lemuka iri iri da snacks da Kuma fruits plate-plate.




Ba b'ata lokaci aka fara gabatar da program d'in bayan manyan wajen sun yiwa ango da amarya fatan zama lafiya da yara na gari aka fara parate Wanda ya k'ayatar da mutane 'yan gidan televisions sai aikin su suke yi hakama masu hoto bayan sun gama sannan aka fara bawa amarya da ango gifts Wanda basu san adadin kud'i da motoci da gidajen da suka samu ba daga manyan ma'aikata abokan Daddy da suka je wajen ba da Kuma manyan sojojin da suka halacci taron ba harma da k'awayen Ummi da Doctor da Abokan Abba Kai sun kwashi dukiya ba kad'an ba.



Su dai sai aikin godiya suke yi ga wata kulawa da suke bawa juna musamman Maleek da duk juyin da Sabeeha zata yi a idon sa mutanen wajen ma sun lura soyayya ce me k'arfi tsakanin su.



Microphone aka bawa Maleek domin jin me zai ce karb'a ya yi ya mik'e tsaye cikin salon sa da sweet voice d'in sa ya yi sallama ya ce "All praise be to Allah subhanahu wata ala really I don't have any word that show you my happiness to everybody here I'm really appreciated then I wish all of you here to go back safely and thanks for attending this program thank u once again our soldiers wish u a safe journey," kallon Sabeeha ya yi kallo mai cike da so da k'auna ya ce "I really thanks Allah for special gift that he has given to me Rukayya u are special gift from Allah so I promise to take care of you like baby and I promise support you my lovely wife," murmushi kawai Sabeeha ke yi ga hawayen da ya taho mata ya Mai da kallon sa ga mutane ya ce "thank you once agains," tafi wajen ya d'auka.



Kallon Sabeeha ya yi ya mik'ar da ita tsaye ya k'ara mata microphone d'in a bakinta a hankali ya ce "Say something dear," murmushi ta yi sannan cikin sassanyar muryar ta ta yi sallama ta ce "As my lovely husband say we thank to almighty Allah countlessly and everyone here thanks for your love our soldiers and our parents thank for ur supporting," tafi wajen ya d'auka sannan ta kalli Maleek ta ce "Let me use this opportunity to give a special thank to my hero my husband my happiness I love you more and more thank u for ur supporting then me too I promise to love u i promise to respect u in every condition," ta fad'a hawaye na zuba a idanunta hannu yasa yana share mata sannan ya rungume ta suna jin wani sanyi na ratsa su tafi aka dinga yi musu da hotuna.



Da haka aka rufe taro da Addu'a cak Maleek ya d'auki Sabeeha duk da mutanen dake gurin ya nufi cikin gida da ita a kan gadon Ummi ya ajiye ta sannan ya ce "Baby bari naje na raka bak'i airport ko?" Mak'e kafad'a ta yi ta ce "Uhm uhm sai dai muje tare nima ai bak'i na ne,"




Zare ido ya yi ya ce "No baby stay here yanzu zan dawo fa," kukan shagwab'a tasa masa dole haka ya rik'e hannun ta suka fita suka aka bud'e musu bayan mota suka shiga suka nufi airport jiniya kawai ke tashi a garin wajen motoci talatin sukayi a haka suka k'arasa airport soldiers d'in suka su Kuma suka juya zuwa mota duk inda suka gilma sai an kalle su suka koma gida tare da sojojin Maleek d'in.
[10/25, 8:52 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️





RUBUTAWA DAGA
HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ)






SADAUKARWA GA
MY DAUGHTER SABEEHA
BILKISU Z.YA'U (🅱️K)
AISHA MAGAJI DABO (AMA)




Page 28


Suna zuwa gida ana gama yin parking ya d'auke ta cak zuwa cikin part d'in Ummi bai damu da mutanen dake falon ba ya wuce Kai tsaye zuwa stairs.




Sabeeha kuwa tuni ta b'oye fuskar ta a k'irjin sa saboda ganin su Mama da Ummi da Kuma Hajiya da ta yi ga su Sameeha da Sabreen da su Rinaz duk a falon.


Zainabu kuwa idon ta kamar ya fad'i k'asa saboda kallo haka ma Lantana.





Yana shiga d'akin Ummi ya zaunar da ita gefen gado "To sarkin jin kunya bud'e idon mun shigo d'aki," bud'e idon ta tayi tana yin murmushi.



Ummi ce ta shiga d'akin tana yiwa Maleek hararar wasa dariya ya yi ta ce "Gaba d'aya kai ka zama mara kunya ko?"



"Ummi ai ban jin kunya indai akan baby ne," girgiza Kai ta yi tare da fad'in "Kai ni bani waje ba wajen ka nazo ba," ta fad'a tare da k'arasawa wajen Sabeeha dake yiwa Maleek gwalo shi Kuma sai cika yake yana batsewa.




"Yawwa Daughter bari na had'a miki ruwan wanka ko," kafin Sabeeha tayi magana Ummi ta shige toilet d'in ta had'a mata ruwan wanka da yasha kayan k'amshi da kayan gyara ta fito ta tana fad'in "Tashi kiyi wankan," daga haka ta fice.



Tashi tsaye Sabeeha ta yi ta fara b'alle bottles d'in shirt d'in rigar sojojin dake jikin ta saurin rik'e hannunta Maleek ya yi sannan ya fara b'alle mata da kansa sai da ya gama sannan ta cire rigar saura farar t_shirt d'in ciki kawai ya Kai hannu zai cire mata tayi saurin rik'e hannunsa tana girgiza Kai "Ni ka kyale mun zan cire da kaina,"



"Ni kam bazan bari ba ni ne zan cire miki," shagwab'e fuska ta yi ta ce "Dagaske fa zan cire," shima ya ce "Uhm uhm fa ni zan cire miki," d'an juya idanu ta yi ta ce "Laa My kaji Ummi na Kiran ka," dariya ya yi ganin wai Sabeeha ce zata yi masa wayo ya ce "Ni banji ba,"




Jan hannunsa hanyar k'ofa ta yi ta ce "To zo muje kaji," suna zuwa k'ofar ta bud'e tana rik'e da hannunsa suna fita ta zare hannunta ta koma cikin d'akin da gudu tasa key.



Dariya Maleek ya yi tare da girgiza Kai sannan ya nufi down stairs.



Yana fita su Sabreen suka tashi da sauri suka nufi stairs domin tun shigowar su part d'in suke so su je su gana da 'yar uwar su amma Mama ta hana su ganin Maleek na d'akin.


Sabeeha na wanka ta ji ana knocking ta jima sannan ta fito d'aure da towel ta bud'e musu k'ofar ganin su yasa ta sakar musu murmushi sannan ta nufi gaban mirrow ta zauna tare da fad'in "Sabreen dear dan Allah ki Kira Rinaz ta waya kice ta kawomun kaya,"




Sabreen bata ce komai ba sai da ta Kira Rinaz d'in bayan ta sanar mata sannan ta kalli Sabeeha ta ce "Dear wankan na meye?" Ta fad'a cikin sigar tsokana murmushi Sabeeha ta yi ta ce "Na shiga turakar miji ne," sai Kuma dukan su suka tuntsire da dariya.


"Wallahi sister abun nan da wuya yaseen," dariya Sabeeha ta yi sannan ta ce "Ai garama ke sis Wallahi," Sameeha kuwa tsuru-tsuru ta yi da ido bata ce komai ba domin ita maganar su ma ta gama tsorata ta "Ke Sameeha dear yadai?" Sabreen ta fad'a tare da kallon Sameeha itama Sabeeha ita take kallo.




"Dan Allah sisters da wuya?" Sameeha ta fad'a idanunta taf k'walla "Bangane da wuya ba kina nufin Wai jiya ba abinda ya faru?" Sabreen ta tambaya cike da mamaki.




"Amma dear jiya da zazzab'i na kwana fa," cewar Sameeha har Sabreen zata yi magana Sabeeha ta rigata da cewa "Kinga manta sister ba wani wuya," ajiyar zuciya Sameeha ta sauke Sabeeha kuma ta cigaba da tufke gashin ta da ribbom.





Rinaz ce ta shiga d'akin da kaya a hannunta a kan gado ta ajiye tare da fad'in "Sabeeha dear ga kayan," tana fad'in haka ta fice tana dariya k'asa-k'asa.



Bin k'ofar da kallo Sabeeha ta yi sannan ta d'auki kayan ta bud'e zare ido Sabeeha ta yi ta ce "Me Rinaz habibty ta mayar dani da zansa wannan rigar," ta fad'a tana d'aga rigar da idan tasa baifi iya gwiwa ba gashi rigar d'aya dogon hannu ne d'ayan Kuma siriri sannan bayan rigar a wawake yake sai igiyoyin d'aurewa rigar dark blue ce sai wasu duwatsu masu kyalli daga saman rigar.




Jefar da rigar saman gado Sabeeha ta yi tana tura baki ta ce "Ni dai kam gaskiya bazan sa wannan arniyar rigar ba," dariya Sabreen tasa ta ce "Amma fa rigar ta yi kyau fa sosai dear to meye matsalar da baza ki saka ba?"




"Haba dear har yaushe na zama mara kunyar da zan saka wannan rigar Kuma a part d'in Ummi haba mana sis,"



"Sabeeha dear da rigima kike Wallahi to kisa mana sai kisa hijabi," Sameeha ta fad'a ita dai shiru ta yi ba kuma alamun zata sa rigar sai ma d'auko hijabi da tayi tasa ka ta zauna suka d'ora da fira har magriba lokacin suna d'aki suna fira har su Doctor sun tafi basu saniba.




Sallah suka yi suna zama aka k'wank'wasa k'ofar d'akin k'amshin turaren Umar kawai Sameeha ta ji da sauri ta mik'e ta yi hanyar toilet tana cewa "Dan Allah kuce mishi bana nan wallahi tsoron binsa nake yi," kafin su yi magana har ta sige ta tura k'ofar.



Sabeeha ce ta ce "Shigo," tura k'ofar d'akin ya yi ya shiga suka gaisa da su Sabeeha sannan ya ce "Sisters Meeha fa?" Da sauri Sabreen ta ce "Tana ciki wai gudar maka tayi," dariya ya yi sannan ya k'arasa k'ofar toile d'in ya murd'a handle d'in k'ofar a bud'e take ya rik'o hannunta ya fito da ita yana fad'in "Meeha meye na gudun taho mu tafi gida ko?" Shiru Sameeha ta yi sai raba idanu da take yi.



"Sabreen sister Sabeeha dear sai da safe," Sameeha ta fad'a "To asuba ta gari dear," cewar Sabreen girgiza Kai Sabeeha ta yi ta ce "Sannu fa," Ummi ce ta shiga d'akin tana fad'in "Wai me ku ka zauna yi a bedroom har yanzu kofa abinci baku ci ba,"




Sabreen ta ce "A'a Ummi ni da Sameeha dear munci d'azu wajen taro Sabeeha Sister ce Kawai bata ci ba," Fauwaz da sigowar sa kenan ya ce "My love an gama firar haka ki taho mu tafi," tashi Sabreen ta yi ta ce "Ok muje my heart Ummi dear sai da safe," ta fad'a tare da bin bayan Fauwaz.



Kallon Sabeeha Ummi ta yi ta ce "Daughter bari na kawo Miki abinci," bata jira cewar ta ba ta fita bata dad'e ba sai gata da ture Mai d'auke da flask d'in abinci da drinks ta ajiye a kan k'aramun table d'in dake d'akin ta zuba mata jallop d'in shinkafar da coslow a plate sai peppe chicken.





Daidai lokacin Maleek ya shiga d'akin sai bulbula k'amshi yake yi ga wani kyau da ya yi ciki k'ananun kaya blue black trouser da white riga ya yi kyau sai wata blue black da ya d'ora a sama Mai kamar ta sanyi domin iska ake a garin ga Kuma hadari ya had'o a garin.





Tunda suka amsa sallamar sa idanunsa na kan Sabeeha kusa da ita ya zauna sannan ya karb'i plate d'in hannun Ummi da take mik'awa Sabeeha ya ce "Ummi kawo na bata," Ummi bata ce komai ba ta bashi sannan ta bar musu d'akin tana fita Maleek ya d'ebi abincin a spoon ya ce "Oya bud'e bakin baby," ba musu ta bud'e ya fara bata har sai da ta k'oshi sannan ya ajiye ya bata ruwa ta sha.





"Baby taso mu tafi," shagwab'e fuska ta yi ta ce "To ba ba kayana a nan ba," ta fad'a kamar zata yi masa kuka "Wannan fa baby?" Ya fad'a yana kallon rigar dake gefen ta ta ce "Wai fa Rinaz habibty nace ta kawo mun kaya shine ta kawomun wannan rigar kumama ni baran iya sawa ba," murmushi ya yi tare da d'aga rigar ya ce "Wow baby rigar tayi mun kyau kisa please," d'an shiru ta yi sannan ta ce "To zansa but sai ka fita sannan," d'an zare ido ya yi ya ce "Haka fa d'azu ki ka kore ni dan haka yanzu ba inda zani," ya fad'a yana wani had'e rai ita dariya ma ya bata ta dake ta ce "Ok shikenan Bari naje bathroom nasa," ta fad'a tare da mik'ewa shima mik'ewar ya yi ya rik'e ta ya ce "Ba fa inda zaki kawo rigar nasa Miki," bai jira cewar ta ba ya amshi rigar ya fara k'ok'arin cire mata dogon hijabin jikin ta.




Rintse idanu kawai ta yi domin bata so su cigaba da sa'in sa tana ji ya zare mata towel d'in jikin ta yana k'arewa surar ta kallo jin shiru baisa mata rigar bane yasa ta tura baki tana bubbuga k'afa cikin shagwab'a

Please Login or Register in order to submit comment