Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta ce "Ni dai kayi sauri ka samun fa Ina so na bud'e idona," ajiyar zuciya ya sauke ganin yadda duk jikin ta ke motsawa saboda buga k'afar da take yi sannan ya sa mata rigar.



Yana gama sa mata ya ce "Wow u are so cute baby looking so amazing my wife," ya fad'a tare da yi Mata wata kyakkyawar runguma ya ce "Oya open your eyes cutie look at ur husband," a hankali ta fara bud'e kyawawan idanunta masu d'auke da zara-zaran eyelashes ta kalle shi shafa sumar kanta ya yi ya ce "Muje ko," ya fad'a tare da sa mata hijabi tasa takalmi suka fita daga part d'in ba tare da sun yiwa Ummi sallama ba.



Bud'e musu mota aka yi ya shiga driver seat ita kuma front seat ya jasu suka tafi direct d'ayan part d'insa shi kad'ai ya nufa bata ce da shi komai ba suna shiga falon Sabeeha ta baje saman kujera Maleek Kuma ya haura stairs yana fad'in "Time d'in sallah ya yi bari naje nayi alwala na wuce masjid," noding kanta kawai ta yi.





Tana zaune har ya fito ya tafi masallaci har ya dawo tana wajen sai dai har ta fara bacci d'aukar ta ya yi ya nufi bedroom da ita ya kwantar da ita tare da zare mata hijabin yana binta da wani irin kallo cire shirt d'in jikin sa ya yi wayar sa ce ta fara ringing ya d'aga daga can Ummi ta ce "Wato shine ka ja daughter ku ka tafi ko to zo ka amsar mata maganinta sannan kar a sake a sake maimata irin ta jiya a barmun daughter ta huta," tana fad'ar ta katse wayar shi Kuma ya nufi k'ofar fita.





Yana fita babu dad'ewa Sabeeha ta tashi domin ita idan har bata yi sallah ba bata iya bacci sai kawai ta d'auro alwala ta shiga dressing room d'insa ta d'auki wani wando robber tasa tayi sallah sannan ta mayar masa ta koma ta kwanta domin baccin da take ji.




Ko da ya dawo ya samu har bacci ya fara d'aukar ta fara Kiran ta ya yi "Baby ki tashi Kisha magani," ai jin an ambaci magani yasa ta k'ara rintse idanunta kamar wacce bacci Mai nauyi ya yi gabas da ita.




"Idan fa baki tashi ba ko yaseen sai nace sai nayi irin ta jiya," kafin ya k'arasa har ta mik'e zaune tana tura masa baki baice komai ba sai maganin da ya bata tasha sannan ya mik'e ya shiga bathroom ya yi wanka sai da ya gama Shirin sa ya feshe jikin sa da turare sannan ya kwanta kusa da ita ya jawota jikin sa ya rungume k'ara mak'alk'ale shi ta yi domin tana jin dad'in jinta a jikin sa sosai a haka bacci ya kwashe su.





Sameeha kuwa duk zillewar ta sai da taba Umar hakk'in sa tab aikuwa langwai ta dinga yi masa Yana aikin rarrashi.



Tom haka dai rayuwar su ta cigaba da kasancewa cikin farin ciki da k'aunar junan su har aka yi sati biyu da bikin.



Sabeeha ce zaune akan kujera a babban falon part d'in su riga da wando ne a jikin ta duk pink ta yi kyau har ta gaji ta kitse gashin ta a gefe kanta apple take ci sai earphone da tasa tana sauraro wak'ar jaywillz (medicine) gyad'a kai take yi a hankali domin wak'ar tayi mata dad'i sosai.




Maleek ne ke saukowa daga stairs yaci gayu sosai cikin wata maroon shadda ba k'arya sai Nasreen dake bayan sa domin daga d'akin ta ya fito tana biye da shi har suka k'arasa cikin falon.




Tunda suka k'arasa falon idanunsa ke kan Sabeeha da Sarai taji takun tafiyar su sai dai bata kalli inda suke ba b'ata san dalilin da yasa take jin ba dad'i ba duk sanda Maleek ya kwana a d'akin Nasreen ba gashi Nasreen d'in duk sanda ya kwana d'akin ta ta dinga iyayi kenan duk sanda ya fita haka zata je wajen da Sabeeha ke zaune tana fad'in "Wash Amma yau ya Maleek ya wahalar dani sai dai ya lashi zumar da bai samu ba wajen wata ya fad'amun cewar Yana jin dad'i na sab'anin wata," haka zatai ta magana tun abin na damun Sabeeha har ta dena damuwa domin ita Sam ba mai son rigima bace.




Zama kusa da ita Maleek ya yi ya zare mata earphone d'in dake kunnen ta had'e da fad'in "Baby baki ga mijin ki bane," murmushi ta sakar masa ta ce "Ina kwana,"


"Lafiya cutie," ya fad'a tare da karb'ar apple na hannunta ya fara ci Nasreen dake gefe a tsaye ta cika tayi fam kallon ta Sabeeha ta yi ta ce "Ina kwana," tsaki Nasreen ta ja bata amsa ba Sabeeha bata damu ba domin dama duk sanda zata gaishe ta bata amsawa.


"Baby zan fita saina dawo,"

"Amma My ai baka yi breakfast ba," Sabeeha ta fad'a tana kallon cikin idanunsa juya idanunsa ya yi ya ce "To baby ya zanyi bayan ba a bani ba zanje wajen Ummi nayi before na fita amma ki dafa mun abinci idan zan dawo," ta ce "Ok shikenan," kiss ya bata a check d'in ta sannan ya mik'e saurin sha gaban sa Nasreen ta yi ta ce "Bangane tayi maka abinci ba ai ba girkin ta bane,"



"D'an bani hanya mana nifa kinsan bazan ci abincin ki ba domin baki iya ba tun farko ke kika yiwa kanki da baki tsaya kin koya ba," yana fad'ar haka ya matsar da ita gefe ya fice.



Nasreen ta ce "To munafuka Wallahi sai kin bar nan gidan sannan idan har kin isa na ganki kina yi masa girkin," ko kallon ta Sabeeha bata yi ba ta mik'e ta nufi hanyar stairs tabar banza a wajen.





Tsaki Nasreen ta ja sannan ta zauna akan kujera ta zabga tagumi sai Kuma ta fashe da kuka sai da ta gama kukan ta sannan ta mik'e ta shige bedroom d'in ta.




Sabeeha kuwa tana shiga d'akin ta ta zauna gefen gado ta Kira Sabreen suka yi firar su sannan ta tashi ta d'auki dogon Hijabi tasa ta d'auki wayar ta ta fice ko da ta fita falo bata samu Nasreen ba sai kawai ta fita.





Tana fita driver tasa ya kaita har k'ofar part d'in Ummi da sallama ta shiga falon Ummi kad'ai ta samu a falon kasancewar weekend ne bata fita office ba Daddy kuwa tun bayan biki ya koma Dubai Rinaz Kuma ta tafi karatu India dan Daddy cewa ya yi dole ne ta tafi makaranta tana kuka tana komai haka ta shirya ta tafi.


A k'asan carpet ta zauna ta gaida Ummi cikin fara'a Ummi ta amsa ta ce "Daughter kin tashi lafiya?"


"Lafiya lau Ummi," Sabeeha ta fad'a tare da mik'ewa ta nufi kitchen tana fad'in "Ummi bari naje kitchen d'in ki yunwa nake ji," ta fad'a tare da shigewa cikin kitchen d'in ta samu kuwa akwai abubuwan ci kala kala zubawa ta yi ta fita falo ta zauna ta fara ci sai da ta k'oshi sannan ta mayar da plate d'in kitchen ta fito suka yi ta fira da Ummi har Fauwaz ya shiga ya same su gaisawa suka yi sannan ya zauna aka cigaba da firar da shi.


Sai yamma sannan Sabeeha ta yiwa Ummi sallama ta tafi tana shiga part d'in su ta samu Nasreen a zaune kan kujera 'yan aiki zagaye da ita sai wani karkad'a k'afa take yi kallo d'aya Sabeeha ta yi Mata ta d'auke Kai ta nufi stairs.




Tana shiga d'aki hijabin ta kawai ta ajiye tana zama ta tuna da girkin da Maleek yace tayi masa da sauri ta mik'e daidai lokacin wayar ta ta fara ringing ko ba a fad'a Mata ba tasan shine domin ring tone d'in sa daban ne d'aukar wayar ta yi sannan ta nufi kitchen tana cewa "Hello my,"




Daga can ya ce "Wato Baby ni kika manta ko?" Ya fad'a kamar wani k'aramin yaro mai shirin kuka "Ayyah sorry My ina wajen Ummi ne shiyasa,"



"Ohk kina wajen Ummi shiyasa ki ka manta dani ba?" Zare ido ta yi ta ce "No ba haka bane kasan dai bazan manta da Kai ba koh ayimun afuwa," ta fad'a tana sakin murmushi.



D'an shiru ya yi sannan ya ce "Shikenan an hak'uran Miki amma idan ki ka k'ara fa?" Wannan karon dariya tayi ta ce "Sai a yafe mun," shima dariyar ya yi ya ce "Zaki yi bayani ne yarinya," haka suka cigaba da yin waya tana yin aikin ta yana jinta sannan suka yi sallama ta ajiye wayar ta cigaba da aikin ta.


Sai da ta gama tas sannan ta jera komai a daining d'in dake falon ta ta fad'a toilet tayi wanka tare da alwalar sallar magrib tana fitowa ta shafa mai ta zira wata rigar atamfa bak'a ce atamfar sai ratsin ja a jiki hijabi ta saka tayi sallah sannan ta zauna d'auki k'aramun veil ta yafa a kanta ta fita falo ta zauna tare da kunna TV.



Jin k'arar bud'e gate ne yasa ta gane Maleek ya dawo bata motsa ba domin tasan ba girkin ta bane bare taje tarar sa cigaba da shafa jikin pretty tayi wacce tayi b'ulb'ul kamar ka sace ta ka gudu.



Maleek kuwa da sallama ya shiga falon ko amsawa Nasreen bata yi ba sai zuwa da tayi cikin iyayi tana niyyar rungumar sa hararar da ya aika mata ce yasa ta tsaya ya yi Mata kallon up and down ya wuce zuwa cikin d'akin sa.



Wanka ya yi yana cikin shiryawa Nasreen ta shiga d'akin ko kallo bata ishe shi ba ya fesa perfumes a jikin sa wayar sa ce ta fara ringing ganin Mai Kira yasa shi sakin murmushi ya d'aga daga can Sabeeha ta ce "Na kawo ma abincin nan?" Ya ce "No gani nan zuwa a gurin ki zanci," daga haka ya kashe kiran ya nufi hanyar fita da kallo Nasreen ta bisa har ya fice.


Da sallama ya shiga falon ta da tun kafin ya k'arasa shiga k'amshin sa ya daki hancin sa amsa sallamar Sabeeha ta yi sannan ta tashi a hankali ta isa gare shi ya bud'e mata hannu ta fad'a jikin sa ya rungume ta ta ce "Sannu da dawowa,"


"Yawwa Sabee na," ya fad'a tare da jan hannunta zuwa cikin falon yana fad'in "Baby yunwa," har daining suka k'arasa tayi saving d'in sa abinci ta tura masa plate d'in gaban sa sai ta ga ko kallon abincin bai yi ba ta ce "Yadai my kace kana jin yunwa ga abincin nan," hararar wasa ya yi mata yana niyyar mik'ewa zare ido tayi ta ce "Sorry my zauna na manta," zaman ya yi ta fara feeding d'in sa abincin har ya k'oshi sannan shima ya bata har ta k'oshi sannan suka koma cikin falon ya zauna ya zaunar da ita saman cinyar sa suna fira sannan ta zame ta kwanta a jikin sa yana shafa lallausan gashin kanta.



Nasreen dake lek'en su ta koma d'akin ta ta fara zage-zage ta d'auki wayar ta ta kira Hajiya Asiya ta fad'a mata aikuwa itama ta dinga masifa tare da cewa gobe zata je har gidan.



Sabeeha kuwa bacci ne ya kwashe ta a jikin sa tayi wajen minti talatin tana baccin sannan ta d'anyi juyi saurin rungume ta ya yi a jikin sa gudun karta fad'i k'asa jin an rik'e ta ne yasa ta yin mik'a a jikin sa wanda hakan ya tafi da imanin sa bud'e idanu ta yi ta kalle shi sai ta kuma zare idanu domin ita ta ma manta a inda ta yi baccin murmushi ya sakar mata ita kuma ta mik'e tsaye tana murza idanu ta ce "My dama kana nan baka tafi ka kwanta ba?"


"To kin danne mun jiki kina bacci ta ya zan tafi?" Tura baki tayi ta ce "To ka tashi kaje ka kwanta ka ga fa dare yayi," hararar ta ya yi tare da fad'in "Au korata ma kike yi?"



"A'a ba korar ka nake ba fa kawai dai naga dare ya fara ne Kuma ka ga ai Nasreen zata jira ka karta ga ba ayi mata adalci ba," tashi ya yi bai ce komai ba ya tsaya a gaban ta tasan me yake nufi Dan haka ta rungume shi tare da kissing d'in sa ta ce "Goodnight and sweet dreams my husband,"



"Same to you Sabee na," ya fad'a tare da ficewa binsa ta yi da ido har ya fita sannan itama ta shige bedroom d'in ta ta yi alwala tayi sallah isha'i sannan ta canja kayan jikin ta zuwa na bacci ta kwanta kusa da pretty dake ta bacci.




Washe gari da wuri Maleek ya fita domin suna da meeting lokacin da ya shiga d'akin Sabeeha bacci ma take yi Dan haka ya fita ko Break fast bai yi ba domin Sabeeha ce mai yi masa Kuma itama bacci take.




Tana tashi kuwa dama tayi sallah da asuba d'akin ta fara gyarawa sai da ta gama tas ta turare ko Ina da turaren wuta sannan ta shiga kitchen ta d'ora breakfast tana gamawa ta jera komai a daining ta shiga d'aki tayi wanka sannan ta fita falon tana mamakin jin Maleek shiru wayar ta ta d'auka ta fara Kiran wayar sa yana d'agawa ta ce "My kana lafiya naji har yanzu baka fito ba?" Dariya ya yi ya ce "Baby ina NDA ne fa muna da meeting amma na kusa dawowa," ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce "Amma ko ka tashe ni nayi maka breakfast ko kaci wani Abu ne?"


"Ba abinda naci Kuma Ina jin yunwa," ya fad'a kamar zai yi mata kuka ita Kuma cikin rarrashi ta ce "Ayyah sorry baby kayi sauri ka dawo kaji kaci abincin,"



"To baby amma fa bayan abincin har da ke kinsan nayi kewar kwana biyun nan," dariya tayi ta ce "Ba kada case My sai ka dawo d'in," daga haka ta ajiye wayar ta nufi down stairs jin ana k'wala mata kira.



Hajiya Asiya ta gani a tsaye sai huci take yi bata damu ba ta k'arasa ta ce "Ina kwana?" Ko amsa gaisuwar bata yi ba ta fara sirfa masifa "Ke dan uwar ki daughter sa'arki ce da duk ranar girkin ta ki ke yiwa mijin ta girki ko ce Miki aka yi ita bata iya ba?," Sabeeha cikin jin hausin zagar Mata mahaifiyar ta da aka yi ta ce "Eh," wani wawan mari umman Nasreen ta sauke mata a fuska daidai lokacin Sabreen ta shigo da sauri ta k'arasa ta ba tare da shakkar komai ba ta d'aga hannu ta wanke fuskar Nasreen da mari zazzafa sannan ta nuna Hajiya Asiya da hannu ta ce "Darajar girman ki ne kawai yasa bazan ramawa Sabeeha dear marin da ki ka yi mata a fuskar ki ba amma na rama a fuskar jakar 'yar ki dan Wallahi sai na baki mamaki akan Sabeeha," daga Umman nasreen har Nasreen d'in mutuwar tsaye suka yi domin rashin kunyar Sabreen ta wuce tunanin su.


Sabeeha kuwa hawaye ne kwance a fuskar ta domin Marin ya shige ta sosai wajen ta Sabreen ta koma ta fara share mata hawayen fuskar ta "Lallai kun d'ebo ruwan dafa kanku ina tabbatar muku sai na gyarawa dukan ku zama," Hajiya Asiya ta fad'a harara Sabreen ta zabga mata ta ce "Allah ya tsinewa Wanda ya fasa," daga haka ta ja hannun Sabeeha suka nufi stairs.





Suna shiga falon suka zauna Sabreen sai huci take yi ta ce "Tunda na tashi naji kawai ke nake so nagani na takurawa my one sai da ya kawoni ashe dama abinda zan tarar kenan yanzu ke dear dama abinda suke Miki kenan ki ka zuba musu ido to Wallahi indai suka Kuma yi miki kivi uban 'yan iska Wallahi har uwar ta karki ragawa," share hawaye Sabeeha ta yi ta ce "Bana so Ina kula su ne saboda a zauna lafiya kinsan halina idan na fara ramawa baza a ji da dad'i ba,"




Sabreen ta ce "Ai gara ki dinga ramawar domin shirun da ki ke yi ne yasa suke to miki hakan domin sunga suna cin banza," Sabeeha ta ce "Baza ki gane ba dear duk sanda nayi niyyar ko fad'awa Nasreen magana ne sai nasihar su Abba ta fad'o min a rai shiyasa nake kyale su ba wai dan sun fi k'arfina ba," ajiyar zuciya Sabreen ta sauke ta ce "Shikenan amma ya kamata ki duba lamarin,"



Sallamar Maleek ne yasa suka mayar da hankalin su wajen sa da sauri ya k'arasa wajen Sabeeha yana tambayar ta lafiya domin da ganin ta ba saika tambaya ba taci kuka ta k'oshi.



Hawayen da suka zubo Mata ta goge ta ce "Bakomai fa kawai kaina ke mun ciwo,"



"Amma Baby yanzu fa muka gama waya dake lafiya?" Ya fad'a domin bai yadda da abinda ta fad'a ba.




Jikin sa kawai ta kwanta zata yi magana kenan Sabreen dake gefe ta ce "Wallahi Ya MG k'arya dear take yi yanzu na shigo na samu Nasreen da mahaifiyar ta sun sata a gaba ita babar Nasreen d'in har da Marin ta,"




Da sauri ya d'ago fuskar ta ya kalla aikuwa gurin yayi ja har da shatin yatsu baice komai ba ya mik'e Sabeeha na Kiran sa amma ko waigawa bai yi ba ta kalli Sabreen ta ce "Meyasa zaki fad'a masa dear," ko a jikin ta Sabreen ta ce "Saboda nasan ko zai yi hak'uri akan komai banda a kanki hakan ne yasa na fad'a masa domin ya yiwa tufkar hanci danni ba mutunci na fiya ba indai a kanku ne," shiru kawai Sabeeha tayi ba magana.





A zafafe Maleek ya shiga d'akin Nasreen inda suke zaune suna kitsa makirci ita da mahaifiyar ta ba Nasreen ba hatta Hajiya Asiya sai da ta tsorata da ganin da ganin yanayin Maleek.



Saurin tashi Nasreen ta yi ta ce "Ya Male..," Marin da ya sauke mata ne ya hanata k'arasa maganar da zata yi ya nuna ta da yatsa ya ce "This is the first and last warning da zanyi miki akan Baby ki fita hanyar ta domin a kanta saina iya d'aukar ko wanne irin mataki a kanki domin bazan d'auki iskanci ba kin kuma San da hakan then ki jawa mahaifiyar ki kunne Ina ganin girman ta nan ba gidan ta bane nawa ne saboda haka karta kuskura na sake ganin k'afar ta a ciki idan kuwa ba haka ba zan d'auki mataki," daga haka ya wuya ya fita ba tare da ya kalli inda Umman Nasreen take ba.





Kuka Nasreen ta fashe da shi ta ce "Kin gani ko Umma Wallahi baya sona yafi son waccan yarinyar ko da da nake yi masa abubuwa bai tab'a marina ba sai yau ko k'ok'arin kashe shi da muka yi bai yi tunanin dukana ba amma ki duba akan waccan jakar yarinyar har marina ya yi hakan yana nuna tsantsar soyayyar da yake Mata ne ke kanki yace karki sake zuwa kawai ki Kira Uncle ki fad'a masa,"




Cikin takaici Hajiya Asiya ta girgiza Kai ta ce "Ba sai an fad'awa mahaifin ki ba Ni da ke k'adai ya isa muji da Sabeeha tare da 'yar uwar ta mahaifin ki kuwa ko ban ce komai ba dama Yana Nan yana gudanar da aiki akan wannan wawan yaron nan da lokaci k'alilan Zaki ga abinda zai faru Wanda zai tarwatsa rayuwar sa da ta iyayen sa da duk wani Wanda ya dangance sa ke wannan yarinyar da ki ke gani mune ajalin ta har shi mijin nata dama na fad'a Miki ba k'aunar ki yake yi ba har da ki ke zancen komawa gidan sa yanzu Kinga abinda nake fad'a Miki?"




"Na gani Wallahi nagani Umma Kuma na goyi bayan ki ke da Daddy kuyi duk abinda ya dace," wata shegiyar dariya Hajiya Asiya ta yi ta ce "Ai kin da zamu baki na Nan kusa Kuma zamu yi nasara a kansu sai sun gwammace kid'a da karatu ni zan tafi duk yadda ake ciki zan yi miki waya domin bazan sake zuwa ba kinsan wannan d'an iskan ba abinda bazai iya ba akan waccan aljanar yarinyar kafin mu tarwatsa musu rayuwa ke dai abinda nake so dake kafin wannan lokacin ki hana gidan nan zaman lafiya," gyad'a kai Nasreen ta yi ta ce "An gama," suka yi dariya har da tafawa sannan Hajiya Asiya ta fita.




Maleek kuwa d'akin Sabeeha ya koma ya same ta a zaune inda ya barta janta jikin sa ya yi ya rungume ya ce "Kiyi hak'uri kinji baby Kuma na rama miki," shiru tayi ba magana ya ce "Kinyi breakfast kuwa?" Girgiza Kai ta yi ta ce "Muje suna daining," dukan su suka nufi daining daidai lokacin Fauwaz ya yi sallama tare dukan su suka nufi daining d'in suka yi breakfast sannan suka koma falo suna ta fira Sabeeha dai tana mak'ale a jikin Maleek.



Ranar yini suka yi a gidan sannan suka tafi da daddare kuwa masoyan biyu Maleek da Sabeeha sun faranta ran juna da daddad'ar soyayya.


Washe gari tun safe Nasreen ta cika gidan da kid'a kamar gidan zai tsage duk dan neman ayi rigima amma ko Maleek baice komai ba duk da kid'an ya dame shi wanka suka yi sannan suka shiga kitchen tare suka yi breakfast suka ciyar da juna sannan suka koma falo suka zauna kad'a kai Sabeeha ta fara domin kid'an ita dad'i ma ya yi mata ta tashi ta fara rawa abinta Maleek kuwa sai dariya yake yi mata.




Haka tai ta rawa har ta gaji sannan ta fad'a jikin sa a gajiye peck ya bata a check d'in ta ya ce "Sannu da aiki Baby," tura baki ta yi ta ce "Bayan baka tayani ba," dariya ya yi har dimples d'insa suka lotsa sosai ya ce "A'a ai naga abin na manyan k'wari ne," itama dariyar ta yi ta ce "My muje wajen Ummi," ya ce "To muje," hijabin ta tasa suka fita hannun su rik'e dana juna ta gaban Nasreen suka wuce basu ko kalli inda take ba wani k'ululun bak'in ciki ne ya turnik'e mata zuciya.



Shi yayi driving d'in su har k'ofar part d'in Ummi suna shiga suka samu Ummi zaune tana danna laptop gefen ta suka zauna suka gaishe ta ta amsa cikin fara'a ta ce "Daughter jiya gaba d'aya baki lek'o ni ba," dariya Sabeeha ta yi ta ce "Ai Ummi yau a nan zan kwana," harara Maleek ya aika mata ya ce "Ummi karki yadda k'arya take yi,"



"A'a ni d'iyata bata k'arya na ma fad'a maka," Sabeeha ta gyad'a Kai irin fad'a masa d'in nan "Yawwa Son nasan baku je kunyi wa Maryam gajiyar biki ba ya kamata kuje,"



"Insha Allah zamu je," ranar dai yinin part d'in Ummi suka yi a nan Sabeeha tayi musu girki suka ci sai dare sannan ya ce "Baby taho mu tafi," mak'e kafad'a ta yi ta ce "Ka manta yau a nan zan kwana kuma a tambayi Ummi ma," Ummi na jinsu bata ce komai ba had'e fuska ya yi ya ce "Ki tashi fa nace," aikuwa ta k'ank'ame Ummi ta ce "Ni dai bazan bika ba," Ummi kuwa mik'ewa ta yi ta nufi d'aki saboda Kiran da Daddy ya yi mata.



Cak ya d'auke ta yayi hanyar fita daga part d'in sai wutsil-wutsil take yi ya ce "Yarinya Zaki sani ne," a mota ya sata sannan shima ya shiga suka nufi part d'in su.




Yana yin parking ta fita daga motar ta nufi k'ofar shiga babban falon gidan ita a lallai ta yi fushi Dan ya hanata kwana part d'in Ummi tana shiga bata lura da b'awon banana da aka zub'e su da yawa a k'ofar falon ba Aikuwa ta taka abinka da tiles ya jata zuuu ta tafi luuu zata fad'i saurin rintse ido ta yi domin tasan dole ne ta Kai k'asa sai Kuma ta jita a jikin mutum a tare suka sauke ajiyar zuciya saboda yadda ya ga ta tafi da ta fad'i tabbas sai ta karye a hankali ta bud'e idanunta ta sauke su a kyakkyawar fuskar mijinta sannan ta kalli k'asa domin ganin me ta taka.




Kana kallon yadda b'awon bananar da yawa kasan da gayya aka zube su a wajen kallon gefe ta yi can ta hangi Nasreen tana lek'e ta k'ofar kitchen ko ba a fad'a mata ba tasan aikin Nasreen ne "Me kike kallo ne haka?" Maleek ya tambaya ta ce "Bakomai mu

Please Login or Register in order to submit comment