Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka cigaba da tattaunawa akan maganar.


Tun ranar Ummi ta sanarwa da Rinaz akan su shirya nan da kwana biyu su je gidan Doctor Maryam Rinaz ta ce "Toh Ummi," tun lokacin ta je ta sanarwa da Sabeeha akan zasu gidan k'awar Ummi Sabeeha ta tambaye ta me zasu yi Rinaz ta sanar mata akan maganar ta ne da Yaya sai kawai ta ce "Ok bakomai Allah ya kaimu,"





Ko da ranar tayi kwanciya Sabeeha ta yi ta ce Wai bata da lafiya ita ba inda zata Ummi ta ce Kawai tunda bata da lafiya a kyale zuwan haka aka bar zuwan Sabeeha kuwa k'arya take yi duk Dan karta je ne tayi k'aryar cuta dan wasan b'uya suka fara yi da Maleek bata bari suna had'uwa shi kuwa hakan na damunsa sosai domin idan ya ganta Yana jin farin ciki amma rashin ganin nata ne ya fara sa shi a damuwa.






Yau ma kwance yake a falon sa yana tunanin ta bai San shigowar Nasreen ba kawai sai ganinta ya yi a kansa tana girgiza domin yanzu sabon salon iskanci ta tsiro da shi akan lallai sai ya kori su Sabeeha daga gidan.




Tashi zaune ya yi yana kallon ta baice da ita komai ba ta ce "Wallahi bazai yuwu ba sai yaran nan sunbar gidan nan tunda bana uban su bane ko Kuma wallahi zan iya illata yarinya," kallon banza ya yi mata ya ce "Ke ki kore su mana tunda ke gidan naki uban ne ke kyale kin da nake yi fa bawai tsoron ki nake yi ba kawai ina raga Miki ne Kuma bari kiji ko kina so ko bakya so ba inda yaran nan zasu Kuma ki shirya karb'ar Sabeeha a matsayin abokiyar zama,"




"Kutmar uba aikuwa Wallahi baka isa ba Kai d'in banza Kai d'in wofi Kuma sannan karka kuskura kace zaka yiwa Daddy na gorin gida Kuma wallahi idan har ka auri yarinyar nan saina kashe ta," Marin da taji a fuskar ta ne ya hamata k'arasa fad'ar abinda ta yi niyya ya nuna ta da yatsa ya ce "Wallahi Ina tausaya Miki a duk sanda ki ka yi k'ok'arin tab'a Sabeeha domin ita ce rayuwata ita nake so sanin kanki ne ke ba zab'i na bace saboda haka baki isa ki hanani auren wacce nake so ba," cikin kuka ta ce "Eh tabbas laifina ne da na aure ka to bari kaji idan har ka auri yarinyar nan sai kayi Dana sanin rayuwar ka Wallahi," barin Mata wajen ya yi yana jin wani b'acin rai a zuciyar sa.





Ita kuwa Kai tsaye wajen Umma ta wuce ta je tana kuka ta fad'a mata yadda suka yi da Maleek cikin masifa Umma ta ce "Mari fa kika ce shiyasa nace ki fita harkar wannan yaron domin bashi da mutunci abinda nake so dake shine ki manta da soyayyar da kike masa domin akwai yaron k'awata da nake so ki aura yanzu haka yana London yafi Maleek komai kyau da ilimi da Kuma dukiya," da sauri Nasreen ta ce "Dagaske Umma?" Ta ce "K'warai da gaske," Nasreen ta ce "Na yadda Umma a d'auki mataki a kansa sannan da Ina gani ya auri wata gara kawai a kashe shi kowa ma ya huta," Dariya Umma ta yi ta ce "An gama dama abinda nake son ji kenan sannan Shirin zai biyo ta 'yan uwan Sabeeha domin dole ne d'aya ta dawo tana mun aiki domin Shirin mu yabi ta kanta yadda ana ganewa nasan Aysha da kanta zata kore su kora irin ta karnuka domin nasan tana matuk'ar son yaron ta so mai tsanani," Nasreen dake zaune ta ce "wannan haka yake Umma," haka suka yi ta kitsa makirci kala kala.
[10/25, 7:40 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️




RUBUTAWA DAGA
HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ)






SADAUKARWA GA
MY DAUGHTER SABEEHA
BILKISU Z.YA'U (🅱️K)
AISHA MAGAJI DABO (AMA)







Page 10


Sabeeha ce zaune a kan gadon su sai pretty dake gefen ta a kwance gyara farcen ta take yi Rinaz ta shiga d'akin da waya a hannun ta ta mik'a mata ta ce "Ga yaya," kallon wayar Sabeeha ta yi sannan ta karb'a Rinaz kuma ta juya ta fice.




Kara wayar tayi a kunnen ta tare da yin sallama daga can had'add'iyar muryar Maleek ta amsa mata sallama sai kuma dukan su suka yi shiru Maleek ya d'an yi gyaran murya ya ce "Ina wuni?" D'an zare ido ta yi sannan cikin jin kunya ta ce "Ina wuni kana lafiya?" daga can ya ce "Ba lafiya," d'an kallon wayar Sabeeha ta yi sannan tasa wayar a handsfree ta ajiye ta cigaba da gyara farcen ta da nail cutter ta ce "Maiya faru?" Marairai ce murya Maleek ya yi ya ce "Please kizo part d'ina Ina so zanyi magana dake ne," jim ta yi kamar bazata yi magana ba sai Kuma ta ce "Ok gani nan," tana fad'ar haka ta katse kiran.



Tana k'arasawa ta mik'e ta bud'e drower ta d'auko k'aton hijabi maroon har k'asa ta d'ora saman riga da wandon jikin tayi kyau sosai ta fice.




Tafiya take yi tana tunanin to lafiya yake kirana ko dai wani abun ne a haka ta k'arasa k'ofar part d'in Kai tsaye ta shiga falon ba kowa a ciki sai sanyin Ac dake falon da Kuma wani daddad'an k'amshi da falon ke yi kujera ta samu ta zauna tana tunanin to ta ya zai san nazo gashi ban taho da wayar Rinaz ba tana cikin tunanin ne ta ji tafiya a stairs.




A hankali ta kai duban ta wajen karaf suka had'a ido da Maleek dake saukowa stairs ya yi kyau sosai cikin coffee color d'in jallabiyya kallon Sabeeha kawai yake yi domin ba k'aramun kyau maroon hijabin ya yi mata ba.




K'asa ta yi da kanta har ya k'arasa cikin falon ya zauna akan kujerar dake facing Wacce take kai yana cigaba da kallon ta yayin da ita kuma take wasa da yatsun ta.



Kad'an ya yi ajiyar zuciya sannan a hankali ya ce "Sabeeha," saurin d'aga Kai ta yi ta kalle shi domin ji ta yi yafi kowa iya fad'in sunan ta sunan ya yi dad'i sosai a bakin sa a hankali ta ce "Na'am," tashi ya yi daga inda yake ya nufi inda take ya zauna k'asan k'afafun ta sannan ya d'aga Kai ya kalle ta ya ce "Sabiha kiyi hak'uri bani da niyyar cutar dake ki tausaya mun ina son ki i really love you with all my heart with every breath I take," shiru ya yi sannan ya ce "Ashe dama haka so yake hankali na a tashe yake saboda rashin sanin matsayina a wajen ki ko da yaushe soyayyar ki k'aruwa yake a zuciya ta ina jin zuciyata tana yi mun zafi a duk sanda na tuna bansan wanne matsayi ki ka ajiyeni ba a zuciyar ki ni ban tab'a soyayya ba ban tab'a jin son wata a raina ba sai ke ki tausayawa zuciyar da batasan komai ba sai k'aunar ki Sabeeha zuciya ta ba kowacce irin zuciya bace ban iya saka abu a raina ba komai k'ank'antar sa sai ya hanani sukuni," a hankali ya kai lallausan hannun sa ya rik'o nata hannun saurin rintse idanu ta yi domin wani shock da ta ji sannan wannan ne karo na farko da namiji ya rik'e mata hannu.



Ya kalle ta ya ce "ki tausaya mun soyayyar da nake miki mai girma ce ki daure ki sanar dani matsayina a wajen ki domin na samu sauk'in abinda nake ji a zuciyata," ya fad'a yana langab'ar da Kai irin ta tausaya masa.



Kallon sa Sabeeha ta yi tabbas ya bata tausayi sosai a hankali ta janye hannun ta daga cikin lallausan hannun sa ta mik'e tsaye ta kalle shi ta ce "Kayi hak'uri bana son ka bazan iya auren ka ba ka nemi wata," tana fad'ar haka ta juya ta fice da gudu tana zubar da hawaye domin ita har ga Allah tana son Maleek sai dai tana tsoron abinda zai je ya dawo a haka ma ba a kyale ta ba balle ta had'a kanta da Maleek ga halin Nasreen da mahaifiyar ta baza ta iya da su ba saboda ita ba 'yar kowa ba a illata ta a banza da sauk'i ma idan abun iya kanta zai tsaya domin tana matuk'ar jin tsoron wani Abu ya faru da 'yan uwan ta.



Tafiya take yi tana zubar da hawayen tausayin Maleek domin ta tabbatar yana son ta so ba Kuma na wasa ba Kuma itama tana son shi sai dai zama lafiya yafi zama d'an sarki.



Da gudu ta wuce Ummi a falo ta wuce d'akin su tana kuka mik'ewa Ummi ta yi tabi Sabeeha da kallo tana tunanin to idan har ga Sabeeha na kuka to wane hali Maleek ke ciki??



KU YI MANAGE DA WANNAN SANNAN KUYI HAK'URI DA JINA SHIRU DA KU KA YI AN SAMU WATA MATSALA NE AMMA INSHA ALLAHU ZAN CIGABA DA POSTING KULLUM KAMAR YADDA NA SABA NA GODE DA KULAWAR KU A GARENI DOMIN NAGA MASOYAN NOVEL DIN NAN SOSAI DA MASU KIRANA DA MASU YI MUN TEXT DA KUMA MASU YI MUN MAGANA TA ONLINE DUK NA GODE ALLAH YABAR ZUMUNCI.
[10/25, 7:40 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️





RUBUTAWA DAGA
HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ)





SADAUKARWA GA
MY DAUGHTER SABEEHA
BILKISU Z.YA'U (🅱️K)
AISHA MAGAJI DABO (AMA)





Page 11


Hanyar fita Ummi ta yi hannunta rik'e da key d'in mota tana fita ta hau motar ta zuwa part d'in Maleek.




Tana zuwa ta shiga falon sai ta tarar ba kowa ta wuce stairs ta tura k'ofar d'akin Maleek ta shiga da Sallama.



Zaune a gefen gado ta samu Maleek a hankali ya juya ya kalli Ummi abinda Ummi ta gani shi ya yi matuk'ar razana ta hawaye ne ke zuba daga idanun Maleek gashi sunyi jajir kamar Wanda aka watsawa barkono a cikin idanun.



Saurin k'arasawa Ummi ta yi ta zauna a gefen sa ta ce "Subhanallahi son lafiya me yake faruwa ne?" A hankali ya share hawayen fuskar sa ya ce "Ummi tace bata sona bazata aure ni ba," ya fad'a wasu hawayen nabin fuskar sa cikin tausayin yaron nata ta jawo shi jikin ta ta rungume shi tana shafa bayan sa ta ce "Son kayi hak'uri kaji?"



"Ummi ni laifin me nayi mata da bata sona meyasa baza ta gane son da nake mata ba k'arami bane Ummi na rasa ta bansan inda rayuwata zata kasance ba Ummi ki taimaka mun," dakewa kawai Ummi ke yi amma ji take yi kamar ta yi kuka domin tausayin d'an nata gaba domin tasan son da yake wa Sabeeha bana wasa bane tunda har gashi yana kuka ta sanadin ta.




Shafa sumar kansa Ummi ta yi ta ce "Son kayi hak'uri haka Allah ya k'addaro maka ka cigaba da addu'a Allah yasa hakan shi yafi alkhairi sannan dan Allah karka bar abin nan a ranka kasan baka da cikakkiyar lafiya please," a hankali ya yi noding kansa.




Ummi ta ce "Yawwa soja na kayi k'ok'ari ka cire soyayyar ta a zuciyar ka kaji kayi ta addu'a," Nan ma gyad'a kai kawai ya yi domin yasan da soyayyar Sabeeha zai mutu domin baza ta tab'a fita a ransa ba.




Nan dai Ummi tai ta lallab'a shi sai dai duk da haka take zazzab'i ya rufe shi dakyar ya yi wanka Ummi ta bashi tea yasha tare da magani sannan ya kwanta.





Sabeeha tana shiga d'akin su kan gado ta fad'a tana rera kuka kamar ranta zai fita sai da ta yi Mai isar ta sannan bacci ya kwashe ta.


Ko da su Sabreen suka ji abinda Sabeeha ta aikata basu ji dad'i ba dan kunyar Ummi suka ji ta kama su saboda yadda ta rik'e su Kuma take son su kamar ita ta haife su amma Sabeeha ba kunya tace bata son d'an da Ummi ta haifa Kuma wanda take matuk'ar k'auna.



Ita kanta Sabeeha kunyar Ummi take ji sosai sai dai gani take yi hakan shine mafitar ta domin ta fuskanci Nasreen da mahaifiyar ta babu imani a zuciyar su ita damuwar ta ba a kanta bane akan 'yan uwan ta ne.



Ummi kuwa bata canja musu fuska ba sai ma ninka kulawar ta da tayi a gare su.




Maleek kuwa rashin lafiya yake yi sosai domin ciwon sa ne ya tayar masa gaba d'aya damuwa tayi masa yawa Ummi ce kad'ai ke kula da shi ko office dena fita ta yi tana gida tana bashi kulawa sannan tana kwantar masa da hankali tana masa nasiha Kuma Alhamdulillah yana rage damuwa domin ko da yaushe yana kai kukan sa wajen ubangiji akan Allah ya sassauta masa soyayyar Sabeeha a zuciyar sa domin soyayyar ta kullum k'aruwa take yi a zuciyar sa kuma gani yake yi idan har soyayyar ta tafi yadda yake jinta yanzu a ransa to ita ce ajalin sa.



Haka Ummi ta dage wajen ba Maleek kulawa har ya warware amma Nasreen ko da wasa bata je wajen sa ba bata ma san bai da lafiya ba saboda ta yanke shawarar rabuwa da shi domin ta samu Wanda ya fi shi a cewar mahaifiyar ta.


A haka har akayi sati biyu Sabeeha duk tabi ta damu kanta saboda ita kanta tasan bata kyauta ba yanzu ma kwance take a d'aki domin yanzu tafi yin wunin d'aki tunda wannan abun ya faru sannan ta lura tun lokacin Maleek bai k'ara shiga part d'in ba sannan tun ranar bata k'ara sa shi a idanunta ba wanda ita hakan shi ya dameta domin itama batasan son da take masa ya kai haka ba sai da ta dena ganin kyakkyawar fuskar sa abinci ma sai dai a Kai masa part d'insa.




Tana nan a kwance Sameeha da Sabreen suka shiga d'akin zama suka yi Sameeha ta ce "Sabeeha dear lafiya tunanin me ki ke yi haka?" Kallon ta Sabeeha ta yi ta ce "Sameeha tunanin Abba nake yi tunda muka taho ba musan halin da yake ciki ba sannan da zamu taho dubu ashirin kawai muka ba zuwaira mai abinci ina so gobe naje naga halin da yake ciki," Sabreen ta ce "Sabeeha sister zanje nima please," girgiza kai Sabeeha ta yi ta ce "A'a dear ni kad'ai zani saboda bana so kawu yasan naje kuma ba kwana zanyi ba," suka ce "Allah ya kaimu," ta amsa da "Ameen,"



Washe gari tunda Sabeeha tayi sallar asuba bata koma bacci ba ta shiga kitchen ta fara had'a breakfast tana gamawa ta jera komai a daining sannan ta nufi d'akin Ummi.




Da sallama ta shiga d'akin ta samu Ummi zaune akan sallaya tana karatun Qur'an sai da takai aya sannan ta juya tare da amsa sallamar ta ce "K'araso mana daughter," k'arasawa ta yi ta zauna ta ce "Ummi Ina kwana?" Cikin fara'a Ummi ta ce "Lafiya k'alau har kin tashi kenan?"



"Eh Ummi dama Ina so ne anjima naje na duba Abba," Ummi ta ce "Lafiya dai ko?"


"Lafiya Ummi kawai dai ina so naje na duba shi ne," Ummi ta ce "To shikenan ba damuwa ku shirya zansa driver ya Kai ku," Sabeeha ta ce "A'a Ummi ai ni kad'ai zanje kuma ba kwana zanyi ba saboda bana so Kawu yasan naje," jinjina kai Ummi ta yi ta ce "Ok to ki shirya sai Alasan ya Kai ki tasha," ta ce "To Ummi," daga haka ta koma d'akin su ta fara shiri.


K'arfe 9 su Sameeha Sabreen da Rinaz suka yiwa Sabeeha wajen mota tana sanye da k'aton hijabi har k'asa har da nik'af a hannun ta saboda rana ta d'anyi idan taje zata d'aura saboda gudun Kar a ganta a kaiwa kawu Bala labari.




Rungume juna suka yi su Sameeha suna jin ba dad'i domin gani suke yi kamar idan ta tafi bazata dawo ba Sabreen ta ce "Dear kice muna gaida Abba," ta ce "Zaiji kuma wataran zaku je ai,"



K'amshin had'adden turaren Maleek da ya ziyarci hancin ta ne yasa ta saurin waigawa ta kalli inda part d'insa yake domin mugun son ganin sa take yi sai dai bata gansa ba sai su Salman dake k'ofar part d'in cikin kakin su na sojoji.



Kalle-kalle take yi ko zata ganshi amma har lokacin bai fito ba sai k'amshin sa da ya cika compound d'in gidan kallon su Sabreen ta yi ta ce "Saina dawo," Rinaz ta ce "Sai kin dawo ki gaida Abban," a sanyaye ta ce "To," sannan ta shige motar suka tafi su Sabreen na d'aga mata hannu.



Juyawa suka yi har zasu shige part d'in Ummi wayar Rinaz ta fara ringing ta tsaya su kuma suka shige.


Maleek ne ya fito daga part d'in sa ya yi wani fitinannen kyau cikin uniform d'insa ya k'ara haske sosai kansa yasha wani aski Mai matuk'ar kyau duk da ya rame amma kyau ba a magana kamar shi sace shi ka gudu da kallo Rinaz ta bi shi domin itama tasan yayan nata mak'ura ne wajen kyau da wanka har ya gaji da had'uwa.



Yana zuwa ya ce "Ina kuma zata?"


"Zata k'auyen su ne duba Abban su," ya ce "Baya da lafiya ne?" Rinaz ta ce "Eh to gaskiya bansani ba," d'an jinjina Kai ya yi ya ce "Alasan zai kaita kenan?"


"A'a zai kaita tasha ne," kallon agogon hannun sa Maleek ya yi ya ce "Ok kice da Ummi naje NDA ba dad'ewa zan dawo," Rinaz ta ce "To a dawo lafiya," ya ce "Ameen," sannan ya juya ya nufi motar sa.


Har zai shiga ya kalli Salman ya ce "Salman ku bi su Alasan har tasha sannan har garin Ina so nasan duk wani information akan ta," Salman ya ce "Ok sir," d'an hararar sa Maleek ya yi ya ce "Don't sir me I'm Maleek," yana fad'ar haka ya shige motar Salman ya rufe yana murmushi domin ogan nasa kuma abokinsa na burge shi.



Jan motocin aka yi suka tafi sannan Salman ma tare da wasu daga cikin sojojin suka shiga mota suka bi su Sabeeha zuwa tasha tun a hanya suka same su Saboda a hankali Alasan ke tafiya suna tafe suna fira sojojin Maleek kuwa duk inda zaka gansu da gudu suke driving.


Har tasha suka bisu kamar yadda aka umarce su suna mota a zaune har motar ta cika driver ya shiga suka tafi su Salman na biye da su.



Maleek kuwa suna zuwa aka bud'e masa mota ya fita direct wani office ya shiga ya samu duk wani babban soja na wajen kowa cikin kakin sa wani soja dake tsaye ne ya ja masa kujera ya zauna sannan ya Kai duban sa wajen shugaban rundunar sojoji dake zaune kujerar dake tsakiya.



Ba b'ata lokaci shugaban sojoji ya ce "Dalilin da yasa aka shirya wannan taron gaggawar wato magana ce akan the most criminal person wato Alhaji Sammani so kamar yadda ku ka sani babu Wanda a cikin mu yasan shi wanene wannan Alhaji Sammani a fuska domin ko yaushe b'oye fuskar sa yake yi yana aikata ta addanci sannan yana kashe bayin Allah da basu ji ba basu gani ba da hanyar magungunan da ake sai da su ba tare da k'a ida ba da kuma shigo da makamai suma ba bisa k'a ida ba saboda shi ya mayar da hakan sana'ar sa to wannan karon yana shirin shigo da cocaine k'asar nan tare da makamai kimanin guda dubu d'aya da d'ari biyu da hamsin Wanda mun samu wannan information d'in ne daga jami'in mu da muka tura dubai domin bincike sannan wad'an nan makamai da hodar iblis za'a turo su ne ta jirgin ruwa kamar yadda ku ka sani Alhaji Sammani yana da mataimaka wad'anda bamu san suwaye ba amma muna bincike bakin k'ok'arin mu domin gano su kuma mu d'auki mataki a kansu,"




Wani cikin sojojin ya ce "But sir ta ya zamu gano su bayan komai a b'oye suke yi?"


"Zamu iya gano su amma idan har anyi nasarar kama wad'an nan kaya da kuma wad'an da suka d'auko kayan,"


Wani daban cikin sojojin ya sake cewa "Sir yanzu wanne mataki za a d'auka?"



"Kusan baza mu tab'a bari a cigaba da kashe al'ummar mu ba saboda haka kamar yadda ku ka sani kuma ku ka shaida sannan ku ka yadda da k'warewa da kuma gogewar rundunar MG Abdul-maleek akan aikin su da kuma jajircewar su saboda mun samu nasarori da dama ta sanadin su saboda haka wannan lokacin ma su kasance cikin shiri domin zamu turasu duk wata hanya da mukasan wad'an nan kaya zasu shigo,"



Gyad'a kai kawai Maleek ya yi domin yasan rundunar sa na musamman ne sun samu horo na musamman suna da k'warewa sosai akan aikin su.




Nan suka cigaba da tattauna ta yadda aikin zai kasance kowa na bada tasa shawarar.




Su Sabeeha kuwa suna zuwa ta sauka a mota ta nufi gidan su su Salman na biye da ita ta d'aura nik'af sannan ta shige gidan su.



Faruk dake zaune akan benci Salman ya ba hannu suka gaisa Faruk d'in nayi musu kallon tsoro ganin su sanye da uniform d'in sojoji.




Salman ya ce "Dan Allah muna tambaya ne," Faruk ya ce "To Allah yasa nasani," Salman ya zauna gefen sa ya tare da nuna masa gidan da Sabeeha ta shiga ya ce "Kasan wata yarinya a gidan can mai suna Sabeeha?" Gyad'a kai Faruk ya yi ya ce "Eh nasan ta k'anwata ce Allah dai yasa ba laifi ta yi ba," murmushi Salman ya yi ya ce "Ba laifi ta yi ba amma ita da su waye a gidan?"




Faruk ya ce "Ita da 'yan uwan ta ne Sameeha da Sabreen amma yanzu dukan su basa nan sunyi tafiya sai Mahaifin su kad'ai a gidan," jinjina Kai Salman ya yi ya ce "Amma mamar su fa?" Ajiyar zuciya Faruk ya sauke ya ce "Mamar mu bata nan gaskiya," Nan Faruk ya labarta musu labarin b'atan Mamar su Sabeeha.



Salman ya ce "Mun gode sai anjima," daga haka suka yi sallama suka juya suka tafi.





Sabeeha kuwa da sallama ta shiga gidan su ta samu Abban su zaune akan tabarma yana jan carbi zare nik'af d'in fuskar ta ta yi Abba yana ganin ta yaji wani farin ciki a zuciyar sa domin tun tafiyar su kullum tunanin sa a kansu yake yana tunanin wanne hali suke ciki shin suna lafiya ko a'a sunci abinci ko a'a wataran har kuka yake yi saboda ba mahaifin da zai so 'yan'yan sa suyi nesa da shi bayan ba aure suka yi ba kuma 'ya'ya mata ba maza ba dole hankalin sa bazai kwanta ba.


Itama Sabeeha tsayawa kallon mahaifin nata ta tsaya yi cikin tausayin sa ganin ya rame sosai.




Bayan ta Abba ke lek'awa domin ganin ta ita kad'ai k'arasawa ta yi ta zauna gefen sa ta ce "Abbana Ina wuni?" cikin murmushi ya ce "Lafiya qalau Ina sauran aminan nawa?" Dariya ta yi ta ce "Abba ba tare muke ba suna gida sunce na gaida Kai sosai kuma suma ai zasu zo wataran," ya ce "suna lafiya dai ko?"



"Lafiya k'alau Abba dama bamu zo tare bane saboda Kar Kawu ya samu labari," shiru Abba ya yi sannan ya ce "Amma me ku ke yi a can d'in hankalina yak'i kwanciya," murmushi ta yi ta ce "Abba ka kwantar da hankalin ka aiki muke yi a wani gida Abba mutanen kirki ne sosai suna kula damu sosai Wallahi Abba matar kamar ita ta haife mu," Abba yaji dad'in hakan sosai ya ce "Alhamdulillah ko dai a can za a samo mun surukan nawa?" Dariya Sabeeha ta yi ta ce "Aikuwa Abba Sabreen dear saurayin ta a gidan yake,"



Abba ya ce "Masha Allah," nan suka cigaba da fira Sabeeha ta ce "Yawwa Abba ya aka yi da Sadam kuwa?" Abba ya ce "Yaya ne ya zo har gida yaci mun mutunci sannan daga baya ya aurawa Zainabu shi," tab'e baki ta yi ta ce "Allah ya basu zaman lafiya," Abba ya ce "Ameen," tashi Sabeeha ta yi ta fara kiciniyar d'ora girki domin tasan Abban nasu ba abinda yaci.




Tana girki suna fira har ta gama ta zuba musu tare suka ci suka k'oshi sannan suka yi sallar azahar.




Su Salman kuwa suna komawa NDA suka wuce direct office d'in Maleek suka wuce suna shiga suka samu yana duba wasu files d'aga kai ya yi ya kalli Salman ya ce "Salman zauna mana," zama Salman d'in ya yi Maleek ya ce "Me yake tafiya?"




Salman ya ce "Mun je kamar yadda ka sani 'yan uku ne sannan su kad'ai ne wajen

Please Login or Register in order to submit comment