Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ganinta juya idanu ta yi ta ce "Lafiya kuwa irin wannan kallo haka," ya ce "Ina sanki," murmushi ta yi ta ce "Love you more sweetheart mu k'arasa ciki," gaba ta yi yana binta a baya har cikin wani falo mai kyan gaske zama ya yi ita Kuma ta nufi fridge ta kawo masa drinks da ruwa ta ajiye sannan ta zuba a cup ta koma gefen sa ta zauna ta mik'a masa.



Karb'a ya yi ya yi sipping kad'an sannan ya ajiye Yana kallon ta ya ce "Farin cikin me ki ke yi ne haka Sabee na?"yar dariya ta yi ta ce "Farin cikina a yau na farko shine ganin ka da nayi yau cikin k'oshin lafiya hakan ba k'aramun faranta mun ya yi ba then Abu na biyu shine ya Umar ne ya ce zai turo iyayen sa ayi maganar auren su da Sameeha dear wayyo farin ciki," ta fad'a tare da mik'ewa tana yin juyi domin ita tsabar farin ciki ma ta manta gaban waye take.



D'an tsalle ta yi ta ce "Ai na fad'a maka lokacin nan zamu sha shagali," dariya Maleek ke yi mata domin video ma yake mata bata saniba.




Jin shiru ba magana ta d'an waiga saurin nutsuwa ta yi ta koma ta zauna tayi k'asa da kanta dariya ya yi ya ce "Ya ki ka zauna Kuma na d'auka ai rawar bikin zaki fara yanzu," ya fara mata dariya.




Had'e fuska ta yi ta ce "Ka ga ka bari," ta fad'a tana tura baki wata dariyar ya yi ya ce "Ok bara kiga wani Abu," d'an matsawa kusa da ita ya yi ta nuna mata video d'in da ya yi mata hannayen ta biyu tasa ta rufe fuska.



Mik'ewa ta yi yasa lallausan hannunsa ya rik'o nata ya mik'e sannan yasa hannayen sa biyu ya zaunar da ita ya zauna gefen ta ya ce "Bud'e fuskar to na fad'a maki wata magana," bud'ewa ta yi sai dai idanunta na k'asa.




"Nikam idan bara ki kalleni ba na fasa sanar miki," Maleek ya fad'a yana kallon ta a hankali ta d'aga kyawawan idanunta ta sauke a nasa ajiyar zuciya ya sauke ida nunsa cikin nata ya ce "Sak'o daga Daddy," gaban ta ne ya yi wata muguwar fad'uwa ta yi saurin rintse idanu ta mik'e tsaye muryar ta na rawa ta ce "Ya fasa amincewa da auren mu ko?" Ta fad'a k'walla taf a idanunta.




Gaban ta Maleek ya tsaya ya ce "Calm down Sabee na," hawayen idanunta ne suka zubo ta ce "How should I calm down my man bayan kunnuwana na so su ji mun abinda bazan tab'a mantawa da shi ba a rayuwata," ajiyar zuciya Maleek ya sauke tare da rik'e k'ugu da hannunsa d'aya d'ayan hannun kuma a goshin sa yana d'an sosawa a zuciyar sa kuwa ya ce wannan wace rigima ce haka Kuma.




Kallon ta ya yi ya ce "Kinga Sabee na ki saurare ni bawai abinda ki ke tunani bane Daddy fa cewa ya yi na sanar miki ki fad'awa Abba zasu zo nema mun auren ki jibi," da sauri ta kalle shi ga hawaye a idanunta amma murmushi take yi ta yi tsalle tana yarfa hannaye ta ce "Dagaske sweetheart?" Jinjina kai ya yi Yana kallon yadda take tsallen kamar baby doll.



Ya ce "Kinyi farin ciki?" Ta ce "Kai sosai fa kenan zan zama matar ka?"




"Eh mana baby ko baki son hakan?" D'an hararar sa ta yi ta ce "Ni kuwa nake so," bari ma naje na sanar da Mama Kiran ta Maleek ke yi amma ko waige bata yi ba tabar falon da gudu girgiza kai ya yi ya kalli agogon sa yabi bayan ta domin tafiya gida ya huta.



Tun kafin ta shiga falon take k'wala kiran "Mamana Sabreen sister Sameeha dear," duk a tare ta same su a falon Doctor kuwa dafe Kai ta yi ta ce "Ya ilahi wad'an nan yara nawa rabbi ya shirya mun ku," fad'awa jikin ta Sabeeha ta yi ta ce "Mamana albishirin ki," kafin Doctor ta yi magana ta nufi Sabreen ta rungume ta ta ce "Dear congratulate me na kusa aure Sameeha dear Sweetheart ya ce su Daddy zasu zo neman aure na," ta fad'a tana rungume Sameeha.



Ihun su na murna da suka saba suka saki suka fara rawar su ta murna har da Sameeha da itama rawa take yi kamar wacce ta samu fitaccen kid'a.



Doctor kuwa kallon yarab nata kawai take yi ganin yadda suka sata a gaba suna rawa cikin farin ciki itama murnar take yi.



Wayar Sabreen ce ta fara neman agaji ta d'auka daga can Fauwaz ya ce "Amarya ta," dariya ta yi ta ce "Yau Kuma amarya na koma my heart?" Cikin farin ciki ya ce "Dagaske kin kusa zama amarya ta su Daddy zasu zo nema mun auren ki har ma da na yaya,"




"Wayyo dad'i kace na kusa zama amarya," ta fad'a tana buga tsalle bata jira ya k'ara magana ba ta katse Kiran suka cigaba da budiri domin su Sabeeha suna jin abinda suka tattauna da Fauwaz nan fa suka k'ara rikita gidan 'yan aikin gidan fitowa suka yi suna kallon yadda 'yan uku suka saki kid'a suna cashewa domin abun ya yi musu dad'i.



Sallamar Abba ce yasa su saurin nutsuwa suka kashe kid'an suka zazzauna kamar basu suka gama zubar da galan-galan na rawa ba.



Zama Abba ya yi Sabeeha ta je ta kawo masa ruwa suka ce "Sannu da dawowa Abba," ya ce "Yawwa," ya kalli Mama ya ce "Doctor yau dai kam daga ke har aminaina na ganku cikin farin ciki ku fad'a mun meke faruwa," kallon 'yan uku Mama ta yi a tare suka yi k'asa da kai.





Mama ta ce "Ooh ni ku ka raina kenan ko to shima ku fad'a masa mana marasa kunya kawai," sannan ta kalli Abba ta ce "Yanzu suka gama rawa nan a gabana saboda Maleek Umar da Fauwaz sunce zasu turo maganar auren su," washe baki Abba ya yi ya ce "Masha Allah aminaina girma ya taho Allah ya kawo su lafiya ai kuna son su ko?" A tare suka ce "Sosai ma kuwa Abba," baki bud'e Doctor ke kallon su da sauri suka tashi suka bar falon.
[10/25, 8:46 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️




RUBUTAWA DAGA
HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ)






SADAUKARWA GA
MY DAUGHTER SABEEHA
BILKISU Z.YA'U (🅱️K)
AISHA MAGAJI DABO (AMA)




Page 21



D'akin su 'yan uku suka koma kowaccen su cikin farin ciki.



Rana d'aya su Daddy tare da wakilan Umar suka je wajen Abba a take aka kammala komai aka sa rana wata d'aya saboda Maleek takurawa Daddy ya yi akan asa bikin wata d'aya saboda nan da wata biyu zai koma Dubai hakan ne yasa akasa bikin wata d'aya har da na Fauwaz Umar ma wata d'ayan yace asa domin a shirye yake.




Haka 'yan uku da masoyan nasu suka cigaba gudanar da soyayyar su cikin farin ciki da son junan su da kuma bawa juna kulawa kowannen su na jin idan ba d'ayan su bazai iya rayuwa ba.





Uncle kuwa sai daga baya Daddy ke sanar masa cewar ansa ranar bikin Maleek wata d'aya abin ya matuk'ar bawa Uncle mamaki domin bai tab'a tunanin Daddy zai yi wani Abu ba tare da sanin sa ba ko da Nasreen ta ji labari ranar wuni ta yi kuka domin tasan idan har Maleek ya auri Sabeeha sunanta sorry domin tasan bata da sauran k'ima da daraja a wajen Maleek duk da dama ba ganinta da mutunci yake ba already Hajiya Asiya kuwa har lokacin bata fasa yiwa Nasreen hud'ubar shaid'an ba.






Kawu Bala ne kwance saman wata yagalgalalliyar tabarma idan ka kalle shi sau d'aya baza ka so ka k'ara ba ya rame ya yi bak'i idan har ka San shi da ka kalle shi yanzu sai ka rantse bashi bane saboda uwar rama duk ya canja kamanni daga gefe kuwa Lantana ce zaune ta zabga uban tagumi tana kallon Kawu Bala cikin tausayawa rayuwar su ta ce "Malam ka daure kasha kunun nan ka ga yau gaba d'aya baka sa komai a bakin ka ba duk da kunun nan kad'ai gare mu Wanda shima dakyar na samu aka bamu bashin sa balle ayi maganar siya maka maganin cutar ka,"




Kawu dake kwance sai ka rantse bacci yake yi sai dai tsabar jin jiki ne yasa ko idanunsa baya iya bud'ewa a hankali ya ce "Lantana nayi nadama na cuci d'an uwana Wanda bani da kamar sa gashi halin da na shiga garama na mutu na huta," kuka Lantana ta saka ta ce "Ka dena fad'ar haka malam insha Allah sai mun had'u da Maryam da Habu harma da yaran su mun rok'i yafiyar su domin samun sauk'i wajen ubangiji," Zainabu ce ta fito daga d'aki sai ka rantse ba haihuwar ta d'aya ba duk ta fita hayyacin ta ta zama tsohuwar k'arfi da yaji ta zauna gefen Lantana ta ce "Lantana ko zaki sanwa habibu kunun nan ya tashi daga bacci sai kuka yake yi," d'an girgiza Kai Lantana ta yi ta ce "Zainabu kunun nan malam na karb'owa yasha," Kawu dake magana dakyar ya ce "Bata Lantana shi yaro ne baisan babu ba," mik'a mata Lantana ta yi ta karb'a ta koma cikin d'akin su da ba komai a cikin sa taba Habibu mai 'yan watanni kunun yasha.



Bikin 'yan uku sai tahowa yake yi yayinda Rinaz dakyar Daddy ya yadda yabar ta sai bayan biki sannan zata tafi karatu tayi kukan ta yi magiyar har ta gaji haka ta hak'ura.


B'angaren 'yan uku kuwa gyaran jiki Mama tasa ake yi musu bata barin su fita ko Ina ko yaushe suna gida abinsu.




Kawu Bala ne ke tafiya Yana layi kamar yasha wani abu domin zaka iya cewa shaye-shaye ya yi sai dai ba haka bane tsabar yunwar dake damunsa ce tasa shi hakan tafiya yake yi baya kallon gaban sa yazo tsallaka titi wata babbar mota data taho da gudun gaske ta yi gaba dashi ya fad'i a wajen matacce.






Firgigit Abba ya farka daga bacci da salati a bakin sa Mama dake kwance a gefe yadda ta ji Abba ya tashi zumbur ne yasa itama ta tashi tare da kunna bedside lamp ta ce "Abban 'yan uku lafiya?" Ajiyar zuciya Abba ya sauke domin ya tabbatar da mafarki yake yi ya ce "Maryam mafarki nayi Yaya yana cikin mawuyacin hali sannan mota ta bige shi ya mutu gobe dole ne naje k'auyen," Doctor ta ce "Gaskiya ne hakan ya yi goben sai muje tare," Abba ya ce "Allah ya kaimu," ta amsa da "Ameen," daga haka suka koma baccin su.



Washe gari da safe 'yan uku nayi breakfast a daining idan ka kalle su saika k'ara saboda wani azababben kyau da suka k'ara brown skin d'insu ta k'ara kyau sai shining take yi ga k'amshin su da falon ya d'auka.




Abba ne da Doctor suka fito daga d'aki sunyi wanka na alfarma Doctor ta yi kwalliya cikin less coffee colour da milk takalmi da jaka da mayafi less d'in ya matuk'ar yi Mata kyau kasancewar ta fara Abba kuwa tsadaddiyar shadda yasa fara sol babbar riga sai k'amshi suke yi.




Tunda suka fito su Sabeeha ke kallon su cikin burgewa waya Sabreen ta d'auka ta fara fella mutu hotuna Sabeeha na taya ta har suka k'arasa daining d'in suma suka zauna domin karyawa.




Gaida iyayen nasu 'yan uku suka yi suka amsa cikin fara'a sannan suka cigaba da karyawa suna gamawa Abba ya kalli agogon sa ya kalli Mama ya ce "Doctor muje time na tafiya,"




"Abba Ina zaku je?" Sabeeha ta tambaya Abba ya ce "Aminiya zamu je k'auye ne wajen Yaya," Sabreen ta ce "Abba Dan Allah zamu je," Doctor ta ce "No Kun manta ne na hana ku fita?" Sameeha ta ce "Please Mama kuje damu," Abba ya ce "Kyale su mu tafi Doctor ku yi sauri kuzo mu tafi," Doctor ta ce "Kuma kuna dad'ewa tafiya zamu yi.





Da sauri suka nufi stairs suka yi Shirin da baza a rasa ba domin already sunyi wanka kaya iri d'aya suka sa dogayen rigunan pich color d'in shadda suka sa da blue mayafai da takalma da jaka duk blue.




Da gudu suka sauka down stairs kamar su Abban zasu gudu su barsu girgiza Kai Doctor ta yi ta ce "Allah ya shirye ku mu tafi to," gaba suka yi suna fitowa suka samu driver na jiran su.




Doctor ta kalle shi ta ce "Yawwa sabi'u idan Faisal na kusa Kira mana shi yanzu," Sabi'u driver ya ce "To madam," ya fad'a tare da juyawa ya nufi wata hanya dake gidan can sai gashi tare da Faisal suna zuwa Mama ta nunawa Faisal wata dank'areriyar bak'ar mota ta ce "Zaka yi driving 'yan uku zamu je k'auye ne," ya ce "To madam,"





Bayan mota Abba ya bud'e Doctor ta shiga shima ya shiga sabi'u ya shiga ya ja motar.




Bud'e bayan mota Sameeha ta yi ta kalli Sabreen dake gefe tana waya ta ce "To dear sai kin taho dan mu mun tafi," da sauri Sabreen ta shige motar tana yiwa Sameeha hararar wasa yayin da Sabeeha ta shiga gaban mota tana yin chart da Maleek.




Jan motar Faisal ya yi yabi bayan motar su Abba sai k'auye.


Suna shiga k'auyen daidai lokacin gidan Kawu Bala ya kama da wuta sosai wutar ta fara ci ganga_ganga ba tare da sunsan dalilin kamawar ta ba rabon su da d'ora tukunya a gidan ba sun manta shekarar ballantana ace wutar murhu ce ta haddasa.





Dakyar suka fito daga gidan suna neman agaji tuni 'yan gari suka hallara aka fara k'ok'arin kashe wutar domin karta shafi mak'ota dakyar aka samu aka kashe wutar sai dai gidan ya yi k'urmus 'yan garin sai tausayin Kawu Bala suke ji domin duk wani Mai imani idan yasan halin da Kawu ke ciki sai ya tausaya masa ballantana yanzu da gidan nasa da shi kad'ai ya rage masa ya k'one.




Tun daga nesa suke hango tarin jama'a wajen gidan Kawu Bala Abba ya ce "Maryam duba kiga taron jama'a wajen gidan Yaya lafiya kuwa," Mama da itama mamakin hakan take yi ta ce "Insha Allah lafiya lau,"


"Dear Kinga mutanen garin a tare a gidan Kawu Allah yasa dai lafiya," Sameeha ta fad'a cikin Sabeeha da Sabreen babu wacce ta kulata domin su mugun haushin Kawu Bala suke ji.



'yan k'auyen ganin manyan motoci yasa su baza idanu suna kallon motocin daga nesa da mutanen kad'an suka yi parking sannan suka firfito daga motar.





Nan fa mamaki ya kuma kama mutanen saboda ganin wad'an da suka fito daga motar musamman wad'an da suka san Abba da Kuma sanin halin da yake ciki da amma yanzu gashi cikin tsadaddiyar mota ga wani canjawa da ya yi kamar ba shi ba haka ma 'yan uku sai kallon su ake yi ganin yadda suka zama bama a zancen Doctor domin ko gane ta 'yan garin basu yi ba zuwaira mai abinci dake lek'e ta katanga ce kad'ai ta gane ta.



Hanya mutanen wajen suka bud'a musu suka wuce zuwa k'ofar gidan turus suka tsaya suna kallon yadda gidan ya k'one saurin juyawa Abba ya yi ya kalli Malam Saleh ya ce "Malam Saleh ina Yaya?" Domin Abba Sam bai lura da Kawu Bala dake gefe ba.




Da hannu malam saleh ya yiwa Abba nuni da Kawu Bala dake gefe a durk'ufe idanunsa sai zubar da hawaye suke yi domin tausayawa rayuwar su halin da zasu shiga yake yi damuwar sa d'aya a Ina Lantana da Zainabu da d'anta zasu dinga zama shi bata kansa ma yake yi ba domin shi namiji ne.




Sai da Abba ya tsorata ganin wadda aka nuna masa a matsayin yayan sa yasan dai yayan sa dogo ne sannan yana da k'iba amma a nuna masa wannan siririn mutumin matsayin yayan sa su kansu 'yan uku da maman su sunyi mamakin hakan sosai ga Zainabu rik'e da d'anta sai kallon su take yi kamar ranar ta fara ganin su yayin da su ko gane ta ma basu yi ba.




A tsorace Abba ya nufi inda Kawu yake durk'ushe yana kukua ya dafa kafad'ar sa a hankali Kawu ya juya domin ganin Wanda ya dafa shi da sauri Abba ya cika shi tare da ja baya cikin rud'ani ganin yadda yayan nasa ya koma gaba d'aya fuskar sa sai k'ashi da fata.



Ganin Abba ne da sauri Kawu ke k'ok'arin tashi tsaye domin tabbatar da abinda ya gani amma ya kasa da sauri Abba ya k'arasa ya d'ago shi ya mik'e idanun kawu Bala na zubar da hawaye ya ce "Habu," Abba bai damu da yadda jikin Kawu yake tumu_tumu ba ga wani tsami da yake yi na rashin wanka da wanki ba ya rungume kawu shima yana hawayen ya ce "Yaya me yake faruwa da kai haka ne?" Rungume Doctor Sameeha ta yi itama tana kukan tausayin Kawu Bala su ma su Sabeeha ya basu tausayi sosai.



Kawu Bala ya bud'e baki ya ce "Habu kayi hak'uri nasan nayi maka ba daidai ba," saurin rufe masa baki Abba ya yi ya ce "Ya isa Yaya a cikin mutane muke yanzu muje mu tafi," Zainabu ce ta taso da d'anta a hannu tana kukan haka ma Lantana.



Doctor kuwa ta kasa cewa uffan tana rungume da Sameeha dake aikin kuka wajen ta Lantana ta nufa tana kuka ta ce "Maryam kece," Doctor ta ce "Ni ce lantana," haka ma Zainabu ta k'arasa tana wani zare ido harara Sabeeha ta galla mata bawai bata tausaya mata bane a'a sai kawai tunawa da irin cin mutuncin da Zainabu tayi musu da ta yi Sabreen ma tsaki ta ja.



Tuni jikin Zainabu ya yi sanyi Doctor kuwa wani kallo ta yiwa Sabreen jin tsakin da ta ja Sabeeha kuwa mazewa ta yi ta fara danna wayar ta yayin da Sabreen ta kalli wani gefe daban.




Abba ne ya rik'o hannun Kawu ya k'arasa gaban su Doctor ya ce "Doctor Ina ga mu tafi gida kawai," juyawa suka yi suka nufi motor yayin da 'yan gari kowa ke jinjinawa Abba da abinda ya yi sanin yadda Kawu ke muzguna masa.




Doctor kuwa duk da haka sai da suka gaisa da zuwaira Mai abinci sannan suka wuce zuwa mota yayin da Sabeeha fafur tace bazata shiga mota d'aya da Zainabu ba duk da hararar da Doctor ke yi mata ganin tana neman tara musu jama'a kamar k'aramar yarinya yasa Abba cewa shikenan kuzo mu tafi a nan.




Gaban mota Sabeeha ta shige Sabreen ma ta shige bayan mota ta zauna Wai itama bazata zauna mota d'aya da su kawu ba Sameeha ce kawai ta shiga gaban motar yayinda Kawu Lantana da Zainabu ke bayan motar da su Sabeehan suka zo a ciki suka tafi.



Tun a mota Doctor ta fara yi musu fad'a baji ba gani Sabeeha sai tura baki take yi Sabreen kuwa shiru ta yi tana sauraren yadda Doctor taita fad'a kamar ta ari baki Abba dai shiru ya yi baice komai ba domin yasan cewa tabbas 'yan uku sun wahala sosai wajen kawu Bala dan haka da wuya sun karb'e su da wuri da haka suka k'arasa gida.




Idanu waje Kawu Lantana da Zainabu ke kallon gidan domin ganinsu suke yi kamar a k'asar turai suna gama parking Sabeeha ta bud'e mota ta fice ta shige cikin gidan da kallo Doctor ta bita ta girgiza kai kawai Sabreen ma kallo su Kawu basu ishe ta ba ta shige cikin gidan.




Doctor ta kalli Sameeha dake gefe a tsaye ta ce "Daughter shiga ki Kira mun Halima kuzo tare wad'an can 'yan uwan naki kuwa ni da su ne," Sameeha ta ce "Mama kiyi...,"




"Kinga ba abinda na saki kenan ba wuce ki tafi," shigewa falon Sameeha ta yi Mama ta waiga ta kalli Kawu ta ce "Amma Yaya kamar baka da lafiya ko?" Lantana ta ce "Eh Wallahi wajen sati biyu kenan,"





Doctor ta ce "Ayyah me yake damun ka?" Nan Kawu ya yi mata bayanin yadda yake ji take Doctor ta gane ulcer ce ke damun Kawu mai zafi Sameeha da Halima ne suka k'arasa wajen Doctor ta kalli Halima ta ce "Yawwa Halima ga bak'i munyi kije da su wancan k'aramun part d'in nasan a gyare yake ki nuna musu yadda ake amfani da kayan toilet d'in zasu yi wanka sannan ku basu abinci suci yanzu zan ba Faisal kud'i ya siyo musu kayan sawa kafin zuwa gobe mu fita shopping Faisal idan ka dawo kaba Halima kayan ta Kai musu sannan ke kuma idan zaki Kai musu abinci ki sanar dani na baki magani ki kaiwa Yaya yasha kafin gobe muje hospital," sannan ta kalli Kawu Bala ta ce "Yaya idan Kun kammala sai ku shigo ciki," Kawu Bala kuwa kasa magana yayi domin mamakin halin kirki irin na Maryam.




Kud'i Doctor ta zaro a jakar ta ta bawa Faisal ta ce "Ka dai ji bayani na ko?" Ya ce "Eh madam," Doctor ta ce "Ku je Halima," ta ce "To madam," suka tafi Doctor Kuma ta ja hannun Abba dake mamakin ta shima suka shige cikin falon.
[10/25, 8:46 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️




RUBUTAWA DAGA
HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ)






SADAUKARWA GA
MY DAUGHTER SABEEHA
BILKISU Z.YA'U (🅱️K)
AISHA MAGAJI DABO (AMA)





Page 22


Har d'aki ta ja Abba sannan ta shige bathroom ta had'a masa ruwan wanka ya shige domin yin wanka Doctor ma ta tafi d'akin ta tayi nata wankan.




Sabeeha kuwa tana shiga d'akin su cire kayan jikin ta tayi ta d'aura towel ta fad'a wanka tana fitowa ta samu Sabreen zaune tana danna waya wuce ta Sabeeha tayi zuwa gaban mirrow ta yi shafe_shafen ta ta zira wata doguwar riga marar hannu maroon tasa hula a kanta maroon tayi kyau kamar yar baby gashin gaban goshinta ya kwanta luf gwanin sha'awa ta kalli Sabreen ta ce "Dear wallahi zuciyata tak'i yin sanyi yau da naga Zainabu sai naji tsanar da nake mata tafi ta ko yaushe har tsanar da nake mata tafi ta Kawu saboda mun girme ta amma hakan baisa ta raga mana ba," ajiye wayar Sabreen ta yi a gefe ta ce "Wallahi kuwa nima haka amma ki duba yadda Sameeha dear ta kama kuka kamar ta manta sanda Zainabu taso kashe ta ba,"




Tashi Sabeeha ta yi ta ce "Ah to nima dai abinda nagani kenan ni bara na fita," daga haka ta fice daga d'akin Sabreen kuwa ta shige toilet don yin wanka.




Sabeeha na sauka down stairs lokacin Mama ta fito daga d'akin ta zata je na Abba "Ke zonan," Doctor ta fad'a wajen ta Sabeeha ta nufa ta ce "Gani Mama," hararar ta Doctor ta yi sannan ta ce "Kunsan Allah ku kiyayeni a cikin gidan nan ku abinda ku ke yi haka ku ka ga ya dace Yaya fa yayan mahaifin ku ne Zainabu yar uwar ku ce ku duba halin da suke ciki haka ya kamata kuyi musu?" Tura baki Sabeeha ta yi ta ce "Mama basu da mutuncin fa dukan su,"




"Rukayya Wallahi ki fita a idona na rufe matsa mun a nan ko yanzu ranki ya b'aci Wallahi," kitchen Sabeeha ta nufa tana buga k'afa ajiyar zuciya Doctor ta sauke tana bin Sabeeha da kallo a zuciyar ta ta ce yaran nan sai a hankali zasu sauko nasan dama za ayi haka ta nufi d'akin Abba.





Abinci Sabeeha ta zuba ta koma d'akin su ta ci sannan ta tashi ta yi alwala ta yi sallah ta kwanta saman gado take bacci ya d'auke ta.




Tana baccin ne ta ji ana tashin ta juyi ta yi ta bud'e idanunta ta sauke su akan Sameeha ta ce "Dear yadai?"



"Kizo inji Mama tana down stairs kuma yanzu fa," tana fad'ar haka ta juya ta fita tashi Sabeeha ta yi ta gyara zaman hular ta tabar d'akin.




Tunda ta fara sauka ta hango su Kawu Bala a falon d'an d'auke kai Sabeeha ta yi ta ja k'aramun tsaki ta k'arasa falon kusa da Sameeha ta zauna ta ce "Mama gani," shiru Doctor ta yi mata.



Abba ya kalli Kawu ya ce "Yaya lafiya kace duk mu taru anan bayan baka da lafiya ai kamata ya yi ka kwanta ka huta," Kawu Bala kuwa hawaye ne ya zubo a fuskar sa ya ce "Habu dan Allah ka gafarce ni kuyi mun aikin gafara nayi maka abubuwa da dama a rayuwa nasan ban cancanci yafiya a wajen ku ba tun muna yara nake k'untata maka har zuwa girman mu Habu duk farke maka shagon da ake yi nine nasa da

Please Login or Register in order to submit comment