Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gumi ta ce "Wallahi Malam mantawa nayi ranar gidan Zainabu na wuni shiyasa," tsaki Kawu ya ja ya ce "Ai shikenan sai muje muyi ta fama tunda kin dai ji abinda bokanya ta fad'a aikin banza aikin wofi," yana fad'ar haka ya yi gaba abinsa.



B'angaren su Sabeeha kuwa wani dank'areren gida suka ga an nufa gidan ya tsaru iya tsaruwa upstairs ne sannan bai da wani girma amma ya had'u matuk'a da.




Ana bud'e musu gate suka shiga da motocin su suka yi parking sannan suka shiga cikin falon gidan da shima ya had'u sosai 'yan aiki ne ke kai da komo a falon zama suka yi akan kujeru Rinaz ta kalli d'aya daga cikin 'yan aikin ta ce "Halima mama fa?" Wacce aka yiwa maganar ta ce "Tana bedroom d'inta," tashi Rinaz ta yi ta nufi d'akin Doctor Maryam tana shiga ta samu tana wanka falon ta koma ta zauna suka cigaba da fira.



Bayan wajen minti talatin motocin Maleek suka yi parking a compound d'in gidan Doctor Maryam fitowa sojojin sa suka yi suka zagaye wacce yake ciki.





Salman ne ya bud'e masa mota a hankali ya ziro k'afar sa sannan ya fito gaba d'ayan sa wayyo ya had'u iya had'uwa har ya gaji da yin kyau shadda yasa blue black sai shek'i da kyalli take yi color d'in ta matuk'ar yi masa kyau tare da fito da hasken farar fatar sa da kullum k'ara kyau take yi kansa ba hula sai bak'in gashin kansa daya sha gyara bana wasa ba askin kan nasa ma abin kallo ne sai kyalli yake yi kamar a tab'a saboda d'aukar hankali.



Bak'in tsadadden agogon dake hannunsa ya kalla ya lumshe manyan idanunsa mai d'auke da zara-zaran eye lashes sannan ya kalli Salman ya ce "Kira mun Umar a waya," yana d'agawa Maleek ya ce "Yane na iso," daga haka ya katse kiran.



Daga can Umar ya mik'e ya ce "Mu k'arasa ciki," wata k'ofa suka nufa suna shiga a tare dukan su suka furta "Wow," domin wajen ya had'u sosai yasha decoration ko ina sai walwali da kyalli yake yi ga wasu fitilu masu color da suke haska gurin wajen sai tashin k'amshin wani d'addan turare yake yi ga k'amshin snacks da kajin dake wajen ga kuma k'amshin turaren su da Kuma sanyin Ac ga kuma wani music dake tashi a wajen mai kwantar da hankali.





Tuni Sabreen da Fauwaz suka fara falla hoto hakama Sameeha da Umar su Rinaz da su Aysha ma lalacewa suka yi wajen d'aukar hoto.




Murmushi Sabeeha ta yi tana tunanin da tuni itama tana nan suna nasu hoton da MG tsayawa ta yi tana kallon su har sai da su Sabreen suka jata sannan aka cigaba da hoton da ita.



Sai da suka gama hotuna sannan su Sabeeha suka nufi inda aka tanada domin su suka zauna cake kuwa yafi kala ashirin a wajen wannan yana wane wannan wannan yana wane wannan wajen kyau da tsaruwa.



Tura k'ofar wajen aka yi aka shiga da sauri Sabeeha ta kalli k'ofar saboda k'amshin turaren sa da taji ya cika falon aikuwa tana kallon wajen suka had'a idanu.




Kallo d'aya ya yi mata ya gane ta saurin kawar da idanunsa ya yi ba dan komai ba sai dan fad'uwa da gaban sa ya yi domin wata soyayyar ta ce ta k'ara dasuwa a zuciyar sa.




Sabeeha kuwa a zuciyar ta ta ce Yanzu kam na gama yadda ya hak'ura dani saboda ko san ganina baya yi sake kallon sa ta yi a zuciyar ta ta ce Masha Allah irin wannan azababben kyau haka gaskiya Allah ya yi halitta a wajen nan.




Kallo ne ya koma kansa saboda had'uwar da ya yi duk da wajen ba wani wadataccen haske Salman dake bayan sa ne ya ja masa kujera ya zauna ya fara danna wayar sa sai basarwa yake yi domin bai cika son kallo ba.


Umar ne ya fara gabatarwa tare da yi musu birthday wishes Fauwaz ya yi Rinaz ma ta yi haka ma su Dija da Aysha suka taya su murna cikin had'adden turancin su wanda ba gargada domin 'yan boko masu ji da aji da ilimi aka had'a a wajen.




Kallo ne ya koma kan Maleek domin shima ya taso ya yi musu wishing amma bai ko motsa ba sai ma danna wayar sa da yake yi Umar ya ce "MG gare ka we are waiting,"




"For what?" Maleek ya fad'a ba tare da ya kalli inda Umar yake ba.




Umar ya ce "U have to say something," hararar Umar d'in ya yi ya ce "No need," har Fauwaz ya bud'e baki da niyyar magana Maleek ya d'aga masa hannu saurin jan bakin sa ya yi ya tsuke.




Sabeeha kuwa bata san sanda ta saki murmushi ba saboda ganin hararar da ya watsawa Umar a hankali ba tare da kowa ya ji ba ta ce "komai ya yi kyau yake masa,"



Murmushi Umar ya yi sannan ya fito da gift d'insa wasu diamond rings ne da diamond watch masu matuk'ar kyau da tsada ya d'auko a cikin wasu akwati ya bawa kowa d'aya sai dai akwai banbanci a zoben Sameeha domin nata anyi masa ado da shape d'in heart.



Godiya suka yi sannan Fauwaz shima ya gabatar da nasa gift d'in shima rings ne sai agogunan gold masu kyan gaske nan ma suka yi godiya Rinaz ma ta yi musu kyautar rings Dija ma da Aysha duk suka basu gifts.




Suna gamawa kowa ya mai da hankalin sa kan Maleek sarai yasan kallon sa suke yi mik'ewa ya yi tare da zaro wasu k'ana nan akwati masu kyau guda biyu daga aljihun sa ya nufi gaban table d'in.



Kowa mamaki yake yi ya kits d'in guda biyu yana zuwa ya ajiye d'aya gaban Sameeha d'ayar kuma gaban Sabreen.



Kowa na wajen tambayar kansa yake yi to Ina na sabeeha fa Sabeeha kuwa k'asa ta yi da kanta ita kanta tasan bata cancanci kyauta daga Maleek ba sai dai lokaci d'aya ta d'aga kanta jin tsayuwar sa a gaban ta.



Hannun sa ya mik'awa Salman dake bayan sa wani had'adden kwali Salman ya mik'a masa shi kansa kwalin abun kallo ne farine tas sai adon Red flowers a jiki sai tashin k'amshi yake yi ya ajiye gaban Sabeeha sannan ya juya ya kalli mutanen wajen ya ce "Kyauta na ta gaba na zuwa," ya kalli Salman dake tsaye.




Hanyar fita Salman ya yi domin ya gane ma'anar kallon.



Kowa zuba ido yake yi domin ganin kyautar Maleek ta gaba.
[10/25, 7:43 PM] Autar Marubuta: ❤️'YAN UKU❤️




RUBUTAWA DAGA
HAFSAT MAGAJI DABO (RUHAZ)





SADAUKARWA GA
MY DAUGHTER SABEEHA
BILKISU Z.YA'U (🅱️K)
AISHA MAGAJI DABO (AMA)






Page 16


Bayan fitar Nasreen zama su Sabeeha suka yi akan kujera kowa zuciyar sa fal mamakin abinda su Nasreen suka so aikatawa Maleek.



Sameeha kuwa har lokacin hawaye take yi ta ce "Wai dama har yanzu akwai masu irin wannan zuciyar a duniya?" Rinaz ta ce "Hmm gasu ma sai dai mu yi addu'ar Allah ya tsare mu daga sharrin su," suka amsa da "Ameen,"



Sabreen ta ce "Ai dama da ganin wannan rafkeken kai na Nasreen bazai yi ja ba," duk da suna cikin jimami sai da suka dara Fauwaz ya ce "Wallahi kuwa my love munsani ma dake muka kyale su," Sabreen ta ce "Wallahi kuwa da wani k'ananun idanun ta kamar na 'yan china," nan ma dariya suka yi banda Sabeeha da take zaune har lokacin bata ce komai ba can ta mik'e tabar falon.



Direct part d'in Maleek ta nufa ko d'aya a cikin sojojin dake tsaron k'ofar ba Wanda ya hana ta shiga domin Salman ya sanar da su matsayin ta a wajen Maleek har Sara mata suka yi ita kuwa shigewa kawai ta yi.




Tana shiga ta hangi Maleek kwance saman kujera idanunsa a lumshe kamar mai yin bacci k'arasawa ta yi sannan ta zauna k'asan lallausan carpet d'in dake malale a wajen tana kallon sa.



A hankali ya bud'e idanunsa ya sauke su a fuskar Sabeeha sannan ya tashi zaune yana mai cigaba da kallon ta ita kuwa ta yi k'asa da kanta tana wasa da yatsun ta.



"Say it out kamar da magana a bakin ki," Maleek ya fad'a yana k'ura mata ido a hankali ta d'aga kanta suka had'a ido a hankali ta ce "Dama tambayar ka zanyi meyasa su Umman Nasreen suke son kashe ka?" D'an murmushi ya yi ya ce "Bansan ainahin dalilin ba amma dai nasan Umman Nasreen ta tsane ni tun ina jariri,"




Zare ido Sabeeha ta yi ta ce "Jariri fa to meyasa hakan?" Ajiyar zuciya Maleek ya sauke ya ce "Sunan kaka na Alhaji Muhammad Mai dala wato wanda ya haifi Daddy kenan yana da mata biyu Hajiya Sadiya da Hajiya Hauwa'u suna zaune zaman lafiya da kwanciyar tare da yaran su Uncle da Daddy shi Uncle d'ane ga Hajiya Hauwa'u Daddy Kuma yaron Sadiya amma idan kaje gidan baza ka iya bambance hakan ba domin suna son junan su da yaran su suna basu kulawa sosai suna gatata su sosai," d'an shiru Maleek ya yi sannan ya cigaba da cewa "A inda aka fara samun matsala shine a duk sanda aka zo ba da result a makaranta Daddy ne ke d'aukar first class saboda yana da k'ok'ari sosai sab'anin Uncle da yake d'aukar kusan na k'arshe duk da ba ajin su d'aya da Daddy ba kuma sosai Uncle yana zuwa makaranta kuma yana Mai da hankalin sa sosai sai dai shi haka Allah ya yi shi kwakwalwar tasa bata d'auka a duk sanda aka raba result suka kaiwa mahaifin su sai ya yiwa Daddy kyauta duk dan saboda Uncle ya k'ara dagewa amma ba wani canji abun sai ya damu Uncle sosai tun yana yin kuka har ya dena ya dawo tsangwamar Daddy da nuna masa tsana shi kuwa Daddy baya damuwa domin sau da yawa ko mahaifin su ya ba Daddy kyauta sai ya barwa Uncle abu kamar wasa Uncle ke nunawa Daddy k'iyayya da mahaifin su ya lura da hakan sai ya fara k'ok'arin daidaita tsakanin su amma abu yaci tura tun yana Nasiha ya dawo fad'a daga k'arshe har duka amma ba abinda ya canja haka iyayen suka zuba musu ido lokacin da Uncle ya gama secondary School d'insa sai aka tura shi k'asar waje karatu yayin da Daddy ke secondary ko da shima ya gama sai aka tura shi Dubai karatu yayinda Uncle ke London mahaifin su ne ya yanke shawarar k'in had'a su karatu a k'asa d'aya domin rashin jituwar dake tsakanin su a haka uncle ya gama karatun sa ya samu aiki a can Landon d'in wani hutu ne da Daddy ya je gida ya samu mahaifin su baida lafiya bayan gajeriyar jinyar da ya yi Allah ya yi masa rasuwa sunyi kukan rashin sa sosai haka ma matan sa haka Daddy ya cigaba da karatun sa yana gamawa ya fito da result mai kyau sai rububin d'aukar sa aiki ake yi a k'asashe daban daban kasancewar sa architecture ne a wani campany a Dubai d'in Daddy ya fara aiki yayin da bak'i ciki yake fal zuciyar Uncle domin ganin babban matsayin da Daddy ya samu a campany ga salary d'in Daddy yafi nasa a haka rayuwar su ta cigaba Daddy na zuwa Nigeria sosai domin duba lafiyar mahaifiyar sa ga Kuma kud'ad'e dake shigowa tako Ina domin zuwa lokacin Daddy Yana da campanies nasa har guda biyar a lokacin ne kuma rashin lafiya ya kama mahaifiyar sa har k'asar waje Daddy ya fitar da ita amma satin ta d'aya ta rasu Daddy ya yi kuka sosai haka ma hajiya Hauwa'u domin sunyi zaman lafiya da Sadiya a haka Daddy ya koma bakin aikin sa wata rana Daddy ya je malesia domin duba wani campany nasa dake can a nan ne ya had'u da Ummi suka k'ulla soyayya har Ummi ta bashi dama ya tafi Nigeria ya samu iyayen Ummi aka gama magana domin Mahaifin Ummi yasan mahaifin Daddy hakan ne yasa da Ummi tazo hutu bata koma ba ta yi aure Daddy ya d'auke ta suka koma Dubai da zama arzik'in Daddy kullum k'aruwa yake yi domin yanzu Campanies d'in sa goma ne kowa yasan shi a haka har maganar auren Uncle ta tashi amma Uncle bai ko fad'awa Daddy ba amma hakan bai hana Daddy d'aukar Ummi su zo bikin ba sai dai basu samu kallon arzik'i wajen Uncle ba sai ma yana d'ora idanunsa kan Ummi ya ji ya mugun tsanar ta domin tafi amaryar sa kyau da ilimi hakan ne yasa uncle ya ji kamae ya fasa auren domin shi baya so a komai Daddy ya fi shi haka aka gama shagalin biki Uncle ya tafi da amaryar sa Landon su Daddy ma suka koma Dubai," shiru Maleek ya yi Sabeeha ta ce "Cigaba please," kallon ta Maleek ya yi ya ce "Bakina ya gaji,"



Langab'ar da Kai ta yi ta ce "Please," d'an shiru ya yi sannan ya cigaba "Bayan auren Uncle ba dad'ewa Hajiya Hauwa'u ta auri wani d'an kasuwa mai suna Alhaji sammani sai dai auren bai dad'e ba itama ta rasu lokacin bayan wata biyu da faruwar hakan aka kori Uncle daga wajen aiki saboda kama shi da laifin cin amana da aka yi haka ya d'auki hajiya Asiya suka koma Nigeria duk wasu kud'ad'e da Uncle ke da shi haka suka saka a gaba suka cinye shi da Hajiya Asiya daga nan ne fa suka fara rayuwar talauci wata rana labari ya jewa Daddy cewar d'an uwan sa na cikin wani hali ko da Daddy ya ji labari sai da ya yi kuka domin jin halin da d'an uwan sa da bai da kamar sa ke ciki Wai ace d'an uwan sa ne ke cikin halin talauci bayan shi gashi baisan adadin dukiyar sa ba ba Wanda baisan shi ba babu shiri Daddy ya tafi Nigeria lokacin Ummi tana da ciki lokacin da yazo Nigeria ya ga halin da Uncle yake ciki sosai Daddy ya yi kuka yana cewa idan laifi ya yiwa d'an uwan nasa ya yafe masa domin bai cancanci haka daga gare shi ba ace d'an uwan sa yana cikin wannan hali amma sai dai ya ji a gari shi Kuma yana can da dukiya me zai yi da ita idan bai taimakawa d'an uwan sa ba duk kukan da Daddy ke yi k'in sauraron sa Uncle ya yi sai da Daddy ya yi sati guda yana rarrashin Uncle akan ya yi hak'uri su bishi zuwa Dubai amma Sam Uncle yak'i yadda haka Daddy ya fara Shirin komawa Dubai domin ya baro Ummi ita d'aya a daren ranar ne Hajiya Asiya ta ba Uncle shawara akan cewar ya ce da Daddy idan har da gaske Yana son taimakon sa to ya dawo Nigeria da zama su zauna tare Kuma a gida d'aya domin so take su cinye duk abinda Daddy ya mallaka take Uncle ya yadda da shawarar ta domin itama Hajiya Asiya halin su d'aya da mijin nata wajen bak'in ciki da hassada ko da Uncle ya samu Daddy da maganar sosai Daddy ya yi farin ciki Kuma ya yadda da hakan domin ko ba komai ya samu hanyar kyautatawa d'an uwan sa ko da Daddy ya fad'awa Ummi itama ta yi farin ciki ko ba komai itama zata baro Dubai domin ta ishe ta gashi idan tana kusa da gida zata fi jin dad'i saboda iyayen Ummi suna Abuja tana da yayye biyu maza sai k'anwar ta mace itama a Abuja ta yi aure," cikin gajiya da magana Maleek ya kalli Sabeeha da ta yi shiru tana sauraron sa ya ce "Zan k'arasa miki wataran yanzu na gaji," mak'e kafad'a ta yi ta ce "Ni dai uhm uhm yanzu nake so,"




D'an girgiza kai ya yi ya ce "Ok kina ji ba cikin k'ank'anin lokaci Daddy yasa aka gina musu wannan gidan shi da Uncle suka dawo sai dai Ummi sam bata jin dad'in zaman gidan saboda Daddy baya samun zama sannan b'angaren zaman ta da Hajiya Asiya kuma ba dad'i domin wani irin kishi Hajiya Asiya ke nunawa Ummi kamar kishiyar ta ga rashin mutunci na yau daban na gobe daban Ummi kuwa ko da wasa bata tab'a gayawa Daddy ba domin tana son a zauna lafiya a haka har aka haifeni Daddy ya yi farin ciki sosai ya yinda Uncle k'iri-k'iri ya nuna bai ji dad'in hakan ba shi da matar sa saboda basu so Daddy ta samu d'a namiji ba domin gani suke yi nan gaba wannan yaron zai kawo musu tsaiko a lamuran su a haka na tashi cikin kulawar Daddy da Kuma Ummina idan naje part d'in Uncle kuwa da kuka nake barin sa hakan ne yasa na dena zuwa domin tsana suke mun ta musamman kamar ma wacce suke mun tafi tsanar da suke yiwa iyayena gashi na yo kamar Ummina hakan ba k'aramar k'iyayya ya k'ara ja mun ba wajen Umman Nasreen Ummi ma hakan ne yasa ta yanke shawarar ta bawa Daddy ni ya tafi dani can Dubai nayi primary da secondary d'ina a can haka muka tafi da Daddy can nayi primary da secondary school d'ina daga nan ne na sanarwa da Daddy nikam soja nake son zama Daddy kuwa ya amince mun da haka lokacin muka zo Nigeria a nan ne na ga wata yarinya a gidan Ummi ke fad'a mun yarinyar Uncle ce wacce namiji suka so haifa ba mace ba ni kuwa ko kallon yarinyar banyi saboda tun tana k'aramar ta bata da kunya ga rashin girmama na gaba da ita ban dad'e a Nigeria ba Daddy ya turani Russia ni da Salman d'a a wajen k'awar Ummi a bayan zuwan mu Russia munyi shekaru da dama inda aka yi passing out ya yinda na fito da wannan matsayin na MG inda ake ji dani sosai a aikin wanda aikina zai kasance a office ne sai dai ni bani da sha'awar zaman office na fi so duk wani aiki na fita ayi shi dani domin taimakon k'asa ta tunda na dawo daga Russia Nasreen ta nuna cewar tana sona amma ni sam bana son ta domin bata d'aya daga cikin irin matan da nake so sai dai ko da Uncle ya fad'awa Daddy maganar haka Daddy ya dage dan dole aka yi auren a yanzu sai abinda Uncle ya ce da Daddy shi ake yi a gidan nan Wanda na rasa dalilin hakan yayinda ni tsanata ke k'aruwa a wajen su Uncle domin sun san bazan tab'a bari su cuci Daddy na ba Ina tunanin hakan ne yasa Umman Nasreen ta yanke hukuncin kashe ni Wanda ita kanta Nasreen ba tasan ainahin dalilin da yasa Umman ta ta yadda da batun a kashe ni ba Sabeeha gidan nan ana yin wata iriyar rayuwa duk wani kud'i da motoci da Uncle ke da shi duk na Daddy ne Uncle na iya iko da komai na Daddy amma sam baya son jinin Daddy abun na d'aure mun kai na samu labarin Uncle na yin wata sana'a amma har yanzu bansan meye ba na dai sa ayi mun bincike wannan shine tarihin gidan nan,"





Wani tausayin Maleek da Daddy ne ya kama Sabeeha har hawaye ta goge jin yadda Daddy ke k'aunar d'an uwan sa amma shi Uncle ba wanda ya tsana kamar Daddy da matar sa dama yaran su duka.




Mik'ewa Maleek ya yi ya nufi stairs shan gaban sa Sabeeha ta yi ta ce "Tambaya d'aya," cikin gajiyawa da magana Maleek ya kalle ta ya ce "Kiyi mun afuwa malama Sabeeha questioner yanzu kam na gaji ma had'u next time," girgiza Kai ta yi ta ce "Please wannan ne na k'arshe," noding kansa ya yi.




Ta ce "To maganar cutar da naji kuna yi da Ummi fa wane ciwo ke damun ka?" D'an murmushi ya yi ya ce "Ciwon zuciya ne Wanda haka na taso na ganni da shi amma yana dad'ewa bai tashi ba saina shiga damuwa," yana fad'ar haka ya ya wuce.




K'ara shan gaban sa ta yi ta yi k'asa da kanta lumshe ido ya yi ya bud'e a kanta ya ce "Yanzu kuma mene?" Murmushi ta yi ta ce "Dama wata tambaya ce d'aya ta rage shine nace bari na tambaya karna manta," dariya taso ba shi ya dake ya ce "Uhm Ina jinki,"




"Daman cewa nayi yaushe rabon da ciwon ya tashi?" D'an shiru ya yi sannan ya k'ara matsawa gaban ta ya ce "Tun sanda ki ka ce baki sona har yanzu Ina kan shan magani," k'asa ta yi da kanta sannan ta d'aga Kai ta kalle shi ta saki murmushi ta ce "To daga yanzu sai ka dena sha,"



"Meyasa hakan?" Ya tambaye ta tare da k'ura mata ido juya idanun ta ta yi ta ce "Saboda yanzu Ina son ka," wani farin ciki Maleek ya ji a ransa ya ce "To meyasa da d'in baki Sona?" dariya ta yi ta ce "Waye ya fad'a maka ai ko da d'in ina son ka kawai dai akwai abinda nake tsoro ne," murmushin da ya bayyana dimples d'insa ya yi ya ce "Yanzu fa?" D'an kara matsawa gaban sa ta yi ta d'aga idanunta ta kalle shi ta ce "Sai dai idan a mutu a kanka," tana fad'ar haka ta juya da gudu tabar falon dariya ya yi ya haye stairs yana jin yanzu bai da wata sauran damuwa.




Nasreen kuwa da kuka ta shiga part d'in su ta baje akan carpet tana rusa kuka domin sai yanzu da Maleek ya sake ta ta gane ba k'aramun so take yi masa ba da sauri Hajiya Asiya ta sauko daga stairs tana cewa "Mamana lafiya ko har ya mutun?" Banza Nasreen ta yi da ita sai ma k'ara volume da ta yi.




Hajiya Asiya ta ce "Ko baki fad'a ba nasan ya mutu yanzu Ina gawar tasa take?" Kallon ta Nasreen ta yi ta ce "Na shiga uku Umma ya Maleek ya sake ni,"



"Bangane ya sake ki ba yana gawar ya sake ki ko me?" Hajiya Asiya ta fad'a tana son sanin Mai ya faru cikin Kuka Nasreen ta ce "Umma bai mutu ba yana raye gaba d'aya waccan yarinyar ta lalata mana shiri," Nan Nasreen ta zayyane abinda ya faru.




Ba tare da alamun nadama ba Hajiya Asiya ta ce "Kutmar uba shi Abdul-maleek har waye shi da zaici mana mutunci to wallahi duk sai sun gane kuren su,"



"Ni dai wallahi Umma mijina nake so kawai ni ki mayar dani," Nasreen ta fad'a tare da hayewa stairs da ido Hajiya Asiya ta bita har ta b'acewa ganinta.



Su Sabeeha kuwa tana zuwa part d'in Ummi basu dad'e ba Fauwaz ya tafi mayar da su gidan Mama.


Maleek kuwa yana shiga d'akin sa wanka ya yi ya fito cikin bak'ak'en k'ananun kaya ya yi kyau ba k'arya Kai tsaye part d'in Ummi ya nufa.




Yana shiga falon ya samu ba kowa sai ya wuce stairs nan ma ba kowa bedroom ya tura ya shiga da sallama Ummi dake zaune gefen gado ta amsa masa sallamar tare da juyawa ta kalle shi a lokaci guda kuma hawaye na fitowa daga idanunta ga idanun nata sunyi ja sosai.


Da sauri Maleek ya k'arasa ya tsugunna akan lallausan carpet d'in d'akin ya rik'o hannun Ummi ya ce "Ummina lafiya maiya faru?" Cikin hawaye Ummi ta ce "Meyasa Abdul me kayi musu da suke son raba ka da duniya wannan wacce iriyar k'iyayya ce?" Ummi ta fad'a tana hawaye d'an murmushi Maleek ya yi domin yasan hakane yasa Ummi kuka ya ce "Ki kwantar da hankalin ki Ummi su basu isa su yi mun abinda Allah bai mun ba kuma duk abinda suke yi Allah na ganin su," jinjina Kai Ummi ta yi ta ce "Allah ya yi maka albarka ya k'ara karemun Kai a duk inda kake," ya ce "Ameen Ummina addu'ar ki mai tasiri ce a gare ni," ya fad'a yana share mata hawaye.




Tashi Ummi ta yi rik'e da hannun sa ta ce "Taso muje na yima abinci nasan baka ci komai ba," mik'ewa ya yi suka sauka down stairs har kitchen ya bi Ummi wai lallai sai ya taya ta girkin.




Tare kuwa suka shiga tana yi tana cewa ya mik'a mata wani abun har suka gama suka fita falo a daining suka zauna Ummi da kanta ta bashi abincin har ya k'oshi ta kalle shi ta yi murmushi ta

Please Login or Register in order to submit comment