Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cike yake, kowa mamakin Alh Ali yake, yau shine yake dukan Farincikinshi? Da girman Zaid yake dukanshi, yake dukan Sadiya diyar da yake gani itace Yar Gwal, ga matar da yake so kamar ranshi, yau itace yake duka da hannu duk ya galabaitar da ita, rigarta har ya yage har kana iya hango abunda ke ciki, da Zaid ya tashi taimaka mata sai ya sa security su rik'eshi.


Manyan Unguwan sai magana suke mishi suna rokonshi da ya barsu haka, amma be tanka kowa ba.


Muhammad ya shigo da Matarshi Asee, kutsawa sukayi tayi, gidan kamar ana shooting film, kutsawa yayi ya shiga, matarshi ta bi bayanshi, daidai nan Alhaji Zaki ya daga wani katako zai kwala ma Mancy kenan ya karasa da gudu.


"Haba Alhaji, Haba, menene haka? Meya sameka Alhaji? Wallahi ba Girmanka bane? Inalillahi wa ina ilaihir rajiun"


Hajiya Shafa'atu ta dago ta kalli Muhammad da tsana, shi ko Alhaji samun kanshi yayi da maimaita Inalillahi wa ina ilaihir rajiun" waigawa yayi yana kallon su yashe a k'asa, abun alfaharinshi, dukkansu yashe a k'asa.


Hajia Shafa'atu tace "nifa su tafi, ina son na huta" kamar an ingiza shi yace "duk ku fitar min daga Gida, yan iska shegu, duk na tsaneku".


"Alhaji ina kake so suje? Basu fa da inda ya wuce nan" ni wallahi sai sun fitar min a Gida, Muhammadu, ba na k'aunar ganinsu"


DanMakaho ya kalli Labiba sosai yace "Kinsan Unguwar nan kaf, ba wanda nake ganin mutuncinshi irin Yayanki?" Labiba ta murmusa tace "Yayana na da kwarjini" yace "ya min abunda ba zan taba mantawa ba, zuwa yayi ya dago ni ya rungumeni, ya lallasheni ya rada min a kunne, ka zama k'arfin Mahaifiyarka da kanwarka, tashi ka rik'o Dalo, muje gidana muyi magana".


Umurninshi na bi, na tashi na mik'ar da Dalo da ke kwance magashiyan a k'asa. Yayanki ya matsa kusa da Matarshi, ya karbi jaririn hannunta yace ki taimaka ma Mancy, bin umurninshi tayi, ta daga ta ta riko hannunta, ta ja ta, ba gardama Mancy ta bi bayanta.


Sosai mutane suka tausaya mana, ina jiyo muryar wani yana cewa "Me ya samu Gidan nan? Me ya samu jin dadi da walwalar Gidan nan" wani yace "ko nayi rantsuwa ba kaffara, wanchan ce, itace Ummul Abais" Wallahi DanMakaho Allah ya saka muku, Allah ya bi muku hakkinku".


Ba mu ce komai ba muka fita zuwa Gidan Yayanki, kan tabarman da suke zaune na kwantar da Dalo, na yi hanyar fita Mancy tace ma Yayanki donAllah kamo min shi, a wahalce take magana.


Mallam Muhammad yace ina zaka?" Zuwa zanyi ya gaya min dalili? Me muka mishi ya tsane mu, Mallam Muhammad Babanmu ya wulakanta mu gaban mutane, Babanmu ya daga hannu ya dake mu gaban mutane, me muka mishi? Me ya chanzashi".


"Zaid"


Mancy tayi kirana.


Na dan choge na tsaya tace "kazo ka zauna, donAllah, kana da Uwa, and i promise you, ba za ku bar Gidan Ubanku ba"


"Mancy, zaman me zamuyi ba kya ciki? Ta ya zamu fara rayuwa a Gidan nan ba da ke ba, Mancy kafarki kafarmu Allah".


Mancy ta girgiza kai, ta kawar da maganar "Maman Amira DonAllah kina da Panadol a ba Sadiya?".


Eh barin dauko mata, ta shiga Ciki, baban Amira ya bi bayan Matarshi.


Mancy ta matso kusa dani ta rik'oni tace "Stay Strong, kaine Gatan Dalo in bana nan".


"Mancy".


Ta katseni "Zaid, kayi min Alakawari, no matter what happens, ba zaka taba barin Gida ba, aure kawai zai rabaka da Gida, zaka kula da Sadiya, zaka kula min da kanku"


"Mancy"


"Zaid, DonAllah".


"Mancy, ba ki ga kallon da Baba ke mana ba? Ya tsanemu fa"


"Still Zaiduna, you wont leave home".


Kai na gyada mata nace "I wont leave home".


Dalo ta sha panadol, amma masassara ta rufeta, kinga yanda muka damu, lokacin Maghrib Yayanki ya sani Alwala don zuwa masallaci, na bar Mancy da Dalo tare da Antynki.


A waje sai kallona ake tayi, wai kinsan me nagani kofar Gidanmu? Labiba ta girgiza kai yace "Katuwar Mota nagani, tana kwashe kayayyaki wanda kallo daya na musu na san kayan dakin Mancy ne da nawa" nufansu nayi, amma yayanki ya rikoni tare da girgiza min kai, yace mu tafi Masallaci kaji?" Jikina rawa yake, idona ya ciko da hawaye, lallai baba yana son Wulakanta mu.


A gidan Yayanki muka kwana, daki daya ya bamu, Mancy tayi ta mishi godia, yace "haba Mancy, ai kowa ya san ke Uwa ce a Anguwar nan, duk me zamu miki ba zamu taba biyanki Alheranki ba".


Washegari Mancy tace "Zaid, Sadiya, yau zan koma Kano gidan Yaya"
Nace Mancy Dalo bata da karfin jikinta Masassara takeyi, ina zaki tafi ki barta? Ni ya zanyi? Mancy karki tafi? Kar ki juya mana baya donAllah, kar ki barmu, atleast not now, kina ganin korar da ya mana, na gya miki an fitar da kayayyakinmu tas".


Mancy tace "Zaid ya zanyi? Wa ke gareni duk dunia in ba Yayana ba? Ina zanje? Sakina yayi fa, saki 3, ina na nufa? Nan gidan zan ta zama? Ai ba zaiyiwu ba, kuna da Mahaifi, da ranshi, yanzu ba anjima ba zan raku Gida, nikuma na wuce, ina so kuyi hakuri da duk yanda rayuwa ta zo muku, donAllah kuyi hakuri, ina sonku sosai, fiye da rayuwa da kanta".


"Mancy"


Ta katseni tace "Zaid mun riga da mun gama maganar nan, dole ku koma Gidan ubanku, whatever happens he is still your Father, ku tashi mu tafi, so nake kafin karfe 11 in isa Kano".


Labiba banson ma Mancy gardama don wallahi a daren ranan bata runtsa ba, a kan idona tayi ta kuka, zuciyata ta karye amma sai nayi kamar bacci nake, banson ta sha wahalata shiyasa kawai na share, na rike dalo sosai ta ma Yayanki Godia, muka fita muka nufa Gida, dukkanmu gabanmu na faduwa.


Karfe 8 saura muka shiga Gida.
Da sallama Mancy ce me k'arfin halin Rafka Sallama.
Wata Yarinya da bata wuce saar Dalo ba ta fito daga kitchen tana mana kallon wulakanci, sai ga wani shikuma ya fito daga daki wanda nawa ne.


Hannayenmu Mancy ta ja, har cikin parlo, ta zaunar damu, Nasiha ta cigaba da yi mana.


Sallama aka sake yi muka amsa Yan Gidansu Babanmu ne, su Aunty Asabe da Baba Sani, Maza da Matansu, sun kai su 15. Wurin mu suka nufa, Mancy ta tashi ta taryesu da faraa, suko kallon tausayi suke mata.
Ina kwananku muka gaishesu, suka amsa Baba Sani yace "Maryama ashe abunda ya faru kenan? Wallahi sai yau da asuba wani abokina ke gaya min" tace "Ya muka iya da k'addara Baba Sani, zama ne ya k'are" duk su Aunty Asabe suka ma Mancy Jaje don sosai suke sonta.


Wannan yarinyar tayi hanyar Dakin Baba da gudu ta na kiran Mummy, Mummy zo kiga wasu sun shigo mana Gida.


Da ido duk muka bita, ba da jimawa ba sai ga shi sun fito Mama da Anty Shafa'atu.


Da Mamaki kowa yace "Shafa'atu"
Ita ko ta shigo ta na yatsuna Baba na binta a baya kamar Rakumi da Akala.


"Su waye suka shigo mana Gida da farar safiya kamar masu bin bashi?"


Kamar kare baba ya fara haushi "Eh.. su waye suke mana Sauko da sassafen nan?"


Asabe tace "Yaya mune, mai Shafa'atu takeyi a gidan nan?"


"Shafa'atu Matata ce, Jiya aka daura mana Aure a Jos, dama chan kune munafukan da kuka sani Sakinta"


Nan aka fara kallonkallo.
Mancy ta mik'e da alamu ba su ma lura da mu ba tace "Alhaji ka sa an firda min kaya ina aka kaisu?" Kamar wuta ya taso, Gidan da na daukoki chan nace a kai maki, don maita ashe baku tafi ba?".


Tace "Nagode da ka sa a kaimin kayyayakina, tafiya kuma yanzu zan wuce Kano, ga dai Yaranka nan".


Shafa'atu tace "Alhaji nan zata bar maka su" nan ya hayayyak'o "Kai ku fitar min a Gida, Wallahi ba zasu zauna min a Gida ba".


Baba Sani yace "Ahh Yaya, ina zata kaisu? Tunda ka saketa, ai yara nakane, Ina zata da Zaid dan Shekara 25 Sadiya yar shekara 15?".


Wani abu kamar Hauka Baba ya fara "Sani ka fita Idona, ina ruwanka da Sabgar Gidana? In yaran kake so ka dauke su ka tafi dasu, nidai ku fita harkana, banda 'ya'ya in ba Annah ba ita kadai ce diyata".


"Wacece Annah?" Injisu. Aunty Shafa'atu tace "Our Only Daughter ga ta tsaye" kowa ya bi Annah da ido, sai faman harare harare take.


Su Asabe suka fashe da kuka, Waiyo Yayanmu me aka maidaka? Zaka dauki diyar da ba taka ba kace itace kadai diyarka? Yayanmu ka manta yaranka mafi soyuwa gareka Zaid da Sadiya?".


Shafa'atu ta fashe da kuka cike da kissa "Yanzu haka Alhaji yanuwanka zasu dinga min gori?ni gaskia ka sakeni ba zan iya ba, dama chan yanuwanka sun tsaneni".


Hargagi ya fara "Kai Buhun Uban da ya k'ara cewa Zaid da Sadiya ne mafi soyuwa a gareni, kai zan fa kulleku, ku fitar min a gida dukkanku, wallahi duk ku fice min, na sake ganin kafar dayanku a cikin Gidana sai na sa a kulle ku a Cell, yan iska, Matsiyata".


Ya juya garemu yace "Ku kuma na sake bude ido na ganku a gidan nan wallahi zan iya kasheku, don baku san yanda nakeji game daku ba na tsaneku sosai".


Wuf Mancy tayi ta mik'e tsaye "Alhaji Sai ka Kashe su fa kace?" Kina waswasi ne? To ki bari na k'ara ganinsu a cikin Gida kika ga mai zan musu.


"Alhaji ban san mai sihiri ya maidaka ba, Yaya Asabe sai kun tashi tsaye kan Danuwanku, a baiyane kunga dai ba yin kanshi bane, sai kuna sanya shi a addua, nima zan taya ku da Addua a matsayinshi na Uban 'ya'yana amma a yanzu zan dauki mataki, duk abunda ya sami yarana a cikin Gidan nan to shine".


Shafaatu tace "to ki tafi dasu mana in ba kya son komai ya samesu, ai rufin Asirinsu su biki kawai, don ko be kashesu ba, zaman gidan nan sai ya gagaresu, ba Ubanda zai tsaya musu duk fadin Kt, so kinga da su biki daga baya gwara kin tasa keyarsu kun wuce yanzu".


Mancy tace "Abunda ba ki gane ba Hajia Shafa'atu shine, Zaid da Sadiya ba inda zasu, ba wanda zai rabasu da Gidan Ubansu, ko da Uban nasu ne kam, kuma in kinga dama duk ranar Allah ki dinga sa wuk'a kina yankar namansu kuna miya, sai kuma wanda zai tsaya musu? Allah, shi zai tsaya musu, ki ja dashi in kina iyawa".


Ta juya ta kalli Yanuwan Baba tace "DonAllah wa zai kaini Gidan Sarki? Ai in ba wanda ya isa da kai Alhaji, ai baka fi k'arfin hukuma ba" Baba Sani da ranshi ya gama 6aci yace "Muje hajia Maryam, muje ni zan kaiki".


Baba Aminu yace "nima zanje, don wallahi wannan Makirar Matar ba zamu barta haka ba" Su Aunty Asabe sukace muma zamu.


"Wai ni zaku kai k'ara? Ni zaku hade ma kai? Ni zaku tona ma Asiri?".


Hajia Shafa'atu tace "Dallah, duk burga ce, suje muga zasu iya Ja da kai" kamar sakarai yace "to ku tafi din, matsiyata, bani ba ku, kar shegen da ya sake zuwa min Gida".


Ba wanda ya kulashi, sukayi gaba,
Dama Motoci kusan 4 suka zo, kowannensu ya samu Wuri ya zauna, suka nufi Gidan Sarki suna sake yi wa Juna Jaje.


Da suka iso Gidan mai Girma Sarkin Katsina, ba su sha wahalan shiga ba don Amaryar Sarki kawar Mancy ce, tun zuwansu makka suke zumunci.


Sasshenta ta shiga, ita kadai, duk sauran na Mota, bayan su gaisa ta gaya ma kawarta tazo ganin Sarki ne.


Gimbiya tace "kin ko ci saa yau kwanana ne, ya kusa shiga Fada, barin ga in yana iya ganinki yanzu".


Mancy tace "ba ni kadai bane, sauran na Mota".


Gimbiya tace "toufa, bari naje naga"


Bayan kusan minti 40 sai ga ta ta dawo "Afuwan Kawata, ashe yana Karamin Fada, yana ganin wasu baki ne, duk da haka kuna iya shiga" Mancy ta mik'e tace "barin je na kira sauran".


Sun samu shiga Fadar, da biyayya suka gaida Sarki.
Wasu tsofi Mata guda biyu na zaune, sai kusa da Sarki wani mutum ne, sai dogarai 4 sai magatakarda.


Mancy ta zauna kusa da k'afar daya daga cikin tsofin ta gaishesu, su Aunty Asabe duk a ka gaigaisa.


Gimbiya tace "Mai Martaba, wannan k'awata ce, ta buk'aci ganinka, duk da na san yau ba ranar ganinka bane na nemi a mana alfarma aji da me tazo" cike da izza ya gyada kai".


Daya daga cikin dogarawa yace "Gyara Kintsi, matso gaba ki fadi damuwarki".


Ko dar Mancy bata ji ba ta matsa kusa da Kafar Sarki, wanda gefenshi wani mutumi ne sanye da Babbar Riga.


"Sunana Maryam, wanchan babban da na ne sunanshi Zaid, waccan itace auta ta sunanta Sadiya, wadannan k'annen Mijina ne na da".


Sarki ya gyada kai alamun yana ji "Muna zaman lafiya da Uban yarana, tafiya yayi, yana dawowa ya min Saki Uku, yace kuma dole da yarana zan tafi, ina zani dasu Mai Martaba? Nace mishi da yara kanannene sai na tafi dasu amma ni ba zan tafi da baligai ko ina ba, banda kowa sai Yayana, ina yake so naje dasu? Wannan shekararta 15, wannan shekarunshi 25 masters ma yakeyi, ina zan kaisu? In ya sakeni me zai sa ya koresu, har yana ikirarin ya bude ido ya sake ganinsu zai iya kashesu?".


Sarki yace "Wanene Mijinki? Yana gari? In yana gari a kirawo manshi yanzu, in be gari na bashi kwana biyu yazo ina kiranshi".


Wani bafade yace "Kiran Sarki Doka".


Mancy tace "Yana Gida, Alhaji Ali Zaki".


Mutumin kusa da Sarki yace "Speaker?" Sai a sannan ta kalli mutumin, daga kai tayi tace "eh shine".


Sarki yace "A aika ma Ali Zaki Sammaci, ace ina kiranshi yanzu".


Baba Sani yace "Harda Matarshi wacce itace ummulabaisi, ita ce ta sa ya saketa, muma yanuwanshi ya wulakantamu, sihiri ta mishi"


Sarki yace "A zo da matarshi".


Suna nan zaune jugumjugum magatakarda ya fita da wani zuwa aiken Sarki.


Da Sak'o ya je musu, Shafa'atu taso ya bijire ya k'i zuwa, amma kiran Sarki ba wasa ba, lallashinta yayi ta hanyar nuna mata illan rashin zuwan, rashin zuwan na iya kawo mishi cikas a Siyasar shi, kuma shi Sarki Uban kowa ne.


Da k'yar ta zura wani minnirin mayafi suka bi bayan dogarai bayan tace Hudu ya kula da Annah.


Bayan Zuwansu ne Alhaji Ali kunya duk ta rufeshi ganinshi gaban Sarki, ga kuma Alhaji Ibrahim Iroro, ita uwar gayyan sai da ta ji shakkun Sarki duk da tsagerancinta.


Sarki ya bada umurni, a ka buk'aci Mancy da ta sake fadan abunda ta fada, kamar yanda ta fada dazun haka ta sake fada.


Sarki ya tambayeshi "meye dalilinka na cewa ba zaka rik'e yaranka ba?".


Alhaji Ali ya keta zufa, gaban Shafa'atu na faduwa Allah ya sa kar yace ita ce bata so.


"Allah ya kara ma Imani, wallahi bana kaunar bude idona na zuba kansu, wallahi banson ganinsu, na tsanesu".


Sarki yace "Aiko ba ka isa ba, wani yace ka haifesu? To ba tare da bata lokaci ba, wannan abun mai sauki ne, a Addinance, tunda Yara Baligai ne, kai ke da hakkin daukarsu, da ace yaran k'anana ne sai ta daukesu, amma wadannan yara gurinka zasu zauna Alhaji Ali".


Da sauri yace "donAllah aa, zan bata ko nawa ne na kula dasu, zan dauki nauyinsu, nidai kawai su bar min gidana".


Sarki yace "to ke kinji, yace zai dauki nauyinsu, amma su tafi da ke".


Mancy tace "Aa Allah ya kara maka Imani, Saki Uku ya min, shari'ah ta bashi damar rik'e Baligai, Shari'ah ta hutar dani da gajaniyarsu tunda ba yara kanana ne dani ba, Allah ya ja nisan kwana, in na samu Miji aure zanyi, ya zanyi in be amince da na zauna da Yarana ba? Ya zanyi in yace na zaba ko aurenshi ko yarana? Ya zanyi in ya fasa aurena saboda Ina da Yara Baligai? Ban k'i su dinga zuwa min ziyara ba, Allah ya ja nisan takawa, ban amince ba, hankalina zaifi kwanciya in Yarana na gidan Ubansu".


Sarki ya jinjina kai yace "Alhaji Ali, Yara zasu zauna a gurinka, zaka dauki nauyinsu kamar yanda duk wani Uba zaiyi, cin su, shan su, suturarsu, iliminsu, tarbiyarsu, komai, duka, kayi maganar zaka iya kashesu, zan sanya ido a kanka, in ka karya doka, doka zata taka ka, kasan kai sananne ne, kayi tunanin mai zai faru a rayuwarka ta siyasa in nace zan tona asirinka, Yara naka ne, amma Girma ya bani Iko a kanka da yaranka da duk wani rai da ke cikin garin katsina da kewaye, ina fatar ka fahimceni".


Kan Alhaji Ali a k'asa ya kasa magana, sai da wani dogari ya daka mai tsawa kafin ya amsa baki na rawa "to to rankai dade".


Mancy ta murmusa tace "Allah ya kara ma Girma da daukaka da daraja, nagode kwarai, ka gama min komai, Allah ya ja da rai ya kera lafiya, Ina neman alfarma a bani kudin motar zuwa Kano".


Duk suka bita da ido, Asabe tace "Maryama yo ai baki gama ba, ko kin manta da Shafa'atu ce silar sakinki, ba kiyi maganar cin kashin da ta sa Yaya ya mana ba".


Mancy tace "Yaya Asabe, damuwata sune 'ya'yana tunda na kwatar musu 'yancinsu banda sauran damuwa, kuma Saki dai ya riga da yayi har uku ba kome, sauran kuma nakune, Allah ya sa a dace".


Mamakinta suke gabaki daya, rana daya ta rikide musu, kamar ba Maryama mai hakuri da kawaici ba.


Sarki yace "a bata kudin Mota zuwa Kano" na kusa da shi yace "ai kano din mukayi, ni da su Hajia sai mu sauketa".
Hajiya da kawarta sukace "aiko dai sai muyi ta tafiya".
Sarki yace "to barka".


Mancy ta tako har gaban Zaid da Dalo inda fuskokinsu sunyi ja saboda kuka, ta dago su gabaki daya tace


"Ina Sonku, kar ku taba mantawa"


Dalo na kuka tace "Mancy karki tafi ba dani ba"


Mancy a girgiza kai tace "mun gama magana Sadiya, ki kula da kanki, Allah ya miki Albarka".


Ta rik'e hannun Zaid da yake ta faman murzan idon Hagunshi tace "sai Idon ya kara kankancewa Zaidu? Kabar murzan idon nan, bana so"


Gyada kai yayi alamun to, bubbuga kumatunshi tayi a hankali tace "Stay Strong".


Zan kiraku kunji?. Ta rungumesu sosai kafin tace ku zauna. Umurninta suka bi suna kuka ita kuma ta fita daga Fadar da sauri, Zaid ya dago kannennen idonshi ya bita da kallo har ta bace ma ganinshi.


Abokan tafiya suka tashi suka ma Sarki sallama suka bi bayan Mancy.


Zaid ya runtse idonshi ya kalli Labiba da ta ke ta sharan hawaye yace "ki tafi Marece yayi" karfe 5 da ta duba agogonta.


Majina ta ja tace "Oh Allah, ban san lokaci ya ja haka ba, zan dawo gobe, zan idasa jin labarin kaji Yayana?"
Banza yayi da ita ya dauko sigari ya sa a baki ya kyasya lighter ya fara zuk'a.


Jakarta ta dauka ta bude kofar sai dai me? Gani tayi har an gama Shafe, an gyara passage dinta, duk an gama gyran bulo din, suna ina har aka gyara wurin? Duk suna aikinme basu san a gyara ba, lallai ta shagala da yawa. Kofar ta bude sosai yanda Zaid zai hango Bangon gidan.


Jinjina kai yayi yace "Wow, har an gyara".
"Yanzu ni ta ina zan bi?" Yace "ta Gate mana ko zaki fasa bangon ne ki fita sai a sake gyarawa?".


Tace "muje donAllah ka rakani" "saboda ni na shigo dake?" Ya tambayeta cike da tsageranci.


"DonAllah nace Yayana"


Banza yayi ya kyaleta, ganin tana k'ara bata lokaci ne ya sa ta sakin kofar ta fita tana mai tafiya sadaf sadaf kamar mai shirin Sata.


Gabaki dayansu suna zaune a Bukka, nan suke zaune duk yammaci su sha Fruits, ganin wata sukayi ta wuce sutana tafiya kamar barauniya tana tafiya tana waigen baya, a tare suka mike tsaye.


Hudu ne ya daka mata tsawa yace "Keeee"


Sai da hanjin Labiba suka kada, chak ta tsaya ta kasa juyowa, jikinta sai rawa yake. Duk suka nufota.


"Uwar wacece ke? Daga ina, barin zo in ga fuskarki" cewar Anty Shafa'atu.


Labiba a tsorace ta fara juyowa taji muryanshi na cewa;


"Beebs, donot turn".


Fasa juyowan tayi ta tsaya tana mai kallon gate, su kuma hudun suka juya suna kallon DanMakahon dake nufosu sauri-sauri gudu-gudu".


Yana zuwa daidai Labiba ya finciko hannunta ya yi gaba ita ko ta bishi a baya hannunsu rike da juna.


Muryan Aunty Shafa'atu sukaji tana cewa "Yau Mun Shiga Uku Alhaji, Karuwa har cikin Gida".




Hello Lovers, Vote and Comment line by line please.


#1love
#DM
#FWASonSo
#anatare
#nagode


Biebee Isa
[14/03 9:35 pm] Biebie: BABI NA GOMA1⃣0⃣


Kalmar Karuwa shine sanadiyar tsayawarta cak, duk wani lakka na jikinta ji tayi kamar an zaresu, a lokaci daya kuma jikinta ya fara rawa.
Baki na rawa tace
"ka tsaya, ni ba karuwa bace, wallahi ni ba ita bace"
K'ara damk'e hannunta yayi ya jata har sai da suka yi daf da fita Gidan.


Muryar Alhaji Zaki sukaji na cewa "Shege, Tsinanne, karuwa kake kawo man Gida ko? Kanwartaka bata isheka ba? Sai ka kawo na waje Gida?".


"Ya Rabb" ta furta da k'arfi, be sake hannunta ba ya cigaba da janta, togewa tayi, ta k'i gaba ta k'i baya, gabanta ya tsaya, ya rik'o kafadunta da duka hanayenshi,
Kai ya girgiza mata, da dan karfi tace
"Tsine maka fa yakeyi, Shegantaka yakeyi, ko baka ki bane? mu koma in mishi bayani, mu koma na gaya mishi ni ba karuwa bace".


Hannunta ya rik'e ya cigaba da janta har suka fita daga gidan baki daya, ko da suka fita Gate be sakar mata hannu ba, haushinshi taji karo na farko a rayuwarta, da kyar ta samu ta fincike hannunta daga nashi.


Ta waiga ta kalli Unguwarsu da ke busy asaboda marece yayi, ta sa hannu ta shafi goshinta ta da ya danyi zufa.


"Baba ba karuwa bace, abunda ya kamata kace kenan, amma ka kasa, har sai yaushe zaka cigaba da karban laifin da ba naka ba? Shiru na nufin fa ka amince da kayi abunda ba kayi ba".


Hannu ya sa ya murji idonshi "Ba zaki gane ba, yin maganata bata da wani amfani".


Ta katseshi ta hanyar cewa "sai kayi, kayi magana ko bata da amfani, yafi ace ka yarda da abunda bakayi ba, maganarka yafi ace ka na neman k'anwarka da lalata, ya fi ace kana kawo karuwa Gidanku".


Gashin kanshi ya dan shafa kafin ya murje idanun duka biyu, sannan ya koma kallonta yana karantarta, ya fada a ranshi "ta na da gardama kuma bata ganewa".


A fili yace "nayi rantsuwa na daina cewa banyi abu ba, duk wani abu da zai fito daga bakinsu, hakan ne, banda k'arfin jayayya, yau ko kisa sukace nayi, kawai hakan ne, they are right".


Takaici ya sa Labiba yin gaba, da sauri bata ma da abunda zata ce mishi, tafiyarta kawai tayi, don tana ganin Zaid be ma da hankali.


Bin bayanta yayi yana kwala sunan "Beebs" amma tayi burus dashi, ta ci sa'ar samun Keke Napep ta hau ta fadi sunan Anguwarsu Aunty Asee.


Tsayawa yayi ya bi Keke Napep din da ido, ya juya ya kalli Gidansu, kurum yaji Garin Katsina ya mai zafi duk da ni'imtaccen iskar da ke bosowa, garin da alamun hadari.


Ya buga tsaki da ya ciro sigari ya kyasta ya koma Gida, suna nan tsaye kamar yanda ya barsu, maganganu suke wanda yake da tabbacin La'antarshi sukeyi, straight hanyar BQ yayi, yana jin Baba na faman kwala mai kira amma yayi burus da shi ya wuce dakinshi.


Yana shiga Daki ya sa mukulli ya rufe ya fada kan Gado yana mai tunanin Labiba.


Labiba ma da tunanin Zaidu ta isa Gidansu Aunty Aseey, jikinta duk a mace,ta shiga Gidan da Sallama su Ameera su ka taso don yi mata oyoyo, da yak'e ta taryesu, ta karasa ciki ta gaida Hajiar Aunty Aseey da 'yan Gidan.


Aunty Aseey tace "Labiba ya makaranta?" Dan jim tayi, yau ko hanyar Makaranta bata bi ba,amma sai tayi karya tace "Alhamdulilah"
Hajiyar su Aunty Aseey tace "ya mukaji da wannan abu? Bango ya Fadi" Labiba tace "eh wallahi Mama, an ma gyara".


Aunty Aseey tace "Kin biya Gidan ne?" Da sauri tace "Aa, nasan dai angama saboda marece yayi, yaya kuwa yace aikin be da wuya".


Aunty Aseey tace "haka ne, tashi ki ci Abinci".
Mik'ewa Labiba tayi tana mai jin haushin kanta, wai itace yau da k'arya har so 2, Allah ka yafe min".


Gab da Maghrib suka koma Gida a Keke Napep, sun tarar da an gama gyaran Bangon, Labiba ta share tsakar Gidan ta shiga kitchen don daura musu taliya, bayan sunyi Sallahr Maghrib, suka ci Abincin, gabaki dayan su suke zaune kan tabarma kasancewar ba Wuta.


Hadari ya taso, iska mai karfi ya taso, da sauri suka nade shimfidarsu,

Please Login or Register in order to submit comment