Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Aisha na sonta matuk'a, kodayake ita dai haka take, indai ta zauna a wuri, to tana da farin jinin mutane, kowa na sonta, ba za a ce don Kyau ba, don ba fara ba ce, a'a, don kyauwun zuciyarta ake sonta, ta iya zama da jama'a, kowa nata ne, bata da zabin mutane da take mu'amala dasu.
Wannan kenan.


Labari suke da Aisha kafin a shiga layin Unguwarsu Labiba, Aisha ke hada ta da Allah tazo gidansu don Mamarta na son ganinta, har k'arya ta mata cewa Mamar ta ce in ita Labiban bata je ba to ita za ta zo gidansu Labiban da kanta, duk dai don taje Aishar ta ce mata haka.
Dariya Labiba ta yi tace "Insha Allahu zanzo wannan Satin, ki ce Mama tayi hakuri.


"Allah ya sa kana da chanjin dubu daya" cewar Labiba, mai Adaidaita ya buga tsako yace "Hajia sai kiyi magana tun wuri ni banda chanji" Aisha tace "nima wallahi dubun ne" mai A daidaita ya fara mita da ya san Chanji ne da be dauko su ba, gashi har ya kusa shiga Tudun Matawalle, Labiba tace "Afuwan, akwai shago a ta wurin zasu samu Chanji" mai Napep yace "ga unguwanku ba dadin shiga, balle jiya anyi ruwa" Labiba dai hakuri ta sake bashi, Aisha dai tsaki tayi tace "ya cika mita".


Daidai Shagon Eskaley ya ci burki, Aisha ta mik'a mishi dubu daya tace "gashi ka samo chanji ka cire duka" ko waigowa beyi ba yace "Yo Anguwarmu ne? ko sani na sukayi da zasu bani chanji?" Labiba ta lura Mai Keke Napep dinnan dan tijara ne, ta sauka tace "bari na samo" Aisha ta bude baki tace "ya za'ayi kije gurin 'yan Shaye-shayen chan? Haba Labiba ba mutuncinki bane a ga kinje chan shagon, ki bari ya samo" Labeeba ba ta tsaya ba, illa ta karasa bencin Eskaley da Sallama.
*


Zaune yake kan plastic chair, cikin wata longsleeve shirt da 3 quartern Sojoji, face cap dinshi wanda ya rufe kanshi har wurin idonshi ruf ma irin wandon ne, kayanshi kenan duk dunia, ya dora k'afa d'aya kan d'aya, Idonshi lumshe. Yana shak'ar k'amshi, yana jin dadin yanayin da World ke sashi,


World shine sunan da 'yan bencin Eskaley ke kiran Tabar Wiwi, a cewarsu, Ita Wiwin Duniya ce, ma'ana komai, in suka zuk'eta, jin kansu suke daidai da Saraki, Sarauta Wiwin ke sasu. In ka zuk'i World, kafi kowa, wannan ma ya sa Zaid zama shi kadai tare da ba su Master baya, wanda suke fama buga Whot ko na Sigari basu dashi.


Duk k'ullin Worlda naira dari biyu Eskaley ke saidawa, yana bada bashin Sigari, amma be yarda ya bada bashin World ba.


Tunda suka ga ta nufosu suka k'ura mata ido, Eskaley ya amsa yana washe hak'oranshi jajjaye, da murmushi ta kallesu tace "Ina wuninku, DonAllah chanji naira dubu nake son ka taimaka min dashi" ta maida hankalinta gun na cikin shagon, Eskaley yace "Ahhh, chanjin dubu da sauk'i, basu kai ba wallahi" Labiba tace "akwai Credit? Mtn?" "Aa wallahi ya k'are" dubu dayan ta mik'a mishi tace "to DonAllah ka dan ara min #350 na ba me keke Napep" Eskaley yayi daria yace "Hajia yau wallahi da sauk'i, yau ba ciniki"


"Oh Allah!" ta fada a gajiye, ta musu Godia ta juya.
"Ga 350" taji an fada murya a dakushe, ta juyo ta ga wa ke magana, bata samu kallon fuskarshi ba sai gani tayi wani ya fincike kudin da aka mik'a mata.


"Shege Mankas, kana da kudi a aljihunka kasa Eskaley ya hana ni World, kai mik'o min World dinnan" ran mankas 6ace yace "donuwarka bata kudin" master ya kalleshi yace "mankas ni zaka ma wulakanci don nace ka siya min World, don ni ba mace ba ce, banda kayan dadi ko? to ranta min uku da hamsin dinnan, zan baka" daidai nan mai Napep ya sake buga horn, Labiba dai ikonAllah take kallo.


K'yallararen idonshi ya dago ya kalli Master bece komai ba, Master ya buga tsaki ya matsa kusa da Labiba yana cewa "Danmakaho ya ga Chikala" da sauri Labiba ta kalli mazauna gurin don ganin dan Makaho, amma bata samu nasarar ganinshi ba don ya juya mata baya, dubu dayan ta mik'a ma Master, tace "ka bashi, na biyo shi chanji, zan zo na amsa" master ya yashe jajayen hak'oranshi yace "Yayata, donAllah ki bar min chanjin mana" tace "aa gaskia ni ba zan baka kudina ka k'ona su ba" da sauri Master yace "wallahi ba Sigari zan sha ba, abinci zanci Yunwa nakeji". Labiba tace "ban yarda ba, nidai ka ba DanMakaho chanjina".


"Haba Babbar yaya kin fi k'arfin dari bakwai da hamsin, nidai Godia nake" Horn mai Napep ya sake buga mata har yana mata masifa, da k'arfi master yace "dallah ware Mallam, zaka ishemu da Oda, ka bita a hankali ko na ci uwarka, Yayarmu Allah ya kiyayeki" Mai Adaidaita tuni ya shiga taitayinshi, kar ya sha duka a banza, Labiba na shiga ya ja Napep dinshi suka shiga cikin Unguwa.


"Master, bani" cewar DanMakaho, "me zan baka?" master yayi kamar be san me yake nufi ba, Haruna yayi wuf yace "kai Master, muna gani fa ta baka 1k, kuma muna ji tace ka ba DanMakaho chnajinta, kawai kawo kowa a bashi world daidaiya" DanMakaho ya dago k'yallararen idonshi yace "ku bani nan" Master yace "haba Mankas, yawa kakeyi wallahi, kai ma fa World dinnan ka taba, kuma ka hanani, ka bari mana Eskaley ya bamu daidaya".


"DonAllah Mankas ka bar mana kudin nan, haba mana yawa kake" mik'ewa yayi ya fizge kudin, tare da cewa "In tazo k'arbar chanji ta uwar me kuke so na ce mata?" Master yayi wuf yace "ta fa bani" DanMakaho ya zira kudin Aljihun gaba inda Kwalin Sigari ke ciki, tare da fadin, "in na bata ta baku".


Barin gurin yayi, ya shiga cikin unguwa, su Master suka bishi da Ashar kala-kala ransu bace.
**


5:20pm


Baccin Awa 2:30 yayi, yana farkawa World ta sakeshi, ko da yake be shak'eta duka ba, Kewaye ya shiga ya dauro alwala, yazo ya hada Azahar da La'asar, rigarshi ya shinshina yaji tana warin zufa da rana ga kuma k'aurin hayak'i, guntun tsaki yayi, be yarda ya zauna da dauda ko k'azanta ba, duk da wadan nan sune suturunsa, sai wata bak'ar jallabiya da yake sawa a duk lokacin da zai wanke riga da wandonshi yana iya k'okarinshi wurin tsaftace su, be son shiga cikin Gida amma dole ya shiga ya dauko sabulu, ya ga dan Shegiar da zai hanashi.


Straight ciki ya shiga, da Hudu ya ci karo ya fito kamar mara gaskia, yana zare ido, da sauri ya wuce boysquaters, da dan mamaki DanMakaho ya kallesh yana mamakin saurin da yakeyi kamar wanda yayi k'arya, amma da yake ba damuwarshi bane sai yayi gaba ya shige Store ya dauko Klin.


Ya na fitowa daga Store yaji Aunty Shafa na cewa "Uban wa ya dauke min Naira Dubun da na aje kan Center Table" Annah ta fito daga daki tace "nidai Wallahi Aunty bani bace, tun dazun ina daki" Fati tace "ni kuma wallahi ban ma san kin aje kudi ba" "duk dauke dauken da ake min bana magana, yau abun ya isheni, daga in aje kudi in shiga in fito sai na nema kudi na rasa? ina Sadiya?" Fati tace "tana cikin dakinta ko?" Aunty shafa tace "na san itace, ya zaayi dama ku dauka, aiko ko ta bani kudina ko na mata mugun bugu, kuma Ubanta yazo ya biyani kudina"


Mankas be gama jin sauran zancen ba ya banko labulen Parlo ya shigo, ya na bude idonshi ganin ina Sadiya, ganin bata cikinsu ya kutsa cikin dakin ya ganta chan gefen gado me kama da na 'yan boarding durk'ushe tana karkarwa, ga dukkan alamu ta ji zantuttukan su Aunty Shafa, kuma ta tsorata, be tsaya kwantar mata da hankali ba ya finciko hannunta ya ja ta har Parlo gaban Aunty Shafa ya tsaya.


"Uwar da ta fasa taba ta, ta raina Uwar da ta haifeta" duk suka yi cirko-cirko ba me motsi, ya juya ga Annah da Fati, yace "duk randa kuka sake daga mata hannu, sai na sassareku" Aunty Shafa tace "Dubu daya ta ta dauka, kuma sai an biyani, DanMakaho ka fita idona, ni ba sa'arka bace, Uwarka ma bata fara yi dani ba, wallahi ku firdo min Kudina kafin Daddynku ya dawo, kaga duk inda yake yana daf da Gida, ku bani kudina, ba zai ji komai ba".


Baki na rawa Sadiya tace "Wallahi Aunty bamu dauka ba" Mankas ya daka mata tsawa yace "dallah kyaleta, munje mun dauka, ba za kuma a bayar ba, in ya dawo me zaiyi? Tsine min? Wani irin tsinuwa ne zai min wanda be min ba? Mtswww" ya buga tsoki kafin ya ja hannun kanwarshi suka fita daga Parlorn.


Daidai nan Hudu ya shigo yana zare ido, "Wai meye ke fariwa nake jin Hayaniya Hajia?" Kwafa Aunty Shafaa tayi tace "dani Dan Makaho yake cikin Gidan nan, wallahi zaman Gidan nan sai ya gagareshi fiye da yanzu, bari Alhaji ya dawo".
*
Zaunar da Sadiya yayi gaban k'ofar dakinshi ya dan bata baki, tare da kwantar mata da hankali ta hanyar gaya mata zai rok'i Babansu kan ya barta taje Gidan Mamansu hutu, sai da ya ga ta saki ranta kafin ya koma daki ya dauko Bak'ar jallabiyarshi ya zura, ya kwaso Riga da Wandon da zai wanke tare da bucket a toilet, cire abubuwan gaban Aljihunshi yayi, da Mukulli, da kwalin Sigari, da Naira dubu daya ya ajiye k'asa, Klin ya Jik'a ya fara tsoma rigar ya fara cudawa.


Be gama wanke Rigar nan ba yaji muryan Daddynshi yana fadin "Ina Dan Makahon yake?" dago idonshi yayi ya kalli Daddynshi da ya nufosu kamar Zakin da ya kwana 7 be ci abinci ba, duk 'yan Gidan sun rufa mai baya, kafin ya ankara Daddynshi ya sakar mai nushi kala biyu a gefen baki, ko motsawa beyi ba, Sadiya ta fashe da kuka.


" Sata? A gidana DanMakaho? Dama duk sace-sacen da akeyi kai ne? Yau dubun ka ya cika, yau wallahi sai ka kwana bayan Kanta" wayarshi ya dauko ya latso DPO, Sadiya ta zube gabanshi tare da rikon kafarshi, tace "Daddy Wallahi ba shi ya daukar mata Dubu dayanta ba, wallahi bashi bane, Daddy, Klin kawai ya shigo ya dauka, Daddy ka yarda damu" Haurinta yayi dai da ta matsa gefe, da sauri Mankas ya karasa gunta ya durkusa tare da dagota yana watsa ma 'yan Gidan mugun kallo, ya tsaida kallonshi ga Mahaifinshi ido cikin ido yake kallonshi.


"Zaid Mahaifinka ne, Zaid kar ka manta Soyayyar da ya wanzu tsakaninku, Zaid kar ka sake ka yi ma Mahaifinka ba daidai ba, duk yanda zuciya ke tunzuraka kan ka mishi wani abu, Zaid ba zan yafe ma ba, kar ka ga tsinuwan Mahaifinka kamar baya tasiri a kanka, Zaid a ranar da zan juya ma baya, Zaid ka rasa Lahirarka wanwar, Zaid Mahaifinka ne, ba komai tsakaninku sai k'auna da kyautatawa" muryar Mahaifiyarshi yaji na mai kuwa kamar a lokacin take magana.


Runtse ido yayi sosai, muryar Hudu ta katseshi inda yake cewa "Lahhh, ga Dubu daya chan" da sauri ya bude idonshi, ya ga Hudu har ya durkusa ya dauka, da azama ya karasa shima ya rik'o kudin, idonshi duk biyun ya bude su yace "Sake min kudi".


Aunty Shafaa ta karade da "Wallahi dubu daya tace, ashe dama kai ka dauka, in kace kana so ai DanMakaho dubu daya ba komai bace, zan baka, amma meyasa zaka daukar man kudi?".


Daddy yace "Zaka sake kudin nan ko sai ranka ya baci?" sai da Daddy ya sake maimaitawa kafin ya sakar, ran Daddy a bace yace "Shege Barawon Banza, kaji haushi" halbi Zaid yayi da Bokitin Wanki, ya shige daki rai a dagule.


***


Zaune suke gaba ki daya , Fira sukeyi har Yara suna dariya, daga bisani sukaji an fara iface iface, sosai su ke jin abunda ke faruwa daga kan tabarmar da suke zaune,


Labiba ta mik'e da sauri ta k'arasa jikin Bangon Gidan, nan taji komai,
Girgiza ka ta farai kamar k'adangaruwa, "Wallahi ba sata yayi ba, Aunty Aseeyah wallahi dubu daya ta ce, kudina ne, ni na bashi, Aunty DanMakaho ba Barawo bane, Ya Illahi".


°°°°°°°
Kindly Vote and Comment Line by Line


#1love
#DM
#anatare
#™SonSo
#FWA


Biebee Isa
[14/03 9:35 pm] Biebie: DANMAKAHO 😉
4⃣


Rikota tayi da hannu biyu, "Labiba, ki yi min magana". Naunayar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta bata labarin abun da ya faru dazun.


Aunty Aseeyah tace "Labiba, akwai abubuwa da yawa dake faruwa gidan Alhaji Ali Zaki, tun kafin zuwanmu Unguwar nan, ba zaki gane ba, amma akwai 6oyayyen alamari tsakanin duk wani rai da ke cikin gidan, wanda ba hurumin mu bane, ba mu da wata alak'a dasu da ta wuce makwafataka".


Labiba ga kalli Matar Yayanta " Aunty, Hakkin Makwaftaka fa? wannan babban hak'k'i ne, ya kamata a yi wani abu a kai, so biyu ina jin Makirar Matar nan na hada makircinta, ba zata tsaya a nan ba, ba za kuma ta bari ba, ya kamata Aunty a tari Alhaji Zakin".


"Hmm, Labiba, fadan da ya fi k'arfinka sai ka maida shi wasa, ba abunda za mu iya yi. Hajia Shafa, ta zarce tunaninki, bana son matsala da Hajia Shafa, yanda ba abunda ya taba hada mu, bana son komai ya hadamu, amma tabbas Dan Makaho da k'anwarshi na buk'atar Addu'a, shi kawai zamu taya su".


Hannu ta sa ta ja dankwalinta baya, murya k'asa k'asa tace " Sakarai! Kamar ba namiji ba, ba ya iya kare kanshi? Meyasa be iya k'aryatasu in sun mishi sharri? Mts"


Aunty Aseeyah tace "Magana kike?" girgiza kai tayi tare da mik'ewa ta shige daki


5/5/2013
1:30pm


Tunda garin Allah ya waye zuciyarta ke mata kitse-kitse, DANMAKAHO k'wak'walwarta ke kwada ma kira, baza ta iya shaidashi a hanya ba don ba saninshi tayi ba, dalili take so ya sa ta ga DanMakaho, kamar shekaran jiya, da tunaninshi ta tashi, ta damu da lamarinshi, abu kamar a film ko a littafan hausa, so take ta shiga rayuwarshi, so take taji damuwanshi, abun da kamar wuya, amma sosai take so ta hadu dashi, haduwarsu ta farko in brief ne, ko ganin fuskarshi ba ta samu tayi ba, gashi yau ba ta zuwa Makaranta balle ta sa ran ganinshi a Waje, haka kurum ta tsiri zuwa Gidansu Aisha.


Yara na Tahfiz, Parlo ta iske Yayanta da Matarshi, a gefen Kujera ta zauna tana musu murmushi "Yaya, ina neman izinin zuwa Gidansu Aisha Usman, Mamarsu ke son ganina, har cewa tayi in ban zo ba, ita zata zo".


Dan dariya sukayi kafin Yayan yace "Kinsan Gidan ne?" Girgiza kai tayi alamun aa kafin tace "kwatance ta min" yace "to bari naci Abinci na saukeki" tace "to shikenan nagode".


*


Da kwatance suka gano Gidansu Aisha, dari biyu ya bata yace " ki hau Adaidaita sahu, kuma kar ki kai Maghrib"
Godia ta mishi, Aisha ta gaisheshi sannan suka shiga Gida.


Ina za'a saka Labiba don murna, tunda ta tako cikin gidansu Aisha ta ke cin karo da Soyyayar mutanen gidan, har Mai aikinsu ta san Labeeba, da kaunar da ke tsakaninsu.


Ya Illahi, haka suke sonta? Barin ma Mamar Aisha da take ji kamar ta goyata, kayan mak'ulashe a ka cika gabanta, daga bisani a ka kawo mata Abinci mai rai da lafia, ita dai Labiba daria take tayi, tana cikin cin Samosa Aisha ta k'atseta da cewa "Zo muje ki gaida Daddy".


Kunya ya kama Labiba, "DonAllah ki bari sai anjima" Aisha bata saurareta ba, sai jan hannunta tayi don ta mik'e tsaye tare da janta ta na gaba Labiba na bin ta a baya.


Har k'asa ta durkusa ta gaida Daddy, Daddy ya amsa cikin kulawa ya dauko dubu biyu ya bata, bata iya amsa ba sai dai Aisha ta amsar mata sukayi Godia suka koma dakinsu Aishan. Sai da Laasar yayi suka yi Alwala don yin Sallah.


Labiba na adduointa ta ji kamar ihu daga waje, sai da ta kasa kunnuwanta sai taji ashe Ihun murna ne da alamun bak'i sukayi, tashi tayi ta ninke Darduma, ta zauna gami da tsiyayo kunun Aya a Cup. Aisha ce ta shigo fuskarta dauke da murna. "Besty kinsan me? Cousins dinmu ne sukazo daga Abuja wallahi dadi kamar ya kasheni".


Labiba tace "Inye, fatan sunzo Lafiya" "Lafiya lau wallahi, taso muje ku gaisa" hararar wasa ta jefeta dashi, ta dan muskuta tace "tafiya zanyi ni, banason marace yayia ina waje, kuma dai zaun daura Sanwar dare" Aisha ta san ta mata tunda tun bayan Azahar tazo, don tace zata tafi yanzu ba wani abu ne. Mikewa tayi tace to "barin sanar da Mama".


Labeeba tace "ke dai jira mu tafi tare, katon gyalenta Khashka me kauri ta yafa, Aisha kuma ta janyo wata yar gyale bayan ta mata packaging su Samosa da Springrolls tace a kai ma su Ameera.


Ba ta Parlor inda ta barsu, ba dai har sun tashi ba? Da sauri ta ja hannun Labeeba sukayi tsakar Gida, inda ta gansu tsaitsaye, kallo ta bisu dashi kafin tace "Yaya Hafeez ba dai kun fito ba". "wallahi kuwa A'i, gwara muje mu gaida Hajia Kaka kafin ta kira Abba tace Munfi Awa 8 a katsina bamuje mun gaisheta ba".


Dariya sukayi gabaki daya, Mama tace za kuci Gidanku, Sirrikar tawa kuke ma iyashege?" daria suka sakeyi. Mama tace "Af! Labeeba ba dai kin fito ba" ta dan k'araso garesu cikin takunta tace "Wallahi Mama gwara na tafi, Marece yayi" Mama tace "eh Gaskia ne".


Dukkansu Maza Ukun idanuwansu suka zuba ma Labeeba, idanuwa taji a kanta, ta dan dago ta kallesu su ukun a lokaci daya tace "Ina wuninku? Kunzo lafiya?" amsawa sukayi a tare suna kallonta sosai, Aisha tace "Besty, wadannan sune yanuwana rabin Jikina, kika tsaga tsokata Jininsu kawai zaki gani".


Dariya Labeeba keyi wanda ke k'ara ma fuskarta kyau, ta cigaba da sauraron Aisha, "ga Yaya AbdulHafiz ga Yaya Abdulmajeed kuma ga Yaya Jawad, yau yau dinnan suka zo daga Abuja don Sada zumunci" wani murmushin ta sakeyi, tace "Barkanku da zuwa Katsina ta dikko Ya Abdulhafiz Ya Abdulmajeed da Yaya Abdul-" ta dan yi shiru tana son tuno sunan gudan, wanda suka kurawa junansu ido shi da ita, murmshi ya mata ya girgiza kai yayi yace "ba Yaya Abdul bane, Yaya Jawad ne" kamar bitar karatu ta maimaita "Yaya Jawad".


Aisha ta katsesu tace "Brothers, ga Besty ta, Labiba Ahmad" a tare sukace "Labiba" Mama ta dan murmusa tace "cikinku wa zan ba Diyata?" ta fada tana dafa Labibar da tayi saurin sadda kai k'asa".


Yaya Abdulmajeed yayi karaf yace "Ni zaki ba Antisco, Yaya Hafiz na da Mata, dama nine online, kinga sai in hada da Aminiyarta na aure, kinga no kishi".


Aisha ta harareshi, tace "sai me don na hada Miji da Besty ai ba wani abu bane, ba dai kai bane Mijin"
Dariya Ya Majeed yayi yace "to ni nace ke na ke nufi ne? Nidai Antisco ina so" Mama ta yi Daria, ta maida dubanta ga wanda take ma Labiba kwadayi tace "Jawad fa?" murmushi kawai yayi da ya sake kallon Labiba.


Ya Hafiz yace "nifa bangane ina da Mata ba, don ina da Mata sai aka ce ba zan iya sake ta biyu ba?".


Antisco tayi daria tace "to zan raba gardama, kuzo ayi tseren gudu, wanda ya riga zuwa bakin Gate, shi zan ba damar daidaitawa da Diyata Labiba".


Kafin ta rufe baki tuni Jawad ya ruga a guje ya isa bakin gate daria suka sa baki dayansu, Abdulmajeed yace "Cheating! Ni fa Mancy ban shirya ba, gaskia a sake" Mama tace "Wani ya hanaka shiri da wuri? Ni Jawad na ba dama" Ya Majeed ya cubune fuska yace "dama Antisco na lura kin fi san Jawad" Daria suka sa baki daya.


Labiba tayi saurin katsetsu da cewa "barin tafi, yamma na k'arayi" Mama tace "ki tsaya su Jawad su sauke ki sai Aisha ta raka ki" Labiba tace "Baban Amira Zaiyi fada, bari dai in samu Keke Napep" duk sai ta burgesu duka.


Mama tace "Gaskia ne, to besty mungode, mungode Allah saka da Alheri, ki gaida Aunty Aseeyar da yaranta" Labiba tayi murmushi jin sunan da Mama ta kirata dashi wai 'Besty' tace "sai anjimanku" tayi Gaba Aisha ta bita a baya.


"Nidai Antisco wallahi tayi min ina so" Jawad ke fadin maganar nan, Antisco tace "dagaske Jawad?" "wallahi Antisco" Mama tace "maza je ka karbo numberta, gwara ta baka da hanunta" da dan gudugudu ya bi bayansu, har sun fita bakin gate, k'arasawa yayi gunsu yana dan haki, Aisha tace "Ya Jawad ya akayi ne kake gudu?" wani kallo me wuyar fassaruwa yabi Labiba dashi tare da cewa, "Zuciyata na biyo, zuciyata, ta tafi dashi" tafi Aisha tasa, ita kuma Labiba ta rufe fuskarta da hannu biyu.
Dan gefe Aisha ta tsaya don basu wuri su dan tautana.


Kallonta yake cikin ido, duk jarumta irin tata sai da ta kasa jure kallon, sadda kanta tayi k'asa, cike da shauk'i Jawad yace "Labee" da sauri ta dago ta kalleshi, jin sunan da ya kirata dashi, murmushi mai nuna jin dadi ta mishi.


"Ba zan tsayar da ke ba, Yamma nayi, ki bani numbernki DonAllah" "ka karba gurin Aisha" girgiza kai yayi da sauri yace "Haram, ke zaki bani da hannunki, in kuma hanani zakiyi shikenan" yayi fuskan tausayi kamar mai shirin kuka.


Dan daria tayi me k'ayatarwa tace "be maka kyau ba" ya dan kallota yace "mene?" tace "shagwabar mana" dan bubbuga k'afa ya fara yi kamar dan yaro, da sauri tace "Ya hakuri Baby kar ka tara min jama'a kawo wayar na sa ma".


"Baby,Wow, sunan da aka bani yayi dadi" da sauri ta girgiza kanta da hannuwanta bibbiyu kamar mai yin bye bye tace "ni fa ba wannan Babyn nake nufi ba, naga kana abun yara ne shiyasa na kiraka da Baby". Kafadunshi ya daga " Oho, nidai zan dauka a matsayin Dayan, yanzu dai gashi ki samin number" karba tayi ta sa Numberta.


Tsaida mata Keke Napep sukayi, Jawad ya bude mata k'ofa yace "kin k'i yarda na kaiki Gida ko?" murmushi tayi tace "Bye Ya Jawad" lumshe ido yayi ya bude "Good bye Labee" Aisha ta bude baki ganin yanda Bestynta da danuwanta suka shagala da aika wa junansu sak'onni, "Hello! An manta dani ko? To ina wurin besty?" Kunya ya sa Labeeba rufe fuska tana daria, ta umarta mai Keke Napep da su wuce.


***
5:45pm


Tuk'i Yaya Hafiz keyi cike da nutsuwa, sun fito daga Unguwar Alk'ali Gidan Kakarsu, zasu tafi su aje Sak'o kafin su wuce Masauki don Gobe zasu wuce Abuja.
Yaya Hafiz yace "Yauwa Majeed, kira Yaron Mancy mu biya mu kai mai sak'on nan don ni gaskia nagaji ni da fita sai gobe".


AbdulMajid ya ciro wayarshi daga Aljihu ya latso numbern da Mancy ta bashi, har wayar ta katse ba a dauka ba, sake dialing yayi nan ma ba answer.
"Ba ya dauka fa" cewar Majeed, Hafiz yace "Kira Mancy ka gaya mata" dialing Numbern Mancy din yayi ringing na biyu ta dauka.


"Assalam Majeed" ta fada cike da Murna, "Hello Mancy ina wuni, dama mun ta kiranshi

Please Login or Register in order to submit comment