Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels

[14/03 9:35 pm] Biebie: Babi na D'aya1⃣
('YAN ZAMAN KASHE WANDO)


3/05/2013


Kamar kullum, zaune suke kan Benchi daidai shagon Eskaley dake farkon layi, zaman banzan da suke yi ke nan duk bayan Sallar La'asar, daga gefenshi Haruna ne ke shan Sigari.
Haruna ya mik'o mishi Sigarin da ke dab da k'arewa, ya karba ya sa a baki zai zuk'a ke nan suka hada idanuwa da halitta daya da yake jin kunya duk duniya, da sauri ya tura karan sigarin cikin doguwar hannun rigarshi ya kawar da kai kamar ba wani abu.


K'arasowa ya yi bakin shagon ya musu sallama. Haruna kadai ya amsa tare da gaishe shi sai Eskaley, shi dai gudan kawar da kansa ya yi.
Naira Dari ya fiddo daga Aljihun gaban rigarshi ya ce da Eskaley "Barka dai! Maggi za ka bani Mai Star da Farin Maggi" karban kudin Eskaley yayi, ya hada mishi kayan daya bukata ya ba shi chanjin Naira Goma Sha Biya(15) bai amsa ba sai cewa ya yi a bashi Ashana da sauran. Sallama ya sake yi musu ya wuce cikin layin don tafiya gidan shi.


Haruna ne ya lura da Zufar da abokinshi ke yi, d'an zungurar shi ya yi da hannu yace "Ya dai Mankas?" Da sauri wanda aka kira da Mankas ya zura hannun shi cikin doguwar hannun rigarshi ya zaro karan Sigari, ya jefar kasa tare da sa kafa ya murjeshi. kafin kuma ya hau nannade hannun rigar. Haruna da mamaki yace "Mankas? Kana da hankali kuwa? Sigari mai wuta ka tura cikin rigarka? Mtss! gashi nan har ya taba fatarka".


Mankas ya kauda kai daga kallon fatar hannunshi da ya yi bororo lokaci guda saboda wutan da ya taba fatar, abunka da farin fata, tuni wurin ya yi Ja.
Garin wata hoda Eskaley ya wurgo ma Haruna ya ce "jik'a ka shafa mai a wurin" Haruna ya bude 'yar takardar, ya dauki fasasshen ruwan ledan da ke gefenshi ya dan jik'a ya kamo hannun Mankas zai shafa, Mankas ya janye hannunshi, da k'yar ya iya cewa "Ka barshi, ba damuwa".


Haruna cike da damuwa ya ce "kai fa Mankas gardama gare ka, ka tsaya don Allah."
Bai ce komai ba, sai ya mik'a masa hannun. Hakan ya ba Haruna daman Shafa masa Powdern a wurin da ya fara tashi.


Suna fira jefi-jefi sauran Abokan zaman kashe wandon suka karaso, nan unguwar ya kaure da hayaniyan yan benchin Eskaley , rabi da kwata duk gardama ce.


Da Sallama ya shiga Gidanshi, Ameera da Sabit suka rugo wurin Mahaifinsu dan taren shi "Baba Sannu da dawowa" kansu ya shafa ya ce "Yauwa sannu, ya makaranta?" suka amsa mi shi, "Barka da Dawowa Yaya" ya kalleta da fara'a ya ce "Barka dai Labeeba, ya Makaranta?" murmushi ta mishi tace "Alhamdulilah" shiga ciki tayi ta dauko Tabarma ta shimfida mi shi, ya cire takalminshi ya hau kai, Sabit ya zauna kan kafar Babanshi Amira kuma ta jingina da jikinshi yana musu tambayoyi suna amsawa.


Aunty Asiya ta fito daga Toilet da Buta a hannu, ta ce "Barka da dawowa Baban Amira" wani murmushi me k'ayatarwa suka ma junansu, da ba dan idon yara ba da sun rungume juna, da kallon kauna ya ce "Asee, ya Gida ya Yaran?" ta ce "lafiya lau, ya Kasuwan?" ya ce "Kasuwa Alhamdulilah, kin san sai da na bar kasuwa na ga message dinki? Sai da na shigo Unguwa na tsaya shagon Eskaley dinnan na siyo Magunan" ya k'arashe tare da mik'a mata ledar Maggin.


Murmushi tayi ta ce "Maggin ke nan nayi amfani dashi a Abincin rana, shi ya sa na ce bari na maka text ka taho mana da shi" ta karba tare da isa kitchen inda ta iske Labeeba na jera Cooler din Abincin Baban Amira a Tray, karban Tray din tayi ta ce "Fasa k'ankarar nan cikin Sobon" Labeeba ta amsa mata da "To" ta bude dan firij din da ke kitchen din ta dauko kankarar ta fasa ta juye a Jug.


Duk da su Sabit sunci Abinci sai da suka taya Babansu cin na shi. Ya ce "Wai ya ba a je Islamiya ba yau?" Ameera ta ce "Baba yau fa Alhamis" yace "Afuwan na shafa'a, to ina Homework dinku, na tabbata an baku" Amira ta ce "Sai da daddare zanyi nawa" Baban Amira ya ce "Aa, kuyi yanzu tun ido na ganin ido, ba sai dare ya yi ba, ba wuta a rasa yadda za'ayi" Aunty Asiya ta ce "tashi ku dauko Aunty Labeeba ta koya muku" Rige-rigen tashi suka yi suka shiga dakinsu.


Baban Ameera ya ce "Labeeba to ya Makarantar?" ta ce "Wallahi Yaya Ranar tsiya, kaji zafi, ga nisan tsiya" Aunty Asiya tace "nan ta shigo min kamar zata kife" dariya ya yi yace "Haha, yarinya yanzu kika fara, baki ga komai ba" tace "Wai Allah!" duk suka yi daria.


Ta danyi kewar Gida, tana kewar Mamarta, da yanuwanta, sosai take kewan mahaifarta inda ta girma, amma tana jin dadin zaman Gidan Yayanta sosai, tana sha'awar yadda Yayanta ke tafiyar da Gidanshi, bata da damuwar komai, to damuwar me za ta yi tana gidan Ɗan'uwanta Shak'iki, ga kuma Matarshi da ko kusa ba ta da matsala, ga Yaran Yayanta masu matuk'ar kaunarta, zama da su kan dauke mata duk wata kewa. Haka yanzu ta zauna ta ci gaba da koya ma Amira Homework dinta, sai da ta gama kafin ta ma Sabit da yake shi Tracing ne.


***
6:35pm


Baban Amira ya tashi ya shiga bandaki ya fito tare da daura Alwala, ya kalli Sabit ya ce "Mallam Sabit muje Masallaci ko?" Sabit ya mik'e da murna ya yi alwalarshi duk da ba daidai bane, ya rik'o hannun babanshi. Aunty Asiya da ke kitchen tana tuk'a tuwon dare Baban Amira ya lek'a ya ce "Asee, mun tafi Masallaci, sai bayan Isha'i in Allah ya kaimu" fatan dawowa lafiya ta musu, Labeeba ma haka suka fita daga gidan rik'e da hannuwan Juna.


Suna nan zaune har aka kira Sallar Maghrib, cikinsu babu wanda ya yi yunkurin tashi zuwa Sallah duk da Massalacin na gefensu.
Har Baban Amira ya ketara su ya dawo baya ya ce "Dan Makaho, kuna ji ana kiran Sallah, kuna nan zaune, haba kuji tsoron Allah mana" Tero yace "kai Mallam kaga an Sallame Sallar ba muyi ba ne?" Baban Amira ya ce "ai gani nayi baku da niyya shi ya sa na ce bari na muku tuni" Haruna yace "Zamu yi anjima" Baban Amira yace "Haba, da hankalinku? Anjima? Yanzu me kukeyi? Kun san hukuncin masu Tarrikus Salat? Jinkiri wurin yin Sallah? Kunsan fallalar Jam'i" Master yace "Kaga ba ruwanka da mu, in kai ke karban Sallahn kar ka karbi namu".


Dan Makaho ya mik'e yana kallonshi da mak'allelen idonsa da k'yar yace "Yanzu za mu tafi".
Baban Amira ya kalli Master yace "Aa bani ke karban Sallar ba, tuni ne nawa, Allah ya shirya" ya ja hannun Sabit suka wuce tare da k'etara Titi suka wuce Masallaci.


Cikin muryan yan shaye-shaye Master yace "Kai Mankas naga sai wani lallaba Gayen nan kake, daka barshi dan uwattai, kallon kafirai yake mana" Dan Makaho yayi tsaki yace "Eskaley bani Ruwa leda biyu" Eskaley ya mik'o mai Ledar Pure water dan gefe ya matsa ya fara Alwala.
Haruna yace "kai ma dai Master, bak'ar magana ka gaya mishi, ni ban ga laifinshi ba" Tero yace "Yan Unguwanan Gulma buroba ne dasu, Master ka min daidai" Haruna ya mik'e shima ya karbi ruwan ya matsa inda Dan Makaho yake shima yayi Alwalarsa. Master kuwa da Tero zamansu sukayi, suna kuna Sigari. Har Eskaley ya fito ya kulle Shagonsa, Master da Tero suna nan zaune.
Su uku suka nufi Masallacin Unguwansu da ake ma lak'abi da Sharp-Sharp.


Vote and Comment line by line


#1love
#DM
#anatare
#FWA
#nagode


Biebee Isa.
[14/03 9:35 pm] Biebie: Babi na Biyu 2⃣
(SHARRI)
4/05/2013


Kan'nannen Idonshi ya dago ya kalli Sady da ta ke zaune a gaban dakinshi, da alama shi take jira, ya dan k'araso da sauri yace "Ya akayi ne Sadiya" ya tambaya fuska cike da damuwa, kamar ba zata amsa ba tace "Barin Gidan nan zanyi" ido ya dan ware kafin ya murza Idonshi yace "me ya faru?" bata amsa shi ba, ta sake jadadda mai da "Gidan nan zan Bari" dan mur ya sha kafin yace "ba inda zaki, ba ki da inda yafi nan, ni a matsayina na miji ban bar gidan nan ba, kema ba zaki bar gidan nan ba" kuka ta fashe dashi ya matso gareta ya janyota jikinshi ya rungume yana shafa bayanta alamun lallashi, ya sama magana a hankali "Sady, komai zi wuce--" Be karashe maganar da ya so mata ba sukaji ana rafka sallati a bayansu "Inallillahi wa ina ilaihir rajiun, DanMakaho kanwarka kake runguma haka? Kana shafa mazaunanta?" cike da tashin hankali suka sake juna suna kallon Aunty Shafa'atu Matar Babansu. Bambamin da ta hau yi ne ya sa mutanen Gidan suka firfito, Aunty Shafa bata bar tafa hanaye tana jefansu da mugayen kalamai ba.


Jikin Sady na bari ta karasa gunta tace "Aunty Shafaatu donAllah kiyi shiru, wallahi ba wani abu bane, kin manta Yaya Zaid Yayana ne Muharramina Shakikina?" hannu Aunty Shafa'atu ta sa ta buge bakin Sady tace "yi min shiru Munafuka, yau kuka fara shafar juna kuna iskanci? Shegia Yar Shegia Karuwar Yayanta.".


Ran Mankas ya baci ainun, be san lokacin da yayi wani tsalle ba ya shak'o wuyan Aunty Shafa'atu ba ya danganata da bango, k'aninta Hudu ya yo kanshi, be saketa ba, k'ak'arin mutuwa take tana jin azaba tace "DanMakaho kasheni zakayi? Hudu ci man ubanshi" kamar umurninta yake jira, nan ya fara dukkanshi yana kai mai naushi ko ta ina, ko motsi beyi ba illa kara matse hannunsa da yayi a wuyanta.


Fati da Annah suka rufe Sadiya da duka durkusawa tayi tana kuka ba su bar dukanta ba, kukanta yaji ya tsananta, ar yanzu su Hudu ba su bar dukkanshi ba kuma be saketa ba, kukan da Sadiya keyi ne ya sa shi sakin Anty Shafaatu ya karasa gun su Fati ya finciko su yana kai musu duka ko ta ina,.
Sarkin yawa ya fi sarkin karfi, nan suka hadu gabaki daya suka ma Sadiya da Mankas dukkan tsiya.
****


Bangon Kantangarsu daya, ko meke faruwa a cikin Gidan Alhaji Zaki musamman ta wurin BQ suna ji kamar a cikin Gidan akeyi, suna zaune baki daya kan darduma sukaji muryar Hajia Shafa'atu na cewa "Inallillahi wa ina ilaihir rajuun, DanMakaho kanwarka kake runguma haka? Kana shafa mazaunanta?" zumbur suka mik'e tare da matsawa kusa da bangon Gidan.
Suna nan tsaye jigum-jigum, sunji komai kamar gabansu ake, jikinta sai bari yake, baki na rawa tace "Aunty Asee kar su kashesu, muje mu rabasu DonAllah" Aunty Asee tace "hmm, Labiba ina mu ina shiga fadan Gidan Alhaji Ali Zaki? Haka suke, ai sun dade ma basuyi ba, haka suke wallahi".


Muryar Alhaji Ali sukaji yana fadin "Me ke faruwa a gidan nan ne? Da alamu yanzu ya shigo Gidan, da sauri suka tashi daga jikinsu Mankas. Anty Shafaatu ta fashe da kuka ta matsa kusa dashi cike da kissa "Nagaji Alhajina, nidai ka sakeni, ba zan iya ba, har sai yaushe Dan Miji zai bar dukana? " Hankali tashe yake tambayarta me ya faru, ta ja majina tace "Zuwa nayi baya naga DanMakaho na ta latsar Sadiya yana mata wasu abubuwan da na kasa hakuri sai da na mishi magana na nusar dashi Kanwarshi ce Muharamma, in kuma aure yakeso ya fada sai a mai, bansan ya akayi ba sai dai kawai naga ya kaini k'asa yana dukana Sadiya na tayashi da kyar su Hudu suka zo suka karbeni daga hannunshi".


Labiba ta bude baki tana kallon Aunty Aseeyah tace "Laah Aunty Karya takeyi, wallahi karya take musu, ba abunda ya faru ba kenan, karya ne" Aunty Aseeyah ta tabe baki ta koma kan dardumanta ta zauna tace "Labiba, meye naki? Sharri ai ba yau ta saba k'ala musu ba, In Allah ya tashi saka ma DANMAKAHO da k'anwarsa wallahi sai Hajia Shafa'atu ta wulakanta ta shiga hakkinsu sosai, wata irin Mata ce da muke neman tsarin Allah daga garesu".


Jin muryar Alhaji sukayi yana cewa "Allah ya tsine maka Zaid, matar tawa ka buga? Allah ya tsine ma ban yafe ba, watsatsse kawai" Labiba ta fashe da wani irin kuka, kamar ita a ka tsinemawa Aunty Aseeyah ta kallota tace "Labiba" cikin kuka tace "Aunty Asee Mahaifinshi ya tsine mai, Mahaifinshi ya laanceshi, be san gaskiar abunda ya faru ba, ya hau kan maganar matarshi, zanje in gaya mai gaskia, wallahi zan gaya mishi matarshi k'arya takeyi" ta zabura Aunty Asee ta taso don kamota, amma bata ci nasara ba, har ta kusa k'ofar Gidan Baban Sabit ya shigo, hakan ya sa tayi turus.


"Ina zakije?" kamar bata cikin hayyacinta tace "K'arya Auntynshi take mishi, wallahi ba haka akayi ba, ina bakin katanga, naji komai, yaya Babanshi tsine mishi yake" Baban Ameera ya kalli Aunty Aseeya, girgiza mai kai, ya sa hannu ya rik'o Labeeba ya jawota har tsakar gida ya zaunar kan tabarma yace "me ya faru" a hankali Aunty Aseeya ta bashi labarin abunda suka ji, jinjina kai yayi yace "to ke me zai dameki?" Majina ta ja kafin tace "Yaya, wallahi Allah sharri suka mishi, k'arya suke" ganin tana magana kamar me shirin fita hayyaci, ya ma matarshi alamu da ta shiga da ita ciki.


Aunty Aseeya ta kamo hannunta ta ja ta zuwa daki, bakin Gado ta zauna ta rafka uban tagumi, Aunty Aseeyah ta fita gun Mijinta, Kubra ta rasa me ke mata dadi, bata da kuzari, ko da suka zo bacci, hakan tayi ta juyejuye, haka Labeeba ta k'arashe darenta.


Washegari da safe idanunta sunyi luhuluhu saboda kukan da taci, bata san shi ba, amma abunda aka mishi ya tsaya a ranta, to shi wani iri ne da ba zai iya kare kanshi ba? Meyasa ba zai iya furta k'arya ake mishi ba? Shi sakarai ne? Haka ta tashi tayi shirin Makaranta, ta shiga ta gaida Aunty Aseeyah, Baban Ameerah ya kai yara Makaranta, Aunty Aseeya tace mata ta tsaya ta yi kalaci amma tace sauri take ta makara, adduan samun nasara ta mata, ta rakota har bakin k'ofar gidan, Adduan fita daga Gida Labiba tayi ta fice ta bi dogon hanyar unguwarsu ta Tudun Matawalle inda zata neman abun hawan da zai kaita National inda zata hau Motar Makaranta (School Bus).


Kasancewar Safiya ce, Unguwar bata cika sosai ba kamar yanda take cika wurin k'arfe 11 na rana, tafiya take cikin dan sauri, unguwar sai an fito bakin Titi ake samun abun hawa.
Daga chan nesa ta ke hango wani zaune na busar sigari, da sauri ta zaro wayarta don ganin lokaci, 8;17am, mamaki ya cikata, wanene ke banka ma cikinshi hayak'i da sassafe haka, da ta k'araso gurin sai ta ga matashin saurayine, daidai nan ya murje guntun da k'afa ya sake kyasta wani da ya zaro daga aljihun gaban rigarshi ya fara zuk'a.
Labiba ta dan yi jim tana kallon bawanAllahn nan, Zuciyarta na tunzurata kan taje ta mishi magana. Har tazo ta gabanshi ko kallonta beyi ba, haka ta tsallaka titi tana waigenshi har ta samu kekenapep da zai kaita National don tafia Hassan Usman Polythecnic.


#1love
#DM
#SonSo
#anatare
#Fikrawriters
#nagode


Biebee Isa
[14/03 9:35 pm] Biebie: Babi na Uku3⃣


('YAN MAKARANTA)


Har lectures din ya k'are Labeeba bata fahimci komai ba, a hanyarsu na zuwa Masallaci yin Sallahr Azahar, Aisha Usman K'awarta take tambayarta lafiya yau ta ganta wani sukuku da ita, jim tayi kafin tace "Kaina ne yake dan ciwo amma ya bari yanzu" Aisha tace "haba ni dai ince, yau na ganki ga ki nan, Allah ya sauwak'e" murmushi Labiba tayi tana kara k'allon k'awarta.


Kafin su k'arasa Masallaci suka ji ana k'wala musu kira ta baya, dakatawa suka yi tare da dan waigawa, cikin hanzari ya k'araso yana me sakin su da k'ayattacen murmushi.


"Aisha, Labeeba, ya kuke?" a tare suka amsa masa da Ina wuni Captain Abu Sideeq? Ya amsa tare da cewa "kun gama lectures din yau ai?" Aisha ta gyada kai, Labeeba tace "eh mun gama" yace "Good, to kuje kuyi Sallahr, ku sameni a Ajinmu, sai mu duba karatun yau ko na 1hr ne" amsawa suka yi tare da wuce shi don nufar Masallacin.


Aisha tace "Son ki yake" Murmushi Labiba tayi, tace "na sani" da doki Aisha tace "I knew it, kema kina sonshi?" Labeeba ta sake wani murmushin kafin tace "ina dai ganin mutuncinshi, yana kuma burgeni, ina son naga mutum me k'wazo da basira" Aisha ta dan tafa hannuwanta tace "a sannu kema zaki fara son shi, ai ya hadune ya hada komai, ga bokon, ga addinin, ga kuma Kyaun".


Labiba tace "ba k'arya".


Daidai nan suka iso Masallaci, ko waccen su ta d'auki buta ta nufi Fampo.


Sun idar da Sallah suka nufi ND2 inda AbuSideeq yake, yana ganinsu ya k'araso yana jefan Labiba da wani irin kallon da shi kawai ya san ma'anarsa.


Murmushi kawai Labiba tayi, yace "muje daga k'arshen Ajin, yana gaba suna bin shi a baya, daga can suka samo Bench suka zauna, shi ne a tsakiyarsu, ba bata lokaci suka hado masa Jotting din Lectures Biyu da suka yi yau, dubawa ya yi kafin ya shiga yi musu bayani cike da k'warewa.


K'arfe 2:30 ya ce su dakata haka. Godiya suka masa me tarin yawa, ganin yadda AbuSideeq ke bin Labiba da wani irin kallo ya sa Aisha ta dan mik'e ta ce "bari na dan amsa waya".


Ganin haka yasa AbuSideeq fara magana "Labiba..." sai kuma ya yi shiru, ya sake fadin "Labiba ina... ina..." sai ya sake yin shiru, sai da, mintuna kusan 4 suka wuce kafin ya ce "bansan ya zaki dauki maganar nan ba, amma ina so in fada miki wani abu, amma kuma dai na kasa, k'ila rashin faden shi ne Alheri, bari kawai in bar shi, tashi muje na rakaku ku samu abun hawa".


Dago idanuwanta tayi ta kalle shi, kafin ta saukar da kai ta fara magana cikin sanyinta ta ce "So na kake yi, kana jin nauyi na, kana tsoron yadda za ka gaya mini, kana gudun kar hakan ya zaman silar bacewar kyakyawar Alak'ar da ke tsakaninmu?" da sauri ya kalleta.


Kai ya fara gyadawa kamar k'adangare. "Haka ne, wallahi haka ne Labiba, tun farkon haduwarmu a office din HOD, lokacin da Yayanki ya rakoki Registeration na kamu da sonki" Labiba ta danyi murmushi ta ce; "Ban yi mamaki ba, its obvious ai".
K'arfin guiwa ya samu, ya ce "Ina fatan zaki amince mini?" murmushi tayi ta ce "wallahi ban sani ba, bansan me nake ji a kanka ba, bansan me zanji nan gaba a kanka ba, amma nasan cewa ina matuk'ar ganin girmanka, sosai kake burgeni Captain, bansan ko nan gaba wata alak'a da ta wuce wannan zata shiga tsakaninmu ba, amma ko me ke nan, Allah ya zaba mana abin da yafi Alheri a rayuwarmu".


Kallonta kawai ya tsaya yi, sosai ta burgeshi, sonta na k'ara ruruwa a zuciyarshi, bai taba ganin irinta ba, bai taba sanin Matan Katsina na iya kallon Namiji haka su gaya masa gaskaya ba tare da wani 6oye-6oye ba, ba ta rufe mishi komai ba, ta gaya mishi iyakar gaskiyarta, hakan da tayi ta matukar burge shi, yana da tabbacin da wata ce, yaudarar shi za ta yi, ko ta ce mishi eh itama tana sonshi ko don wani abu, ko kuma ta bata mishi lokaci, ko kuma ta ja mishi aji, haka yake so Mata su kasance Straightforward, in ana haka, da ba a samu Yaudara da cin amana a cikin Soyayya ba.


Mik'ewa yayi yace "tashi muje na nema muka abun hawa" murmushi tayi tare da sa6ar jakkarta, ta bi bayanshi, a bakin kofa suka ga Aisha, tace "muje ko?" Labiba ta gyada kai, a haka har suka fita bakin makaranta ya tsaida musu keke Napep, fadin inda zasu sukayi, mai Keke Napep yace "ke ta tudun Matawalle ciki zaa shiga?" Labiba tace "eh ciki ne ta wurin Makarantar Hope" yace "150 ne kudinki, ke kuma ta k'ofar k'aura layout ki bada 250" da yake hakan suke badawa ba su tsaya ciniki ba.


Aisha ta fara shiga kafin Labiba, Labiba na ganin AbuSideeq ya sa hannu cikin Aljihu tace ma Adaidaita sahu, mu tafi kaji" ba tare da bata lokaci ba ya ja Kekenshi, ta dan juyo ta daga ma Captain hannu, shi ko yatsarshi ya nuna mata alamun "ke ko" kafin suka sakar ma juna murmushi.


Aisha tace "Bawan Allah, be gajia" Labiba ta gyara zamanta tace "kullum cikin Hidima yake".


**
Abu Sadeeq Abu, dan Department of Engineering HUK Poly, wani irin Yaro ne me matuk'ar k'okari, HND2 yake, a nan ya gama ND ya jona HND dinsa, a Dept din kowa na sonshi sabida kyakyawar Alak'ar da yake dashi da Malamai da Dalibai, k'okarinshi be daura mai Girman kai ba.


So da yawa in ana darasi, kace ma Mallami ba ka gane darasin yau ba, zai ce "ka sa min AbuSideeq a HND2 ya ma bayani zaka fi ganewa" hakan ne ya faru da Labiba a ranar da suka samu Mallama Amina bayan darasi, tace "ta sake mata bayanin wani fannin da bata fahimta ba" mallamar tace "Wallahi sauri nake, amma kije HND, ki samu a AbuSadeeq a HND2, kice ni na aiko ki, ya miki bayanin topic din". Labiba ta mata godia ta ja Aisha suka tafi inda Mallama ta mata kwatance.


Ko da sukaje sukayi tambaya, nuna musu shi akayi, yana tsakiyar maza biyu da mata 3 daga gani 'yan ND2, yan gaba da ajinsu Labiba, yana ta faman musu bayani. Aisha tace "mu jira ya gama, ko muje mu dawo" Labiba ta girgiza kai ta musu Sallama" suka amsa tace "ina wuninku? DonAllah Abu Sadeeq muke nema" kallonta yake yi sosai, yarinyar nan ce da Yayanta ya kawota office din HOD ranar da yake ciki, murmushi ya mata yace "Ga wani Abu Sadeeq nan"
Murmushi tayi sosai, ta ganeshi, shine HOD yace mata in tana da matsalar karatu ta zo gurinshi zai mata bayani".


"Sannu da Aiki, Mallama Amina ce tace na sameka, wani abu ne ya shige min duhu a course dinta, shine nakeso in kana da lokaci ka dan min bayani" Agogo ya kalla, kafin yace "Alright ba damuwa, amma ga yayyinki nan muna karatu, saidai in mun gama" tace "lahh dama ai sai kun gama" yace "to nam da 30mins InshaAllahu" murmushi ta sakar masu duka, sosai ta burge duk na wurin, tace "bari mu dawo" ta ja hannun Aisha da ba tace ma kowa komai ba.


Ya musu bayani yanda ya kamata, Labiba da Aisha sun fahimta, suka mishi godia sosai, yace musu daga yau duk bayan ko wane lectures suzo ya sake musu bayani, hakan zaisa su fi fahimta. Godia suka sake mishi, tare da exchanging numbers.


Tun zuwansu Poly Aisha ke tare da ita, tana son Labeeba sosai, duk da a Ajin Maza sunfi Mata yawa, matan basu wuce sha biyar (15) amma Aisha bata da k'awar da ta wuce Labiba, ko wata daya basu rufe a Makarantar ba, amma Aisha na jin Labiba har ranta.


Labeeba za ta iya rantsuwa

Please Login or Register in order to submit comment