Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba, suna ta yabon Zaid don yana zagayowa jefi jefi.
Nan aka sanar dashi Mijin Mariya diyar kanwar Mamarsu ya rasu.
Da mamaki yace "Mariya tayi Aure?"
Shiru sukayi, basu manta wulakancin da ya musu ba da sukaje neman taimako suna so ai mata kayan daki.
"Kai Kai, Allah ya tsine miki Shafaatu, ban yafe miki ba, kin shiga tsakanina da Yanuwana, Allah ya mana sakayya suka amsa da Amin".
Zuwa sukayi suka mata gaisuwa, Goggonshi ta kebe dashi tace "Mariya ta kusa fita takaba, in kana so ka nemeta".
Alhaji Ali yayi saurin kallon Dalo.
Dalo tayi daria tace "Allah Baba ka aureta, ai Aunty Mariya mai kyau ce".
Ya harareta, bai dai ce komai ba.
Goggo tace "Mariya na da hankali, da kuruciyarta, ko shekara 34 bata yi ba, yaruwarka ce, tun da kai ka ki auren zumunci, amma yanzu shi zamu maka, ko ka ki ko ka so".
Yayi daria yace "Ban ma k'i ba ina so".
Tayi daria tace ja'iri.
Bai bar Family house ba sai da aka kawo mus trailer na kayan abinci, ko wani gida sun samu buhu uku uku na shinkafa da kwalayen taliya, jarkan mai, har ta ashanar da zasu kunna sai da aka kawo
*****


Mancy ta iso Asibitin dauke da breakfast wanda Antisco tayi, bayan sun gaisa tace ya masu jiki, Baban Amira yace "ah jiki da sauki".
Ta kallesu tare da murmusawa bacci suke gabaki dayansu".
Tace "Mallam Muhammadu ka tafi gida kayi wanka, zan zauna dasu".
Yace "to ya tafi Mancy ta zauna ta jira har farkawansu".
Suka gaisheta Labiba tace zata shiga toilet Mancy ce ta taimaka mata har toilet, ta dawo da ita, ta basu breakfast, ta ba Zaid na shi ta hada ma Labiba tea ta na bata a baki, kunya duk ta kama Labiba. Zaid kam yaji dadin yanda ya gansu.


Ta isa Gidan maigadi yace ai sun fita, Asibiti ta nufa bata ga kowa ba sai Mancy.
Mancy tsoro ya kamata. Kar ta musu wani abu, waya ta kira Sadiya tace "ina Babanta? Ga Shafaatu nan tazo".
Aiko dalo na gaya ma Baba suka nufo Asibiti a sittin.




#1love
#DM
#anatare
#SonSoFWA
#nagode


Biebee Isa
[14/03 9:35 pm] Biebie: DAN MAKAHO πŸ˜‰


πŸ’ƒπŸ»AURE πŸ’


K'ARSHE


Zaid ya kalleta yace "me kike yi a nan?".
Tace "ashe baka mutu ba, naji haushi".
Yace "Ki fita daga dakin nan".
Shafaatu tace "Ubanka nike jira yazo, in yazo sai na tabbatar da ba zaku sake ganinshi a rayuwarku ba".
Mancy tace "Ashe abunda kika min da 'ya'yana bai isheki ba?"
Shafaatu tace "kar ki sake ki dameni, bari zan jira shi a waje".
Mancy ta basu labarin abunda ya faru jiya da daddare sosai sukayi Al ajabi.


Sai ko gasu sun iso da danginshi kusan su 12.
Tana ganinshi ta warwaro Powder din ta nufeshi gadan gadan zata shafa mai a goshi.
Tuni K'anin Alhaji Zaki ya tande mata k'afa ta fadi k'asa, kamar jira suke suka fara dukkanta Mazansu da Matansu, ko wannensu na fanshe bakincikin da suka k'unsa sanadiyarta. Ihu takeyi sosai.


Tuni sun mata Habo baki ya kumbura ido ya kumbura jini ta baki, ita burinta ta shafa mai Powdern nan a ka.
Rirriketa sukayi Alhaji Ali ya tako gabanta yace "Tsakanina dake sai Allah ya isa, ba abunda zance miki, sai tsinuwar Allah su tabbata a kanki, Allah ya saka mana tun a duniya, da ni da yarana ba zamu taba yafe miki ba, Allah ya sa ki wulakanta ki kask'anta anan dunia, Allah ya isa, mai sama mai kowa mai komai zai mana maganinki".


Wani daria ta fashe dashi wanda duk wanda yaji ya san bana lafia bane.
Chan sai taji muryan Mallaminta Baban Annah yace "ba na ce karki hada aikina da nakowa ba? Karshenki yazo".


Kamar an kunna mata battery ta fashe da daria "Hahahah, Alhajina, ni ce fa Matarka Shafaatu, ka manta ka tsani Dan makaho, ka tsine mishi ko zan ji dadi".
Da k'arfi kamar Lasfika ta fara tona ma kanta Asiri.
Nan dangin Alhaji Ali suka sake rufeta da duka kamar dama jira suke, mutane suka zagayesu suna kallo kamar film.
Daga dakin su suna jiyo duk abunda ke faruwa a wajen Amenity.
Ba me ce ma kowa komai, suna mamakin irin aikin sharrin da Shafaatu ta tafka.
Zuwan Alhaji Ahmad Dakata ne ya tsaidasu, yace "haba, ku kyaleta, so kuke ku kasheta? Kar ta mutu a hannunku, ku badata ga Hukuma".


Saketa sukayi, ko zafin da jikinta yakeyi bataji, mikewa tayi ta kakkabe jikinta tace "K'uran ko a jikina , ta musu gwalo".
"Alhajina tsaya in shafeka da hodar nan mana, boka yace "da ya taba goshinka zakayi duk abunda na saka".
Danginshi ka sa jurewa sukayi, wani k'anenshi mai zafin rai ya fincikota ya sata Mota, ya shiga ya Jata ya je ya yasar a wajen Asibitin kamar wata Bola.
Nan ta fara tsince tsince tana tattarawa a rigarta, chan sai ta ji wani shagon saida films na tashi da sautin kida, rawa kawai ta saka mai karfi, hankalin mutane ya dawo kanta, tunbur tayi haihuwar uwanta, wani maigadi ya biyota ta arta a guje, lokaci guda ta fita hayyacinta duk ta haukace ta susuce.
*
Hajia Clean aka gaya ma angs Hajia Shafaatu ba bin bololi a Hanya, Hajia Clean ta tsorata da taje ta gane ma Idanunta, dawowa tayi ta fattataki Annah tace ta fitar mata a Gida.
Annah taje ganin Mamarta a inda Hajia Clean tace ta ganta, tana ganinta ta kasa karasawa saboda warin da Mamarta keyi, Shafa ko na ganin Diyarta ta dinga binta da Gudu, Annah ta zabure ta ruga a guje tana kiran a taimaketa Mahaukacia na binta.
Annah ta samu wani shago ta boye, nan taji wani dan daudu na cewa yana da ikon sa yanmata yin kudi, Annah tace "ya taimaka mata" yace to baki da damuwa zakije ko ina ne? annah tace "ko ma ina ne zani wallahi".
Yace "kar ki damu, ni zan chanza miki rayuwa, zakiyi kudi".
Washegari Annah ta bi dandaudun nan Lagos tafiar Mota ce, dukta wahala.
Wannan shine Silar shigan Annah Dunia.
****


Kwanansu Zaid bakwai a Asibiti sosai suke jin dadin jikinsu, kullum zuwa ganinsu akeyi, har 'yan bencin eskaley sunzo, ana gobe zaayi Sallama Dr Ali ya bukaci a je a ma Zaid Xray a ga status dinshi.
Nurse tazo ta tafi dashi.
Akayi aka dawo dashi sai bayan 4hrs Dr Ali ya bukaci Labiba da Zaid a office dinshi.
**
Dr Ali yace "Zaid, na kiraku ne nan don na gaya muku status dinku duka".
"Labiba you are fit, amma kai Zaid akwai wata 'yar karamar matsala wanda in ka kiyaye to ba wani abu bane, ribs dinka is affected yayi bak'i, in baka bar hayak'i ba it can backfire anytime and you wont be lucky as you are now, amma in dai zaka dinga shan magani, kuma ka daina shan Sigari to lafia lau, and then zaka dinga samun frequent attacks, in dai kana shan magani, komai zai zo da sauki".
Zaid ya murmusa yace "Nagode Babana, na bari wallahi".
Dr Ali yace "Allah Sarki Yasmin, da kina nan da sai kin fi kowa jin dadi Zaid ya bar Hayak'i".
Zaid yayi murmushi mai ciwo yace "Yasmeeen, Allah ya rahamceki, Allah ya biyaki da Aljannah".
Labiba ta amsa da Ameen.
Dr Ali yace "barin je round"
Ya mik'e ya tafi ya barsu.


Labiba tace "kayi Missing dinta ko?".
Ya girgiza kai yace "fiye da tunaninki, nayi missing Yasmin, banda abunda zan biyata da shi, Yasmin ta mutu lokacin da ban taba zato ba, amma na ji mata dadin Shahadarta, Allah ka amshi Shahadar ka sa Yasmin na cikin walwala yanzu".
Labiba ta amsa da "Amin, sai ka mata takwara in mun haihu".
Zaid ya dan kalleta yace "Aure? Aure zamuyi?".
Ta daga mai gira tace "Yesss".
Yace "bakiji yanzu ance zan dinga samun attacks ba? I can die any time in nayi wasa da magani".
Tace "Sai mu jira mutuwarka, sai nayi takaba".
Ya kalleta confidence din na nan, sarcasm din na nan yace "i am serious, nifa ba zanyi aure ba, kar nayi aure na mutu at young age, na bar matata maybe da diyata ko yaro a karamin lokaci".
Labiba ta harareshi tace "aure kam zamuyi".
Yace "ba zan iya ba, zan ha'inceki na aureki yanzu, i am still sick wallahi, aurenki saura wata daya ke da Jawad".


Tace "to ka na nufin na baka Hantata a Banza? Kai tsaya ma kaji, wallahi baka isa ka zauna ba aure ba, ba kuma ka isa ka auri wata ba ni ba, Hantata a jikinka sai ka auri wata banza chan? Chabda, shi kuma Jawad ai he is not stupid, na san wallahi ba zai aureni ba, ya zaayi ya aureni bayan ya san abunda nayi, bayan ya san akwai wanda nikeso?".
Zaid ya kalleta cike da kauna yace "wa kike so?"
Tace "Zaid Ali Zaki nakeso".


Yayi daria yace "In Abbanki zai bani ke ina so".
Tace "Abbana zai baka ni InshaAllah, ehen Mallam, kadai ji ance ka bar shan hayaki ko? Wallahi duk randa na kamaka da ko lighter ne sai mun dawo Asibiti an sake budeka an ciro Hantata an mayar min cikina, ba zan yarda ka kona min Liver ba".


Yayi dariya yace "au Gori zaa min?"
Ta harareshi cike da k'auna tace "an maka goruba ma ba gori ba, kaidai ka kiyaye".
Yace "Yes Ma".
**
Suna fitowa daga Office din suka ci karo da Jawad.
Zaid ya dan kauda kai tare da yin gaba.
Jawad ya rik'o shi tare da cewa "Masoya, soyyayan har a office din doctor?" Ba wanda ya iya cewa komai.
Yace "Ya jikinka Brother?".
Zaid yace "Na ji sauk'i Alhamdulilah"
Jawad yace "Thanks to Labiba ko?".
Zaid yayi shiru kafin yace "Yes, thanks to Labiba kam, kar ka damu i know shes your wife to be".
Jawad yayi murmushi yace "Nooo, You can have her".
Sukayi saurin kallonshi ya gyada "kai yace kai take so, ko ba shi kike so ba ni kike so?".
Da sauri ta gyada kai "aa shi nakee so". Yayi daria yace "Allah ya barku tare, in an dauko maganar zan gaya musu na bar maka ita".
Zaid zai yi magana Jawad yayi gaba abunshi.
%%%%


A tare aka sallamesu.
Alhaji Dakata ya tattara Iyalanshi suka tafi Masaukin da Alhaji Ali ya basu.
Alhaji Ali ya kalli Dalo yace "zamuje gidan ne?".
Sadiya tace "Baba lets go on a date, ni da kai da Yaya Zaid".
Baba yayi daria yace "Ni Masoyinku ne da zaku date dani?".
Dalo tace "sosaii Ma".
Baba ya kalli Zaid yace "Muje?".
Murmushi yayi yace "Muje Baba".
Alhaji Abu yayi murmushi tare da mik'a ma Alhaji Ali hannu yace "to Alhaji a sha Soyayya da 'ya'ya lafia, mu bari mu isa gidan Hajia".
Yak'e kawai yayi tare da gyada kai.
Mancy ta ma yaranta byebye ta shige motar Mijinta, Jawad ya rufa musu baya.


Alhaji Ali yaga Mancy ta shige Motar Mijinta sosai ranshi ya sosu, ya kamata ya cireta a ranshi, ya san cewa ta mishi nisa, don yana da tabbacin ba zata rabu da Mijinta ba don ta dawo gunshi, abu ne da ba zai taba yiwuwa ba, ya san ta wuce mai nesa ba kusa ba, dole ya cireta a ranshi, ya zama dole ya hakura da ita
**^^**


Dakin ya zamana daga Labiba sai Maminta da Abbanta, tunda suka zo sai yau suka kebe.
Labiba cike da kunyansu tace "wallahi na san ban kyauta ba, wallahi Mami nasan na tada nuku hankali ranku bace yake".
Mami tace "Labiba baki da hankali, baki san ciwon kanki ba, ance miki So Hauka ne? Wani irin rashin tunani ne haka, namiji kike ma wannan zazzafan So? Baki san Namiji ba dan goyo bane".


Abba yace "Amina, godiar da zakiyi ma Allah kenan?"
Tace "dole fa a mata fada, bata kyauta ba, wani irin abune wannan? Yarimya ta task tundaga Edo State, tazo wai Katsina gun saurayi? Haba wannan rayuwa da mai tayi kama".
In akwai abunda Labiba bata so to fushin Iyayenta, nan tashiga basu hakuri tana kuka.
Tsakanin da da mahaifi sai Allah, nan suka yafe mata tare da mata fada sosai.
@@@


Zama sukayi a k'ayattacen wurin cin abinci, kowa ya fada abunda zai ci, a ka kawo musu, sai da suka gama ci kafin Baba yace "Zaid, ni fa kunyarka nikeji, ban san ta ina zan fara ba".
Zaid ya murza idonshi yace "Baba kunyan me fa?".
Baba yace "Zaid, ban kasance uba nagari wanda zakuyi alfahari dashi ba".
Zaid yace "Nagane inda ka dosa Baba, ba zan yarda ka nemi gafara na ba, ni wanene da zaka roki gafara na".
Baba yace "Zaid, na zalunceka, da bakina na laanceka, nine silar fadawan ka shayeshaye, na maka Illah".
Zaid yace "ba a hayyacinka ba, na san Babana na sona, a hayyacinshi ba zai taba furta min mummunar kalma ba, ban manta ba a da kana fada da duk wanda ya kirani da sunan DanMakaho, a cewarka sunan Banza ne, ta yaya zaka furta wani zagi da bakinka? Baba wallahi ko a da na san cewa ba yin kanka bane, shiyasa ban taba rikeka a raina ba".
Dalo tace "Baba nagaya ma tun ranar, wallahi muna sonka fiye da duk wani Namiji a duniyar nan, kar ka roke mu komai, mu zamu rokeka yafiya in bamu kasance 'ya'ya nagari ba".
Baba yace "Haram wallahi, kune ko 'ya'ya nagari, ina sonku fiye da komai wallahi, ku yi hakuri na kawo wacce ta rusa mana farinciki, ba zan taba yafe ma Shafaatu ba, gashi tun a dunia ta fara ganin sakamakonta, ina da Labarin ta haukace an kamata an tafi da ita Asibitin Mahaukata.
Tabe baki sukayi irin ko a jikinsu.
Yace "donAllah ku rokar min Mamarku gafara, ta yafe min".
Dalo tace "Allah Baba bakomai, kowa fa ya san duk abunda kayi ba yin kanka bane".
Yace "nidai please ku ce ta yafe min".
Zaid yace "InshaAllah Baba".
Baba yace "Zaid ka tuna Aunty Mariya?"
Zaid yace "Eh Baba, Mijinta ma ya rasu".
Baba yace "ka sani ohh nine dai bansani ba".
Zaid yace "me ya sameta".
Baba yace "wai Goggo wai na aureta".
Daria suka sa gabaki daya Zaid yace "to Baba ayi mana, ai dama ba zai yiwu ka zauna haka ba ba mata".
Baba yace "kun Amince?".
Sukace "dari bisa dari".
Yace "Allah ya muku Albarka ya sa ku gama da dunia Lafia".
Suka amsa da Amin.


Baba yace "Zaid Credentials dinka na nan, Alhamdulilah ban salwantar da su ba, Masters dinka kana da shaawar komawa London kayi ta?".
Zaid yace "Aa baba, barni in huta for now".
Baba yace "to shikenan, da degree dinka ai zan samo maka aiki mai".
Zaid ya yi alwashin tashi ya tsaya da k'afarshi yace "Baba, zan gabatar maka da abunda nike so nan ba da dadewa ba".
Ya kalli Dalo yace "ke kuma fa? Karatu ko Aure".
Dalo tace "Lahh Baba aure fa kace? Chab nawa nike ni? Ni gaskia Baba ka bari".
Baba yace "amma na fa ce ko karatu, bance aure zan miki ba, why are you focused on the last option?".
Zaid yace "because its what she wants, Aure take so Baba".
Baba yace "Exactly".
Dalo ta turbune fuska wai zatayi kuka.
Baba yace "wallahi Zaid ba zan kyaleka ba ka sa min yarinya kuka".
Sukayi daria, tare suka kasance aranar gabaki daya kafin suka koma gida Gab da Maghrib.


A na Gobe 'yan Edo da 'yan Abuja zasu koma garinsu suka hadu a wakeken Parlorn Alhaji Abu Shamsu dake nan garin Katsina.
Alhaji Abu Shamsu ya bude taro da addua.
Yace "To abubuwa da yawa sun faru, wanda duk abunda ya faru yana daga cikin pegin layin k'addararmu, dubararmu ba zata iya hanata faruwa ba.
"Alhamdulilah Allah mungode maka, Allah ka sa duk mu ci wannan jarabawar, Allah kanyafe mana duk mu yafi Juna, kuma wannan zumuncin Allah ya riga ya hada babu mai rabawa".


Alhaji Ahmad Dakata "ya dora nashi jawabin yana kuma mai bada hakuri, tare da cewa Jawad yayi hakuri da Labiba, don kamar ya kwareshi ne in ya bashi Labiba, Labiba zata cigaba da Makaranta har Allah ya kawo mata wani Mijin".


Alhaji Abu yace "wani Miji? Ai Allah ya kawo mata tuni da dadewa".
Sun san inda ya dosa Alhaji dakata yace "anya amma Jawad Adalci in aka ba Zaid Labiba?".
Alhaji Abu yace "yo saboda me? Da Zaid da Jawad duk 'ya'yana ne, ko ni ba zan aura ma Labiba kowa ba sai Zaid, Sadakinta na hannunka ka manta wanchan mancewa nayi da naje Edo, so nayi nace nazo neman auren ma Zaid Aure na ce Jawad subutan baki ne".


Alhaji Ali Zaki yace "wai ya ake ta min passing passing da diya ne? In ba ku so ku bar min ita, na kaita madina tayi karatu ta kawo min balarabe, ha'an".


Sukayi daria Alhaji Abu yace "Allah baka hakuri su masu diya".
Alhaji Dakata yace "ni dai koms meye sai naji daga bakin Jawad, in har be amince ba, wallahi sai dai ciwon so ya kashe Labee, sai dai ta auri wani ba Zaid ba".
Jawad yace "Abba wallahi bakomai, na bar mishi ita, na yarda, Zaid ai danUwana ne, Allah ya kara musu Son So"..


Alhaji Abu yace "Fak'at, Hajiyoyi me zaku ce?".
Mancy tace "ai kun dai gama Magana, in aka raba Zaid da Labiba ai Nigeria ta mana kadan, don wallahi guduwa zasuyi".
Mami tace "in dai ba so kuke kunmata wani auren ba, Zaid ya zo yana bukatan dashin Zuciya Labee ta kaso aurenta ta je ta bashi ba to wallahi tun wuri ku aura mata shi, tunda dai ta ji tagani 'yar kutsun uwa.
A kayi daria yace "Na bawa Zaid Labiba".
Alhaji Abu yayi daria yace "na amsarwa Zaid Labiba".
Duk sukayi Hamdala.
Zaid ya saukar da kanshi yana ma Labiba Signal tare da kashe mata kannenen idonshi, ita ko bata ma kalleshi ba balle ta tankashi.
%%%


Da Yamma Aisha tazo wurinta ranta bace tace "wai ke yanzu Besty shikenan ba zaki auri danuwana ba?"
Labiba tace "danuwanki fa yace baya sona, ba zaiyi ba wai".
Harararta tayi tace "kafin yace baya so ai ke kikace ba kya so".
Labiba tayi murmushi tace "Allah zai ma Jawad zabi nagari, nidai ya min".
Aisha tace "dan Shaye shayen?".
Dif Labiba ta dauke wuta tace "kar ki sake bana so Aisha".
Bata taba ganin baci ran Labiba ba sai yau hakan ya sa Aisha wayancewa.
"Yi hakuri, yanzu Abu Sadik ai dole ya hakura da ke".
Labiba tace "bawan Allah".
Aisha tace "yanzu wai har da ke zaaa tafi Edo? Makarantar fa?".
A takaice tace "Abba ya cireni".
^^^^
Alhamis Aunty Mariya ta fita takaba, Jumaah aka daura mata Aure da Alhaji Ali Zaki.
Bayan anyi gyare gyare a Gidan ta tare tare da 'ya'yanta biyu wanda Alhaji Zaki ya bukaci ya rikesu.
Zaid da Dalo sun tafi Kano gidan Yayan Mancy Daga chan suka nufa Abuja.


B A Y A N 'yan kwanaki.
E D O
Labiba ta kira Aunty Bilkisu Matar da taimaketa a hanyar Katsina.
Bayan sun gaisa tace mata "Labiba ce".
Aunty tace "Allah Sarki Labiba, ya kike ya jikin Dan Makaho?".
Tace "Aunty baki manta ba?".
Tace "ina Zan manta beebs? Ai dan Makaho ya tsaya min a rai, tausayinshi nakeji".
Labiba tayi daria tace "Aunty wallahi jikinshi ya warke sosai, next month aurenmu".
Aunty tace "ke haba bari donAllah".
Labiba tace "wallahi kam".
Sosai Aunty Bilki ta tayasu murna ta musu fatan Alheri.
Tace "baya da raayin Civil Defense dinne?".
Labiba tace "kinga ko gaya mishi ma banyi ba".
Tace "to InshaAllah, in yana so ki bashi Email address dina yanzu zan turo miki, kice ya turo CV dinshi da address din".
Labiba tace "yanzu kuwa zan Aunty, zan sake kira, gaida min da kannena".
Aunty Bilki tace "zasuji inshaAllah".


Numbershi ta latso.
Dauka yayi full of energy yace "Yes bee to the beebs bae to be".
Daria tayi da jin iyarshegenshi.
"Wai Masoyin kana son aikin Force?".
Yace "Soldier?"
Tace "Nope Civil Defense".
Yace "Sosaiii ma, zaki samo min ne?".
Ya tambayeta cikin wasa.
Tace "eh in kana so".
Cike da zolaya yace "ina so Comptroller Labiba Ahmad Dakata".
Tace "Send your CV to the email address din da zan turo maka yanzu".
Yaji she sounds serious yace "babe are you serious ?"
Tace "stop asking too much, just send the cv, zan kiraka anjima i love you".
Kita ta kashe wayar, ko 30seconds baayi ba ta tura mishi email adress din, da mamakin Labiba ya tura Cv dinshi ma address din.


Aunty Bilki ta kirata, Labiba na dauka tace "Zaid Aliyu Zaki? Age 27".
Labiba tace "wai har ya turo?".
Aunty tace "eh wallahi, ina son masu zafin nama, inshaAllah zanyi kokari naga ya samu, inshaAllah".
Labiba tayi ta zabga godia tare da sa mata Albarka.




K A T S I N A


'Y A N B E N C I N E S K A L E Y.


Su 4 Zaid ya ma jagoranci har Parlon Baban.
Cike da Ladabi da biyyaya suka gaida Alhaji Ali Zaki tare da zama kasan Carpet.
Alhaji Ali yace "duk ku gaya min A ina karatunku ya tsaya".
Eskaley yace "ni ban taba zaman Aji ba".
Terro yace "Ni tun Primary ban cigaba ba".
Haruna yace "ni ina da Diploma".
Master yace "ni ina da Secondary School Certificate.


Alhaji Ali yace "Alhamdulilah,
ina so kuje kuyi tunani ku dawo ku gaya min burinku, wani sanaa kuke so ku fara? Zan baku jari".


Dadi ya mamayesu.
Master yace "ai Baba a nan zamu gaya ma, ba wani tunani".
Yace "ina jinku".
Yace "nidai Baba shago nike so a bude min a sa ka min lemuka da yogurt a sawo min blender da generato, a saka min freezer , zan dinga dama fura da yogurt ina saidawa, a sama ko a buga min tambarin Master Fura da Nono and juices".
Daria suka sa, Baba yace "an yi an gama".
"Kai fa Eskaley?"
Yace "Baba ni dai so nake a fadada min Kiosk ina a cika min Shago a habaka min shi, duk unguwan nan nikadai ke da shago".
Baba yace "ba kiosk ba, wannan shagon gefenka Empty naji ance ana neman me siya, zan kama maka in cika maka shago da provisions kayi ta saidawa".


Terror yace "ni dama Baba chan da na iya irin Takalma da Jakka Handmade, ina so a bani jari da shago na dinga yi".
Yace "to naji"


Kai kuma Haruna me kake so?
Haruna yace "Baba ina da diploma na, ina so na koma Makaranta na hado Degree dinnan, sai na dinga bussiness".
Baba yace "bussiness din me?".
Haruna yace "ko Shadda haka".


Yace "to naji, dukkanku zan baku naira dubu dari biyar, miliyan biyu kenan."


Ina Aljannah su sakashi, godia kawai suke kwasa, suna sanya mishi Albarka, "suna cewa sai Baba, mungode, Allah ya kare mana kai, ya sa ka fi haka, Allah ya maka Gwamnan Katsina, Allah ya kareka daga sharrin Mahassada".
Baba yace "To Amin nagode, amma fa da sharadi".
Suka natsu yace "ba cash zan baku ba, Idrisu zan sa duk ya siyo muku abubuwan da kuka lissafo da kudinku, don kar ku kashe su a banza".
Suka ce "mun yarda wallahi, mun fi so dama a siyo mana komai".
Yace "kuma duk wanda na sake naji ko na gani yana shaye shaye, to zan amshe abuna".
Haruna yace "nidai Baba na bar World na bar Sigari, dama wallahi rashin abun yi ne ya sa nake sha, amma yanzu haram".


Master yace "ni tun da naga Mankas kwance ya kusa warewa nace na bari don kar na baro ma kaina aiki uwayena basu da kudin biya a man aiki, Allah nidai na bari".


Terror yayi shiru, don ya san karya ne yace zai bar shan sigari lokaci guda, ya riga ya zame mishi jiki yace "nidai baba kar na ma karya, InshaAllah ba zaka ji ko ka gani ba, amma dai ka sani a addua, zan bari"
Baba yace "Allah ya sa, nidai na gaya muku, randa na ganku ko naji labari, zan amshe abuna ne, kaifa Eskaley ance kai ke sayar da world din yace "Wallahi Baba na bari".


Yace "kaifa Mallam Zaid?".
Zaid ya murmusa, Soyayyar Mahaifinshi na tsaga bargonshi da jinin jikinshi ya murmusa yace "Baba ni ai na bari, Labiba tace in ta kamani ina shan sigari wai zata sa a budeni a ciro mata hantarta
A maida mata cikinta wai ba zan kone mata hanta ba".
Sukayi daria ga baki daya yace "Diyata ta min daidai, to ku tashi ku tafi Allah ya muku Albarka".
Nan suka dinga shi mishi Albarka suna Gode mishi.
Cikin kwana biyu ya cika musu Alkawarin da ya daukar musu.


Kamar Shekarun Baya, haka aka dawo, ko wani Gida a Tudun Matawalle akwai kwanon Abincinsu a Gidan Alhaji Zaki, amaryarshi bata da kyashu bare hassada, duk wani mai neman taimako gidan yake zuwa, ya taimaki Danginshi, ya taimaki Na waje, kowa na yabawa da Alhaji Ali Zaki.


A B U J A


Jawad ya shigo Parlorn ya iske Mancy da Umma sai Abdulmajeed, Mimi na bacci.
"Jawad yadai?"
Yace "Mancy wai Sadyy har yanzu bata dawo ba?"
Ta kalleshi tace "Jawad Chan zata kwana".
Ya zaro Ido "don me zata kwanar musu a gida kamar basu da gida, nidai ta dawo".
Mancy tace "kamar dai wani gida taje? Gidan Abdulhafiz ne fa, matarshi take tayawa aiki ka sam tayi nauyi, ya gaji ne ba zai iya dawowa da ita ba yace sai gobe".
Jawad yace

Please Login or Register in order to submit comment