Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

auren".


"Wallahi ina da wanda zai aureni ya sakoni a yau dinnan" Er Rabi tace "dakata Hajia, ina ke ina aure yau? Ko kin manta shari'ah ne? Akwai Idda a kanki, bayan nan ma dai ina so na farko ki kwantar da hankalinki, na biyu kuma ki yarda dani ki bar min komai".


Share hawayenta tayi tace "eh na bar miki komai, na yarda dake".


Washegari Er Rabi ta fita tun kan gari ya waye, Shafa'atu ba ta tashi ta ganta ba, kasa hakuri tayi tayi wanka ta fita zuwa Gidan Alhaji Ali, kamar jiya masu gadi suka ci mata mutunci, suka hanata shiga, wuri ta samu ta rakube a inda marok'a ke zama don jiran fitowan Alhaji Ali duk safiyya, ta san ya kusa fita Office, bayan 1hr sai ga Motocinshi sun fara fitowa, da sauri ta mik'e tsaye ta nufe Motar da take da tabbaci yana ciki don ya tsaya yana sallamar marok'a, yana hangota ya ciro kudadden da be san yawansu ba ya ba wani Yaronshi yace ka raba ma kowa, ya kallo driver yace mu tafi, kafin ta karaso tuni driver yayi gaba, sauri sauri gudu gudu ta bi bayan motar, daga bisani ta tsaida kekenapep tace ya kaita Office din Speaker, tana isa kuwa ta iske karnuka irin police dogs dinnan, securities suka sake mata su bisa umurnin Ogansu, a guje ta bar gurin da kyar ta tsira ta koma Gidan Er Rabi tana haki Rai a bace.


Daidai da dawowan ErRabi, rik'ota tayi ganin tana neman kifewa "Hajia Shafa'atu meya faru? Lafiya?" Tana haki tace "Karnuka Ali ya sa aka sakar min, da kyar na tsere".


Ran Er Rabi bace tace "yanzu wurin shi kikaje Shafa'atu? Gashi ya wulakantaki a banza".


Sai da nace ki bar min komai" ita dai Shafa'atu bata bar kuka da kumbure kumbure ba.


Er Rabi tace "saurareni da kyau, daga gurin mallamina nake, na kai mishi kukanki, amma yace na kaiki, don ya kalli kwayar idanunki ya karanto miki matsalolinki, kinsan shi baa mai katsalandan, shiyasa banje dake tun wuri ba, in ba shi yace azo da mutum ba, ba a mishi jaye-jaye, aikinshi kamar yankan wuka, kuma ba kya fadin damuwarki da ya kalleki ya san damuwarki ta mecece"


Shafa'atu da ta natsu tana sauraronta tace "Er Rabi, kina da tabbacin zai magance min masalata, shi da bai santa ba ta ina zai maganceta?"


Shafa'atu tace "La Ilah, ya kike magana? Wai baki yarda dani bane?".


Hawayenta ta share mata ta kwantar mata da hankali, sai da ta ga hankalinta ya dawo gareta kafin ta fara magana,


"Banda haufi kan Mallam, sai dai in ban kai mai kuka na ba, da naje yake magance minshi"


"Yace inje dake" wuf Shafa'atu tayi tace "to wai jiran me mukeyi ne? Danallah mu tafi"


Er Rabi ta mike, suka fita gabaki daya basu tsaya ko ina ba sai tashar da zai kaisu kauyen Marmara.


Babban Gidane don Gidan kadai ne gini bulo, maigadi bai tsaya musu iso ba don Er Rabi yar Gida ce.


Mallam na zaune a wani parlorn da yaji kayan alatu, rik'e yake da wani zungureriyar chasbaha a hannayennshi biyu.


Daga wani tuntun Er Rabi ta zauna, ganin haka yasa Shafa'atu zama kusa da k'afar ErRabi. Er Rabi tace "Mallam kaga nadawo ko? Mutuniyar ce ba ta da sany shiyasa muka taho yau ba gobe ba".


Mallam da tun da suka shigo yake bin Shafa'atu da wani kallo, cikin rashin sabo da irin kallon da ya ke mata ta gaisheshi, ya amsata da faraarsa.


Ya fara magana ba tare da ya daina jan Chazbaharsaba
"A gurguje Sunanki Shafa'atu, kin auri mai girma Speaker Alh Ali Zaki tun baida komai, kin so shi tsakani da Allah, ba ki taba haihuwa ba, kin shanye bakin cikin dangin Miji, kin zauna da kishiyarki lafiya ba wai don kina sonta ba, sai don Mijinku, ta haihu, son duniya Alhaji Ali ya daura ma dan nan, kika zo kika fara kishi da dan, kika nakasa mishi ido, Alhaji Ali ya miki Saki uku, yanzu kina sonshi, kina so ki dawo gidanki, kina so wannan karon in kin dawo ki mallake komai,ki juya komai kuma kar wanda ya kalleki ya ce miki don me, ko ba haka ba?".


Da mamaki yanda ya karanto mata labarin Rayuwarta take gyada kai "hakane wallahi, ka taimakeni, da na sake aure zan kashe auren in koma ya aureni, bana so na samu matsala, bana so wani ya bani matsala wurin komawa Gidana, bana son kowa ya sake daga kai ya kalleni a wulakance".


Mallam yace "kije ki gama Idda ki dawo" ba gardama ta tashi tayi gaba Er Rabi kuwa ta tsaya suka danyi magana da Mallam kafin ta fita.


Bayan ta gama Iddah


Er Rabi ta jadadda mata kan Rashin yi ma Mallam Gardama, da kuma bin duk wani abunda yace tayi, ka nan suka koma Gidan Mallam.


"Shafa'atu aikina ba kamar na saura bane, bana aikin Ammaja, ina da kudi, bana karyar aiki, bana aikin da zai warware bayan shekaru dubu, ko mai zai faru aikina nike warwareshi da hannuna, ki gaya min, zaki iya bin sharrudda na?"


Da sauri ta gyada kai, don ita ta matsu ta koma Gidan aurenta, a yan watanni hudu, ji take kamar an rura mata wutan son Alh Ali tace "Mallam na shirya, zanyi duk abunda kace"


"Aikina ba a hadashi da na kowa, ni na fara sa hannuna cikin Alamarinki, ni na bude aikin ki, in kika koma gun wani ya miki aiki daga yanzu, aikin da na riga na sanya hannu, to zaki biya da ranki, mutuwa zakiyi".


Baki na rawa tace "Ni wallahi ban san kowa ba"


Yace "kamar yanda na gaya miki a zuwanki na wanchan karon, in har na karanceki daidai, a yanzu kina so ki koma gidanki, kina so wannan karon in kin komaki mallake komai,ki juya komai kuma kar wanda ya kalleki ya ce miki don me, ko ba haka ba?".


"Eh haka ne, haka nake so"


A takaice yace "to hakan ba zai faru a yanzu ba".


Gwalalo ido tayi hankalinta tashe yace "na duba sosai, ba wani abun kirki da na hango, ba Alheri, ko kin koma ba zaki tarar da komai ba sai bakinciki da kunci, kyara, hantara da tsangwama, ke babu ma hanyar komawarki a yanzu don ba karamar tsana dangin suka miki ba, kuma akwai kariya sosai a Jikin Alhaji Ali da Iyalenshi, so a yanzu ba zai yiwu ba, shawara, ko kiyi hakuri har sai lokacin da zan dubo daidai, ko kuma shi Alhaji Alin ki hakura da shi baki daya".


Fashewa tayi da kuka tace "Bangane ba, wallahi ba zan iya hakuri da shi ba, zan jira har sai lokacin da ka gano Alheri, ko nan da shekara 50 ne".


Dariya mallam yayi yace "be ma kai shekara50 ba, shekara sha biyar(15) ne ba yawa".


Fargaba, tsoro suka dura a kirjinta a yayinda ta hango iyakar gaskiarshi, cikin rudu take cewa "bangane shekara 15 ba, Mallam donAllah bar wasa muyi maganar da ya kamata".


Dariya yayi yace "Kina ganin kamar wasa nake, kije ki gwada auren Alhaji Ali, ai ba ma zaiyiwu bane, in kina son burin ki ya cika, ki daure ki cika shekaru 15 dinnan zaki ga ribar hakuri, har ki dafa dutse ki sha romonta".


"Mallam wai wani irin Shekaru 15? In na mutu kafin nan fa? In shi ya mutu fa? Kai in akayi K'iyama kafin shekarun su zagayo fa?"


"Ke ki bar wannan tunanin bana so ki hango komai sai nasara, ki kallo nasara har kin sameshi, a lokacin Arziki ninkin ba ninkin, kuma sai yadda kikace, kuma a duk inda kike, in dai shekarun suka cika, sai ya nemoki, ko da kina kasar sin".


Shiru tayi tana wasu tunani, ta waiga ta kalli ErRabi wacce take daga mata kai alamun amincewa, basirarta ta dode, zuciyarta ta bushe, hangen dogon buri take, take zuciyarta ta dinga hasko mata abubuwan jin dadi da ke jiranta nan da shekara Sha biyar.


"Na fahimta Mallam, shekara wata rana kwana ce, kamar gobe ne, Allah ya kaimu".


Mallam ya murmusa "to akwai wasu maganin da zan dinga rubuta miki a, ke da kanki zaki dinga wanke shi"


Ido ta gwalalo, tsoro ya rufeta.
"Kwantar da hankalinki, ni zan aureki, kinga kawai da nagana aiki a kanki, da na sakeki, kawai sai ki aure tsohon mijinki".


Da yake zuciyarta ta dakushe, ba ta da mafadi, ta amince da bukatar Mallam, Mallam ya aureta, ya cigaba da aiki a kanta a cewarshi, sakinta yayi bayan Sati 1.


Abun mamaki wai don auren da sukayi na kwanan 7. Shafaatu ta samu ciki, murna Shafaatu tayi harda kuka, gani take aikin Mallam ya fara ci, bata son Mallam ko kadan, amma inta tuna nan da shekaru sha hudu da rabi zata auri masoyinta na asali sai ta ji dadi.


Ba yanda Mallam beyi kan ta zubda cikinta ba ta ki, son cikinta take sosai, kuma ita da ba ta taba ko da bari ba akan me zata zubar da cikinta, aiko ta na son abunta".


Mallam yace "shi ko ba ruwanshi"
tace "ta yarda".


Yace "Kiyi tafiyarki, ki cigaba da rayuwarki kamar kowa, 18/10/2008 Alhaji Ali zai zo wurinki a duk inda kike,ki rubuta ki ajiye, ki fara irga kwana daga yau".


Da Murna ta bar Gidan Mallam ta koma Gidan Er Rabi, ta hade kayanta da yan kudadden da take dasu ta koma Gidansu da ke Jos.


Uwarta ta shiga tashin hankali da ta gaya mata sakinta a kayi, amma ta kwantar da hankalinta ganin hankalin diyarta a kwnace yake. Zaune suke da dadi ba dadi, lokacin haihuwarta ta yayi ta haifi diya Mace suka sa mata suna Amina suna ce ata Annah.


Bata damu ta gaya ma mallam ba don ya riga da yace ba ruwanshi da diyar, don shi mallam bai san iya adadin yaranshi ba.


Haka Shafa'atu tayi rayuwar Jos da dadi ba dadi,duk da son Ali Zaki beta bacewa ba.
Shafa'atu na da Labarin Gidan Alhaji Zaki kaf dinshi, duk abunda suke ciki Er Rabi na gaya mata.
Tare take da Mahaifiyarta, da diyarta da k'aninta Hudu da ba zai wuce tsaran Zaid ba, ko ya girmeshi ba da yawa bane.


A shekararsu ta 5 ne Mamarta ta fara wani irin ciwo, sosai rashin Lafiyarta ya kwantar da ita a babban Asibitin Jos, bincike ya nuna Hantarta ce ta kumbura, kuma tana buk'arta a mata open surgery.


Hankalin Shafa'atu ya tashi, ta rasa inda zata neman kudi, gashi ba kudin nan, damar duk buga buga ce.


Duk inda zata aron kudi sai ace babu. Ta kira Er Rabi a waya tace ta ara mata dubu dari3, Er Rabi tace "wallahi bata dashi babu" hankalinta ya tashi, ErRabin ce hope dinta, yanzu ya zatayi? Katsina zuciyarta ke kira mata, kawai taje gurin Alhaji Ali.


Ba doguwar Shawara washegari ta shirya Annah, suka bi Motar haya zuwa Garin Katsina, shi kuma Hudu zai zauna wurin Mama kafin su dawo.


Suna isa duk a gajiye, Annah ta fita hayyacinta, ga yunwa ga gajiyar Mota, direct ta nufa Offishinshi duk da Marece yayi.


Wurin Secretary dinshi ta buk'aci ganinshi, Secretary tace "ba ki da appointment, kuma 4 ya wuce, baya ganin visitors, kuma he is about to leave, ki bari sai gobe" magiya ta fara yi mata, Annah ta fara kuka.


"Meke faruwa a nan?" Muryarshi ta doki kunnuwanta, da sauri ta waiga inda yake tsaye, ya fito daga office ga wasu mutane masu bakin suit da bakin Gilashi suna gefenshi.


Idonshi ya sauka kanta, nan da nan fuskarshi ta hade, kafin ta yi magana yace a kausashe "me kikeyi a nan? Bana ce kar ki kara fitowa gaban idona ba? Bance miki bana son sake ganinki ba? Bance miki na tsani ko da kalonki ba? At this instant, bace min daga gani kafin na sa a Wulak'antaki".


Dama tuni take zube gabanshi, kuka take tana girgiza kai "Alhajina, ka taimakeni, Mama na chan kwance bata da lafia"


Bai saurareta ba yayi umurni da a fitar da ita.


A wulakance a ka fitar da ita, tana kuka ta karasa Gidan Er Rabi, ErRabi ta basu Abinci, ta tausheta da cewa nan da shekara 10 zata dawo Gidanshi sai ta fanshi bakincikin da ya kunsamata na shekaru, a haka ta dinga lallabata.


"DonAllah muje ki rakani wurin Mallam, kila zai taimaka min, ga Annah ma, be ma san ya take ba, kuma diyarshi ce"


Er Rabi tayi saurin katseta, "aa Shafa'atu ba haka kukayi ba, sai da yace zai baki magani ki zubar da cikin Annah kikace aa, kikace ya bar miki cikinki, harda kuka, yace kar ki taba zuwa gabanshi da diyrki, kar ki taba ambatonshi a matsayin uban diyarki, kikace kin amince, yanzu kuma kice muje gurinshi? Karki manta yace ya gama aikinshi kanki rana kawai zaki jira, yace duk randa kika zo mishi da maganar diyarki zai kwance komai da ya kulla kinga kinyi jiran banza, Shekara 5 ta tafi a banza, komai ya tashi a banza, ke dai kiyi hakuri yanzu, gobe ki koma Jos a fara ma Mama maganin hausa zaa dace".


Kuka Shafa'atu kawai take, Washegari da Asuba tayi Sakkon komawa garin Jos ranta 6ace, ta na dawowa da kwana daya Mamarta tace ga Garinku nan, ta girgiza da mutuwar Mahaifiyarta ta sha kuka son ranta tana tausayin kanta da na kaninta Hudu, basu da kowa, basu da komai.


Rayuwa ya mata zafi, dole ta rayu kafin Burinta ya cika, dole ta zama karfin Annah da Hudu, dole duk su rayu, mikewa tayi tsaye ta fara Abincin Saidawa kamar yanda sukeyi a da, kasancewar ta iya Girki, kuma akwai Tsafta ya sa take samun Customers. Kuddirinta na nan, ranta chunkushe, Ganinta Ali zaki ne yayi sanadiyar mutuwar Mahaifiyarta, da ya taimaka mata, da amma Uwar ta aiki da ta warke, Ta k'agara Shekaru 10 su cika ta fanshe Bakincikinta.


Bayan Shekara Goma
18/10/2008


Yau take Sallah a gurin Hajiya Shafa'atu, kwalliya ta ci ta sa tsaddaden leshin da Allah kadai ya san inda aka samu kudin dinkawa, harta lalle sai da aka K'unsa mata, yanda ka san Sabuwar Amarya.


Da karfe 1 na rana Annah ta shigo dakinsu, tace "wai ni Mummy ina Baban nawa? Har yanzu bai iso ba?"
Shafa'atu ta fara girgiza kafarta, ita fa a ganinta ko garin yau be idasa wayewa ba zata ga Alinta, gashi har an fara kiraye kirayen Sallah.


Ba ta so ta sa shakku a Aikin Mallam, Shekaru 15 tayi tana jiran Ranar nan, ga ranar tazo, gashi ranan ya mata kama da sauran ranakun da suka shude, ba wani abu special game da ranar yau, ko dai tayi wauta da sakaci da ta yarda da maganganun Mallam? Ko Annah bata amsa ba ta ciro wayarta ta latso Er Rabi, Er Rabi na dauka ta fashe da kuka.


Yau waya kala kusan 10 sukayi, Er Rabi tace "Yaya ne? Ya iso ne?"
Shafaatu ta fashe da kuka tace "wani isowa? Har yanzu shiru, sai da nace miki zanzo Katsina kila gidan ya mai wahalar ganewa, er Rabi ya zanyi? Ko dai mallam ya wanke mu ne?"


Er Rabi tace "ke dai baki da hakuri, ki bari ranar yau ta kare mana kafin kiyi korafi, kinsake hakuri, kar ki sake kirana sai yazo" dif Er Rabi ta kashe waya, ran Shafaatu a bace.


ABUJA


Zuciyarshi ke mishi Zafi tun bayan Sallahr Asuba, Ji yake kamar a na yankar Naman jikinshi. Meeting sukayi , amma be fahimci komai ba.
Meke damunshi? Ya tambayi Zuciyarshi.
"SHAFA'ATU"
A takaice zuciyar ta amsa mai.


Yana son ganinta, ta na ina? Tayi aure? Akwai auren wani a kanta? Ta mutu? Da sauri ya girgiza kanshi da ke barazanar tarwatsewa, tunanin Mutuwarta na neman dauke mishi numfashi, in ta mutu sai ya bita, in kuma tana da aure ko zaiyi yawo tsirara sai ya raba auren nan ya dawo kanshi, zai biya Mijin da duk wani k'addara tashi.


"Ina zan fara nemanta?" Ya tambayi zuciyarshi.
JOS ta amsa mai, kamar ana karanto mishi abunda zaiyi haka yake ji, kurum ya kira PA dinshi yace a siya mishi ticket din Jirgi zuwa Jos, haka ko a kayi, a gurguje suka isa Airport, suka nufa Jos bayan Mintuna da basu kai 50 ba suka isa Jos.


Akwai Convoy din da suka zo tarbenshi, be manta Unguwarsu ba, ya gaya ma driver cikin 30mins suka iso Unguwarsu Shafa'atu.


Kamar ana ingizashi ya fada Gidan, ko Sallama babu, abunka da me jira, ta na zaune tsakar Gida, tana ganinshi ta mik'e tsaye, murna ya sa ta fashewa da kuka, da niyarta in yazo ta dan gasa mai gyada a hannu ta ja aji, amma ganin yanda ya shigo, ta manta da duk wani bacim rai da ya taba kunsa mata a rayuwa, Son shi ya goge mata komai, daga inda yake ya choge tsaye, hankalinshi ya dan tashi ganin ta na zubda hawaye kai ya girgiza mata tare da ware hanayenshi Biyu, da gudu ta fada jikinshi ya rungumeta gam yana samun wani irin natsuwa.


Murya a dishe yace "Shafata, ina kikaje kika barni cikin kewanki, Shafata me na miki kika barni?" Kiyi hakuri kizo mu cigaba da Zamanmu, Ina sonki, kece wacce na fara so a rayuwata" ganin yanda yake sake rungumeta ya sata cewa "Yarinya na kallonmu,Alhajina ai Sakina kayi, Saki Uku ma" da sauri ya tureta yace "Inji Ubanwa yace Sakin ki nayi? Nifa ban sakeki ba, ta ya zan rabu da rayuwata? Baki da labarin kece Rayuwata".


Dan tabe baki tayi tace "Ya kayi da Shekaru 15 da suka wuce?" Yana son yin dogon tunani amma ya kasa cewa yayi "Ni bansani ba, kar ma ki tambayeni, abunda na sani shine, san karashe rayuwata dake, ba zan taba bari kiyi man Nisa ba".


Wani Farinciki ya ziyarceta, dadi kamar tayi tsalle, "Shafata, Katsina zan tafi dake, ba zan iya kwana ba da ke ba, yau dare yayi, gobe zamu dau hanyar KT kinji?"


"To wa ya ce maka zan bika? Ina da Auren wani a kaina" ganin yana neman haukacewa tayi saurin cewa "Wallahi wasa nake maka hahaha" kamar yayi kuka yace "kina son wahalar dani ne? Ki zo mu tafi Masaukina" Cike da shagwaba tace "Auren fa? Ba zaa maida ba?"


Yace "Yanzu kuwa zaa maida, Da anyi sallahn maghrib sai a daura" Dadi kasheta, nan ta mishi introducing Annah a matsayin diyarta da Babanta ya mutu, Hudu kuma kaninta.


Yace "duk baki da damuwa, Annah Diyata ce, Hudu kuma kanena, dukkansu na dauki nauyinsu na tsaya musu, tare zamu tafi dasu".


Godia tayi mai sosai, bayan Sallahn Maghrib aka daura Aurensu sadaki dubu dari 5, a ranar duk basuyi kwanan Gidansu ba, sai a kayattacen Hotel dake Jos.


Washegari da Sassafe suka hau Jirgi suka nufi Kano, daga Kano suka hau Mota zuwa Katsina.
Suna isa KT ya bada Umurni a kai Annah da Hudu Shopping Mall suyi siyayyan Kaya.
Shikuma suka nufi Gida tare da Amaryarshi.


^^^^^^^


Kiraye kirayen Sallahr Azahar akeyi, ashe ta dade a wurin Dan Makaho, ita ina ta lura lokaci ya ja? Wuri ta samu ta buga tagumi, tana ta nazarin Labarin danMakaho, wayarta tayi k'ara Jay ta gani a gaban screen.


Numfashi ta ja ta saki ta dauka wayar da Sallama "Labeenah, ina kika shigane? Nayi missing dinki sosai" In Ina ta fara "Eh wallahi lecture mukeyi, nima nayi missing dinka"


"Yaushe zaki ban lokaci na zo Katsina?" Murmushi tayi tace "duk lokacin da kazo, ina maraba da kai"


Hangoshi tayi daga inda take, ya dawo dauke da wani abu a hannu, mancewa tayi da Wayar da take ta mike zuruf ta kuka tsallaka fasasssun Blocks din ta bishi daki har ta kusa bashi tsoro.


"Ke wai meyasa baki da hankali ne? Ta ya zaki ta shigo min daki ne? Wato ba kiji warning din da na miki ba ko?"


Baki ta tabe ta kalli ledar hannunshi, Bread ne sai Sardines, tace "ni karashen labarina nazo ji"


"To ba zaa bada ba"


Wuri ta samu ta zauna harda daura kafa daya kan daya tace "gama ci dai".


Tsaki yayi, gardama da ita aikin banza ne ya bude Kifin gwangwaninshi, ya na dangwala mai din da bread yana ci, be kulata ba, ita kuma latsar wayarta kawai take.


Daga waje kuwa Blocks aka kawo da Cement da Yashi zaa fara aiki.


"Kina ji ba?" Da ya gama kenan, da sauri ta ajiye wayar tace "eh ina jinka.


"Jikin Mancy Rawa kawai yake, rik'ota nayi na mata garkuwa da kafada na" ban bi ta kan Dalo da ke kuka ba, Mancy ta zare jikinta daga gareni tayi hanyar cikin gida duk sai muka bita.


A parlo muka tsaya inda muka ga Baba da Anty Shafa'atu suna magana, ce mishi take ita ba zata iya zama a dakunan nan ba, bata san surkullen da ke ciki ba, kafin ya bata amsa ya hngo mu, Baba na ganinmu kamar an aiko mai da mutuwa, dif annurin fuskarshi ya dauke, ya ja hannunta ya fita, muma muka bishi riiiiiii,


Mancy ta dan Matsa kusa dashi tace "ka riga da ka furta, ba aure tsakaninmu, aure ya k'are, ina so na san me na maka da na chanchaci Saki Uku gaban Yarana?" Kamar jira yake ya hau kan Mancy da duka, hankalina ya tashi na shiga tsakaninsu, na janye Mancy ina ma Baba Kallon Mamaki.


"Ki fitar min A Gida Maryama, ki kwashi yaranki ki bar min Gida bana son ganinku ku duka, na tsaneku"


Mancy ta share hawayenta, nikuma ina tsaye kamar gunki, Dalo kuwa na zaune dirshen a k'asa.


Mancy ta matsa kusa da Dalo ta tallafota gabaki daya.


Yanayin da ban taba ganin Mancy a ciki ba, ta bude murya tace "Zaid, Sadiya, zamana ya k'are a gidan nan, rabonku ne dama ya kawoni gidan nan, ku sani Nan Gidan Ubanku ne, ba ku da inda ya fi nan, ko ma mai zai faru, i mean no matter what will happen, this is Your Father's house, kar ku taba mantawa, kar ku manta da kalar Soyayyar da ke tsakaninku, kar ku bari kowa ya shiga tsakaninku"


Hannayenta ta daga Sama "Ya Allah, ga Bayinka nan, Allah ga Zaid, Allah ga Sadiya, Allah kaine gatansu,Allah ka sakama duk wanda aka zalunta"


Shafa'atu ta fashe da Ihu "Ni Alhaji sai dai ka Sakeni, Matarka so take ta kafurtani".


Aiko ya yunkuro zai bige Mancy nayi saurin tareshi ina girgiza kai don ban ma da k'arfin magana.


Ki tafi da yaranki" Baba ya sake jaddada mata, tace "ba inda zani dasu, nan ne gidansu, gidan ubansu, Ba inda zani dasu, kamar Zaid? Yana Masters? Ina zani dashi? Dalo da ba nono take sha ba ina zani da ita? Ai suna gidan ubansu, su ba Mata bane balle a sake su, 'Ya'yane su".


Nan suka fara hayaniya, da karfi, ban taba sanin Mancy ta iya fada, don ko an kure hakurinta ne.


Kinsan mai hakuri in an taboshi.
Shafa'atu tace "kinga Maryama rufin Asirinki ki tafi dasu, kika san me zan musu in suka zauna? Ba kya tsorona ne? Ki tafi dasu, wannan Gidan daga ni sai yaran da zan haifa ma Alhajina Magada Babansu".


"Huh tsoro? Bana Shafa'atu, bana tsoron makircinki, ko da ba tsoronki nake ba, kawai na fi so a zauna lafia, kuma yarane gasu nan, ki sa kansu gabas ki yanke, suna Gidan Ubansu, haihuwa kuma Allah ya kawo miki 100, duk dai yaran da zaki haifa ba zaki taba haihuwan Yayan Zaid ba, koma Sadiya, dole sai Kannensu zaki haifa".


Sosai kalaman Maryama suka bata haushi, me zata mata ta bak'anta mata rai? Alhaji wai tsayawa zakayi tana gaya min magana? Wallahi sai dai ka sakeni".


Yana jin haka ya rufe Mancy da duka a karo na biyu, na shiga tsakani ya hada dani, Dalo ma ta shiga tsakani aka hada da ita, ya dinga dukanmu ko ta ina yana halbemu, mu ko muna rungume da junanmu, Dalo sai kuka mai sauti take.
:::::


Zaune yake da 'yar Matarshi, da jaririnsu, wani abu yake ji daga Makwaftanshi kamar hayaniya, kasa kunne yayi sosai,
Gabanshi ya yanke ya fadi, Gidan da ya sani a matsayin Gida da suka kansu a kan Soyayya, Aminci da juna, abunda be taba ji ba, hayaniya, ya ji kamar ana maganar Saki, ya ji kamar maganar Barin Gida ake, wacece Matar nan da ta shigo tsakanin Gidan nan da basu son komai ba sai SO?.


Matarshi ya kalla yace "Aseena, akwai matsala". A tsorace tace "Wai Sakin Mancy aka yi? Inallilahi" kafin ya bata amsa sukaji kamar kuka, da suka kasa kunnensu sai sukaji ashe dukansu yakeyi, da sauri suka tashi a sittin sukayi Gidan Alh Ali Zaki.


Kamar an tara Mutane don wurin

Please Login or Register in order to submit comment