Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tace "Wai yanzu Aunty Shafa ce zata dinga juya ki, ba zaki bar Bokanci ba? Mummy har kin kai matakin Kisa? Waiyoni
Mummy i am driving and its raining heavily, kin ki daukan waya, in har dagaske ne kina so na, in har dagaske kina sona fiye da komai, in har komai don ni kikeyi, zaki tayani Son abunda nike so, zaki tayani kare abunda nake so, zaki tayani Son Zaid, in har dagaske kike Mummy, zaki min Alfarmar nan".


Ta karanta wannan last message din yafi so 20,
tana kuka sosai tana "Yasmin ki yafe min, na kasance banzan uwa, sakarya da bata san meke mata ciwo ba, lallai Shaidan ya kada min kidi na kuma tika rawa sosai, na tsani kaina, na raina kaina, tir da ni wallahi, duk karfina da ikona, na kasa baki abu daya da kike so a rayuwa. Zaid kadai na kasa baki a rayuwa, yanzu ina mai matukar nadama da na kasa baki Zaid.


Baban Labiba yace "Kayya Er Rabi, kaiconki, tir da ke kam
K'arfi? Iko? Wani karfi kike dashi da iko? Bokanci? Shirka? Wayace miki rayuwa a hannun ki take? Da har zaki zabi wanda zaki raya da wanda zaki kashe, gashi garin neman ran dan wani kin nema naki, Kin kashe diyarki da kanki, wallahi ke kika kasheta".
Tsinuwar Allah su tabbata a gareki hatsabibiyar Mace, wurin gaisuwa da yawa cewa sukeyi ashe Yasmin na da Uba, kin maidani wani hoto mara amfani, banda ikon amsa sunan Uban Yasmin, don ma Yasmin na So na, mutuwarta ce silar kubutata daga duk wani kaidinki, nayi imani duk wani asirin da kika min ya rushe, saboda daga ran da Yasminta koma ga mahallincinta naji na tsaneki, na bar tsoronki, na kuma bar shakkanki.
Kuma na san mutuwa hutu ce ga Yasmin, bata da yanda zatayi nayi imani da sai ta chanza Uwa, ke annoba ce, yanzu sai ta huta lafia.


Allah ya Isa Er Rabi, Allah ya isa da kika rabani da kowa, da dangina da asalina kika maidani kamar bawanki, Allah ya isana da kika dauki shekaru kina maidani Mace sai yanda kikayi dani Allah ya isa tsakanina da ke, duk da kin gama dani, na sakeki saki Uku, abu na karshe da zan ce miki, in kinga dama kar ki fasa, ki cigaba da neman ran abunda diyarki har ta mutu tana So".


Ya tsallaketa ya fita daga dakin Yasmin ya barta zaune kamar an dasata, ta kasa motsi, banda hawaye babu abunda ke sintiri a idaniyarta, yau itace duniya ta juya ma baya?".
*****


LABIBA FA?




Tunda ta shiga Motar Suleja ta ke kuka sosai, abu 3 take ma kuka.
Na farko Mutuwar Yasmin, in ta tuna ta Mutu sai ta ji ranta ya sosu wanda tunatan na zuwa mata da hawayen ido.
Na biyu kuwa rashin sanin halin da Masoyi yake ciki, ta kira ta kira wayar a Kashe.
Na Uku kuma fitowan da tayi ba tare da sanin Iyayenta ba, fitowar da tayi ita kadai, babu wani muharammi, tafiyan awa 12 tayi jiya, gashi ta dasa.


Awa 5 zuwa 6 ya kawo su Suleja don ita ta da fito tun asuba sai 12 suka isa, ta fara galabaita tun kafin su shigo Suleja. Tunda suka shiga ta nemi Abinci a Tasha ta ci kafin taji cikinta ya dan dauka.
Bayan awa daya suka tashi don tafia Katsina.


Da gangan ta kashe wayarta, don ta san ba zaa dade ba za a san bata gida, tafia suke ta ci sosai, idanunta duk sunyi luhuluhu saboda kukan da ta keci.
Tafian wani Awa 6 zuwa 7 ne daga Suleja zuwa Katsina, in ta tuna tsawon awannin da ya rage da zai kaita Katsina sai ta ji jikinta duk yayi sanyi.
Suna ta cin tafiya, ba sa tsayawa komai sai Sallah.
Karfe 3 suka tsaya don hada Sallah Azahar da Laasar.
Wata tafiyar awa 4 ce kuma, sa kai yafi bauta ciwo, haka suka sake daukan Hanya suna ta tafia, suna ta sharara gudu, Labiba ta cigaba da zikirinta.


Tsautsayi ya samu Motar, tayar su ta fashe gab da Maghrib a daidai Wajajen Gidan Mutum daya, an dauka minti kusan 40 ana gyara, karshe akace Motar ba zai gyaru ba, sai dai su kwana, matsalar Motar haya kenan, ya zata kwana a nan? Zaid fa? Wani hali yake ciki? Ya zata kwana cikin Maza? Matansu ba su wuce 3 ba, bata damu da tafiya ita kadai wani abu ya sameta ba, ta fara tafiyarta, ganin Signboard wanda ya nuna arrow din zuwa Charanci sai taji kamar dama ta iso Gida.


Tafiya kawai take, bata san adadin tafiyar da tayi ba, ita dai ta san ta dade tana tafiya har kafarta ya fara ciwo, amma bata tsaya ba, saboda ta bar inda mutane suke, ta shigo daji, ita ko tsoro bama ta ji, ba ruwanta, batayi nadama ba, ita dai ta ganta a Katsina gaban Masoyi.


Jefi jefi ta kan sa hannu don tsaida Mota don samun Lift, amma babu wanda ya tsaya da Motarshi, tsoro ya fara mamayeta a lokacin da duhu ya soma yi, kiran Sallahr Magrib taji, da sauri ta kara sauri don isa ga Masallacin.
Tun bata hango Masallacin har ya kai ga tana hangowa.


Ta ci uwar tafiya tana isa Masallacin Matan ta zube a k'asa, tana mayar da numfashi.
Wata mata na Sallah,yaranta biyu na zaune, daya ta idar da Sallah daya yarinya ce tana shan ruwa mai sanyi.
Labiba tace "ki tsanmin ruwanki in sha donAllah".


Yarinyar ta mak'e kafada alamun "aa".
Yayarta ta ma Labiba murmushi tare da ce ma kanwarta "Give her the water".
Yarinyar tace "No".
Labiba ta dan kwantar da kai tana ajiyar zuciya lokaci lokaci tace "Sweetheart, i am really thirsty, can you give me please?".
Yarinyan tace "Noo, its mine".


Labiba da dan karfi tace "Arrggh" tare da kwantawa rigingine tana kallon ceiling tana maida numfashi.
Daidai da Sallame Sallar Mamarsu ta kalli Labiba dake maida numfashi sosai.
Zahra duba Mota kiga sun idar da Sallah? Akwai Ruwan Sanyi ki dauko mata".
Yar budurwar ta tashi ta nufi Motarsu da ke waje ta dauko ma Labiba ruwan sanyi.
Tunda Labiba ta kafa kai a robar Faro, sai da ta shaye shi tas, ta aje tana mayar da numfashi, ta dade a wannan halin, kafin ta daidaita numfashinta.


Matar kam Kallon Labiba kawai takeyi.
Labiba tace "Ina wuni?".
Hajiar tace "Lafia lau Yanmata".
Labee tace "Wallahi tafia naci a k'asa, shine fa duk na gaji".
Hajiar tabi Labibs da ido, tana karantar ta, to ko dai 'yar kauyen ce? tace "Okay, ke 'yar nan ce?".
Labiba ta gyada kai tace "aa wallahi, Daga Edo nake motar mu ta lallace wai sai dai a kwana a hanya, nikuma Wallahi ba zan kwana da Maza cikin Mota ba, mu ka san abunda zasu mana in dare ya tsala? Allah ya tsareni daga masu warin baki sai masu warin hammata, nan kaina duk ya gama sarawa, ya fiye min na kwanta a Masallacin nan da safe in nemi Lift".
Hajiar ta kalleta tace "Ina zakije ne? Kaduna?".
Tace "Aa, Katsina".
Shiru tayi tana kallon Labiban dake danna k'irjinta, bata san wacece ba amma ita da ta barta a nan ta kwana gwara ta tafi da ita".


Matar tace "Katsina Zamu yanzu".
Labiba tace "lah ashe chan kuka nufa, sallah kuka tsaya kenan".
Matar tace "Eh daga Abuja nike nima, ni da Iyalina zamuje Bikin diyar Wa na"
Labiba tace "Allah sarki".
Hajiar tace "muna iya tafiya dake".
Farinciki ya mamaye Labiba tace "Allah Hajia? Ba zan takura ba?".
Tace "haba ba wani takura, kiyi Sallahr ke dai".


Da sauri Labiba ta fita ta doro Alwala tazo ta hada Sallahr Magrhib da Isha'i.


Motar High Lander ce.
Yaranta suka shige chan baya, ita kuma da Labiba suka shiga mai bi mishi.
Driver da Yaron Hajia suka zauna gaba.
Yar budurwar ta zunguri Labiba da Ledar takeaway tace "ga snacks".
Labiba ta murmusa ta amsa tare da amayo godia.


Dadi kasheta, yunwa takeji, rabonta da Abinci tun a Tasha.
Ham ham take cin Meatpie dinnan kamar mayunwaciya.
Sai da cinye da donut ta sha Cway Juice taji tayi k'at.


Sun danyi tafiya na minti 10, Hajiar duk na nazarinta, tace "Sunana Hajia Bilkisu, kinga wannan yara na ne, na gaya miki biki zamuje Katsina, tsakaninki da Allah mai ya kawo ki Katsina tun daga Edo ke kadai, guduwa kikayi ko?".


Labiba tace "aa wallahi,zan koma".
Hajiya Bilki tace "kinga, zakiyi saar babbar yarinyata, kuma ki gaya min gaskia, bana son karya, zan taimakeki in kika gaya min gaski, in kika min k'arya in sa driver ya saukeki a nan Dajin Allah".
Window Labiba ta kalla taga bata ga Gida ko daya ba sai Bishiyoyi tace "Wallahi Aunty nidai ba duniya na shiga ba, Katsina nake karatu, Wannan ne baya Lafia kuma wayarshi bata shiga,hankalina ya kasa kwantawa shiyasa nazo ganinshi".


Hajiya tace "Saurayinki?".
Labiba ta sadda kai ta dan murmusa.
Hajiyar tace "tsakaninki da Allah iyayenki sun san kin taho?".
Cike da rashin gaskia tace "Aa".
Matar tace "guduwa din dai kikayi, kika taho dubiyan saurayi, anya kuwa ba karya kike min ba lafiyarshi lau ba? Soyyaya zai sa ki zo wurinshi ku gudu ko?".


Da sauri Labiba tace "aa wallahi, wallahi ni ba mutuniyar banza bace, wallahi dan shaye shaye ne, sai mu fi hours a dakinshi amma ko hannuba bai taba tabawa ba".


Labiba kam ta gama kashe matar a zaune, baki a bude take bin ta da ido.
"Dan Shaye Shaye? Kike so? Har kike zuwa dakinshi?". Ta kalli diyarta dake back seat tace "yo in diyata ce ai da na yankaki naji kina shiga dakin namiji, meyasa kike kai kanki wurin namiji? Wallahi wasu matan su ke kashe kansu".


Da sauri ta girgiza kai tace "Aunty donAllah kar ki man Mummunar fassara da fahimta, tsaya kiji".
Tiryan tiryan ta kwashe duk wani labari da ta sani game da Zaid ta ba Aunty Bilki.
Da mai saurin kuka ce da tayi amma irin dakakkun matan nan ne, diyarta dai tana ta hawaye.


"Allah ka mana tsari da kishiyoyi irin Hajia Shafaatu, Allah ka mana tsari da mummunar kishi, Allah ka mana tsari da yi ma 'ya'ya mugun Alkaba'i, tabbas naga mutuwar Dr Yasmin a Social Media sosai kuwa, kila mutuwarta ce ya taba lafiyarshi.


Labarin Zaid abun taussyi ne amma Labiba what you did is very wrong, kowa ya ganki yanzu he will give you a bad impression na kin baro gida zakije Katsina gun Namiji, ba wanda ya ga niyyarki, kowa zai daukeki a matsayin mutuniyar banza, ba ma haka ba, yanda kika fito ba da sanin kowa ba, wani abu ya sameki a hanya Allah shi kyauta wa gari ya waya? Me zakice? Laifin waye? Duk laifinki ne".


Sosai ta ma ta fada da nasiha, ta kuma bata baki akan tausar zucia, don a dan labarin da taji ta lura she's an extrovert, tana fadan abunda take so a lokacin da take so babu dam sakayawa, saboda gatsau tace mata "Aunty ina sonshi don ni na fara furta mishi So".
Sosai Aunty Bilki ta yi ma Labiba fada har ta sha kuka.


Aunty tace "to wallahi da kinga lafiyarshi wallahi ki kama hanyar Edo gobe ki koma Gida, ki rok'i gafarar Iyayenki, ga dubu 10, ki mayar ma Maminki kudin da kika sata, sauran kiyi kudin Mota".


Labiba ta murmusa tace "inshaAllahu Aunty, na daukar miki Alkawari, nagode sosai".
Suka iso Katsina Lafia, har tudun matawalle suka kaita, har gaban gidan Alhaji Ali Zaki.


Labiba ta bude Mota.
Tace "Ba zaki shigo ku gaisa da Matar Yayana ba?"
Aunty Bilki ta girgiza kai tace "aa Labiba munyi dare".
To nagode kwarai, Allah ya saka miki da Alheri ya tsareki ya tsare miki 'ya'yanki, yanda kika taimakeni Allah ya taimakeki, inshaAllah yaranki zasu zama abun Alfahari a dunia baki daya".
Ta amsa da "Amin Amin nagode da adduoinki, naji dadinsu Allah ya amsa"
Labiba tayi sallama da yaran Hajia, har ta juya zaya tafi gida Hajia ta dakatar da ita.


Labiba ta dan Matso bakin window, Hajia tayi rubutu a wani takarda ta ba Labiba tace "Ina So na samo ma DanMakaho aiki, ina da hanyar Civil Defense, in yana da raayi ki bashi email address dina gashi nan ya tura min CV dinshi ko da secondary certificate ya samu ai yafi mishi zaman banzan nan, ga number nan kuma ki kirani inji ko kin koma Edon".


Hajia bata tsaya jin Godiar Labiba ba tayi whinning glass shi kuma Driver ya ja mota aka bar Labiba tsaye da mamakin Hajia Bilki.
Haka Allah ke abunshi, haka Allah ke sa jinin mutane haduwa ba tare da jini mai gudana ba.
Ita ta san haduwarta da Hajia Bilkisu Alkhairi ne.
"Hajia Bilkisu Beebbs nagodia, Allah ya baki farinciki a duk inda kike" mai makon ta shiga Gidansu kawai ta fada gidansu Zaid.
Yau ta Gate Beebs aka shiga Gidansu Zaid.


Ba ta tsaya ko ina ba sai dakin Zaid,
Wayam bashi ba alaminshi, wayarshi ta gani a k’asa da sauro ta dauka, tana kunnata ba charge, ta tura toilet taga baya ciki, yana ina? Ko yaje Bencin Eskaley, da sauri ta fita waje ta nufa Bencin Eskaley.


Suna ganinta suka mimmike, “Yayarmu ina wuni”
Bata amsa ba tace “donAllah ina Zaid?”
Sukace “Yo ai duk yau bamu ga Mankas ba”.
“Baku ganshi ba?”
Be fito ba gaskia, bamu ganshi ba, jiya dai mun ganshi har muka mishi Taaziyar Yasmin”.
Bata tsaya gama jin zancen ba ta koma Gidansu Mankas din.


Ba tsoro ta shiga Parlorn suna zaune.
Alhaji Ali tace “Ina wuni?”.
Zai yi magana Hajia Shafa tace “wacece ke?”.
Tace “sunana Labiba, ina neman Zaid ne”.
Shafaatu kamar an watsa mata garwashi tace “ba zaa bashi Hantar ba, ya mutu dole ne?ina ruwanmu”.
Labiba bata gane inda ya dosa ba tace “Mene? Ni Zaid na zo nema”.
Annah tace “Dallah Mallama ki fitar mana daga Gida”
Labiba ta kallesu tace “Ni fa ba wai zuwa nayi ku daga min jijiyoyin wuya ba, tambaya ce na muku, in baku san inda yake ba, ku gaya min, sai na je wani gu na tambayeshi”.
Annah tace “Karuwa har Gida kike biyoshi?”.
Sosai Labiba taji zafin zancen cikin fushi tace “Uwarki ce karuwa”.
Shafa’atu tace “kam bala’i uwarta ni kenan?”.
Labiba ta rausayar da kanta ta kalli Baban Zaid, sai taji ya bata tausayi”.
Fita kawai tayi a Parlon ta bar gidan, har zata shiga Gidan Yaya Muhammadu ta fasa ta dawo Gidan Alhaji Ali tace da Maigadi “DonAllah ko ka ga Fitar DanMakaho?”.
Maigadi yace “Eh, bai da lafia sosai wallahi dazun ni na kama ma wani abokinshi muka sashi Mota Abokin ya tafi da shi General.


Da gudu Labiba ta fita, bata shiga Gidansu ba tayi hanyar bakin Titi hankalinta a tashe.
Yan Bencin Eskaley nata mata magana tayi banza dasu.
Keke Napep ta tsaida tace a kaita General Hospital.
Ta na isa ta nufa Accident and Emergency, ta bada sunanshi gun reception akace anyi moving dinshi an bashi gado Amenity room 7.
Bata san ina ne Amenity ba amma bata ma tsaya tambaya ba.
Da taimakon Signboards ta gano Amenity, ta shiga ta fara neman dakuna.
Tana ganin room 7 ta karasa a guje ta bude da karfi.
Chan kan Gado ta hangoshi kwance kamar tabarma, da sauri ta karasa gunshi kamar zata daukoshi daga kan Gadon.


A hankali Zaid ya bude idonshi ya saukesu fes kan Labiba a wahalace da sauri yayi yunk’urin tashi, tayi saurin maida shi ta sakar mai murmushi mai ciwo, kauda kai yayi bai so ta ganshi cikin ciwo, bai so ta san weakeness dinshi.


Sannu ta shiga jera mishi, bya juyo ya kalleta yana niyyan magana bata ji meya ce ba, ta sa kunneta a daidai bakinshi yace “Yasmin ta tafi Beebs”.
Tace “Yasmin ta tafi Allah ya gafarta mata, lets focus on you now, you are sick”.
Yace “I am dying”.
Tace “shuttup gashi ana kara maka ruwa da jini inshaAllah kafin su kare ka warke”.
Murmushi kawai ya mata.
Socket ta nufa tace “Wayarka ba charge, daga gidanku fa nake”.
Da charger dinta ta jona mishi charge.
Ta dawo ta zauna a kan kujeran da ke gabanshi.
Tace “Sannu”
Yace “ya kamata ace kina Edo”.
Tace “Masoyin baida lafia”.
A hankali yace “Ta yaya kika zo?”.
Tace “in ka warke zan baka labari”.
A hankali aka bude Kofar.
Labiba ta juya ga k’ofar Drs ne su biyu suka shigo
Ta mike da fara’arta.
Tace “Sannunku”.
Dr Ali yace “Zaid bak’uwa akayi?”.
Zaid ya kanne idonshi yana so ya ma Dr Ali inkiya da kar ya gaya ma Labiba.
Labiba tace “Yauwa Dr, ya mai jiki? Stress ne ko?”.
Dr Habib yace “dama Stress ne da sauk’i, he is very sick wallahi”.
Tace “toufa, what exactly is wrong with him?”.
Dr Habib yace “Liver is damaged, he needs a transplant”.
A firgice tace “He Needs a Whatttt?”.
Zaid yui saurin runste Ido.


Da sauri ta kalli Zaid kafin ta kalli Dr Ali kafin ta kalli Dr Habib.
“Bangane ba Dr”.
A gajiye, a galabaice Zaid yace “Beebs”.
Ta san da kyar muryar ta budu, amma ta ki kallonshi tace “Dr kamin bayani?”.
Dr Habib yace “Are you a Family”.
A kagaucd tace “Ni zai aura, mun kusa aure, and i think i deserve to know what is wrong with my Fiance”.
Dr Habib yace “follow me”.
Bata jira komai ba ta bi bayanshi.
Zaid yace “Ali, donAllah ka hanashi magana”.
Ali yace “Budurwarka ce?”.
Zaid yace “it doesnt matter ka taimakeni kar ta san komai, tell her malaria ce kawai”.
Dr Ali ya fita ya bi bayansu, ko da ya shiga Labiba na zaune tana sauraron Maganganun da ke fita daga bakin Dr Habib.


Hawaye tuni sun wanke mata fuska, Zaid na dauke da ciwukka all this while bata taba sani ba? An fi shekara da akayi diagnosing dinshi amma ko da wasa bata taba sani ba? Ya Illahi, zuciyarta ta dafe dake barazanar fitowa.


Cikin Kuka tace “To a mishi surgery din mana me ake jira? Da bakinka kace Emergency ne”.
Dr Ali yace “Wallahi ba mai donating, naje Gidansu na gaya ma Babanshi baki ga wulakancin da suka min ba da gatari suka bini, Mamarshi kuma bata nan, nace zanyi contacting dinta yace baida contact din Mamanshi tunda suka rabu, nace kanwarshi yace “ta tafi Ghana wurin kakansu, nace dangin Babanshi ya ki magana tun dazun”.
Labiba tace “K’arya, yanzu what will happen in be samu Surgery din ba?”.
Dr Habib ya dauko Xray ya na nuna mata yace “he will slowly Die, dont forget his Ribs are Infected, and its close to the Heart, when he breathes in the Heart touches the veins of the liver, its risky”.
Da sauri tace “then mai ake jira, muna bata wani lokacin ne, lets have the surgery now”.
Sukace “who is donating?”
Tace “Me, prepare for the surgery now”.
Ta mike ta fita ta barsu su biyu suna binta da kallon mamaki.
Dakin ta koma.
Ta karasa da kallon tausayi tace “Kayi hakuri, duk wannan wahalar ka shata kai kadai, i am sorry you went through this alone, i am here for you now”.
Ko bata fada ba ya san me take shirin yi, yasan mai zatayi
Ya girgiza kai yace “Labiba Dont, karki yarda a budeki, mutuwa zanyi, theres a possibility ko an yi surgery din ba zan rayu ba, kuma donor din will be at risk, kar kiyi, ba zan yarda ba, i am dying”.


Murmushi take mishi mai tarin ma’anoni daidai ta digar hawayenta tace “ZAN RAYU DA KAI, ZAN MUTU DA KAI”.


#1love
#DM
#anatare
#FWASonSo
#nagode




Biebee Isa
[14/03 9:35 pm] Biebie: DAN MAKAHO😉


BABI NA ASHIRIN DA TAKWAS 2⃣8⃣
(MAKOKI).


Hankalinta kasa kwanciya yayi kwata kwata, kiran number takeyi yafi so nawa amma kwata kwata wayar bata shiga, me zatayi? Me ya samu diyarta? Ko ta aika Aljanni ya dubo mata Yasmin? Gani tayi process din zai bata mata lokaci ya sa ta kira Driver Mallam Haladu don tafiya Kankia.


Mutanen Kankia an rasa abunyi, babu abunda ya tsira bayan Plate number na Mota.
Muhawara aka tafka na tafia da gawar Asibiti ko police station, 'yan kauyen suka sa baki aka tafi da gawar Asibiti don kaiwa Mortuary, tuni aka gane mai Rasuwar ta hanyar Plate Number din.
Kafin kace kobo Mutuwar Dr Yasmin K'amshi ya zagaye garin Katsina da kewaye ta hanyar Social Media, wane ya gani ga wane haka mutuwar Dr Yasmin K'amshi ya zagaye Nigeria baki daya.


Mutuwarta Abin tausayi ne, in ka duba Statuses din mutane Hoton Dr Yasmin ne, da yawa masu sakata ma basu santa ba.


Shigowar Hajia Er Rabi Asibitin Kenan ta ga tayi wata irin cikowa, a hanyarsu ta zuwa taga wata Mota tayi accident a bakin titi ta wurin Gidan Mutum daya, ta fi zaton ko wanda sukayi Accident din ne aka kawo Asibiti.


Reception ta tsaya tana tambayar Dr's Quarters.
Receptionist cikin rashin walwala tace "wa kike nema? Duk suna common room".
Da murmushinta tace "Diyata Dr Yasmin".
Receptionist ta rasa mai zatace mata, ta kalleta da kallon tausayi, ba huruminta bane fadan mutuwa, tace "zo muje".
Er Rabi ta murmusa tace "yauwa nagode".
Receptionist tayi gaba Er Rabi ta bita a baya, ba su tsaya ko ina ba sai common room, nuni ta mata da ta shiga ciki.
Er Rabi bata tsaya wani tunani ba ta shiga cikin Dakin.


Doctors ne a ciki Maza da Mata wasu zaune wasu tsaye, Matan kuka suke wi wi, Mazan kuma akwai masu hawaye wasu dai idonsu yayi ja.
Er Rabi batace ma kowa komai ba ta bisu da ido, da ta gama rarraba idanuwanta tana neman diyarta bata gani ba ya sata magana.


Doctorn da ya fi kusa da ita ta kalla tace "Dr, danAllah ina Dr Yasmin?".
Hankalin kowa dake common room ya dawo kan Hajia Er Rabi.
Tambayar ta sake yi, wani yace "wacece ke?".
Da faraarta tace "Nice Mummy, Mummyn Dr Yasmin".
Jin sautin kukan wasu matan ya k'aru.
Tace "wai ya? Meke faruwa ne?".
Wani Dr yayi ta maza yace "Mummy saidai muyu hakuri, Dr Yasmin ta rasu bayan Accident din da tayi 1hr ago".
Er Rabi tace "kutumar Uba ne, meye rasuwa? Kai dallah baka santa ba".
Taje kusa da wata ta mace da ke kuka tace "ke kawar Yasmin ce? Ta na ina? Muna cikin waya wayarta ta mutu, muje ki nuna min ita please".
Dr ta fashe da kuka mai sauti.
Wani Dr yace "Mummy zo muje ki gani".
Ba gardama ta bi bayanshi
Tace "Haladu, fito zo" driver ya bi bayansu da Mota, a tunaninta Wurin Yasmin zaa kaita taji yana cewa "Mummy, kinga ruwan saman nan bai dade da tsayawa ba ko?" Ta gyada kai yace "ba mu dade daga fitowa daga OR ba ni da Yasmin, wallahi Mummy sai gawar Yasmin nagani da idona".
Mummy ta buge mai bakitace "kai bakinka ya sari danyab kashi, Yasmin nawa gareku? Ba dai tawa ba, ni fa yanzu yanzu muka gama waya da tawa Yasmin din".
Yace "kiyi hakuri, yanzu yanzu sai Allah, in ta Gidan Mutum daya kika biyo zaki ga wata Motar da ta kone bakin Titi, wallahi motar kamshi ce"


Wani irin razanannen Ihu tayi wanda duk wanda yaji ya san ba na lafia bane, zubewa tayi k'asa Sumamma.
Tuni Drs sukayi kanta aka basu Gado.
Haladu Driver ya kira Mijin Er Rabi ya sanar gasu a Asubiti Hajia ta suma Yasmin ta mutu.
An dade a kan Hajia Er Rabi amma bata san wake kanta ba, ba ta farfado ba.
Baban Yasmin yazo da wani kanenshi, hankalinshi ya tashi, dalili daya da ya sa yake zaune da Er Rabi saboda Yasmin ne, Yasmin na sonshi, in Mamarta ta guma mishi bakinciki ita ke lallashi tana bashi hakuri, yayi kuka kamar zai shide da ya ga gawar Yasmin.
Karban gawar sukayi suka wuce Katsina ba tare da ya damu da duba halin da Er Rabi take ciki ba.
Duk Doctors sun biyo don suma a samu Taaziya dasu.
Ya gama waya da Yanuwa da abokan Azziki da ya isa zaayi janaiza, gata daya zai ma Yasmin, da an isa Katsina a mata sallah a kaita makwancinta kafin Er Rabi ta farfado ta musu jahilci, don yasan ba zata taba bari a rufe Yasmin ba.


Messages dinta ya gani na ban hakuri sai na karshe na tafiyarta Edo gida amma zata dawo ba da dadewa ba, Zuciyarshi ta gama karyewa da jin ta tafi, kila ba zata dawo ba, amma layin karshen message dinne ya bashi tabbaci inda take cewa "Na maka Alkawari zan dawo, kasan kuma Labiba Kaifi daya ce, nace Zan dawo, zan kuwa dawo ma". Da tunanin Beebbs dinshi ya shiga cikin Gida don girka abinda zai jefa a bakin shan Sigari.


Hudu da Shafa'atu na zaune a parlo, bakinta har kunne tana jira ta ji haukacewar Zaid ko mutuwarshi kamar yarda Er Rabi ta shaida mata.
Wuce su kawai yayi ya shige kitchen.


Hajia Laraba ta fado Gidan ko Sallama babu.
Hajia Shafa'atu ta rikota tace "ke lafia? Me ya sameki?".
Cikin tashin hankali tace "Daga Gidan Er Rabi nake, kinga mutane sunfi 1000, wai Yas ta rasu, tayi accident ta kone".
Hajia shafaatu ta kar kade kunnenta tace "mene mene mene?".
Tace "wallahi wai Yasmin din Er Rabi ta mutu".
Zaid ya ji wani jiri na

Please Login or Register in order to submit comment