Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka shige dakunansu.
Baban Amira yace "Oh Allah ka ci da ginin bangon nan kar ya rushe" Anty Aseeyah tace "ai sai yanda ta yiwuwu dai kawai"


Jugum-jugum suka zauna suna sauraron ruwan Sama, sai ga ruwa kam da bakin kwarya, suna jin ginin ya sake faduwa wurin da aka gyara, ta window sukayi ta lek'e suna jimami.


K'arfe har k'arfe 10 saura ruwa bai tsaya ba, duk sunyi bacci banda Labiba da ke daki tana waya da AbuSideeq inda yake tambayanta dalilin rashin zuwanta makaranta.


Karya tayi Kamar yanda ta gaya ma Aisha da sukayi waya dazun haka ta gaya mishi, bata lafiya. Sannu ya mata ya mata sallama da fatan samun sauk'i.


Ruwan saman nan na kawo ma duk wani bawa mai rai nutsuwa, saboda yanda yake sauka cikin wani yanayi mai sa Nishadi. Jugum tayi zaune tana latsar wayarta kadan ne babu cikin karfe 10.


Me ya keyi? Bacci? Ya koyi Sallahn Isha'i? Ko ma ya ci abinci? Ko ya suka k'are dazun da Babanshi? "Ya Rabb" ta fada da ta tuna yanda sukayi dazun, shaf ta manta da wani fushin da tayi dashi.


Haka kurum Zuciyarta ke k'yank'yasa mata Zaid cikin daren nan, Son ganinshi take son yi, son sanin halin da yake ciki takeyi, kawai tana son ganinshi da daren nan, har ya kai ga ta na ji kamar ba zata iya bacci ba in har bata saka shi a Idanuwanta ba.


Juyi ta koma yi kan Katifarta, da duk numfashin da ke sauka daga kirjinta tana mai hasassho halin da Zaid yake ciki a wannan Dak'ikan.


Wuf ta tashi kamar an tsikareta, ta yanke hukuncin da bata san ko ya kamata tayi abunda take shirin yi ba.


Dakin DANMAKAHO zata.


Hijabinta ta dauko ta daura kan Rigar baccinta ta fita sadaf sadaf tayi hanyar bangon da zai sadata da Gidansu DanMakaho kamar barauniya. Chogewa tayi ta tsaya kuma tana wani tunani.


Bai ka mata ba ko kadan ace taje Dakinshi a wannan daren, ba ta san halin da yake ciki ba, ba ta san mai zai mata ba, it is wrong, so wrong, daya daga cikin zuciyarta na cewa "Dont Labiba, Dont". Dayar ko Ingizata takeyi.


Zai rantse be taba jin wannan yanayin ba, zai rantse bai taba zama yayi tunanin wata haka ba, tunanin wata bai taba lik'ewa a k'wak'walshi ba, tun dazun ya ke tunaninta, yanda ranta ya baci ne ya dameshi, duk abubuwan da yake gaya mata ko yake yi mata bata taba fushi dashi ba, ba ya so ya chanzata, ba ya son ya k'ure hakurinta, tunda har ta shiga rayuwarshi, gobe InshaAllah zai bata hakuri.


Ji yayi kamar ana taba k'ofarshi, duk da bai sanya sakata ba amma kofar datse take,ba wanda ya damu da dakinshi, wa zai zo yanzu? ko dai iskan ruwan da akeyi ne yake hurowa? To ai Kofar datse take, kuma kofar irin ta manyan wood din nan ne, iska ba zata budeshi ba, da sauri ya tashi ya bude k'ofar.


A kallo na farko ya zata Dalo ce, sai da ya kalleta sosai ya gano Labiba ce, a cikin sakwan kadan ya finciko hannunta ya jawota cikin dakin ya rufe kofar kamar mai tsoron kar wani ya gansu.


Hannu ya sa ya murji idonshi, tana tsaye tana farfar da ido tana rawan sanyi, Hijab dinta duk ya jik'e.


"Bibbs ba kya jin magana meyasa ba kya ji? Me kika zo yi nan?".


Murmushi tayi tace "Bango ya sake faduwa".


Ba wannan yake sonji ba "how could you be so reckless? Don me zaki dinga zuwa min daki? Ba kya tsorona? Ba kya tsoron ina iya danneki cikin daren nan? Baki ga tsinuwan mahaifi a kaina ba? Ba ki san mutuncin mutum na zubewa ba idan aka ganshi da ni ba? Ba ki san dazun da sun ganki ba sai sun bata miki suna ba? Don me zaki dinga zuwa inda nake? Da daddare, wai ke baki san ni Namiji bane of 28years? Baki san me ke faruwa ba in Namiji da Mace suka kebe? Are you not worried about yourself? About your Family? About Mami? Kin manta Gidanku baa karatun boko amma mahaifinki ya yarda ya turo ki karatu saboda ya yarda dake? Ya yarda zaki kama mutuncin kanki, ki kare martaban gidanku, amma zuwa dakin Namiji mutunci ne? In yayanki ya kamaki ya zaiji?".


Kyafta idanuwa tayi, tace "Ya Zaid, na yarda dakai, ba zaka cutar dani ba" ba tare da ya tanka YaZaid din da ta kirashi dashi ba yace "baki sani ba Bibbs, baki san ko zan iya cutar dake ba ko ba zan iya ba, World fa nake sha...Uhm Wiwi".


"Dagaske na san ba zaka cutar dani ba, ba zaka min abunda zakaji haushi ba in anyi ma Dalo". DanMakaho ya tsura mata ido kafin yace "DonAllah DonAnnabi me kike so, its late, ki koma Gida, gobe zamuyi magana".


Kai ta girgiza tare da zama kan kujerar dakin tace "ni bana jin bacci, ba kuma abinda zanyi, so yafi ka idasa bani labarin".


Idonshi ya murza sosai kafin ya zauna yana harararta, ita ko sai murmushi take sakar mai.


Sarki ya mana Nasiha kuma yace in muna da wata damuwa da Babanmu ko Matarshi muzo mu gaya mai, sarki ya sallame mu.


Baba da Aunty Shafa suka fita daga fada ransu a bace, Baba Sani ya dauke mu ya maidamu Gida nida Dalo bayan ya mana nasiha sosai ya bamu hakuri.


Daga wannan rana komai ya chanza mana Beebs. Da muka Shiga Gida mun tarar da Baba, Aunty Shafa, Hudu da Annah zaune a Parlo, jikinmu yayi sanyi yanda mukaga suna kallonmu, jan hannun Dalo nayi zan sadata da Dakinta amma na jiyo Ihun Baba.


Danubanku kuzo nan. Beebs, bamu saba ba, Babanmu baya zaginmu,Babanmu ba ya daga mana murya, k'ara matse hannunta nayi muka shiga Parlon sosai.


A gefe muka dan rakube, ran Baba bace yace "yanzu ni Maryama ta tona ma asiri ko DanMakaho? Kuna ganin uwarku ta kaini k'ara Gidan Sarki, bayan duk abubuwan da na mata, duk hallacin da na mata ta rasa da me zata saka man sai ta kaini Kara a Fadar Sarki? Ni Alhaji Ali Zaki?".


Mu dai ba muce komai ba Baba ya cigaba da cewa "to tunda Maita ta hanaku bin Uwarku, ku zauna, amma ba ruwanka Zaid da cikin Gidana, Boysquarter zaka koma, ban yarda da kai ba, ina da Diya Mace, kar kazo ka keta mata haddi, wani irin yammmm naji a jikina, na dago kai na kalli Babana, wanda banda tabbacin ko shine ko ba shi bane,anya Baba na ne Mahaifi? Me ji dani? Me yin duk wani abunda nakeso?".


Ya cigaba "Ke Sadiya, Annah tace dakinki take so, so ki koma BQ tare da Yayanki, ko ki koma gunsu Raliya masu dafa Abinci". Dalo ta dago baki zatayi magana sai kawai ta fashe da kuka.
Ni ko na fara girgiza kai alamun rashin yarda nace Baba ta ya Dalo zata koma Boysquaters? Dakuna nawane a cikin Gidan nan da har sai ta koma BQ? Haba Baba kar ka juya mana baya".


Hayyayakowa yayi "DanUbanka DanMakaho ina fada kana fada? Rashin da'a zaka min? Danubanka nace ba ku zama min cikin Gida, ku koma BQ, bana son ganinku, ina laifi ma da na barku a BQ din".


Zaid ya tashi inda yake rak'ube yace "Baba, wallahi ba zata yi zaman BQ ba, in ka matsa yanzu sai naje Gidan Sarki na gaya mishi "
Baba ya tunzura, danubanka ni zaka tona ma Asiri? Kaje ka gaya mishi to, tsinanne watsattse, da sauri na tashi hankalina a tashe ban ma ganin gabana na dinga jefa kafata kasa na fita daga Parlon.


Aunty Shafa tace "barshi Alhaji, kaga dai abunda Sarki yace, kar a kama mu da saba ma Umurnin sarki, Baba ya amince, Anty Shafa tace ke Sadiya ki koma dakin kusa da naki, naki Annah ke so, Sadiya bata da rigima duk da ta san Dakin da ake so ta zauna ba komai ciki daga Gado sai toilet amma na ta har Tv akwai bayan decoration din dakin da akayi da pink and purple color. Kai ta gyada alamun ta amince, Anty Shafa ta koreta cewar zasuyi magana ta zauna musu, sumsum ta mik'e ta wuce dakin da aka ce ta koma.


Ni kinsan abun bai dameni ba zaman boysquaters don na san in 2days zan koma makaranta so Dalo ma ne nake jiye ma zaman bakincikin da zatayi.
Duk ranar wayar Mancy a kashe yake, na kirata yafi so dari naji ya take, me take ciki, karamin hauka na kusa yi. A waje na zauna bayan Sallahr Maghrib, ga yunwa ina ji bana ma son shiga Gida balle naga kayan bacin rai, kawai na wuce gunsu Raliya masu dafa Abincin Unguwa, aiko na samu Jollof din Shinkafa a wurinta, ta na tausata da bani baki kan mu jure duk wani abun da zamu gani daga yanzu.


Washegari da safe na tashi na tafi cikin Gida don ganin yanda Dalo ta tashi, kallo daya na mata na lura da tsantsar ramar da tayi na kwana daya, tausayinta ya kamani, na karasa gunta ta dago da murmushi mai kama da yak'e.
"Ya Zaid, har yanzu ba ka samu Mancy din ba? Wayarta a kashe" ta fada cike da karaya, ka sa amsata nayi, na durkusa daidai tsawonta nace "ba kiyi breakfast ba, tashi mu shiga kitchen na hada mana kalaci".


A Gidanmu kowa ke hada breakfast dinshi da kanshi, saboda rarrabuwan raayi, in kuma k'osai da koko din Raliya kake son ci sai kaje baya kaci.


Na rik'o hannunta muka shiga Kitchen, muka kalli juna cike da mamaki, ba wai ba komai cikin kitchen din ba, aa sai ganin babu abubuwa da yawa, trolley din kayan tea, ba komai, ba kwai ba komai cikin fridge dana duba, yanda na lura duk wani abunda zaa sarrafa a sa a baki babu, da mamaki muka kalli juna, yaushe akayi wannan kayekayen? Dalo tace "maybe suna a Store" da sauri na karasa store na jishi a gark'ame.


Da karfi na kwada ma Raliya kira, sai ko gata nan da saurinta, tnace wai ina kayan Abincin gidan nan? Ta duba kitchen din da idonta tace "toufa, kamar an kwashe komai, na jinjina kai na san aikin matar chan ce, nace Raliya Yunwa mukeji, tace ai DanMakaho akwai Kalaci a kitchen din baya, bari na kawo muku. Parlo muka zauna muka jira Raliya ta kawo mana Breakfast.


Dadi kosai da koko dinta, sosai mukaci don jiya rabonmu da abinci tun rana. Muna cikin breakfast sai ga Aunty Shafa'atu ta shigo da nightgown jikinta. Da mamaki ta kallemu tace "ina kuka samu Abincin nan?" Daga kai nayi na kalleta nace "meye amfanin kwashe kayan abincin kitchen da kikayi? So kikayi kiyi starving dinmu da yunwa? Ko so kikayi ulcer ma ta kama mu? A gidan ubanmu? To ba zai yiwu ba, wallahi baki isa ki horar damu yunwa ba a Gidan Ubanmu".


Fuuu ta wuce ta banka dakin da Baba ke ciki, ko bacci yake ko zaune yake oho, amma da karfi naji tana cewa "ni yanzu a sallami su Raliya masu Abincin Gandu". Baba yayi dan jim kafin yace"Shafata, Abinci sukeyi wanda ake rabama yan Unguwa, da yawa da nan gidan sukayi relying, in aka Sallamesu wa zai dafa Abinci har a ba Makwafta? Kicinkicin tayi da fuskarta tace "nidai Alhajina kana shagwaba talakawa, in ka dinga basu abinci kullum ta ina zasu samu zuciyan neman na kansu? Zuciyarsu bushe take, su a ganinsu sun samu bati ni dai kawai ka sallame su Raliya, daga yau an gama Abincin Badawa".


Da sauri Baba yace "kuma fa? Hakane mutane son banza garesu, daga yau ba zaa k'ara Abincin badawa ba, ko wani shege ya tashi ya nemi na kanshi, ai maza a kira man su Raliyan".


Well ina gaya miki Beebs, baba ya ma su Raliya da masu taimaka mata wurin dafa Abinci, Sallaman Wulakanci Aunty Shafa na tunzurashi kamar wani robot take control dinshi, ni kuma da na ga haka, nace su jirani naje Bank, da sauri na dauki Motata na nufi Bank, na zaro dubu 200 na basu nace su ja jari, godia suka dinga min kamar zasu min sujadda, suka dinga min addua suna mana fatan Allah ya karemu daga sharrin Matar Uba, Raliya da yake zata girma Mancy, ta dinga min Nasiha da kuma na kula da Kanwata, suka min Sallama suka kwashe kayayyakinsu.


Ashe Hudu ya ga lokacin da na mik'a ma Raliya Kudi, ashe ya je ya barar ma Yayarshi, yayarshi ta tada ma Baba rigima da haka yake barina ina kashe kudi? Be san kudi na bata yaro ba? Ita gaskia ba zata yarda ba?.


Hahaha Labiba Babana ya kira Manager ya sashi freezing account dina, bayan ya kwace makulan Motanshi, da wayar hannuna a cewarshi da kudinshi na siya, God, to ban ma dai yi mamaki ba sai da bayan kwana biyu na samu Baba game da son komawa Makaranta.


Nan ne Baba ya min Wulakanci gaban Matarshi da Diyarta da k'anenta.
Da farko banza yayi dani ya k'yale sai da na sake magana nace "Baba lokacin da ya kamata na koma Makaranta yayi, jarabawa zaa fara da sati 2, zan koma na fara shiri".


Baba ya dan kallo Anty Shafa, da ido ta mishi magana, haba sai baba ya fara Spark, wani irin Makaranta, Kai dan iska ina sane da duk wata burobar da kake a k'asar Ingila ba, Shekarar 6 a chan amma ka kasa hado degree, sai dai kaje ka shek'e ayarka da yanmata, ka dawo Nigeria ka kuma koma London san da kaga dama, to ba zaiyiwu ba wallahi, ba zai taba yiwuwa ba".


Nan ne ya kasheni da Mamaki, baki na nauyi nace "Baba, wani Degree kake magana? Ina Degree din da na amsa ranar da kukaje London kai da Mancy da Dalo? Baba har fa Graduation Dinner sai da kukaje, ko kuma ka manta na riga da nayi joining Masters, befi min Wata daya nagama ba? Yanzu da na koma nayi Exams fa na gama".


Baba ya dinga zare ido "kai ni ban san wannan ba, ni sisi na ba zan k'ara kashewa a kanka ba DanMakaho" hankalina ya tashi amma na daure nace "kayi hakuri babana, ka bude min account dina, akwai kudi na, ni zan dauki nauyin kaina, i need to go back Baba".


Tsawa ya daka min yace "Bazan ba, nace bazan ba, na cire kudadden Account dinka tas, London kuma ba zaka kara zuwa ba". Guiwowina na dire a kasa ina kuka "Baba ka min rai donAllah, kar ka hanani komawa, Baba in wannan shine abu na karshe da zaka min a duniya donAllah ka maidani London, don Girman Allah baba".


Kafa ya sa ya shure ni sai da na k'ume, a kausashe yace "bazan kai ka ba, naira daya ta gama kuka a kanku".
Shafa'atu tace "kaima Alhaji ka rabu dashi, tunda shi ya fi so a yi ta magana daya".
Raina ya baci ban san sanda nayi wani kukan kura ba na chakumo wuyanta, na mak'ureta kamar zan kasheta, Hudu da Baba suka yo kaina, suka rufe ni da duka amma ko gezau banyi ba, na cigaba da matse hannuna a wuyanta ita ko sai k'akarin mutuwa take.


Dalo ta fito daga daki da gudu da ta ga hayaniya tayi yawa, ni ko wani karfi ya zo min na ingiza Baba da Hudu, na hau dukkan Aunty Shafa'atu, Dalo na kuka tana Yaya donAllah ka rabu da ita, ina sam ban ji ta ba, ita ko a galabaice take kukan wahala, Hudu ya rikoni ta baya, Baba ya dunkula hannunshi ya dinga kai min naushi ko ta ina kamar zararre, itama Aunty Shafar ta mik'e ta nufoni tana dukana Dalo ta rike mata hannu ta wurgar da ita.


Kamar daga Sama mukaji ana Sallami, muryar tsohuwa ce ke cewa "Ki kori Mahaifiyarsu ki juya kan ubansu yanzu ku mishi rubdugu? To wallahi baki isa ba, sai na ci uwarki, yau sai na ga Bokanki, daga nan har Pilatu sai na ga Uban da ya tsaya miki a Najeria".


Dalo ta dago kai ta kalli Tsohuwar da ta ke niyar cin danmara, a wahalce tace ;


NENE..


Ai Nene ba ta bi kan dalo ba ta shiga cikin fadar nan ta finciko Shafaatu ta kaita k'asa, ta dinga kilarta kamar Allah ya aikota, Baba yazo shiga tsakani ta sa hannu ta tsokale mishi ido, ganin haka na maida hankalina kan Hudu, ni da Nene muka kaisu k'asa ina kilar kani Nene na kilar Yayar, baba hankali tashe ya wawuro wayarshi ya latso kiran Police Station.


Wai tsohuwa Nenen nan sai da ta ma Shafa habo kafin ta tureta, ta rik'o hannuna da na Dalo tayi gaba, tana maida numfashi, tana haki tana cewa "ni ai ko bokon Saude sai da ya tantance Aminene Mamman, zaki zo ki shiga tsakanin da Da Mahaifi, shegia K'abilar banza".


Muna jin Aunty Shafa'atu na cewa "wacece wannan Alhaji?" Kafin Baba ya bata amsa Nene tayi karaf tace "Uwarki ce, kaii a'a ni ban haifi Azzaluma ba, Sunana Aminene Mamman kije kiyi tambaya kaina".


A tsakar Gida muka tsaya ta kalleni rai bace tace "kai danubanka sai kayi tsaye suyi maka taron dangi?" Ta kalli Dalo tace "ke kuma sakara kin tsaya kin bare baki kamar famfo kina ta kuka ana dukan Yayanki, baki dauko wuka ki watsa taron?"


Baki bude nake kallonta na san Matar kamar zararra take amma me take nufi? Nace Nene fa harda Baba fa, kai dallah arr, ni sai na bugeshi tunda ni ba ubana bane, sai na mushi mugun bugu tunda shi sakarai ne shanyayye".


Kai ni ina Gida Raliya ta kawo min zance abunda ya faru, to wai danuban Maryaama tana da wadda ta fini ne duk garin Katsina, ashe cin kashin da Ali ya mata kenan? Bayan ya wulakantata harda bugu? Ni ina me baa zo an sanar dani ba? Wato ni hoto ce, banda wata amfani".


Zaid ya dafe kai, matar nan tana son saka mishi pressure da yamman nan, ni yanzu kiyi hakuri Nene, wallahi ban ma cikin hayyacina cikin yan kwanankin nan".


Kai dallah ar raggon maza, ba ka biyo masu Sunan ba, Zaidu Bawan Allah jarumi ne".


Labiba ta share hawayenta amma yanzu murmushi na dauke a fuskarta tace "Wacece wannan? Kakarku ce?".


DanMakaho ya murmusa shima yace "Ba dangin Iya bara ne Uba, wai kawar Mancy ce, amma fa tsohuwa ce kuma a haife ta haifi Mancy".


Labiba da mamaki tace "Kawa kuma?"
Yace "Eh kinsan Mancy na yawan zuwa Hajj da Umrah, to a chan suka hadu, dakinsu daya a cewarta Mancy ta taimaketa sosai da hidima a Makka shiyasa suke kawance, to tunda suka dawo suke zumunci ko muje ko tazo, tsohuwa ce amma bata da hakuri, karfinta kamar na garada Goma". Sosai Labiba ke daria.


Ya cigaba
Kafin wani yayi magana sai jin siren din Motan yansanda mukayi. Baba ya fito Shafa'atu na biye dashi a baya, ke wai Baba ya shigo da YanSandan nan yace a tafi damu a rufe mu bayan karta harda Nenen.


Nene kuwa tayi kukan kura tace "duk uban da ya tabani sai naci kutumar ubanshi, yara ba ku sanni ba" ta zaro wayarta a purse ta mik'o min tace "latso min Zaidu Bawan Allah, kai ba ma shi zaka kira ba, latso min Habibu Lema, in na tuna da kyau harda shi yayi silarka ka zama abin da ka zama a yau".


"Yo ku kadai kuka san manya? Nima dana Habibu ai suke da gwamnati, kuma shi ba tsaranka bane, kai soko maza kira man shi" ko mai Baba yayi tuna oho sai cewa yayi "ku bar tsohuwan, ku tafi dashi ku kulle, ku lallasa min shi".


Haka yan Sandan nan suka kamani kamar barawo, Dalo ta fashe da kuka.


Nene tace "oho, nidai ba uban da ya isa ya kulleni, shi da ka isa dashi ka sa su tafi dashi, ke kuma ki ma mutane shiru komai kuka, kai kuma Danka ne, ka barshi a chan bayan karta kar Allah ya sa ka firdoshi, ka barshi chan ya mutu Sakarai shanyayye, ke kuma a juri zuwa rafi".
Ta fizgo wayarta daga hannuna ta wuce fuuu kamar zata tashi sama.


Ba su jira wata ba suka tusa k'eyata suka sakani a bayan motarsu suka tafi dani, hankalina tashe, yau nine haka a wulakance, ba wani wata wata a ka wurgani bayan karta.
Wani zauri ya bugi hancina, ga k'uda, ga k'azanta daga wani bangare, hawayen bakinciki suka soma kwaranyo min, yau ni ni ne a Cell? Yau ni ne a wulakance, meyasa na ma dawo hutu? Meyasa nake da rabon ganin wanan rana? Kuka nake sosai ban damu da kallon da yan bayan kartan ke bina dashi ba, ban damu ba.


A sannu na yi ta hasasso rayuwarmu a da, da rayuwarmu a yanzu, komai ya chanza Alkalamin k'addararmu tayi zanen da ba zata kankaru ba, sosai nake kuka, na dade kuma ina kukan, bansan minti ko awan da dauka ba ina kuka.


"DanMakaho" naji an fada
Da sauri na dago kai don ganin me min kiran nan wanda tabbas ya sanni tunda ya kirani da sunan da yan Unguwa kadai ke ce min.


Na sanshi, ina ganinshi a Unguwa, Dan shaye-shayene, ya sha rokona kudin da zai ci abinci duk da na san karya ne shaye-shaye zaiyi dadu ban taba hanashi ba, da shi da yan bencin Eskaley na sha raba musu naira dubu dubu.


Da kyar na ambaci sunashi "Haruna, me kakeyi a nan?" Haruna ya danyi daria yace ai ni nan bana sati 2 k'warara banzo nan ba, kai ne dai zan tambaya me kake anan. Ban iya ce mishi komai ba na duk'ar da kaina.


Gaskia DanMakaho Babanku ya kwafsa, ji yanda ake ganin mutuncinshi amma wa shine zai yi wannan kwafsin? Harda dukan Hajia Mancy gaban kowa, Kai ya mugun kwafsawa.
Kamar jira nake na fashe da wani sabon kukan, be lallasheni ba, bai hanani ba, bai kuma tafi ya barni ba".


Sai da na tsagaita kuka na kafin na dago kai na ga hannunshi a mik'e alamun wani abu yake so na karba daga hannun.


World kenan, ka sha shi, wallahi ka sha shi damuwar da kake ciki zai bace bat, ka dan ta6a world ba ka da wata matsala.


Kallo daya na ma kullin garin na kauda kai. Zama yayi kusa dani


Kagane ko ka sha taimaka min, ka sha fiddo ni cikin damuwa da yanayi, in ka bani kudi, kaga abunda nake siya nan, dagaske in na sha shi wallahi bana da wata sauran damuwa, wallahi World duniya ne, duk yanda kake cikin damuwa, bakinciki, kuncin rayuwa, da ka zuk'a so daya damuwar zata kwaranye, zuk'a ta biyu kuma zakaji kanka a kan gajimare, ka gwada zuk'a daya, da kanka zaka nemi k'ari, in kuma ka zuk'a damuwarka bata gushe ba kayi kan duk abunda kake so".


Runtse Ido na nayi, na yarda gajeran tunani gareni, shaidan ya buga min ganga, a cikin Cell dinnan na zubdar da duk wani tarbiyan da Mancy ta min shekara 25, Wallahi Beebs da na bude World na fara zuk'a ta hanci, sai da na zukeshi tass, Haruna ya so ya kwace amma na hanashi, burina damuwa na ta kau".


Ido na a runtse na ji ni a wani irin yanayin da ban taba shiga ba, wani yanayi mai wuyar fasali, wani yanayin da ban taba saninshi ba. Wanda suka dade a harkar da wuya su ja World fiye da biyar, ni ko na ja shi ya fi so 20, mamaki na Haruna keyi yanda ya ga nayi bagas a k'asa ido na a runtse in rausaya da kaina hagu in rausaya da shi dama.


Haruna na tsoron kar na haukace, don in yayi yawa yana sawa a zare, sunana ya fara kira
DanMakaho
DanMakaho shiru ba amsa ido na runste


A kira na uku ne na bude ido tare da sakin wani irin murmushi.
Cikin jin dadi haruna yayi wani juyi, tare da jinjina hanayenshi guda biyu alamun ya sara min gami da cewa;


MAANNNKAAAASSSSS.......


Yes Guys your one and Only Nene is here
Who's happy?


Vote and comment line by line please


#1love
#DM
#anatare
#FWASonSo
#nagode


Biebee Isa




[14/03 9:35 pm] Biebie: Babi na Sha Daya1⃣1⃣
(MANKAS II)


(Note: wannan Events din ya faru ne Bayan dawowan Nene daga London lokacin da Nasiban Rafeeq ta Haihu. Fahimt?)


A kan idonta a ka wuce dashi cikin motar yan sanda, ranta a bace, sai dai ya ta iya? Fuuu ta shige bayan motar da aka kawota, ko magana bata iya mishi ba ta wuce Gidan Lema.


"Banda Sakarai shanyayye,

Please Login or Register in order to submit comment