Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

murmushi kamar tana gabanta "Ummanmu ina wuni?" dama a handsfree wayar take dadi ya kama Jawad, "Lafiya lau Labiba, ya kike ya su mamanku?" Labiba ta amsa mata, Umma ta tambayeta ya Makaranta, kafin ta mata addua sukayi Sallama.
"Ameen Ummanmu, Nagode Allah ya k'ara Girma ya kuma ja Kwana".


Labiba mai Farinjini tuni Umman Jawad taji ta na sonta sosai, tace "Jawad, Labiba wayayya ce, ba ruwanta" Jawad yace "sai ma kin ganta a fili" Umma ta kai mai dukan wasa tana cewa "wuce ka zubo abinci Ja'iri".


ALHAJI ABU SHAMSU


Asalinshi dan Garin Katsina ne, Alhaji Abu Shamsu na da k'ani daya rayyaye, sauran duk sun Rasu, Alhaji Abu Shamsu fitattacen dan Kasuwa ne mai zaman kanshi wanda ake damawa dashi a k'asa, Hajiya Lubabatu itace Uwargidanshi tun auren saurayi da budurwa, itama 'yar Katsinar ce, tun Abu Shamsu na 'yan buga-buganshi sukayi Aure har Allah ya mishi budi.
Alhaji Abu Shamsu da Hajiya Luba na da yara Uku, duk Maza, Abdulhafiz shine babba, sai AbdulMajeed sai auta a cikinsu Jawad.
Amaryar Alhaji Abu Shamsu wacce basu rufe Shekara 4 da aure ba Sunanta Hajia Maryam, diyarta daya Aminatu ana ce mata Mimi.
Wannan kenan


Ruwan Sama akeyi ba k'ak'autawa, tun k'arfe 10 dare, har wayewar Gari, da Asuba Baban Amira ya fito don yin Alwala don tafiya masallaci yin Sallahr Asuba, gabanshi ne ya fadi ganin bangon da ke tsakanin gidanshi da Alhaji Ali Zaki ya rushe, "Subhanallah, Inallillahi wa ina ilaihir rajiun" ya furta, da kyar ya daure ya shiga kewaye ya dan zagaya tare da yin alwala ya fita masallaci.


Bayan Sallahr Asuba suka hadu da Alhaji Ali Zaki, Baban Amira ya karasa wurinshi sukayi musabaha cikin mutuntawa.
Alhaji Ali yace "Mallam ya Iyali?" Baban Amira yace "Alhamdulilah, sai ga tsautsayi kuma" Alh Ali yace "Subhanallah, me ya auku?" be yi mamakin rashin sanin da yayi ba saboda bangon ta baya ne, ta inda Boysquaters yake, Baban Amira yace "jiya Ruwa yayi Gyara, Bangon da ke hade dade da Gidanka ne ya fadi".


Alhaji Ali yace "Subhanallah, IkonAllah, wallahi ban gani ba, ko don ban lek'a bayan ba, ta wurin DanMakaho ne kenan, InshaAllahu zaa gyara, bari gari ya waye" Baban Amira yayi Godia suka taho Gida tare, "ai Alhamdulilah tunda bangon be fado ma wani ba" "Ai don dare ne, amma wurin Iyalina suke shimfida don wurin akwai inuwa" Alhaji Ali yace "IkonAllah, Allah ya k'ara tsarewa"
A haka suka iso Gida, Baban Amira ya shigar dashi ta Gidanshi ya gani, suka sake jajantawa juna Alhaji Ali kuma ya tabbatar mishi da cewa da Safe zaiyi waya a siyo Bulo da k'asa da Siminti sai a gyara. Godia ya sakeyi kafin ya bi ta dan hanyar ya shige Gida.


Aunty Aseeyah haka ta tashi ta ga Ikon Allah, da mamaki, Baban Ameera ya mata bayani, ya kuma gaya mata yanda sukayi da Alhaji Ali, jinjina lamarin tayi kafin ta k'ara da Allah ya tsayar nan, dan tautaunawa sukayi, Baban Amiran ya yanke Shawaran su fita gabaki daya, sai ita Asiyar ta tafi Gidansu, in Yara sun tashi daga Makaranta sai a kaisu gidansu Aseeyar, Labiba


Sallah tayi ta shiga dakin Labiba da Yara, Labiba na fashin Sallah. Aunty Aseeya ta fara tada yaran don suyi shirin Makaranta yau Monday.
Labiba ta farka ta gaida Aunty Aseeyah, ta amsa tace "sai kika ga Bango ya fadi ko?" Wuf Labiba ta mik'e zaune tace " "Bango? Na ina? Inallillahi, ya akayi?" Aunty Aseeyah ta mata bayani, Labiba ta jajanta abun, Aunty Asiya tace "to yanzu dai k'ofar k'aura zamu yini, zuwa anjima InshaAllahu anyi gyaran. In kin tashi daga Makaranta ki wuce chan, yayanki yace zai gaya ma Mai Adaidaita sahun su Ameera da ya kaisu chan in sun tashi" Labiba tace "to shikenan Allah shi kyauta ya tsare".


Yara suka fara tafiya Makaranta, kafin Baban Amira ya fita Kasuwa, Aunty Aseeyah tace "karfe nawa kike da lectures?" Labiba tace "9 ne" "Ohh, na zata yanzu ne, bari na jiraki sai mu fita tare" Labiba tace "ki tafi kawai Aunty, in na gama sai na kulle Gidan ko?" sai da suka danyi mahawara kafin Aunty Aseeyah ta amince.


Itama 8 daidai ta shiga wanka, ta fito ta shirya cikin riga doguwar Riga Bak'a, Jan gyale medium ta sa ta yane kanta, ta kulle kofar Dakin, dama Aunty Asiya ta rufe Dakinta da Parlo da kitchen. K'ara saba jakkarta tayi ta yi hanyar fita, bata san dalilin juyawa ba, sai juyawa tayi ta hada Ido da k'ofar dakin da ke kallonta na Gidan Alhaji Zaki, kuma tana da tabbacin daya daga Ciki na DanMakaho ne,


Kila ko Sallahr Asuba beyi ba cewar zuciyarta, har tayi gaba, zuciyarta ta tunzurata da ta je ta kwankwasa mai, ya tashi yayi Sallah, samun kanta tayi da bin umurnin Zuciyarta, tsallake rusassun bulo din ta dinga yi har sai da ta dangana da Gidan Alh Ali Zaki, amsa kuwar zuciyarta take yi , duk da faduwan gaban da take jin zuciyarta nayi, bata fasa tafiya ba
har ta k'arasa gaban k'ofar dakin.


K'wank'wasawa tayi amma ba amsa, Zuciyarta na harbi da sauri sauri, gabanta na tsananta faduwa, ta lek'a ta window, kwance ta ganshi ruf da ciki.
Sake k'wankwasawa tayi, tare da murda handle din k'ofar.
"A bude take, k'ofar a bude take, ki shiga ki tadashi yayi Sallah" cewar Zuciyarta
Girgiza kai tayi tare da runste ido, amma zuciyarta na sake tunzurata.


Ki kiyaye mutuncinki Labiba, ki tsare mutuncinki, a kullum maganar Maminta kenan a duk lokacin da sukayi waya.


Ta san abunda take shirin yi is wrong, babu Macen arzik'in da zatayi hakan, ba Macen da zata shiga dakin Namiji Baligi ba Muharamminta ba, duk abunda ya faru da ita, ita ta jawa kanta, ita ta kai kanta, ko dakin Yayyinta Mahaifinta ya masu iyaka da shiga sashensu, balle wannan da ba zatayi shaidarshi a kan komai ba, bata san menene ke sa tana biyewa zuciyarta a 'yan kwanakin nan, ba halinta bane, amma bata san yanda zata tsayar da abun ba,


Bude k'ofar tayi tare da sa Kanta, tattaro Natsuwarta tayi kafin ta bubbuga kan Katifar da yake kwance tace "DAN MAKAHO"


Firgigit ya tashi, k'anannen idonshi ya dago ya kalleta da mamaki, kafin ya mik'e tsaye kyam yana binta da wani irin kallo, cikin Labiba ya bada k'ulululu, ta zabure zata ruga a guje, da sauri ya sha gabanta fuska daure yace "Ina kuma Zaki?".


Yayyyyyy people, Labiba ta kawo kanta fa.. Ba shi ya kirata ba, ita ta kawo kanta
Yau Mankas zai Angwance Rengyem
Me kuke tunanin zai faru?
Drop your thoughts here


Biko Vote Vote and Vote.


#1love
#DM
#SonSoFWA
#anatare
#nagode


Biebee Isa.
[14/03 9:35 pm] Biebie: Babi na Shidda (WACECE KE?)


Vote before reading please don ku kai karshe kun manta da wani zancen voting, just vote now. Thanks


"Saurin me kikeyi? Ina zaki ba wurina kika zo ba? To ina kuma Zaki? Ba so kike ki san ko ni waye ba, to yau ko zaki sanni, ba ke 'yar iska ba, kin san yanda ake zuwa dakin Namiji ko? Aiko zaki gaya musu, kwanta dan ubanki, yau sai na miki lagalaga" ya fada yana me yunk'urin tu6e riga don ya tsorata ta.
Runtse ido tayi cike da kidima, hawayenta su ka soma kwaranyowa, tana girgiza kai da k'yar ta lalubo kalmomin nan "ni Sallah na zo tadaka kayi, kuma wallahi ni ba 'yar iska bace".


Hanayenshi ya rungume a k'irjinshi, yana kallon yanda take rantsuwan ita ba 'yariska bace, iyakar gaskiyarta ya gano, daurewa yayi yace "yanzu in zagi uwarki kiji haushi, ni yaro ne da zakizo tadani yin Sallah? Bude ido tayi a tsorace, bata son ganinshi ba riga, amma da rigarshi.


Baki na rawa tace jiya fa naga sai daga garin Allah ya waye ka hada Salloli har Maghrib da Isha'i, shine nayi zaton ko bakayi ba, shine nace barin zo na tadaka ,ko zan samu lada, in ba haka ba, ba abunda zai kawo ni nan, saboda na damu da kai, ina so mu tsira tare ranar gobe k'iyama".


Kallonta sosai yake yana nazarinta, daga bisani yace " kin damu dani? Ni k'anin uwarki ne ko na ubanki?".


Kai ta girgiza tace "Aa, kai ba daya daga cikinsu bane, k'annen Mahaifana ba haka suke ba, kuma na lura Zagi kamar a jininka yake, na san na maka shishigi, ina kan maka shishigi a rayuwarka, amma ina rok'onka, wannan ya zama karo na k'arshe da zaka Zageni, kar ka k'ara zagina DanMakaho, babu mai ganin Mutuncinka a duk Unguwar nan, ni kam Ina ganin mutuncinka, inshort ni kadai ke ganin mutuncinka, so be kamata ace kana danno min Ashar ba" ta fada cike da sanyi, murmushi be kauce daga fuskarta ba.


DanMakaho ya kalleta sosai, yana mamaki, be taba sanin a Arewacin Nigeria akwai Mata masu Confidence irinta ba, be taba sanin akwai Matan da zasu iya expressing kansu kamarta ba a Katsina ba, yana mamakinta sosai.


Kallo ya bita dashi a hankali yace "WACECE KE"


Ta amsa mai da "Labiba Ahmad".


Ya Girgiza kai yace " Aa, wacece ke, kamar yanda kike son sanin Ni wanene haka nake so ki sanar dani ke wacece, sai na san ko ke wacece kafin zan iya sanar da ke ko ni waye".


Murmushi tayi tace "Makaranta zanje, nidai kaje kayi Sallahr Asuba".


Jim ya danyi, yace "Nayi" ta kalleshi da alamun rashin yarda, yace "ke ni fa bana k'arya, ba Bango ya fadi ba?nagani da Asuba". Murmushi ta sakar mai tace " tabbas kayi Sallah, to ni na tafi School".


Bai ce da ita komai ba, ta raba shi ta wuce, har ta kai bakin k'ofan ta dakata, zuciyarta na kitsa mata da ta tsaya suyi magana, opportunity ne ta samu, k'ila daga yau ba zata sake samun irin damar nan ba.


Dakata wa tayi ta juyo gareshi tace "lets talk Dan Makaho".
Ya dan waigo yana mamakin rashin tafiyarta yace " lectures din fa?".


Wuri ta samu daga gefe ta zauna, ta dago ta kalleshi, ta sakar mishi da murmushi tace "We are going to have our lectures here".


Bata jira yace komai ba ta fara magana;


Alhaji Ahmad Dakata


Alhaji Ahmad Dakata dan asalin k'asar Nijar ne, Maraya ne, baya da kowa, ya zo ya fara 'yan bugabuganshi a Garin Katsina, da yake yana kaifin basira da fasaha, nan ya fara shigeshige yana samun k'anannun kwangiloli.


Baiwa gareshi, yana da Ilimin Hak'a Rijiya da gina mugudanun ruwa, da ilimin Quantity surveyor amma be taba shiga Aji ba ma'ana beyi karatu ba, a shekaru da yawa a baya saboda kwarewarshi ya sa ake daukan shi gari gari don yin Aiki,


Da ya dan samu kudi yake zuwa Maradi gurin Tsohon da ya tashi a gidansa, a nan ne aka aura mishi Wata buzuwa Zaharau, marainiya ce itama, ya taho da ita Katsina.


Da Likafa ta cigaba mai, a ka dinga fita dashi garuruwa don yin kwangilar Tituna da Hak'on rijiyoyi, da janyo ruwa daga wani kauye zuwa babban Birni.
Babban kwangila ta sameshi inda zaiyi aikin kusan Shekara a Garin Edo Benin City da Zara'u ya tafi, lokacin tana da jaririn ciki, nan ya dan kama musu dan karamin Gida, ya hau aikinshi. Ganin aikinshi ba ha'inci, ya sa shi kafin ya gama wannan aikin ya samu wani aikin, haka zaman Edo ya kamashi, sai ya zama ya fara jin dadin Edo fiye da duk wani garin da yake zuwa, a nan ya kafa Iyalinshi.


Alhaji Ahmad Dakata Yana da Mata Biyu, Hajia Zahara'u, da Hajiya Jamila wacce ya aura bayan dawowanshi Edo kwatakwata, ko wacce da iya adaddin yaranta don Haihuwa suke MashaAllah.
Hajiya Zaharau itace UwarGida ta haifi yara Sha daya amma Uku ke da rai Mata 2 namiji daya , Yaya Muhammadu, Yaya Hajara, sai Auta Labiba daga kanta Mami kamar yanda suke ce ma Mahaifiyarsu bata sake haihuwa ba.
Hajiya Jamila itace Amaryar Alhaji Ahmad, Yaranta 7, 3Maza Yaya Aminu, Yaya Muntari, Mata Yaya Salisu, Yaya Fadime, Yaya Zaliha itace tsarar Yaya Hajara, sai Samira tsarar Labiba duk da ta girmi Labiba da 'yan watanni sai Auta Halisa.


Gidan Alhaji Ahmad kamar yawancin Gidaje ne Masu mata biyu maana mai Kishiyoyi, akwai kishi tsakaninsu, sa'anan akwai 'yanubancin.
Alhaji Ahmad yana tsayawa tsayin daka akan hade kawunan iyalanshi, amma abun da kamar wuya, a cikin kaso Dari, suna zaman lafiya kashi Tamannin, amma dai ana iya cewa na ciki na ciki, akwai ganin k'yashi da hassada musamman wanda 'yan wannan dakin ke ma wanchan.


Muhammad da Aminu suna da Shekaru 18 aka haifi Samira ba da dadewa ba aka haifi Labiba.
Sun taso kamar 'yan biyu, amma Labiba ta faye wayau, ganin tana da Wayau sosai, ga Shegen tambaya Muhammadu yayanta ya kwadaitu da son autar mamanshi ta shiga boko, don ba zai bari Babansu ya ma yarinya mai saurin daukan abu kamar Labiba abunda ya musu ba.


Alhaji Ahmad Dakata be damu da sanya yara a Makarantar Boko ba yana dai sanya su a Islamiya, in Namiji ne in ya kai shekara 10 yake fita dashi wurin aiki ya koya musu Aikinshi, in kuma Mace ce, da kin samu Miji zai maki aure, .


Daga Samira sai Labiba da Auta Halisa ne kawai basuyi aure ba, yawanci ba Hausawa suke aure ba, amma Maza kuwa daga Yaya Muhammad da Yaya Aminu wanda ke zaune cikin Gidan Alhaji Ahmad Dakata da matarshi.
%%%%%%


Da yaje wurin Baban da bukatar sanya kanannun yaran Makaranta, Baban fir yak'i, bayan Muhammadu ya kwantar da kai ya ma Baban bayani sosai kan Muhimmancin Karatu musamman ga 'ya Mace, sai suka tafka muhawara, daga k'arshe Baban ya amince. Aka sanye Labiba da Samira wani Private school.


Samira bata da passion din karatu, Labiba kuwa tana son k'aratu sosai, har suka gama Primary School. A lokacin ne Zamani ya fara dakushe tauraron Alhaji Ahmad Dakata, sai ya rage samun Kwangiloli, a nan ya Umurci yaranshi da su fita su samu Aikin hannun da zai ma kowannensu, ko wanne ya kama gabanshi, Muhammadu ne yayi Arewa a garin Katsina, yanemi izinin Babanshi da ya bashi hayar Gidan da yake Katsina zai zauna Baban yace yaje dai ya zauna in ya mutu a sa Gidan a Gado. hakan kuwa akayi amma hakan ya taba zuciyar yan uba. Muhammad ya tafi katsina da ya fara 'yan bugabuga, ko shekara baayi ba da zamanshi Katsina, ya samu mata ya aura a Katsina, har Allah ya sa mishi Albarka a kasuwancinshi ya bude dan madaidaicin Provision store a Kasuwa.


Samira ta tsani karatu, daga JSCE tayi ta zillewa bata son karatun, Mamanta ta biye mata, shi kuma Alhaji Dakata tunda be da damuwa kan Karatun boko, be matsa mata ba.
Amma Labiba ta dage da bada himma a karatunta ta shiga Senior Secondary School. Labiba ta ke kutsawa cikin 'Yayan kudun nan ta dau ilimi, bata fiye k'awaye Mata ba saboda gulma da fada, yawancin abokanta Maza ne kuma Kiristoci, don Musulmai basu fiye yawa ba, a nan ne ta koyi tambaya akan komai, ta iya mu'amala da kowa, tun tana primary ake fita Debate da ita, bata jin komai Magana gaban dubannin mutane, ba kuma ta kunyar tambaya.


Labiba tafi so ta sanya dogon Wando budadde, da rigar da ta wuce mazaunanta, tana da burin zaman Injiniya saboda duk abokanta Maza da tunanin zama Engineer suka tashi, duk tunanint irin na Maza ne amma ko so daya bata taba tunanin kwace hanyarta ba, tana da ilimin addini, bata wuce gona da iri ta fanin nan, ko hannu namiji ya bata sai ta galla mishi harara.


Wayon Labiba ya girmi shekarunta, shiyasa take samun laifi da Mama kamar yanda suke cema Mamansu Samira, Mama tana son lak'afa mata sharri, ita kuma in ta san batayi abu ba, ba zata taba amincewa ba, ko me zaa mata.


A lokacin da ta gama Secondary School Samari suka mata chaaa, ba sa gabanta, in sun zo zata fita ta sha hira dasu, amma kar take gaya musu ba wanda zata aura cikinsu, burinta dai tayi karatu ta zama Injiniya, in har suna sonta su jirata in ta zama Injiniya zata dawo, sai ko wannensu ya gwada bajintarshi, a hakan ta samu suke shafa mata lafia .


Result sun fito, duk sunyi kyau, ta kira yayanta Muhammad ta na kuka sosai kamar ranta zai fita, ta nuna mai tana son cigabawa da Makaranta amma tasan Babansu ba zai taba bari ba. Yayan ya kwantar mata da hankali ya shaida mata zaizo k'arshen Wata..


Bata gaya ma kowa ba burin son cigabawa da karatu, harta Maminta bata sani ba, sai da Yaya Muhammad yazo da Iyalanshi, Aunty Asiya da Ameera da Sabit, murna wurin su baa magana don sai sufi shekara 3 ba suzo Edo ba sai dai waya,


Aunty Asiya na san Mami don bata surukkuta da ita, tana son k'annen Mijinta, Labiban ma na sonta, da ta shiga gaida Mama, a dage ta amsa, gani take kamae Muhammad yafi yaranta kudi da arziki.
A lokacin da Muhammad ya shiga da bukatar son Labiba ta cigaba da karatu, ran Baban ya baci, yace shi aure zai musu karatun da tayi a baya Allah ya amfana. A nan ma wata Muhawarar suka sake tafkawa amma Baban yace shi sam Diyarshi ba zatayi Jami'ar Edo ba, ba zatayi karatun gaba da Secondary cikin Arna ba, muma shi tsakani ga Allah aure yake son musu, ya lura kan Labiba na rawa, wai rannan nan har tistitsiyeshi tayi da tambaya don me be sa sauran yaranshi Makaranta ba.


Muhammad dariya yayi, yace in zai yarda zai tafi da ita Katsina ya sanyata a Polytechnic, kuma ya mishi Alkawari da ta samu Miji, zai dawo da ita a mata Aure da k'yar Baban ya yarda, tara su yayi gabaki daya ya shaida musu hukuncin da ya yanke, nan Mama ta fara jin zafi, tace "Haba Alhaji, anya kuwa? Duk cikin 'ya'yanka, Maza da Mata, ba wanda ya taba karatu sai Labiba yanzu kuma kace zaka kaita wani gari tayi karatun Jami'ah? Ina guje maka dana sani Alhaji, Wallahi AbdulFatah ya nuna ya na sonta, gwara ka mata aure".


Labiba tace "Allah ya sauwak'e in auri mai shan taba, ki aura mishi Samira" Mami ta wurgeta da harara, Samira tace "Kinga Labiba Mama na ba tsaranki bane, wallahi ki daina maida mata magana in tayi" Alhaji Dakata yace "to nidai na amince Muhammad ka tafi da Labiba, amma idan Labiba ta kwaso abun kunya, ko tayi wani abun da zai kunyatani a idanun jama'a, to ba ruwana da kai da ita da Mahaifiyarku" Mami ta kalleshi cikin tashin hankali, Labiba kuwa ko a jikinta dom ta san ba zata taba basu kunya ba, dadi ya rufeta tace "Niko wallahi sai na baka Mamaki Abbah, zan zama abun alfaharinku, da Allah, ba zakayi dana sani ba, Mami karki damu, wallahi karatu kawai zani Katsina, sai na kula muku da jikokinku" wasu sukayi dariya wasu ko sukayi fuska.


Hakan kuwa akayi, Muhammad ya koma Katsina ya mata Appying HUK poly, don bin sharrudan uban, tunda Diploma Shekara 2ce, kuma akwai sharadin in ta samu Miji za tayi aure. Labiba na daga cikin wanda aka dauka da farko, saboda ko Jamb dinta Mark din yan jami'ah ne, ya gama mata preparation nan da wata biyu zata zo katsina fara lectures.


Abbansu ya kirata daki, ya mata nasiha sosai, ya bata kudi Naira dubu ashirin yace kuma InshaAllahu zai dinga turo mata ko da dubu uku ne duk wata, godia tayi sosai, ta rungume Abbanta.
Maminta ta ki rata daki tace "Na zauna a Katsina shekaru da yawa, na san yanda suke, yanda suke ma'amala da mutane ya sha bamban da yanda mukeyi a nan, baki taba barin Edo ba, Arewa zaki Labiba, dole ki koma halaiyar 'yan Arewa, kije kasuwa ki dinko atamfa da ankara, ki dinga shigan Hausawan usul, ba zasu miki uzurin ba a chan kika taso ba, zasu miki fassara in kikayi wani dabi'ar da ba tasu ba, ke ke son Karatu, dole ki zama irinsu ba zan so ki fito da wani penti duk kankantashi ba, kingane? Labiba ta gyada kai, Mahaifiyarta ta dade ta na mata nasiha kan kare Mutuncinta.


Tana son karatu, tana son fidda mahaifiyarta kunya, zatayi komai don ganin ta cimma burinta, ta shiga kasuwa ta siyo manyan gyaluluwa da atamfofi, ta dinka su. Lokacin zuwa Katsina Yaya Muhammad ya zo da kanshi don tafiya da ita, kowa na alhinin tafiyar Labiba, don tana da shiga rai, harta Samira da ba sa shiri tayi kukan rabuwa da ita, haka suka ma Edo Sallam suka taho Katsina ta dikko dakin Kara.


Gidan Yaya Muhammad dakuna biyu ne sai Parlo, da kitchen da toilet a waje, k'aramin Gida ne, Dakinta Aunty Asiya ta bar mata da Amira babban diyan Yaya Muhammad, ita kuma Aunty Asiya da Sabit suka koma dakin Yaya Muhammad.


Yaya Muhammad ya raka Labiba Registeration ba wai don ya san yanda ake ba, Sati guda ya kashe yana kaita Makaranta, ta hanyar bin School Bus, ya kuma koma ya daukota, ce mishi tayi ya bari hakan nan, ta gane hanya, zata iya zuwa ta dawo da kanta, a sati na biyu ne ta fara zuwa da kanta a lokacin har tayi k'awa Aisha Usman.
Wannan kenan.


Zaid ya gama jinta lokacin da ta gama bashi tak'aiceccen labarinta da murmushi dauke a fuskanta, kallon da yake binta da shi ne ya sa tace "ya akayi ne?" mur Zaid ya sha "are you stupid?" kallon mamaki ta mai tace "me ya faru?".


Hannu ya sa ya murza idonshi "wai ke lafiyar ki lau? Alk'awarin da kika daukar ma Maminki kenan? Don me zaki shigo dakina? Kare mutuncin kenan? Kinsanni ne? Yanzu in na danne ki, na miki abunda ba kya zato, me zakice mata? Kin san me kikayi risking? Farincikin ki, na Yayanki, na Mahaifiyarki wanda barazana ne ga aurenta, to kinyi risking kin shigo dakina, for what? Is it worth it?".


Labiba tayi shiru "nasan ban yi daidai ba, but kamar yanda nace ma, wallahi kamar ana controlling dina, bansan meyasa when it comes to you, nake yin abubuwa da yawa, i am just curious, Ya Rabb, amma kasan me? Wallahi banyi dana sanin shigowa dakinka ba, bansanka ba, bansan what you are capable of ba, amma na san ka san abunda kayi, shi za'ayi ma, na san kana da k'anwa Sadiya, na san in ka shiga gonan da ba taka ba, itama zaa shiga tata, nasan ba zaka min abunda ka san ba zaka ji dadi ba in an mata ba, na san fandarewarka a busa ma ciki hayak'i ne, kuma ina da tabbacin kai ba mazinaci bane".


Idon ya sake murzawa ya kwantar da murya, kamar zaiyi kuka, damuwa taji a muryarshi yace"Labibaah, you cant be so sure, ba a gane daniska a fuska, baki san abun da wani zai miki ba, ba kowa ke da irin zuciyar da kike tunani ba, wasu suna da abun ban mamaki, baki gane bak'in halinsu, nidai please kar ki kara shiga dakin kowanne namiji, ina tsoron abunda wani zai miki".


Ido ta lumshe ta bude ta sakar mai murmushi, tana me jin dadin muryar nan, tace "ka damu dani?" hannu ya sa a cikin gashi kafin ya daure yace "ke dallah, tashi ki tafi School" raurau tayi kamar me shirin kuka, nifa ba inda zani, already an fito 1st lecture, kawai na baka labarina sai kuma kace zaka koreni, ai ba haka mukayi ba?".


Tsaye yayi yana kallonta, itama kallonshi takeyi, sun dau mintuna fiye da uku suna kallon kallo, ko wannensu fa da abinda yake sak'awa, Wayarta ne ya katse su.


Aisha ce, dauka tayi "Hello Aisha? Ya kike, eh wallahi Ruwan Jiya ya

Please Login or Register in order to submit comment