Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kije Maryama, ya na jiranki".
Mik'ewa tayi ta shiga kitchen don hado tray dama akwai Hijab cikinta straight parlon Yayanta tayi, tun daga k'ofar Parlon take jin wani daddan kamshi, nan gabanta ya shiga dukan uku-uku, kafanta yayi sanyi amma haka ta shiga da sallama, ganin mutumin da ke zaune ne ya sata karasawa cike da mamaki, amma sai ta dake ta fara mai murmushi.


Gaishe da shi tayi sosai da faraa a fuskarta, ya amsa shima cike da jin dadi, tambayar Hajiarsu tayi ya gaya mata tana Katsina lafia, shima tambayan mutanen gidan yayi ta amsa da Lafiyar kowa lau.
Shiru suka danyi kafin yace "Mancy"
Da sauri ta dago kai ta kalleshi cike da Mamaki, murmushi yayi yace "haka naji Zaid ya ce miki rannan a Gidan Sarki".
Sadda kanta tayi tana wani murmushi sakamakon irin kallon da Babban mutum kamar Alhaji Abu yake mata.


"Nasan zuciyarki na cike da tambayoyi kan me ya kawo ni ko? Ba tare da bata lokaci ba Mancy, so nake na shiga cikin jerin Zaurawanki don neman Aurenki, hak'ika bayan rabuwan mu na kamu da sonki duk da a farko tausayinki nakeyi amma daga baya na lura So ne, shiyasa ko da na ba Mamata labari ta karfafa min guiwa kan na nemeki".


Mancy tayi shiru ta cigaba da wasa da yatsunta.
"Uhmm?"
Ta dan dago tace "ni yanzu har wani aure zanyi? Ina da kamar Zaid? Sai dai in jira aurenshi".
Yayi yar daria yace "Shekararki nawa?"
Dan turo baki tayi tace "43" murmushi yayi yace "duka nawa kike? Ni ina da 65 shekarun babban Dana 32, amma bance na tsufa ba sai ke? Kuma ni fa ban ma yarda kin kai ko 25 ba".


Dariya ya sata sosai tace "Shekarun Zaid fa kenan".
Ji yayi ta sake burgeshi, har ranshi yake jinta cikin sanyin murya yace "Maryama, mu ba yara bane, bakiyi tsufa ba, koma kin tsufan nikam gani nakeyi kamar yar shekara 18 kike, ina so naji ta bakinki, in baki amince dani ba ba zan miki dole ba".


Shiru tayi ba tace komai ba
Ganin Shirun na neman yawa ne ya sashi cewa "ina iya baki Lokaci, kiyi shawara kiyi tunani, har zuwa jibi da nake shirin komawa Abuja".
Tace "to shikenan nagode".


Ba jimawa ya mata bankwana sukayi sallama ta shiga ciki ta ma Yayanta magana ya koma wurinshi ya rakashi har Gate ya sake jinjina mai dagaske yake sonta yake da Aure.


Da daddare ne Yaya Umar Ya kirata suka yi maganar Alhaji Abu Shamsu, Shawara ya bata a matsayinshi na Yayanta, yace "kar ta dakusar da kuruciyarta, kar ta manta Alhaji Ali saki Uku ya mata in ma tana tunanin koma mishi ne, tace "haba Yaya, tana sonshi amma wallahi ya fitar mata a rai, ba ta tunani ko aure ta sake ta fito zata iya sake aurenshi, ta hakura dashi" yace "to Ina ganin ya kamata kiyi tunani kan Alhaji Shamsu, ba zan miki dole ba, amma kar ki bari Alhaji Abu Shamsu ya subuce mata".
Godia tayi ta tashi ta koma dakinta.


Ta san ba zaiyiwu tayi ta zama a gidan Yayanta ba, duk da Uwa daya Uba days, yau da gobe sai Allah, Alhaji Abu baida wani aibu a zahiri, Zuciyarta tayi ta karanto mata shawarwari, har tayi naam da Alhaji Shamsu.
A ranar da zai tafi ya dawo, nan ta mishi Albishir da ta amshi bukatarshi, sosai ya nuna murnan shi, yace "zai basu Wata Biyu su Fahimci Juna, kuma ya na fatan suyi Bincikenshi kafin nan don da Wata biyu ya cika zasuyi Aure. Ita gani take kamar anyi gaggauwa amma shi cewa yake bata lokacin me zaayi.


Haka Alhaji Abu Shamsu yake zuwa Kano duk bayan Sati bibbiyu, har Mancy ta sake jiki suka shak'u sosai, suna fahimtar juna a lokaci daya kuma Yaya Umar na binciken Alhaji Abu Shamsu.


Wata rana suna tsakar Gida suna Zance kan Carpet, Alhaji Abu yake ce ma Mancy, in sunyi aure ta karbo su Zaid, Mancy tayi murmushi tace aa su yi zamansu a chan abunsu, yace "wai saboda me? Tace haba ina zani da manyan yara kamarsu? Dan shekara 25 da 'yar shekara 16?" Yace " to menene? Zan dauki nauyinsu, zan kula dasu a matsayin nawa" tace "aa Alhaji, ka barsu wallahi nagode sosai". Yace "to a dauko Macen" tace "aa ba wanda zaa dauko cikinsu, zasu dinga zuwa mana hutu". Ya juya kai cikin rashin jin dadi yace "to shikenan".


Ba su san shigowan mutum ba, sai dai suka ganshi tsaye kansu, hawaye ne ke kwaranyowa daga idanuwanshi, duk yayi bak'i ya rame ya jeme.


Da sauri Mancy ta mik'e zata rik'oshi yayi saurin yin baya kamar wanda wuta zai taba.
Alhaji yace "lafiya wanene ne wannan?"
Baki na rawa Mancy tace "ZAID".


Alhaji da faraa yace "Mallam Zaid muna lafia?".
Ba tare da yace ma kowa komai ba ya juya zai fita daga Gidan.
Mancy ta bi bayanshi tana kwala mai kira amma yak'i tsayawa.
Murya a kausashe tace
Zaid Aliyu Zaki kar ka sake ka fita daga gidan nan.


Chak ya tsaya. Ta taka har gabanshi ta tsaya tana kare mai kallo, idanuwanta suka ciko da hawaye amma sai ta dake, hannu ya sa zai murza idonshi ta rike hannunv.
"Baka ganni da bako bane Zaid?".
Juyawa yayi ya karasa inda Alhaji Abu ke tsaye yace "Ina Wuni?".


Alhaji Abu Shamsu ya amsa da Fara'arsa. Zaid ya juya ya kalli Mancy kafin ya dawo da dubanshi wurin Alhaji Abu yace "Daddy, ka aureta ka tafi damu Gidanka DonAllah".
ZAID mancy ta fada a kausashe.


Alhaji Abu yace "zan so hakan Zaid, zan so na hadaku da nawa 'yayan, kuma 'yayane, InshaAllah zan ga hakan ya faru".
Mancy tace "to lallai ka manta da maganar Aurenmu, na fasa ba zanyi ba kuma".


Alhaji Abu ya rikide yace "haba Maryama mai yayi zafi? Kiyi hakuri, dama ai sai da amincewarki zan daukesu, kiyi hakuri, ni niyyata masu kyau ne". Da sauri tace "Allah ya baka ladan Niyya, amma zasu tsaya Gidan ubansu" "Faqat".


Wani murmushin takaici Zaid yayi yace "Mancy, kina son mu kuwa? Mancy? Wace irin Uwa ce zata dafkar da Yaranta kamar wasu kayan wanki, ta tsallakesu ta yi tafiyarta, ta k'i waiwayonsu, ta ki nemansu? Ko sun nemeta ta guje musu? Mai muka miki? Ko mai na miki? Mai dalo ta miki? Eh Mancy?"


"ZAID mu shiga ciki mu gaisa ya kake?" Ta na mai nuni da Alhaji Abu da ke tsaye da Ido.


Bai damu da ba su kadai bane ba, yace "Mancy,kika tafi kika barmu, bai isheki ba, kika kashe wayarki baki neme mu ba, Mancy Mu kira Baba Umar, ko su Walid da Ummi, su baki wayar ki kashe ki ce zaki neme mu, baki taba neman mu ba? And now zaki ce min Ya nake? Really Mancy? Ya nake? Do i look alright to you? Bakiga nayi bak'i na rame ba? Bakiga na k'azance ba? To na ma fi kyan gani kan Dalo, ita in kika ganta so daya ba zaki so sake daga ido ki kalleta ba, saboda rama".


"Mancy Gidan Ubanmun da kike ta ik'irari bamu da wani gata ko galihu, Idi yafi mu matsayi a Gidan, Mancy ba wahalar rayuwar da ba ma gani, ba kallar Sharri da kazafin da baa mana, Mancy me muke ci a Gidan Uban da ba zaki bari a dauke mu ba, nan Kano zanzo sai da naci bashin Naira dubu daya wurin Eskaley, Mancy kamar ni yau ni ke ci bashi? Huh. DonAllah ki firda mu daga wannan k'angin, ki tafi damu duk inda zaki, Babanmu ba sonmu yake ba ba zai damu da duk inda zamuje ba, bai k'i mu shiga dunia ba, think of our Future wanda nawa ya fara rugujewa, da kanshi wanda kike son Aura ya miki tayin daukar mu amma kin hana, wai saboda me? Anjima sai kice kina Sonmu, kalar soyayyar taki kenan?".


Ganin yana magana ba tare da ya tuna wa yake ma magana ba ya sa ta daga hannu ta mareshi.
Dakata wa yayi tare da matse kuncinshi.
"Har Gobe, har abada ni Mahaifiyarka ce, ka san yanda zakayi man Magana". Kai ya sadda k'asa yace "kiyi Hakuri Mancy, ki yafe min, amma DonAllah ki tafi damu".


Alhaji Abu yayi tunanin tafia ya barsu don yana ganin kamar zasu zo su kebe, yayi hanyar Fita da sauri Mancy ta dakatar dashi ta hanyar cewa "dakata Alhaji, donAllah ka dawo, akwai abunda nikeso dukanku ku fahimta, mu zauna".
Alhaji ya dawo ya zauna
Shima Zaid din Zama yayi a bakin Carpet.


Mancy ta fara "Alhaji Nagode kwarai da kala Soyayyar da kake nuna min, na san Son da kake min ne ya shafi Yarana, nagode kwarai amma donAllah indai bani nace maka ina so ka taimaka ma Yarana ba kar kayi komai". Alhaji yayi mamakin Mancy Sosai, shakka babu bata da kwadayin abun dunia.


Ta kalli Zaid tace "Zaidun Babanshi, Mancy bata kyauta ba da bata nemeku ba, Mancy tayi laifi ku yafe mata kaji?" Kauda kai yayi yana son murza idonshi ta rik'o hannun tace "Haba DanMakaho na" murmushi ya subuce mishi don Mancy ba ta kiranshi da sunan sam sai in tana son sa shi daria.


Tace "to ka fahimceni, wallahi duk runtsi duk wuya baku da Gidan da ya wuce na Mahaifinku, kun fiso na tafi da ku Agolanci? Kama san meye hakan? Kana da Shekara 25 kake so ka bar Gidan Ubanka ka koma Gidan Mijin Mamarka? Haba Zaid kayi tunani mana, ban yi hakan ba don bana sonku, na yi hakan ne don na kwatar muku yancinku, ku zauna Gidanku, ku ma Mahaifinku Biyayya, ku maido da sonku zuciyarshi, ku samu albarkarshi".


Murmushi Zaid yayi yace "Ya riga da ya Tsine min, ta sa ya tsine min Mancy". Ba ta san lokacin da ta fashe da Kuka ba. Ganin haka Alhaji Abu yayi saurin Mik'ewa ya zaro kudi a Aljihu wanda zasu kai dubu 20 ya damk'a ma Zaid a hannu yace "barin tafi Zaid, kangaida Dalo, ku cigaba da Addua, Allah baya bacci". Yayi Gaba Zaid ya mik'e ya bishi a baya, Mancy kam bata yi yumkurin mikewa ba.


Sosai Zaid ya ma Alhaji Abu Godia, ya rakashi har Mota kafin ya dawo Gun Mancy dake durkushe a gurin, Zaid ya cigaba da bata labarin tun bayan rabuwar su zuwa yau da ya yanke hukuncin biyo Mancy. Sosai take Kuka kafin ta share hawayenta, Zaid ya yi zaton ta janye qudurinta amma da yaji tace "Allah ba ya bacci, ku cigaba da hakuri, gaskia zatayi halinta, kuma in dai ba saba mishi kayi ko addininka ba, to bakinshi ba zai bika ba, ba zai kamaka ba" ya gane cewa tana kan bakanta.


"Mancy ya maida tsine min fa kamar wak'a ko karatu, wata rana ko zai kamani". Mancy tace "Allah yana tare da ku Zaidu" sanin Mancy yar magana daya ce ya sashi mik'ewa don shiga ciki, ya san Magiyarshi da duk abunda zaiyi ba zai chanza mata raayinta ba, Mancy kaifi daya ce, ajiye mata kudin da Alhaji Shamsu ya bashi yayi, riko hannunshi tayi ta bashi kudin, tace na kune, ni banda kudin da zan baku da na k'ara maku, muje ka ci Abinci ka koma Katsina".


Murmushin takaici Zaid yayi yace "ba ma zan kwana ba?" Ta gyada kai tace "eh ba zaka kwana ba".


Mai makon yaji haushinta sai cewa yayi "Ya Rabb" zuwa yayi ya rungumeta sosai yace "nayi Kewanki da Yawa Mancy, ki kunna wayarki ki kira Dalo donAllah". Kai ta gyada mishi ya shiga ciki gurin Danginshi, sun ko ji dadin ganinshi sukayi ta rungumeshi suna fira, Ya gaida Kawunshi da Matarshi, Walid ya jashi zuwa Dakinsu, Ummi ta zubo mai Abinci, yayi Sallah Asahar da Laasar kafin ya mike don haraman tafiya, Walid ne ya fito don saukeshi a tasha, yaso sake kebewa da Mancy amma tak'i yarda. Haka ya musu Sallama Walid ya daukeshi zuwa Tasha.


Sai Gab da Isha'i Zaid ya isa Katsina, tun a hanya yace yau shagali zaiyi shi da kanwarshi, daga tasha ya wuce Chimex don siya musu Shawarma, ya tsaya a Mansho Suya ya siya Gassashen Kaza, ya siya musu Lemu da ruwa, kafin ya tsaya a Wani Shago ya siya ma Dalo Chocholates kafin ya hau Machine ya wuce Gida, sai da ya tsaya ya biya Eskaley dubu dayanshi kafin ya karbi World na dubu biyu, ya dan zuk'a kafin ya wuce Gida.


Yana Shiga Gida ya hau kwala ma Dalo Kira, babban parlo ya shiga ya gansu gabaki daya banda Dalo, hanyar Dakinta yayi yana kiranta da k'arfi, fitowa tayi da murna ta rungumeshi cike da jin Dadi "Ya Zaid ashe gun Mancy kaje baka tafi dani ba? Ya Zaid nayi waya da Mancy na, Mancy na ta kirani" Zuba musu ido yan Parlorn Sukayi, Shafaatu bakinciki kamar ya kasheta, wannan farincikin da sukeyi ya fi daga mata hankali, bata so ta ga ko da hakori daya ne ya fito da sunan daria, ranta ya baci.


Kasa hakuri tayi tace "DanMakaho tafiya kayi? Wa ka gaya ma zakayi tafiya?" Kallonta DanMakaho yayi yace "Kar naje gun Uwata? Sai na nemi izini? Kin yi kadan na nemi izininki" ya kalli Dalo da ta ki bari ranta ya baci yace "muje daki Dalo, muje kiga abunda na siyo miki" tsalle ta daka tace "Allah Ya Zaid naji dadi ko ba ka siyo min komai ba, da Mancy na nayi waya, kuma tace za mu dinga waya kullum" daria yayi wanda ya kara bak'anta ran Shafa, yace "muje Daki kar su huce.


Binshi Dalo tayi sai ji sukayi tace "ina zaki da daren nan? Dakin Yayanki? Ke karuwa ce zaki bi namiji dakinshi?" Zaid ya mika mata ledojin yace jeki gani nan zuwa ta bi umurnin Yayanta. Zaid ya taka har Parlo inda suke tsaye yace "Uwarki Ce Karuwa"
Hudu ya taho Zaid yace "kar ka soma, Agolan banza, ka san kayi gigin wani Abu bugun burauba zan maka yanzu".
Ya kalli Annah, yace "kinyi Asarar Uwa, Agola".


Ya kalli Shafa da take tsaye kamar an disata yace "Ni da Dalo muna nan zama daram a Gidan Ubanmu, baki isa ki koramu ba, ba ki isa ba wallahi, ko me zakiyi kiyi, ko me zaki sa ya mana ki sashi, amma baki isa ki sa ya koremu ba don ba inda zamu wallahi, in kinga mun bar Gidan nan, to Aure mukayi".


Ya juya yayi tafiyarshi, sai huci rai bace tace "bari Ubanka ya dawo" daga bakin kofa ya dakata yace "sai dai shi da kika raina, kar ki fasa hada mu da Mahaifinmu nikuma ba zan fasa miki duka ba, kinga ba wani abu bane don DanMiji ya bigeki" ya sa kai ya fice.


Wani ihun Bakinciki Shafa ta sake, Hudu da Annah sukayi kanta, bangaje su tayi ta wuce daki ta rufe.


DanMakaho Ya iske dalo a daki har ta fara cin shawarmanta dadi kamar ya kasheta.
"Yaya nagode nagode this is the happiest day of ny life tun bayan tafiyar Mancy".
Daukan shawarman yayi shima ya zauna yace "Nasani Dalo, i know".


Alhaji Abu Shamsu ya isa Gidanshi da Dare, yau ne yayi shirin gaya ma Uwargidanshi Hajia Lubabatu da Iyalanshu batun Aurenshi wanda zaizo a sati 3 masu zuwa.
Da Sallama ya Shiga Parlon Inda suke jiranshi gabaki daya.
Hajia Luba da Yaranta biyu Abdulhafeez da AbdulMajeed suna sanye cikin shiga ta alfarma.
Sannu da zuwa suka mishi gabaki daya, ya amsa da fara'arshi.
Direct Dinning Area suka wuce don yin Dinner.


Suna ci suna sha suna fira cikin jin dadi da soyayyar junansu. Alhaji yace "nikam Abdulhafiz ina Ummita ne? Kazo kana cinye min abincin gida" daria sukayi gabaki daya yace "Abba ta tafi Biki Kaduna sai ranar Lahadi zata dawo" Hajia tace "Ai Gauro ne bai da mata" suka sake daria.


AbdulMajeed yace "Abba da kaje Katsina ka ga Aisha?" Abba ya kurba ruwa yace "na ganta wai har ta kai SS2, ikonAllah yara suna ta girma". Umma tace "amma ka dai san dalilin da yasa Majeed ya tambayeka ko ka ga Aisha ko?" Majeed ya fara shurin Umma da kafa kan tayi shiru ta fara Dariya tace "to ba zan fada ba" Abdulhafiz yace "ni zan gaya ma Abba in ke baki gaya mishi ba".


Abba yayi daria yace "na san Zancen, ai sai ta gama Secondary zamuje ayi magana". Shidai Abdulmajeed kunya ya kama shi. Suka cigaba da cin Abinci kafin suka gama, suna niyan tashi ne Abba ya dakatar da ita, ta zauna su kuma suka wuce parlo.


Ya kalli Ummar yace "Hajia Luba, akwai abunda nake so na gaya miki".
Ta tattaro nutsuwanta ta bashi, "Hajia Luba, kin tuna Maryama wacce na baki labari? Da muka zo Abuja da Hajia?" Kai ta gyada tace "eh naganeta wanda Mijinta ya saketa ko" Alhaji Abu ya gyada kai sannan yayi dan Jim, kafin yace "So nike na Aureta".
Dimmm taji kafin ta dafe kirjinta tace "Aure kuma Alhaji? Wani irin Aure?" Yace "afuwan, donAllah kar ki daga hankalinki".


Nifa bangane ba, a kan wani dalili zakayi aure? In tausayinta kakeji ka bata jari mana, ba sai ka aureta ba, baka sakr aure tun kuruciyarka ba sai yanzu? Haba Alhaji".
Lallashinta ya fara yi, amma bata tausu ba ta cigaba da bude murya har sai da Abdulhafiz da Abdulmajeed suka zo.


Abdulmajid yace "Abba meke faruwa?"
Kafin Alhaji Shamsu yayi magana Umma tayi karaf tace "Majeed ni Abbanku ke son tonawa asiri, wai aure zaiyi, yana da Yara kamarku wai zai sake aure, ko Autanshi Jawad na neman shekaru 25 shine yake son tona min asiri".


Duk da sun ji maganar wani iri amma ba su nuna ba AbdulMajeed ya karasa gunta ya dafa kafadarta yace "Umma donAllah kar ki tada hankalinki".


Cikin karaji tace "Aure fa zaiyi, mai na rageshi dashi?" Abdulhafiz yace "Haba Umma, menene haka kike shirin yi? Ba mu taba jin kanku ba, menene don Abba zai kara aure? Umma ba a kanki zai ajeta ba, Umma Abba ba zai ki yin adalci tsakaninku ba, in Abba yau ya kawo wacce zata raina ki, kinsan mu Yaranki ba zamu yarda ba, donAllah ki kwantar da hankalinki, kiyi fatan a kawo maki ta gari wacce zaku zauna ku sake kwantar ma mahaifinmu da hankali" Abdulhafiz ya kalli Abbansu yace "donAllah Abba in wacce kake son aura zatazo ta tarwatsa maka farincikin Gidanka ne DonAllah kayi watsi da lamarin, amma in har zata kwantar maka da hankali ta k'i tada hankalin Mahaifiyarmu to Allah ya kawota Lafiya".


Fuuu Hajia Luba ta wuce daki, Da sauri Alhaji Abu yace "wallahi Maryama ba ta daga cikin Mataye masu tarwatsa farinciki Gida, in kuka ji labarinta zaku tausaya mata kuma zaku so ta kasance Aunty a gareku".
Abdulmajeed yace "In har ba zata daga Ma Mahaifiyarmu hankali ba to kana da goyon bayanmu Abbanmu, zamu tayaka shawo kan Ummanmu".


Hadesu yayi ya rungume yana sanya musu Albarka, Madallah da yara masu hangen nesa.


Da ban baki da Nasiha suka shawo kan Hajia, aka dai samu ta sauko daa fushin da tayi da Abbansu.
Biki ya matso aka sake gyara Gidan aka ware mata dakuna Biyu a cikin Gidan.


Zaid da Dalo kullum sai sunyi waya da Mancy, sun san zatayi aure, Mancy tace "suyi zamansu ba sai sunzo ba.


Haka aka daura Auren Maryama da Alhaji Abu bisa sadaki naira dubu 30 a nan kano, kamar auren Fari haka abokan Alh Abu suka zo.
Danginsu sunzo, Abdulhafiz da AbdulMajeed suka dauko Matar Babansu tun daga Kano har Abuja, ba ruwansu da taya Mamansu kishin haukan nan wanda yawancin mata keyi in aka ma Mahaifansu kishiya.


Nan aka danyi Walima wanda da shawararsu Majeed Hajia Luba ta hadashi. Dangin Maryama suka damk'a ma Hajia Luba Maryama, ba yabo ba fallasa sun karbi dangin Mancy, aka musu adduar zama lafia.
Da dare Alhaji Abu ya hada iyalanshi ya musu Nasiha ya musu fada ya masu fatan Allah ya hada kawunan su.
Abdulhafiz ma ya musu Nasihan zama lafia don kwanciyan hankalin Mahaifinsu, ya gargadesu kan su toshe kunnuwansu da ga jin tsegumin mutane.
**


Zama sukeyi da juna tsakani da Allah, ko wacce burinta ta burge Mijinta, Kishi irin na Yan Bariki sukeyi, Hajia Luba ta lura Mancy bata zo da raini ba, bata da matsala ko kadan, shiyasa ta kwantar da Hankalinta suke zamansu, Mancy ko ta na biye da ita, abunda yake dan sosa ran Hajia Luba shine yanda Abdulhafiz da AbdulMajeed ke son Mancy, komai Mancy Mancy, harta Matar Abdulhafiz ko ta zo Gidan da sun gaisa da Hajia Luba sai ta wuce dakin Mancy ta shantake, in Abdulhafiz yazo daukarta da ya shiga gun Mancy to fitowarshi ba lokacin ba sai sun sake bata lokaci, ta rasa mai suke cewa. Duk da ta san Mancy da son labari da jan fira shiyasa ta saye zuciyan kowa.


A duk lokuttan da suka shude tun bayan Sabon auren Mancy, ta kan tura ma su Zaid kudi duk wata, shiyasa ba ya rasa kudin zuk'an World.
Akwai wani Rana da Mancy ta aiko musu da kaya Shadda laces da atamfa kai harda provisions cike da Ghana Mustgo, Zaid yaje Tasha ya karbo, yana zuwa Gida ya kira Dalo ya na nuna mata Sak'on Mancy, kamar daga sama sai ga Alhaji Ali da Hajia Shafa.


Hajia Shafa tace "wannan kayan fa?" Banza Zaid yayi da ita ya cigaba da firdo da kayan ya na nuna ma Dalo, daka mishi tsawa Alhaji Ali yayi yace "bakaji ana magana ba? Wadannan kayan daga Gidan Uban wa suke?" Shiru yayi bai da niyyar amsawa.
Dalo tace "Mancy ta aiko mana dashi".
Sai da gabanshi ya fadi ya bi kayan da Ido. Hajia Shafa tace "ina ta samu kudin siyan wadannan kayayyakin tana zawarci?".
Dalo ta zuro baki tace "ta fa yi Aure".


Gaban Alhaji Zaki ya fadi da sauri yace "Maryamaa Tayi Aure?" Hajia Shafa da tsoronta kar ace Mancy Auren Kisan wuta ta yi don ta dawo dakinta, da sauri tace "to sai me in Auren tayi?" Nan ya fara "Sai me in Aure tayi? Ina abunda ya damemu da aurenta, zancen banza zancen hofi?".


Zaid tsaki yayi ya fara maida kayan cikin Ghana, Aunty Shafa tace "wai yanzu kai Alhaji ce mata sukayi kai baka daukar nauyinsu ne? Baka basu ci ba ka basu sha da zata aiko musu da provisions? Har da kayan sakawa, harta lipton don tonan asiri? Duk k'okarin da kakeyi a kansu ba sa gode ma ba sa godeAllah? Sai sun ce baka musu?" Ran Alhaji yayi dubu ya baci, yace "Allah ya tsine muku marasa gode Allah, duk abunda nike maku ba kwa gani?" To wallahi ba ku isa ku tona min Asiri ba, kamana ace ana turo da irin kayyayaki nan kamar na Mabuk'ata a gidana, ina Samson, kuzo ku k'onemin Kayayyakin nan".


Da Gudu Samson yazo don cika Umurnin Alhaji, Zaid yayi yunkurin hanawa amma Alhaji tuni ya fara tsinanshi, Dalo ta runtse Ido ta riko hannun Zaid, ta jashi baya, suna hange aka cinna ma Kayan Wuta.


Fargaban Hajia Shafa ace Mancy auren kisan wuta zatayi, ta samu Sarari ta kira Er Rabi ta gaya mata fa Mancy tayi aure a yi bincike a ga wata aure. Nan ErRabi ta kira Hajia Shfa tace "ke Maryama ta fi karfinmu don tana Auren Wani k'usa" nan kuma sai bak'inciki ya kaure.
**
Ran Mankas ya baci Ainun, amma Dalo ta taushe shi, ba su gaya ma Mancy ba, itama bata daina turo musu Sak'o in ta samu dama ba.
Ba da dadewa ba Mancy taje Dubai ita da Alhaji da Hajia Luba, ta musu Tsaraba, ta aiko musu dashi bayan dawowan su.
wani Jallabiya Dalo ta saka cikin tsaraban Dubai, Annah na ganin kayan taji Kayan sun mata kyau, cewa tayi ta je ta cire ta bata, dalo ta kalleta da mamaki, kafin ta bata amsa sai dai ji tayi Hajia Shafa tace "ina kika samo rigarnan? kije ki ciro ki bata kafin ranki ya baci, don munafunci ba Babanku ya hanaku karban abubuwa daga gurin Mahaifiyarku ba? Kije ki cire ki kawo ma Hannah ko yau Babanki ya tsine miki a karo na ba adadi. Jiki na rawa ta shiga ta ciro ta ba Annah, Annah ko ta fuzga taje ta chanza.


Annah ta ci kwalliya wai zata Gidansu kawarta, ta fita tana karairaya wurin inda ake prking Mota, kamar daga Sama sai ga Zaid, a Hak'e yake don yanzu ya zuk'i world yace "Ke wannan ba rigar Dalo bace? Tace "Aa" hr yayi gaba ya dawo baya yace "danubanki ba rigarta bace? Uwar wa ya siyo miki?

Please Login or Register in order to submit comment