Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mana gyara. Bangon Gidanmu ya fadi, shiyasa banzo ba, Ayyah Allah sarki, ya lectures? Ok to".


Ashe Aisha na tare da Abu Sadeeq, bashi wayar Aisha yayi suka gaisa ya mata jaje, ya shaida maya da yana missing Dimta, murmushi ta mishi kawai ta kashe wayar.


Har yanzu be fasa kallonta ba, wani kiran ya sake shigowa, kallon screen din wayar tayi taga Jay mamaki ta ba kanta da ta kasa daga wayar har wayar ta tsinke, don me zata k'i daukar wayar? ta tambayi kanta, kafin ta ba kanta amsa wayar ya sake ringing, sai ta daga ido a hankali ta kalli DanMakaho da sauri ta ajiye idonta k'asa tana wasa da hanayenta, wayar na kan Katifa tana ruri.


Wayar ta katse ta sake ruri, DanMakaho ya cire idonshi daga kanta, ya ga Jay a screen din, da kyar yace "Saurayinki na kira".


Da sauri ta daga kai ta kalleshi da kuma sauri ta sauke kanta kasa ta kawar da kai gefe, "Oh baki iya dauka a gabana?bari na fita" ta san in ya fita nan zai barta, ganinshi aiki ne tayi saurin cewa "aa, donAllah ka tsaya zan iya dauka".


Da sauri ta dauka "Hello Jay, zan kiraka, ina lectures ne" tayi saurin katse kiran, DanMakaho ya kalleta da mamaki.


Da murmushin mugunta yace "Lectures? Seriously? Wow, ashe kin iya k'arya" itama tayi mamakin k'aryan da ta sharara amma sai ta dake ta daure fuska tace "Ina Jinka, ka gaya min wanene kai?"


Wuri ya samu ya zauna daga gefe a sanyaye yace "Labarina bai da dadin ji" gyara zama tayi tace "zan iya saurarenka" yace "Labarina akwai tsawo" ta gyara zama tace "i have the whole day. (Ina da dukkan rana).


Murmushin takaici yayi
Yace "Sunana Zaid, Zaid Aliyu Zaki"


Da sauri tace "Meyasa ake ce maka DanMakaho? Meyasa ake kiranka da Mankas?"


A fusace yace "Zaki man shiru ko kuwa? in azarbabi zaki min tashi ki fita".


Hannu ta sa ta kama bakinta "Afuwan, nayi shiru".


A hankali ya soma Magana.
°°°°°°°
Wa zai iya mana hasashen Labarin Zaid?






Vote Vote Vote please.


#1love
#DM
#SonsoFWa
#anatare
#nagode


Biebee Isa
[14/03 9:35 pm] Biebie: Babi na Bakwai (ASALIN SU)


Alhaji Aliyu Umar Zaki tsohon dan Siyasa ne da yayi tashe a Da.
Yana da Shekaru 28 ya auri Shafa'atu 'yar mutanen Jos. Ya hadu da Shafa'atu ne lokacin da yaje Gaisuwar Mamar wani Abokinshi.


A GURGUJE


A lokacin, Mamar Shafa'atu na da Gidan Abinci, kafin Ali yaje Gidan Rasuwan ya fara zuwa Shagonsu Shafa'atu dake bakin hanya don cin Abinci.


Shafa'atu ce ta zo ta same shi, a natse ta gaishe shi ta tambayeshi abunda za'a kawo mishi, kallonta yayi yace "ki kawo min Shinkafa da Miya da Wake, sai kan Kifi" Shafa'atu ta dago ta kalleshi da mamaki tace "babu kan Kifi, saidai gangar Jiki da Bindi".


Ya dan tuburne fuska yace "ni kuma Kan Kifin nakeso" ta dan sa yatsar ta a baki tana nazari, su ba sa ba Customers kan kifi, amma wannan ya buk'aci da a bashi, tace "ka dan bani mintuna na soya maka" murmushi yayi don sosai 'yar budurwar ta burgeshi.


Bayan wasu 'yan mintuna ta dawo da abunda ya buk'ata, sosai ya ci Abincin nan, don ya sha tafiya, rabonshi da abinci tun kafin ya baro Katsina, sai ruwan da ya sha a Tasha, tambayar kudin Abincin yayi, tace mishi "kudinka naira dari da hamsin ne" cirowa yayi ya bata.


Ali sai ya manta da abunda ya kawo shi garin Jos, ya ja Shafa'atu da fira, haka ta biye mishi, da yaga Maghrib na neman yi baije yayi abunda ya kawo shi ba, ya ciro takardan da aka rubuta Adireshin Gidan Rasuwan, ya gwada mata "ko kin san Anguwar nan?" tace "eh ba nisa" nan ta sake mai kwatance.


Sallama sukayi tare da shaida mata zai dawo Gobe, murmushi suka sakar ma junansu, Ali ya tafi kwatancen da ta mishi da taimakon wani mai a kori kura ya gane Gidan. Sosai Abokinshi yaji dadin ganinshi, ya mishi godia sosai.


Washegari Ali ya koma Shagon su Shafa'atu, tun wurin k'arfe 10 na safe, dama da tunaninshi Shafa'atu ta kwana, taji dadin ganinshi yau, nan suka zauna suna ta fira, ba abunda ke tadata sai in Customers sunzo da ta basu abincinsu take dawo gurin Ali, Mamarta bata damu ba in dai kudi na shigo musu bata da matsala.


Maimakon kwana 1 da Ali yayi niyyan yi, sai gashi har kwana Uku be koma Katsina ba, duk da yayi Sallama da Abokinshi.
A cikin 'yan kwanakin nan Shak'uwa mai k'arfi ya shiga tsakanin Ali da Shafa'atu don Soyayya har ta shiga tsakaninsu kamar Almara.


Ranar da yace zai koma kar hankalin 'yan Gida ya tashi, Shafa'atu ta sha kuka sosai, a cewarta in ya tafi ba zai dawo ba, shi kuwa ya mata Alkawarin dawowa nan bada jimawa ba don zuciyarshi na wajenta a k'arshe ma ya tabbatar mata da cewa da labarin Aure zai dawo Mata.
Da wannan batu suka rabu Ali ya dawo Gida Katsina.


Ali ne Babba a Gidansu, yana da k'anne Maza da Mata.
Yayi karatun Arabi da Boko a Kano, be da wani aiki takamaime, amma yana da shige-shige da kutse-kutse, in yaje wuri sai ya tabbatar da an san shi a wajen kafin ya bar gurin, shiyasa abokan shi ke mai Inkiya da Ali Zaki ko suce Zaki kawai.


Tunda ya dawo Katsina yake ta tunanin Shafa'atu, hankalinshi dungurugum na gurinta, zuciyarshi na gaya mai ya koma Jos, nan ya bi zuciyarshi, ya sanar da Mahaifiyarshi zai koma Jos don ya samu Mata a chan, Mamarshi tayi mamaki sosai, amma sai tace "yanzu Ali duk Matan da ke garin nan da k'auyen garin nan basuyi maka ba sai ka dangana da Jos? Da dai ka bar maganar ta Jos ka zo ka bincika cikin Dangi, kasan Babanku dai" nan ya hau mata Magiyan donAllah ta goya mishi baya, zai samu amincewar Baban in har ta goya mishi baya, bayan ya dan sha wahala ya ci nasarar convicing dinta daga k'arshe.


Bayan 'yan kwanaki ya Koma Jos da Babanshi da k'anenshi sukaje ma Maman Shafa'atu da maganar Aure. Ta amince da hannu bibbiyu, Baban Shafaatu be da ta cewa don sai abun da Mamar tace, abu dai kamar wasa aka daura Auren Shafa'atu da Aliyu Zaki.


Bisa Alada aka rakota nan Gidansu Ali da ke Katsina inda a ka kaita dakin Ali.


Sosai Ali ke Son Shafa'atu, itama haka take sonshi, tana kyautata ma Mahaifiyanshi da k'anenshi, zaman lafiya sukeyi sosai.
Ali na dan fita yayi 'yan buga buganshi ya samu na cefane, ya kawo Gida a dafa kowa ya ci, zama suke na tsakani da Allah.


Bayan wasu yan Shekaru


Har Shafa'atu tayi shekara 3 a gidan bata taba ko da bari ba, wannan ya ja hankalin Dangin Mijinta gareta, abun ya soma damunta. Alin ne ke kwantar mata da hankali yana sake tunatar da ita kan Haihuwa ta Allah ce, yana ba wanda ya so a duk lokacin da ya so.


A lokacin ne Ali ya fara Shiga Siyasa, da yake yana da baki, ya iya magana sai hakan ke jawo mai Alheri daga Manyan 'yan siyasa, nan ya siya fili dan madaidaici ya fara gini, don su koma tare Matarsa duk don ya kwantar mata da hankali don ya lura rashin haihuwar nan, na damunta sosai.


Har wasu Shekarun suka k'ara shudewa, Shafa'atu bata yi ko da batan wata ba, abubuwa da yawa sun faru, Baban Ali ya rasu, duk nauyin Gidansu ya dawo kan Ali.


A Lokacin Ali ya shiga Siyasa tsundum don a yanzu ya wuce dan kwarako, a nan ta buk'aci da ya kaita Jos don a ganinta bata da Lafiya, ya kan ce mata "ta bar irin maganganun nan, don Haihuwa ta Allah ce, k'ila lokacin Haihuwar beyi ba" bata saurarenshi sai tayi ta kuka don danginshi sun sanga mata udo, habaibaici sukeyi mata, don Matan k'anenshi daga mai yara daya sai biyu, ita dai ya taimaka ya kaita ta samu magani".


Ba don ya so ba, ya kaita Jos da Motarshi, ya barota chan, nan Mamarta ta shiga dirka mata magungunan samun ciki.
Watanta daya a Jos Ali ya dawo daukarta don yayi kewar Matarshi sosai.
K'ulle mata magungunan akayi, har da na hayak'i, a ka kuma hadota da k'aninta Hudu dan shekara 4, Ali bai damu ba, don zai iya yin komai don Matarsa..


Shiru-Shiru bayan Watanni babu wata alama, hankalinta yayi mugun tashi da taga ba sarki sai Allah, sai ta bar yin maganin ta zubawa sarautar Allah ido.


BAYAN WASU 'YAN WATANNI


Alhaji Ali yayi suna, ya lula cikin siyasa tsundum, a lokacin shine Dan Majalissar dake wakiltar Katsina a Birnin tarayyah Abuja. Tunda Allah ya buda mishi yake kai danginshi aikin Hajj.Ya hada da Mahaifan Shafa'atu.


Wata rana, Alhaji Ali na hanyar zuwa Katsina daga Abuja shi da Drivernshi, suka tsaya a Masallacin Matafiya da ke Zaria. a gidan mai Masallacin yake. Bayan sun idar da Sallah ya hadu da wani Abokinshi Alhaji Usman Shehu da suka yi Karatu a Kano tare.


Da Murna suka rungume juna, bayan sunyi gaisuwa, Alhaji Ali yace "Haba Abokina ka boye" Alhaji Usman yayi dariya yace "Ina talaka zai ganka kana dan majalissa, ai ka zarce ni" Dariya sosai Alh Ali yayi yace "kai har yau baka bar iskanci ba" sukayi dariya baki daya. "Daga ina zuwa ina?" Alh Usman yace "daga zariya zamu koma Kano , chan nake zaune da wallahi iyalaina" Alhaji Ali yace "yaranka nawa?" "su 3 ne muje ku gaisa na san sun idar da sallah suna Mota" Tare suka je inda yayi parking Motar shi, ya bude yace ma matarshi ta fito su gaisa da abokinshi, fitowa tayi daga mota yaran suka fito su ma suka gaisheshi, daya bayan daya ya daukesu yana tambayan sunayensu yana mai sha'awarsu, sosai yake son yara, barin ma na k'annenshi, so yake ya dauki wasu daga cikin yaran k'annen nashi, amma da yake suna da yawa be son daukan dan wani ya bar na wani, kar ace ya nuna bambanci ko fifiko ga wani da kuma be so Shafa'atu taji an mata ba daidai ba don ita bata haihu ba, shiyasa be taba bijirowa da son rike 'ya'yan kanenshi ba.


"Kaifa yaranka nawa?" dan murmushi yayi yace "tukunna dai Allah bai kawo ba" Alhaji Usman sai yayi nadamar tambayarshi don kar yaga kamar yana son ci mai fuska ne, Alhaji Ali ya lura da yanayin da abokinshi ya shiga yace "kai daniska, kar ka damu, haihuwa ai ta Allah ce, idan da rabona zan samu D'an cikina ko ba dade ko ba jima zan samu, kawai ka tayani da Addu'a" InshaAllah Abokina inji Alh Usman.


Alhaji Usman ya kalli matarshi yace "wai ina Maryama ne?" dan murmushi tayi tace "ta na cikin masallacin mata muka barota bata idar ba" da mamaki Alhaji Usman yace "k'assarun?" tayi dariya tace "shi fa, ka santa da dadewa gun sallah" yace "danAllah je kirata muna kan hanya kar muyi marece" kafin waninsu ya sake magana hankalin Alhaji ya kai bakin Masallaci da wata halitta fara ta fito daga ciki tana gyara zaninta wanda shine matsayin mayafi.


Yauwa gata nan ta fito cewar matar, bude baki yayi yace "sallatu yi sauri ko?" da murmushi ta k'araso, ta kalli Alh Usman da ya shagala wurin kallonta tace "ina wuni" kasa amsa mata yayi sai da abokinshi ya lura dashi ya sa hannu ya zunguro shi kafin ya amsa mata. Oya a shiga mota, ya umurce su.


Alhaji Ali yace "Abokina wacece wannan?" yace "Maryama ce kanwata ko" dan shiru yayi kafin yace "indai har baku yi mata miji ba ina so, zan aureta".
#############
Dariya Alhaji Usman yayi "kai wallahi Ali ba ka rabuwa da shiririta" tamk'e fuska Alhaji Ali yayi yace " kai ni wallahi dagaske nake, in dai wallahi ba kuyi mata Miji ba, ina so".


Kallonshi Alhaji Usman yayi sosai yaga iyakar gaskiarshi kenan, yace "in har dagaske kake, to wallahi ka samu Maryam, kai dai kawai ka zo Gida, sai mu sake tautaunawa".
Hannunshi ya rike yace "Wallahi zanzo, kawai ka bani full address dinka." Alhaji Usman yace "ba damuwa".


Paper ya fallo a cikin Motarshi ya rubuta mishi Adireshin Gidanshi a Kano, shi ko Alhaji Ali hannu ya sa a Aljihu ya ma yara Alheri suna ta Godia, a nan ne kowanensu ya shiga Mota suka ma juna Oda kafin suka wuce.


Tunda ya zauna yake lumshe ido yana sake hasaso ma kanshi Maryama, haka Driver ya ta shatata gudu Alhaji Ali na ta begen Marayama a zuciyarshi.


Ya iso Katsina lafiya, sai da ya fara zuwa Gidansu ya gaida Mahaifiyarshi, kafin ya sauke mata tsarabar da yayi mata, ya ma Matasan Gidan Alheri kafin ya wuce Gidansi.
Shafa'atu ta tarbeshi kamar yanda ta saba, cikin shiga ta alfarma, suka rungume juna don sunyi kewan juna, sai da ta kaishi yayi wanka, kafin ta zubo mishi Abinci suka ci tare.


WasheGari, ya dauki hanyar Kano.


Alhaji Usman Aminin Alhaji Ali ne tun suna Makaranta, Maryama k'anwarshi ce, kasancewar Mahaifansu sun Rasu, Alhaji Usman ne ke rik'on Maryama tun bayan Rasuwar Mahaifiyarsu, yana kula da ita sosai don har makarantar Unguwanzomanci ya sakata(Midwifery).


Da Azahar suka karbi bak'uncin Alhaji Ali, Alhaji Usman yayi mamakin ganinshi, don beyi zaton zai zo nan kusa ba, lallai ya nuna mai dagaske yake. Abinci Matar A. Usman ta gabatar mai da shi, ya ci sannan ya gabatar mai da buk'atarshi,
Alhaji Usman yace "ba damuwa, shi dai ya bashi ita, kuma ya san yarinya ba zata bashi kunya ba, don Matsayin Uba yake a gunta" ya mik'e tare da cewa "bari ya turo mishi ita".


A daki ya isketa tana zaune kan wata kujera tana duba wani littafi, zama yayi a dan nesa da ita, tana ganinshi ta gyara zamanta tare da kulle littafin da ke hannunta.
"Maryama, ina so ki Saurareni, a Parlo, akwai abokina Alhaji Ali, wanda muka hadu jiya a Zariya a Masallaci! Na san kin ganeshi, to shine ya zo neman aurenki gurina, ni kuma na bashi ke, saboda na san kyawawan halaiyanshi, na san ba zaki watsa min k'asa a ido ba".


Shiru tayi batayi magana ba, yace "Maryama, ba dai bijiremin zakiyi ba ko?" da sauri ta girgiza kai tace "Yaya, kai ne Uwana kai ne Ubana duniya banda sama da kai, na san ba zaka zaba min abinda zai cutar dani ba, Nagode da zabinka gareni, Allah ya shige mana gaba". Da fara'a ya amsa da "Ameen, ni na san ba zaki bani kunya ba, ina Alfahari da ke Maryama, maza tashi, ki sanya Mayafi kije gareshi yana jiranki". Kanta a k'asa ta ciro Zaninta ta yafa ta fita waje.


Da Sallama ta shiga Parlorn kanta a k'asa, zama tayi a kan kujera daga farko, kafin ta dan rusuna ta gaisheshi, shi ko da kallon So da Kauna ya bita, ya amsa gaisuwarta cikin shaukin soyayya, a hankali a hankali ya ke tambayarta tana bashi amsa, sun dau lokaci suna zantawa, daga bisani yace "ta shiga ciki ta turo Yayanta".


Alh Ali ya gaya ma Alh Usman shifa ya samu Mata, ba bata lokaci yace "suje ya gabatar dashi wurin Kawun su".
Alhaji Ali be bar Kano ba sai da ya tabbatar an bashi Maryama.


Da farinciki ya koma Katsina, ya je ya sanar da Mahaifiyarshi yana neman Aure, ta sa mishi Albarka, Danginshi ko sunfi kowa Murna don su na son su ga gudan jininshi, k'ila Auren Rabo ne ke zuwa, nan fa aka fara shirin Biki.


Ba wanda ya sanar da Shafa'atu game da Auren.
Kudade ya biya masu dimbin yawa aka fara gina Mishi Katafaren Gida a wani Anguwa da kusan shi kadai ya fara Gini a wurin wato Tudun Matawalle,


Shafa'atu kuwa tausayinta yake sosai, yana shakkar gaya mata maganar Aurenshi, be so taji kamar zai kara aure ne saboda haihuwa, baya so ta ga kamar ya gaji da ita ne, baya son bata mata sam, karshe dai ya biya mata kudin Umra ta tafi Makka, kuma ya siya mata 190, a lokacin da wuya kaga Mace na tuk'a mota, amma ita ya mallaka mata Motar kanta, Bayan tafiyarta Makka ya samu ya fara shirin bikinshi a tsanake.


Ana saura Sati 3 Biki
Shafa'atu taje Gidan Surikanta da Akushi dauke da Tuwo Miyan Kubewa busassa dominos uwar Mijinta, tunda ta shiga ta ji gabanta ya fadi, da Sallama ta shiga k'urya, zaune k'annen Alhaji Ali suke su 9 suna diba kaya, da alamu lefe ne, akwati 2 manya, da fara'arta ta gaishesu, da Hajiyarsu, Hajiya ta amsa tana dan jin nauyinta, basu san zata zo ba.


Shafa'atu ta kallesu tace "to, lefe ne ake kallo? Karime wa aka kawo wa lefe bamu sani ba?" Karime ta dan kawar da kai gefe tana yak'e ta rasa me zata ce mata, Shafa'atu ta sa hannu tana daga kayayyakin tana gani tana yabawa "wai Kayan waye? Wa aka kawo mawa?" Ladidi tace "wa dai zaa kai ma wa ko?"


Karime ta zungurota da hannu, da yake Ladidi ta fi ki jinin Shafa'atu tace "har sai yaushe zaa boye mata? Ke Shafa'atu lefen Yayanmu ne, za'a kai Kano Gobe in Allah ya kaimu" Shafa'atu da dan yak'e a fuskarta tace "Ahh, Yaya Shehu Aure zai sake? Waiyo Allah shi kaimu, ashe muna da biki".


Ladidi tace "Iyeeee, wato Shehu kadai ne yayanmu? To babban Yayanmu nake nufi" Hajia tace "Ladidi kiyi shiru" Shafa'atu da bata fahimci komai ba tace "bangane ba, Babban yayanku? Wanne kenan?" Ladidi tace "baki gane ba? To Yaya Ali nake nufi" tsalle Shafa'atu tayi ta dire tace "Ba ku da hankali, kun ga dai bana san irin wasan nan" Asabe tace "wake miki wasa? Tunda kin kasa haihuwa, zaa auro me haihuwa".


Karamin bori Shafa'atu ta hau, ta hau facali da kayan cikin Akwatunan, kafin ta wawuri Akushin Miya ta bude Miyan ta juye a jikin kayayakin, nan suka yo kanta, ta dire ta yi kan Hajiyarsu. "munafuka, ke kikace yayi aure ko?" aiko su Ladidi sukayo kanta, suka hau dukanta wai ta zagar musu mahaifya da k'yar Hajia ta hanasu dukanta, har tace "zata tsine musu in suka sake bugunta"


Ina bakin shafa bai mutu ba, ta dinga surfa musu Zagi, tana laantarsu, tana cewa itace Ajalinsu, shegu k'azamai, talakawan banza, duk kyautata muku da nakeyi? Ni zakuyi wa butulci, biye nake da ku kamar na muku sujadda shine zaku saka min da wannan? Aiko zaku sha mamaki, ayi auren mu gani, ta fita fuuu, ko zaninta bata dauka ba, ta ci karo da Ali a hanya ko kallonshi bata yi ba ta fada motarta ta danna a guje, Ali ya ji gabanshi ya fadi. Ya shiga Gidan da sauri


Hajia ce tace "ta ga kayan lefen ne, ka bita ka lallasheta" kallon kayan yayi yace "meye wannan kamar miya?" Ladidi ta chafe tace "Wai baka ga ruwan wulakanci da tayi a gidan nan ba, har ta na zagin Hajia, kanta farau kishiya?" ran Ali ya baci yace "Ta zageki Hajia?" Hajia ta girgiza kai tace "aa ba fa ta zageni ba ladidi" tana wurgar Ladidin da harara, kai dai ka je ka san me za ka ce mata kasan mata ba sa son Kishiya.


Tashi yayi jiki a sabule ya nufi Gida, ya jima a bakin gate kafin ya shiga, zaune ya ganta har ta bashi tsoro don ta ci kuka har ta gaji, k'arasawa yayi a tsorace, be san ta inda zai fara ba, yana karasowa ta ci kwalarshi, tana jijigashi tana dukanshi ko ta ina, ni zaka yaudara Ali don kayi kudi, ni da nake zaune da kai tun baka da komai, ni zaka ci amanata Ali? Kasa magana yayi, ya kasa motsi, ta cigaba da dukanshi kafin ta fashe da wani irin kuka, rungumeta yayi tsam tun tana motsi har tayi lamo a jikinshi tana mayar da ajiyar zuciya, sai da ta daina motsi kafin ya soma magana.


"Shafa'atu na san ban kyauta miki ba da na boye miki maganar Auren nan, amma ki san cewa ina sonki fiye da zatonki, duk wata Macen da zan aura a bayanki take, kar ki manta irin Son da nake maki, ki dauka wannan Auren k'addara ce, ki bani goyon baya nayi auren nan, wallahi ba zan taba wulakantaki ba, wallahi Shafata kin fi karfin wulakanci a wurina, Shafa'atu ba ayi macen da take karshena da zata wulakantaki ba, in naga ba zata girmamin ke ba, wallahi ina iya rabuwa da ita, ki taimaka min" abun mamaki hawaye ta gani kwance a idanuwanshi tana son Mijinta sosai, kalamanshi sun darsu a zuciyarta, bata da wani zabi illa ta danne zuciyarta.


Bayan ta gama kumburinta ta sauko, hakan ya bashi kwarin guiwa ya cigaba da sabgarshi, amma walwalarta sam bata dawo ba, da tsanar danginshi da ya darsu a ranta, danne zuciyarta kawai take.
***.
Ba wai don tsoronta yake ba kawai don a zauna lafiya ya sakar mata ragamar bikin gaba ki daya, sai yadda tace ake yi, harta dakin da Amarya zata zauna ita ta za bar mata, ya so ta ba Amarya daki biyu, amma tace nata ne kawara daya ne na amarya, be damu ba don ya san da ya gama gininshi zasu koma sabon Gida kowa da Dakinshi da Parlornshi, shiyasa be ce mata komai ba.


A ka zo jere, da katifa da kujera da kayan kitchen duk aka jera a daki daya kasancewar dakin k'ato ne.


Tun daga jere dangin Maryama suka gano matsala daga gun Abokiyar zaman Maryama, amma basu ce komai ba gudun sa mata tsoro da fargaban kishiya, kuma sun lura Dangin Ali na son Abun.


"Kinsan Shafa'atu, ki bi a sannu, kinsan Mijinki yana daidai gwargwado gurin kyautata miki, to in kika faye zak'ewa kika kureshi, zai bar bi takanki, ke dai kawai ki bi ta bayan fage ki kori amaryar nan, ki mata zagon k'asa, kishin mimik'e zakiyi, kar ki yarda a gane ba kya sonta kin gane?" ta jinjina kai tana kwasan karatu gurin Aminiyarta Hajiya Er Rabi,


Nan ta kwantar da kai ta bi har Gidansu Hajiar Ali ta basu hakuri, kan haukan da tayi sharrin shaidan ne, Hajia tace ba komai ya wuce dama an san mata da kishi, balle ita da aka boye mawa.


Jumu'ah na zuwa aka daura Auren Alhaji Ali Zaki da Maryama Adamu a garin Kano ta dabo, an kawo Amarya dakinta.
Uwar Dakinta Matar Yayanta ta dade tana jadadda mata nasihan da yayanta ya mata, kafin suka bar Katsina, Maryama ta sha kuka kamar idanuwanta zasu fadi.


Murmushi ya mata yace "nagode Allah ya miki Albarka Maryama"
Shafa'atu kamar ta fashe amma sai ta hau yak'e tace "bari ta dauko musu Abinci".


Da sauri ta mik'e ta fice hanyar kitchen, Ali ya dinga bin Maryama da kallo ita ko kunya ma yake bata.
Tare sukaci abinci kafin suka gama, Shafa'atu tace bari ta shiga ciki ta musu sai da safe.


Shiga daki tayi ta dinga gwala kanta a bango, tana kukan bakinciki, anya hanyar nan mai bullewa ce? Anya zata cigaba da nuna komai lafiya lau ne alhalin ba haka bane? Gaskia da sake.
Su ko maaurata tuni suka shige dakinsu.


A GURGUJE


Bayan wasu 'yan Satittika


Zaman lafiya suke kadaran kadahan, Maryama dama sanyi gareta, biye take da Shafaatu, sun raba kwana bibbiyu, ko wacce burinta ta zama tauraruwa wurin Mijinta, sosai Shafa'atu ta danne zuciyarta don su zauna lafiya da Maryam, barin ma da ta ga bata da matsala.
****
Ta gane tana da ciki, saboda sauyin da ta ji jikinta nayi, bata ce ma kowa komai ba ta cigaba da harkokinta.
Sosai Mijinta ke nuna mata k'auna, a gaban Shafa'atu ya kan nuna kawaici, amma in suka kebe kamar ya hadiyeta.


Sannu a tashi alamun

Please Login or Register in order to submit comment