Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

matar danuwansu.
**


Antisco da Aisha sunzo, ta kawo musu Babban Darduma da Basket din Abinci suka shimfida daga Waje don baa zama a cikin ICU.
Mancy tace "ai da baki wahala ba Antisco, wanda Jawad ya kawo dazun da saura, ya jikin Uncle dinsu".
Antisco tace "haba ai ba wani abu, ke dai Allah ya basu Lafia".
Aisha tace "Aunty Aseey, me kike yi a nan, waye be lafia?".
Aunty Aseey dai cikinta ya duri ruwa bata iya cewa komai ba.
Antisco tace "kin santa ne?"
Aisha tace "Lah, matar yayan besty ce"
Antisco tace "Ah haba, Allah sarki, Mancy surikarki ce, kanwarsu Jawad zai aura".
Gaban Mancy ya fadi tace "Labiba Jawad ke So?".
Antisco tace "kin ma san Labiba kenan,ah Lallai Jawad baya jin kunya ya baki labarin budurwarshi?".
Mancy ta girgiza kai tace "na shiga uku na, dazun Jawad naga ya fita rai bace, ashe dalili kenan?".
Antisco tace "me ya faru da Jawad?".
Mancy tace "Antisco, Matar da Jawad zai aura, ita taba Zaid Hantarta aka diba aka dasa mai".
Aisha tace "Kaiii, Labiba ta ba danki Hanta? Ina ta sanshi Mancy?".
Ikon Allah.
Mancy dai bata sake magana ba, Aishar ma haka, ba wanda ma dai ya sake cewa komai.


Anty Aseey ta rafka uban tagumi tana jiran isowarsu Mijinta.
Har su Antisco suka karashi zamansu suka yi musu Sallama tare da tabbatar musu da cewa zasu dawo gobe.


Tafiyarsu Antisco ba dadewa ba Mutanen Edo suka iso, kasancewar suna wajen ICU yasa basu sha wahalar ganesu ba.
Su ka k'araso.
Aunty Aseey ta rik'o hannun Mami saboda da kyar take tafia kafarta ta kumbura sosai saboda zaman Mota, sai sannu Aunty Aseey ke jero ma surukarta.
Ko ba a fada ba ansan Mamin Labiba ta sha kuka.
Mancy kamar ta goya su sai gaisuwa take kwasa.
Yaya Muhammadu yace "Hajia ashe kina nan, ina Labibar?".
Mancy tace "kuyi hakuri bata farfado ba".
Mami tace "Labiba ta mutu ko?"
Mancy tace "aa wallahi, allurar ce bata saketa ba".
Mami tace "amma shi dan naki ya farfado?".
Mancy cike da kunya tace "eh ya farfado".
Abba yace "muje mu ganta".
Lokacin Visiting ya wuce wai ba zasu barmu mu shiga ba.
Baba Muhammadu yace bari na ma security magana.
Da kyar aka samu ya bari suka shiga da niyyar suna ganinta zasu fito.
Mami ko sai da tayi magana ta na kuka tace "Labiba in kin Tafi na yafe miki, wallahi na yafe miki, Allah ya rahamsheki, in kuma baki tafi ba Allah ya tashi kafadunki, Zuciyar Mami na zafi, ki tashi ki lallasheni, kice Mami zuciyar ta bar Zafi haka nan ga ki nan, donAllah".
Da kyar Baban Amira ya fitar da ita ganin kuka take sosai.
Abba yace "Labiba kin san dai Dukkan nan sai kin sha shi ko? Ki tashi in zaneki, ki tashi hakan nan".
Ganin shima kukan zaiyi ya sa shi fita da sauri.
Mancy tace "Sannunku kun sha Hanya, ku zauna donAllah ku ci Abinci gashi nan".
Yaya Muhammad yace "Mami kiyi hakuri ki zauna ki ci Abinci"
Mami ta kauda kai.
Mancy da durkusa a kan guiwowinta tace "ba dan ni ba, kiyi hakuri donAllah, laifi laifina ne da banzo da wuri ba, wallahi da ina nan ba zan taba yarda a bude diyarki har a diba wani sassa na jikinta ba, donAllah Mama kiyi hakuri, dole ranki ya baci, donAllah kiyi hakuri ki ci Abinci".


Abba yace "ashe mutum be san ya dauki k'addara ba? To ko cewa akayi Labeen ta mutu ne? Amina bani son dogon zance, zauna ga Abinci kici".
Zama tayi, Abba ya zauna, Yaya Muhammadu ya zauna, sai kanenshi Hamza shima ya zauna.


Jikina rawa Mancy ta bude cooler din Abincin Gidan Auntisco ta zuzzuba musu Faten Dankali da Shinkafa.
Ko wanne ta kai mishi gabansh, tayi serving dinsu.
Ta ja hannun Dalo suka wuce chan Amenity dakin da Zaid yake.


Sun gama cin Abinci Abba yace "muje mu gano shi Masoyin Labeen".
Fit Mami tace "ba inda zani".
Abbansu yace "kinga Amina ki shafa ma zuciyarki salama, to in Allah yace lokacin Labiba yayi kumburin da kike shi zai maidota? Ke baki san kaddara ba, maimakon ki ta rokon Allah ya bata lafia ya tashi kafadunta kin tsaya kina fushi? Har kina ma da lokackn Riko? Haba itama kinga hankalinta ba kwance yake ba, danta na chan shi kadai, amma ta na nan zaune gun diyarki har sai da mukazo, wallahi ki natsu".
Nasiha ya mata kafin ta yarda zataje ta ga Zaid.


**
Zaid na ganin Mancy yace "ta farfado?"
Mancy ta girgiza kai cike da tsoro.
Rufe ido yayi kawai ya kawar da kai.
A ranshi yana fata in mutuwa Labiba tayi Allah ya dauki ran shi, ba zai iya rayuwa babu ita ba".


Mancy na ganinsu ta mik'e tana taba Zaid, Zaid bude idonka kaga Baban Labiba ne da Mamarta.
A hankali Zaid ya bude idanunshi, yana ganinsu yayi yunkurin tashi Abban ya maidashi, yace "ka adana k'arfinka, zaka buk'aceshi".
Zaid yace "donAllah kuyi hakuri, laifi na ne, wallahi laifi na ne, Labiba batayi komai ba, nine mai laifi, ni zaku hukunta, ni zakuyi fushi da, Labiba batayi komai ba".


Mami ta ji son Zaid da tausayinshi, tace "inshaAllah zata farfado, kayi hakuri".
Ba su k'ara minti Uku ba aka gunguro gadon Labiba.
Duk suka mik'e suka tarbesu.
Ta farfado, daga kallon fuskarsu kasan suna matukar farinciki.


Kwance fa take ba ta wani k'arfin kuzari tace "Ina Zaid? Yaya jikinshi, Dr yace ya farfado, yana ina".
Da dukkan alamu sambatu ne, bata san su waye ke kanta ba.
Mami ta kalleta sosai, kallon da take mata in tayi laifi.


Kamar zata gudu tace "Lahh, Maminmu, kiyi hakuri kar ki bugeni, wallahi aiki aka min yanzun na farfado".
Daria ta ba Mami, Mami tace "Allah ya baki lafia Labee, sai na miki dukan tsiya, bari dai ki warke".
Labee ta turo baki tace "kuyi hakuri".
Nurse tace "haba Mama, ya kuna haka ne? Daga farfadowanta kun fara sa ta kuka? Abeg ku fita visiting ya kare sai gobe kuma".
Haka nurse ta tarkata su ta kora waje.
Mancy ta dawo wai tayi mantuwa, ta duka kan Labiba ta na murmushi tace mata "In maminki ta gama dukanki nima zan miki nawa, waya ce miki ana satan hanya a zo gun saurayi? Kika bashi Hantarki? Da icce zamu bigeki".
Ta durkusa ta manna mata kiss a goshi tare da gyara mata kwancia zuwa gefen Damarta.
Mancy na kaucewa idonta ya fada kan na Zaid da ya tsura mata ido, wani Sonta na cizgarshi.
Nurse ta gama duba ruwa da jinin hannun Labiba, kafin ta fita ta barsu su biyu cikin daki irin na mutum biyu daya.


Lumshe ido sukayi a tare Zaid yace "kin wahala ko?".
Ta murmura tace "aa ba wahala, kai fa?".
Yace "Sannu Kinji".
Tace "Nagode"
Yace " for what?".
Tace "for Staying alive, nagode daka warke, ina ma Allah Godia da ka rayu".
Zaid yaji hawaye na zuwa mishi, wannan wani irin So take mishi, like yanzu fa ta samu kanta ta farfado amma she's still worried about him.
Murmushi yayi yace "focus and recovering and take that beating from Mami".
Ta marairaice fuska tace "Zaka karbar min Bulala?."
Yace "aa gaskia, bulala fa na kine, ke za a zane, ni meye nawa na shisigi? Kawai ki karbi bulalanki da kanki kizo muci gaba da gashi".
Tace "yanzu Masoyi ba zaka iya tsayawa a dakeka mai makon ni ba?".
Zaid ya girgiza kai yace "Nope".
Tace "waiyo heartbreak, let me just die now".
Ya wani zaburo yayi saurin komawa sakamakon zafin da yaji gefen na mishi, ya cije baki, ta na lura dashi.
Yace "Kar ki sake, kinsan how worried you got me? Labiba da baki farfado ba, da bansan ya zanyi ba".
Ya kalli Sama yace "Allah kar ka barni da iyawata ban iya komai ba, Allah ka bar min Labiba".
Tace "Ameen Masoyi".
Yace "Ina Sonki".
Tace "Ina sonka Masoyi".
Soyayyarsu suke zabgawa a gadon Asibiti, ba su da wata damuwa.


Su ko Darduman Waje suka zauna suna dan fira jefi jefi.


0000000000


Tun da garin Allah ya waye take surkullenta.
Wani k'ok'o ta dauka ta fita dashi a hannunta, ta kira aljannarta da ke binciko mata abunda take so tace "je duba man kiga ina Dan Makaho yake?".
Ko minti daya batayi ba ta sanar da ita cewa Dan Makaho na Asibiti kwance.
Hankalinta ya tashi "kar fa ya mutu, diyarta bata mutu ba don shima ya mutu, dole ya rayu ya ji dadi kamar yanda Yasmin ta mishi fata, ta manta rayuwa ba a hanunta yake ba.
***


Tun da ya dawo take mishi mitan Hudu, bai ji dadi ba sam, hakuri yake bata yana cewa kar ta damu, zai siya mata sabbi, chan sai taga yayi shiru tare dafe kanshi, wani irin Ja Idonshi keyi, zufa ke keto ma Alhaji Ali Zaki kamar yana dakin Gidan Biredi.
"Alhaji baka lafia? Tashi mu tafi Asibiti"
Bai iya ce mata komai ba ya tashi ya fita ta bi bayanshi, Annah ma ta bisu a baya.
Mota su ka shiga, har yanzu kwakwalwarshi juyawa take yana ganin abubuwan da suka faru kamar film.
Tuni ya fara tari ba k'ak'autawa, ganin ya amayo wani K'aton dutsi ya sa Hajia Shafa'atu kara gudun motarta don ta tsorata sosai.
Sai sannu suke jero mishi ita da Annah.
General Hospital suka nufa.
Emergency suka nufa.
Fitowar su kenan suka hango Er Rabi da ke tunkarosu ta kallesu daya bayan daya.
Shafa'atu tace "Er Rabi ina kika shiga tun jiya wayarki bata shiga , Daddyn Annah na kawo Asibiti baya jin dadi".
Cike da umurni tace musu "ku biyoni".
Tayi gaba rungume da k'ok'onta a kirji, tafia sukayi a k'afa har Amenity ba wanda ya tambayeta din me kamar ta rufe musu baki.


A bakin k'ofar ta gansu zaune da alamun Sallahr Isha'i suka idar.
Mancy da Dalo na ganinsu suka mike tsaye.
Alhaji Ali yayi saurin durkusar da kai , Shafa'atu kuma na ma kawarta ido don me suka zo nan?.
Er Rabi tace "Yauwa, nayi farincikin ganinku a nan, ni da na zo gurin Zaid na fasa k'wai ashe kuna nan".
Shafa'atu ta tabo kawarta.
"Menene? Bangane ba Er Rabi, me ke faruwa ne?".
Er Rabi ta murmusa tace ina Zaid? Ina so komai zaayi a gabanshi?".
Mancy a dan tsorace tace "me ya faru? Zaid na kwance bai lafia an mishi Surgery, menene?".
Er Rabi tace "Kwai zan fasa, zan tona ma Shafaatu Asiri kuma zan tona ma kaina Asiri, ni dinnan nan da kuke gani, bokanya ce ni".


Mamin Labiba da Aunty Aseeyah suka saurin mik'ewa cike da tsoro.
Baban Muhammadu da Abbansu ma suka mik'e Er Rabi tace "duk kuyi mun shiru, kar wanda yayi katse man magana".
Kamar ta sa kwado ta rufe musu baki ba wanda ya iya magana, duk wanda yayi yunkurin magana sai ya ji ya kasa da alamu siddabarun ta musu ta fara magana.


"Sunana Hajia Er Rabi, ke Maryama kinsanni." Ta kalli Alhaji Ali tace
"A yau Zan fasa k'wai, Matarka Shafcy bata da Aminiyar da ta wuceni, bayan ka mata kishiya, ta haihu ka so danka fiye da kowa da komai, bayan ka saketa, na kaita wurin wani bokana, baban Annah kenan".
Annah ta gwalalo ido. Er Rabi ta harareta tace "Eh Babanki Boka ne, babanki shi yace ta dawo bayan shekara Sha biyar zata samu Alhaji Ali Zaki, zata juya shi yanda take so, ba zai mata gardama ba, zata mallakeshi amma sai bayan Shekara 15, bayan shekara 15 ta dawo Dakinta sakamakon Asirin da baban Annah ya tafka, shiyasa a ranar da ta dawo gida aka ma Maryama Sakin Wulakanci, ya juya ma 'ya'yanshi baya sai abunda tace yakeyi, ta rabaka da Danginka da komai sai abunda tace kake so".
Shafa'atu so take tayi ihu, so take ta sa Er Rabi yin shiru, me yasa take mata haka? Meyasa take tona mata Asiri?" Gashi ta kasa ko da motsi, Er Rabi ta kafe su, ta sa sun k'ame k'am.
Alhaji Ali Fitsari yaji kawai na zuwa mishi ta k'afa.
Mancy da Dalo kam hawaye ke kwaranyowa daga idanuwansu.
Sauran kam sai zare idanuwa suke.


Er Rabi ta cigaba "Ni ba wannan bane damuwa na, damuwa na shine Zaid, zuwa nayi na rok'eshi gafara na kuma cika burin marigayiya Diyata da ina jin ta fi son Zaid a kaina, Sonshi take har ta koma ga Allah, har ta mutu tana rok'ona na kare mata Zaid, na tayata sonshi, ta na so na kula mata dashi, ta na son Zaid, ni kuma ina son abunda Diyata take so, yau na fasa k'wai, zan kuma zare hannuna daga duk wani abunda zai sa Zaid din Yasmin ya cutu ko wani masoyinshi".
Er Rabi ta fasa k'ok'on hannunta wani bak'in ruwa da k'adangare suka fito daga ciki.


Er Rabi ta kalli Sama tace "Yasmin... kinji dadi? Na cika miki burinki".
Er Rabi ta kalli Shafa tace "Dalilinki na rasa diyata, dalilina duniyarki zata juya".
Ta wuce ta k'yallesu chan suka fara motsi.
Aunty Aseey tace "K'urungus k'aryar 6era ta k'are".
Shafa'atu ta ja hannun Annah da gudu suka shige Mota babu wanda ya kulasu.
Alhaji Dakata ya musu nuni da su koma ciki, Mamin Labiba da Aunty Aseey suka matsa gefe don ba su wuri tare da barin Alhaji Ali, Mancy da Dalo kamar ba su da lakka a jiki.


Alhaji Ali ya kalli Dalo da rinannun idanuwanshi yace "Sadiya, Ina Zaid?".
Dalo ta fashe da kuka ta rungumo Babanta. Kamar jira yake ya fashe da kuka.
"Baba nayi kewanka".
Baba yace "Darlingg".
Sadiya tace "Ba darling ba dalo".
Cikin hawaye suke daria.
Baba ya kalli Mancy zuciyarshi yaji kamar zata tarwatse.
Yana son Matarshi sosai, Shafa'atu ta rabashi da ita har tayi wani auren.
Yace "Maryam, yaya kike?".
Mancy kasa magana tayi tana cin kuka.
Ina Zaid? Yana ina? A zo a diba Hantata a bashi, in ma Zuciyata za a sa mishi, a cire nawa a samishi donAllah, ku ceci yarona, ina son mishi magana".
Mancy na kuka tace "Baban Zaid, an riga anyi Surgery din, Zaid na nan ya farfado, nurses ne suka koromu wai sai gobe".
Baba yace "ku kaini wurinshi donAllah".


Da kyar aka barshi ya shiga.
Yana bude kofar ya hada ido da Zaid.
Kallo daya Zaid ya mishi ya hango k'auna, soyayya, nadama, ban hakuri a ciki.
Baba kuwa karasawa yayi gadon Labiba, kamar zai fashe da kuka yace "Sannu ko? Sannu, Allah ya baki lafia".
Labiba tace "Ameen nagode".
Baba yace "kin gode? Da me? Ki bari kawai yarinya, Kiyi shiru donAllah".
Labiba ta bishi da ido har ya karasa gadon Zaid.
Dafa goshin Zaid yayi yace "Sannu, me ke maka ciwo?"
Da tsantsan mamaki Zaid yake kallon babanshi yace "babu komai, ban dai da karfi".
Baba yace "dama karfi ba yau ba, yau fa akayi aikin, dole kaji kasala, sannu".
Zaid kai ya daga, Baba ya kallesu a tare yace "Ku warke da wuri kunji".
Kai suka sake dagawa.
Ya fita.
Labiba ta ja dogon numfashi tace "I think this is actually your Father, he is back".
Zaid da ma ya rasa abunyi yace "Wannan shine baba na, tabbas, Allah Nagode".'


Ya na fita ya ci karo da Mancy ta na waya, da alamu da Mijinta suke waya don ya dan ji maganar samasama inda take cewa "Goben zaka taho? To Allah ya tsare min kai ya kawo min kai Lafia Mijina".
Dam ya ji gabanshi ya fadi wani abu ya sokeshi a zuciya.
Tana waigowa ya kirkiro murmushi.
"Sannunku, kun sha fama".
Murmushi kawai yayi.
Ya wuceta ya nufa Gunsu Alhaji Dakata, Sallama ya musu ya mika ma Abbansu hannu kamar zai durkusa, Abban Labiba duk tausayinshi ya kamashi.
Ba abunda Alhaji Zaki yake sai zuba Godia yana gode musu.
Kan darduman suka zazzauna.


Alhaji dakata yace to ai dare nayi, ba zamu ta zama a nan ba, Muhammadu dauki matarka ku wuce Gida, yaranku na chan na zaman makwafta".
Baban Amira yace "to Baba da wai ni na kwana da Labiba, ai ba a barsu su biyu a Asibiti ba".
Alhaji Dakata yace "aa sam, ni da Maminku zamu kwana, kai dai ka dauki Matarka da Haruna".
Alhaji Ali yace "Aa Alhaji, ya zaayi ka kwana? Mallam Muhammadun ya kwana".
Mancy tace "aa duk ni zan kwana duk ku tafi masauki".
Aunty Aseey tace "Mami muje Gida".
Mami tace "ni zan kwana gidanki?".
Aunty Asy tace "Mami lalura ce, ni bama ki taba zuwa Gidana ba".
Mami tace "ba kuma zanzo ba ehe".
Daria sukayi, wai ita bata zuwa gidan danta na fari.


Dalo ta rada ma Babanta a kunne "Baba daga Edo State suke, ba su da inda zasu kwana".
Alhaji Ali yace "to Abunda Za ayi, Shi Muhammadu ya tafi da Matarshi gida, Alhaji da Hajia ku tafi Masauki, Hajia Maryama kema ki tafi Masauki, Asibiti ne, ICU baa jinya, amma yana da kyau wani ya tsaya a nan".
Baban Amira yace "Ni zan kwana".
Mancy tace "Aa fa ni zan kwana da yarana".
Alhaji Ali yace "kin tambayi Mijinki? Ba zaki kwana ba gaskia".
Be jira amsar kowa ba ya matsa gefe, yana waya ya dan jima yana waya kafin ya dawo.
Cikin Mintuna da ba su wuce 20 ba Motoci 3 suka zo harabar Amenity.


Alhaji Ali yace "Alhaji ga Mota chan, Driver zai kaiku Masauki Please, kuje chan ku huta, gobe da safe zai maidoku".
Zasuyi gardama Baban Amira yace "donAllah Abbanmu kuje ku huta, kun sha tafia".
Abba yace to shikenan Muhammadu muje ka bude mota ka bamu kayanmu"
Mami tace "Sai da safenku".
Mancy tace "to mungode kwarai".
Alhaji Ahmad Yayi gaba Matarshi na binshi a baya.
Alhaji Ali ya kalli Yaya Haruna yace "kaima bisu, akwai wurin kwananka" da sauri ko ya bisu.


Ya kalli Dalo yace "ku ina zaku kwana?".
Dalo tace "Baba in zo muje Gida?".
Kallonta yayi, beyi mamaki ba don ta nemi izinin binshi Gida.
Yace "Dalo kizo muje Gida".
Mancy ta mata ido, alamun kar taje, har ta manta abunda Hudu ya so mata? Ga Shafa'atu.
Dalo tace "kar ki damu Mancy, Babana zai kareta daga sharrinsu".


Alhaji Ali ya kawar da zancen yace "Dalo ki raka Mamarki Masaukinta, driver zai kawo ki Gida, kuje da Matar Muhammadu".
Ba tare da ya kalli Mancy ba yace da Baban Amira "Sai da Safenku".
Mancy ta masu Sallama suka shige dayar Motar ita da Dalo da Aunty Aseey.
Suka tafi Gidan Uncle Usman, gidan Antisco.


Baban Amira ya gunguro Motarsu ya kawota gaban Asibiti, Alhaji Zaki kuma ya fada Dayar Motar driver ya ja, suna fita daga Asibitin baki daya ya fashe da wani irin Kuka.
Yafi 1hour yana rike kukanshi, yafi 1hour yana son kukaye bakincikinshi, yafi 1hour daya yana son samun salama ta hanyar kuka.
Driver ya dan tsorata yace "Alhaji"
Alhaji ya goge hawayenshi yace "ka hau Machine ka tafi Gidanka" driver ya bi umurni.


Da ya tuna abunda ya ma yaranshi shekaru kusan 4 da suka wuce sai ya fashe da kuka mai tsuma zucia.
Shafa'atu itace ta rabashi da dukkan wani farincikin shi, sai da yayi kuka son ranshi kamar wani dan k'aramin yaro kafin ya ja Mota don isa gida kafin Dalo taje ta iske baya nan.
*****


Bata da damuwa don ta san aikin da Mallam ya mata ba zai taba karyewa ba, ta yaya ma zai karye? Don Er Rabi ta yi barazanar fasa wata er k'ok'o sai ta tsorata ta karaya? Haba dai, Aikin da akayi shekara 15 ana yinshi? Ai bata da haufi har yanzu Alhaji Ali na bayan tafin kafarta zata takashi ta murje hannunshi ba tare da komai ya faru ba.
Ita ba komai ya bata haushi ya bata mata rai ba irin yanda Hajia Er Rabi ta tona mata asiri gaban mutane, yanda Diyarta ta tsareta da tambayar in ita diyar bokace, ita Er Rabi zata ma haka? Aiko zatayi mugun nadama, don wallahi sai tayi maganinta.


Yana isa Gida yaga Motar Shafa'atu.
Lallai matar nan bata da kunya, mai ta dawo yi? Ko kayanta tazo kwashewa?".
Tsayawa yayi a bukka yana jiran Zuwan Dalo, kusan 20 minutes sai ga ta ta iso Driver ya sauketa.
Ta shigo tace "Baba ya baka shiga ciki ba?"
Ya murmusa yace "ke nake jira"
Tace "to mu shiga".
Yace "ina Matar Muhammadu?".
Tace "ta shiga dayan gidanchan kwaso yaranta".
Baba yace "Halimattus Sadiya".
Dalo ta kalleshi da sauri, da wayonta bata zaton ya taba kiranta da sunan nan.
Yace "Baba Mutumin Banza ne ko? Kin tsani Baba ko?"
Da sauri ta rufe mishi baki tace "Baba donAllah kar ka fara, kar ka fara".
Yace "Sadiya, ban kasance Uba nagari a gareku ba, na wofintar daku, na fiffita bare a kanku, na zabi wasu a kanku, na laanceku, na zalunceku, kuyi hakuri, ku yafe ma tsohon banzan nan".
Dalo na kuka tace "Haba Baba, meye haka kakeyi? Wallahi wallahi ban taba tsanarka ba a rayuwata, kai Mahaifinmu ne, mun son kai mai son mune, kar ka bari komai ya tsaya maka a rai, mun san komai da ya faru ba yin kanka bane, asiri gaskia ne, yayi tasiri a kanka, wallahi ko kadan ban rikeka a rai ba ko a da, na dauka hakan kamar fim ne a shafin rayuwata, fim din kuma ya kare, Babana ya fi na kowa kuma ina sonshi fiye da kowa".
Ta ja hannunshi suka shige Gida ba tare da barinshi yayi magana ba.


Suna shiga Gidan suka ga Shafa'atu zaune kan kujera tana karkada k'afa.
Tana ganinsu ta mik'e tsaye.
"Alhaji wani irin iskanci ne zaka dade a waje kuma yanzu ka dauki Sadiya? Uwar me zata mana? Ba ta koma gun uwarta ba".
Wani Mari da ya mata ta rantse taga taurari kusan dari lokaci daya.


Cikin k'unanrai yace "baki da kunya Shafa'atu, kunya bata isheki ba, har kina iya dawowa Gidana?".
A tsorace da fargaban da zuciyarta bata gama aminta dashi ba tace "ni zaka mara? Nan ba gidan aurena bane? Ina zani!".
Yace "Ke Jahila ce wallahi, to in sai na miki gwari gwari, daga lokacin da Asirinki ya tonu, aure ya kare tsakaninmu, ki fitar min daga Gida".
Aiko da sauri ta fita, ina ta ga ta zama? Ai chan zata nemo hatsabibin boka ya kashe mata Er Rabi, ya mallake mata Alhaji Ali, ba zata dawo gidan nan ba, sai ta mallake Alhaji Ali kaf dinshi".
Bata bi ta kan Annah ba da ke ta kwala mata kira.
Annah ko ta dinga binta kamar Jela.
^****^


Jawad kam tun da ya bar Asibitin bai koma ba, a daren rannan ya yanke ma kanshi hukuncin rabuwa da Labiba.
Aure? Ba zai iya aurenta ba ma, bayan ya san ga wanda take so, ai babu ma maganar aure, ba zai yiwu ace ya aureta amma zuciyarta da ruhinta suna wurin waninsa, gwara ya barta ta auri wanda take so, shima Allah ya hadashi da nashi, Allah ya hada kowa da rabonshi.


A Gidan Er Rabi.


Sam ya shiga dakin Uwargijiyarshi don yaji ta shiru, kwance ya ganta shameshame kan carpet kumfa na fita daga bakinta.
Ga wani magani a hannunta cikin er kwalba da alamu maganin ta sha.
Ajali ne yazo? Kashe kanta tayi? Lokacinta ne yayi? Allahu Aalam, ba wanda ya san mai ya kashe Er Rabi.m
Shi dai Sam ya bude Wardrobe dinta ya dau abunda zai dauka ya cika wa bujenshi iska.




Bayan Barinsu Gidan Alhaji Ali, Gidan k'awarta Hajia Clean suka tafi, ta gaya mata yanda Er Rabi taci amanarta, Hajia Clean tace karki damu, ni ai bana zuwa ma Er Rabi da matsalata, ina da bokana aikinshi kamar yankan wuka ne" donAllah muje ki rakani".
Tace "ki bari gari ya waye, dare yayi fa".
Tace "aa wallahi, da zafizafi ake bugun karfe, so nake na ci uban kowa wallahi".
Tace "kina da kudi?"
Tace "ina dashi a account".
Tace "kwaso su tas, yanda zai miki aiki da kyau".
Tace "Annah ta zauna a nan, zataje ta dawo".
ATM tayi ta zari makudan kudin a bankinta, tas ta kwashe kudin. Ta koma gida Hajia Clean.
Hajia Clean ta dauketa suka hau kauye chan gaba da Ajiwa.
Boka sarkin k'arya har bayan kwana sukayi wai yana aiki sai wurin karfe 12 na safe ya gama aikin, sai da ya karbe mata kudinta, ya bata wata 'yar hoda yace da ta shafa shi gaban goshin Alhaji Ali Zaki to ko kisa kika ce yayi sai yayi.
Da murna suka koma.
.....
A daren Jiya Alhaji Ali baiyi bacci ba, zuciyarshi zafi take, zai iya rantsewa ya kamu da hawan Jini.
Da farar Safiya aka kawo musu breakfast, Alhaji Ali ya umurci Dalo da tayi wanka zasu fita.
Bayan tayi wanka suka fita hannu rike da juna.
Gidan Mahaifanshi ya fara zuwa.
Da mamaki aka dinga zuwa daki daki aka tada masu bacci aka sanar dasu ga Yaya Ali yazo.
Nan da nan gida ya kaure da Yaya Ali ya dawo garesu, cikin lokaci k'alilan, dangi duk suka zo gidan, don yin barka.
Alhaji Ali ya ba 'yanuwanshi Labarin abunda ya faru.
Su Aunty furera sai da sukayi kukan jin dadi suka dinga tsine ma shafaatu.
"Wallahi Yaya da Police station ka sa aka kulleta, Shedaniya ce, barin irinsu masifa ne".
Yace "Bakomi, Allah zai mana Sakayya".
Ya nemi gafararsu suka ce bai musu komai ha, tunda ba yin kanshi bane.
Ya dade tare da Danginshi, ina zaa saka dashi da dalo akeyi, kowa na son ya burgeshi, nan da nan aka fara cika cooler don zuaa ganin Zaid ya gaya musu Zaid baiji dadi

Please Login or Register in order to submit comment