Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

numfashin da nake ja ina saki, na san kina sona, ba sai kin sadaukar min da ranki ba, ba sai kin min haka ba, beebs donAllah ki bari, na rok'eki da Allah".
Labiba ta kyafta idanuwanta so biyu tace "Ina Sonka Sabida Allah, abin Alfahari na ne ace yau akwai ni a jikinka, in Allah ya sa an dace, zamu rayu tare, in ba haka ba, zamu mutu tare".
Yace "kinsan hakan na nufin kin kashe kanki da kanki, kinsan hukuncin wanda ya kashe kanshi?".
"Ni ba haka nake nufi ba, Allahn da rai na ke hannunsa ya san Zucia na, ya san niyyata, zaa dibi Hanta ta a dasa maka, end of discussion ".


Kyaleta yayi ya runtse ido tare da juya mata baya, gwalo ta mishi tare da maida hankalinta kan k'ofar da aka turo.
Dr Habib ne, Dr Ali yace "za a tura kudin Surgery account din Asibiti before a shiga da shi Operation Room".


Labiba ta dan kalleshi tace "Ohh, I thought Government Hospital ne, gwamnati ba ta biya ba?".
Dr Habib ya kalleta, yana son Confidence dinta yace "Gwamnati na dai tallafawa, amma ai ana biyan Aiki, ba kamar private hospital ba, sosai ba zaki hada kudin da na chan ba, akwai sauk'i rangwame sosai".
Tace "Okay nawa ne?".
Yace "ga takardan nan kije bursary department, ki basu zasu baki bank details da transaction slip ki biya sai ki kaima cashier ta baki receipt dai ki kawo mana".


Zaid na jinsu yayi lamo, hankalinshi ya dan kwanta, ya san bata da kudin da zata biya, ko da 20k ne balle ya san sai ya fi.
Direct chan ta nufa da taimakon sign boards.
Ta bada slip din, a computer akayi danne danne aka mata printing.
Expenses din naira dubu dari uku da saba'in.
Gaban Labiba yayi mugun sarawa.


Chabda, in ba a biya kudin nan ba zata iya rasa Zaid ko? Aikam ba zata iya jure rashinshi ba, ya kama ko meye zatayi don ta samo kudin nan, dakin Ta koma hankalinta a dan tashe.
"Kanaji ba?".
Banza yayi ya kyaleta.
Tace "Masoyin, na fa san ba bacci kake ba".
Ya juyo fuska daure yace "Meye?".
Tace "Wai kudin Aikin 370k".
Yace "Alhamdulilah, your Liver is safe".
Tashi tayi tace "kayi ka gama, zan je neman taimako".
Yace "Ina? Tace ko ma ina ne, ko bara ne i will do it, but ganin bamu da time zan rok'a su mana bashi zamu biyasu".
Zaid kallonta kawai yakeyi, sonta na tsaga hantarshi mai ciwo, komai nata na burgeshi, wautarta na kayatar dashi.
Cikin wasa yace "ke kika aje su da zasu miki aiki Kyauta? Ohh bashi kika ce ko? Tsoron ki sukeji Ko?".
Ganin yana son maida abun wasa tace "ka yi ka gama, banda lokacin wannan yanzu barin je in ga Dr Ali".


Har ta kai gaban k'ofa ta choge ta tsaya, mai ta tuna oho, maida kofar tayi ta rufe ta dawo cikin Dakin Zaid na kallonta.
Mai take shirin yi?
Wayarshi ta dauko ta kunna, har tayi 19%.
Har gabanshi ta tako ta dauki yatsarshi ta dangwala a wurin thumbprint wayar ta bude.
Hoto yaga ta daukeshi kusan guda uku, kafin ta dauki takardan hannunta hoto.
Kallon Mamaki yake binta dashi.
Matsawa tayi dan gefe amma yana kallonta taka danne danne a wayarshi.
Baayi minti 3 ba yaji wayar tayi ringing.
Amsawa yaga tayi ta sa wayar a Kunne.


Tana jin muryar ta san hankalimta a tashe yake "Hello? Zaid meya sameka? Me ya faru?".
Labiba ta amsa a ladabce "Assalam Alaikum Mancy, Sunana Labiba Ahmad Dakata".
Da sauri Zaid yayi yunkurin tashi amma ya kasa.
Mancy tace "wacece ke? Me ya samu Zaid? Ina yake?"
Labiba tace "Ya na bukatar Emergency Open Liver Transplant Surgery".
Kusan da karfi Mancy tace "Lahaula wa la kuwatta illa billah, Zaid din? Me ya sameshi haka?Liver Transplant fa kikace"


Labiba tace "Emergency ne,Hantarshi ya fara damage, suna so a cire infected area a saka wani, an samu donor, amma ba a samu kudin Aikin ba".
Da sauri Mancy tace "DonAllah zan kiraki, Ina zuwa".
Mancy ta kashe wayar ta fita,dalo ta bi bayanta.


Wai Beebs ke baa gaya miki magana kiji? Ba kya jin maganata ko? Ba a isa a hanaki abu ba ko?".
Kulle idonta ta tayi ta bude, murya ta sassauta tace "ya kake so ayi?".
Shima ya saukar da murya yace "kar ki wahalar da kanki, ki bar Hantarki, Hanta fa ba kamar k'oda bane, aka samu matsala, akwai yiwuwar daga ni har ke babu mai tsira".
Tace "to ai yafi nayi ta zaman jiran gawan shanu, yafi ace na zauna banyi komai ba, yafi ace na kasa taimaka ma wanda nikeso, donAllah mu bar maganar nan, Mancy tace zata kirani".


Zaid yace "Beebs ba kya jin magana".
Ta murmusa tare da mikewa don amsa kiran Mancy tace "nima ina sonka".
Harara ya galla mata ta fits tana daria.


Alhaji Abu Shamsu ya karbi wayar yana magana da Labiba, itama Office din da ta bar Dr Ali da Dr Habib ta nufa, ta ba Dr wayar, nan ya ma Alhaji Abu Shamsu bayani, da cewar an samu Donor wani bawan Allah, kamar yanda Labiba tacr musu su ce.
Alhaji Abu yayi ma Dr Ali Transfer din kudin, tare da basu go ahead din yin aikin.


Hankalin Mancy da Dalo ya kasa kwancia, sun kasa daurewa sai kuka suke, Alhaji Abu yace "Ku shirya ku bi jirgi gobe, sai Jawad ya rakaku".
Mancy ta dan ji sanyi, don gobe da sassafe zasu tafi, duk nadama ta mata katutu, bata ganin laifin kowa sai nata, itace sila, da bata barsu a Kt ba, da baiyi shaye shaye ba, da bai jama kanshi cuttutikan zamani ba, laifinta ne, in ta rasa Zaid yanzu bata san ya zatayi ba.
Alhaji Abu ya cigaba da kwantar mata da hankali yace "InshaAllah komai zai wuce, zai warke, Allah zai tada kafudunshi.


Bayan an gama komai ance su shirya kasancewar taci Abinci shima yaci suka kara 5hrs kafin su yi aikin, sai gab da Asuba zaayi aikin.
Zaid ya dan runtsa, ita kam ta fito waje.
Zama tayi kan kujera tana tunani.
Tsoro ya dan kamata, data ga dai dagasken aikin zaayi, ba zata fasa abunda tayi niyya ba, ba kuma tayi nadaman zuwa katsina ba, amma In bata rayu ba bayan aikin? Ya kenan? In ta mutu fa? Iyayenta fa, ya kamata ta nemi yafiyarsu, gwara su san halin da take ciki k'ila adduarsu ta bita.
Da sauri ta kunna wayarta ta ga messages da yawa bata bude ko daya ba, ta shiga create message ta hau typing, tana yi tana kuka, ta kusa daukan minti talatin tana yi kafin tayi marking ta tura ma Maminta da Abbansu.
Sai da ta tabbatar sun shiga kafin ta kashe wayar.


E D O


Cirko Cirko sukayi, Mami har tayi kuka ta gode Allah, ba wanda bai zo ba, kowa tambayar kanshi yake ina Labee ta shige.
Da yawa sun zata kidnapping Labiba akayi, Amma kidnapping har gida? Ko ta fita baa sani bane suka ganta suka sace, maganganu kala kala dai, kowa da abunda yake sak'awa.


Message ya shigo ma Abbansu lokacin wayar na hannun Abba yana amsa gaisuwar jaje da ake kira ana mishi.
Da dan murna mai sauti yace "Labee Ce, Labee ta yi sak'o".
Tuni aka yayyabeshi aka zagaye shi kowa na son jin meye a cikin message din.
Abba bai yi boko ba amma ya iya karatun hausa da k'arfi ya fara karanta message din


*"Abbanmu da Maminmu, zan fara da neman yafiyanku, ku yafe min don Girma da darajan Allah, kar kuyi fushi dani, ku saka min Albarka danAllah Abbanmu da Maminmu, yanzu kuce Allah ya miki Albarka Labee"
Abba ya kalli Mamin a tare suka ce "Allah ya miki Albarka Labee".
Abba ya cigaba da karantawa *kunce? Yauwa".*


*"Allah ne shaida, kun min tarbiya kun nuna min So amma na muku laifi babba, na fita bata da saninku ba, nayi abunda mutane da yawa zasuyi tunanin banda mafada ne ko banda magayanmasu min fada, na manta da halin da zaku shiga, na tsallake na fita, na san hankalinku dole ya tashi, to wallahi ina Katsina, eh fa Katsina na zo ni daya".*
Nan duka parlorn suka dau sallalami.
Ja'ira ashe Katsina ta tafi.
*"Kuyi hakuri, kuce Allah ya shiryaki Labee" Abbansu ya girgiza kai cike da takaicinta yace "Ya Allah ka shiryaki Labee" ya cigaba da karantawa "yauwa kunce?".*
*"To, Wallahi Abbanmu, nazo Katsina naga Zaid baya da lafia, bansan yanda zan muku bayani ba, amma wallahi baida lafia sosai, Hantarshi ta baci shine ake neman wanda zai taimaka a diba nashi a dasa a nashi, shine ba a samu wanda zai bashi ba, shine fa nace a diba nawa".*
A tare suka "Lah Illah ha illallah Muhammadan rasulillahi sallalahu alayhi wa salam".
Mamin wani jiri taji ya debeta.
Da kyar Abban ya iya mik'a ma Yaya Haruna wayar ya cigaba daga inda ya tsaya.


*Gabanku ya fadi? "DonAllah kuce Inalillahi wa ina ilaihir rajiun*".
*donAllah kuyi hakuri, bansan me zanyi bane, taimakon da zan iya mishi kenan, ku sakani a addua, bansan ko zan tashi ba bayan aikin, bansan ko zan rayu ba, shiyasa nace barin sanar daku, ku sanyani a addua, in akwai abunda nafi yarda dashi a rayuwan nan wallahi be wuce Adduarku ba, ku min Addua Iyayena, in na mutu ku yafe min ku sanya min Albarka, in kuma Allah ya sa na rayu in na dawo ku hukuntani wallahi, zan dauka, ni din mai laifi ce*


*"Mami wallahi dubu biyar dinki na dauka, nidai wallahi karki ce sata ne, amma dai ki yafe min, in Allah ya sa na warke, na fara aiki zaki fi kowa jin dadi a rayuwa, zan zame miki abin alfahari, kuce ma Baban Amira yayi hakuri ya yafe min, na bashin ciwon kai da yawa, Mami in mamansu Samira na miki fada ki daina mata shiru, in samira ta miki rashin kunya ki mareta, in Yaya Zaliha ta haihu ta samu mace kice a sanya mata Labiba, ace kar ta zama kamar goggonta, ta rayu da kyau, haha kamar ina bada wasiyya ko? ba fa wasiyya bace, zan dawo inshaAllah, nasan Mami zaki gurji rayuwata da dorina zaki bugeni? Ina sonki, donAllah kar hankalinku ya tashi, ku mana addua, Allah ya sa a dace, karfe 4am zaayi aikin, addua donAllah, kar ku manta, a gaida min su Samira, ina son su duka, Abbanmu Maminmu, kuce Allah ya miki Albarka Labee".*


Kafin a kai karshen Wasikar, an kira layin wayar kashe, masu raunin zuciya tuni suka fara kuka, barin ma Samira da ke kuka wiwi kamar an ce mata Labeen ta mutu, sai da Abbansu ya tsawatar, yace "kai ku kwashi iyalanku ku koma gidajenku, ku kuma ku wuce ku kwanta".
Ba wanda ya iya cewa komai aka fara fita daya bayan daya.
Yaya Hajara wanda mamarsu daya da Labiba ta rik'o hannun Mami ta jata zuwa dakinta.
Mami ta ci kuka sosai, ranar batayi bacci ba tana kan dardumarta tana kai kukanta ga sarki mai Sama, Allah ya raya mata diyarta ya kareta a duk inda take.


K A T S I N A


4:40am


Batayi bacci ba itama, Zaid dinne yayi gyangyadi ya farka, har nurses suka shigo dauke da kayan da ake ba marasa lafia su saka in zaa musu aiki.
Labiba ta amsa Zaid ya mata Alama da ta zo taji.
Matsowa tayi da kunnenta daidai bakinshi.
Yace "beebbs, kina da halin chanza hukuncinki, kina da halin cewa kin fasa, ki chanza tunani kafin ki makara".
Labiba tayi murmushi tace "ni dai na gama magana, ina kan bakata".
Zaid ya girgiza kai yace "Allah ya shiryaki mai taurin kan tsiya".
Daria tayi sosai tace "Nima ina sonka Masoyi".
Ta shige toilet.


Jim kadan Labiba ta fito daga toilet sanye da kayan theater, murmushi tayi data ga an chanza ma Zaid irin kayan sunyi anko, gadon gefe da aka tanada don ita ta hau, nurses kam suka gungura Zaid da Labiba a kan Gado zuwa Operation Room.
Kowacce Adduar da yazo bakin Labiba yi takeyi.
A cikin OR idanunsu akan junansu bacci ya kwashesu sakamakon allurar da aka musu ta


Drs suka dukufa kansu suka farka su sukayi duk wani abunda suke bukata cikin kwarewa kafin suka dinkesu.
A zahirance aikin ya tafi daidia, zaace it's successful sai a jirayi farfadowansu..
%%^^


Ana Sallahr Asuba Mutanen Edo suka shiga Mota, Baban Amira ne da Abbansu da Mami, da an biye ma Mutanen Gidan, sai kowa ya bisu, Maminma da k'yar Abbansu ya yarda ta biyosu, wani tsohon direban Abbansu ke tuka motar a Golf din Abbansu.


Su ko mutanen Abuja karfe 9 jirginsu ya tashi daga Abuja zuwa Kano, daga Mancy sai Dalo sai Jawad, Abba yace in basu dawo zuwa jibi ba zasu biyosu.
Da suka isa Kano Yaya Usman Yayan Mancy ya zo ya dauke su a Airport.
Sai da suka biya Gidanshi kafin ya ba Driver Mota ya kawo su Katsina basu tsaya ko ina ba Sai General Hospital.


Ba su sha wuya ba suka gano Dakin da aka kai Zaid da Labiba bayan am fito da su daga OR.
Basu farfado ba nurse ta sanar dasu.
Mancy tace "DonAllah zan shiga in ganshi".
Nurse tace "da dai kin bari sun farfado".
Mancy ta matsa, nurse ta bata umurnin shiga ita kadai, tana shiga ko ta saka kuka ganin yanda Zaid yake kwance lifeless, gefenshi ta kalla ta ga wata yarinya kyakyawa kwance itama a dayan gadon.


Mancy sosai ta ke jin haushin kanta, ba zata daina jin laifinta bane, itace sila, itace ummul abaisin shigan Zaid wannan yanayi, da bata barsu ba, da bai tagayyara ba haka, da kyar ta iya fita daga dakin.
Ta dawo inda su Dalo da Jawad ke tsaye.
Jawad yace "Mancy muje Gidan Uncle Usman muyi Sallah mu ci Abinci, in yaso sai mu dawo Anjima".
Mancy ta girgiza kai tace "Aa Jawad, bana jin zan iya tafiya na bar Zaid, zan jira ya farfado, ka tafi da Sadiya".
Dalo ta mak'e kafada tace "zan jira farfadowan Yaya Zaid".
Jawad yace "To bari naje Gidan, zan taho da Abinci, naga famfo chan kuyi Alwalla kuyi Sallah, sai na dawo".
***


Hudu ne a Gidan Hajia Er Rabi don yi mata gaisuwan Yasmin.
Ya shiga Parlon yana ta tafka uban Sallama, muryoyi yake ji amma zai rantse ba na Mutane bane.
Tashi yayi zai fita yaji an daka mai tsawa.
"Hudu, Shafa'atu ta tarwatsa min farincikina, Shafa'atu ta sa na rasa Farincikina, wallahi sai ta gwammace bata shigo duniyan nan ba, sai tayi nadamar sani na, ta jirani kawai".
Yanayin yanda ake maganar ya sa Hudu fita gidan a Guje fitsari na bin wandonshi.


Yanda ya koma Gida hankali a tashe ya tabbatar musu cewa ba lafia, Shafa'atu tace "Wai Hudu uban me ya sameka? na lura tunda ka so danne Dalo ka fita hayyacinka, duk ka zama wani lusari, barinje Jifatu na dawo".
Ya bita da ido, Annah ta galla mai harara ta wuce dakinta.
Yafi minti 10 zaune kafin ya tashi
ya nufa dakin Alhaji Zaki.
Dakin yaji a kulle, sai ya fada dakin Yayarshi.


Direct Wardrobe dinta ya nufa.
Ya bude yan kunne da sarkanta zinari ya kwashe kusan set 4 ya zurasu a wando.
Yayi 'yan bincike bicinkenshi duk abunda ya gani wanda zai kawo mishi kudi sai da ya dauke, kudi kau ya kwashe tas kusan 200k.
Ya samo leda ya cikashi da karikitai ya fita.


Ya fita jikinshi na bari.
Ya hadu da Anna, tace "Uncle Hudu ina zaka da kayan Mummy?".
Banza yayi ya k'yaleta, tayi saurin rikoshi, ya juya ya mareta tare da sake mata nushi a ciki dama ya dade yana jin haushinta.
Tana kaiwa kasa ya fita a guje, maigadi na mai magana yayi banza dashi, saarshi daya ya ci karo da dan Achaba a kofar Gida ya hau yace "muje kawai".
**


Shafa'atu ta shigo gidan a fusace sakamakon kiran da Annah ta mata tana ambaton sunan Hudu.
"Wallahi Hudu kace zaka ma Annah Tumasancin da kakeyi sai naci ubanka, in wannan tsohuwar ta kyaleka ni ba zan kyaleka ba, ina Hudun yake?".
Annah da ke rik'e da kumatunta ta na kuka tace "Mommy Uncle Hudu ya kwashe miki kaya, duba dakinki ki gani".
Hankali tashe ta shiga dakin kamar zata kife, maajiyarta ta gani a hargitse, ta dubata ga babu kudinta, babu zinarints, babu duk abubuwa masu mahimmanci, wani ihun sunanshi tayi "Huduuuuuu, ni zaka ma Sata? Wallahi sai na kasheka".
Wayarshi ta shiga nema tana kiranshi amma baa dauka ba, daga karshe taji wayar a kashe.
Sosai hankalinta ya tashi domin tas Hudu ya yasheta, bata da komai a dakin, huci take kamar kura cikin fushi tace wallahi ko birnin sin kaje, sai na sa Er Rabi ta dawo min da kai, shege butulu mara godian Allah".


Garin zai bari, zai je ta fara rayuwa inda ba wanda yasanshi.
Bank ya nufa ya ciro kudi kafinya wuce Tasha ya hau Motar Kano.
A kano ya sayar da sark'okinshi a wulakance a wurare daban daban.v


Jawad ya dawo Asibitin wurin k'arfe 3 da coolern Abinci.
Zaune ya ga Mancy kan wata tabaarman da bai san inda ta sa mota ba, Dalo kuma na kwance kan cinyarta.
Jawad yace "Bai farfado ba? Mancy ta gyada kai alamin eh, yace "to ga Abinci kuci, Antisco na gaidaku tace "inshaAllah in mutane sun ragu zata zo ganinshi".
Mancy murmushin karfin hali tayi tace "Yaya jikin Uncle Usman din?".
Jawad yace "ah da sauki yace ran Monday zai fara Azuminshi".
Tace "Allah ya k'ara Sauk'i".
Yace "Ameen, wai wannan barci take?".
Mancy tace "Eh bacci takeyi".
Tsugunno yayi kusa da ita a hankali yace "Sadyy, tashi ki ci Abinci".
Bude ido tayi ta zube kanshi.
Mancy tace "Oya tashi kuje chan ki ci Abinci kinji Dalo?"
Baki ta turi cike da Shagwabab ta tashi.
Jawad yace "Mancy ke fa?"
Tace "Jawad, wallahi ba zan iya ba, bari dai Zaid din ya tashi".
Jawad ya kada kai ya bi bayan Dalo da ta fita daga Amenity zuwa wani wuri da aka tanada don fira.


Yace "Oya zuba kici"
Dalo ta shagwabe fuska tace nifab na k'oshi, banson Mancy tayi magana ne kawai amma wallahi banjin yunwa".
Hararta yayi yace "baki isa ba".
Ya bude coolers din ya zuzzuba mata a plate yace "Eat".
Zata yi magana ya sha mur yace "ina wasa dake? Ki cinye duka ko na miki dure".
Shagwabe fuska tayi tace "Ya Jawad ba fa haka akeyi ba".
Ya harareta yace "haka akeyi, eat up".
Murmushi tayi ta sa hannu tana cin abincin, shi ko Jawad kallonta kawai yake yana mamakin yanda yake sakewa gabanta.


Sai da yayi Sallahr Laasar kafin ya shiga Asibitin.
Suma zaune suke kan tabarma, Dr da nurses suka ga sun nufo dakin da Gudu.
Mancy tayi saurin mikewa ta rufa musu baya.
Tana shiga ta ga idonshi a kan nata
"Alhamdulilah Zaidu na ka farfado".
Ta nufeshi da sauri ta rungume yana a kwance ta shiga kissing dinshi cikin jin dadi, Dalo ma ta rukunkume yayanta tana kuka.
Shidai yana kwance yana binsu da ido.
Nurse tace kuyi a hankali kar ku fama mishi aikin da akayii.
A galabaice yake kallonsu, ya ma Dr Ali ido da yazo yaji
Dr Ali ya matsa tare da daura kunnenshi saitin bakinshi.
A wahalce yace "Labibaaa".
Dr yace "Sorry bata farfado ba, Alluran bai saketa ba".


Mancy ta kalli Labiba da ke kwance kamar Matatta takawa ta farayi zuwa gadonta tace "wai itace ta yi donating Liver dinta?"
Dr Ali yace "Eh itace, ta damu jiyan nan har sai da dai aka yi Aikin nan".
Dalo ta matso wurin tace "Lahh Mancy, k'anwar Mallam Muhammad ne".
Mancy tace "Wa?".
Dalo tace "Makwabcinmu, Mijin Aseeyah".
Mancy tace "yana da kanwa ne?".
Dalo tace "eh daga garinsu ta zo karatu ne".


Jin haka ya sa Jawad yin sauri zuwa gadon idonshi ya gane mishi Labiba.
Gabanshi ya fadi, yayi saurin kallon Zaid da yake kallon gadon amma baya iya komai, ya hango hawaye kwance a idon Zaid.
Jawad yaji jiri na dibanshi.
Da bango ya jingina.


Mancy tace "Dr, akwai wanda yazo gunta?".
Dr yace "anya kuwa babu fa".
Mancy tace "to ya haka?"
Chan ta mik'e tsaye tace "ko dai ba su sani ba? Kar dai yarinyar nan ta bada Hantarta ba btare da sanin Magabatanta ba?".


Dr ya k'ara da cewa "Gaskia bana tunanin sun sani, ita kadai tazo jiya, ta sha kuka, ta kuma nace kan sai anyi aikin cikin gaggawa, nikuma gaskia i had no choice saboda i was desperate to help my friend recover, shiyasa mukayi operating kanta".
Mancy tace "Without consulting her Parent or Guardian? Is this how you do things here?".m
Ganin Ran Mancy ya baci ya sa Dr Ali yace "Sorry, amma she's an adult, ita ta zabi hakan".
Mancy tace "Dubeta Yarinya ce fa, banji dadi ba gaskia sam".
Dr Ali ya ma Nurses ido suka fita shima ya sabe don ya saba dokar Asibiti.


Mancy tace "Sadiya zo kije Gidan Mallam Muhammadu donAllah kice yazo Asibiti, kira Drivern, no ba time ki hau keke napep".
Sadiya tace "to ta fita".
Mancy ta rik'o hannun Labiba tana jin Son Labiba na ratsa duk wani bargo na jikinta.
Zaid kam baida karfin yin komai,hawaye kawai ke sintiri a idanunshi.


Dr Ali ya sa nurses maida Zaid Amenity tunda ya farfado, aka gungurashi kan Gado aka bar Labiba a ICU.
Dalo ta bi gadon Zaid.
Mancy kam ta tsaya tana leken Labiba ta window don ba a so ana shiga ICU.


Jawad kam bai san mai ke mishi dadi ba.
Duk wani karonsu da Zaid ya shiga dawo mai, sai yanzu ya gane, ashe Son juna suke? Ashe kishinshi Zaid yake in ya ganshi da Labiba yayi ta wasu abubuwa."
Itama Labibar, Wani irin so take mishi haka? Da zata sadaukar mishi da rayuwanta.
Haaa ga matar da zai aura kwance magashiyan rai hannun Allah, matar da zai aura ta ba Saurayi Hantarta, saurayin ma wani bashi ba? Lallai akwai matsala, akwai babbar Matsala".
Yana ganin wucewar Dalo, ya kasa binta domin jikinshi yayi sanyi sosai.
***
Sadiya ta isa Anguwarsu, ta dade tana kallon Gidansu, kafin ta shige Gidan Mallam Muhammadu da Sallama.
Aunty Aseey ta fito da Amsa sallamar tana wata kamar Dalo.
Dalo ta murmusa suka gaisa.


Tace "ya Abuja? Ance kin koma chan".
Dalo tace "Eh,Aunty Aseey Baban Amira fa?".
Tace "yana chan Edo fa".
Ta yi shiru, da dukkan alama ba su san meke faruwa ba.
Aunty Aseeyah tace "Lafia kuwa?".
Dalo tace "Mancy ce ta aiko ni, Labiba na Kwance a Asibiti".
Aunty Aseey tace "wace Labibar?".
Dalo tace "Labiba taku".
"Ban fa gane ba, Labibar mu ai tana Edo".
"Aa ta na nan, a Asibiti, an mata operation".
Cikin rashin gamsuwa tace "tsaya kiga na kira miki ita".
Aunty Aseey ta kira number Labiba tajita kashe, tace "barin kira baban Amiran".
Da kyar ta sameshi. Yana dauka suka gaisa tace "Ina Labiba wayar ta be shiga".
Yace "Afuwan Asiya, ban kiraki ba, gamu nan a hanya, inshaAllaj kafin Maghrib mun iso Katsina".
Tace "kai da wa? Da Labiba?"
Yace "Aa, da su Abba da Mami".
Tace "Labibar fa?".
Tana jin karaya a muryarshi yace "Asiya Labiba na nan Katsina, sai munzo zakiji komai".
Aunty Asiya ta kalli dalo, ta amince da maganarta tace "ga Dalo nan tazo wai Labiba na Asibiti wai har operation an mata, meke faruwa Baban Amira? Dama Labiban bata da Lafia?".
Da sauri yace "Wai har anyi? Wani Asibitin ne?"
Ta tambayi dalo, tace "General Hospital".
Yace "Ga mu nan InshaAllah sai munzo".
Ya kashe waya.


Aunty Aseey tace "me ya faru da Labeen? Menene?".
Dalo ta warware mata zare da abawa.
Da gudu da shiga daki ta fizgo Hijabinta ta ciro mukullan gida tace "Muje, dalo muje".
Tace "Yaran fa? In sun dawo?"
Tace "muje in sun ga gida kulle sa shiga makwabta, inallilahi Allah ka tashi kafadar Labiba, wallahi Labiba bataji".
Ita dai Sadiya bata tofa komai ba suka hau Napep suka nufa Asibiti


Suna Isa Asibitin Mancy ta rungume Aunty Aseeyah.
Ta window aka nuna mata Labiba
Kuka take tace "Wallahi Aunty Maryam Labiba bata jin magana, babu yanda ba ayi ta rabu da Dan makaho ba amma ta ki ji, daga Edo fa ta saci hanya tazo, zataci ubanta na sani, bari su Abbanmu su zo".
Mancy dai yak'en dole takeyi, ta na jin yanda ake kyamar danta kamar wani mai najasa, da alamun Asiya ta manta wacece ita a wurin Zaid da batayi wasu zancen ba.
Mancy tace "ni in ga ta farfado ya fi man komai, ta farfado ko meye zai biyo baya".
Suna zaune jigum jigum.


Gidan Kakansu Jawad ya wuce, bayan sun gaisa ta tambayeshi sanadiyar zuwa, ko wannan karon ma budurwa aka zo gani, dan tsaki yayi yace "wace budurwa? Yaron Auntynmu akayi ma Aiki dashen Hanta, shine na rakosu, Abba bai kiraku ba? Suna General a ICU be san surutu ya shige chan k'urya yana ta fira da zuciyarshi.
Kakar tashi ta kira Abba ya kara mata bayani, haka tayi ta kiraye kirayen wayan 'yanuwa ta na cewa suje su dubo Dan Mancy a Asibiti.
Da yawa 'yan Anguwan Alk'ali sunje ganin Zaid amma an hanasu ganinshi saboda yau ya fito daga OR, zasu iya stressing dinshi, saidai su gaisa da Mancy, su koma, sosai su ka ma Mancy kara a matsayinta na

Please Login or Register in order to submit comment