Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba zan sake wanen kuren ba, da ku zan tafi, tuni maigidana yake son hakan".


Zaid yace "its too late Mancy, zan Zauna a Gidan Ubana, zan zauna har sai ya dawo hayyacinshi, zan zauna ya dawo hankalinshi yace Zaid Allah ya maka Albarka, in hakan bai faru ba, zan mutu a Gidan Ubana, wata k'ila in ya ga Gawata ya mun Addua".


Bata gane mai yake cewa ba tace "ZAIDD".
Share mata hawaye yayi yace "Maigidanki na jira, ki tafi Mancy, ga Dalo nan ki tafi da ita".
Dalo ta koma gun Zaid ta rungumeshi tace "ba zakaje ba? Ba zanje ba nima".
Zaid ya murmusa yace "muje Parlor.
*
"Kutumar Uba ba Kaciya ba, Hudun zaku lak'a ma Sharri? Saboda tsana?".
Mancy ta tako gaban Hajia Shafa'atu.
Ganin hakan ya sa Nene yin shiru.

Hajia Shafa'atu tace "ke kuma wacece?".
Mancy ta murmusa tace "Hajia Shafa'atu, in har kin dauki Alhakin 'ya'yana Allah ya isar musu".
Dan baya tayi Hajia Shafa tayi, gabanta ya fadi, tsoro da tashin hankali suka bayyana, mamaki take, anya itace? Ta ga alamun kudi da kwanciyar hankali a tattare da ita, tayi k'iba ta kara kyau, ta murje abunta, baki na rawa tace "Maryama, kece haka?".
Murmushi kawai Mancy tayi.


Nene tayi charaf tace "kina mamaki ne? Ai Allah ba ruwanshi, duk zakaran da Allah ya nufa da chara, ko ana muzuru
Maryaman ce dai da kika raba da Sullutun Mijinki, tduba chan kinga wanchan Alhajin, shine Mijinta, ya fi Mijinki dattako, ya fi Mijinki kudi da kyau, kalleshi chan Fulanin usuli, dan babban Gida dan Anguwan Alk'ali, kinga ko sawun giwa ya badda na rakumi, ruwa ba tsaran kwando bane, kuma bakin rijiya ba wurin wasan yaro bane".


Nan da nan bakin ciki, k'yashi, hassada suka bayyana a fuskanta.
Alhaji Ali Zaki ba abunda yakeyi sai Kallan Maryama, bakinshi na san magana, amma bai san mai zai ce ba, duk yadda yake so ya furta wani abu ya kasa.
Master yace "ya zamuyi da dan akuyan nan?".
Mancy ta juya ta kalli Hudu, ta ga yanda akayi jinajina dashi, tace "ku kyaleshi, mun gama da nan kuma".


Hajia Shafa'atu ta fashe da kuka ta dinga jijjiga Alhaji Ali "yanzu kana gani a shigo cikin Gidanka a ci man mutunci? A wulakantani gaban yan Unguwa, a lakafa ma k'anena sharri, a mishi dukkan yan wanki, a ci mana fuska, kuma kana tsaye ka kasa cewa komai?".


Kamar wanda aka jona da Electric Shock ya fara bambamai, "Iskancin banza, uban wa yace ku shigo min Gida? Ke tsohuwar nan ba na hanaki zuwa min Gida ba? Yau sai na kori Maigadin nan". Nene tace "kai arr dallah yi mana shiru, sai wani haushin kare kake mana a nan".


Alhaji Abu Shamsu ya gyara Murya yace "Alhaji Ali Zaki, donAllah zauna".
Baba ya kalli Abba yana jiran umurni daga gun Hajjaju.
Nene tace "kai dallah zauna".
Baba ya bi umurnin Nene ya zauna a daddare ba tare da ya lura da mugun kallon da Haj Shafa'atu ke jefanshi dashi.
Abba yace "Hajiya zauna, magana zamuyi".
Cike da rashin kunya tace "ba zan taba zama da ku ba, ai kunne ke ji, yi maganarka".


Alhaji Abu Shamsu yace "hakane. Alhaji Ali Zaki, sunana Alhaji Abu Shamsu, nine Mijin tsohuwar Matarka Maryama, inda da yaram 3 da baiwar Allahn chan lokacin da na auri Maryama, tun a lokacin na buk'aci rik'on Zaid da Sadiya ya dawo guna, ta nuna min da Aa tafison Yaranta su tashi wurin Mahaifinsu, ban ja ba, to yau munzo ganinsu, muka ga k'anin matarka na niyar afka mata, Allah ne ya tsareta, to ganin hakan ya sa Thank na yanke hukuncin Tafiya da Zaid da Sadiya Gidana, ko Mancynsu na so ko bata So, daga ranar da na auri Maryama, 'ya'yanta suka zama nawa".


Burinta ne Zaid da Dalo su bar mata gidan tunda dadewa, maimakon tayi murna da jin cewa zasu bar mata gidan sai ta tsinci kanta cikin wani matsanancin bakinciki.
Barin su nan ya zama jin dadinsu ko? Zai zama sun fi Annah jindadi? Ranta ya dinga tuk'ik'i,har yanzu tana Kishin Maryama.


Tace "yanzu Alhaji yarda zakayi a tafi da yaranka? Zaa rabani da su, duk sabo da shakuwan da mukayi, barin ma Dalo da muke kwana muke tashi tare, ya zaayi a rabani dasu bayan na fi kowa sansu?" Dalo da kanta ke kan kafadun Zaid ta dago ta kalleta jin furuncin nata wani iri, wannan ko k'arya bata iya ba ma.


Kamar an jonashi "ba inda zaku tafin min da Yara, ba inda zasu, ku tashi ku fitar mina Gida".
Alhaji Abu yace "da su zamu tafi, in kuma zaka bamu matsala sai muje gaban hukuma".
Shafaa tace "Hukumar da zaka saye suyi abunda kake so?".
Alhaji Abu yace "Sarkin Katsina fa? Ko shima sayeshi zanyi? Ni na ma fi so a je gaban Sarkin, na bashi labarin komai, Ya mallaka minsu, kinga k'aninki sai a yanke mishi Hukunci daidai da wanda ya aikata".


Bubutai ta fara na borin kunya. Alhaji Shamsu ya kalli Iyalenshi yace "ku wuce mu tafi".
Jawad ya saba Mimi a jiki, Umma ta fita, Abba yace "Zaid ku mu tafi" ba gardama Zaid ya ja hannun Dalo da ke ta kakkarwa ya rufa ma Umma baya, Mancy ta rufa mai baya, kafin Alhaji Abu Yace ma Nene "Mun tafi Mama".
Nene baki har wuya tace "Sai munyi magana, Allah shi biyaka"
Ya amsa da Amin ya sa hannu ya ciro dubu 3 ya ba 'yan Bencin Eskalay.
Master ya sa hannu zai karba Nene ta fizge tace "yi tafianka Alhaji, sigari zasu sha".
"Wallahi Nene ba shi zamu sha ba".
Alhaji yayi gaba abunshi yana murmushi, shi bai taba gani tsohuwa irin Nene ba.
Nene ta galla ma su Harara ta mika musu kudin tace "Shiryayyu, ku raba, ban yafe ba kuka sha Sigari".
Suka hau shewan sai "Nene".
Sun manta da wasu halittu bayansu a gurin, suka fice suna murna.
Nene ta galla ma Shafa ta Mijinta Harara, tace ma Aisha Lema "mu tafi Maminsu" kamar jiran umurni take ta fita suna fita Hajia Shafa'atu ta bi bayansu ta rufe k'ofar Parlo ta saka Ihu.


Me ke faruwa ne? Duniyarta ta fara juya mata, Mancy ta zarce tunaninta, ta ya akayi haka, zuciyarta wani tuk'ukin bakinciki yake,me zatayi Ta huce, wani hutu da ta gani jikin Mancy ranta na sosuwa matuk'a, me zatayi? Me zatayi? Hudu ya rarrafo gun kafarta yace "Aunty wallahi karya suke min" haushi ya bata kamar ta halbeshi, ita ba wannan ne damuwarta ba, damuwarta bai wuce Jin dadin da ta gani jikin Mancy ba, tsallake Hudu tayi ta shige daki tare da rufo kofar.


Annah ta shigewarta Daki itama tana jin zafin sharrin da aka ma Uncle Hudu.
Alhaji Ali Zaki zaune kan three seater yana kallon Hudu, so yake ya tashi ya shak'eshi, amma bai san mai ke danneshi ba, tsanar Hudu ke rufeshi, amma ba zai iya komai a kai ba, ganin mugun kallon da Alhaji Ali ke mai ne ya sashi mikewa sum sum yana jan kafa ya shige daki.


A Babban Parlorn Gidan suke zaune.


Alhaji Abu yace "Ni zan rik'eku amana, duk abunda zan ma dan cikina inshaAllahu zan muku, baku da matsala dani, na tabbatar ba zaku samu matsala daga sauran mutanen Gidan ba".
Dalo dai na chan k'udundune, har yanzu ba ta dawo daidai ba, ta kan firgita lokaci zuwa lokaci, kuma a tsorace take.
Mancy sai zabga fara'a take jin furucin Mijinta a kan 'yayanta.


"Wannan shine Yaya Abdulhafiz sai AbdulMajeed sai Jawad sai Ummanku ga ta nan".
Zaid ya murmusa yace "Alhaji".
Alhaji Abu yace "Abba daii".
Zaid ya sake murmusawan yace "Abba,mungode Allah ya biyaka da Aljannah, mungode kwarai, amma ni gaskia zan tsaya nan Katsina".
Mancy tace "Zaid.."
Zaid yace "Kiyi hakuri Mancy, amma ba zan iya binku Abuja ba".
Mancy zatayi magana Alhaji ya dakatar da ita ta hanyan daga mata Hannu.
Yace "Zaid, kwanakin baya, da Allah da Annabi kake hadawa a tafi da kai Abuja, yanzu kuka kace baka so? Mai ya sa?".


Zaid yace "Abba, Mahaifina yana zaune da wata Hatsabibiyar Mace, ba zata taba barinshi ya dawo hayyacinshi ba, zata cigaba da cutanshi, ina so na tsaya a kusa dashi, tafianmu na nufin mun rabu dashi kenan, baya da wani hope din dawowa daidai, ni na san Akwai Son mu a wani Sashe na zuciyarshi, ba duka ta mutu ba, zan jira har sai wannan shashen ya mamaya sauran sassunka, zan jira har sai ya kalleni da so da kauna, ba zan bar Baba ba gaskia, na san yana nan a makale".


Duk sai da suka tausaya mai Alhaji Abu yace Allah ya maka Albarka, Allah ya dawo muku da Mahaifinku daidai, ya shiga tsakaninshi da muguwa azzalumar Mata".
Suka amsa da Amin.
Yace "Oya kowa yaje ya kwanta gobe da safe zamu wuce"
Suka amsa mai.
Umma tace AbdulMajeed ya kai mata Mimi dakinta, yau tare zasu kwana.
Abba yace "Zaid sai ka bidaya daga cikin yanuwanka gasu nan".
Umma tace "ai mai raba Zaid da Mancy yau sai Allah".
Sukayi daria, hakan kuwa akayi
Zaid da Dalo da Mancy daku daya suka shige suna firan yaushe gamo.
Har Dalo tayi bacci akan cinyan Mancy
Zaid ya ba Mancy rayuwarshi bayan rabuwarsu kaf
Sosai tayi kuka da nadama, ta kuma yi ma Shafa'atu Allah ya isa yafi cikon kwando.


Jawad ya so ganina Labiba amma ta mishi karya wai tana Dutsinma.
Be ji dadi ba don sosai ya so su hadu ya tamvayeta kan chanjinda ta mishi cikin kwanakin nan.


W A S H E G A R I


Bakinciki da Hassada basu barta tayi bacci ba.
yanda taga rana haka taga dare.
Ta kira numbern Er Rabi wayarta Kashe.
Gari na wayewa ta isa Gidan Er Rabi, sai dai Maigadi ya tabbatar mata da cewa Er Rabi tayi tafiya zuwa Agadez, gobe zata dawo.
Kamar tayi ihu don haushi, meyasa Er Rabi bata gaya mata irin tafiyar nan? Yanzu ya zatayi? Wa zai share mata kukanta? Haka ta koma Gida rai a bace, bari Er Rabin ta dawo, dole ta dinga barin mata kayan aiki incase of Emergency.
*
Gabaki dayansu suka tafi Gidan Daddy Usman don duba jikinshi da yi musu bankwana
Jikin da sauki sosai.
Suka musu sallama
Sukaje Anguwan Alkali family house.
Harda Zaid aka yi zagayen.
Daidai Tollgate na Farewell from katsina suka tsaya, duk suka firfito.
Alhaji Shamsu ya ba Zaid numbernshi da na Abdulhafiz yace "duk abunda kake so ka kirani ko ka kira yayanka".
Zaid ya amsa mishi da "to"
AbdulMajid sukayi Musabaha yace "take care of yourself bro".
Zaid yace "i surely will big bro".
Sukayi daria
Zaid da Jawad dai Basar da juna sukeyi.
Dalo kam tayi kukan rabuwa da yayanta.


Mancy ta ja Gefe tace "Zaid DonAllah kar ka sake shan World ne ko meye kuke ce mishi"
Yace "Mancy na bari".
Tace "Zan shirya yanda zaka koma School, you need to start afresh".
Wani School? Shi da ke daf da mutuwa? Shi yasan ciwo na cinshi ta ciki, amma me zai ce? Murmushi kawai ya mata".
Har saida ya bar ganin Motarsu ya tsaida Machine don tafia Gida.


Lokacin da Zaid ya shigo Gida ya yi mamakin ganin Babanshi zaune A bukka shi kadai, har zai wuce ya dai karasa gunshi ya zauna, idon Baban ya kalla yace "Ina kwana?".
Baba ya lumshe ido ya bude yace "Baka bisu ba?".
Zaid yace "ba zan tafi na barka ba Baba"
Baba zaiyi magana yaji harshenshi yayi nauyi.
Zaid yace "Na san ka nan, fight it, overcome it".
Ya tashi ya shige cikin Gida, Baban ya bi bayanshi da kallo.


Kamar Gadinshi take ta window, ta shiga da Asubar fari baya nan, dakin ma baiyi kama da wanda aka kwana ba, yana shiga daki ta faki idanuwa ta shiga.


Da mamaki yace "Beebs?".
Tace "Me ya faru da kai? Ina kaje jiya? Me yasa wayarka kashe? Mankas kayi Jiya ko?"..
Murmushi yayi yace "Good Morning Sunshine, i love you".
Hararshi tayi tace "Start Talking".
Yace "Abubuwa da yawa sun faru, Mancy Was here jiya, tazo ta tafi damu".


Murna Labiba harda tafi tace "Finally Mancynmu tazo garemu, Dalo must be happy, ta na ina yanzu?".
Zaid yace "sun wuce Abuja".
Tace "da wuri haka?".
Yace "Eh sunzo dubiya ne dama".
Ta dan rage girman idanuwanta tace "kai meyasa baka bisu ba? Baka son missing dina ai?"
Yace "ashe kingane + ba zanje agolanci gidansu saurayinki ba".
Tace "ban gane ba".
Yace " Mancy na auran Babansu Jay ne ko Kay".
Zaro ido Labiba tayi "kana nufin Mancy ma auran Babansu Jay?".
Hararata yayi yace "so kike na maimaita? To ba zan ba".
Tace "Wow, Its a small world indeed, jiya ya kirani wai yana Kt nace mishi naje Dustin Ma".
Zaid ya kashe mata ido yace "you did well".
"Ke, yau ba Sunday ba? Baban Amira ba ya nanan ba? Sai ya nemeki?".
Tace "eh fa, ba zai ganni ba".
Suna dan fira sai ga Yasmin ta kira.


Sai da ya kalli Labiba ya ga ta tsura mishi ido kafin ya Amsa tare da sa Speaker.
Muryarta ya cika dakin "Zaidun Bibbs".
Labiba ta sake wani murmushi jin furuncin Yasmin.
Zaid yace "K'amshi, k'amshi yana tashi".
Tayi 'yar daria tace "kana lafia?".
Yace "Lafia lau, Dama yanzu nake shirin kiranki".
Tace "ta samu ne?".
Yace "Albishirinki"
Tace "Goro"
Yace "Mancy came for us, tazo har ta tafi da Dalo".
Yana jin sautin dariayarta mai dauke da murna sahihhiya.
Tace "Alhamdulilah, naji dadi, Dalo na jikin Mancy right now am so sure about it".
Yayi daria tace "i need details daga farko".
Yace "i will fill you in, ga wata ku gaisa".
Labiba ta girgiza mai kai, ya gyada mata kai alamun tayi magana.


Labiba tace "Assalam Alaikum"
Wani shewa taji Yasmin tayi tana daria tace "waalaikum salam Beeeebsss dinmu oh my God kece?".
Tace "Eh Aunty Yas nice ina kwana ya aiki?".
Yasmin tace "Lafia lau, ya School? Ya kike ya su Yaya Muhammadu?".
Tace "kowa lafia lau, yaushe zaki zo?".
Tace "Yau nike call, gobe ma haka inshaAllahu Jibi Tuesday kenan, zan zo na ganki, yauwa akwai wata colleague dita da ta kawo wasu Malaysian Shoes, size nawa kike sawa? In dauko miki random colors".
Kunya ya cika Labiba tace "ki barsu".
Yasmin tace "'yar kauye, come on tell me size dinki".
Labiba cike da kunya tace "37-38".
Yasmin tace "Oh oh, na tuna fa our biebbs is a small person hahaha, to inshaAllah zan dawo miki dasu jibi kinji?".
Labiba tace "Nagode Aunty Yasmin".
Yasmin tace "abunda zakiyi kawai ki kula min da Zaid sosai, love him endlessly, take good care of him, and kiyi fushi in ya sha Sigari ko world".


Labiba da Zaid suka kalli Juna, idon Zaid ya cika sosai da ruwa, ya kawar da kanshi, har yanzu yana jin Yasmin a ranshi sosai, soyayyar da take mishi mai tsafta ce, ita burinta kawai Zaid ya samu Farinciki".


Sukaji muryarta tana cewa "Ohh, bibbs, kina gabanshi ko? Kar ya ji sirrin mu, ki karbi numebrna donAllah ki min flashing zan kiraki zuwa anjima"
Labiba tace "Tou Aunty Yas, zan karba".
Zaid yace "Me ake ce mata?".
Yasmin tace "ina ruwanka ba sai ka ji ba".
Yayi daria yace "kun fi kusa".
Labiba ta mishi alama da zata tafi.
Ya daga mata hannu tare da muting Yasmin na two seconds yace "I love you".
Labiba ta amsa mishi ta fita ta fada gidansu da sauri.


Zaid suka cigaba da waya da Yasmin.
Har ya bata labarin Hudu da duk abunda ya faru
Jikinta rawa yake tayi tana Tsine ma Hudu, wallahi da kun kaishi Police station"
Yace "Mancy tace a kyaleshi, tunda Allah be bashi nasara a kanta ba".
Yasmin tayi ta fada, kafin tace "kai wallahi all needs to stop, bari dai na zo Katsina Jibi InshaAllah"
Murmushi yayi yace "Allah ya kawo ki K'amshi k'amshi".
Sunyi fira fiye da 1 hr kafin sukayi hanging.


Cikin Gida ya shiga don hado breakfast.
Yana kallon Shafa'atu na ta sintiri.
Tace "Dan Makaho baku tafi ba? Amma na ji dadi ina Dalo?".
Mugun Harara ya zabga mata ya shige kitchen.
*
Bari ta shiga ta gaida Yayanta da Aunty Asey.
Ta shiga da Sallama, ba wanda ya iya amsa mata, ganinsu tayi a kafe kamar an kafasu, ba mai iya motsi sai dai kallo daya zaka musu ka san cewa ransu a bace yake.
Labiba tace "Yaya lafia? Aunty Aseey meya faru?".
Babu wanda ya amsa mata sai chn yace "Labiba, Zauna".
Jin muryarshi tayi ba wasa ta zauna kan kujerar da ke kallon Gadon da suke.


Yace "Yanzu Labiba, tsakaninki da Allah, mai ya kaiki dakin Dan Makaho?".
Ta dan tsorata amma sai tace "Yaya, wallahi tun jiya nake ta kiranshi wayarshi a kashe, kuma banji duriyarshi ba, shine na je duba shi naji ko lafia ashe mamarshi ce tazo jiyan".
Ba wannan yake son ji ba.
Yace "dama chan kina zuwa dakinshi?"
Kai ta saddar k'asa tace "Eh Yaya".
Yace "Wallahi Labiba kin bani mamaki, kin ban mamaki matuk'a banji dadi ba, Labiba da na ga kin fito dakin dan makaho wallahi sai da zuciyata ta tsaya, wai kanwata da na fi so a rayuwa ta fito daga dakin Namijin da ba muharamminta ba, Labiba me kike so ki zama ne wai? Me kike maida kanki? Ba kya tsoron ya miki wani mugun abun?".


Da sauri ta giirgiza kai tace "aa yaya ba abinda zai min, na yarda dashi, ba zai min komai ba ba haka yake ba".
Baban Amira a kausashe yace "Labibaa, kar na sake ganinki kin shiga dakinshi, Labiba kar na kuma jin an ganki da DanMakaho, Labiba ki fita idona, na gaya miki sadakinki na gurin Abbanki, shekarunki 18 ke ba yarinya bace, Labiba kar ki yarda in sa miki ido a gidan nan".


Labiba ta sauka kan guiwowinta tace "Yaya kayi hakuri donAllah, ka yafe min, amma ni wallahi ina son dan Makaho Yaya, shi nake son aure, ka san labarinshi, danMakaho abun tausayi ne".
Ya sausauta murya yace "kinsan me kike cewa? So fa kika ce? Aure? Tab, Tausayinshi kike na tabbata, ki rufa ma kanki Asiri, banso mu bata dake Labiba".


Labiba tace "kayi hakuri Yayana Babana, inshaAllah ba za ka sake ganina a dakinshi ba, kayi min hakuri, ba zan kara ba, Aunty ki ba Yaya hakuri, ba zan sake ba". Ta tashi ta fita daga dakin.
Suka bita da kallon tausayi, kamar ba a hayyacinta take ba, lokaci daya ta zama wata zararrara.
"Ta na Sonshi" inji Aunty Aseey.
"Wani irin so"
Aunty Aseey tayi murmushi tace "Baban Amira So gaskia ne".
Yayi shiru yace "ya zanyi? Kar Labiba ta bamu kunya".
Aunty Aseey tace "donAllah kayi kokari dai ka rufe Wurin chan".
Yace "Aseey Bulo tsada , wurin chan zai ci Bulo 50 zuwa 60".
Tace "ko zaka ma Alhaji Zaki magana, tunda ba bayan yake zuwa ba na tabbata ya manta da tuni ya gyara".
Yace "gaskia ba zan mishi magana ba, kwanaki bakiji me yace ba".
Yanzu dai barinyi buga buga na ga zan iya siyo Langa Langan nan a rufe kafin na samu kudin Blocks, ya fita ta mishi fatan dawowa Lafia.


Aunty Aseey ta shiga gun Labiba ta ganta zaune ta na kuka.
Aunty aseey ta dafata tace "Labiba".
Labiba ta dago kanta ta kalleta.
Aunty Aseey tace "Me zakiyi da dan shaye-shaye?".
Da sauri ta share hawayenta tace "ni na san me zanyi dashi, Sonshi nike, Sonshi nake domin Allah Aunty Asiyah, Allah ka sa ya aureni, Allah ka sa in zama matar ZAID ALI ZAKI".
Da tsananin Mamaki take kallon Labiba, tafi zaton wani abu ya tabeta a k'wak'walwa.
**
Ta na zaune ta ga Message din Zaid, numbern Yasmin ya turo mata, kiranta tayi.
Yasmin na jinta ta kashe ta sake kiranta, sun dade suna waya. Kafin ta kashe ta kwanta don yin bacci kafin Azahar.
*


"Hello, gani k'ofar gida"
Hargowanta yaji "toufa, ba kuje Habujan ba? Sai yaushe?".
Zaid yace "donAllah nidai ina waje".
Baa yi minti 3 ba sai gata ta fito ko mayafi babu.
"Danubanka baka daina kirana kace kana waje, budurwarka ce ni? Zance kazo guna?".
Zaid ya harareta "wallahi zan danneki na dura miki World".
Harararshi tayi tare da kawo hannu kusa dashi, da ba dan ya gota ba da ta mareshi "Ubanka zaka dura min ba wall ba".
"Gaya man, kun fasa zuwa Habujan ne?".
Yace "sun tafi fa, suna hanya".
Tace "toufa, kai ya bakaje ba".
Yace "ni Nene? Ina zani? Babba dani, ni ina nan Gidan Babana"
Ta harareshi "ka zauna nan matar uba ta cigaba da gasa ma aya a hannu".
Yace "yo ai Nene ko da chan bata gasa min Aya a Hannu ba".
Tace "Ina dan shegiyan nan, kanenta, ai da Alhaji ya barni sai na gilleshi, na gunduleshi".
Sai yanzu abun ya fado mishi yace "wai da an barki sai ki yankeshi?".
Tace "Chab, takwaran Zaidu Bawan Allah har yau baka sanni ba, tsaf zan yankeshi billahilazi".
Zaid yace "Ni Yunwa nikeji Nene".
Tace "aiko yanzu na jefa Danwake, bakaji dadin da yayi ba".
Bata fuska yayi yace "Danwake kukayi?".
Tace "Kai wannan abun sukayi Macaroni, ban fa ci, shine fa na jefa danwaken".
Yace "Ni Macaroni zanci"
Ta bata fuska tace "Jibeka uban yan iyayi, wanda iyakan ka Nigeria, ko iyaport baka taba zuwa ba, ka tsaya feleke, to jikata Nasiba na chan Ingila tana bina na aika masu da Garin danwake".
Zaid ya girgiza kai yace "Zaki ban Abincin ko ba zaki bani ba".
Kallon Sama da kasa ta mishi tace "Zan baka, Ubana, Mamman, Macaroni ko? Jira na zubo ma, kar ka juyan baya na shiga duniya, naga sai wani kallo kake man kamar zaka zagar min Uwa".
Da hannu biyu ya dafe kai yana Nadamar duk abunda ya sashi zuwa Gidan Lema Gun Nene.
*
Ta tashi bacci, ta fito yin Alwalar Azahar ta ga Gidan duk Langa Langa, an rufesu, ta san aikin Ya Muhammad ne, girgiza kai kawai tayi ta shiga Toilet.
Zaid ma ya sha mamakin ganin an katange Gidan da langa langa, haka kurum sai ya ji ba dadi, amma ya zasuyi?.


Da Laasar suka hadu a Masallacin Bakin Titi.
Gaishe shi yayi ya amsa ba yabo na fallasa.
Yace “DanMakaho, meke tsakaninka da Labiba? Ka gaya min gaskia tsakaninka da Allah”.
Zaid ya dan murji Idonshi yace “Yaya Sonta nikeyi, kuma ina son Aurenta”.
Baban Amira yace “Ashe sonta kake? Dan Makaho kayi nauyin baki, akwai wani mai Sonta, sunje chan Gida Edo, an bashi Labiba, karshen magana ma, Sadakin Labiba na hannun Babanta”.

Gaban Zaid ya fadi, yace “Yaya, na san ba zaka so tarayyata da Labiba ba, amma dagaske nake sonta, kuma wallahi na bar shan komai, har sigari, donAllah kar ka raba ni da ita Yaya”.
Tausayi ya bashi yace “kayi hakuro Zaid, wallahi dagaske nake, an bayar da Labiba, wallahi sadaki naira dubu 50 na gun Baba, daurin Auren cikin kwana 40 da wani abu, wallahi kaji na rantse ma”.


Jiri ya ji yake dibanshi sosai, sai da Baban Amira ya tallafo shi, kwacewa yayi yayihanyan Gida, sauri sauri gudu gudu.
Hankalinshi in yayi dubu ya tashi.
Gadonshi ya fada, zuciyarshi wata irin zafi take.
Wayarshi yayi ringing, ‘yar halak ce, ya dauka.
“Hello Soulmate”.
Da kyar ya iya cewa “Bibbs, meyasa ba ki fada min you are engaged ba”.
Gabanta ya dan fadi tace “Inji wa?”.
Yace “ba Inji wa ba, gaya min dagaske ne?”
Tace “Eh dagaske ne amma..”
Bai tsaya jin mai zatace ba ya katseta yace “babu amma, abunda nake sonji kenan, ina miki fatan Alheri, Allah ya sa Alheri ya baki dauwammen Farinciki a rayuwa”.
K’it ya kashe wayar.


Hankalin Labiba in yayi dubu to ya tashi, ta kira wayar kashe, da sauri ta tashi ta fita, karo sukaci da Baban Amira, ta dan ja birki, me ta tuna me ta tuna ta koma cikin daki.
Shikam Zaid Zuciyarshi wani irin tafasa take.
Mai zaiyi? Ji yayi kamar zata tarwatse, abu daya ya zo mishi, ba tare da wani dogon tunani ba, ya janyota daga karkashin Gado, sai da ya hadata sosai kafin ya kyasta, shegiar ce World, abunka da an dade ba a hadu ba, ya zuketa kamar ba gobe, yama gamawa ya hada da sigari, nan inda yake yayi Mankasss sai bacci.


Baban Amira zaune yayi a kan kujera tsakar Gida Labibata fito, kamar ba abunda ya faru tace “Yaaya, Babansu Aisha yayi Accident, ina so naje na duboshi”. Yarinyan nan wayau take so ta mishi, kila wani wuri zata hadu da Zaid.
Yace “Muje na rakaki, nima sai na duboshi”.
Mamaki ya kamata, meye haka? Don dai kar ta fita ita kadai? Tace “to muje”.
Haka suka fita, ya tsaida musu Napep, suka shiga tare sukaje Gidansu Aisha, tace da Yayanta suke, aka mishi iso, ya shiga ya gaidasu ya musu Allah kyauta gaba, ya tusa keyar Labiba suka koma Gida. Ba abunda ke fitar dashi sai Sallah Maghrib da Ishai, har yanzu wayar Zaid kashe.


A B U J A
7:45pm


Masu Aiki sun musu setting Abinci a kan Table, kowa ya samu guri ya zauna, banda Dalo da tace ta k'oshi.
Alhaji Abu yace "Ina Sadiya?".
Mancy tace "wai bata jin yunwa".
Alhaji Abu yace "yo me taci? Tun lemun da kowa ya sha a Mota? Ban yarda ba".
Ya kalli Jawad da

Please Login or Register in order to submit comment