Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Zaki gaya min gaskia ko sai na yankaki?" Da sauri tace "A ra min tayi" damk'o wuyarta yayi yace "cire don ubanki" jiki na rawa tace "barin je daki zan bata abunta" daka tsawa ya mata yace "a nan zaki cire danubanki".


Ihu ta kwala "Mummy" Mari ya katse mata hanzari, ya ja rigar tun daga Sama har kasa ya dire, ya fincikota ya kwabe mata rigar tas, kuka ta fara sosai ga cin mutunci gashi ya farka rigar. Allah ya so ta da vest a jikinta amma sharara ne har ana ganin Bireziyarta.


Shafa ta fito hankali tashe tana tambayar Annah me ya faru? Be bi ta kansu ba ya barsu a gun bayan ya dauki farkaken rigar ya saka a Bolan kusa dashi yayi hanyar dakinshi yana cewa da kuci arzikinmu gwara kowa ya rasa.


Ranan Har Daki Baba ya bi Zaid ya na ta tsinanshi kamar zai ari baki, shi ko Zaid din ko a jikinshi.
***


Watan Mancy 9 ta haifi diyarta Mace mai kama da Babanta, sosai akayi murnar samun karuwa a cikin Dangi balle duk yaran Alhaji babu Mace, dangi daga Katsina da Kano sukayi ta zuwa barka.
Hajia Luba ma ba a barta a baya ba don ta nuna Son Jaririyar.
Ranar Suna diya taci sunan Hajiar Alhaji Abu wato Halima amma ana ce mata Mimi.
Mimi na da Wata Biyar Autan Hajia Luba ya dawo daga Makaranta da sakamonshi na Masters wanda ya hado a Malaysia.
Jawad Miskili ne, shine Autan Umma, yasan Babanshi yayi aure amma ba ruwanshi da Mancy, daga gaisuwa shikenan, be iya shiga wurinta ya zauna kamar yanda yayyinshi keyi, indai Sun hadu a Parlo yana mik'a hannu ya karbi Mimi don Mimi son kowa ce, baya ganan bai da matsala da Mancy.


Wannan Kenan.


Jaje suka sake yi ma Juna a Massalaci, Alhaji Ali ya sake tabbatar ma Mallam Muhammad kan cewa kar ya damu shi zai sake gyara Bangon Gidan.
Kamar jiya Aunty Aseeyah ta tafi Gidan Iyayenta ta bar Labiba da niyyar in 10 tayi zata wuce Makaranta.
Kamar Jiya haka ta sake sando ta shiga dakin Mankas, yana zaune yana cin Bread da k'wai.


Kallo daya ya mata ya dauke kai, ko sau daya tunaninta bai fita daga kwakwalwanshi ba.
Da murmushi ta ce "Ina kwana YaZaid".
Shareta yayi ya cigaba da Breakfast dinshi ta k'araci zamanta bai tankata ba, ta mik'e da murmushi a fuskarta tace "ni na tafi Makaranta sai na dawo". Tak bai ce mata ba, haka ta fita ta barshi zaune ya bi bayanta da ido,ta tsallaka blocks ta fice abunta.


Runtse ido yayi ya bude, zuciyarshi na mishi wani irin zugi, sigari ya dauko ya fara zuk'a cikin Zafin nama.


Washegari


Haka aka sake Wani Ruwan Saman Ginin ya sake Rushewa, sau 3 kenan kasancewar lokacin damina ne kusan kullum sai anyi Ruwan Sama.
Hajia Shafa tace da Alhaji "wai kai ke da kudin banza? Kar ka sake ka kara gyarawa, in banda son banza shi ba zai gyara ba? Kuma su ma ake rufa ma Asiri tunda tsakar Gidansu ake gani, in abun ya dameshi ya gyara, kai kar ka k'ara Gyarawa kaji ai?" Da sauri Alhaji yace "Ba zan kara gyarawa ba, ai Muhammadu akwai son banza, ai kudin ba a bishiya nake katso su ba, in bai gyara ba ruwanshi". Da murmushi tace "yauwa Alhajina".


"In har ba damuna ta tsaya ba, Ginin nan ba zai bar rushewa ba"
Cewar Yaya Muhammad cike da damuwa.


"To ya zaayi" inji Aunty Asiya.
Baban Amira yace "wallahi ni kunyan Alhaji Zaki ma nike, ace duk rushewan da bangon yakeyi ko so daya ban taba gyarawa ba?" Tace "Ai ya san baka dashi kar ma ka damu". Yace "bari InshaAllah zan gaya mishi a bar gyaran haka har sai ruwa ya tsaya, in ba haka ba Allah na tuba asara zaayi tayi, anayi yana rushewa" Aunty Asiya tace "eh gaskia, Allah dai ya rufa Asiri".


A zuciyar Labiba kuwa ba ma taso a gyara, ita bata k'i a zauna a haka ba, hakan ne zai sa ta ga Sanyin Idaniyarta, sosai take jin shi a ranta, yanzu ma Jira take Baban Amira ya fita ta faki Idon Aunty Asiyah ta shiga.


Aiko yana fita tayi sadap sadaf ta fada Gidan Alhaji Ali.
Ba tare da jira ba ta fada dakin Zaid wanda daidai yake da fitowanshi daga Toilet daure da Towel a k'ugunshi.


Da sauri ta runste Idonta shi ko cikin zafin rai ya fincikota ya wurgata kan Gado yace "yau sai kin ci Ubanki, Wallahi yau ba zan daga maki ba".


Gadangadan yayo kanta...


Ghen Ghen.
Whats about to happen? Anyone?


Vote and comment line by line please


#1love
#DM
#FWASonSo
#anatare
#nagode


Biebee Isa
[14/03 9:35 pm] Biebie: DAN MAKAHO 😉


Babi na Sha Hudu1⃣4⃣
(FUSHI😒😏)


Jin tambayar tayi wani iri, shi kuma gani yayi kamar ba ta ji bane, ya sake maimaita mata, "kin bar So na ne? Me na miki to da zaki bar So na? Ki cigaba da So na, kar ki daina".


Baki ta hangame ta na sauraro zantuttukan bakinshi, takaici ya turniketa, bai zo don ya fada mata yana sonta ba, ko kuma don yayi kewanta sosai, ta zata ya zo nemanta ne kamar yanda ya gaya mata cewa in tayi Aji k'ila ya kawo kanshi gareta, shin ba ta yi Ajin ba? Ko yin Ajin ya wuce Kama kanta na kwana biyu? Cikin daren nan zuwa yayi kawai ya gaya mata ta cigaba da sonshi? Seriously? Ya ma mugun raina mata wayau cikin zafin nama ta k'arasa wurin k'ofa ta bude ta sosai tace "Fita".


Sosai yayi mamakinta amma abun mamaki shine yanda ta rikide ta chanza lokaci guda.


A kausashe tace "ka fitar min a daki, kar kuma ka sake shigo min daki, duk randa ka fado min daki haka kamar yanda kayi, wallahi zan maka Ihun Barawo, tun muna Shaida Juna yanzu, ka fitar min a daki".


Sosai yayi mamakinta, jiki a sanyaye ya daga kafaffunshi da kyar ya fita ta gabanta, yanayi yana waiwayonta, ya na sa k'afa ya fita daga dakin ta datse kofar da k'arfi tana numfashi samasama, hawaye ta fara, ta ba kanta wahala , ta wahalar da zuciyarta.
Tashi tayi maimakon ta kwanta, sai ta cigaba da Sallolinta har bacci ya kwasheta a gurin.
Zaid kam tunda ya bar dakin k’afafuwanshi suka mishi nauyi, da k’yar ya isa dakinshi, ya zube kan Gado.


Hannun damanshi ya sa ya murji idon hagunshi, a baiyane yace “Mai ke faruwa da Beebs? Ya Allah!”.


A haka ya yi bacci. Washegari bayan Asuba, be shiga dakinshi ba ya tsaya bakin kofa ya kwala mata kira a waya, no answer. Yana tsaye ya ga fitowarta daga daki, ta shiga toilet dauro Alwalan Asuba, minti 10 ya bat, ya tabbatar da idar da Sallahn, ya sake kira, bata amsa ba, haka yayi ta trying amma ba amsa karshe sai jin wayan yayi a rufe.


Tsaki yayi ya ji kamar ya fada Gidan. Zama yayi dabas, a kan idonshi gari ya waye, kan Idonshi Yayanta ya fito dauke da dan karamin jaka da alama tafiya zai yi, kan idonshi Labiba ta fito don yi mishi sallama, tana fitowa kuwa ta kalli Inda Zaid yake, idanuwansu ne suka sark’e ma juna.


Musayar Kallon kallo sukeyi ma junansu, ko wannensu da abunda yake kitsawa a ranshi, daga baya Labiba ta watsar ta bi bayan Aunty Aseey suka raka baban Amira har kofa yana ji suna mai Fatan sauka lafia kafin suka dawo suka shiga dakin Aunty Aseeyah.


Muryar Dalo ta katseshi “Ina kwana Ya Zaid” firgigit ya juya ya kalleta murmushi suka sakar ma junansu kafin yace “Sadyn Mancy” karasowa tayi ta na kallon gidan Mallam Muhammad bayan ta zauna kusa da Yayanta tace “Mai ya faru nan?”.


Zaid ya dan Kalleta yace “Sadiya Ali Zaki, anya kina Gidan nan kuwa?” tace “Yo Yaya yaushe rabon da nazo Boysquarters? Baka zama, kuma ko da yaushe kai ke zuwa, kafin nazo ka riga kazo cikin gida” yace “haka ne, ruwan saman da akayi last 2weeks me ya rushe bangon, an gyara amma ko kwan beyi ba ya k’ara rushewa, am not sure whats taking so long da ba a k’ara gyarawan ba”.


Tace “ya kamata a gyara, wurin is too open, komai fa na gidan ana gani, they need privacy, ka san har tsakar Gida suke zama, bansan yanzu ya sukeyi ba”.


Zaid ya murji idonshi yace “Na san Mallam Muhammadun bai da kudin siyan sabbin blocks da ya siya, don shine a takure”


Dalo tace “ai baba ya kamata ya dauke mishi gyaran”.


Zaid yace “ba wuya Matarshi ta hanashi gyaran”.


Dalo tayi murmushin takaici tace “Allah shi kyauta”.


“Ya gidan? Wa ke takura miki?” Daura kanta tayi kan kafadunshi tace “Ba kowa, sai dai Yaya, Uncle Hudu yayi ta sani dafa mai tea yana sa ina kai mishi daki, i dont like it”.


Zaid ya cije baki har jijiyan gefen kunnenshi ya taso, yace “kar ki sake ce mishi Uncle, ba k’anin uwarki bane, kuma ya sake kiranki dakinshi karki je, ya sa annah, itace diyarshi ba ke ba, God meyasa ban ma ga hatsarin zaman shi cikin Gida ba? Da sakel, ba zaiyiwu ba ma, wait, dalo, tsaya, tun zuwan su Hudu Gida, ya ta ba miki wani maganar Banza, ko ya tabaki ko ya rik’eki?” Da sauri ta girgiza kai tace “aa” yace “Ko so daya?” ta gyada kai tace “eh be taba ba, da fa baya min magana, ko Aunty na zagina tayata yakeyi, amma just recently ya fara sa ni aiki, yana cewa in kawo mishi daki”.


Murmushin takaici yayi yace “He is developing intrest in you, aiko zai ci ubanshi, wallahi billahi ya tabaki sai na kasheshi”.
Firgita tayi sosai, Tsoro yayanta ya bata, bata taba ganinshi a irin yanayin nan ba, yanzu ta ankara da wani irin magana yakeyi irin ta ‘yan sara suka, yan daba.


Sai tayi nadaman gaya mishi, tace “Yaya, be fa min komai ba”
Zaid yace “Stay the hell away from him, duk randa yace ki dafa mishi ruwan zafi kice ba zaki iya ba, ke ba yar aikin uwarshi bace ba, in kuma ya matsa ki zo ki gaya min kinji ai?” Yaya “ba zan iya mishi rashin kunya ba” tureta yayi yace “nikuma ki bijire min, zan ko ci uban Hudu”.


Da sauri tace “yaya kayi hakuri, ba haka nake nufi ba, kayi hakuri donAllah, yaya wallahi be ta ba min wani magana ba, ruwan zafi kawai yake cewa inkai mishi, i am not complaining, i just dont feel comfortable entering his room, amma in ya min wani abunda ba shikenan ba, yaya zan gaya maka, kayi hakuri donAllah, ban son tashin hankali kuma”.


A hankali yake sauke numfashi, zuciyarshi na danyin sanyi, kallonta yayi, suka sakar wa juna da murmushi, tace “Yaya ka kira min Mancy, banda kudi a wayata” ‘yar nokia dinshi da ta ci robali ya miqa mata ta bi wayar da kallo, bata ce komai ba ta kira Mancy.
Da farinciki suka fara waya da Mancy, aka bata Mimi suka gaisa da gwalondonta. Shima ya amsa wayar suka gaisa da Mancy da Mimi. Kamar kullum Mancy ta tambayeshi akwai wata damuwa? Sai yace “aa” sai tace “zan aiko maku da sak’o a account Allah ya muku Albarka” suka amsa da Amin.


Fitowa Labiba tayi idonta kan wata wanda ta jingina da kafadun Zaid, gabanta ya yanke ya fadi, zuciyarta ya fara dukan uku-uku. Aunty Aseeyah da ke bayanta ta karasa fitowa daga Dakin, inda Labiba ta ke kallo ta bi da kallo.


Ameerah da Sabit ne suka fito suma, hayaniyansu ya sa Dalo da Zaid maida kallonsu ga Gidan Mallam Muhammad. Da sauri Dalo ta mike da faraa a fuskarta ta tsallaka zuwa Gidan. Labiba kam ta hade girar sama da k’asa, wacece kuma wannan? Itace Yesmin ko? Me za ta zoyi? Kafin ta ankara taji muryan dalo na “Allah sarki Ameera da Sabit nayi missing dinku”.


Labiba ta waiga taga Sabit da Amira jikin budurwar Zaid, suko sai dadi suke ji suna murna. Labiba ji take kamar ta finciko yaranta.
“Sady ya kike kwana biyu?” Dalo tace “Allah sarki Aunty Asiya, ina kwana?” “Lafiya lau ya kuke?” Wallahi lafiya lau, ta juya ga labiba da murmushi a fuskarta tace “Ina kwana?” Labiba fuska murtuk ta raisayar da kanta kamar bata ji ba, dalo kam bata lura ba ta juya ga Aunty asiya tana tambayarta ina baban su amira, “be dade sa fita ba, Maradi zaije”


Abunda Labiba tayi tsaf kan Idon Zaid, sai ya ji haushi, wato fushin da ake dashi ya shafi k’anwarshi ko?.
Aunty Asiya tace “yanzu Sadiya zumunci yayi wuya? Kina nan? Bakya lek’o mu duk tsawon shekarun nan? Tunda Mancy ta bar unguwar nan ban k’ara ganinki ba Sadiya, sai dai Baban Amira yace min yana ganin DanMakaho a hanya ko Masallaci”.


Dan yak’e Dalo tayi tace “ Aunty Asiyah Wallahi ba inda nake zuwa, ina gida ko da yaushe, baba ya hanani fita, ya sa tsaro a kaina, tunda nayi Candy ko bakin gate ban zuwa wallahi, kin san yanda abubuwan suke, wallahi ko gun Ya Zaid bana zuwa shi ke zuwa inda nake, ni na ma fi san zaman daki, kin san komai Aunty Asee, amma da na san bangon nan ya rushe ai wallahi da zan dinga zuwa ana gaisawa, sai yanzu fa da na zo gun YaXaid naga wai ashe bango ya rushe”.


Aunty Asiya ta jinjina kai cike da tausayin Dalo tace “na san Komai Sady, ba wani abu, ku cigaba da hakuri, mahakurci mawadaci”.


Yak’e mai kama da kuka Dalo tayi tace “barin koma kafin ya zama wani abun, sai anjimanku” ta kalli Labiba da ta daskare a lokacin da ta fahimci Dalo ita ce Kanwar Zaid, wanda kishi? Eh kishi ya hana gane wacece”.
Aunty Asiya ban gane wannan ba, Aunty Asee tace “Labiba ce Kanwar Baban Ameera, karatu take a Poly”.
Dalo tace “Ayyah, Allah ya bada saa, sai Anjimanku”. Labiba ta sakar mata da murmushi mai kayatarwa, tayi dana sanin rashin amsa gaisuwarta, ta na so ta samu lolaci da Dalo, tana so su saba, ashe haka take? Tana kama da Zaidunta, son da take ma Zaid ya shafi Dalo, sosai ta ji tana k’aunar k’anwar Masoyi.


Sauri-sauri gudu-gudu Dalo ta koma inda Zaid yake, har yanzu yana nan tsaye inda ta barshi, hannu ya daga ma Aunty Aseeyah da yaranta, suma suka daga mai hannu, ya kalli Labiba ya riko hannun Dalo, yace “oya wuce ciki kafin Baba ya tashi ya ga ba kya nan, kinyi breakfast?” Ta girgiza kai “Aa” yace “barin je in siyo mana K’osai, ki dafa mana tea sai mu sha da bread da kosai”.


Tace “Okay Yaya, barin je kafin ka dawo, daki ya shiga, ita kuma ta wuce cikin Gida, sai gashi ya fita kuma, duk kan Idon labiba.


A kitchen ta iske Aunty Asee ta na hada Tea a k’aton Jug. Kafin tayi magana tace “Lab kece ke ta son ganin Dan Makaho, to wannan shine dan Makahon” wani murmushi tayi tace
“Aunty, ashe wannan itace k’anwar DanMakaho kenan” “Eh Labee, itace, Sadia, kai Allah ya isansu, wallahi duk tayi bak’i ta rame, baiwar Allah”.


“Aunty, meyasa ba kya shiga Gidan” Aunty Aseeyah ta zaro ido tace “niii Lab? Ni gidan Alhaji Zaki? Wurin wa? Wurin Hajia Shafa? To har gobe ban san kamannin Matar ba, ko mum hadu be wuci randa aka saki Mancy ba, da duk yan unguwan suka shiga Gidan, amma wallahi ba zan iya shaidata ba, to wannan matar Anamimiya mai zanje na mata? Matar da bata tsoron Allah? Ba abunda zanje yi Gidanta wallahi”.


Labiba ta jinjina kai tace “haka ne, amma zumunci ai daban yake, yanda kukayi zaman kirki da Mancy, ya ci ace ba ku hofintar da ‘yayanta ba, kamata yayi ace kuna duba yaranta, musanman ma Sadiyan da take mace.


Kallo daya Aunty Asee ta mata ta juya ta cigaba da motsa sugar, wata sa’in Labiban bata ganewa, kamar mai jin magana ta guiwa.
Labiban ma shiru tayi tana tunanin Yanayin da ta gani a idon Masoyi dazun.


Da Yamma


Zaid yayi ta kiran Labiba, ta k’i dagawa, ta na gani, shikuma duk inda ranshi yake ya baci, wai meye haka? Wai don me zai dinga kiranta? Mai ya sa ma ya damu? Dan uwarta, don ta ga yana bibiyanta, shine zata dinga ja mishi Aji? Murmushi ya subuce mishi ba tare da ya sani ba. AJI? Aji? Hahahah Aji? Ajin kenan? Fushi tayi wai dama? Hakan ne? Ko kuma wani abun ne? Tsaki yayi ya jefar da wayar tare da kwance k’ullin World ya hau zuk’a.


Bayan Maghrib ya farka, jikinshi duk ya mutu, da k’yar yayi wanka, ya rama sallolin da ake binshi, ya kasa hakuri, ya lalubo wayarshi ya fara dialing wayarta, ringing take tayi, tana rejecting, sosai ranshi ya baci, ya buga tsaki ya dauko Sigari ya kunna mata wuta, ya fito waje yana zuk’a don yana da tabbacin ba zai ga Dalo waje a daren nan ba, waje ya fita, zaije benchin Eskaley, don in ya tsaya a gidan nan, ba abunda zai hanashi afkawa gidan Mallam Muhammad.


7:50pm
A bencin Eskaley, Mankas ya daura k’afa daya kan daya yana shan Sigari na 11 tun bayan fitowanshi daga Gida, Yana kallonsu suna ta gardamansu kamar yanda suka saba.
Kamar daga sama ya hango wata daga nesa mai irin tafiyarta, rike da yara biyu, ko idonshi ne? Da sauri ya girgiza kai, ita ce, zumbur ya mik’e, me ya fito da ita da daren nan? Ina zata? Ita da Amira da Sabit, ina zasu, jira yayi ta k’araso, amma abun mamaki, wurin su ta nufa, Bencin Eskaley ta tunkaro, mamaki yake, mai ya kawota? Ko ta kasa hakuri ne ta biyo shi? Ko taje daki ta ga baya nan sai tace bari ta biyo shi Bencin Eskaley? Bari dai ta k’araso”.


Da Sallama ta k’araso gurin, bata kula su Master da ke ta fadin “yayarmu barka da fitowa” ta wuce gaban kiosk din Eskaley tace “Akwai Shafto?(Mosquito Coil?) Eskaley yace “eh akwai” “ a bani Kwali daya” ta mik’a dari biyu ya dauko ya bata, ta amsa ta juya, ba tare da ta kalli gefen da Zaid yake ba, ta san yna wurin, jikinta ya bata lallai Zaid na wurin”.
“Wai ya? Ana miki magana kina jinmu? Haba yayarmu yawa kike” cewar su Master.


Dan Makahon da ke zaune, Mamaki ya gama kasheshi, wato ba shi ta zo nema ba, ba ta shi take ba?tsaki yayi mai karfi ya murje guntun sigarin da ke hannunshi ya rufa mata baya, mai su tero zasuyi? Shewa suka fara suna tafi.
“MANKAASSSS”
“Sai Mankassss, shawo mana kanta, ita yar jami’ah bata wa mutane magana, saito mana ita”.


“Uwarku!” Kadai yace ya cimma Labiba da ta gama jin duk abunda suke cewa.


Sabit ya daga Sama, Labiba bata ce komai ba, a jikinshi ya kwantr da Sabit, ya dinga binta, Amira tace “Ya Zaid me kakeyi a Bencin Eskaley? Da sauri yace “Uhm Uhm Amira, naje siyan maganin sauro ne” tace “lahh muma shi mukazo siya” yace “Me yasa baku zo tun dazun ba sai dare? Kuma ina babanku? Mai yasa bai zo ya siya da kanshi ba?”.


Amira tace “Abba yayi tafiya, Aunty Lab bata san ya k’are ba, sai yanzu da zamu kwanta, tazo daukowa taga ashe ya kare, kuma sauro dakinmu, in ba da shafto ba cizonmu zasuyi, kuma ba mai siyowa, shine Aunty Lab tace Umminmu ta bada kudi mu siyo, Ummi tace ko ta fito muje tare duka, sai Aunty Lab tace aa, ta bari muje mu siyo, umminmu tace mu bi a hankali, bencin Eskaley ba mutanen Kirki, shine Aunty Lab tace “ita ina ruwanta da su? Shafto kawai zamu siyo mu dawo”.


Labiba tayi mamakin surutu na Amira shi ko Zaid ya jinjina kai yace “Aunty Lab, kika ce ba ruwanki da yan Bencin Eskaley?” Banza tayi ta kyaleshi ta cigaba da jan Amira suna tafia, daidai kunnenta yayi kasa da murya yace “har ni ba ruwanki dani?” Tak bata ce mishi ba, yayi ta magana tak’i amsawa yace “baki min magana wai? Fushi ake dani? Eh Beebs? Fushin ne har yau? Ki gaya min ne na miki? Beeeebs kina fa jina, mai Masoyi yayi? A ma Masoyi hakuri to, Daria ta so kufce mata amma ta dake daidai isowarsu Gida, mik’a mishi hannu tayi alamun ya bata Sabit.


Sake mata Sabit yayi yace “Seriously? Seriously Beebs? Ba zaki ce min komai ba?DonAllah Fushin ya isa haka”.
Bata amsa shi ba ta shige Gida ta barshi tsaye a wurin.


Gida ya wuce shima rai a jagule, be samu zuwa gun Dalo ba ya shige daki ya banki World ya kwanta ruf da ciki bai farka ba sai k’arfe 9 Washegari Lahadi.


Ya Tashi ya fada toilet yayi wanka yayi Alwala, ya dauko Jallabiyarsa yayi Asuba, yana idarwa ya chanza zuwa Riga Body Hug da 3quater wandonshi irin na sojoji, ya dauko Face Cap ta k’wama a kanshi ta baya, ya fita don shiga Cikin Gida.


Suna kan Dining Table gabaki dayansu banda Dalo, dakinta ya wuce Straight, ya ganta zaune tana shan Shayi da Bread, gaisheshi tayi da murmushi a fuskarta ya amsa yace “kin tashi Lafia? Ta amsa da lafia lau” yace “zakici abunda suke ci kan table?” Da sauri ta girgiza kai tace “aa wallahi, na k’oshi da wannan ma” ta san in tace eh zataci zuwa zaiyi ya debo mata, kuma ayi rigima Babba.


Yace “Okay, kun gaisa da Mancy yau?” Tace “eh munyi waya da Asuba” yace “ naga missed call dinta ina bacci, zan kirata zuwa anjma”.
Barin je in nemi abinda zanci” be jira amsarta ba ya fita yayi hanyar Kitchen.


Baba, Aunty Shafa, Hudu, Annah ne kan table suna cin Shagali, kallon table din yayi baida niyyan gaida uban nashi balle matarshi, haka kurum yau yaji yana son cin Abincin.


Kitchen kawai ya shiga sai gashi ya fito da Plate da fork, duk suka zuba mishi ido, coolern ya bude ya zuba Dankali, ya zuba sauce din Hanta, ya dauko kwai, baki bude shafah ke kallonshi, baba ko daure fuska yayi ya cigaba da cin Abicinshi.


Shafa tace “na shiga Ukuna, Alhajina kana kallonshi ko gaisheni beyi ba zai ci min abinci, ni baiwarshi ce? Ni banda matsayi a gurinshi na girmamawa ina matar ubanshi? Gaskia ya ajiye min Abinci”.


Haba Kamar an kunna TV baba ya fara Bambamin bala’i
Yo ina zai gaishe ko? Ya gaisheki yana watsatsatse? Kina gani ko ni Mahaifinshi be min kallon kirki ba balle ke matata? Tsinanne, shege, Allah ya kwashe maka albarka Zaid”.


Ko a jikin Zaid don daukar Plate dinshi yayi, fork din ya sa cikin plate din Shafaatu ya chaki hanta ya sa a baki, ya karama wandonshi iska, kamar an kunna baba, ka dawo da abincin nan dan shegia, ka ci Abincin nan Allah ya isa tsakanina da kai, ina Zaid ko waigowa beyi ba, ya wucewar shi dakinshi. Dalo kuwa ta fashe da kuka a daki. Shafa ko in ranta yayi dubu ya baci don raini harda caka mata fork a plate dinta? Lallai Zaid dan duniya ne, wallahi maganinshi zatayi, shi ko Baba yayi ta haushi kamar tsohon Kare.


Bayan La’asar Yara na Islamia


Labiba ta dauki wayarta da ke Ringing taga Abu Sideeq ne ke kiranta, da sallama ta amsa yace “Hajajju, ya kike?” Daria tayi tace “Lafia lau Alhaji bu Sideeq” yayi daria yace “wallahi Baba ya aiko ni wani Gida a Tudun Matawalle, har na kawo sak’o na tuna Unguwar fa kike, niko nace ba zan bar Unguwar ba sai na ganki sanyi idona”.


Tayi daria tace “rigima, kai da zamu hadu da kai gobe?” Yace Uhm Uhm, ban yarda ba, ni gaskia ki mun kwatance, in zo mu gaisa, ko 10mints ba zamu wuce ba donAllah don Annabi”.


Bata so yana mata magiya, tace “to sarkin Magiya, ka tambayi Gidan Alhaji Ali Zaki, in kazo ka kirani” yace “to shikenan”.


Aiko da kwatancen ya k’araso Gidan Ali Zaki, don gidan a Unguwar Tudun Matawalle ba 6oyayye bane.
Kiranta yayi yace mata yazo, tace to gani nan zuwa, hijab dinta ta saka ta shiga dakin Aunty Aseey tace “aunty bari in dan gaisa da dan makarantarmu, gashi wai yana waje”. Daria tayi yace “ke dai ko dan samrayin ne?” Labiba tayi daria tace “haba dai” ta fita.


Baki Gate ta sameshi, ta mishi alama da ya karaso kofar gidansu, ya dan tako ta murmushi dauke a fuskanshi.


Ko gaisawa ba su kai

Please Login or Register in order to submit comment